Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

mata uku amma me ya gwammaci ya ringa aikata zina yana Neman matar aure wlh Ameer ban ragi Adnan da komai ba ina iya bakin k'ok'arina dan naga na faranta masa amma ina duk abinda nake yi baya gani yana can yana hangen Na Haram Allah ya shirye su idan suna da rabon shirya"

Ameer k'afe Aliya kawai yayi da ido yana kallon yanda take magana cikin nutsuwa da tarin ilimi a hankali ya waiga ya kalli tashi watsatsiyar matar dake kwance lifelessly da tarin zunubi yayi mata yawa ga rashin bin iyaye ga rashin bin miji ga cin amanar Aure uwa uba ma Wanda ya halliceta ba kasafai take bauta masa ba"

A tunzure ya nufi wajenta sabida k'unnar da zuciyarsa ke yi

Bai tsaya neman ruwan da zai watsa Mata ba sabida ta farfad'o daga suman da tayi ya mata wani mugun bugu dayasa Zara sakin wani marayan k'ara.

Shak'eta yayi tare da mik'ar da ita

Zara kuwa ta yi lagwaf kamar mattaciya a hannunsa ya d'aka mata wani mummunan tsawan daya sa ta tsaya akan k'afafunta duk da cewar gidan juya mata yake yi kanta kuwa kamar ya fad'o sabida azabar da take sha.


"Inaso kafin na kirga biyar kije ki kwashi duk wani Abu da kika san naki ne ki bar min gida na sakeki saki uku idan ana saki d'ari ma ni na miki na tsaneki Zara bana kaunar in bud'e inganki wlh wlh wlh idan sai na yafe miki zaki shiga aljanna bazan tab'a yafe miki ba kije ki had'a kayanki kizo kicigaba Da zama da kwartonki duniyace da sannu zata koya miki hankali ki wuce kafin zuciya ta d'ebeni na kasheki da hannuna.


Zara yunkurawa tayi dan ta fice da gudu ta zub'e a k'asa sabida jirin da ya kwasheta.

Ameer a fusace ya bita ya damkota ya fara janta a k'asa har suka fice daga palon.


Aliya hawaye ne suka fara zubo mata data fara bin ko'ina da kallo take ta tuna ranar da aka kawota cikin gidan zuciyarta fal farinciki sabida an kawota gidan masoyinta soyayya da suka sha da Ameer a cikin palon ne duk ta ringa tunowa take ta fashe da wani irin kuka ko shekara batayi da Aure ba amma ji kaddarar da ta fad'a mata kuka take sosai tana kallon k'ofar d'akin Adnan tamkar shi take kallo a hankali ta fara bin hotunan su dake cikin bangon palon duk suna murmushi sukayi hoton wani irin mik'ewa tayi ta fara Ciro hotunan tana wurgi dasu sai kuka take.

Adnan kuwa tunda ya shige d'akinsa ya samu ya kulle k'ofar d'akin ya zub'e a k'asa yana jin irin zugi da rad'ad'in da jikinsa ke masa kamar ya cire kansa ya wurgar sabida azabar dayake masa dan Ameer yafi bugunsa a fuska Wanda hakan ya haddasa masa mummunan ciwon kai gabansa ma kuwa kamar ya tsinke ya yar sabida yanda yake shan azaban zafi.


Numfashi kawai yake fitarwa da k'yar duk abinda su Ameer suke yi yana ji juyi kawai yake na azabar dayake ji.


Ameer kuwa sai daya k'ara dan mamangarar Zara data ringa zub'e masa a k'asa dayace ta kwashe kayanta.

Ahaka Zara ta ringa kwashe kayanta tana zub'ewa a k'asa Ameer kuwa a zuciye ya ringa fitar da kayanta waje jikinsa rawa kawai yake.


Sai daya gama kwashe kayan Zara tas babu abinda ya rage acikin gidan daya wuce kayan d'akin ta

Ya damki Zara ya wurgar da ita kusa da kayanta yace tasan inda dare ya mata kafin ya dawo.


Adai-dai lokacin Aliya itama tafito daga b'angarensu bayan ta gama yiwa gidan kallon k'arshe tana share hawaye


Ameer dake kulle k'ofar b'angaren su juyawa yayi yana kallon Aliya dake ta share hawaye tana nufar bakin gate ko kallon inda shi da Zara dake kwance a k'asa batayi ba


Da sauri ya tadota adai-dai lokacin da ta fice daga gidan yace "Aliya ki tsaya na tare miki abun hawa na rakaki har gida dan motata tana company mu"


Aliya juyawa tayi a hankali ta kalleshi tace "karka damu Ameer basai ka wani rakani gida ba ba zan iya zuwa gida dakaina"

"Dan Allah Aliya kibari na raka ki gida bai kamata aga kina tafiya kina kuka ba nasan abinda Adnan ya miki da ciwo nima yanda kike ji haka nake ji a zuciyata amma ya za muyi hakuri zamuyi Allah ya bi mana hakkinmu"


Aliya murmushi tayi mai ciwo tace "hakane Ameer ngd amma ka bashi ngd "



Babu yanda Ameer bai yi da Aliya ba akan ta bari ya tare mata abun hawa ya rakata gida tak'i akan dole ya rabu da ita ta hau tricycle ta tafi.


Ameer kuwa sai da ya daina hango tricycle d'in data hau ya koma ciki a fusace ya ya nufi wajen da Zara ke kwance kusa da kayanta tana cije lebb'e sabida azabar da take sha Ameer damkota yayi yana janta da k'asa har sai daya kaita can waje.

Ya koma ya ringa kwasar kayanta yana jefa mata har sai daya gama kwashe wa ya jefa mata dubu d'aya akan ta hau mota ta tafi gidansu baya san ganinta idan kuma zata dawo wajen kwartanta ne su cigaba daga inda suka tsaya ne to ta fara zuwa gida asan cewar shi yanzu ba mijinta bane"

Zara da azabar da take ciki ma kawai ta isheta banda jiri jiri dake dibanta kwanciya kawai tayi akan kayanta tana numfarfashi.


Ameer kuwa wayarsa ya Ciro daga Aljihunsa ya kira Mommy Hauwa awaya aikuwa tana d'agawa Ameer ya fara gaya mata duk abinda ya faru ya kuma ce Bai saketa ba sai da ya gansu da idonsa dan haka karta ga laifinsa.


Mommy Hauwa suman zaune tayi kawai tana sallati har Ameer ya kashe wayarsa bata dawo dai-dai ba.....

*M🅰K'OTAN JUN🅰*


*REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS* *P.M.L.*



*REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS*
(P M L)
​ɯɛ ɖơŋ'ŧ ơŋٳყ ɛŋŧɛřŧąıŋ ŋɖ ɛɖųĆąŧɛ, ცųŧ ɯɛ ąٳŞơ ŧơųĆɧ ɖ ɧɛąřŧ ơʄ řɛąɖɛ'Ş​


#WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
​#IG PML WRITERS​
#https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035
#http://maryamsbello.blogspot.com


*written by*

💅💅💅 *SADNAF*💅💅💅



*Follow me on wattpad @Sadnaf*



*WANNAN SHAFIN NAKUNE 'YAN GRP D'IN SADNAF NOVEL NGD KWARAI DA KAUNARKU GARENI JINJINAN BAN GIRMA GAREKU HUGUMA CONVERSATION ROOM INAJIN DADIN COMMENT D'INKU FIYE DA TUNANIN MAI TUNANI FADEELA Y KHAN MAMAN MAMY INA GODIYA DA KAUNARKU AGARENI MY WATTPADIANS FOLLOWERS WLH INA ALHAFARI DAKU INAJIN DADIN KWARIN GWIWAR DA KUKE BANI TNX SO VERY MUCH*



*MY OND EN ONLY GUARDIAN AUNTY SIS💖💖💖 AM PROUD TO HAVE U BY MY SIDE WISH U OLL D BEST*



*page 22*


Zara wajen Adnan ta nufi dake mata wani irin kallon da bata gane ko na k'yamarta ne ko kuwa na kiyayya.


Zama tayi a gefensa ta k'au da fuskarta sabida kar yaga wawulon nata tace cikin sanyin murya

"Ad wlh Ameer ya cuceni dan Allah dubi yanda ya cire min hak'oran gaba kamar wata tsohuwa Pls ka shirya anjima ka kaini asaka min hakoran roba bazai yiwu na zauna haka ba kai kanka nasan zaka iya tsanata"

Ta juyo tana kallonsa dan taga yanda ya k'arbi maganarta

Adnan mik'ewa yayi ya nufi hanyar band'aki yana "banida kud'in da zan kai ki asaka miki hakoran Roba yanzu duk ke kika jawo mana halin da muke ciki yanzu ciki kuwa har da aikina danake Neman rasawa dan a sanadinki na fara wasa da aikina ni ayanzu mafita kawai nake nema da zaki taimakawa kanki da kin tafi gidanku k'illa su taimaka miki su kaiki asibiti asaka miki hakoran robar inyaso nima idan nasamu nutsuwa sai mu san nayi"

"Ad u must be joking idan ana magana ka daina cewa in tafi gidanmu domin mahaifina ya Riga da ya haramta min zuwa gidansa ko da kake cewa laifina ne Ad all I did is because of d love I have for u ka daina blaming d'ina and babu yanda za'ayi kace min bakada kud'in da za'a samun hakoran roba sai dai kawai idan rashin mutunci ka taka"

Adnan wani irin kallo ya watsa mata yace "Ke kiringa tauna magana kafin ki fad'a min ita idan ba haka ba wlh ubanki zanci dan naga alamar bakida kunya kowace irin magana ta fito bakinki fad'inta kawai kike tunda nake da Aliya bata tab'a min rashin kunya ba so ki kama kanki inada kudin bazan biya bane kuma wlh idan kika isheni korarki zanyi dan kina neman zame min masifa ko ma nace kiringa kin zame min"

"Ad ni kake gayawa magana san ranka? ina san daka ce kana yimin tun ba'aje ko'ina ba kana neman juya min baya"

Tsaki Adnan yayi ya shige band'aki wani irin haushin Zara na rufe shi dan kamar yaje ya rufeta da duka da take magana dan tamkar ba ita ba dan Tayi wani irin muni.


Ameer kuwa su Alhaji Abubakar na tafiya ya koma ciki yayi wanka ya shirya ya fita.

Minti goma da fitarsa sai gashi ya dawo da katon akori kura da wasu maza majiya k'arfi suka shiga gidan suka hau fito da kayan Zara suna lodawa aciki sai da suka kwashe komai daya kasance na Zara ne ko cokali basu bari ba.


Ameer ya basu kud'i ya musu kwatancen gidansu Zara yace su kai kayan gidan.

Suna tafiya shima ya hau fiddo da kayansa masu mahimmanci yana lodawa acikin motarsa sai da ya kwashe komai nasa sai gadonsa da rage bai d'auka ba.

Ya kulle gidan ya hau motarsa ya nufi gidansu dan ya kai kayan nasa.


Dangin tuni suka zagaye Aliya kowa nasan nuna bajintarsa ta hanyar kula da ita dan Mahaifinta mutumin kirki ne gashi dan dangi kowa sai tofa albarkacin bakinsa yake ana la'antar Adnan dan duk anfad'a musu abinda Adnan yayi mata.


Aliya kuwa d'auriya kawai take ta na nuna musu hankalinta akwance yake amma can k'asan zuciyarta ita kad'ai tasan mai take ji.


Mommy Hauwa tunda aka fara shigo da kayan Zara hankalinta ya k'ara tashi ta rasa mai ke mata dadi jiya ko kad'an batayi bacci ba sabida batasan inda Zara take ba ballantana ta san halin da take ciki.


Tana tsaye suka gama shigo da kayan suka tafi.

Zama Tayi a tsakar gidan tare da zubawa kayan ido hawaye suka hau zubo mata.

Sunanta da Dr ya kira ne yasa ta d'ago tana kallon shi

Sai da ya k'arewa kayan dake zub'e a harabar gidan kallo ya maida kallonsa kan Mommy Hauwa da ta zuba masa ido tsoro ya bayyana a fuskarta.


Dr wani irin murmushi dayafi kuka ciwo yayi yace "Zara ta kaso Auren nata kenan to yayi kyau amma inaga kinada masaniyar nace kar Zara ta sake ta k'ara taka k'afarta tazo gidanan ko da mutuwa nayi banyarda abarta tazo cikin gidanan ba idan kuwa kika barta wlh bazan tab'a yafe miki ba kuma yanzu na kara jadadda miki ko ayanzu data kaso Aurenta ban yarda tasa k'afarta ta tako gidanan ba taje duniya ce ta ishi kowa Riga da wando insha Allahu sai ta kwashi dashin da ta zuba da hannunta"

"Haba Dr bai kamata kace haka ba karka manta Zara bata da sama damu ina zata je Indan kace kar tazo gidanan dan Allah kayi hakuri ka yafe mata matakin daka d'auka akanta yayi tsauri duk lalacewa 'yarmu ce bazaka so ta tagayyara ba dan Allah ka yafe mata abinda tayi ma"

"Hauwa yarinyar da ta bud'i baki tace min bak'in mugu azzalumi Allah ya isa bazata yafe ba ita kike cewa na yafe mata kema kinzo da ganganci wlh bazan tab'a yafe miki ba idan kika bari ta shigo min gida kaf cikin 'ya'yana babu Wanda ya tab'a min abinda Zara Tayi min dan har dangina zan kira akan ban yarda su saurari Zara ba idan taje musu ban kuma yarda su taimake ta ba"


"Haba Dr dan Allah ka daina cewa haka hannunka baya rub'ewa ka yanke ka 'yar kayi hakuri yarinta ne"

Mommy Hauwa tace cikin matsanacin kuka tana Jan majina


Dr Tsaki yayi ya shige ya barta awajen.

Mommy Hauwa ta k'ara fashewa da kuka ta d'auki wayarta tana kiran layin Ameer.


A lokacin Ameer har ya sauke kayansa a gida ana gyara masa d'akinsa shi kuma ya tafi office yana kan aiki kiran Mommy Hauwa ya shigo wayarsa.


D'agawa yayi da sallamarsa kukan da mommy ke yasa jikinsa yayi sanyi

Ba tare da b'ata lokaci ba mommy Hauwa tace "Ameer kaga har yanzu Banga Zara ba bata zo gida ba gashi har an kawo mata kayanta"


Ameer shiru yayi ya rasa mai zai cewa Mommy Hauwa sai data k'ara cewa hello yayi sauri yace

"Mommy wlh bansan inda Zara take amma ni nasan duk inda take hankalinta a kwance yake amma zan duba miki wajen saurayin nata dan k'ila tana wajensa".



Mommy Hauwa runtse idonta tayi sbd wani irin d'aci ta take ji a mak'ogaranta idan dataji Ameer yace saurayin Zara tana bala'in jin haushin kalmar bata iya cewa Ameer komai ba ta kashe wayar.


Ameer kuwa yabi wayar da kallo yana girgiza kai dan yana bala'in jin tausayin Mommy Hauwa.

Tunanin ya fara yi inda Zara zata tafi tunda ba gidansu taje ba

take Adnan ya fad'o masa arai

Zai kuwa yi mamaki idan Zara na wajen Adnan amma dan ya tabbatar anjima zai lek'a gidan yaga ko Adnan ya dawo dan idan Zara bata wajensa dole zai iya sanin inda Zara taje.

Adnan da Zara kuwa kamar wasu tom en Jerry dan in banda hararar juna babu abinda suka ringa yi abinci ma daban daban suka ci haushin juna kawai suke ji

K'arshe ma Adnan ficewa yayi ya barta a d'akin ita kad'ai dan wani mugun haushin ta yake ji idan ya tuna halin da yake ciki na aikinsa dake rawa sai hankalinsa ya tashi gida yake so yaje dan yasan by now Ameer baya nan

Bai tsaya b'ata lokaci ba ya hau motarsa ya nufi gidan nasu.


Yana parking a k'ofar gidan

k'aton motan company su na parking gabansa ne ya yanke ya fad'i a lokacin dayaga ma'aikatansu su uku sun fito daga motar mataimakin ogansa shima ya fito daga bayan motar sun nufi cikin gidan.


Adnan jiki na rawa ya fito daga motar yabi bayansu a zuciyarsa ya ringa tunanin k'ila zuwa sukayi suce ya koma bakin aikinsa.

Suna k'ok'arin k'wank'wasa k'ofar suka lura da Adnan dake tsaye abayansu jikinsa na d'an rawa.


Cikin d'aurewar fuska mataimakin ogansa yace

"Dama wajenka muka zo"

Hannu ya zura a Aljihunsa ya d'auko wani farin envelope mai d'an nauyi ya mik'awa Adnan.


Adnan kuwa k'asa k'arba yayi gumi na tsatsafo masa cikin rawar murya yace "takardar me wannan"?

" ka k'arba takadar sallama ce oga yace mu kawo maka dan har ya Samu Wanda zai maye gurbinka takardunsa ma yafi naka kyau dama idan baka manta ba sabida Alhaji haruna yayi maka alfarma ya k'arbeka Bawai dan ka cancanci ya d'auke kan ba yace ka kwashe kayan ka gabad'aya daga cikin gidan gobe wancan zai dawo cikin gidan amma kar ka damu akwai dubu d'ari biyu dake Cikin takadar zai isheka ka d'an rage Zafi kasan oga akwai shi da mutunci da tausayi"


Adnan wani razanan ihu ya k'wala yana zub'ewa ak'asa tare da kamo k'afar mataimakin ogansa nasa "ka taimaka kayimin rai ka roki oga kar ya koreni daga wajen aiki wlh dashi na dogara yanzu daga ina zan fara wlh ko fili bani dashi ballantana gida nashiga uku na lalace a ina zan zauna idan ya koreni daga gidanan"


Mataimakin ogansa fusge k'afarsa yayi yace "kayi hakuri Adnan aikin da aka samu muke yi yanzu ma haka wadanan da muke tare dasu cewa akayi su tayaka fito da kayan dan ayau zasu kwaso kayan wancan d'in su dawo dashi nan ka tashi ka bud'e mana k'ofa su shiga su fara fito da kayan"


Adnan ihu ya k'ara sawa ba sallati ba komai ya fara birgima a k'asa kamar wani k'aramin yaro yana cewa suyi mishi rai suje su rok'i ogansu daga ina zai fara.


Mataimakin ogan nasa yana ganin Adnan na b'ata musu lokaci ya basu umarni su b'alle k'ofar su shiga su fara fito da kayan.


Aikuwa cikin minti uku suka lalata mukullin suka fara fito da kayan daga cikin gidan.


Adnan kuwa sai ihu yake yana birgima.


Ana cikin fito da gadon Aliya suka ji k'aran bud'e gate d'in gidan

Adnan da sauri ya waiga tare da tashi daga k'asa aikuwa sai ga yan gidansu Aliya sun shigo fuskarnan tasu a d'aure mamakine ya rufesu dasu ga Ana fito da kayan Aliya tamkar sun san zuwa suka yi su kwashe kayan dan Alhaji Abubakar tuni ya azalzale su akan su zo su kwashe kayan Aliya ko cokali karsu barwa Adnan ballantana ya mora.



Gaban Adnan ne ya k'ara fad'uwa a lokacin dayaga sun bud'e gate d'in gidan gabad'aya a kori kurar da zasu kwashe kayan dashi ya shigo cikin gidan ko kallon inda yake basu yi ba suka fara kwasar kayan Aliyan suna sawa a mota


Adnan Hannu ya k'ara d'orawa aka dan inka d'auke kayan sawa komai na cikin gidan na Aliya ne .


Cikin minti Arbain danginsu Aliya suka gama kwashe kayan suka k'ara komawa ciki dan su tabbatar da babu abinda ya rage a cikin gidan ganin babu abinda ya rage yasa suka je suka hau motarsu suka tafi bayan sun zubawa Adnan wani mugun kallo.


Adnan kuwa helplessly ya zauna kawai yana bin suturunsa dake watse a k'asa da kallo adai-dai lokacin da suma 'yan company nasu suka rufe gidan da sabon kwad'o suka bar shi azauna awajen da kayansa agaba da takadar sallamarsa daga aiki.


Adnan yafi k'arfin minti arbain a zaune a k'asa yana tunanin daga inda zai fara ina zai dosa a cikin kwana biyu ya had'u da iftilai haka na farko ya rabu da Aliya matarsa saliha mai kaunarsa na biyu ya rasa aikinsa na uku bai san daga ina zai fara ba"


A hankali ya d'aga kansa ya kalli k'ofar b'angarensu da aka kulle da sabon mukulli wani irin bak'inciki da danasanin abinda yayi ya rufe shi tabbas Aliya rahama ce a gare shi gashi daga rabuwa da ita ya rasa aikinsa ya rasa komai nasa.

Zara kuwa masiface agare shi dan sai daya fara muamalla da ita ya ringa had'uwa da masifu iri iri dan sabida ita ya ringa wasa da aikinsa har aka sallame shi ga mugun dukan dayaci a hannun Ameer duk asanadiyar ta wani mugun tsanar Zara ne ya darsu a ransa yaji inama ya ganshi a gabanta da shi ma sai ya cire mata sauran hakoran dan duk ita ta jawo masa wanan masifar.


Ganin ya zaune lokaci nata tafiya yasa ya mik'e ya fara tattara kayansa yana cusawa a katon jakarsa sai da ya gama saka kayansa ya zuge jakar da k'yar ya d'auko envelope d'in da suka ajiye masa a k'asa yasaka a cikin Aljihunsa yafara Jan jakar dan bazai iya d'aukar jakar ba sabida nauyi.


Bai sha wahala samun abun hawa ba ya hau nufi hotel d'in da ya kama.


Tunda ya fita Zara wani irin Zazzabi ya rufeta Wanda sai da ta shige cikin bargon sabida sanyin da take ji d' Tayi amai ya kai sau uku tunda take bata tab'a irin wanan zazzabin ba sai baccin zazzabi ya fara kwasarta sai taji zuciyarta na tashi sai ta nufi band'aki da gudu.


A cikin wanan halin Adnan yazo ya sameta tabi Tayi zuru zuru.


Ko sallama bai yi mata ba inbanda mugun hararar daya watsa mata ya ajiye jakar da ya shigo dashi gefe ya nufi band'aki dan ya watsa ruwa ko zai ji sanyi a zuciyarsa.

Zara binsa kawai ta ringa yi da ido sabida bazata iya magana ba sabida halin da take ciki.

Tana kallo ya fito daga wanka yazo ya canja kayan jikinsa ya Ciro envelope d'in daga cikin kayan daya cire ya Ciro wrapper dubu dubu guda biyu ya ajiye agaban mudubin d'akin ya fice daga d'akin yana watsa mata harara.


Zara kuwa mik'ewa Tayi da sauri duk da bata jin dadin jikinta ta nufi gaban mudubin ta d'auki wrapper d'aya na kud'in ta koma ta kwanta dan ta samu kud'in da zata saka hakorin roba abakinta sai dai duk abinda Adnan zai yi yayi.

Tana kwanciya Adnan ya shigo da plate d'in abinci a hannunsa

Ya zauna akan kujerar dake d'akin ya fara cin abincinsa batare da kalli inda Zaran ke kwance ba fried rice ne dayaji kayan had'i da luk'a luk'an cinyar kaza ga maltina a gefe yana korawa idan ya had'a ido da Zara sai dai ya zabga mata harara dan gabad'aya gani yake itace matsalarsa .


Zara kuwa duk da bata tabbacin zata iya cin abincin sabida rashin appetite mik'ewa Tayi daga kwancen da take tace

"Ad ina nawa abincin nima fa yunwa nakeji ga wani irin zazzabin dake damuna"

Adnan ko d'agowa baiyi ba ya cigaba da cin abincinsa

Zara k'ara nanata maganar tayi

Adnan ya d'ago a fusace yana "idan yunwa kike ji ki tafi gidanku mana mai hadina dake naga dai ba hakkina bane na baki abincin Zara inda kin san tsanar Dana miki da baki tsaya kina min magana ba da kin tashi kin tafi gidanku dan babu abinda zanyi dake dan zama dake masifane a gareni kin janyo min asarar da bazan iya mayar ba asanadiyarki na rabu da matar da har na koma ga Allah bazan tab'a samun irinta ba asanadiyarki na rasa hanyar cin abincina asanadiyarki na rasa inda zan zauna babu abinda kika janyo min sai asarori Zara if u knw wat is good for u wlh ki tafi gidanku idan kuwa kika dage akan zaki zauna dani wlh sai na lahira yafiki jin dadi I would make your life a living hell ki daina kallona da wanan katon wawulon bakin naki I hate u"


Zara da kalmomin sa suka masifar girgiza ta hawaye ne ya hau wanke mata fuska take wani irin ciwon kai ya rufeta babu tunanin da take da ya wuce idan Adnan ya koreta ina zata nufa mai ta jawo wa kanta ne ita tana tunanin rabuwarta da Ameer shi zai sa Adnan ya aureta cikin sauki sai gashi tun ba'aje ko'ina ba yana gwada mata irin tsanar daya yi mata"

Zuba masa ido Kawai tayi tana sheshek'ar kuka

Adnan kuwa ya cigaba da cin abincinsa hankali sa kwance sai daya gama ci tsaf yayi gyatsa ya mik'e ya nufi gaban mudubin daya ajiye kud'i dan fita zaiyi ya nemi gidan da zai kama haya dan bai ga ta zama ba gobe kudin hotel d'in Zai yi expire.

Turus yayi daya ga babu wrapper d'aya ya juyo yana kallon Zara data zama statue tana kallonsa hawaye na zubo mata


"Ke ina kudin Dana ajiye Anan yake"?

Adnan yace cikin mugun d'aurewar fuska dan Zara tasan ba wasa yake da ita ba.


Zara wani irin d'auriya da k'arfin hali ne yazo mata ta koma ta kwanta tace " kabani ajiyar kudinka ne ka tambayi gaban mudubin ya gaya maka inda ya kai kudinka"


"Zaraaaa kina hauka ne kina san naci ubanki na k'arasa cire miki ragowan hakoran da suka miki Saura ko zaki bani kudina ko kuwa ashe bayan iskancin ke barauniya ce ya daga ni sai ke a d'aki zan nemi kudin Dana ajiye na rasa Zara don't try my patient wlh zan sauke duk haushina akanki na miki dan bazan duka na kakaryaki kifito min da kudina"


Zara duk da ta tsorata sabida yanda Adnan ya koma tamkar wani zaki d'aurewa tayi dan Sam bazata iya bashi kudin ba bashi kudin na nufin ta cigaba da zama ahaka ba hakora ko ita da take da kanta bata sha'awar kallon kanta a mudubi sabida munin da tayi inaga kuma wani ya ganta ahaka ita tasan rashin hakoran ne ma yasa ya tsaneta tashi d'aya.


Cikin fad'uwar gaba ta juyar da kanta tace "sai kayi kuma ni ban d'aukar maka kud.."


Adnan bai bari ta k'arasa ba ya fuzgota daga kan gadon ya hau kwallo da ita yana cewa ta fito masa da kudinsa

Zara kuwa sai ihu take tana neman taimako

Ganin Adnan na dukanta cikin fitar hayyaci yana neman aikata lahira yasa tayi sauri tace "ka tsaya zan baka wallahi kar ka kasheni"


Adnan tsayawa yayi yana maida numfashi yace "maza bani barauniyar Banza barauniyar wofi"


Zara da sauri ta d'aga katifar ta d'auko kudin tana mik'a mishi tare da tare jinin dake zubowa cikin hancinta wani irin jiri na d'ibarta yana k'arbar kud'in ta zube

Please Login or Register in order to submit comment