Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

lokacin nan awajen wata mata mai siyar da abinci nake kwana nake tayata wanke wanke jiya ta koreni akan zata koma garinsu jiya ma abakin titi na kwana shine nace yau bari nazo gida na nemi yafiyarku dan banida sama daku Mommy dan Allah kubani Abu naci yunwa nakeji"?


Mommy Hauwa hankalin ta a tashe ta mik'e tare da rik'e hannun Zara ta taimaka mata ta mik'e tana "Amma Ameer bai kyauta ba ya za'ayi ya sake ki da ciki ko tausayi babu kuma nayita kiransa a waya yana raina min hankali duk abinda kika masa ai ko dan cikinsa dake jikinki bai kamata yayi ta korarki ba duk da nasan Zara bakida gaskiya haka kawai bazai sakeki ba tare da kin masa laifi ba muje kici abincin Na kira shi awaya"


Ciki suka Nufa Khaleed da tunda suka fara magana yana daga gefe yana kallon Zara cikin tsananin tausayi kamar ba Zara 'yar gayun da ya sani ba.


Mommy Hauwa shap ta manta da Dr Na zaune a Palo suka nufi cikin palon.

A bakin k'ofa sukayi kicibis dashi shima zai fito waje dan tunda khaleed yazo yayiwa Mommy Hauwa rad'a a kunne suka fice a tare yake ta tunanin mai tafi ta waje yi ganin basu dawo yasa ya fito dan yaga ina taje.


Mommy Hauwa da Zara a tare gabansu yayi mummunan fad'uwa Zara tayi sauri ta koma bayan Mommy Hauwa da sauri tana b'oye fuskarta.


Dr kuwa take annurin fuskarsa ta b'ace b'acin rai ya bayyana a fuskarsa.

Ko khaleed dake bayansu sai da hantar cikinsa ya kad'a.


Mommy Hauwa kallon Dr kawai take itama tana tattaro duk wani k'arfin halin da ya rage mata dan yau zata mishi tijara bai isa ya kori Zara daga gidan nan ba.

Dr cikin tsananin b'acin rai yace "Hauwa mai wannan yarinyar take nema a gidanan bana ce kar ta sake ta k'ara tako k'afarta ta shigo min cikin gida ba"


"Mai kuwa zata nema a gidanan Dr karka manta bata da sama da gidanan bata da inda zata zauna daya wuce gidanan kayi hakuri ka yayafawa zuciyarka ruwan sanyi hannunka bai rub'ewa ka yanke ka yar Zara ta zama dolenmu bata da sama da mu duk lalacewa bazaka so rayuwarta ta tagayara ba kama dubi halin da take ciki tsakanin mutuwa da rayuwa Na cikin da take d'auke dashi kayi hakuri ka yafe mata karka manta sau d'aya tayi maka rashin kunya Nikuwa tun suna yara suke min rashin Kunya har zuwa lokacin da tayi ma ni Dana tsugunna Na haifeta nasan zafin nakudarta nikuma nace me? Dan haka kayi hakuri yanzu Zara na bukatar taimakon mu"


Dr wani irin mummunan kallo ya fara bin mommy Hauwa dashi idonsa ya kad'a yayi jajir

Zara kuwa kafafunta in banda rawa babu abinda suke d'an cikinta kamar ya fad'o sabida fargaba haka ma kirjinta lab'ewa ta k'ara yi abayan Mommy Hauwa zufa na keto mata bayan taga irin kallon da Dr keyiwa Mommy Hauwan

Mommy Hauwa duk da a mugun tsorace take gabanta na fad'uwa hakan bai sa ta yarda ya nuna a fuskarta ba illa ma d'aura fuska da ta kuma yi sabida Dr yasan wanan karon babu wasa a maganarta.

Cikin wani irin murya Dr yace "Hauwa gidanki ko gidana kafin na kirga uku yarinya nan ta bar gidanan idan ba haka ba bazakiji dadin abinda zan miki ke da ita ba har gobe zagin da tayimin yana amsaa kuwa a kunenna *Allah ya isa bak'in mugu azzalumi* wai yarinya Dana fifita ta akan sauran 'ya'yana nake mata duk abinda takeso itace yau ta bud'i baki ta zageni yanzu haka danake kallonta agabana tamkar a yanzu take min wanan zagin yarinya nan bata cancanci yafiyata ba ko wane irin hali kuwa zata shiga bazan yafe mata ba abinda yayi daga yayarta har 'yayy'en nata da kaninta babu wanda ya tab'a zagina duk da akwai 'yan shaye shaye a cikinsu ko da sun sha ya gaya musu karya hakan bai sa sun tab'a zuwa sun zageni ba dan sun san ni mahaifinsu ne dan haka *Bak'in mugu azzalumi* bashida gidan da zata zauna aciki dan haka ta fitar min daga gida yanzu nan kafin Na fitar da ita da kaina"

Zara zub'ewa tayi a k'asa sabida kafafunta daya k'asa rik'eta ta fashe da wani irin kuka tana "Daddy dan Allah kayi hakuri Na tuba bazan kara ba wlh Sharrin shaidan ne yanzu idan ka koreni banida inda zanje Daddy dan Allah kayi hakuri"

A tsawace Dr yace "Ba damuwata bace kije duk inda zakije kibar min gidana yanzu nan kafin Na fitar dake"



Wajen Zara ya nufa gadan gadan

Mommy Hauwa ta sha gabansa da sauri cikin d'aurewar fuska tace "Dr babu inda Zara zata je domin abinda kayiwa naka mahaifiyar Zara tayi maka karka manta duk abinda ka shuka sai ka girbeshi banso nayi wanan maganar agaban 'yayanka ba amma naga ya zama dole Na tunatar dakai abinda ka manta abinda kayiwa Hajiya shi 'yarka tayi ma kaji idan da dadi ina da labarin duk abinda kayiwa Hajiya Na rashin kyautatawa Ina da labari har ta mutu baka samu ka nemi yafiyarta ba dan haka ba wai gori nake ma ba nasan yau da zaka maida hannun agogo baya da sai ka nemi yafiyar Hajiya da ka gyara kurakurenka dan haka karka wani ga laifin da Zara tayi ma abinda kayi akayi maka Allah ne ya sakawa Hajiya ta hanyar nuna maka ishara akan abinda ka Haifa sabida haka Zara ta cancanci ka yafe mata tunda har ta gane ta kuma zo akan ka yafe mata"


Tunda ta fara magana hawaye suka hau zubowa Dr zuciyarsa Na sama da k'asa kamar ba namiji ba

Mommy Hauwa duk da hawayen da ta ga yana yi ya bala'in karya mata zuciya har itama taji hawayen Na Neman zubo mata hakan bai sa ta nuna a fuskarta ba in banda ma kau da kanta da tayi dan taga alamar idan ba haka tayi mishi ba ba zai shiga hankalinsa ya gane shine silar rashin tarbiyyar 'ya'yansu ba.


Dr kuwa jikinsa wani irin rawa ya ringa yi ya zubawa Mommy Hauwa ido dan ta tona mishi b'oyayyen sirrinsa agaban 'ya'yansa

Sai da suka kwashi minti goma ahaka in banda sheshek'ar kukan Zara babu abinda yake tashi.

Dr da k'yar ya bud'e bakinsa yace "Hauwa ai bansan abun naki ya kai har kimin gori akan ban kyautatawa mahaifiyata ba karki manta rashin kyautatawar da ban manta ba bai wuce Dana fara aiki bata ci kudina ba bayan wahalar da ta sha dan taga Na kai wanan matsayin amma idan kika d'auke hakan ban tab'a mata rashin kunya ba ban tab'a zaginta ba ina bata girmanta Na mahaifiyata shima kudin da ban kashe mata ba sharrin matan Dana ringa mu'amalla dasu ne a lokacin Hauwa ngd da abinda kika min kuma tuna min da kikayi da rashin kyautatawa mahaifiyata da banyi ba ba shi zai hana Na kori Zara ba dan gidana ne ba naki ba Idan kinga bazaki iya ba zaki iya binta Na sauwake miki kije tayi ta miki rashin Kunya amma ba a gidana ba"

Mommy Hauwa ido ta zubawa Dr hawaye na zubo mata dan bata tab'a ganin Mai irin halin Dr ba

Dr kuwa tsaki yayi ya juya ya koma ciki bayan ya zubawa Zara mugun harara.


Khaleed wajen Mommy Hauwa ya nufa ya rik'e hannunta yana

"Mommy kiyi hakuri karki wani d'aga hankalinki yanzu Daddy yayi fushi sosai wanda sai an d'auki lokaci zai sauko idan ba haka ba a yanzu ba zai wani saurareki ba tunda kinga akan Zara har yana ambatar zai sauwake miki"


Mommy Hauwa kukan bak'in ciki da takaici ta fashe dashi Tana "Haba khaleed Meyesa daddynku baya yafiya Meyesa zai d'auki irin wannan matakin akan Zara Ina yake so Zara ta tafi da wanan uban cikin Allah ma muna masa laifi mu nemi yafiyarsa ya yafe mana ballantana mu 'yan Adam Meyesa yake haka"


Zara cikinta ta rik'e sakamakon zillon da yake mata ga wani irin jiri dake kwasarta sunan Mommy Hauwa ta kira da k'arfi tana

"Mommy kibani abinci zan mutu"

Khaleed a guje ya shiga palon Mommy Hauwa kuwa ta tare Zara sabida kar ta fad'i k'asa.



Kular dake dining Khaleed ya kinkima yayi waje dagudu

Ya ajiye agaban Zara.

Zara bata wani tsaya jiran plate ba ta bud'e kular hannunta Na rawa taga tuwon shinkafa ne da aka mulmula a farin Leda ko jiran khaleed daya koma d'auko miya batayi ba ta warware guda d'aya ta fara cusawa a bakinta kafin Khaleed ya dawo har ta kusa cinye mulmule d'aya.


Mommy Hauwa ido kawai ta zubawa Zara hawaye Na cigaba da zubo mata dan ba k'aramin tausayin Zara taji ba.


Khaleed miyan agushin da yaji namomi ya zubo a cikin plate ya kawowa Zara.

Cikin minti biyar Zara ta ci tuwo wajen mulmule uku ta ringa lashe kwanu wanda hakan yasa Khaleed zubar da hawaye dan tamkar wacce bata tab'a cin abinci ba haka ta ringa lasar kwanun.

Mommy Hauwa kuwa kallonta kawai take Tana tunanin mafita dan Sam bazata iya barin a kori Zara ba sai dai idan itama barin gidan zatayi.

Sai da Zara tasha ruwa ta koshi har da gyatsa ta kalli Mommy Hauwa Tana "Mommy kiyi hakuri nasan Daddy yayi fushi ne sosai shiyasa ya fadi haka akaina bazan bari aurenki ya mutu ba ki kira Aunty khadija awaya ki roketa akan zan zauna a gidanta na d'an lokaci kafin Daddy ya huce nidai fatana ki kara yafemin abinda nayi miki ki tayani rok'on Daddy"


Mommy Hauwa mik'ewa tayi tace "Ba kiranta zanyi a waya ba zuwa zanyi da kaina bari na d'auko Hijabina"

Daga haka ta shige ciki Zara kuwa ta kalli Khaleed tace "Khaleed dan Allah d'auko min leda na juye abincin nan anjima nasan zanji yunwa sai naci"


Khaleed girgiza kansa yayi cikin tausayawa yace "Haba Aunty mai yayi Zafi haka ai akwai abinci a gidan Aunty khadija har sai kinci kin ture ba sai an juye miki a leda ba"


Mommy Hauwa kuwa fuska a d'aure ta shige d'akinta Dr kuwa da tunda ya zauna a Palo yake tuna irin rayuwar da yayi abaya na rashin kyautatawa mahaifiyarsa inda tunanin hakan yasa yayi ta zubar da hawaye yana nadama dan Mahaifiyarsa babu abinda bata siyar ba sabida shi amma wai ya rasa wacce zai yiwa rowa idan ta tambayeshi kudi sai ita ayau duk abinda ya mallaka ta silarta ne Inama hannun agogo ya koma baya da sai ya bata duk abinda ya mallaka a cikin wanan halin yake Mommy Hauwa tazo ta wuce shi ya bita da kallo har ta kuma fitowa sanye da Hijabinta.


Gabansa ne ya fad'i a lokacin daya ga Tayi hanyar waje da Hijabi a jikinta cikin tashin hankali ya mik'e tsaye yace "Hauwa ina zakije"?

Mommy Hauwa juyowa Tayi fuska a d'aure tace " ba kace nabi Zara ba binta zanyi sai ka zauna kai kad'ai tunda haka kakeso".


Daga haka Mommy Hauwa ta fice daga palon duk kiran da Dr ke mata ko juyawa batayi ta kalleshi ba.

Hannun Zara ta rik'e sukayi waje Khaleed yabisu abaya sai da ya tsayar musu da tricycle yaga tafiyarsu kafin ya koma ciki inda yana komawa ciki Dr ya rufeshi da Fad'a yana akan me bai hana Mommy Hauwa tafiya ba ya barta ta tafi tamkar ya rufe Khaleed da duka haka ya ringa zuba masa fad'a.

k'arfe 9 dai-dai suka isa gidan Kanwar Mommy Hauwa Aunty khadija.


Aunty khadijar kuwa tana ganinsu ta dafe kirjinta dan kana ganin idon Mommy Hauwa kasan taci kuka ta gode Allah a rud'e ta fara tambayarsu abinda ya faru sai da Mommy Hauwa ta samu guri ta zauna ta bawa Aunty khadija labarin duk abinda ya faru babu abinda ta b'oye mata dan bata da sama da khadijar babu sirrinta da bata sani ba.

Aunty khadija Zaran dake ta gyangyadi ta bi da kallo tace "Tashi kishiga d'akina ki kwanta gobe sai muyi magana dan naga agajiye kike ki kuma shirya fad'amin gaskiyar abinda ya faru dan nasan halin ki Zara Ameer haka kawai bazai miki kazafi ya sakeki ba"


Zara bata wani tsaya jin mai take cewa ba ta nufi d'akin tana Hamma sabida mugun baccin da takeji tana kuwa zubewa a shimfidaddiyar gadon bacci mai nauyi tare da nutsuwa yayi awon gaba da ita.


Mommy Hauwa kuwa tana shigewa ta Ciro wayarta daga jakarta ta latso lambar Ameer ta saka a handsfree tana girgiza k'afa tamkar agabanta yake.

Adai dai lokacin Ameer ke waya da Aliya yana janta da hira dan k'arfi da yaji yakeso ya cusa kansa awajen Aliya har ya samu ta saki jiki dashi .

Kiran dake ta shigowa wayarsa ne yasa ya cire wayar daga kunnensa dan yaga wanda yake ta kira haka ganin Mommy Hauwa ke kiransa yasa ya d'an waro ido yana mamakin kiran da take masa ganin har lokacin kiran na shigowa yasa yacewa Aliya bari ya d'aga wani waya yanzu zai kirata.

Yana katse kiran ya d'aga na Mommy Hauwa tare da sallama

Inda Mommy Hauwa ta fara zabgawa wayar harara kafin ta amsa sallamar ko gaisuwar da yake mata bata tsaya amsawa ba tace "Ameer yau Zara ta dawo gida da tsohon ciki Ashe da ciki ka saketa haba Ameer ban tab'a tunanin haka daga wajenka ba duk da nasan Zara bata da Hali ban tsammaci zaka mata haka ba duk da rokonka da naringa yi akan ka dubi girman Allah ka ringa hakuri da ita amma koda daka kamata da wanin ka kuma ga da cikinka ajikinta ai sai ka sausauta mata kabari ta haihu kafin ka koreta"


Ameer bai iya bari Mommy Hauwa ta cigaba da magana ba yace "Innnalillahi wa inna ilahi rajiun Mommy wlh wlh ba cikina bane kinga na rantse miki sai dai idan cikin Adnan ne dan rabona da Zara kafin na saketa kusan wata uku ban kara kusantar ta ba idan ma tana d'auke da cikina yaci ace ta haihu zuwa yanzu wlh Mommy ba cikina bane kuma zan iya rantsuwa da Al Qurani ina Zaran take kibani ita ta rantse tace cikina ne"

Mommy Hauwa jikin ita da Aunty khadija ne yabi yayi sanyi aka rasa wanda zai iya magana acikinsu

Sai da Ameer ya kara cewa Hello

Mommy Hauwa Tayi k'arfin halin cewa "Zara bata kusa Tayi bacci"


Ameer da sauri Yace "Mommy zanzo dakaina gobe nazo da Qurani indafa ta dafa indai ta dafa tace cikina ne wlh zan amshi cikin"

Mommy Hauwa magana takeso Tayi Ameer yayi sauri ya katse dan ransa ya bala'in b'aci jefar da wayar yayi yana wani irin huci dan bai tab'a tunanin Rainin hankalin Zara ya kai haka ba shi zata bawa cikin Adnan k'arfi da yaji lailai batasan waye shi ba dan indai akan wannan cikin ne har kotu sai suje.


Ameer kiran da bai kara yiwa Aliya ba kenan sabida b'acin rai inda Aliya duk tabi ta damu da rashin kiran nasa kamar ta kirashi haka ta ringa ji.


Mommy Hauwa kuwa Ameer yana katse wayar ta zuba uban tagumi hawaye na zubo mata Aunty khadija kuwa ajiyar zuciya ta sauke cikin tsananin tausayin jarrabawar da yayarta ke tagani akan y'ay'yanta tace "Kiyi hakuri Aunty Hauwa watarana komai mai wucewa ne insha Allahu dan Allah karkisa tunani aranki ki kamu da hawan jini"


Hawaye Mommy Hauwa ta share tace "na nawa kuma khadija sai dai kuma hawan ruwa khadija ina ganin jarrabawa akan yaran nan daga yan shaye shaye sai mai bin maza wanan wane irin rayuwa ne khadija ke shaida ce banyi wa iyayenmu haka ba bansan ya nawa yaran suke min haka ba"


Aunty khadija da sauri tace "ki daina fad'ar haka Aunty Hauwa kiringa musu addu'ar shiriya insha Allahu Allah zai shirya miki su kizo muje na rakaki naga dare yanayi"

"Murtala ya dawo ne"?

Aunty khadija da sauri tace " aaa har yanzu ai bai dawo daga Ghana ba shi da zuwa ma sai wata mai kamawa"


"To babu inda zani Anan zan kwana dan naga abinda banyi ba tun lokacin yarinta na sai Nayi yanzu Dr zai shiga hankalinsa"

Aunty khadija murmushi Tayi tace "Aunty Hauwa ba dai Yaji kike nufin zakiyi ba"

"Gashi kuwa kin fad'a Khadija yanzu ya zanyi idan dai wannan yaron Ameer dagaske yake cikin Zara ba nasa bane ina zan kai wannan kayan kunyar innalillahi wa inna ilahi rajiun Khadija ban tab'a kusantar zina ba amma gashi 'yar cikina harda ribar zina"

Khadija da sauri tace "aaa aunty kima kwantar da hankalinki cikin Ameer ne b'acin rai ne yasa ya fad'i haka"

Mommy Hauwa badan ta yarda ba tace to ameen

Daga nan suka cigaba da hira Aunty khadija na kwantar mata da hankali


B'angaren Adnan kuwa Zara na tafiya yaga gidan ya k'ara masa fad'i da Zafi haka ya ringa shiga d'aki yana dawowa Palo har a lokacin yana gwada wayar Ajjidde ganin idan baiji muryarta ko yaganta ba bacci bazai yi gigin d'aukarsa ba yasa ya d'auki mukullin motarsa ya nufi gidan Ajjidde a lokacin da ya isa mai gadi bai hana shi shiga ciki ba dan yariga da yasan Ajjidde ta san shi.


Adnan kuwa kansa tsaye ya shiga cikin gidan tare da nufar palon gabansa na d'an fad'uwa.


A k'asan carpet yaga Ajjidde a zaune da wani narkakken mutum tumbinsa kamar mai cikin wata Tara Ajjidde sanye take da bom shot da wani farin vest shi kuma mutumin sanye yake da gajeran wando nononsa kamar na kirjin wata buduruwar (meela)😛😛 kansa sai kyalli yake sabida sanko tukunyar shisha ce a tsakiyarsu suna ta zuka ga kwalaban cordien nan a zuzube a k'asa da can d'in coke.


Adnan wani irin zufa ne ya hau keto masa gabansa ya ringa fad'uwa jikinsa kuwa sai rawa yake cikin kinkina yace "Ajjidde"


Ajjidde juyowa Tayi da rinannun idonta da suka kad'a sukayi jajjir cikin muryar mayye tace "uban me kazo yimin a gida zanci uwarka fa dan bana san naci dan shegiya kai ka kiyayeni fa zan ci ubanka yaseen"


Lukutin mutumin dake gefenta shima d'agowa yayi cikin muryar mayyen yace "Ajjidde waye wanan mai kama da maigadinki"


Adnan sallati yasaka da k'arfi yana kallon Ajjidde zuciyarsa kuwa kamar ta fado k'asa wai matar da yake so ya aura ta zama uwar 'ya'yansa ce a cikin wannan halin wai ma tukuna waye wanan katon dake gefenta???.........

*M🅰K'OT🅰N JUN🅰*


*REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS* *P.M.L*




® REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS

ɯɛ ɖơŋŧ ʝųŞŧ ɛŋŧɛřŧąıŋ ŋɖ ɛɖųĆąŧɛ, ცųŧ ɯɛ ąٳŞơ ŧơųĆɧ ɖ ɧɛąřŧ ơʄ řɛąɖɛřŞ


# WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
# IG PML WRITERS
# https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-




*Written by*

💅💅💅 *SADNAF*💅💅💅



*Follow me on wattpad @ Sadnaf*


*dedicated to Aunty sis*💖💖


*page 31*


Adnan kamar wanda aka dasa haka ya tsaya yana kallon su jikinsa na rawa

Ajjidde kuwa cikin mayye ta cigaba da surfa mishi ashar tare da mik'ewa tana tangal tangal

Wajen Adnan ta nufa dake tsaye a bakin k'ofa ta fad'i yafi a kirga tana mik'ewa.

Adnan cikin buguwar zuciya ya cigaba da kallonta har ta k'araso gabansa ta d'aga hannunta daya mata nauyi zata mari Adnan.

Adnan yayi sauri ya rik'e hannunta yace "Ajjidde wai me haka mai yake damunki"?

Cikin muryar mayye Ajjidde tace "ubanka ne yake damuna mai yasa kake damuna ne ka fitar min daga gida"

Adnan a zuciye yafara gigirza ta yana "Ki dawo hankalinki Ajjidde Nine fa Adnan ko"""

Aman data fara shek'a mishi ajikinsa ne ya katse masa maganar da yake

Adnan cikin tsananin takaici ya rik'eta har ta gama kwara aman ta zube a k'asa idonta a rufe tana maida numfashi.

Adnan kayan jikinsa yabi da kallo cikin kyankyami ya zare rigar daga jikinsa.

Ya ajiye a gefe ya kinkimi Ajjidde yayi hanyar wajen da yake kyautata zaton d'aki ne.


Akan k'aton Royal bed d'in dake d'akin ya kwantar da ita.


ya zauna a gefenta ya zuba mata ido santa na gudun tsere a zuciyarsa ahankali yafara bin ko'ina na jikinta da kallo yana hadiyar yawu dan Ajjidde ta bala'in haduwa fatar jikinta glowing kawai yake yana kyalli kirjinta dake tsaye yafi ko'ina d'aga masa hankali tuni ya ma manta da wani b'acin ran daya tsinci kansa a ciki na halin da ya zo ya riskesu.


Ya kai hannunsa a hankali yafara shafo kirjinta yana lumshe ido

Ajjidde kuwa baccinta kawai take Adnan a hankali ya cigaba da shafata hankalinsa na tashi daga zaunen dayake.

Ganin idan ba controlling kansa yayi ba zai iya aika aika kuma bashida wanan intention d'in Aurenta kawai yake so yayi d'auke hannunsa yayi a hankali yana mai sauke nannauyan ajiyar zuciya ya mik'e ya shiga band'akin ya d'ebo ruwa Dan ya goge mata jikinta da aman ya b'ata.

K'aramin towels d'in dake Jere a band'akin ya d'auko d'aya ya tsoma acikin ruwan ya goge mata jikinta dashi ganin vest d'inta ya jike yasa ya cire mata.


Adnan kamewa yayi a lokacin daya cire mata vest d'in yasha huld'a da 'en mata iri iri amma Ajjidde ta daban ce numfashinsa ke fita Sauri da Sauri sai da yayi dagaske ya iya saisaita kansa bayan ya k'ara shafo kirjin nata da kai musu wani irin zazzafan kiss kamar ya haye kanta haka yake ji.

Farin lallausan bargon dake gefen gadon ya janyo ya rufeta ya bar fuskarta awaje ya cigaba da kallonta sai a lokacin ya tuna da k'aton daya zo ya tarar dasu a tare take Yaji ransa ya baci wani irin bak'in kishi ya rufe shi da Sauri ya mik'e yayi palon inda ya tarar dashi da shirgegen cikinsa ya baje yana ta munshari.

Adnan ji yake kamar ya rufe shi da duka inda kuma yafara tunanin mai had'in Ajjidde da mutum irin wanan da ya kusa haifarta wanda ko kyan gani bashi dashi sai wani zuciyar nasan rayya masa Ajjidde zaman kanta take kila saurayinta ne lura da dukansu biyun babu suturar arziki a jikinsu sai kuma yayi Sauri ya kau da tunanin haka a ransa dan sam bayasan wani abun da zai sa yayi mummunan tunani akan Ajjidde yanda yake jinsa duk aibun halin Ajjidde bazai iya rabuwa da ita ba dama yasan hardly mace ta zauna ita kad'ai batare da ta samu wani tangarda a tarbiyyarta ba fatansa dai Allah yasa a iya shaye shayen ta tsaya kuma wanan katon daya gansu taren Allah yasa d'an uwanta ne da sannu zai hanata shaye shayen da wanan tunanin hankalinsa ya d'an kwanta bayan ya kaiwa katon mutumin naushi a ciki amma ko gezau mutumin baiyi ba.


Adnan haka ya zauna a palon yana duba agogo akai akai yana lek'o d'akin Ajjidde yaga ko ta farka dan Sam bazai iya tafiya yabarta da wanan shirgegen mutumin ba.


Ajjidde ba ita ta tashi ba sai wajen ukun dare a lokacin Adnan Yana rik'e da rigarsa da amai ya b'ata yana gyangyadi.

Ajjidde sai da ta samu minti goma sha biyar a zaune tana karewa kanta kallo sannan ta tuna kamar Adnan yazo gidan tana cikin mayye zata iya tuna a Palo ta zauna ita da Alhaji Al gazaru suna shaye shayen su to waye ya kawo ta d'aki ina Alhaji Gazarun"


Da wannan tunanin ta duro daga kan gadon ta d'auki k'aramin towel ta kare kirjinta dashi ta nufi palon.


Mamakine ya rufeta a lokacin data ga Adnan a zaune akan kujera yana gyangyadi Alhaji Al gazaru a baje a k'asa yana ta zuba munshari.

A take tunanin ta ya bata Adnan ne ya maidata d'aki ya dawo Palo ya zauna.


Juyawa tayi ta kalli agogon palon taga uku har da rabi wajen Adnan ta nufa tana rik'e da towel d'inta a kirjinta tana tab'a shi yayi Sauri ya bud'e idonsa.


Ajjidde fuska a d'aure tace "Ya akayi baka tafi gida ba"?

Adnan zuba mata ido kawai yayi yana kallonta take Yaji hankalinsa ya tashi dayaga yanda ta d'aura fuska.

Ajjidde kau da kanta tayi daga kallonsa tace " Adnan kana crossing limitation d'inka zan iya fasa auranka tunda ka kirani kaga ban d'aga ba ya kamata ka san takura ne banaso ga d'aki can kaje ka kwanta idan gari ya waye sai ka tafi dan dare ya Riga da yayi zamuyi magana gobe kafin ka tafi"


Daga haka ta juya ta nufi d'akinta


Adnan bin bayanta yayi da kallo har ta shige ya hadiyi wani irin yawu mai tauri dan yasan tabbas ya d'ebo ruwan dafa kansa dan Sam bai Samu fuska a wajenta ba ballantana har yayi mata

Please Login or Register in order to submit comment