Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

a hankali ya runtse idonsa shima hawayen tausayin Aliya na zubo mishi yana zabga mata addu'a.

Nurses d'in da suka shigo dan su baiwa Adnan da Dr taimakon gaggawa suna d'an yayyafa musu ruwa suka farfado.

Inda Dr yafarka da sallati yana zabga wa Zarah addu'a jiyake inama ace shi mutuwa ta d'auka ba Zara ba.


Adnan kuwa Zumbur ya mik'e bai ko ji nauyin da kansa ke masa da jirin dake d'ibansa ba ya nufi wajen Gawan Zara jikinsa na wani irin k'yarma tsoron Allah na shigarsa ko ta ina Addu'a yake yi Allah yasa Zara dogon suma tayi ba Mutuwa ba.

Tsugunna wa yayi a bakin gadon ya janye rufin Zanin daga fuskar Zara.

Mommy Hauwa da Aunty khadija da ta Dade da maidata gefe tana tausarta tana gayyato mata duk wani d'auriya a matsayinta na uwa akan ta d'aure sabida sauran yayanta kar ta d'aga musu hankali sabida irin kukan da take karta manta kowane rai sai ya dandana mutuwa Ba kuka ya kamata tayiwa Zara ba addu'a ya kama ta tayi mata inda kamar da remote take controlling d'in ta Dan take ta fara rage kukan da take yi ta fara sallati a zuciyata ta fara duk adduar da yazo bakinta Adnan Suka zubawa ido daya tsugunna agaban Gawan Zara yana bud'e fuskarta mommy Hauwa tayi sauri ta kau da kanta wasu sababin hawayen na kara bulbulo mata gani take kamar Mafarki take wai Zara ta mutu Zaran da take adduar Allah ya bata dama tayi tsaftaciyar rayuwa dan a yanzu ta fito daga duhu zatayi rayuwa a haske a yanzu ne Zara zata san rayuwa ta san mai take yi sai gashi Allahn daya bata Zara ya k'arbi abunsa.

Adnan kuwa kallon Zara kawai yake kirjinsa na sama da k'asa hawaye na zubo mishi ya kasa yarda wai Zara ta mutu a tsakiyar lokacin da yake bukatar ta kuma ta mutu ta sanadiyar cikin daya mata runtse idonsa yayi da k'arfi daya tuno shine sanadin shigarta koma mai tayi dan da bai taka k'afarsa ya shiga b'angarensu ba babu Yanda za'ayi har Zara ta kauce hanya da babu Yanda za'ayi tak'i zaman aure har tayiwa mijinta biyayya banda dan banzan wahalar da ya bata ya mata sanadin mutuwar Aurenta ga dan banzan dukan da ta ringa sha a hannunsa cima ta arziki babu banda wulak'anci da ya ringa zuba mata sai gashi a lokacin daya gane gaskiyar abinda yake aikatawa yazo dan ya gyara kuskurensa ya biya mata bukutar ta da ta Dade tana mafarkinsa na hanyar Suyi Aure sai gashi Zara ta tafi mutuwa ya d'auketa ta bar shi da mugun nauyin da har ya mutu bazai daina jinsa ba dan bazai iya yafewa kansa abubuwan da yayi mata ba wani irin kuka ya fashe dashi yana "Zara meyesa kika tafi a lokacin danake bukatarki meyesa baki bari munyi aure munyi tsaftaciyar rayuwa ba kika tafi kika barni ni d'aya abun da kika Haifa da zan ringa gani ina tunaki ma ya biki kuka barni ni kad'ai Alhalin banida sama daku yanzu da wa kukeso nayi Rayuwa Zara inama Mutuwa tare ya d'auke mu muje muyi rayuwarmu acan Zara dan Allah ki tashi dan nasan bazaki min haka ba bazaki tafi ki barni ba Wlh na gane kuskurena bazan k'ara zallintarki ba nima Allah ya shiryeni nagane abubuwan da nake yi basu da kyau "


Adnan kuka yake sosai har yana shid'ewa numfashinsa na d'auke wa .


Mommy Hauwa kuwa girgiza kanta kawai take yi tana sallati dan ita kad'ai tasan mai takeji.
Dr kuwa waje yayi duk da jiyake kamar iska zata d'auke shi ahaka yaje ya zauna acan nesa da asibitin yasamu waje ya zauna yafara Rusa kuka kamar wani k'aramin yaro dan yaji mutuwar Zara fiye da tunanin mai tunani dan kaf cikin 'yayansa yafi santa dan sunan mahaifiyarsa da taci da kamanin da suke da ita mutuwar Mahaifiyarsa dawowa yayi sabo fil a zuciyarsa inda kukan ya zame masa guda biyu na nadamar abubuwan da ya aikatawa Mahaifiyarsa da yafiyar ta da bai samu ya nema ba har ta mutu har gwara Zarah ita ta nemi yafiyarsa shi fa da har Mahaifiyarsa ta mutu bai nemi yafiyar ta ba da kila har ta mutu da bakincikinsa a ranta inama shima yasamu damar da 'yarsa ta samu haka kawai ya danganta duk abubuwan da yayi ne Allah ya jarrabce shi ta silar 'yarsa.


Ahaka Dr ya zauna yana ta kuka har mutane Suka taru suna kallonshi.


*Juma'atul Babbar Rana*

Ana saukowa daga sallar Juma'a akai kai Zara gidanta na gaskiya da rakiyar dubanin mutane dan har babu hanyar wucewa inda Ameer adnan da Dr sune kusan mutanen Na karshe da aka bari inda Suka tsaya suna ta jera mata addu'oi Dr kuwa sai tsiyayar hawaye yake yi Ameer kuwa shima sai da hawayen suka zubo mishi Na Tausayin Zara da tsoron Allah daya shige shi wai Zara yar gayu wayayya da komai nata classic ce yau a kwance k'asa ya rufe mata ido duk san da danginta suke mata da abokanan arziki gatan da zasu mata a wanan lokacin shine addu'a yanzu suma zasu tafi su barta shikenan sai dai kuma ayi labarinta Lailai rai ba abakin komai yake ba da ace mutane zasu gane da basu tsaya batawa Kansu lokaci wajen neman duniya ba tunda koman daren dadewa ko ka k'i ko ka so dole zaka barta.


Adnan kuwa sai da aka binne Zara ya k'ara jin wani irin tsoron Allah na shigarsa daya tuna tare fa Suka ringa sab'awa Allah sai gashi ita ta rigashi mutuwa gani yake mutuwa na iya d'aukarsa shima a kowane lokaci.

Da k'yar Ameer yaja Adnan suka bar wajen inda Suka koma suka cigaba da amsar gaisuwa.


Cikin gidan ma Acike yake tap har babu wajen zama acikin 'yan zaman makokin ma har da Aliya dan ko gida bata koma ba sabida yanda mutuwar Zara ya shigeta kuka kawai take tana zubawa Zara adduar dacewa da rahamar ubangiji dan ba Laifi Zara tana da saukin kai da dadin Zama.

Sai wajen k'arfe biyar Na yamma Aliya ta fito daga gidan dan Ameer ya maidata gida inda Suka kuma yiwa su Mommy Hauwa gaisuwa da Dr da Zazzabi ya rufeshi tunda Suka dawo Mommy Hauwa kuwa ko magana bata yi ballantana ta amsa gaisuwar da ake mata.


Adnan kuwa ganin Su Ameer zasu tafi Har Aliya tayi wajen motar ta tsaya yasa ya mik'e yabi bayan Ameer idon nan nasa yayi jajir banda wani irin ciwon kai dayake yi na b'ari d'aya.


Adnan cikin muryarsa da baya fita yacewa Ameer "Dan Allah Dan uwa Ka yafemin abinda nayi maka nabi san zuciyata Na sab'awa Mahallicina naci amanar mak'otaka Ka dubi girman Allah ka yafemin Ku biyun nake so na nemi yafiyarku ko na d'anji nauyin da zuciyata ya min ya ragu"


Ameer da Sauri yace "karka damu Adnan na Dade da yafe maka banaso ma Ka ringa yin maganar nan sabida wacce kuka sab'awa Allahn da ita ta Riga mu gidan gaskiya Ko ban tambayi Aliya ba nasan itama ta yafe maka fatan mu Allah ya kara shiryaka kaje kayi ta istigifari kana neman yafiyar Allah mutuwar da Zara kawai tayi ya isa ya zame maka ishara Allah ya jikanta da rahama".

" Ameen" Suka ce atare Adnan kuwa ya juya ya kalli Aliya yana k'ok'arin magana Aliya ta d'aga mishi hannu tace "Ba sai kace komai ba Adnan na yafe maka duk abinda kayi min Allah ya yafemu gabaki d'aya"

Daga haka ta bud'e motar ta shige.

Adnan kuwa ya ringa zubawa Ameer godiya yana tsaye har sai da Suka tafi inda Hawaye masu dumi Suka kara zubo mishi Na nadamar abubuwan da yayi yau gashi babu Aliya babu Zara babu dangi kusa take tunanin komawarsa Maiduguri ya k'ara darsuwa aransa inda ya yanke ana Yin sadakan bakwai d'in Zara zai koma Maiduguri ya fara neman yafiyar yayansa kafin yaje Niger fatansa dai Allah yasa su yafe mishi.




Ahaka ya koma suka cigaba amsar gaisuwa sai da akayi isha ya shiga gidansu Zarah ya k'ara yiwa matan gaisuwa ya koma gidan Safwan tare da wani irin zazzafan Zazzabi.


B'angarensu Aliya dinner da basu je ba kenan ita da Ameer dan har gwara Ameer ya d'an fi Aliya dauriya duk da Zara tsohuwar matarsa ce Aliya kuwa dayake mace ce tana da rauni haka ta kwana sukuku babu walwala in banda tunani da adduar da take jerawa Zara dan Ameer har mamakin Yanda Aliya ta d'aga hankalinta yake akan mutuwar Zara sai iya Summayya ce taje dinner da aka had'a musu da angonta.


Washegari k'arfe goma sha d'aya aka daura Auren Ameer da Aliya Sumayya da Angonta Nura ana gama daura Auren Ameer ya kuma komawa gidansu Zarah ya kara yiwa su Mommy Hauwa gaisuwa da Dr har da Adnan da ya zama wani irin silent da fuskarsa kawai zaka kalla tsantsar tausayinsa ya rufeka.

K'arfe biyar Na yamma aka mik'a amare gidajensu inda aka kai Aliya katon gidanta dake 'yankaba upstairs har yanzu mutuwar Zara bata saketa ba dan in banda kuka babu abinda take yi haka kawai take ganin kamar taci amanar Zara da ta aure mata miji.


Ameer kuwa tuni mutuwar Zara ta sake shi farincikin Auren Aliya ya mamaye mishi Zuciya Na irin tanadin da yayi wa rana irin ta Yau na Mallakar Aliya.


Ango bashi ya shigo gidan ba sai da kowa ya watse da fara'arsa ya shiga gidan da ledojinsa amma tozalin da yayi da fuskar Aliya daya kumbura sabida kukan data sha yasa jikinsa wani irin sanyi zama yayi a gefenta ya jawo ta ya rungume ta sabida ya rarrasheta inda Aliya tayi saurin janye jikinta haka kawai tana jin kamar tana ta cin amanar Zarah.


Ameer kuwa dayake wayyaye ne komai nashi a tsare yake a ilimance ya kuma san yanda zai bi da amaryarsa a hankali yafara kwantarwa da Aliya hankali har ya samu ta saki jikinta dashi inda suka gudanar da duk abinda Amarya da ango sukeyi na nafilfili da sauransu awajen kwanciya Aliya taso bijire masa dan kuka take bil hakki tana CE mishi bazata iya cin amanar Zarah ba amma dayake Ameer a matse yake ya dade rabonsa da mace tuni yayi duk wata dabararsa da duk salon daya sani a matsayinsa na namiji har ya samu ya mallaki Amaryarsa daya jita tamkar buduruwa sosai ya samu nutsuwa da Aliya inda wani irin bacci mai balain dadin gaske yayi awon gaba dasu...



Naso na karkare a shafin nan Amma ina wlh da magriba ma fara typing sabida rashin lafiya da yarana ke fama dashi amma da izinin Allah zan karkare a next page dina thanks for ur love en support...

*M🅰K'OT🅰N JUN🅰*


*REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS* *P.M.L*




® REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS

ɯɛ ɖơŋŧ ʝųŞŧ ɛŋŧɛřŧąıŋ ŋɖ ɛɖųĆąŧɛ, ცųŧ ɯɛ ąٳŞơ ŧơųĆɧ ɖ ɧɛąřŧ ơʄ řɛąɖɛřŞ


# WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
# IG PML WRITERS
# https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-




*Written by*

💅💅💅 *SADNAF*💅💅💅



*Follow me on wattpad @ Sadnaf*

*Page 38*


*Nagode kwarai da adduoinku ga d'ana Affan ya samu sauki Alhamdulillahi Allah ya saka muku da alherinsa ngd kwarai*


A ranar da akayi sadakan bakwai d'in Zara gidan Dr a cike yake tap da jama'a tamkar a ranar akayi rasuwar inda makusantar Zara mutuwar Zara ya kara dawo musu sabo fil tamkar a ranar tarasu amma ina kwananta bakwai yau da k'asa ya rufe mata ido wanda ahankali Zara ta fara Zama tarihi sai dai ayi labarinta.

Ango Ameer da Amarya Aliya suma sai da suka zo Sadakan bakwai inda Aliya tozali kawai da tayi da gidan sai da hawaye ya hau zubo mata da kuwa ta shiga cikin gidan ta zauna a cikin jerin wayanda suka zo gaisuwa sai da ta fashe da kuka data ga ana fito da kayan Zaran waje sabida za'a kyautar da wasu za'a kuma akai wasu gidan marayu.


Mommy Hauwa kuwa har lokacin Azumin magana take duk da zuwa lokacin ta bar zubar da hawaye a fili sai dai a ciki yatsunta kuwa wani irin zafi suke mata sabida Yanda take Jan carbi babu dare babu rana harshenta kuwa kullum cikin ambaton Allah yake da addu'ar samun rahama ga 'yarta.


Dr kuwa har lokacin bashida cikakken lafiya dan ko k'adan baya iya zama sabida rashin kwarin jiki kallo d'aya zaka mishi tausayinsa ya rufeka.

Adnan kuwa da tunda akayi rasuwar bacci kawai ke maidashi gida da sassafe yake dawowa gidansu Zara.

Shima kana ganinsa zai masifar baka tausayi sabida ko kad'an idonsa baya rabo da hawaye banda wani irin tsoron Allah dake hud'a shi duk kwanan da zai yi ya tashi shima bakinsa kullum d'auke yake da isitigifarin abubuwan da ya aikata komai na duniya ya fice masa arai babu abinda yake sha'awa arayuwarsa yanzu sama da gyara Lahirarsa da sauran lokacin da yake dashi abinda ke d'ad'a d'aga mishi hankali bai wuce wayar garin da yayi da kaikaiyin gaba ba dan kamar yayi k'aramin hauka idan yafara mishi kaikai sai ya samu kusan minti talatin yana Sosa gabansa kafin kaikai yin ya lafa mishi kuma ko kad'an babu alamar kuraje agaban nashi ahaka ake zaman makoki dashi yana yi yana tashi sabida yayi susa yasan koma menene cuta su Ajjidde suka saka mishi dan dama yasan za'a rina sabida yawan mazan da take mu'ammalla dasu idan shima jarrabtar da Allah zai masa kenan a gidan duniya zai amshe shi da hannu bibiyu har Allah ya bashi ikon cin jarrabawar idan kuma cutar ta zame masa Ajali addu'arsa a kullum shine Allah yasa ya dace da rahamar ubangiji.

Koda lokacin dasu Aliya suka zo da Ameer gidansu Zara akan idonsa ne da kallon sha'awa ya bisu yana inama shi yake da kwanciyar hankalin Ameer ba tare da fargabar komai ba inama shi yasamu yayi ingantaciyar da tsaftataciyar rayuwar da Ameer ke yi ko da bakasan Ameer ba kasan hankalinsa a kwance yake dan banda bud'in arziki dayake ta samu ga mace tagari da Allah ya bashi ga wani haske da Annuri dake fita a jikinsa baya mantawa ada bala'in kauyancin Ameer yake gani amma a yanzu Ameer shine ya zame masa abun sha'awa da kallo Aliya kuwa dama bama zai soma kallonta ba dan ta yi mishi mugun nisa sai dai hange daga nesa.


Akan idon shi Aliya ta k'ara fitowa daga gidansu Zara Ameer dake cikinsu a zaune ya mik'e ya mimik'a musu hannu tare da addu'a ga Zara ya nufi wajen motarsa ya bud'ewa Aliya suka tafi.


Adnan hawaye ne suka ciko masa a ido ya kara sharewa ya kara maida kansa ya sunkuyar ya cigaba da Jan carbinsa a hankali yafara jin kaikai na taso mishi tun yana d'aurewa yana sallati sai da ya mik'e da Sauri ya nufi band'akin dake boys quarters d'in gidan dan wani azabar kaikai gabansa ke masa.

Da hannu bibiyu yafara sosawa yana kuka dan har jiwa kansa ciwo yake yayi agarin sosawa sai da ya lafa masa ya fito d'aga band'akin yana jin azabar rad'adi.


Yana gidansu Zara har akayi sallar Ishai inda suna dawowa daga Massallacin aka fara fito da abinci kamar Yanda aka saba dan suci amma ko kallon abinci baiyi ba dan dama bayaci bazai iya tuna rabonsa dayasa abu a bakinsa ba dan Sam bashida kwanciyar hankali.

Ana fara cin abincin ya tashi ya shiga cikin gidan inda suka kusa karo da Khalid daya fito dan ya kai musu ruwa.

Sai da Khalid ya kai ruwan ya dawo ya same shi atsaye batare da b'ata lokaci ba yace dan Allah ya mishi iso cikin gidan yana san ganin Mommy Hauwa da Dr dan idan ya tafi yau bazai sake dawowa ba sai za'ayi sadakan arba'in idan dai yana da Nisan kwana.


Khalid ce mishi yayi yana zuwa ya fad'o musu inda yaje ya samu Mommy Hauwa data k'unshe kanta a d'aki ita kad'ai tana zaune akan Sallaya idonta a rufe tana Jan Carbi kamar dai Yanda ta sab'a tunda akayi rasuwar.


Bata ko d'ago ta kalli Khalid daya gaya mata sakon Adnan ba har sai da ya kara maimaitawa.

Inda Mommy Hauwa ta mik'e Khalid yabi bayanta dan bashida burin daya wuce yau yaji Mommy Hauwa tayi magana dan rashin maganarta na damunsu tun a asibiti data yi magana bata k'ara magana ba.

Haka ya ringa binta a baya har sai da ta shiga palon da Dr yake a kwance shima yana rik'e da nashi carbin.

Ta samu guri ta zauna Khalid na ganin haka yagane mai take nufi yayi waje ya yiwa Adnan iso har palon.

Sai da Adnan ya zauna a k'asa Khalid ya fice.

Inda Adnan yayi k'asa da kansa sosai yana k'ara yiwa Mommy Hauwa gaisuwa da Dr.

Dr da muryarsa bata fita sosai ne ya amsa.

Mommy Hauwa kuwa ta ringa gyad'a kanta tana kallon shi can k'asan ranta tana mai bala'in tausayin shi dan tana ganin idan aka d'auke ita da Dr babu Wanda yaji mutuwar Zara kamar Adnan ko wayanda suke jini d'aya basu ji mutuwar ta haka ba.

Adnan cikin rawar murya yace "Daddy Mommy zuwa nayi na nemi yafiyarku akan abinda na aikatawa Margayiya dan Allah Dan annabi ku yafe min wlh sharrin shaidan ne na kuma yi nadamar abinda na aikata bantab'a sanin"""


Mommy Hauwa ce tayi saurin d'aga mishi hannu hawaye na zubo mata ta bud'e bakinta dayayi bala'in yi mata nauyi sabida maganar da batayi ba kwana biyu tace "Adnan baka yi mana komai ba wacce kake neman yafiyarmu akanta ta Riga da ta Riga mu gidan gaskiya fatanmu Allah ya gafarta mata yayi mata rahama banaso na tuna wani abu da Zara tayi illa ma na ringa tuna ta da alheri ina mata addu'a dacewa da rahamar Allah kai ma ina mai baka shawara kaje kayi ta neman yafiyar Allah kana istigifari ka kuma nemi yafiyar wayanda ka b'atawa kayi amfani da damar da kake dashi ka kusanci Mahallicinka dan mu muke ganin muna da lokaci amma lokacinmu kalilan ne dan kana rayuwa ne baka san lokacin da mutuwa zata d'auke ka kamar Yanda Zara ma ban tab'a kawo mata mutuwa kusa ba Ashe mutuwa na tafe mun yafe maka Allah muma ya yafe mu gabad'aya".


Zuwa wanan lokacin Mommy Hauwa Dr da Adnan kuka suke sosai da hawaye suna jin wani iri a zuciyarsu Inda wani irin fargaba da Nadama ya rufe Dr da Adnan Dr shi yana nadamar abubuwan da yayi wa Mahaifiyarsa Adnan kuwa na nadamar abubuwan da ya aikata.



Adnan godiya ya ringa musu sosai inda Mommy Hauwa da Dr suka ringa binshi da addu'ar har ya tashi yatafi.



A ranar Adnan ko kad'an bacci bai d'auke shi ba sabida matsuwa da yayi gari ya waye ya d'auki hanyar Maiduguri dan Gabad'aya hankalinsa ya koma can burinsa ya gansa agaban Mahaifiyarsa ya nemi yafiyarta Dana yayansa Anwar dan yanzu wajen shekara biyu da rabi rabon shi dasu hankalinsa kan tashi idan ya tuna Yanda Mahaifiyarsa ke damuwa akan shi.



Da Asubar fari ya d'auki hanyar Maiduguri bayan doguwar addu'ar daya yi na Allah ya sauke shi Lafiya.


K'arfe biyar na yamma ya isa Maiduguri inda duk guraren daya sani suka cacanja mishi sabida sababin gine ginen da akayi.

Machine ya hau dan ya kai shi Family House d'insu dake can idan ya huta sai yaje gidan Yayansa Anwar ya nemi yafiyarsa ya kuma rok'eshi akan ya raka shi Niger wajen Mahaifiyarsa dan babu Yanda zaiyi ne da a yau zai je Niger dan babban Burinsa yanzu yayi tozali da Mahaifiyarsa ya nemi yafiyar ta.


A lokacin da ya isa Family house d'in Nasu da Cousin din Mahaifinsa ke Zaune a ciki da 'ya'yansu bai gane gidan ba sabida mugun canza shin da akayi ya dawo na birni ginin 'yan gayu dan bene aka maidashi banda wasu irin fitilu daya haska gidan tuni ya shiga tashin Hankali dan yana tunanin siyar da gidan akayi suka tashi sai da yayi tambaya akace basu tashi ba suna nan hankalinsa ya kwanta.

Jiki a sanyaye ya shiga cikin harabar gidan inda kansa ya k'ara d'aurewa dan shima cikin gidan an canza shi ya zama part part jiki ba kwari ya nufi part d'in da yake jiyo maganganun mutane A bakin k'ofa ya tsaya yafara rafka Sallama da k'arfi sabida su jiyo shi.

Inda kawun shi Abdullahi ya amsa tare da nufo k'ofar dan sam bai gane shi ba cike da nauyi da jin kunyar gudarsu da yayi ya zube a kasa yana gaishe shi.

Inda kawu Abdullahi ya amsa yana so ya tuno inda yasan muryar shi dan sam bai gane wanan siririn mutumin da gashi ya cika mishi fuska ba.

Ganin wahalar da kansa kawai zaiyi ba iya gane shi zaiyi ba yasa yace "Bawan Allah Daga ina wa kake nema"?


Adnan cike da fargaba da tsoro cikin inina yace " Kawu nine fa Adnan"

Kawu Abdullahi waro ido yayi cikin tsananin mamaki yaja da baya da Sauri yace "Wane Adnan d'in Adnan dai Dana sani"?


Adnan da Sauri ya gyad'a kansa hawaye na sauko mishi yace " Nine Kawu"

Sallati Kawu Abdullahi ya rafka yana tafa hannuwa yana "kai Mai ya sameka haka cuta kayine ko yaya"


Adnan kuka ya fara yi ya kasa magana inda sallatin da yayi ne yasa mutanen cikin gidan suka fara firfitowa suna tambayar Kawu Abdullahi Lafiya waye wanan d'in?

Sai da Kawu Abdullahi ya gama rafka salallami ya iya fad'a musu Adnan ne inda dukansu suka hau tafa hannaye suna mamakin sabon Adnan d'in dake gabansu da bashida maraba da mai cutar kanjamau sabida rama dan tsohon Adnan dan gaye ne na fitar hankali gashi dan dumur dumur wanan kuwa kamar kayi bulala dashi.


Matar kawu ce tayi k'arfin cewa ya shigo Daga ciki inda ganinsa da sukayi yasa suka tuno da Asmau Mahaifiyar Adnan da ta rasu watani uku da suka wuce inda hawan jini yayi ajalin nata sabida yawan tunanin Adnan da take yi da sa shi da tayi aranta wani kaddara ma kaf cikin yayan nata tafi san shi babu irin kasashen da Anwar da ya zama fitaccen d'an siyasa bai kaita ba dan kawai ta ringa rage tunanin Adnan Amma hakan ya faskara dan musamman ya k'ara nadar k'afa yaje neman Adnan dan kawai ya farantawa Mahaifiyar tasu dan ba dan ita ba ko kad'an babu abinda zai sa ya Kara waiwayar Adnan sabida ma irin wulak'anci da ya mishi dayaje kano dan ya bashi shawara akan ya daina wulak'anta Mahaifiyar su ya ringa zuwa yana ganinta.


Inda sai daya samu kwana biyar a kano yana jigilar neman Adnan sabida wasu ne a gidansu Adnan.

Akan dole ya koma Maiduguri inda Jikin Mahafiyarsu ya rikice dataji labarin ba'asan inda Adnan yake ba ahaka jininta ya ringa hawa Kullum tana kuka inda Anwar da Aliyun daya zama fitaccen dan kasuwa suka ringa iya k'ok'arinsu dan su kwantar mata da hankali kowane na iya k'ok'arin yaga ya faranta mata rai amma a Banza dan ta Riga da ta sa Adnan a ranta.

Ahaka ta ringa fama da rashin lafiya tana rokon a nemo mata Adnan inda wanan karon Aliyu shi yazo kano dan ya nemi Adnan Amma shima Sam bai ko samu labarinsa ba ahaka ya hakura ya koma yace mata yasa a nemo shi ta kwantar da hankalinta Adnan zai zo.


Amma ina dawowar Aliyu kamar kara mata rashin lafiyar yayi sabida gani take kawai B'oye Mata suke yi Adnan ya mutu.

Tunda ya dawo jikin nata ya rikice inda suka kaita Egypt dan a duba lafiyarta Anan Allah ya amshi ranta suka dawo gida da mugun bak'in cikin rasa Mahaifiyar su Inda suka ji tsanar Adnan a ransu dan a tunaninsu a sanadinsa Suka rasa Mahaifiyar su Anan kowane ya yanke koda sunga Adnan ya dawo musu sai sun kore shi dan ba jininsu bane shi Aminatu ce kawai bata yi fushi da Adnan sosai ba sabida raunin da take dashi.



Adnan da ido ya ringa binsu dayaga suna share hawaye a b'oye kawu Abdullahi kuwa ya sunkuyar da kansa.

Adnan gabansa ne yayi bala'in fad'uwa ya zubawa Kawu ido yana k'ok'arin magana kawun ya d'ago da kansa yana "Adnan ina ka shige duk tsawon lokacin nan aka ringa nemanka Adnan kasan tun lokacin da kazo akan aje a nema maka Auren matar da ka aura baka kara zuwa gida

Please Login or Register in order to submit comment