Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

a k'asa ta sume awajen.


Adnan kuwa ya k'ara hamb'areta yana d'aukan kudin dake gaban mudubin ya had'a da Wanda ya k'arba a hannunta ya fice yana Allah yasa ta mutu kafin ya dawo.


Yana barin hotel d'in ya hau motarsa ya fari bin unguwa unguwa yana neman gidan haya sai daya samu awa biyu yana nema daga Wanda yayi mishi tsada sai Wanda gidan yayi mishi kad'an ahaka dai har ya samu wani d'an madaidaci mai saukin kudi d'akuna biyu Palo band'aki da kitchen.

A take ya bada dubu d'ari da ashirin ya biya ya samu wasu Almajirai suka share masa gidan suka mopper shi.

Sai da ya siyo sabon katifa da zanin gado ya kai cikin gidan ya baro gidan da zummar yaje ya kwaso kayansa.



Gabansa ne ya d'an fad'i a lokacin dayaga Zara na kwance ayanda ya barta dazun.

Da sauri ya nufi wajenta yana jijjiga ta amma ina ko motsawa batayi ba take hankalinsa ya tashi ya d'ebo ruwa yazo ya watsa mata amma abanza ko motsawa batayi ba.


Cikin tsananin tashin hankali ya kinkimeta yayi waje da ita da sauri bai tsaya sauraran wayanda suka ringa tambayar shi mai ya sameta ba ya saka ta a motarsa da sauri ya nufi wani k'aramin private hospital dake can k'asan hotel d'in


Zirga zirga kawai ya ringa yi a harabar asibitin hankalinsa a tashe wani b'angare na zuciyarsa na addu'ar Allah yasa Zara ta mutu ya huta wani b'angare na zuciyarsa na addu'ar Allah yasa kar ta mutu.

Sai da aka samu awa d'aya da rabi kafin likitan dake duba Zara yafito yace ya zo ya same shi a office.


Adnan kamar zai hantsila sabida saurin da ya ringa yi a lokacin dayabi bayan likita dan duk ya matsu yaji halin da Zara take ciki.


Likita sai daya gama rubuce rubucensa ya d'ago yace masa "matarka na cikin critical condition amma alhamdulillah mun samu mun shawo kan matsalar dan har Karin jini akayi mata pls ga wanan tana bukatarsu sosai sabida cikin dake jikinta"

"What"?

Adnan yace yana dukan tebur d'in dake gabansa "

"Mai kace likita ciki fa kace"?

Likitan a d'an mamakince yace "ee ciki nace dama bakasan tana da ciki ba tana d'auke da ciki har wata biyu da sati d'aya"

"Innalillahi wa inna ilahi rajiun Dr dan Allah ka cire cikin nan ban shirya zama uba ba yanzu ko nawa ne zan baka dan Allah ka cire cikin nan"


Likita da sauri yace "am sorry to say bama zubar da ciki a asibitin nan kuma a condition d'in matarka wlh idan kace zaka zubar mata da cikin zata iya rasa ranta mai yayi zafi haka kai kuwa bawan Allah cikin da wasu suke nema ido rufe wasu har da kudinsu basu samu ba kai ka samu kana so ka zubar."


Adnan kallon likita kawai yake hankalinsa a tashe tunani kawai yake inda zai kai Zara da cikinta shi da yake so ya korata gidansu kuma sai ga ciki ya b'ullo Anya ba guduwa zaiyi daga asibitin ba Idan sun gaji da rik'eta su koreta ta tafi gidansu tunda dama Zara batasan gidan daya koma ba........

*M🅰K'OTAN JUN🅰*


*REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS* *P.M.L.*



*REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS*
(P M L)
​ɯɛ ɖơŋ'ŧ ơŋٳყ ɛŋŧɛřŧąıŋ ŋɖ ɛɖųĆąŧɛ, ცųŧ ɯɛ ąٳŞơ ŧơųĆɧ ɖ ɧɛąřŧ ơʄ řɛąɖɛ'Ş​


#WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
​#IG PML WRITERS​
#https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035
#http://maryamsbello.blogspot.com


*written by*

💅💅💅 *SADNAF*💅💅💅



*Follow me on wattpad @Sadnaf*



*page 23*


"I advise u idan haihuwane baka so kabari idan ta haifi abun cikin nata sai ka d'orata akan family planing I think that's d best solution"


Likitan ya k'ara cewa yana kallon Adnan dayayi zurfi a tunanin

Likitan dukan teburin yayi Adnan yayi sauri ya dawo daga tunanin daya tafi

"Inata maka magana kana tunanin"


Adnan ajiyar zuciya ya sauke yace

"Sorry banji bane bani takardar na amso mata magungunan"


Likitan mik'a masa takadar yayi

Adnan yafice daga office d'in.


Adnan kuwa yana fita ya hau motarsa ya bar harabar asibitin sai da yayi tafiya mai d'an nisa ya tsayar da motar ya k'ifar da kansa a steering d'in yana tunanin abinda ya dace yayi

Tunaninsa ne ya rabu gida biyu wani nacewa daga nan kar ya k'ara komawa asibitin wani nacewa ya koma inyaso idan an sallamo Zara sai ya samo maganin zubar da cikin ya d'ura mata har sai cikin ya zub'e dan yanzu ma ko ya gudu Zara zata haifi abun cikinta kuma dole Wataran a nemo shi.


Da wanan tunanin Adnan ya tada motarsa yaje wani pharmacist ya siyo magungunan daga nan ya tamb'ayesu ko suna da maganin zubar da ciki ko allura idan suna dashi su bashi ko nawane zai basu.


Aikuwa mutumin da tsada ya bashi wasu kwayoyi guda shidda yace ta shanye guda hud'u tasaka biyu agabanta cikin zai b'are.


Adnan da saurinsa yasaka kwayoyin a aljihunsa yana d'an jin relief d'in tashin hankalin da yake ciki.


Sai da ya kai musu magungunan ya koma gida dan Sam bazai iya wani kwana a asibitin ba.



A takaice sai da Zara ta samu kwana uku a asibiti kafin a sallamota duk da lokacin Tana azababben laulayi duk da magungunan da allurai da ake mata.


Adnan kuwa duk zuwan da yake bai wani nuna mata komai ba in banda d'an tattalinta dayake yi dan so yake ya samu ya shawo kanta tasha maganin zubar da cikin.

Tun da suka baro asibiti suka d'auki hanyar hotoro danmarke suka fara kutsawa cikin unguwani


Zara ta gyara zamanta akan kujerar Tana bin unguwar da kallo dan bata ma san unguwar ba.


K'asa hakura tayi sai da tace "Adnan wai ina zamuje ne"?


Adnan bai juyo ya kalleta ba yace "gidana zamuje mana"

"Gidanka kuma a unguwar nan"?


Zara tace Tana kallonsa cikin mamaki

" Adnan tsaki yayi yace "idan bazakije gidan nawa ba ai zaki iya sauka ki tafi gidanku dake G.R.A"


Zara girgiza kanta kawai tayi ta cigaba da kallon unguwar Tana mamakin Yanda zata yi rayuwa a cikin irin unguwar nan


Ganin Adnan yayi parking ne yasa tayi sauri ta juya Tana kallon k'ofar gidan da sukayi parking bata gama tunanin da zatayi ba Adnan yafito daga motar ya nufi gidan Tare da zaro mukulli a aljihunsa ya bud'e gidan.

Ko kallon Zara dake zaune a cikin motar bai yi ba yayi shigewarsa


Zara kuwa jiki a sanyaye tafito daga motar ta rufe ta tsallaka k'aton kwatan dake k'ofar gidan ta shige ciki Tana kalle kalle


Sai da ta karewa tsakar gidan kallo Wanda rijiya ke gefe ta nufi wajen da take kyautata zaton Palo ne.

Bud'e baki tayi a lokacin da taga babu komai a palon ko labule babu in banda tiles d'in dake k'asan palon ga palon k'ararrami.


D'akuna biyun dake palon tabi da kallo ta nufi d'aya daga ciki nan ma ta bud'e taga babu komai a ciki


Jikinta ne ya k'ara bala'in sanyi ta nufi d'akin da take kyautata zaton Adnan na ciki.


A kwance ta ganshi akan katifar yana danne danne a wayarsa gefe kuma kayansa ne a zub'e birjik.



A hankali ta k'arasa wajensa ta zauna a gefensa Tana cigaba da kallon d'akin dan shima in banda katifa babu labule a d'akin.


"Adnan wai mai ke faruwa ne kanaso kacemin ka baro wancan gidan ka dawo nan da zama kenan"?


"Gashi kuwa idonki ya gane miki an koroni daga wancan gidan a dalilin ki Na rasa komai nawa adalilinki so nan ma da kike gani haya ne idan zaki iya zama ruwanki idan bazaki iya zama ba zaki iya kama gabanki dan nikam zamanki awajena ma takura ne dan bansan kalar asarorin da zaki kuma janyo min ba"


Adnan yace yana mai zabga mata harara


Zara sakin baki tayi tana kallon shi ganin Adnan ya juya mata baya yana zuba tsaki yasa tace

"Haba Ad wai meyesa kake d'oramin laifin duk abunda ya sameka kar fa ka manta ina da laifi kana da laifi nakan ma yafi yawa dan kai kafara nuna interest d'inka akaina kafin nima nafad'a kogin sanka har na k'asa controlling kaina gida da aikin da ka rasa can be replaced iyaye fa bazan tab'a iya replacing d'insu ba akanka nayiwa iyayena rashin mutunci na zab'eka akansu na rabu da mijin aurena akanka karshe ma har wani b'ari na jikina na rasa duk sabida kai amma kuma tun ba'aje ko'ina ba gashi kana neman juya min baya haba Ad wlh ban cancanci haka daga wajenka ba"

"Ai ke mahaukaciya ce shiyasa kika zabi namiji akan iyayen da suka kawoki duniya ni bance miki kiyi zurfi a sona haka ba d way u dress attract me har yasa naji ina mugun sha'awarki amma bawai wani sonki nake ba I lost everything I have ciki kuwa harda salihar matata dan ni nasan Wlh Aliya koda babu aure a kanta bazata yarda wani ya rik'e mata hannu ba ballantana akai ga ya santa 'ya mace wlh not even in my dream idan aka rantse min zanyi rayuwa a irin gidanan na yarda amma gashi a dalilin ki dole na fara rayuwa aciki u have cost me a lot of damages"


"Enoughhhh Ad lokaci yayi da zaka daina d'oramin laifin duk abunda ya sameka d time u are riding and raining love on me meyesa baka hango zaka shiga irin wanan matsalar ba sai yanzu koda abaya sha'awata kake bawani sona kake ba kamar Yanda ka sha fad'a abaya to yanzu kuwa ya zama dole ka koyi sona tunda zama dani ya zama dole dan ga cikinka a jikina"


Adnan wani mummunan kallo ya watsa mata yace "Sai kin cire wanan shegen cikin dake jikinki dan nariga da nasan ke ba Kunya gareki ba tunda kika iya neman wani mijin da aurenki Auren naki ma ya mutu kika k'asa tafiya gidanku ko iddan nan da ake yi kika k'i yi dan ki raini cikin shege ki haife shi ba wahala zai miki ba amma kisani ni da sauran kunyata bazan iya k'arbar shege a d'a ba dan haka ki zubar da cikin nan ki koma gidanku idan kinyi jini uku sai nazo na aureki asan ke mata ta ce"


"Adnan a kalmominka Nagano cewar kai katon jahili ne ina aka tab'a idda da ciki sai dai idan na haihu na koma gidanmu sai ka zo ka aureni bani zakayi wa wayo kace na zubar da cikin jikina ba daga nan ka gujeni"


Tunda Zara tacewa Adnan jahili jikinsa ya fara rawa ransa yayi bala'in b'aci ita kuwa Zara itama harararsa take ta mik'e gabanta na d'an fad'uwa sabida rawar data ga jikinsa nayi tasan zai iya kawo mata duka


Adnan mik'ewa yayi yana nuna kirjinsa yace "ni kike cewa jahili"?


Zara baya ta fara yi tana cigaba da harararsa ganin ya nufota yasa ta kwasa aguje ta bar d'akin ya kuwa rufa mata baya ya damkota ya fara kwallo da ita


Zara kuwa sai ihu take sai da yagaji da jibgarta ya koma d'akin da sauri ya kwaso k'wayoyin da ya siyo na zubar da cikin ya nufi wajenta bayan ya d'auko pure water guda d'aya

Zara kuwa kuka kawai take tana birgima


Adnan kuwa ya d'urk'usa agabanta ya janyo ta jikinsa ya danneta da k'afafunsa ya matse bakinta sosai Zara kuwa tsananin azaba yasa ta bud'e bakin ya kuwa watsa mata tablet hud'un a bakin ta ya bud'e ledar ruwan ya dura mata aciki.


Zara kuwa da sauri ta had'iye tana zaro idonta waje sabida Yanda ya matse mata baki.


Bai saketa ba ya k'ara matseta tare da raba k'afarta gida biyu ya cusa hannunsa k'asan ta ya tura sauran guda biyun aciki.


Zara kuwa ido kawai take zarowa sabida tsaya mata da magungunan sukayi a makogaro

Adnan kuwa ya rik'eta gam dan kar ta tashi tayi yunkurin amai.

Zara kuwa mutsu mutsu ta fara yi dan ya cikata sabida aman daya taho mata amma ina Adnan kara riketa yayi

Aikuwa Zara ta sakar masa aman ajikinsa sai ga tabs d'in kuwa guda hud'u ta amayo su ko alamar narkewa bai yi ba

Adnan wani irin kullutun bak'inciki ne ya taso ya tokare masa makagaro a lokacin dayake bin tabs d'in da kallo

Zara kuwa ta ringa sauka ajiyar zuciya sabida wahalar da tasha

Adnan tureta yayi daga jikinsa ya mik'e a fusace.


Yace "kwanciyar hankalinki shine ki zubar da cikin jikin nan idan kuwa kika k'i wlh sai na ringa gana miki azaba iri iri har sai cikin ya b'are"


Zara ita dai ajiyar zuciya kawai ta ringa saukewa tana binsa da ido dan yanzu wani irin tsoron Adnan take ji.

Adnan d'akin ya koma ransa a mutuk'ar b'ace ya shige band'aki dan yayi wanka

Zara kuwa yana shigewa ta mik'e a hankali ta nufi band'akin d'aya d'akin ta cire wandonta ta sa hannu ta Ciro tabs d'in daya sa mata dan har wani tokareta yayi ta wanke jikinta ta fito ta kwanta a k'asan tiles d'in d'akin ta lumshe ido tana jin kanta dake Sara mata tsoro take ji ta fita Adnan ya kara jibgarta ko kuma ya k'ara d'ura mata maganin zubar da cikin.


Adnan kuwa yana fitowa daga wanka ya shirya ya d'auki ATM d'insa ya fice daga gidan dan so yake yayo siyayya daga nan ya k'ara samo wani maganin dan sai cikin jikin Zara ya zub'e hankalinsa zai kwanta.




*heeee sweetys nayi missing dinku sosai naji dadin so da kaunar da kuka nuna min wlh next week nayi niyyar typing amma sabida Yanda kuka nuna min kauna yasa nace bari nima.na faranta muku rai da magriban nan nayi typing inasan kusan kuna raina ina san jin dadinku ngd sosai da so da kulawa tnx for d prayers u guys should manage Aunty khady hope u are happy now*🤪🤪🤪


*Diana chef bhal am coming to have a delicious meal ooo*

*M🅰K'OTAN JUN🅰*


*REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS* *P.M.L.*



*REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS*
(P M L)
​ɯɛ ɖơŋ'ŧ ơŋٳყ ɛŋŧɛřŧąıŋ ŋɖ ɛɖųĆąŧɛ, ცųŧ ɯɛ ąٳŞơ ŧơųĆɧ ɖ ɧɛąřŧ ơʄ řɛąɖɛ'Ş​


#WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
​#IG PML WRITERS​
#https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035
#http://maryamsbello.blogspot.com


*written by*

💅💅💅 *SADNAF*💅💅💅



*Follow me on wattpad @Sadnaf*


*WANAN SHAFIN NAKINE KAWATA KHADIJA MATAZU (KHADNAF) INA YINKI IRIN TOTALLY*

*sakon gaisuwarki ya iskeni Hussaina Mahmud m/fashi ina kaunarki fissabillillahi*


*page 24*

Adnan sai da ya fara Ciro kudi a bank kafin ya nufi wajen da ake siyar da kujeru dan so yake yayi furnishing gidan ko gidan ya d'an haska.


Masu d'an saukin kudi ya siya ash en red ya siyi labulayen dasuka dace da kalar kujerar.


Daga nan ya wuce inda ake siyar da kayan kallo ya siyi plasma maidaidaiciya da sauran kayan amfani na gida irinsu hearter bokitai kayan abinci gas cooker generator k'arami da sauransu


A katon akori kura aka loda masa kayan ya shige motarsa a kori kuran na binsa abaya.


Ita kuwa Zara wahallalen bacci ne yayi awon gaba da ita ak'asan tiles d'in d'akin bata san tsawon lokacin da ta kwasa tana baccin ba har sai dataji muryar Adnan nayiwa mutane umarni dasu shigo da kaya.


Mik'ewa tayi daga kwancen da take da sauri tana yamutsa fuska sakamakon ko'ina na jikinta dake mata ciwo.


Mik'ewa tayi tana cije lebb'e ta nufi k'ofar d'akin ta bud'e dan ta ga mai ake ta shigo dashi.


Had'a ido tayi da Adnan dake tsaye a gefe ana ta shigo da kayayyakin da ya siya

Hararar da ya galla mata ne yasa ta koma ciki da sauri tana rufo k'ofar dan yanzu tana bala'in shak'arsa da tsoronsa


Zub'ewa ta k'arayi a k'asan tiles d'in tana rik'e cikinta dake k'ugin yunwa.


Cikin awa d'aya da rabi Adnan da wayanda suka kawo masa kayan suka shirya palon suka saka komai a muhallinsa tuni gidan ya haska kamar na amarya.


Nan da nan Adnan ya kamo tashan daya saba ji ya ware kid'a a gidan kamar bashi da wani matsala dan shi mutum ne mai san holewa.


Sai daya gabji rawa ya gaji ya zub'e akan kujera yana maida numfashi

Mik'ewa ya k'ara yi sakamakon yunwar da yake ji ya nufi d'akin da Zara take.


A kwance ya sameta ta rik'e cikinta sai hawaye take
Wani mugun tsawa ya daka mata yana "ke dalla tashi ki d'orawa mutane abinci dan bani da kudin da zan ringa yin take away kullum ga kayan abinci can na siyo babu abinda babu har tukunya ki tashi ko jollof d'in taliya ne ki d'ora mana zan shiga wanka ki tabbata kafin na fito kin gama"


Zara mik'ewa tayi dak'yar sabida rawan da jikinta yake yi tace "wlh Ad ban iya girki ba sai dai idan indomie zan dafa maka"


Wani mugun harara Adnan ya zabga mata yace "aikuwa yau zaki koya dan bazan yi tolerating nonsense ba ace babu abinda kika iya sai iskanci ke yanzu ahaka Ameer ya zauna dake batare da kin iya girki ba tab ba zai yiwu ba na baki minti goma sha biyar ki tabbata my food is set kafin na fito"


Daga haka ya juya ya bar d'akin ya bar Zara da zubar hawaye

Duk da jirin da take ji iska na d'aukar ta ahaka ta mik'e ta nufi tsakar gidan inda kitchen yake


Babu abinda zata nema dan komai Adnan ya siyo har da greter gas d'in ta kunna ta d'ora ruwa ta zabga mishi farin mai maggi tumatir d'in leda curry da gishiri ta rufe.


Ta farka kwallin taliyar ta zaro guda d'aya ta k'ara bud'e tukunyar ta kakarya taliyar aciki ta zuba sardine guda biyu ta rufe ta koma bakin k'ofa ta zauna tana jiran ya dahu ta juye dan ji take kamar taci babu sabida yunwar da take ji.


Taliyar ko nuna baiyi ba ta sauke ta d'auraya plate guda biyu ta zuba mishi nashi itama ta zuba nata ta d'auka ta nufi palon jikinta sai rawa yake

Ajiye mishi tayi a tsakiyar palon ta d'auki nata ta koma d'aki tun kafin ta zauna ta d'iba da hannu Tana kaiwa bakinta sabida tsabar yunwa da takeji.


Aikuwa k'asa had'iyewa tayi sabida gishirin da yayi yawa gashi bai dahu ba ga karnin kifin gwangwanin da ta saka

Rufe ido tayi ta had'iye ta k'ara kai hannu da zumar deb'o wani ta kai bakinta wani irin Amai ya kwace mata amai take bilhakki dan Rabin aman ruwa ne sabida babu abinci a cikinta a cikin wanan halin Adnan ya banko k'ofar da plate d'in abincin a hannunsa yana mata wani irin kallo duk da ba kallonsa take ba amanta kawai take yi.


Adnan shiga d'akin yayi ya dire plate d'in agabanta duk da har lokacin bata d'ago ba kakarin aman kawai take


" Kema kanki kin kasa cin guban da kika dafa da sunan abinci ballantana ni kinsan Allah koda zaki amayo kayan cikinki wanan abincin shine na darenki idan shima bakici ba shi zaki ci da safe dan wlh bazaki ringa janyomin asara ba common taliya jollof kin kasa dafawa"


Zara d'ago da kanta tayi dak'yar Tana kallonsa sai numfashin wahala take saukewa.


Adnan kuwa ya zabga mata harara ya ja tsaki ya bar mata d'akin dan ko kallon minti biyar baya so yayiwa Zara.


Kitchen ya koma ya dafa indomie mai rai da lafiya yaci ya koshi ya koma d'aki ya shirya cikin kananan kaya a lokacin ana kiraye kirayen sallar magriba sai da yayi alwala ya fito ya tsaya a massallacin unguwar yayi sallah ya d'auki hanyar gidan abokinsa Safwan.



A zaune suke a palon Safwan Safwan ya zira masa ido bayan Adnan yagama kora masa jawabin abinda ya same shi babu abinda ya b'oye masa dan amininsa ne tun secondary school kuma halinsu yazo d'aya.


"Kayi kuskure Adnan mai ya kai ka huld'a da matar Aure matar Auren ma matar mak'ocinka"


Ajiyar zuciya Adnan ya sauke yace "bazaka gane ba Safwan wlh Zara nan shaidaniya ce ko Kaine nasan u would fall for her ni ba wanan ba Safwan dan Allah kayi min k'ok'ari na samu aiki a companynku dan bansan Yanda zan fara rayuwa idan sauran chanjina suka kare ba"

"Zan maka k'ok'ari insha Allahu tunda ga takardunka nan ka Riga da ka kawo yanzu ya zakayi da cikin dake jikin nata tunda yak'i zub'ewa"


"Ai yanzu ina bar nan wani maganin zan kuma zuwa na siyo na kai mata yarinyar kamar mayya tak'i tafiya gidansu ta mak'ale min da wallahi guduwa nayi niyyar yi"


Safwan mik'ewa yayi yana gyara zaman face cap d'in dake Kansa dan shi bashida aure holewarsa kawai yake cewa yayi


"Ya kamata kam idan bahaka ba abun ne zai maka yawa nifa club zani zan biya na d'auki Sara dan yau chasun mai Zafi ne"


Adnan mik'ewa yayi shima yace "nima bari na biku ko na samu mai deb'e min kewa da banida wani damuwa amma wlh zuwan yarinyar nan rayuwata ya zame min matsala"

Safwan kanne masa ido d'aya yayi yana "that's kwartanci for u baka san Zata zame maka matsala ba a lokacin da kake enjoying d'inta sai yanzu da abubuwa suka kwab'e maka naso ina wajen mijin nata ya kama Ku hhhhhhhh"


Adnan duka ya kai masa a kafad'a yayi sauri ya k'auce yana Dariya ahaka suka fice daga gidan suka hau motacinsu suka d'auki hanyar club.


Adnan a ranar ko gida bai koma ba dan tuni zuwansa club ya saka shi nishadi yana tunanin tamkar lokacin da yake saurayine dan ga 'yan mata iya 'yan manta sai wacce ya zab'a ya darje.


Zara kuwa tunda tayi amai ta koma gefe ta k'ara kwanciya dan bata da kwarin da zata zauna ko kad'an.


Tana jin lokacin da Adnan ya fice daga gidan ganin bai dawo ba har 8:30 yasa ta rarrafa ta fito dan ta fara ganin bibiyu sabida yunwar dake nukurkusarta.

Indomie da Adnan yaci ya rage tagani a palon tayi sauri ta d'auka tayi mishi kwasa d'aya ta danna a bakinta

Sid'e plate d'in tayi jikinta na rawa dan kamar k'ara ingizo yunwar tayi a hankali ta mik'e tana dafa bango ta nufi kitchen tana zuwa ta d'ora ruwan zafi

Ta zauna a k'asan kitchen d'in ta fara hargitsa kayan abincin tana Neman kayan shayi.

Wani nanauyan ajiyar zuciya ta sauke a lokacin da tayi tozali da kayan shayin aikuwa jiki na rawa ta had'a shayi mai kauri ta samu slide bread guda goma ta fara kora shayi da bredin kamar wacce bata tab'a cin abinci.


Luckily kuwa har ta sha shayin bataji tana jin amai ba sai dai gyatsa da ta ringa yi kamar aman zai taso mata sai kuma taji ba aman bane.


Sai a lokacin ta dawo dai-dai ta mik'e ta bar kitchen d'in ta koma d'akin Adnan ta shige band'aki tayi wanka tare da d'aura alwala dan rabonta da sallah tun lokacin da take gidan Ameer.


Kayanta ta mayar jikinta dan ta hargitsa kayan Adnan gabad'aya babu kayan ta a ciki sai a lokacin ta fara tunanin inda Adnan ya kai mata kayanta.


Ahaka tayi sallah da k'aramin mayafi sallar ma shap shap tayi ta kwanta a katifar d'akin sabida wani irin bacci da take ji aikuwa tana kwanciya bacci ya d'auketa.


Cizon da Sauraye suka ringa kai wa fatarta ne yasa ta bud'e idonta.


Da sauri ta maida idonta ta rufe sakamakon duhun da ya mamaye d'akin dan 12 aka d'auke wuta kirjinta ne ya hau bugawa da k'arfi data ji haushin karnuka ko ta ina gashi babu waya a hannunta ballantana ta haska ta kuma ga k'arfe nawa duk a tunaninta Adnan ya dawo Ashe bai dawo ba ita kad'ai ya bari a gidan.


Baccin da Zara bata koma kenan ba sabida tsananin tsoro sai da aka fara kiraye Kirayen sallar asuba aka dawo da wuta da sauri ta mik'e daga kwancen da take ta fito daga d'akin ta nufi hanyar waje dan taga ko gidan a bud'e yake.


Aikuwa a bud'e taga gidan tayi sauri ta saka sakata wani tsoron na k'ara rufeta

Aguje ta koma ciki ta kulle k'ofar palon ta shige d'aki tana fashewa da kukan wulakancin da Adnan yayi mata wato idan ma saceta akayi ko kasheta akayi bai damu ba.



Sai da gari ya fara wayewa bacci ya saceta tana sauke ajiyar zuciya.


Adnan kuwa sai k'arfe goma ya farka da shi da Linda d'in data taya shi kwana a gidan Safwan mik'ewa yayi da sauri daya tuna Zara ya fad'a band'aki yayi wanka a hanzarce yayi alwala yafito yana iddar da sallah ya d'auki mukullin motarsa ya

Please Login or Register in order to submit comment