Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ya cigaba da Jan k'afarsa

Mommy Hauwa kuwa ta cigaba da masa magiya dan ta d'auka zuwa zaiyi ya daki Zara.


Zara dan bata Dade da lek'asu ba tana zaune akan gado ta buga tagumi tana tunanin yanda zata bar gidan dan har yanzu tana gwada wayar Adnan a kashe


Mik'ewa tayi da sauri a lokacin da su ka shigo d'akin zata gudu

Dr Cikin k'arfin hali da sauran kuzarin da ya rage masa ya daka mata tsawa yana "dakata kike sake kikayi taku d'aya Sai na kasheki da hannuna"

Zara cak ta tsaya jikinta na wani irin k'yarma har Dr ya k'araso wajen data tsaya


Mommy Hauwa kuwa tunda taji Dr yace zai kasheta da hannunsa itama jikinta ya fara mugun rawa gabanta na fad'uwa

Sai da ya share Hawayen da ya zubo masa ya kalleta yace "Zara ni kikewa Allah isa nine bak'in mugu azzalumi Zara ni mahaifinki kika zaga"


Cije lebb'ensa yayi wasu sababin hawayen na zubo masa

Zara kuwa sunkuyar da kanta tayi babu wani alamar nadama a tattare da ita sai tsoron kar a tab'a lafiyarta dan da akwai hali sai tace eee d'in ta fad'a

Dr sai da ya samu minti biyar bai iya ce komai ba sabida Jan numfashin da yake yi dak'yar

"Daga yau karki k'ara taka k'afarki kizo min Cikin gida na yafeki a Cikin 'ya'yana kije duniya ce ta isheki Riga da wando har da zanin d'aurawa"


Mommy Hauwa ido kawai ta gwallo tana kallon Dr

D'aurewa tayi tace "Dr kalaman nan sun mata tsauri kayi hakuri ka nema mata shiriya a wajen Allah"

Dr ko juyawa bai ba ya kalli Mommy Hauwa yace "karki k'ara minti biyar a gidanan"


Daga haka ya juya ya nufi hanyar fita

Mommy Hauwa tayi sauri tabi bayansa tana "Dr idan ka koreta ina zataje"?

" idan Kinga dama zaki iya maidata gidan mijinta idan kuma bazaki iya ba kibarta ta shiga duniya"

Dr yace yana nufar d'akinsa dan idan ya cigaba da magana numfashinsa zai iya d'aukewa


Ajiyar zuciya Mommy Hauwa ta sauke tana "Allah ka shirya mana zuria"


Daga haka ta nufi d'aki ta sako Hijabinta ta koma d'akinsu Sadiq

Zara tana nan a tsaye a inda suka barta


Cikin d'aurewar fuska tace "kifito na maidaki gidan mijinki idan kuma kin gwammace ki shiga duniya to gaki gata Allah ya baki sa'a yanzu ma zaki iya zagina idan zagi ya miki kad'an ki dakeni".


Daga haka ta juya ta bar d'akin.


Zara tana ganin ta fita ta ja tsaki tana " ai da inada halin wlh da sai na dakeku amma ba komai dan ni na kwaso k'afata nazo wanan mitsayacin gidan naku ba sai kun k'ara ganina ba zaku tab'a lafiyata"

Itama Cikin minti biyu ta fito da shirinta dan jinta take kamar akan k'aya fuskarnan tata a murtuk'e.

Mommy Hauwa kuwa Allahuma ya hadiki kawai take cewa a zuciyarta.


Adai daita sahu Mommy Hauwa ta tare musu babu Wanda yace da wani uffan.

Mommy Hauwa ta fad'a musu inda zai kaisu.


Tafiyar minti goma sha biyar ya k'ara so dasu gidan a lokacin Tara da rabi.

Zara ce agaba Mommy Hauwa abaya

Zara tana tura gate d'in kamar had'in baki

Adnan ya fito daga b'angarensu da shigar sa ta kananan kaya yayi masifar kyau


Ameer shima ya fito daga nasu b'angaren sanye da manyan kaya kayan kuwa sun masifar amsar shi.

Zara tuni ta manta da halin da take ciki sakamakon taga sanyin idaniyarta ta gayyato wani irin murmushi a fuskarta tana yaba kyaun da Adnan yayi a zuciyarta ko d'auke idonta ta k'asa yi.

Adnan kuwa kallo d'aya yayi mata yayi sauri ya d'auke kansa gabansa na d'an fad'uwa dan haka kawai yake tsoron Ameer aransa kuma yana mamakin yanda akayi aka dawo da Zara.


Ameer kuwa kallon da Zara ke bin Adnan da shi har tana Neman bangaje shine yasa ya kalli inda take kallo yaga Adnan dake k'ok'arin bud'e motarsa ya shiga take kallo haka.

Wani irin bak'inciki da takaici ne suka rufe shi adai-dai lokacin da ta bangajeshin sabida bata kallon gabanta

Tureta yayi yace "ballagaza kawai Mara kamun kai sai kibi shi ai"

Daga haka ya ratsa ta gefenta ya k'arasa wajen Mommy Hauwa da gwiwarta ya sage sabida wanan Abu da Zara tayi dan tunda suka shigo taga abinda Zara keyi kamar zata lashe Adnan.


Aliya da Adnan na fita daga gidan ta fito da gudu daga d'akinta tazo ta tsaya daga bakin window dan taga tafiyarsa.


Mamakine ya rufeta data ga abinda ke faruwa take numfashinta ya fara fita da sauri da sauri data ga irin kallon so da kauna da Zara ke bin Adnan dashi Wanda har ta k'asa d'auke idonta sai data bamgaje mijinta..


Zara kuwa a fusace ta fara yiwa Ameer rashin kunya tana ita ba ballagaza bace yaje ya nemo ballagaza daga haka taja ta tsaya tana girgize girgize tana jiran yazo ya bud'e k'ofar ta shige k'asan zuciyarta kuwa ta matsu ta kebb'e ta kira Adnan......
[21/07, 03:26] Nabila maishanu Fbk Gusau Zamfara: *M🅰K'OT🅰N JUN🅰*


*REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS* *P.M.L*




® REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS

ɯɛ ɖơŋŧ ʝųŞŧ ɛŋŧɛřŧąıŋ ŋɖ ɛɖųĆąŧɛ, ცųŧ ɯɛ ąٳŞơ ŧơųĆɧ ɖ ɧɛąřŧ ơʄ řɛąɖɛřŞ


# WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
# IG PML WRITERS
# https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-08144932303




*Written by*

💅💅💅 *SADNAF*💅💅💅



*Follow me on wattpad @ Sadnaf*


*page 12*


Ameer kallonta kawai yake zuciyarsa na tafasa Wanda b'acin ran hakan ya Gaza b'oyuwa a fuskarsa ahaka Mommy Hauwa ta k'araso ta samesu


Ameer ya shanye b'acin ransa tare da tsugunnawa ya gaisheta.

A sanyaye ta amsa gaisuwar tashi tace mishi yayi hakuri ya bud'e k'ofar su Shiga daga ciki.


Ameer bud'e k'ofar yayi Zara tayi sauri ta shige bayan ta gama harare su biyun.

Ameer mamakine ya rufeshi dayaga har da Mommy Hauwa ta had'a ta harara

Bata tsaya a palon ba ta wuce d'aki



Ameer kuwa yayiwa Mommy Hauwa iso har kan kujera ta samu guri ta zauna.


Gaisawa suka k'arayi sai da Mommy Hauwa ta sauke ajiyar zuciya ta fara magana.

"Ameer bazan gaji da baka hakuri ba akan abubuwan da Zara take maka Yarone ka haifeshi baka haifi Halinsa ba wlh bansan inda Zara ta kwaso wanan dabiun nata ba babu ranar da zata fito ta fad'i ban yi musu addu'a ba akan Allah ya shirya min su yanzu Zara bata da gidan da ya wuce gidanan Kaine uwarta Kaine ubanta anan Dan Allah dan annabi Ameer ka cigaba da hakuri da Zara kana tayata addua a matsayinka na mijinta insha Allah zata shiryu nasan kana hakuri da ita ka k'ara wani hakurin dan ko mu iyayenta bata barmu ba icce tun yana d'anye ake lank'wasa shi bata lank'wasu ba tun tana yarinya kaga kuwa sai a hankali insha Allah zata gyara halayenta nima Ina daga gida zan ringa binta da addu'ar Allah ya shiryeta ka ringa kai zuciyarka nesa idan tayi ma ba dai-dai ba idan zan samu ne dan Allah ko islamiyya ne ka sama mata ta ringa zuwa".

Tunda ta fara magana Ameer ya sunkuyar dakansa k'asa sai da ta gama magana ya d'ago tare da sauke ajiyar zuciya haka kawai yaji yana bala'in jin nauyin Mommy Hauwa amma idan ba haka ba wlh babu abinda zai hana ya bata takardata yana jin tausayinta dan muryarta rawa yake har ta gama magana.

Cikin sanyin murya shima ya fara cewa

"Insha Allahu Mommy zan ringa hakuri da Zara amma Mommy naso ace kun barta agaban naku ta d'an koyi hankali kafin a dawo da ita Mommy wlh Zara babu abinda take yi a cikin gidanan kullum da b'acin ranta nake kwana a gidanan a matsayina na Mijinta ban isa tayi min girki ba sai dai ta bani cornflakes da madara tace basa cin abinci mai nauyi a gidansu bata bin umarni na Mommy Aure kana yin shine dan ka samu kwanciyar hankali da nutsuwa amma ni hankalina a tashe yake kullum yaushe zama zai yiwu ahaka fissabilillahi Mommy a gaskiya idan Zara bata canza halinta ba wlh Aure zan k'ara dan dama na gama gini na fenti ya ragemin"

Mommy Hauwa da sauri tace "Ameer wlh na baka goyon baya ka karo auren k'ila asanadin Auren da zakayi idan taga yanda kuke zaman Auren da wacce ka auro d'in ta shiryu"


Ameer girgiza kansa yayi yace "to shikenan Mommy ngd da kika goyamin baya"


"Allah ya maka albarka yauwa nace ka k'arbe wayar hannunta idan da hali ka canza mata sabon sim k'ila kawaye ke hure mata kunne idan ka canja mata layi ta rasa contact d'insu zata shiga hankalinta"

Mommy Hauwa ta fad'i hakane dan Wanda yake neman Zara da Aurenta ya daina samun layinta bazata iya fitowa ta fad'awa Ameer dalilinta ba.

"Insha Allahu mommy zan canza mata layi dan dama inada niyyar haka dan wani zubin idan ta fara chattn dasu bata iya d'aga kai ta kalleni"

"Hakan yafi gaskiya dan kasan wasu kawayen suna kai mutum ga halaka kirawomin ita zan tafi"

Ameer mik'ewa yayi ya nufi d'akin Zara ya tarar da ita agaban mudubi tana duba fuskarta daya fara d'an sab'ewa daga kumburin da yayi dan ta daku awajen Mommy Hauwa da Dr sai Allah ya isa take musu aranta akan sun canza mata kamani kila shiyasa ma Adnan yana mata kallo d'aya ya d'auke kansa.

Ameer fuska a d'aure yace "sai kifito Mommy tana kiranki zata tafi"


"Kace mata bazan zo ba"

Shine Kalmar daya fito daga bakin Zara tana zubawa Ameer harara

Cikin tsananin mamaki da Razanar Kalmar daya fito daga bakin Zara ya saki baki yana kallonta kunnensa na maimaita masa abinda tace ganin ta cigaba da tab'e tab'e a fuskarta yasa ya d'aure ya k'ara cewa

"Kinsan mai nace kuwa Mommy Mahaifiyarki ce tace na kiraki zata tafi"

"Naji sarai ko ba Hauwa kake nufi ba nace kace mata bazan zo ba"

"Kin fara shaye shayene Zara kinsan mai kike cewa kuwa Mahaifiyarki nace fa tana kiranki wacce ta tsugunna ta haifeki ita kike cewa naje nace bazaki zo ba har kike kiran sunanta gatsau"

"Ai sai kayi tinda uwarka nacewa bazan zo ba nace bazan zo ba ko ana dolene"


Ameer bai San lokacin daya lailayo wani ashar ba ya maka yana "Zara Ashe jahilicin naki har akan Mahaifiyarki kanki d'aya kuwa ko kin fara shaye shayene"?


Zara tsaki tayi ta shige band'aki ta barshi a tsaye dan ta gasa jikinta


Ameer kuwa yafi k'arfin minti biyar atsaye tsananin mamaki ya hana ya motsa

Sai da yaji Mommy Hauwa ta fara k'walla masa kira yaja k'afarsa da k'yar ya nufi palon dan har wani gumi ya had'a na kad'uwa da abinda Zara tayi.


Murmushin dayafi kuka ciwo Mommy Hauwa ta sakar masa a lokacin da take mik'ewa tsaye tace muryarta na rawa

" Karka damu Ameer najiyo abinda tace duniya ce Wanda bai zo bama jiranta take Allah ya shiryeta yasa ta gane da wuri kafin lokaci ya kure mata na tafi Ameer kayi hakuri ka kuma cigaba da hakuri da ita abinda tayi yanzu kad'an ne akan Abubuwan da tayi mana nida mahaifinta hannunka baya rub'ewa ka yanke ka 'yar Allah ya ganar da ita"

Siraran hawayen da suka zubo mata ta share ta nufi hanyar fita daga palon

Ameer da jikinsa ya mutu murus k'asa rakata yayi har ta fice daga palon.


Har yanzu kunnensa basu daina jiyo masa abinda Zara tace ba astagfurullahi kawai yake nanatawa dan gani yake Zara babban zunubi ta aikata


Akan kujera ya zube yana so yayi tunani amma kwakwalwarsa ta cushe bai tab'a tunanin rashin hankali da Jahilcin Zara ya kai haka ba har ta iya bud'ar baki ta zagi mahaifiyarta wai ya akayi yaje ya Aure mace irin Zara ?"Kaddara" yaji ya fad'a a fili tabbas kaddara ce idan ba haka ba Zara Sam ba matar Aure bace"


Ya Dade a zaune yana tunanin hukuncin da matakin da zai d'auka akan Zara a k'arshe ya mik'e a fusace ya nufi d'akin Zara yana huci.


Zara kuwa tana fitowa daga wanka ganin ta daina jin motsin su Ameer a palone yasa tayi sauri ta zauna a gefen gado ta fara kiran Adnan


Tayi mishi miss call wajen biyar bai d'aga ba hankalinta ba k'aramin tashi yayi ba ta cigaba da kiransa awaya ganin bai d'aga ba yasa ta fara mishi text adai-dai lokacin Ameer ya banko k'ofar

Zara d'agowa tayi a firgice Ta maida wayar bayanta tana Zara ido tsoro duk yabi ya cikata


Ameer kuwa wajenta ya nufa yana zuwa ya kwasheta da Mari kafin tayiwani yunkuri ya k'ara mata wani ya jawo hannunta data maida baya tana b'oye wayar ya murd'e hannun tare da k'wace wayar baiyi wata wata ba ya rotsa wayar da k'asa ya k'ara d'aukar wayar duk da ta fashe ya k'ara makata da k'asa jikinsa sai rawa yake dan ji yake kamar ya shak'e ta har lahira


Sunkuyawa yayi ya d'auki wayar tare da zare Sim d'in yace "Dabba akuya dakikiya ban tab'a sanin cewar ke katuwar jahila bace sai yau abun naki ya wuce daga kaina ya koma kan iyayenki da suka kawoki duniya to bari kiji na fad'a miki wlh wlh bazan jure iskancinki ba nayi mugun Dana sanin aurenki kuma zan gyara miki zama na haramta miki rik'e waya har sai naga kin fara shiga hankalinki"

Daga haka yasa kai ya fice daga d'akin yabar Zara dafe da kumatunta tashin hankalinta bai wuce wayarta daya rotsa ba ya zare mata sim yanzu da wane waya zata kira Adnan gashi bata rik'e lambarsa ba kukan bak'inciki ta fashe dashi tana tunanin yanda zata samu number Adnan.


Ameer kuwa yana fitowa ya kakarya layin ya zubar ya koma ya canza kayan jikinsa ya fice daga gidan yana tunanin lokaci yayi da zai fara neman Aure ko da ba Auren so zai yi ba dan ya bala'in tsanar Zara albarkacin Mommy Hauwa kawai takeci.


Adnan kuwa yana kallon kiran Zara yak'i dagawa dan duk a tunaninsa Ameer ke kiransa ta layin dan kila ya gano lambarsa awayar Zara a mutuk'ar tsorace yake inda yake tunanin sai ya canza takunsa idan ba haka ba tsaf asirinsa zai tonu dan yaga alamar Zara tana cikin tashin hankali dan yaga yanda fuskarta ya kukumbura kuma yasan ba k'aramin abu ne ya hana jiya tak'i d'aga wayarsa.



Aliya kuwa kanta ne ya d'aure ta kamo wanan tunanin ta saki ta kamo wani zuciyarta nasan diga ayar tambaya akan Zara da Adnan wani b'angare na zuciyarta na hanata dan bai kamata ace Adnan daya San Zara tana tana da Aure ya nemeta ba duk da kad'an da aikin mazinaci amma mai ma'anar kallon da Zara ta ringa bin Adnan dashi dazu?


Kusan haukata kanta tayi da tunane tunane inda a k'arshe taci damara sai inda k'arfinta ya kare zata saka musu ido sosai dan ta gano idan akwai wani Abu a tsakaninsu.


Zara kuwa baccin wahala ne ya kwashe ta sai kusan uku na rana ta farka cikinta sai kug'in yunwa yake aguje ta fito tafara dube dube ko zata samu abunda zata saka abakinta amma ina babu sai dai kayan abinci da indomie.

Indomie ta dafa taci ta fara tunanin ina zata samu aron waya ta kira Adnan ta gaya masa halin da take ciki idan zata samu ne ma ya kama mata haya ta tattara tabar gidan Ameer ta samu yancin kanta da dan ta bala'in tsanar Ameer gashi ba kud'i bane a hannunta ballantana ta saci fita ta siyo koda k'aramar waya ce da Sim dan su ringa communicating da Adnan amma ko da yake tasan dabarar da zatayi zata fita waje ta tsaya har taga dawowar Adnan ta tare shi ta fad'a masa halin da take ciki da wanan tunanin ta saki ranta tare da komawa ta kwanta tana murmushi ita kadai dan haka kawai abinda ya shiga tsakaninta da Adnan ya hau yawo a idonta tana lumshe ido ita kadai ta bala'in missing komai nashi.



K'arfe biyar da rabi Zara tayi wanka ta d'anyi kwalliya dan tafita waje taga dawowar Adnan dan tasan yana Riga Ameer dawowa K'arfe shidda yake dawowa wani zubin bakwai.

Ashar ta fara qundumawa data ga Rabin kayanta da take sawa babu su a wadrobe sai manyan kaya da dogwayen riguna da basu wani matseta ba Ashar ta fara lailowa Ameer tana zaginsa kamar yana gabanta sai bambami take tana dube dube amma har ta gama duba kayan bata ga irin Wanda takesan Sawa ba.


Takaici da bak'inciki ne suka bi suka rufe ta kamar ta kamo Ameer ta hau ruwan cikinsa tayi ta dukansa ganin lokaci na ta tafiya yasa ta d'auko wani doguwar rigar atamfa mai d'an dama dama acikin kayan tasaka ta feshe jikinta da turare ta yafa wani k'aramin gyale tafito da sauri ta nufi gate d'in gidan tare da ficewa.


Aliya da bata Dade da gama aikace aikacen gidan ba tana cikin turare gidan tana bin labulen palon tana sakinsu taji motsin ana bud'e gate d'in gidan da sauri ta yaye labulen dan taga waye adai dai lokacin Zara ta fice daga gidan

Aliya haka kawai ta tsinci gabanta da fad'uwa da tunanin inda Zara zataje da irin wannan shigar daga dawowarta yau jikinta na rawa ta ajiye kask'on turaren hannunta ta zari Hijabi tayi waje sai data tsaya ta lek'a ta wajen ramin k'ofar aikuwa ta hango Zara a tsaye a tsallaken gidansu ta nad'e hannayenta a kirjinta ta kalli hagu ta kalli dama.


Aliya gyara tsayuwarta tayi ta cigaba da lek'ata dan taga mai take jira sun samu kusan minti Ashirin ahaka daga ita har Zaran, Zara sai kalle kalle take yi Ita kuma Aliya sai tsaki take yi tana tunanin mai nata ma zata zo ta tsaya tana lek'enta.

Gajiya tayi da tsayuwar ta juya da zumar komawa ciki aikuwa ta jiyo k'arar motar Adnan dan ko a mafarki take tasan k'arar motarsa da sauri ta maida idonta ta cikin ramin k'ofar aikuwa ta hango Zara ta d'aga hannuwanta biyu tana tsayar da Adnan.


Gaban Aliya ne yafara dukan uku uku ta k'ara ware ido tana kallon ikon Allah

Adnan kuwa a mutuk'ar tsorace yafara waige waige kafin yayi slow da motar kai kana ganin idonsa kaga katon kwarto

Zara da murmushinta ta nufi motar Adnan yayi sauri yafito daga motar yana waige waige yana "ke kinada hankali kuwa ko so kike akama mu bakya tsoro Ameer ya taho yanzu ya ganmu a tsaye"


Zara wani irin rangaji takeyi tana wani farr da idanuwa tana zabga wani irin murmushi kamar zata rungumeshi haka ta tsaya agabansa tana "ka fiye tsoro wlh to sai me dan yaganmu kai nifa babu dan iskan danake tsoro indai akanka ne I miss you" ta k'arshe zancenta tana kashe masa ido d'aya


Adnan kuwa waige waige kawai yake alamar bashida gaskiya yace cikin sauri "Zara mai haka we are not save at all za'a iya ganinmu a tsaye pls kije anjima zan miki text idan kina free"

"mtsss wane text babu waya a hanunna we have alot to discuss dan Allah ka shiga mota mu tafi wani wajen muje muyi magana tunda naga u are not comfortable tsayuwarmu anan"


Adnan da Sauri yace "kina hauka ne muje ina dan Allah Zara ki rufamin asiri I promise zamuyi magana dan Allah kije kar 'yan unguwa su ganmu a tsaye Ameer zai iya dawowa at any time inya dawo yaga bakya nan fa pls kije idan ya fita gobe zanzo muyi magana"


Zara wani irin narkewa tayi ta langab'ar dakai tana mishi wani irin kallo kamar mai jin bacci a hankali tace " i miss u Ad dan Allah gobe yana fita ka shigo"


Da sauri Adnan ya gyad'a mata kai yana waige waige kafin ya shige mota yaja da sauri tare da nufar gate d'in.


Aliya a 360 ta shige b'angarenta jikinta na wani mugun rawa zuciyarta sai harbawa yake ji take duniyar na juya mata a daddafe ta shige d'akinta ta zube a bak'in k'ofa kamar wacce tayi tsere ta ringa jera ajiyar zuciya.



Sai da Adnan ya shiga da minti biyar Zara itama ta shiga gidan tana wake wake dan wani irin farinciki ke ratsata tunda taga Adnan she really love this guy.


Adnan kuwa yana shiga b'angarensu ya d'aura fuska dan haushin Aliya yake ji shi zai bata hakuri ta cigaba da wani ja mishi Aji yau har ya gama cin abincinsa bai sata a idonsa ba ita tasani su zuba shi da ita ita zata kawo kanta ne idan ta gaji.


Ameer kuwa da b'acin ran Zara ya wuni a office ko abinci ya k'asa ci tunani kawai yake matakin da zai d'auka akan Zara ahaka ya wuni a office d'insa zuciyarsa a cunk'ushe ana sallar Magriba ya nufi gidansu dan ya gayawa Mahaifiyarsa halin da yake ciki ta kuma taimaka ta samo mishi yarinya mai hankali ya Aura.


Sai da ya gama cin dadd'an abincin da Mahaifiyarsa ta jera masa yayi gyatsa da hamdala ya tank'washe k'afafunsa ya kwashe irin zaman da suke yi da Zara ya gaya mata da irin hakurin da yake yi da ita da kuma matakin dayake tunanin zai d'auka na k'ara Aure.


Mahaifiyarsa Hajiya Ameena sai data Dade tana jimami da al-ajabin halin Zara ta sauke ajiyar zuciya tace "Allah ya shiryeta ta gane gaskiya bakayi dace da mace tagari ba kwata kwata zan tsaya maka kasamu mace ta gari akwai wata Batula dake k'asan layinmu muna mutunci da mahaifiyarta sosai asanadin haka yarinya tana shigowa wani sa'in mu gaisa har d'an aikace aikace tana tayani na Dade ina sha'awar inama inada wani d'a namiji ya aureta sabida hankali da nutsuwar yarinyar insha Allahu zan yiwa mahaifiyarta magana idan dai ba'ayi mata miji ba sai kaje ka ganta idan tayima"


Ameer da sauri "yace insha Allahu ma ba'ayi mata miji ba idan tayi miki nima tayamin Allah ya zaba mana abinda yafi alheri jibi ma za'a fara fentin gidana dan wancan d'in a takure nake"

"Masha Allah Allah ya taimaka"

"Ameen Ameen"


Hira suka cigaba da yi da ita inda Rabin hirar na Batula ne duk da Ameer bai ganta ba jiyake duk muninta zai iya Aurenta sai wajen sha d'ayan dare ya dawo gida ko kallon k'ofar d'akin Zara bai yi ba yayi shigewarsa d'aki dan ya riga da ya cika cikinsa.......
[21/07, 03:27] Nabila maishanu Fbk Gusau Zamfara: *M🅰K'OT🅰N JUN🅰*


*REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS* *P.M.L*




® REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS

ɯɛ ɖơŋŧ ʝųŞŧ ɛŋŧɛřŧąıŋ ŋɖ ɛɖųĆąŧɛ, ცųŧ ɯɛ ąٳŞơ ŧơųĆɧ ɖ ɧɛąřŧ ơʄ řɛąɖɛřŞ


# WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
# IG PML WRITERS
# https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-08144932303




*Written by*

💅💅💅 *SADNAF*💅💅💅



*Follow me on wattpad @ Sadnaf*



*ZUWAIRA MUHAMMAD WANAN SHAFIN NAKINE KE KAD'AI NA GODE DA KAUNARKI AGARENI MUCH LOVE DEAR*



*Page 13*


Aliya aranar tamkar mahaukaciya haka ta zama dan ko kuka ta k'asa yi ko yaya ta juya Sai ta ga yanda Adnan ke juye juyen rashin gaskiya ta kuma hango irin kallon so da sha'awa da Zara kebin Adnan da shi bata tab'a tunanin Adnan rashin tsoran Allahnsa ya kai haka ba ya iya Neman matar mak'ocinsa wanan wane irin masifa ne tun yaushe suka fara soyayya ba tare da ta sani ba

babu shakka gidan da Zara taje Adnan yaje suka had'u har taji k'amshin turarenta a jikinsa da shattin Jan bakinta.


Aliya bata tab'a sanin Kuka rahama bane sai Aranar dan wani abune ya tsaya mata a kirji da mak'ogaro babu abinda take yi Sai juyi tana hasko yanda taga Adnan da Zara dazu.

Sai da ta Dade a matsanacin hali tare da tafasar zuciya kafin abin da ya tokareta a kirji yafara narkewa Hawaye suka hau zubo mata.

Aliya tayi kuka idonta har wani Zafi yake

Tana tausayin kanta dan babu mummunan jarrabta daya wuce Allah ya jarrabceka da Mazinaci Wanda bai San hakkin mak'otaka ba bai dubi darajar mak'otaka ba babu tsoron Allah a ransa ya iya muamalla da matar Aure ina Adnan zai kai wanan zunubin ga k'eta had'in Aure ga na mak'otaka bata wani ga laifin Zara ba dan can asali bata da kamun kai babu abinda bazata iya aikatawa ba

Adnan fa yasan Zara tana da Aure matar mak'ocinsa ce amma ya iya huld'a da ita wanan wane irin bala'i ne dame ta ragi Adnan da zai ringa Neman mata banza awaje ciki kuwa har Da matar Aure dame Zara tafita tayi tunanin Duniya taga abinda take mishi da har bata iya gamsar

Please Login or Register in order to submit comment