Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

masa man gyada ,tunda jaguwa yayi masa duban farko bai sake dago kai ya dubesa ba domin mummunar fuskarsa me saka faduwar gaba ce da firgici.”


Yaja kujera ya zauna agaban kujerar daaka daure jaguwa yana mazurai kai kace wanj gawurtaccen zakin daya nemi abinsa ya rasa ,zuciyar jaguwa ta cigaba dubansa madadin kwayar idanunshi dan kallonsa zai sa ya hadiye zuciya “.
mutumin ya ajiye kulkinsa da karfi akan table jaguwa ya dago yayi duba zuwa ga kulkin dake ajiye akan teburi dake gaban wannan katon mutumin yaji gabansa yayi mugun faduwa yau kam tashi ta kare domin duk wanda aka buga da wannan kulkin to kuwa sai dai wani bashi ba ahankali aka sake turo kofar asp isa ya bayyana acikin dakin da sauri wannna kato ya mike da sauri tare da kamewa
“sir!. ya fad’a yana raba idanu .”

Asp isa ya dubi jaguwa “menene sunanka?”ya fada shiru adinanu yaki magana “yaya sunan babanka ?”ya sake jefa masa wata tambayar sai lokacin jaguwa ya dago yana kallonsa batare daya bashi amsa tambayar da yayi masa ba, kusan minti goma ana jiran aji amsa daga bakinsa amman yayi shiru yaki cewa komai “asp isa ya cigaba da tambayarsa “ko zamu iyasanin wadan da suka dauki nauyiku da kuke wannan taadanci.”
“su wa kenan suke yin taadanci “?jaguwa yayiwa
asp isa wannan tambayar a dake ba zakace shi din me laifi bane shima asp isa shiru yayi dan shima miskilan kansa ne sautin muryar jaguwa ce tasa ya dago ya tsura masa ido “ni ba dan taada bane .”
Shiru asp isa yayi yana cigaba da dubansa gabansa na wani irin faduwa kafin daga bisa ya cigaba da magana “idan kai ba dan taada bane wanene kai “.
still yaki magana ya bashi minti goma yana jiransa amman stil yaki cewa komai asp isa ya ciza lip’s dinsa da karfi aransa yana cewa “wannan tantirin yafishi miskilanci .”
dan haka ya mike tsaye tare da duban wannan katon mutumin “sajan tomy ku tambayesa har sai ya gaya mana gaskiyar abinda yasa suke aikata wannan taadanci da kuma wadan da suke daure masa gindi yana gama fadar haka yasa kai ya fita daga dakin cikin bin umarnin ogansa tomy ya kai hannu ya zari kulki yayi kan jaguwa ya fara buga masa bai ji bai gani tun yana iya kare kansa har ya kasa dan tsabar galabaita da yayi , sai da tomy ya sumar dashi sannnan ya hakura ya barshi ya fice daga dakin.”

A matukar firgice ammi ta farka ta zauna dafe da qirjinta dake dokawa da karfi tamkar ana buga mata guduna ,ta kunna wutar daki ta waiga bayanta ido hud’u sukayi da hally dake kwance a gefenta tana fitar da numfashi sama sama da alamun ma kuka take ganin irin duban da ammi take mata yasa ta kai hannunta daya ta dafe goshinta dan karta lura da halin da take ciki .”
Bata ce mata uffan ba ta sauko daga kan gadon stil tana cigaba da jin bugun zuciyarta inda wayarta ke ajiye ta qarasa ta dauka tana dubawa a tunaninta zata ga missed call’s din jaguwa kamar kowani dare sai ya kirata ko idanunta biyu ko tana bacci sai dai idan aiki ne ya sha kansa , wani lokacin idanunta biyu wani lokacin kuma tayi bacci sai dai tabi kiransa amman yau babu tayi shiru tana jin mummunar faduwar gaba .”

Ta dawo ta zauna abakin gado tana neman layinsa sai dai kira take ana fada mata number switch off ta kira yafi sau goma amman stil abu daya ake fada mata ta daga kanta zuwa bangon dakin tana duba agogo karfe goma ta wuce da wasu mintuna tayi shiru tana tunani can tayi tunanin ta kira number anas shima abinda aka fada mata ana jaguwa shi aka fada mata jikinta yayi mugu mugun sanyi sai dai a fili tace “yanayin aiki ne .”
Ta dubi inda hally take kwance “kinci abinci kuwa .”?
“Ammi bana jin yunwa .”ta fada atakaice tana danne kukanta ammi ta girgiza kai kawai tana cewa “allah ka iya mana abinda bazamu iya ba wanda zamu iyama karka barmu da iyawarmu ka tsaya mana ,
Ammi ta kasa komawa bacci ta mike ta shiga bayinta dake hade da dakinta ta dauro alwala ta fito ta tada sallar nafila har kusantowar asuba ammi na zaune tana kaiwa allah kukanta haka zalika tana neman layinsa .”

*******
Washegari har kusan karfe biyu na rana tanwer tana kwance tana sharar bacci hankali kwance yayinda mumy da dady ke adduar allah yasa idan ta farka ta dawo haiyacinta ,IB ma ya zo dubata yadda iyayenta basu fada masa dalilin kwanciyarta hospital ba haka shima bai tambayesu ba saboda tunaninsa ya fara zuwa wani guri dabam ,dan kafin yazo gurinta hospital daaka zarce da alqali ya fara zuwa kuma yayi masa bayanin komai wanda hakan ya kusan tarwatsa masa zuciyarsa ya tsura mata ido kawai yana kallonta .”
har ya gama zamansa bata farka ba karfe uku daidai ta farka da ihu da fixge fixge likitoci da iyayenta suka rufa akanta sai dai taki yarda kowani likita ya tabata ta bude idanunta sosai ta zauna a tsakiyar gadon marasa lafiya daya daga cikin likitocin dake duty yace “kwantar da hankalinki ki fada mana abinda kike bukata ya fadi haka ne saboda ya fahimci ta fara fita hankalinta “bana son komai wanda nake so baba ya kai shi qara gurin hukuma dan su kashesa kuma sunyi nasarar kashesa alhalin yasan ina son shi ,”na baya masa ina son shi ina son shi amman yaki barin muyi aure me yasa yayi min haka ?” bani yanci ne akan abinda ya shafi rayuwata ? ta qarasa maganar tana sauke wani irin numfashi da karfi “ku fad’a min fadawa soyayya laifi ne?.”ya girgiza mata kai cikin tsananin mamakinta domin bai ta’ba tunanin alamarin soyayya zai shafi lafiyar ta ba .”


“Please tanwer karki maida kanki mahukaciya bayan da hankalinki why are you like this”?ta bude ta qara idanunta sosai ta kalli sister sabera sannan ta dauke idanunta akanta ta dubi ruky “ruky ina jin yunwa ki kira min adnan ya bani abinci yunwa nake ji sosai ta matso kusa daita “naji tanwer zan kirasa amman kafin nan bari na baki abinci kici da hannuna .”

“Ruky ….”.!

“Karki damu zan kira miki shi kuma zai zo amman kafin nan kici abinci daga gareni “ta fad’a kamar zata yi kuka “nashi kawai nake son ci abincin hannunsa nake so, ku kira min shi nan ta runtse idanunta tana tuno adnan dinta yanayin jikinsa irin rayuwar da sukai yi yanzu ace ya mutu ya barta da tarin soyayyarsa da sauri ta bude idanunta ta mike zata fita daga dakin da sauri suka yo kanta gabadaya suka riketa har iyayenta “ku barni gida zani na hakura bana son komai yanzu bana son ganinsa shima yana da sanya hannu gurin mutuwarsa ,nace masa ya daina aikin fashi yaki ,fashi ba sana’ar bace ko sana’ace ?” ta fad’a tana kallonsu daya bayan.”

ta tsuguna tare da fashewa da kuma suma duk suka tsugunawa agabana ta suka fashi da kuka tanwer ta rasa abinda yake mata dadi , mumy ta rasa ya zatai da alamarin tanwer kalmar inna lillahi wa inna ilaihi rajiun kawai take furtawa nan ta mike taje ta kawo mata abinci tare da ruwa ta kawo mata bata ‘bata lokaci ba ta hau cin abinci bata ji bata gani alamar tana tare da jin yunwa mai tsanani bayan ta gama ta kwanta agurin tana cewa “dan allah ku kiramin adnan na gansa can kuma sai ta rufe idanunta da sauri tace “karku kira shi bana son ganinsa yana bani tsoro har bacci ya dauketa cikin wannan halin .”
💗💗💗💗💗💗
KUSKUREN BAYA
     💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗

PAID BOOK

WRITING BY
AYSHA .A BAGUDO


WATTPAD @HAUESH

bismillahirrahmanirrahim

Wannan  littafin na kudi ne  mai bukata karanta shi  ya tura 500 ta wannan  account number din  1438775094 Aishat Abdullahi Access bank ,Idan an tura sai a turawa wannan number+234 703 534 8686alert  domin tabbatar da an tura ko wadan nan number's din 09136918331 or 08059623096 Idan Kuma vtu za'ayi  sai a tura ta wannan number 09136918331 domin sauraran littafaina a tuntubi Channel dina ta Hausa bakwai.

🅿️47


……Mumy tasa tanwer gaba tayi kuka har taji babu dadi dady kanshi ya kasa jurewa halin da tanwer take ciki  gabadaya ya daura laifin Akansa sai yana ganin kamar shine silar fad'awarta cikin wannan halin shima tsugunawa yayi a gabanta yana goge hawaye yana jin babu dadi aransa "ina ma yaron bai da wannan katoton mugun tabon a rayuwarsa?".
"Ina ma wani hali garesa ba fashi yake ba? ".
yanzu yana shiga cikin maganar reshe ne zai juye da mujiya cewa za’a yi yana cikin wadan da suke mara masu baya ,mumy da dady sunyi kuka sosai kafin daga  bisani   likitocin suka dauketa cak tamkar wata jaririya saboda rashin nauyi suka d’aurata akan gado
sannan suka fice daya bayan daya daga dakin cike da matsanancin tausayinta ."

Hally ma rufe kanta tayi a dakin ammi ta sha kukanta ta koshi babu wanda ya sani in ta gaji sai tayi ta addua wani irin radadi son mijinta take ji yana ratsa sansar jikinta tare da jin tausayin kanta yadda abubuwa ke tafiya yana matukar bata tsoro nan ta zaro wayarta ta bude hotonsa tana kallo wanda kullum anan take samun natsuwa da karfin zuciya da sanyi rai murmushinsa na kwantar mata da hankali sai taji ta tsinci kanta da yi masa murmushin .”

Wunin ranar da wannan tashin hankali  mumy da dady sukayi shi tanwer da zarar ta farka zata fara ihu tana  fixge fixge tana fadar abu daya , hakan yasa lokitoci suka fahimci ba wai da gangan takeyin haka ba hankalinta ne ke  kokarin barin jikinta , dole kuma su tashi tsaye domin  ganin hakan bata kasance ba dan irinsu da zarar anyi sakacin barin sun fita kamar yadda take kokarin yi suke qarasa zarewa gabadaya."

Bayan awa daya da fitar  tomy daga dakin  babu wanda ya sake shigowa  shi kuwa jaguwa sanyi sanyin asuba ne dake shigowa ta window yana shiga ilahirin jikinsa ne ya farfado dashi  ,banda  numfashi sama sama babu abinda yake fitarwa babu wanda yazo zuciyarsa kamar mahaifiyarsa da anas da tanwer ,gara ma amminsa da tanwer yasan suna guri daya kuma duk runtsi duk wuya laifinsa bazai ta'ba shafarsu ba amman halin daya baro su anas fa ba wanda zaa iya jura bane . “

Bai sake ganin kowa acikin ma'aikatan polisawa ba sai da yammacin kamar jiya wani murdade me  irin siffar jikinsa ya kutso ya shigo cikin dakin shima hannunsa rike da makeken kulki kamar na mutumin jiya yayinda dayan hannunsa ke rike da wata katuwar tocila me shegen haske saboda tsananin duhun dakin koda rana duhu ne babu haske ."


wani irin  kallo yayi masa yana mazurai "na shiga uku wannan ma da alamun duka zai sha agurinsa?"
ya fadi haka acikin ransa sai dai a zahiri bai nuna gazawarsa ba ,ya kafesa da kunburarun idanunshi jaguwa bai ankara ba yaji saukar wannan kulkin a damtsensa inda harbi ya samesa wani irin qara ya saki guda daya me karfi yana dafa daidai gurin tare da dukar da kanshi yana ciza lips dinsa na kasa da karfi dan shi kadai yasan irin zafin daya ji ya ziyarci ilahirin jikinsa."
Mutumin ya tako har inda ya matsa duke da kanshi ya daga habarsa "zaka mana bayanin kanka da kuma wadan da suka dauki nauyin wannan fashin da kuke yi ? shiru ne ya biyo baya "baza kayi magana ba sai na karairayaka "?ya fada yana nuna masa jikinsa cikin ciza lip's dinsa ya shiga girgiza masa kai alamun bazai fad'a ba ".


Police din yayi dariya me kama da sautin kukan saniya yace "lallai taurin kanka ya burgeni amman kuma kana tare da katuwar wahala idan kace bazaka fadi inda sauran abokan aikinka suke ba sannan da wadan da suka dauki nauyunku ba ."Ya kuma gyara zaman kulkin dake rike a hannunsa fuskar nan tashi ko alamun tausayi babu rashin mutunci da rashin imani ne kawai ke tattare acikinsu."
Jaguwa ya runtse idanuwanshi wadan  da suka yi luhu luhu saboda tsabar azabar da suka shiga sakamakon shirga masa shirgegen kulkin da mutumin jiya yayi ga kuma na yau wanda ke nuna alamun zai fi na jiya rashin mutunci dan daga ganinsa ma kasan bazai yi tausayi ba ko yace da marasa tausayi aka hadashi  ."


Rufe shi yayi da duka har sai daya ga alamun ko hannunsa bai iya dagawa kana ya fice ya barshi shi ba matacce ba kuma babu wani alamun  na mai rai idan ka dauke numfashi dake fitarwa da kyar daga wannan dakin aka kwashesa aka sake canza masa wanj daki na mussaman ,wanda rodikan dake cikinsa sun kai girman muciya."
Wannan dakin daki né na mussaman domin adana masu manya manyan laifuka irin su jaguwa da irin wadan da ake biyansu kudi su kashe mutane suka watsa shi kamar kayan wanki lokaci daya ya sake sunewa allah ne kadai yasan adadin awanin daya dauka cikin wannan halin amman ya kudurcewa ransa duk runtsi duk wuya bazai furta komai ba koda kuwa zai mutu ne ya gwamaci mutuwa daya furta inda sauran abokan aikinsa suke ."


Mumy na zaune a gefen gadon da tanwer take kwance ta zuba mata ido kawai tana kallonta hawaye masu zafi na gangaro mata sakamakon sambatun da tanwer din ke yi cikin zubar da hawaye tace “ki dauki qaddara tanwer adnan bai mutu ba har yanzu yana hannun hukuma idan ma mutuwa yayi kisa aranki allah ne ya baki adnan idan kuma ya karbi abunsa sai ki karbi qaddara daya daura miki .”cike da matsanancin mamaki mumy taji sautin muryarta cikin tsananin tashin hankali “haka né mumy nayi Imani da allah can kuma ta birkice,me yasa allah zai min haka “?wani irin zunubi na aikata da allah zai jarabeni da rashin adnan rayuwata ?” rayuwata né adnan ,duniyata né adnan ki kira min shi mumy bamu tsara cewar zai mutu ya barni ba ,zan bisa duk inda yake ta qarasa maganar tana kokarin durowa daga daman gadon mumy tayi wuf ta rikota da iyakacin karfinta ta rungumeta ajikinta tana wani irin kuka mai ta’ba zuciya gabadaya acikin kwana biyu duk ta fita haiyacinta.”

Doctor muyis yayi matukar jin mamakin wanda tanwer take kokarin haukacewa akansa d’an fashi ne da kasa ta dade tana nema “lallai karfin soyayya ya zarta kowani karfi da asiri tasiri ajikin dan adam .”bayan ya shiga inda take ya duba kafiyarta ya koma office dinsa ya shiga bincike game da ciwo mai kama da tabin hankali dake kokarin kama tanwer ,da kyar yayi nasarar gano abinda zaayi a shawo kan natsalar bayan ya gano komai ya tara sauran likitocin da suke aiki tare domin su tautauna ,a wannan daren ma shima kamar daren jiya ya kasance agurin iyayen tanwer da likitoci dake aiki a hospital din domin kuwa kwanan wahala sukayi sakamakon bakinciki , bacin rai ,kewa , dacin zuciya,hauka tare da fixge fizgen zata tafi gurin adnan dinta .”

Gari ya dauki zafi ko ina ka gilma magana biyu ake yi jaguwa dan fashin da hukuma ta dade tana nema ya shiga hannun da kuma labarin diyar minister ta samu tabin hankali wasu suce shaye shaye ta fara bai karbi kwakwaluwarta ba yayinda wadan da suka san gaskiya suke fadar albarkaci bakinsu .”
Haka yan gulma da tsegumi da kuma wasu daga cikin matan abokan minister suka dinga zariya zuwa hospital sai dai mumy bata barin a ganta domin tasan abinda zasu gani dabam abinda zasu qarar dabam ko hajiya basera basu yarda sun fada mata gaskiyar musababbin ciwon tanwer ba ta boye mata gaskiyar alamari d’an matsalar ba kowa né zai fahimta ba kuma duk zuwan da take bata cin sa’ar samunta ido biyu bare tayi hauka agabanta .”

Bayan kwana biyar

Dady yayi nasarar ganin kwararun likitoci da doctors muyis ya gayyato daga hospital dabam dabam tare da neman shawarasu ciki kuwa har da sadiq Kanin jaguwa wanda kusan shi yafi kwarewa akan irin matsalar tanwer sai dai alokacin bai samu damar amsa gayatar ba sakamakon tafiyar dake gabansa zuwa abuja ,tunda likitoci suka fara magana akan abubuwan da zaa fara mata domin gano ta inda zaa shawo kan matsalar dady ke dubansu yana sauraronsu one by one mutun na karshe ne yayi bayani kamar haka wanda yasa jikin dady ya qara yin sanyi “ firgici da tsananin tunanin da yayiwa brain dinta yawa ne yasa take qokarin losing momery dinta amman a hankali da zata samu abinda take zafafa tunaninta akanshi zata dawo normal .”
Naunayen ajiyar zuciya ya dady ya sauke dan yasan inda matsalar take ,ahalin yanzu ya sadaukar da komai kuma yayi Imani adnan shine rayuwar diyarsa shine farincikinta, kuma tabbas zata iya mutuwa ko haukacewa muddin babu shi ,dan haka ya tatttara komai ya sake watsarwa ya dauki dukkanin wata kulawarsa da lokacinsa ya mayar akan rashin lafiyarta tare da qoqarin ganin yadda zai yi ya fito da jaguwa wanda hakan ya janyo hankalin mumy ya dan kwanta dan ita kanta tana tsananin jin tsoro da fargaban tanwer ta haukace ,don yanzu kam ta zama kamar tababbiya tunda kullum cikin kukan son adnan take da son ganinsa take tana ihu tana kiran sunansa amman da zarar ance zaa kira mata shi sai tace bata son ganinsa.”

Tun lokacin da labarin wannan maseefar ta afkawa Ib ya kasa samun natsuwa sannan irin kyawawan halaiyan jaguwa da yaji a bakin jamar unguwar ya qara jin tsanar da yayiwa jaguwa ta kau domin dai ya sake komawa unguwar duba da yadda yaga mutanen unguwar suke kai kawo a headquarter har suna kokarin daukar masa lauya , saboda manya manya unguwar sun zo ba’abari sun gansa ba ,haka zalika zuwan malam mudi biyar sun hanashi ganinsa sun kuma tabbatar masa babu halin da zasu bashi damar shiga koda kuwa da lauya ne dan har lokacin basu samu wata hujar daga bakinsa da zatasa su bada damar a daukar masa lauya ba ”a halin yanzu shi kansa ib ya daina ganin laifinsa sai na mahaifinsa da sauran azzaluman da’aka fito dasu daga gidansa .”

Hajiya basera na zaune a falo tana kallo labarai cikin haka aka soma watso sabin labarai ciki kuwa har dana su jaguwa kamar almara taga hoton mijinta yana zayyono magana tiryan tiryan nan take ta shiga gagarumin tashin hankali mara misaltuwa jikinta na rawa ta mike tsaye zata nufi bangaren ib dake ranar ta kasance lahadi ce yana gida turus tayi sakamakon ganinsa tsaye a bakin kofar shigowa ya harde hannunwansa duka a qirjinsa yana dubanta hannunta dake rawa ta kai tana nuna masa tv “da…..dadyn..” sai kuma ta kasa magana ta cigaba da nuna masa tv.
Ya sauke hannunwansa yana sauke naunayen ajiyar zuciya sannan yayi taku uku ya qaraso inda take tsaye ya kamota ya zaunar daita akan kujerar data tashi shi kuma ya zauna akan center table yana dubanta a tsanake kamar ya zubar da kwalla “nasan komai daya faru umma murna da farinciki ya kamata kiyi zaki rabu da maseefa data dade tana damunki .”girgiza masa kai ta shiga yi tana cewa “mahaifinka ne fa Ibrahim duk lalacewarsa bai kamata ka kirasa da maseefa ba, idan ni na kirasa da hakan kai bai kamata ba .”

“Ya kamata Ummu wannan maseefar tasa naji na tsani kaina tasa naji dama ni din shege ne ,da samun gurbataccen mahaifi kamarsa wallahi gara babu ,
wallahi umma ina tsananin jin kunya cewar shi din mahaifina ne yay shiru yana furzar da iska me zafi daga bakinsa .”
A qalla ya dauki tsawon minti biyu sannan ya numfasa ya cigaba da magana cikin sanyayyar murya “duk tarin qaunar da nakewa tanwer na kasa sake zuwa ganinta ina tsananin jin kunyar abinda dady ya aikata mata ,ina jin kunyar abokan aikina in fact na tsanani kaina “.
Umma na zubar da hawaye tace “hakuri zakayi Ibrhim hannunka baya rubewa ka yanke ka yar dole dai shi din uba ne agareka ni kuma miji ne agareni bai kamata mu barshi cikin wannan halin ba ,zamu daukar masa lauya “what ?”


Ya furta cikin tsananin fushi “lau me Umma ?”
“Lauya Ibrhim yanayinsa da komai ya nuna mahaifinka yana cikin danasani abinda ya aikata ya mike tsaye jikinsa na kyarma tare sa soke hannuwansa duka cikin aljihun wandansa yana cewa”bazaki daukar masa lauya ba haka zalika nima bazan daukar masa lauya ba abarshi ya girbi abinda ya shuka .”
“Haba Ibrahim kar….”
“Wallahi Umma gara na daukarwa jaguwa lauya dana daukarwa dady lauya ya katseta ta hanyar fadar haka yana dubanta ido cikin ido yana gama kallonta bai sake cewa uffan ba ya juya fuuuuu cikin fushi ya fita daga falon bayansa tabi da kallo hankalinta na qara tashi tasan halinsa yana da matukar hakuri amman kuma bai iya fushi ba .”


Bangaren hally ma ta shiga damuwa sosai tana son tasan halin da mijinta da yayanta suke ciki amman babu ta inda zata sani dan haka kullum cikin kuka da tunani take lokaci daya ta zabge ta rame tayi duhu ta fita haiyacinta ,itama ammi ma ta shiga damuwa me tsanani kuma ta yarda ta amince wani mummunar abu ya faru da danta da surukinta a duk inda suke ,”
Tunda wannan bala’i ya faru da jaguwa ammi bata nemi kowa ba sai yau ta kira sadiq ta fada masa komai ,nima ammi naji akwai damuwa ajikina domin tun last week nake kiran layinsa baya shiga haka ma number anas baya shiga amman karki damu ammi zan biyo jirgi yau din nan zan dawo musan abunyi nan take suna gama waya ya soma kokarin siyan ticket .”


Ammi bata ajiye waya ba ta kira diyarta shafiq tace “maza maza tazo tana son ganinta sadiq ya biyo jirgi daga abuja zuwa lagos cikin tashin hankali kai tsaye gidan ammi ya wuto kusan a tare suka qaraso da shafiq suka kulle kansu adakin ammi domin neman mafuta batare da sun bari hasera ta fahimci wani abu ba ,dukkaninsu zuciyoyinsu babu dadi domin kuwa daga dubansu kasan wannan taron ya sha bambam da sauran da sukayi domin kana hango fuskokinsu zaka gano dimbin damuwar dake tattare acikin zukatansu.”
Tunda aka soma gudanar da taron hally ke zubar da hawaye yayinda zuciyarta ke hasko mata fuskar mijinta ,murmushinsa kawai take gani wanda ya zame masa jiki ko cikin fushi yake dole sai anga wannan murmushin,sosai zuciyarta ke cike da keyarsa, sadiq yayi gyaran murya “kukan nan ya isa haka hally karki manta da condition din da kike ciki damuwarki zata iya haifar da matsala wa abinda kike dauke dashi addua zakiyi masu a duk inda suke allah yasa lfy ya dauke idanunshi akanta ya maida kan ammi da itama yanayinta ya nuna dauriya kawai take “zanje yanzu na samu malam mudi mu tautauna akan alamarin domin nasan bazai rasa sanin halin da’ake ciki ba .”
“To shikenan sadiq sai na jika allah ya tsare yasa muji kyakkyawan labari “Ameen ya fada tare da mikewa ya wuce .


*******


Mumy na zaune taji sallamar Unty maryam tare da turo kofar dakin dake an fada masu a second flow no 20 tanwer take kwance mumy ta amsawa Aunty maryam matar uncle jamil ce kanita tana gama kutso kai sai ga uncle jamil da diyarsa amira me sunan mumy suka shigo kana ganin fuskar mumy kasan tana cikin damuwa da tashin hankali amira dake biye da uncle jamil ta qarasa da sauri ta fada jikin mumy tana tambayarta tanwer “mumy ina aunty tanwer take ita nazo na gani please ki kaini gurinta kinji “.?
Da kyar mumy ta bude baki tace “karki damu zan kaiki gurinta kinji takwarata ta fada tana shafa kanta tare da yiwa kaninta da matarsa sannu da zuwa “aunty ya me

Please Login or Register in order to submit comment