Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yana gama katsewa  ya juya  ya  nufi  cikin hotel  din   Inda   wani Kiran ya shigo bai dauka ba har sai daya shiga  d'aki,  yana   shiga d'akin ya  d'auka   " hello ! jaguwa   ya fad'a a hankali daga can bangaren  enamdi  Sunday yace "hello how are you doing  my  friend  ?"am fine inamdi   jaguwa ya fad'a idanunshi  na  kallon Inda tanweer ke kwance ."

"daman na kiraka ne akan sakon dana turo maka d'azu  hope kaga sakona ? "Bangani  ba me sakon ya kusan ?   gobe  akwai  makudan kudaden da za'a shigo  dasu  murtala  international airport wani abokin
mai gidana   ne  alhj aminu zai yi  harka shine  nace  na sanar  daku   jaguwa yay murmushin gefen baki yayi "infomer " daga can bangaren enamdi yayi murmushi yana tsotsa keya ya cigaba da mgn " Kuna  shigowa office din dake kallonku  nan office dinsa yake  dan Allah kuyi aiki da fasaha kmr yadda kuka saba  kar a samu matsala  domin  aikinku  akwai hatsari sosai  any singul mistake komai  zai  iya faruwa saboda jami'an tsaron dake gurin "you don't have to worry  inamdi komai zai tafi dade  aikina dana  d'auki tsawon lokaci Ina yi   bana tunanin akwai matsala idan ma  matsalar tazo nasan yadda zanyi handover  din komai jaguwa ya qarasa  maganar yana sham kamshi kmr yana gabansa  ."
"yauwa friend ai Ina alfahari da Kai  sai maganar percentage dina karka  manta  kasona yana nan kamar da dai ko ?"    ai  muna da  cika  alkwari  inshallahu sosai I bet you wannan karon ma  zakaji dadin muamula damu zamu baka kaso d'aya cikin uku  " to to shikenan  na  gode sosai inamdi ya  fad'a "ni ne da godiya  ". Inji cewar jaguwa ,alright bye thanks yana  kokarin  katse wayar wani Kiran ya shigo haka yayita receive calls na tsawon lokaci  madadin ya koma gurinsu jabir  su cigaba da holewa sai ya karasa kusa da tanweer ya yaye bargon  da  take ciki ya shige jikinta ya lullubesu yana  jin  wani  irin abu  na yawo a gbdy ilahirin jikinsa wanda ya haddasawa qirjinsa tsananta bugawa da tsananin sha'awa  hannunsa  d'aya ya d'aura akan ruwan cikinta  yana  lumshe sexy eye's dinsa yana sauke numfashi  cikin   kankanin  lokaci bacci  yayi awon  gaba dashi ."

*****"
bangaren  Zahra kuwa daren ranar   kasa bacci tayi  tana  zaune cikin tsananin tashin hankalin data tsinci kanta dan gbdy ta kasa runtsawa data runtse idanunta da zumar bacci jaguwa take gani tare da yarinyar da bata san ko sunanta ba , daf da asuba  bacci ya  fixgeta a matukar  firgice  ta farka ta  zauna  tana haki , jikinta ya d'auki zafi kmr garwashin  wuta  tsinuwa kuwa  ta  tsinewa yarinyar  yafi sai babu adadi  daga  karshe ta rushe  da  matsanacin  kuka "wayyohhhly  Allah   naci amanar  kaina ,  na yaudari  kaina dana d'auki  soyayyar duniya na daura ma Adnan  kuka  take sosai har da shesheka, bazan taba barinka haka ba sai na tabbatar da na kawar da hankalin  kowace mace akanka tsam ta sauko daga kan katifa ta jingina jikinta da bangon d'akin ta runtse idanunta masu zubar da zafafan hawaye masu zafin gaske tana Neman mafuta.
wata zuciyar na bata shawarar ta hakura dashi  yayinda wata zuciyar ke karfafa mata gwiwar  tabi kowace hanya dan ta mallaki jaguwa  sosai tayi zurfi cikin tsananin tunani da tashin hankali  ,babu wacce tazo mata sai  kawarta   blessing da suka had'u  a shurem  blessing yar asalin edo state  ce akwai shakuwa mai karfi a tsakaninsu blessing ta sha bata shawara ta dinga binta zuwa garinsu idan zata domin ta had'ata da manyan bokaye  dan ta qara samun d'aukaka a harka karuwanci amman taki naunayen ajiyar zuciya ta sauke na samun mafuta dan kuwa tasan blessing zata taimaka mata tun da asuban  fari  ta  kirata tana kuka ta sheida mata halin da take ciki  take blessing  tace  "ki  shirya kawai  ki zo muje garinmu na gode blessing ai muddin kika min wannan taimakon bazan taba mantawa dake ba  "karki damu zahra ai wannan ba wani abu  bane amman Ina tabbatar miki muddin na Kai ki gurin malamai sai yadda kikayi da  jaguwa  sai ya zamo tamkar  bawanki  "na gode na gode ",Kai haba Zahra ai mun zama daya tuntuni kece dai baki d'auki hakan ba ki shirya mu hadu a iyanapaja  dan  Ina royal  stream  hotel nan kwana zan k'arasa na siya mana ticket kafin kizo "okay sai nazo  cikin saurin ta soma shirinta  tana jin sanyi da natsuwar zuciya."

Mika  jaguwa yayi  had'e da salati Ya  sake  kwakumeta tsam  ajikinsa yana sauke  numfashi a hankali kmr bazai bud'e Idanunsa ba amman dole ya bud'e sakamakon wayarsa dake Kiran sallah alamun lokacin sallah  yayi  ya bud'e tsumammamun idanunshi ya kunna wutar d'akin wanda yasa ta d'an motsa tana shigewa jikinsa hade da d'aura hannunta akan chest Kuma daidai nipples dinsa sauri d'auke numfashi yayi gabansa na faduwa  yayi shiru na tsawon lokaci yana tunaninta abubuwa dayawa akan yarinyar ya d'an dade kwance idanunshi biyu sannan ya  cire hannunta a chest dinsa ya sauko a natse ya karasa Inda wayoyinsa suke ya d'auki daya yana dubawa karfe bakwai saura na safe bai so  wannan lokacin ya taddashi a hotel din ba shi daya so tun asuban fari ya bar hotel din Kai tsaye bayi ya shiga ya fara da sakarwa jikinsa ruwa sannan ya dauro alwala ya fito ya saka kayansa ya Kalli gabas ya tadda sallah byn ya idar ya mike ya Isa Inda take kwance ya Kai hannuwansa tsakiyar kafafunta yana shafawa a hankali ta bud'e idanunta sakamakon jin damshin ruwan hannunsa na ratsata idanunshi cikin nata yace "tashi kiyi sallah lokaci na tafiya ta janyo bargo ta lullu'be jikinta sosai dan babu komai ajikinta  muryarta can kasa tace "okay  ka  miko min  towel na d'aura "Dan Allah malama  ki  tashi kije dauka karki bata min lokaci  ya k'arasa maganar a fusace  shagwabe fuska tayi kmr zatayi kuka  "babu komai ajikina fa tsaki yaja ya mike ya janyo towel ajikin kofar bayi ya jefa mata  a fuska  ta d'aura ta   soma k'okarin  saukowa  "kiyi sauri please Ina da appointment ya fad'a kwayar idanunshi na kanta  bata ce Komai ba ta nufi bayi yabi bayanta da kallo yana kallon every step of her komai nata dabam  ne ta had'u sosai ilarta dai rashin kunya har ta  shige bayi idanunshi na kanta  itama sai data yi wanka sannan ta dauro alwala ta fito a lokaci da yake waya da anas "karka damu ku bani minti ashirin yanzu zaku gani murmushi yayi yace "Kai anas me yasa ka fiyye damun kanka nace maka ba abinda kake tunani bane  shikenan koma dai menene ba abinda kake zato  bane  ya katse Kiran ya kira ammina Inda yake sheida mata Yana da aiki me mahimmancin da zashi shi da abokan aikinsa yana bukatar adduarta"Allah ya tsareku yasa ayi aiki cikin nasara amman dan Allah kabi a hankali kasan Kai ne rayuwarmu sannan  da zarar ka kammala da komai kazo
naganka karka ce sai karshen sati zaka zo gbdy "karki damu ammi inshallahu bazan Kai ba me zan taho Miki dashi ?".Shiru tayi  tana tunanin kafin daga baya tace "komai ka kawo amminka zatayi farinciki murmushi yayi yace "shikenan my happiness murmushi tayi daga bangarenta ta sake Aiko masa da addua komai dare idan na dawo zan kiraki karki yi bacci har sai Kinga kirana kinji ammina  tace "to Adnan inshallahu zan jira kiranka   sun d'auki  minti biyar suna waya har da kannensa ,sanda tanweer ta kammala shirinta taja ta tsaya tana kare masa kallon tsab  yana matukar burgeta yadda bai wasa da lamarin mahaifiyarsa  da kannensa a dan zamanta dashi ta fahimci yadda yake mugu mugun son mahaifiyarsa har sanda ya k'araso gareta ya riko tsintsiyar hannunta tana can duniyar tunani   kumatunta ya ja kadan tayi firgib  ta dawo natsuwarta tana sauke ajiyar zuciya  tsurawa juna idanu sukayi batare data ce masa komai ba
ya  nufi hanyar  fitowa daga d'akin daita tana  biye  dashi ."

Yana  fitowa haraban hotel din idanunshi suka ci karo da motar alqali  murfin motar a bude  wasu mutane na tsaye suna duba cikin motar ,sai lokacin ya tuna da yasa a tsare masa shi ,Kai  tsaye gurin motarsa ya nufa ya bude wa  tanweer gaban mota ta shiga  ta zauna ya rufe ya zagaya ya shiga bangaren direba ya shiga ya zauna ya tadda motar yana fitowa ya sawa motar wuta kamar Wanda zai tashi sama "kabi a hankali please  Ina matukar son rayuwata  domin  tana da matukar mahimmanci ga iyaye saboda nice duniyarsu  "Ina  da mahaifiya da kanne day day har guda uku  mafi soyuwa a zuciyata bazan so suyi  maraicina ba bare ki fada min  maganar banza yayi mgnr a tsawace yana dukan stearing motar shiru tayi tana zance zuci kafin daga bisani ta motsa  labbanta  a hankali  "kana son mahaifiyarka  da kannenka   sosai  ?" tayi maganar tana kallonsa da gefen Ido da kmr bazai yi mgn ba sai dai mahimmancin su ya wuce ya banzatar da  amsar  dan haka yace "kwarai  kuwa  ina matukar son mahaifiyata  da kannena  so na  gaskiya  son da bana Jin akwai wani mahalikin da yake wa ahlinsa "Amman shi ...."  maid your thought   karki  sake  furta komai akan  ahlina  ya fad'a yana  cigaba da murza stearing ,dole taja bakinta tayi shiru ".

cikin kankanin lokaci ya k'araso gida  Kai tsaye bangarensa ya wuce da tanweer ta tsaya tana dubansa "ki kwanta ki cigaba da baccinki nasan bai isheki ba "batun komawata  gida fa ?"zan maidake amman ba yanzu ba  ki bani lokaci tayi kicin kicin da ranta kamar wacce aka aikowa da sakon mutuwa  "gsky nifa na gaji wallahi gida nake bukata idan baka yarda ka maidani ba  zan bi ta kowani hanya na bar gidan nan  "ki gwada ki kigani idan hakan abu ne me sauki yayi mgnr tare da yin  shiru yana dubanta  dan tuni idanunta sun cicciko da ruwan hawaye "ban San me yasa kake min haka ba ,idan km kasan kana da dalilin rikeni ka fad'a min nasan zaman da nake yi amman bawai ka rikeni ba alhalin ni din ba muharamarka bace  ta k'arasa maganar tana jan numfashi da danne kukanta tabbas  jikina na bani akwai  sirrin da  kake boye min meye shi  Ina son sani ?".Tayi taku daya  biyu ta qaraso gabansa qirjinta na dokawa da matsanacin karfi ta cigaba da magana a natse zuciyarta na rawa "zuwa yanzu ya kamata ka sanar dani menene shi abinda kake k'okarin  boyewa " take jikinsa yayi sanyi kmr Wanda aka jefa cikin kankara "zuciyata ta fara jefo min abubuwa masu wuyar misaltuwa akanka  sai dai na shirya jin koma menene ta k'arasa maganar tana kuka dan ta kasa rike kukanta ."

ya Kai hannuwansa duka yana  qokarin zagaye kugunta ta zame jikinta  ta koma bakin gado ta zauna ta kife Kanta akan cinyarta  tana cigaba  da  kukanta ya k'araso ya janyo stood ya zauna a gabanta ya riko hannunta daya cikin nasa ta d'ago runannun idanunta ta zuba masa tana sauraron abinda zai ce sai daya furzar da iska mai zafi daga bakinsa sannan ya fara magana a natse kmr me koyon mgn  "kunnewanki  bazasu iya Jin dalili
ko sirrin dayasa nake rike dake a gidan  ba , hankalinki bazai iya dauka ba wallahi zuciyarki zata buga idan kikaji mafi alkhairinsa ki bar wannan maganar "na bar wannan maganar saboda me byn kana rike da rayuwata ka tsareni ka hanani naje ga iyayena alhalin suna cikin damuwar rashina ta k'arasa maganar tana fixge hannuwanta ya sake riko hannuwanta da sauri  "shikenan ki bani  lokaci kad'an  nasan dai bazaki sake d'aukar lakacin da kikayi tare dani  ba a gidan  nan ".  ya qarasa mgn Yana  goge mata  hawayenta dake tsiyaya a idanunta  tare da yin shiru yana  kallonta itama shi take kallo  zuciyarta  na zafi "to shikenan amman kayi min alfarma ka bani waya  Ina son Jin muryar iyayena ,Ina kwadayi jin muryarsu dan Allah karka ce a'a".

" ya  mike  tsaye yana cewa  "zanyi  nazarin  akan haka  yana gama fad'ar haka ya fita daga d'akin ta kwanta sharaf  akan makeken gadonsa tana kuka tana  tunanin yadda zata bar gidan  ta kowani hali .Kai tsaye d'akin ajiya makamansa  ya nufa Inda ya iske  abokansa  da yaransa suna zaman  jiransa a hankali  ya shiga yi musu bayanin Inda kowannensu zai tsaya da zarar sun Isa  airport ya d'auki sama da awa biyu yana  musu  bayanin har sanda  karfe  goma shabiyu  ta buga  ya d'ago yana duba agogon dake d'aure  a tsintsiyar hannunsa  a natse ya d'auke kyawawan idanunshi ya d'aura akan   Scorpio tare da bashi  umarni  "kaje ka siyowa  tanweer  abinci ya lumshe sexy eye's na second biyu sannan  ya Bude ya  jiyo ya Kalli  eku "Kai  Kuma  kaje ma'ajiyin  kudi ka diba ka  siyo kayan  d'anye abinci da duk abinda kasan za'a bukata na abinci ka tabbatar ka siyo "okay boss ".
gbdy  abokansa suka zuba masa Ido kawai suna kallonsa cike da tsananin mamakinsa " kamil ne yayi karfin halin tambayarsa "me za'a yi da  d'anye abinci  Kuma ?""Wa wannan  yarinyar ne ya bashi amsa atakaice yana furzar da iska , duk da  yaki  yarda da  son yarinyar  yake  amman su sun fahimci  matakin soyayyar  da  yakewa yarinyar , soyayya ce me zafi  da  wuyar bari, soyayya ce da mutun bai Isa ya iya barinta ba  cikin dadin  rai    " jaguwa  amman dai ...." saurin  d'agawa  anas  hannu yayi  saboda yasan  me  zai fito daga bakinsa "ya zaka katseshi ka barshi yayi magana mana ?".bazan barshi ba dan nasan maganarsa  iska ce da shirme  ya fad'a yana runtse idanuwanshi tare da shafa sumar kanshi  . kamil yace "kenan mu din yan iskanka ne sannan mashiririta  ? tsuke bakinsa yayi yana kallonsu d'aya byn daya yana girgiza musu Kai  alamun a'a "haka ne mana jubi ya fad'a "ada Kai din mai son a fad'a maka  gsky ne amman me yasa yanzu  duk ka canza bafa ayi haka damu  ba ,ba'ayi damu zamu d'auko yarinyar mutane mu ajiyeta ba meye ma amfanin rike musu yarinya idan kana son yarinyar why not ka fada mana mu san abunyi ?"no no jubi  Sam babu wannan a raina ta ya ma zan d'aukarwa  kaina soyayya  soyayyar ma da diyar minster Sam Sam hakan ba me yiwu bane ?
"me yasa zaka fadi  haka byn zuciya gareka kamar  kowani  halitta "kunga dan Allah ku bar maganar nan haka, bama zan iya wata soyayya ba a yanzu  kawai dai Ina gudar mata  sharrin wannan mutumin ne  me  Katon ciki  ban San wani tuggu zai sake had'a  mata ba  Ina tausayinta Ina Jin kamar zai cutar daita ne Idan na mayar daita  ",saboda zunzurutun qaunar da kake  mata  ba  shiyasa kake Jin tausayinta ",oh my god jubril wai ya kuke min haka ne ?"idan Ina son yarinyar nan wallahi zan fad'a muku dan bamu Saba boyewa juna komai ba , ku yarda bana son yarinyar nan " shiru sukayi  suka cigaba da kallonsa  ba dan sun yarda dashi ba  har ya juya  ya kusan kofar fitar  sannan yace " eku   Scorpio  "zaman munafurcin  me kukeyi  dan Allah ku tashe kuje kuyi abinda na sakaku bamu da lokaci "  da sauri suka mike suna shafa kansu  ."

       
Cikin  takun  Isa  da Jin shi wani ne  ya nufi  haraban   gidan  hannunsa d'aya soke  cikin  aljihun  wandonsa   eku da Scorpio   suka  fice da  sauri  suka nufi Inda  ya aikesu , yana  nan tsaye yaga fitowar   tanweer   tana  karewa haraban   gidan   kallo  fuskarta d'auke da   murmushin  jin dadi ba kamar   d'azu   ba ,  a kallon   da  yake   mata    ya   lura   hankalinta   na   kan   shukokin     gidan    ne  ,yana  kallonta  ta   cigaba    da    takawa    a hankali   har   ta  Isa   Inda   shukokin suke  tana  shafawa   a hankali  tana lumshe idanu , a  natse   ta  karya  kwana  tabi hannunta  na   hagu  ,cike  da natsuwa ya biyo bayanta , bata tsaya koina ba sai  gurin   fararen   fure  dake shuke   cikin  ruwa  har  lokacin  fuskarta da murmushi , ya  k'araso  ya  tsaya  a bayanta   yana  sauke numfashi, saukar  numfashinsa  yasa ta juyo  a  tsorace  har qirjinta na ta'ba  nashi  saurin  d'auke numfashi yayi qirjinsa  na tsananta  bugu ,  ganin  shine  tsaye  yasa  ta sauke  naunauyen  ajiyar zuciya  sannan  ta juya ta cigaba da kallon fararen  fure  muryarta a sanyaye  tace " ina son fararen fure ko zaka tsinko  min? ta fad'a tana duban Inda yake  tsaye  har lokacin  hannunsa na  soke cikin aljihunsa " kina son fure ne haka ? ya tmbyeta  yana  kare  mata kallo  tsab " sosai Ina qaunar fararen  fure arayuwata  ya  qara taku biyu  yayi kusa  daita sosai yana cewa   "yarinyar da nake so itama  tana matukar son fure " qirjinta ne yayi wani irin bugawa da karfi , taji saukar maganarsa  kamar  saukar aradu ,zafi ta dinga ji a qirjinta tamkar ana diga mata ruwan dalma  nan take ta nemi natsuwarta ta rasa    idanunta na kan furen tace "wacece ita yarinyar da kake so ? ta tambayesa  kwayar idanunta cikin nashi ,bai  bata  amsa  ba duk da ya lura da canzawar da tayi a lokaci  daya  sakamakon  jin yana son wata  dariya taso  subuce  masa dan  yadda  ta had'e rai abun babu sauki kace shi din mijinta ne .

ranta a  'bace ta soma tafiya zuwa wani  bangaren "ke   Ina   zaki  ?itama banza  tayi masa kamar yadda yayi mata  "ba dake nake magana ba kina jina ? still banza ta masa " ki   koma  ciki  kar  na   sake  ganin  kafafunki  kin fito  haraban  gidan nan bare nan. "dan   me  yasa bazan fito ba ? ta fad'a a fusace  tana Jin wani irin zafi mara misaltuwa sannan   ta juyo ta fuskancesa  fuskarta a had'e tamakr ba itace take murmushi a sakwanin da suka wuce  ba , ta rasa dalilin wannan so da take masa  , soyayyarsa me  karfi ce  agareta  ,bata ta'ba sanin  tana  da  kishin irin haka ba sai yanzu daya  furta  yana  son wata ba ita ba  yace baya son zahra sannan baya sonta to wacece wannan daya furta da bakinsa ?   Ido  cikin Ido suke kallon cikin kwayar idanun  juna  kamar ta rufesa da duka ko zata samu sausauci ,k'okarin danne kishin tayi ta sanyawa jikinta  jarumta   "ko bazanje koina ba ka barni na dinga  fitowa Ina ganin fararen  fure tayi mgnr kmr zatayi kuka ,bai ce mata Komai ba   ya riko tsintsiyar hannunta ya soma tafiya daita bai tsaya a koina ba sai d'akinta ya bud'e kofar ya turata "iya nan na yarda kiyi rayuwa aciki ko falon gidan nan ban yarda ki fito  ba  idan Kuma kikayi kuskuren fitowa zaki  ga abinda zan miki ya k'arasa maganar tare da  ya janye kofar ya rufe garam , ita duk wannan abun  da yayi  bai dameta ba akan zance budurwa da  yayi  mata shi yafi komai ta'ba zuciyarta  da d'aga mata hankali, tsaki taja yafi sau goma ajere  " Allah! Allah !! ka tsi ...." shiru tayi ta kasa tsine masa shi da budurwar da yake so  ta koma karshen gado ta zauna tare da zuba  tagumi  ."

ya  shiga d'akinsa  ya cire kayan jikinsa ya shiga  wanka ya tsaya  shiru cikin bathtube ruwa na tsiyaya a sansar jikinsa  yana tunanin maganar abokansa  akan yarinyar "duk suna min kallon d'an soyayya alhalin ba haka bane acikin zuciyarsa ," taimako ai  ba soyayya ce?  ya tambayi kanshi  ya  d'an dade ruwa na sauka ajikinsa sannan ya fito kugunsa d'aure da farin towel wanda bai wuce cinyoyarsa ba   byn ya goge jikinsa
ya shafa body lotion yayi cumb din sumar kanshi ya soma shirya kansa cikin Kanana kaya  riga blue wanda a gabansa  aka rubuta  polo  1967  yayinda wondon  da canvers din kafafunsa suka kasance ja ,kansa sanye da facing cap ja kmr yadda rigar jikinsa  yake , tsintsiyar hannunsa  d'aure da agogon  rolex   ya rufe idanunshi da  glass baki  ya feshe ilahirin jikinsa da turare mai sanyi kamshi, sosai  kyawunsa ya bayyana ya soke hannunsa daya cikin aljihun wandonsa kamar Koda yaushe ya nufi kofar fita,  falon ya dawo Inda ya iske scopio ya dawo bai tsaya bata lokaci ba ya karbi farar ledar hannunsa ya juya zuwa d'akin da tanweer  take ."

 tana Jin shigowarsa amman  taki  d'agowa daga kwance da take  dan wani irin haushinsa take ji ,ya ajiye ledar akan bedside yana cewa  "ga abinci nan ki tashi kici sannan zanje  wani aiki me mahimmanci  zan dan dade kafin na dawo batare data d'ago ba tace "a dawo Lafiya amman dan Allah ka bani waya ". "ki  daina  damun kanki ba waya ba gidan ma zaki bari gbdy  idan lokaci yayi  ya juya ya fara tafiya  cikin hanzarin wannan karon d'akin dake gefen  d'akinsa ya shiga ya jima sosai dan kusan awa d'aya  yayi sautin muryar scopio ya fito dashi "boss komai ya kammala "okay kana iya tafiya   ya fad'a d'akin tanweer  yana cewa "   nasa a kawo  komai na kayan abinci muje kiga kitchen  din ". banza tayi masa taki cewa komai hakazalika taki tashi hatta abincin da ya kawo bata ci ba   ya zuba mata Ido har kusan minti biyar  kome ta tuna tayi zumbur ta mike tsaye tana dubansa  yayi gaba ta biyosa a baya har cikin had'ad'd'en kitchen din ."

a hankali ya dinga nuna mata komai daki daki kitchen  din  very Niet  kamar mace ce ke amfani dashi  babu abinda babu na kayan abinci  komai gashin nan  ajiye   yasa  an  kawo," ki duba ko akwai abinda bai miki ba a canza akawo miki wanda kike so ".  idanunta  da suka canza kala sukayi jazir  tsabar kishi ta d'ago ta sauke su akan fuskar  jaguwa dake tsaye a gabanta  yana kare mata kallo ,Shep dinta yafi komai daukar hankalinsa irin  matan nan ne masu  shep din cocakola   "dan tani da baka tanadin wad'an nan abubuwa ba dan ba sune abinda nafi bukata ba bukatata na .." ".shiiiii ya d'aura yatsansa akan lips dinta yayi kusa kusa daita har suna iya jiyo numfashin juna wani irin tsalle zuciyoyinsu yayi  wanda har sai da hakan ya haifar musu da tsayuwar numfashi , take jikinta ya soma kyarma   rungumeta   ajikinsa  yayi tsam yana busa mata numfashinsa .
 tuni zuciyarta ta karye hawayen kishinsa da kewar gida   ya soma zuba bisa kuncinta ya rungumeta  sosai ajikinsa kamar zai mata numfashi yana shafa gadon bayanta .

wani irin haushi  ne  da bata ta'ba  jin irinsa  ba  ya diran mata a kahon zuciya  ,kullum yana ikararin baya sonta amman ya iya nesanta kanshi daita yana son maidata yar  iskar karfi da  yaji   ta soma mutsu mutsun kwatar  jikinta domin zuwa wannan lokacin   zuciyarta  ban da zafin  kishinsa babu komai aciki ,ganin yaki sakinta yasa ta soma dukan qirjinsa da iyakacin  karfinta amman yaki sakinta  ya kamkameta tsam  yana son yaga karshen karfinta   "Kai dai wallahi mugu ne Kuma azalumi inshallahu yadda kake quntata min wallahi Kai ma sai Allah ya  quntatawa  kannenka ".  cak  ya saketa   yana furzar da numfashin mai zafi  daga bakinsa   idan  akwai abinda ya tsana bai wuce a ta'ba kannensa ko aibantasu da mugun abu ba . ta zube kasa bisa gwiwowinta tana wani irin kuka tare da Kiran sunan iyayenta , muryarsa  a tsarke yace"tan ...."bata d'ago  ta kallesa ba "karki sake sako kannena cikin shirmenki   idan kina son ki zageni kiyi amman kannena karki sake ."
"Dan Allah malam ka min shiru daga yanzu  muddin  baka maidani ga iyayena ba  wallahi na dinga ma kannenka  mugayen fata kenan , ada na dauka ka taimakeni  ne sai dai a yanzu taunina ya  Kashi dabam dabam tare da tambayoyi masu wuyar amsawa "waye Kai Adnan ? Ka fad'a min waye Kai Ina son sani kai din  waye ?cikin sauri ya juya ya bar kitchen din   zuciyarsa na rawa bai ta'ba Jin tsoron wani yasan sana'arsa ba ko sanin ko shi waye  sai yau , bazai iya sheida mata shi din waye ba , zai barta a matsayinsa na me taimakonta  bazai ta'ba yarda tasan ko shi waye ba yana tafiya yana jan tsaki ji yake kmr zuciyarsa zata buga .
ya rufe kofar falon ya fita zuwa  haraban gidan , tuni su  kamil ,anas, jubi, da jabir  da sauran yaransa sun hallara har wasu ma sun shiga mota sun zauna  shi kadai suke jira yana daf da karasowa eku ya  bud'e

Please Login or Register in order to submit comment