Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

dashi amma Ina bata gano abinda take mishi ba.


Aliya tayi kuka kamar hawayenta zasu k'afe Wanda sabida kuka da tunani kanta ya ringa wani irin ciwo ko sallah ta kasayi sabida tashin hankali da rashin nutsuwa.



Adnan kuwa bai waiwayi d'akin Aliya ba duk da yana jiyo sheshek'ar kukanta tab'e baki yayi yace ita tasani yana zaune zata kawo kanta amma idan shi take jira ya bita d'akinta ya bata hakuri zata shekara duk da yana tsananin bukatar ta abincin da ta dafa ya take a cikinsa yayi gyatsa ya koma d'akinsa yayi wanka ya shirya ya k'ara ficewa daga gidan dan yana bala'in bukatar mace zai fita ya zab'a a cikin 'yan good evening masu tsayawa a bakin titi suna jiran masu tayasu at least ya rage zafi kafin ya samu Zahra.



Zarah kuwa juye juye kawai take tana Allah Allah gari ya waye Ameer ya fice daga gidan Adnan yazo dan tana San kasancewa tare dashi ta kurmance akan Adnan ta makance bata sha'awar zama da Ameer ko k'adan bata da burin da ya wuce ya saketa ta Auri Adnan.



Washegari da sassafe Ameer ya shirya ya bar gidan dan baya San abinda zai ringa had'ashi da Zara ko kad'an dan tsanarta link'uwa yake aransa a duk lokacin da ya tuna irin rashin Kunyar da tayiwa Mommy Hauwa.



Zara tana jin Fitarsa taji kamar ta buga tsalle ta taka rawa dan mafarkai kawai take da Adnan abun shaidan wani mugun sha'awarsa takeji Yanda take ji indai ta samu Adnan ya shigo gaskiya sai ya kashe mata k'ishin dake damunta.


Adnan kuwa bashi ya koma gida ba sai k'arfe hud'u na asuba dan bacci ne ya d'auke shi daya biya bukatarsa da karuwar da ya d'auko suka yad'a zango a hotel itama sai da ya mata rashin mutunci dan ba duka kud'in data bukata ya bata ba a fad'arsa ta yaudareshi itama Surarta ciko ne ga nankarwa ko ta ina ahaka yafito ya barta tana jera mishi Allah ya isa.

Aliya tana jin lokacin da ya dawo gidan hawaye ya k'ara wanke mata fuska bata tab'a nadamar Auren Adnan irin yau ba da tasani bata biyewa san zuciyarta ta Auri Wanda takeso ba da ta Auri Muktar saurayinta mai bala'in santa ya za'ayi ta cigaba da Zama da Adnan ahaka idan ya kwaso cuta ya sa mata fa gaskiya da sake bazata iya cigaba da zama da mazinaci ba daga haka ta mik'e ta fara had'a kayanta.

A cikin k'aramin akwatinta ta had'a kayanta ta koma ta kwanta tana jiran gari ya waye ta fice daga gidan duk da zazzabi da ciwon kai da ke Neman sumar da ita ajiyar Zuciya kawai take saukewa sabida kukan da ta sha.


Adnan kuwa yana shiga d'aki yayi wanka ya d'aura alwala sai da yayi sallar asuba ya koma kan gado ya kwanta dan ba laifi ya d'an Samu nutsuwa jiya ko kad'an bayi tunanin ya duba Aliya yaga halin da take ciki.

Bacci ne yayi awon gaba dashi sai wajen 8 na safe yunwa ta farkar dashi mik'ewa yayi yana hamma tare da nufar k'ofar fita

A dai-dai lokacin da Aliya itama ta fito jikinta sanye da doguwar Riga da dogon Hijabi idon nan nata kamar an watsa borkono tana janye da k'aramin akwatinta.


Adnan da ya d'auki hanyar dinning dan duk a tunaninsa ta gama breakfast kamar yanda ta Saba cak ya tsaya yana kallon Aliya data fito da akwati tana nufar k'ofar fita daga palon ba tare da ta juyo ta kalleshi ba.


Tana dab da fita yace "Ke Aliya gidan uban wa zakije da Wanan akwatin hannun naki"

Aliya ko kula shi batayi ba ta fice daga palon zuciyarta na k'una


Adnan har yayi taku biyu zai bi bayanta yaji akan me zata tafi gidansu da kaya har a akwati ya fasa wani zuciyar na ingiza shi akan ya rabu da ita uban me yayi mata banda kishin balai irin nata daga ganin Jan baki a rigarsa zata bi ta d'agawa kanta hankali duk da ya bata hakuri tak'i ta hakura idan ma yaji tayi take tunanin zai je bikonta tayi karya Yanda ta bar gidan da kanta ita zata dawo da kanta tunda bashi yace ta tafi gida ba.


Yana tsaye a bakin window yana kallon Aliya dake ta share hawaye har ta fice daga gidan yaja wani dogon tsaki yana "Allah ya raka taki gona nama sakata in wala idan kin gaji zaki dawo da k'afarki"

Aliya kuwa duk a tunaninta Adnan zai zo ya sha gabanta ya rungumeta ya nuna mata tsantsar nadamar da yayi akan abinda ya aikata ya bata hakuri ita kuma ta nuna mishi illar abubuwan da yake yi da kuma tarin zunubin da yake kwasarwa kansa na huld'a da matar Aure sai gashi ko ajikinsa ya barta ta tafi mai amfanin zama da Wanda baya kaunarka mai amfanin zama da wanda bai San darajarka ba

bai damu da damuwarka ba ko da mutuwa kayi babu abinda ya dameshi Adnan hasali ma ganinta da yake yi tamkar ta takura masa ne


Aliya tafe take abakin titi tana surutai ita kad'ai hawaye na zuba a fuskarta sai da tayi tafiya mai d'an banzan Nisan dan da a hayyacinta take bata isa tayi wanan tafiyar ba

sai da wata mata ta tsayar da ita tana ta cewa "baiwar Allah mai yayi zafi haka kina tafe kina kuka komai yayi tsanani maganinsa Allah"

Kallon matar kawai tayi bata iya ce mata komai ba kawai ta ciri hannu ta tsayar da tricycle ta fad'a mishi inda zai kaita dan tama kusa isa unguwar tasu a k'afa ba tare da tasani ba.



Zara kuwa motsin bud'e gate d'in gidan yasa ta mik'e da sauri ta lek'a ta window taga Zara ce ta fice da uban akwati a hannunta


Zara wani uban tsalle ta daka murna fal cikinta dan tasan kila fad'a Aliya da Adnan sukayi shine tayi yaji dama Aliya ta tsaya mata a hanci


Fitowa tayi da sauri taje ta kulle gate d'in gidan data ga daga ita sai Adnan acikin gidan ta koma b'angarenta da sauri dan tayi wanka ta shek'a kwalliyar da zata tafi da imanin Adnan.


Cikin minti goma tayi wanka tayi kwalliya ta saka wani doguwar Riga da ya bayyana ko ina na jikinta tazo tayi wanka da turare ta jefa cingum abakinta ta nufi b'angarensu Adnan dan gani take yana b'ata mata lokaci tunda har yanzu bai shigo ba kamar Yanda ya alkawarta.


Adnan kuwa yana ganin Aliya ta fice ya nufi kitchen dan ya had'a shayi ya sha bazai iya tsayawa dafa indomie ba
Sabida yunwa dayake ji.

fitowa yayi Palon hannunsa d'auke da tea cup d'in shayin d'aya hannunsa kuma d'auke da bread da butter sai da yasha shayin yaji ya koshi.

Ya k'unna TV tare da kamo tashar da yake masifar so wato Bomb TV dan kad'e kad'e da Raye Raye kawai ake a tashar tamkar Wanda bashida wani matsala ya ware volume d'in sosai yafara taka rawa yana juyi shi kad'ai dan shi ma'abocin zuwa club ne Auren Aliya yasa ya daina zuwa yana cikin tikar rawa har yana gumi sabida shayi mai zafin daya sha yaji ana kwankwasa k'ofa


Yana bin wakar ya nufi k'ofar ya bud'e numfashinsa ne ya kusan d'aukewa da yaga Zara a tsaye da sauri ya d'aga wuyansa dan yaga inda Ameer ke parking motarsa yaga baya nan sai a lokacin yayi ajiyar zuciya ya dawo da kallonsa kanta yafara binta da wani irin kallo tundaga sama har k'asa yana wani irin Abu da ido


Zara kuwa ji take kamar ta daka tsalle ta rungume shi dan tsananin so da irin shigar da ta gani a jikin Adnan arayuwarta tana bala'in San namiji yasa 3qtr da Armless kwantacen gashin dake kirjin Adnan ta zubawa ido taji wani Abu na tsirga mata tundaga tafin k'afarta har tsakiyar kanta.


Adnan kuwa Hannu ya mik'a mata dan bashida fargabar komai Aliya bata nan Ameer baya nan

Da sauri Zara ta mik'a mishi hannunta ya jawo ta da k'arfi ta fad'a jikinsa ya rufe k'ofar da Hannu d'aya

Har tsakiyar palon ya jata suka tsaya yana binta da wani irin kallo

A hankali yasa Hannunsa ya zagaye k'ugunta ya matso da ita jikinsa ya saka hannunsa d'aya ya rik'e mata hannu ya fara rawa da ita.

Zara da sauri ta fara bin step d'in rawar tana b'angala murmushi dan arayuwarta tana San irin wanan rayuwar ta wayewa Adnan irin Wanda take mafarkin samu ne ya had'u ko ta ina.


A hankali rawar tasu ta fara sauyawa zuwa romance inda su biyun suka rikice suka dakumi juna kamar zasu maida junansu ciki Adnan kuwa ganin Tsayuwa na Neman gagararsu ya sa ya d'auketa cak ya nufi d'akinsa da ita shaidan kuwa ya ringa kad'a musu ganga suna k'ara k'wadaituwa da juna.


Abunka da shedan Zara ji tayi tunda tazo gidan duniya bata tab'a jin dadin da taji da Adnan ba

Adnan kuwa had'in kan da Zara ta bashi ya sarrafata San ran shi yasa yaji bai tab'a gamsuwa da wata 'ya mace tamkar Yanda ya gamsu da Zara ba duk da yasan idan aka zo kan Matarsa Aliya ita ta dabban ce.


Sai da Zara ta kwashi awa uku a b'angarensu Adnan kafin Adnan ya rok'eta akan ta koma b'angarenta kar ta damu yanzu zasu ringa had'uwa akai akai tunda Aliya tayi Yaji Zai kuma samo mata waya da sim su ringa communicating dan sai da suka gama watsewarsu Zara ta kwashe duk abinda ya faru ta gaya masa

Da k'yar Zara ta bar b'angaren dan bata k'i su Dawwama da Adnan ahaka ba.


Adnan kuwa cike da farinciki yayi wanka ya shirya yabar gidan kafin ya bar gidan sai da Zara ta k'ara fitowa da gudu ta rungume shi suka k'ara wata romance d'in ta bar shi ya tafi.



Sallati kawai Hajiya Rukayya ke yi a lokacin da Aliya ta shigo gidan dan gabad'aya a hargitse take cike da fad'uwar gaba ta mik'e dan duk a tunaninta mutuwa Adnan yayi sai da ta Dade tana tambayar Aliya akan abinda ya sameta amma Aliya ta k'asa magana sai kuka take tana rik'e kanta .


Hajiya Rukayya
Hannu tasa ta tab'a jikinta taji da zafi zau tana bukatar taimakon gaggawa

da sauri ta fara k'wallawa kanwar Aliya kira Sumayya akan tazo ta kira mata likitan dake k'asan layinsu ya duba mata Aliya.


Sumayya a gigice ta fita waje bata tsaya tambayar abinda ya sameta ba dan kana ganin Aliya kasan tana cikin matsanacin hali


A tak'aice sai da aka yiwa Aliya karin ruwa har dasu allurar bacci sabida tasamu ishasshen bacci

Likita kuwa yana gama treating d'inta yacewa Hajiya Rukayya "A gaskiya 'yarku tana cikin wani Hali a daina d'aga mata hankali a daina bari tana tunani mai zurfi dan asanadin haka ta kamu da hawan jini kuma bai kamata mai juna biyu jininta ya ringa hawa haka ba dan Allah kuringa k'ok'ari kuna hanata yawan tunani bai dace mai juna biyu jininta ya ringa hawa haka ba"


Hajiya Rukayya babu abinda take nanatawa sai hawan jini da juna biyu da aka ce Aliya na dashi.

Godiya tayi mishi tace insha Allahu zasu kiyayye daga haka Likita yasa kai ya fice daga palon.


Zama tayi a gefen Aliya da duk da bacci take ajiyar zuciya kawai take tabi ta rame ta dashe idonta ya shige ciki.

Hajiya rukayya tunanin ta fara yi akan mai zai haddasawa Aliya hawan jini ga ciki a jikinta wane irin abu ta saka aranta haka

ko dai sakinta Adnan yayi sai a lokacin hankalinta ya kai akan ta kira Adnan ta tambayeshi abinda ke faruwa tunda taga Aliya har da kayanta ta tazo.


A lokacin Adnan yana Zaune a office d'insa sai juyi yake akan kujerarsa fuskarsa d'auke da farin cikin cikar burinsa babu abinda ke amsaa kuwa a kunnensa sai ihun da Zara keyi alamar tana jin dadinsa haka yakesan mace arayuwarsa Aliya kuwa ba k'aramin Abu zai mata tayi ihu ba shi kuwa ihun nan k'ara masa k'arfin gwiwa yake yana kuma jin wani k'arfi agaskiya yaji dadin kasancewa da Zara.


Ringing d'in da wayarsa keyi yasa ya daina juyi akan kujerarsa ya d'auko wayar ganin "inlaw" ke kiransa yasa ya tuna da Aliya tana gidansu sai da ya dai-daita kansa ya samo abinda zai cewa Hajiya Rukayya ya d'aga.


Tamkar yana gabanta ya rusuna yana gaisheta cike da ladabi


Hajiya Rukayya amsawa tayi bayan ta tambayeshi aiki da sauransu tace mishi

"Adnan wai mai ke faruwane naga Aliya ta dawo gida da kaya na tambayeta mai ke faruwa tak'i gayamin sai kuka take ga zazzafar zazzabin dake jikinta sai Dana kira likita ya dubata yace tana da hawan jini ga juna biyu mai yake faruwa haka Adnan"?


Tunda Hajiya Rukayya ta ambaci ciki gaban Adnan ya buga da k'arfi dan Sam Ba yanzu ya shirya haihuwa ba sai nan gaba ganin ta k'ara cewa hello yayi sauri yafara magana yana

" Hajiya wlh ni kaina bazan ce miki ga abinda yake damun Aliya ba kwana biyu haka ta tsiri zama a d'aki idan na tambayeta mai yake damunta sai tace min kar na dameta Data ga na tsananta mata tace min ita cikin jikinta ne bataso sai an cire Hajiya nikuma danaji ta ce sai ta cire shine nace mata ni Kuma ban yarda ta ciremin ciki ba shikenan tun daga lokacin na daina gane kanta bata min girki babu abinda ke had'amu sai harara sai jiya na dawo daga wajen aiki ina zuwa na ganta a zaune a Palo tana k'ok'arin ta sha maganin zubar da cikin shine nayi sauri na watsar na rufeta da fad'a shine tun jiya daddaren take kuka tana rantsuwa akan sai ta bar min gidana ta tafi gidansu yau da sassafe naga ta fito da kayanta babu irin rok'o da magiyar da ban mata ba akan kar ta tafi amma haka ta tureni tayi ficewarta"


Adnan yace yana sauke ajiyar zuciyar irin wanan karyar da ya sharara


Hajiya Rukayya sallati kawai takeyi da taji abunda Adnan yace dan bil hakki ta yarda da abinda Adnan yace tunda muryarsa har rawa take

Hakuri ta fara bawa Adnan akan yayi hakuri tana farkawa zata taso keyarta ta dawo da ita za kuma tayi mata fad'a


Adnan da sauri yace "Aa Hajiya dan Allah karki mata fad'a kinsan ciki babu abinda baya sawa kibarta ta huta idan an kwana biyu zan zo na d'auketa da kaina inaga cikin ke sata wanan abunda take yi dan Allah kibita ahankali idan fad'an zaki mata ki Bari sai hankalinta ya kwanta sosai"


Hajiya Rukayya girgiza kanta kawai tayi tana sa mishi albarka tace masa nan da kwana uku yazo ya d'auki matarsa


Yace mata insha Allahu zai zo daga haka sukayi sallama Adnan na k'ara sauke ajiyar zuciya yana jinjinawa kansa irin wannan karya daya sharara.



Hajiya Rukayya kuwa duk da bacci Aliya take ji take kamar ta tasheta ta rufeta da duka sabida irin rashin hankalin da tayi sai fad'a takeyi ita kad'ai.


Da Yamma Adnan ya koma gida sabida ya bawa Zara wayar da ya siyo mata da sim ya kuwa ci sa'a Ameer bai dawo ba lokacin bai sha wahalar shiga b'angarensu Zahra ba aikuwa ta tafi fa gudu ta rungume shi kamar wani mijinta sai da sukayi kiss mai tsayi har Zara ta fara k'ok'arin kai shi kan kujera yayi sauri ya janye daga jikinta ya d'auke ledar wayar daya yasar a k'asa ya mik'a mata yace gashi su ringa communicating yayi wa wayar full charge ta b'oye karta bari Ameer ya gani.


Zara k'ara rungumeshi tayi tana mishi godiya Adnan kuwa yayi sauri ya fice daga b'angarensu ya nufi b'angarensa dan so yake yayi girki ya kallon ball dan ba laifi ya iya girki.


Yana girki suna chattn da Zara sai exchanging dirty talk suke inda Zara tace bari tazo ta taya shi girki yayi sauri yace ta rufa masa asiri da k'yar yasamu ta hakura da zuwan dan yaga alamar Zara bata tsoron asirinsu ya tonu babu kuma Kunya a tattare da ita.


Ameer kuwa ana sallar Magriba ya nufi gidansu dan ya matsu yaji ya Hajiya Ameena tayi da iyayen batula.

K'asa ma cin abincin da Hajiya Ameena ta jera masa yayi kawai so yake yaji an bashi dama ya fara zuwa wajen Batula.


Sai da Hajiya Ameena ta wana shi tace mishi sunyi magana sunce babu matsala zai iya zuwa su fahimci juna ga lambar wayarta nan

Jiki na rawa Ameer ya shigar da lambar wayarsa Hajiya Ameena sai Dariya take mishi kamar wani saurayin da bai tab'a buduruwa ba.


Abincin da bai ci ba kenan ya mik'e ya nufi gidansu Batula bayan ya kirata awaya yace mata gashi nan zuwa muryarta kawai yaji yasan zata kwanta mishi idan ya ganta.


Ameer tsurawa Batula ido kawai yayi a lokacin da ta fito da shigarta irin ta Aliya duk da sunkuyar da kanta tayi hakan bai hana yaga mugun k'yaun da take dashi ba.

Ameer kusan shi kad'ai ya ringa maganarsa dan Batula ta k'asa magana sabida kunya Wanda hakan kuwa yayi masa dadi sosai yana San mace mai kunya bai San tsautsayin da ya kai shi ya Auri Zara ba ahaka yayi mata sallama ba dan ya gaji da ganin fuskarta ba sai Dan ganin goma ta kawo kai.


Sai da ya koma gidansu ya samu Hajiya Ameena yace Batula tayi mishi over ta fad'awa kanin babansa yaje ya nema masa Aurenta dan in zai samu ma da ita zai tare a sabon gidansa ahaka sukayi sallama da Hajiya Ameena zuciyarsa fal da farinciki.


Batula ma kuwa tunda ta shiga gida take murmushi ita kad'ai dan Ameer yayi mata itama tana ganinsa taji tana sansa.



Ameer sai wajen k'arfe goma sha d'aya ya shigo gidan sai da ya kulle ko'ina na gidan zai nufi d'akinsa yaga bak'in agogo na maza a k'asa a hankali ya sunkuya ya d'auki agogon yana mamakin mai agogon namiji ke yi a cikin palonsa dan wannan ba agogonsa bane take gabansa ya yanke ya fad'i da yayi tunanin ko dai Zara ce ta kawo mishi namiji har gida dan tunda yaje gidansu yafara zargin k'ila tana huld'a da maza awaje tunda da idonsa yaga Wanda tayi niyyar zuwa wajen sa badan ta ganshi ba aranar.


Bai tsaya wani dogon tunani ba ya nufi d'akin Zara a fusace


Zara da ta cire kayanta ta shige cikin bargo suna video call da Adnan sai lumshe ido take tana zaro harshe waje.

Ji tayi ana buga k'ofar kamar za'a b'allata tayi sauri tayi wurgi da wayar hankalinta a tashe ta duro daga kan gadon dan tasan Ameer ke neman b'alla Mata k'ofa

Ajiyar zuciya ta sauke a lokacin da ta tuna ta kulle k'ofar tabar mukulli a jiki

Tsaki tayi ta koma cikin bargo duk da tanajin irin kiran da Ameer ke mata kamar zai fasa makogaronsa.


Adnan kuwa yana ganin Zara tayi w'uli da wayar yayi sauri ya kashe wayarsa gabad'aya gabansa na fad'uwa...



*Am seriously sick I need your prayers da k'yar nayi wanan wlh*
[21/07, 03:28] Nabila maishanu Fbk Gusau Zamfara: *M🅰K'OT🅰N JUN🅰*


*REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS* *P.M.L*




® REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS

ɯɛ ɖơŋŧ ʝųŞŧ ɛŋŧɛřŧąıŋ ŋɖ ɛɖųĆąŧɛ, ცųŧ ɯɛ ąٳŞơ ŧơųĆɧ ɖ ɧɛąřŧ ơʄ řɛąɖɛřŞ


# WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
# IG PML WRITERS
# https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-08144932303




*Written by*

💅💅💅 *SADNAF*💅💅💅



*Follow me on wattpad @ Sadnaf*



*Page 14*


*ALHAMDULILLAHI NAJI SAUKI THANKS OLL FOR D PRAYERS LOVE EN CARING SAKALLAHU BI KHAIR MY WATTPAD FOLLOWERS STAY BLESS UMMU RAHMA TNX ALOT*

*DEDICATED TO AUNTY SIS*💖💖💖💖💖



Zara kiranshi ta ringa yi amma taji a kashe taja tsaki tana mai jin haushin Ameer da yazo ya katse mata jin dadi badan tana tsoron asirinta ya Tonu ba da zuwa zata yi ta taya Adnan kwana tunda Aliya bata nan tana San kasancewa dashi.

Pillonta ta jawo ta rungume ta lumshe ido tana tunanin moment d'insu da Adnan sai murmushi take ahaka bacci ya d'auketa.



Ameer kuwa a fusace ya nufi d'akinsa yana ayyana irin rashin mutuncin da zai yiwa Zara dan yanzu zarginta yake bai yarda da ita ba kwata kwata duk da baya jin digon Santa a zuciyarsa amma babu Yanda za'ayi ya zuba mata ido ta ringa abinda ranta yakeso tunda da Auransa a kanta.


A ranar kiran Batula da yayi awaya yasa yaji ya manta da duk wani b'acin ran Zara yaji wani irin farinciki da nutsuwa na shigarsa.



Aliya kuwa sabida allurar baccin da aka mata ba ita ta tashi ba sai wajen k'arfe biyar sai da ta samu minti biyar da farkawa ta tuna abinda yasa ta baro gidan Adnan hawaye na ya hau zubo mata ta gefen fuska


Hajiya Rukayya dake zaune a gefenta tana girgiza k'afa sabida jiranta kawai take ta farka wani mugun harara ta fara zabga mata duk da Aliya bata lura da ita ba dan idonta a runtse yake.

"Kukan uban me kike wa mutane ba haka kikeso ba ki dawo gida mu jere Aliya Ashe bakida mutunci bansani ba Aliya tarbiyyar Dana miki kenan Allah ya baki kyautar da bazaki iya siya ba wasu da kud'insu ma suke nema basu Samu ba amma Aliya sabida rashin mutunci da rashin hankali kice bakya so sai kin zubar har ya kai ki barin gidan sabida kawai ya hanaki zubar masa da ciki"


Zumbur Aliya ta mik'e duk da sai da ko'ina na jikinta ya amsa ta k'walalo ido tana kallon Hajiya Rukayya

Hajiya Rukayya kuwa ta cigaba da zabga mata harara tana "ai dole ki mik'e Mara mutunci kawai Wlh kin bani mamaki badan Allah yasa mijinki mai hakuri bane da yanzu tuni ya sakeki cikin sunna fisabillillahi kice sai kin zubar yanzu da kika taho gida uban me kika zo yi"? Ko kina tunanin muma shashashai ne biye miki zamuyi"



Aliya cikin tsananin mamaki da d'aurewar kai tace murya na rawa "Umma wlh bangane inda maganarki ya dosa ba umma mai kike nufi"?

Hajiya Rukayya wani mummunan kallon ta k'ara watsawa Aliya tana girgiza kai dan gani take Aliya ta gama raina mata hankali sai da aka samu minti biyar batayi magana ba tana watsawa Aliya kallon Banza


Aliya kuwa jikinta sai rawa yake kanta na Sara mata Dan tana so ma ta had'a maganganun Ummanata waje d'aya ta gane inda maganar nata ya nufa amma ina kanta ya kulle.

" Lailai Aliya abin naki yazo da rainin hankali ni kike ma cewa baki gane inda na dosa ba ko Aliya rashin mutuncin da kikewa Adnan d'in nima zaki min ko"?


Aliya kuka ta fashe dashi tana "Wlh umma bangane abinda kike nufi ba mai zan zubar"


Hajiya Rukayya fad'a ta rufe Aliya dashi ta inda take shiga bata nan take fita ba kamar zata rufe Aliya da duka acikin fad'ar da take fad'a mata yanda sukayi da Adnan.



Aliya kuwa kukan da take ne ya tsaya cak ta zubawa Hajiya Rukayya ido cikin tsananin mamakin abinda tace Adnan ya gaya mata wani irin kukan bak'inciki ta k'ara fashewa dashi

badan na karyar da Adnan ya mata ba sai Dan yardar da Hajiya Rukayya tayi da Adnan alhalin ya kama ta ace ta Riga da tasan abinda zata iya aikatawa da Wanda bazata iya aikatawa ba ada bata da burin da ya wuce ace yau ta samu ciki cikin ma na Adnan amma yanzu babu Wanda ya kai ta bak'incikin samun cikin dake jikinta.


Hajiya Rukayya baki ta rik'e tana kallon Aliya dake kuka kamar numfashinta Zai d'auke bak'inciki itama ya rufeta inda ta fara tunanin k'ila sai ta rufe Aliya da duka zata shiga hankalinta zuba mata ido tayi taga iya gudun ruwanta.


Aliya kuwa da k'yar ta tsagaita kukan da take numfashinta na d'aukewa tace "Haba Umma ya Zaki yarda da maganar da Adnan ya gaya miki batare da kin tambayeni ba kinji ta bakina karki manta Umma babu Wanda ya kai ki sanin halina ciki da waje kinsan abinda zan iya aikatawa kinsan abinda Bazan iya aikatawa ba akan me zan zubar da cikin da Allah ya bani Umma akan me zan zubar wlh tallahi karya yake min ni banma San inada ciki ba sai yanzu da kika fad'a wlh karya yake

Please Login or Register in order to submit comment