Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tambaya wani irin takaici da bak'in ciki ne suka rufeshi dan ba dan mugun kaunarta dayake ba da ya mata dan banzan duka na raina masa hankalin da tayi.

Ahaka ya cigaba da zama bayan bacci ya mishi k'aura tunane tunane kawai yake na yanda zai iya juya Ajjidde idan ya aureta dan tafi k'arfinsa ko ta ina da yana da Hali da ana kiran asuba zai bar gidan amma ina bazai iya ba tunda har tace ya tsaya haka zai tsaya yaji wane maganar zasuyi duk da yana so yasan matsayin wannan katon iska dake kwance a wajenta.


K'arfe hudu dai-dai Alhaji Al Gazaru ya farka inda suka had'a ido da Adnan dake zabga mishi mugun harara da sauri ya mik'e zaune yana kalle kalle dan yama manta inda yake sai da ya dawo dai dai ya maida kallonsa kan Adnan da idonsa ke Neman fadowa.


Alhaji Gazaru kau da kansa yayi yana tunanin k'ila daya daga cikin customers d'in Ajjidde ne shima yazo rage dare shine yazo ya tarar dashi bai kara kallon inda Adnan yake ba ya nufi d'akin dake kusa Dana Ajjidde dan ya kimtsa jikinsa yazo ya dau hanya dan bai isa ya soma zuwa d'akin Ajjidde a yanzu ba dan ta Riga da ta sallame shi ya kuma san rules d'inta indai ba kudi Mai bala'in tsoka ka biyata ba baka isa ka kwana da ita d'aki d'aya ba.


Adnan kansa ne ya d'aure da yaga ya shige d'aya d'akin inda take yaji hankalinsa ya kwanta dan ayanzu yafi kyautata zaton d'an uwanta ne ba Saurayinta ba take ya nemi bacin ran sa ya rasa baccin daya Dade yanaji yayi awon gaba dashi.


K'arfe goma Adnan ya farka daga baccin daya d'aukeshi inda ya mik'e da sauri yana mamakin yanda ya Dade yana baccin d'akin dake kusa Dana Ajjidde ya shiga ya d'auro alwala a bandakin yana tunanin inda Alhaji Al Gazarun yayi dan bai ganshi a d'akin ba sai da yayi sallah ya kuma fitowa palon ya zauna yana jiran Ajjidde tafito duk da yana so ya tafi gida amma haka zai jira har ta fito.


Haka Adnan ya cigaba da zama a Palon sai wajen sha biyu Ajjidde ta fito daga d'akin sanye da wani arnen less taci uban kwalliya in banda kamshi babu abinda take yi.


adnan kuwa ya hadiyi yawu yafi a kirga tamkar mudubi haka ya maidata yana kallonta.


Ajjidde kuwa kujerar dake fuskantarsa ta zauna bata ko kalli inda yake ba ta hau kwallawa 'yar aikinta kira.


Aguje 'yar aikin nata tafito daga d'akinta tazo ta zube agabanta ta gaisheta ta gaida Adnan

Ajjidde umarni tayi mata data kawo musu abun karyawa.

Cikin minti biyar ta jera kulolli agaban Adnan da Ajjidde.

Ajjidde kuwa ganin taki kallonsa ne yasa ya d'aure ya hadiyi bak'in cikin dake cin ransa ya gaisheta.

Da mamakin sa amsawa tayi batare da taji nauyinsa ba amatsayinta Na wacce ya kamata ta fara gaishe shi inda take ya k'ara jin ransa ya b'aci.

Ji yake kamar ya bud'e zuciyarsa ya Ciro santa yayi ta kwallo dashi dan ba laifi Ajjidde Na wulakanta shi.

Ajjidde kuwa serving kanta tayi ta fara cin abincin ta hankalinta kwance bata d'ago ba sai data koshi ta ture table d'in gefe ta kalli Adnan tana "kai bazaka ci abincin bane kafasan bazan maka wata magana ba har sai kaci abinci tukuna"


Murmushin data sakar masa ne yayi melting duk wani b'acin ran dayake ciki ya maida mata martanin murmushin data masa daga haka ya debi dankali da kwan dai dai yanda zai iya ci ya ya koshi ya sha shayin kad'an shima ya ture tebur d'in gefe tare da Hamdala.


Sai da yace mata yagama ta ajiye wayar da take ta dannawa ta kalleshi tace "Yauwa maganar da zanyi ma shine banasan takura arayuwata idan aka takura min tsanar mutum nake idan dai ka shirya aurena kazo a d'aura mana aure kawai idan baka shirya ba ka daina takuramin da waya har ka ringa nado k'afa kana zuwa ka bari idan ka shirya Sai kazo karkuma ka manta sharrud'an Dana gindaya maka kafin ka aureni dama maganar da nakeso nayi maka kenan"


Adnan da sauri yace "Na shirya Ajjidde ko a gobe ne ma a d'aura mana aure dan wlh bana iya bacci idan banji muryarki ba.

Ajjidde Sai data kare mishi kallo tundaga sama har k'asa tace " Are sure u are ready"?

Adnan da sauri ya gyad'a mata kai

Ajjidde kuwa ta sauke ajiyar zuciya tace "to shikenan gobe zan kira Wanda zaiyimin walliyi a d'aura Auren a palon gidana kaima ka taho da naka walliyin karka manta nace maka aurenka bazai hanani sana'ata ba babu ruwanka da samun ido abinda naga dama shi zanyi aurena bashi yake nufin zaka nade k'afa ka zauna ba zuwa zakayi ka cigaba da Neman kudinka a kuma gidana zaka zauna ka yarda"

Adnan tsabar farincikin zai mallaki Ajjidde a gobe da sauri ya washe bakinsa yace ya yarda"


Ajjidde ta girgiza kai tace "kamar yanda Na fad'a maka ba Sai kayi min komai ba sadaki kawai nakeso kuma ni zan yanke maka sadakin da zaka bani miliyan d'aya zaka min sadaki dashi lura da bakada kudi yasa bazan ce kayimin akwatin gold ba idan dai fa ka shirya aurena kenan"


Take murmushin dake fuskar Adnan ya b'ace gumi ya hau tsatsafo masa babu abinda yake nanatawa sai Miliyan d'aya inda Ajjidde ta zuba mishi ido cikin mamakin yanda yabi ya rude yana wani nanata miliyan d'aya.

"Ko dai Miliyan d'ayan yamaka kad'an ne idan kuma baka dashine kaje ka Tara idan ka samu sai kazo a d'aura mana Auren dan bazai yiwu ka aureni a sadaka ba"

Ajjidde tace tana w'ulawa Adnan harara

Adnan wani irin yawu ya hadiye bayan ya hararo dubu Dari hud'u da hamsin d'in daya rage masa a account yafara lissafin inda zai nemo cikon Dari biyar da hamsin dan bashida ita ballantana ya kai ga ya bawa wani ajiya gabansa wani irin fad'uwa ya fara yi hankalinsa yayi mummunan tashi dan bazai iya jure rasa Ajjidde ba.


Ajjidde kuwa wayarta ta d'auka ta mik'e tana "Ni zan shiga daga ciki idan ka gama tunanin kamin magana"


Adnan da sauri ya tsayar da ita yace "Allah ya kaimu goben insha Allahu zan kawo walliyina da Sadakin"


Ajjidde murmushi ta sakar masa tana "sai goben kenan k'arfe hudu za'a d'aura mana Auren ka d'an zo da shirinka akwai wani k'aramin liyafa da zan had'a mana ka kuma kwaso komai naka tunda Anan zaka zauna"



Adnan murmushin yak'en ya sakar mata dan hankalinsa a tashe yake yace "pls zan iya miki waya kafin goben"?


" eee zaka iya kirana idan kayimin kira uku ban d'aga ba karka sake kira kila ina wani uzurin ne ko banasan d'aga waya"


Adnan girgiza mata kai yayi yace "to shikenan Na tafi sai goben"

Daga haka ya juya ya bar palon Ajjidde kuwa ta bishi da kallo tana murmushin mugunta.



Adnan kuwa da rawar k'afafu da jiki ya k'arasa cikin motar hankalin sa a mugun tashe dan bai san daga ina zai fara neman kudi ba waye zai yarda ya bashi rancen dubu Dari biyar har da hamsin alhalin an san bawani aiki gare shi ba.

Adnan dafe kansa yayi dake Sara mishi yana tunanin ma fita inda a karshe ya nufi wajen Safwan dan ya gwada sa'arsa.

Abun mamaki a lokacin daya gayawa Safwan abinda ke tafe dashi Dariya ya ringa kyakyata masa yana cewa a ina zai samu kudin da zai biya shi da Biyar biyar d'in da ake lik'awa awajen biki zai biya shi ko da me zai biya shi a takaice Baram baram suka rabu da Safwan inda ya cigaba da karad'e sauran abokanan nasa ko zai dace sai dai ina dukansu rashin mutunci suke masa tunani ya fara yi na ya hakura da Ajjidde kawai ya huta amma me kamar kara rura masa wutan santa ake akan dole ya yanke hukuncin siyar da motarsa sabida shi kad'ai ne abinda zai iya siyarwa ya samu kudin da zai cika ya biya sadakin Ajjidde Inda can k'asan zuciyarsa murnar Mallakar Ajjidde kawai yake dubu Dari takwas da ashirin ya siyar da motarsa yayi banking kudin ya dawo gida yafara had'a kan kayansa dan a gobe zai koma gidan Ajjidde da zama yana kyautata zaton da sannu zai koyawa Ajjidde yanda zata so shi har ya juyata san ransa da dukiyarta.




B'angaren Ameer kuwa tunda yayi sallar asuba bai koma barci ba wanka yayi ya shirya yana jiran gari ya k'ara sa wayewa ya nufi gidansu Zara dan ko kad'an bacci bai ziyarci idonsa ba sabida b'acin rai.


K'arfe bakwai dai-dai ya d'auki hanyar gidansu Zara da Quraninsa izzu sittin dan sai Zara ta rantse da Qurani akan cikin jikinta nashi ne hankalin sa zai kwanta.

K'arfe bakwai da minti ashirin yayi parking a k'ofar gidansu Zara fuskar Nan tashi a had'e

Yana k'ok'arin fitowa daga cikin mota Khaleed yafito daga gidan da kayan ball zai fita training d'in safe mamakine ya rufe khaleed a lokacin daya ga Ameer yafito daga motarsa ya nufo wajensa hannunsa rik'e da Qurani


Khaleed gaishe shi yayi a lokacin daya k'araso Ameer kuwa ya mik'a masa hannu sukayi musabiha.

Ameer bai tsaya b'ata lokaci ba yace yacewa Mommy Hauwa yazo yana waje.


Khaleed ce masa yayi ba'a gida suka kwana ba suna gidan Aunty khadija ita da Zara.


Ameer kasancewar yasan Aunty khadijar ya kuma san gidanta juyawa yayi ya koma motarsa ya d'auki hanyar gidan Aunty khadijar cikin 'yan mintuna ya k'arasa gidan Ameer bai sha wahala ba aka masa iso har cikin palon gidan sabida a gidan suka fi zance da Zara kafin suyi aure.


Aunty khadija dake kitchen tana had'a breakfast ba k'aramin mamaki tayi ba a lokacin data ga Ameer a gidansu da sassafe gaisawa sukayi bayan yan tambaye tambaye Ameer yace mata wajen Mommy Hauwa yazo yaje can gidan ance suna nan da Zara.


Aunty khadija mik'ewa tayi jiki a sanyaye tace bari ta taso ta Dan bacci take.

A lokacin data shiga d'akin a zaune ta tarar da Mommy Hauwa ta zubawa waje d'aya ido tana tunani ita kuwa Zara ta baje tana ta baccinta cikin kwanciyar hankali dan ko juyi batayi ba tunda ta kwanta sabida yanda take jin dadin baccin.


Mamakine ya rufe Mommy Hauwa a lokacin da Aunty khadija tace mata Ameer yazo yana Palo yace wajenta yazo.


Mommy Hauwa take jikinta ya k'ara sanyi dan tasan idan Ameer bashida gaskiya babu yanda za'ayi ya bugo wannan samakon cikin tsananin takaici ta d'akawa Zara duka a cinya.


Zara kuwa tayi sauri ta bud'e idonta tana Sosa cinyarta.

Mommy Hauwa Harara ta galla mata tana "ki tashi ki wanke fuskarki kizo ki samemu a Palo dan ga Ameer can yazo yace ki rantse agabansa akan cikinsa ne ajikinki"


Zara kwalalo ido tayi take dan cikinta ya motsa ta dafe kirjinta tana "Mommy yanzu haka Ameer Na gidanan"

"Kwarai kuwa yana gidanan ba dai kince da ciki ya sake ki ba kizo muje yana Palo yana jiranmu"


Daga haka Mommy Hauwa ta mik'e tayi waje dan Aunty khadija ta Dade da yin waje dan ta duba abinda ta d'ora.


Zara kuwa hankalinta ne yayi bala'in tashi ta hau gumin k'arfi da yaji dan bata isa ta kalli idon Ameer tace cikinsa bane jikinta ne ya hau rawa gabanta Na fad'uwa a lokacin data jiyo Mommy Hauwa Na kwalla mata kira sabida gigicewa daga ita sai doguwar rigar jikinta ta fita babu ko dankwalli.


Mommy Hauwa kuwa tunda suka gaisa da Ameer ta sunkuyar da kanta tana hawaye ganin Zara ta shanyasu yasa tafara kwalla mata kira dan Ameer yace bazai yi magana ba sai Zara tafito.


Karar bud'e k'ofar d'akin ne yasa Ameer d'agowa inda suka yi ido hud'u da Zara da turtsetsen cikin ta.

Jikin Zara ne ya fara bala'in rawa kamar zata fad'i sakamakon tozali da tayi da Ameer daya zama bature sabida kyau da ya kara yi ga wani mugun kallon da yake binta dashi........

*M🅰K'OT🅰N JUN🅰*


*REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS* *P.M.L*




® REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS

ɯɛ ɖơŋŧ ʝųŞŧ ɛŋŧɛřŧąıŋ ŋɖ ɛɖųĆąŧɛ, ცųŧ ɯɛ ąٳŞơ ŧơųĆɧ ɖ ɧɛąřŧ ơʄ řɛąɖɛřŞ


# WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
# IG PML WRITERS
# https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-




*Written by*

💅💅💅 *SADNAF*💅💅💅



*Follow me on wattpad @ Sadnaf*


*Kuna ina 'yan Zauren biebie isah Wannan shafin nakune ina jin dadin kasancewa daku ina jin dadin comment d'inku ina muku son so cos kuna burgeni ba ni kad'ai ba duk writer da take cikin grp d'in Biebie isah zata ji dadin kasancewa daku pls u guys should keep it up*😍😍😍😍😍


*Page 32*

Zara a kusa da k'afar Mommy Hauwa ta zub'e ta sunkuyar da kanta dan bazata iya jure kallon da Ameer ke mata ba dan wani mugun tsanarta take hangowa a kwayar idonsa cikinta murd'awa kawai yake gumi Na tsatsafo mata.


Mommy Hauwa ganin Ameer yak'i magana in banda mugun kallon da yake bin Zara dashi kamar ya tashi ya rufe Zara da duka yasa tace

"Ameer ga Zaran nan agabanka jiya ta dawo daddare tace min da ciki ka saketa babu irin wuyan da bata sha ba dan wata mata mai siyar da abinci take tayawa aiki take bata abinci to a jiyan ta koreta sabida zata tafi garinsu ganin babu yace


zata je yasa ta dawo gida inda shima Mahaifinta yace baza ta zauna masa a gida ba akan dole na biyota nan jiya na kuma kira ka awaya dan na tambayeka gaskiyar lamarin dan nayi mamaki da tace min da ciki ka saketa"


Ameer cije lebb'ensa yayi cikin tsananin takaici nan take idonsa ya kad'a yayi ja Zara dake rawar d'ari kawai yake kallo sai da ya kwashi minti biyar kafin yace "Mommy wlh wlh wanan ba cikina bane cikin Adnan ne dan tunda na kawo Zara gida akan kuyi mata fad'a na kuma maidata babu abinda ya k'ara shiga tsakanina da ita har muka rabu kuma NA fad'a miki dalilin da yasa na saketa Mommy Zara cin amanata take da mak'ocina wlh da idona na gansu Bawai gayamin akayi ba idan kuma tace cikina ne yanzu zan d'auko Qurani acikin motata ta rantse akan cikina ne ni kuma zan k'arbi cikin"

Ameer sai da ya numfasa yace "Zara"

Zara d'agowa tayi hawaye na zubo mata jikinta na rawa suka had'a ido

"Tsakaninki da Allah cikin dake jikinki cikina ne"?

Ameer yace yana jifanta da wani irin kallo

Zara k'asa magana tayi ta cigaba da kallonsa ta na jin wani tsohon san Ameer na taso mata

Ameer sai da ya maimaita tambayar sau uku Amma Zara ta k'asa magana.


Mommy Hauwa a Zuciye ta kai mata duka tana " bakiji mai yace bane yace ki rantse da girman Allah akan cikinsa ne"

Zara sunkuyar da kanta tayi ta fashe da kuka tana tunanin Halin da Adnan ya jefata ya za'ayi ta soma cewa cikin Adnan ne agaban Mommy Hauwa fad'ar hakan na nufin d'an tausayinta da take ji ta daina itama ta gujeta Ameer ya k'ara tsanar ta gwara kawai ta dage akan cikin Ameer ne shine kawai ma fita agareta inyaso idan ta haihu sai ta fad'a musu gaskiya.


Zara kukan ta cigaba da yi sai da Mommy Hauwa ta k'ara kai mata duka ta d'ago cikin sheshek'ar kuka tace "Ameer wlh cikinka ne"

Ameer sakin baki yayi yana kallon Zara cikin tsananin mamaki wani irin bak'in ciki ya k'ara rufe shi dama wacce ma take jahila ta keta alfarmar Aure ya ma za'ayi tak'i rantsuwa akan karya kad'an da aikinta kenan.


Mommy Hauwa itama kallon Zara take dan haka kawai taji bata yarda da Zara ba.

Ameer kuwa mik'ewa yayi yacewa Mommy Hauwa yana zuwa yana fita waje Mommy Hauwa ta rufe Zara da fad'a akan gwara ta fito ta fad'i gaskiya tunda har taje tana muamalla da wani namijin al halin da aurenta to cikin jikinta bana Ameer bane dan da nashine bazai karyata har yazo musu da sassafe ba.

Zara ita dai kuka kawai take tana cewa cikin Ameer ne.


Ameer kuwa yana fita waje ruwan faron daya sha ya rage ya d'auko daga cikin motarsa yayi alwala ya d'auko Quraninsa ya koma ciki.


Zama ya k'ara yi daga inda ya tashi yacewa Mommy Hauwa nayi alwala a waje ga Qurani nan izzu sittin Zara itama taje tayo alwalar zan rantse akan ba cikina bane idan cikina ne Quranin nan ya tozartani itama ta rantse kamar yanda NA rantse akan cikin jikinta nawane idan ba nawa bane Quranin nan ya tozarta ta nikuma idan ta rantse haka wlh Mommy zan k'arbi cikin"


Mommy Hauwa da sauri tace "Haba Ameer mai yayi Zafi haka har za'a rantse da Qurani ai abun be kai haka ba wlh ma yarda da kai dan nariga da nasan halin Zara nasan kuma mai zata iya aikatawa"


Ameer da sauri ya katseta yace "aa Mommy ki bari dan Allah mu rantse sai hankalina yafi kwanciya ke Zara tashi kije kiyo alwalar ina jiranki"


Zara tunda ya shigo da Qurani hankalinta yayi bala'in tashi dan ko giyan wake tasha bata isa ta soma rantsuwa da Al Qurani ba kallon Ameer kawai take jikinta na rawa"

Mommy Hauwa kuwa dan ta gwada hankalin Zaran tsawa ta daka mata tana "ki tashi mana kije kiyo alwalar kizo ki rantse tunda kince cikinsa ne"


Zara kuka ta fashe dashi tana "mommy bazan iya rantsewa ba wlh ba cikinsa bane na Adnan ne dan Allah Mommy ki yafemin wlh sharrin shaidan ne nayi nadamar biyewa san zuciyata tun ba'aje ko'ina ba na fara girbar abinda na shuka Mommy dan babu irin wulak'anci da Adnan bai yimin ba har dukana yake shine ma ya koroni yace nadawo gida nace cikin Ameer ne"


Kuka Zara ke yi sosai tana rik'e k'afafuwan Mommy Hauwa

Inda mommy Hauwa ta ringa zabga sallati tana girgiza kai

Ameer kuwa runtse idonsa yayi wani mummunan Tsanar Zara na kuma tsirga mishi tabbas had'uwarsa da Zara da Auren mace irin Zara yana cikin kundun kaddararsa idan ba haka ba ina shi ina Auren watsatsiya Mara kamun kai irin Zara.


Babu abinda ke tashi a palon sai kukan Zara Dana Mommy Hauwa inda Zara ta kankame k'afar Mommy Hauwa ta na ta Neman yafiyarta


Mommy Hauwa fusge k'afarta tayi ta ture Zara tana 'kinyi Asara Zara wlh kin bani kunya da aurenki kika ringa aikata zina hardasu ciki dame Ameer ya rage ki Zara? Irin tarbiyyar Dana miki kenan Zara ooo ni Hauwa ina zan sa kaina sabida kunya wlh banyiwa iyayena haka ba Zara dawane ido kike so na kalli mutane da wane ido zan kalli Mijinki innalillahi wa inna ilahi rajuin"


Kuka mommy Hauwa takeyi sosai inda tausayin Mommy Hauwa ya rufe Ameer yace


"Mommy ki bar fad'in haka Allah ne ya jarrabceki kiyi addu'a Allah ya baki ikon cinye jarrabawarki Alhamdulillahi naji dadi data fito ta fad'i gaskiya dan banaso kuringa mun kallon mugu ko Mara mutunci danace cikin ta ba nawa bane aganina ta kai Ku wajen Adnan d'in yasan cewar kunsan ba cikina bane nasa ne nima sai yanzu hankalina ya kwanta dan wlh jiya ko runtsawa banyi ba Allah ya rabamu da san Zuciya Mommy ni zan wuce dan yau ko Hajiya ta ban gaisheta ba na taho nan.

Ameer mik'ewa yayi yana kallon Zara dake ta kuka numfashinta na Neman d'aukewa

Mommy Hauwa kuwa ta tsagaita kukan da take tace " Ameer dan Allah kayi hakuri ka haifi d'ana baka haifi Halinsa ba wlh bansan a ina ta d'ebo wanan halin nata ba wlh kunyarka nakeji"

Ameer da sauri yace "Haba mommy dan Allah me na bani hakuri wlh ba komai Allah dai ya shiryeta ki cigaba da mata addu'a Akan Allah ya shiryeta kuma ku tabbata kun d'au mataki akan Adnan dan kar ya barku da hidimar cikinsa"


Ameer hanyar waje yayi mommy Hauwa kuwa ta dakawa Zara tsawa tana "dan ubanki ki tashi ki bishi ki nemi yafiyarsa ko zaki samu saukin masifar da kika janyowa kanki dan idan bai yafe miki ba bazaki tab'a ganin dai-dai a rayuwarki ba dan kin cutar dashi"

Zara mik'ewa tayi da turtsetsen cikinta tabi bayan Ameer da saurinta a lokacin har ya kusa isa gate.

Sunansa ta fara kira sabida duk saurinta bazata iya tado shi ba

Ameer kuwa ya juyo fuskarsa a had'e dan yana raga mata ne kawai dan yanajin kunyar Mommy Hauwa.

Da mugun kallo ya ringa jifanta har ta k'araso wajensa tana share hawaye.

Zara zub'ewa tayi akan gwiwarta tace "Ameer dan Allah Dan annabi ka yafemin cin amanar ka da nayi nasan nayi maka ba dai dai ba na cutar da kai ban kyauta maka ba wlh Ameer nayi dana sanin biyewa san zuciyata Ina zaman zamana Adnan ya kawo kansa wajena lokacin dayake shaidan yana ingiza ni nima sai na biye masa Ameer dan Allah ka yafemin ko zanga haske a rayuwata bansani ba ma agarin haihuwar ko rai yayi halinsa kaga idan baka yafemin ba na shiga uku"

Ameer kallon Zara kawai yake yana tuno yanda yaganta da Adnan take yaji zuciyarsa na masa zafi cikin wani irin murya mai nuna tsantsan b'acin ran da yake ciki yace "Zara kenan ai ba yanzu ya kamata kizo ki nemi yafiyata ba dan bakiga komai ba tukuna zaki nemeni a lokacin dana iya manta abinda kikayi min Wanda kema kinsan har na koma ga mahallicina bazan iya manta abinda kika min ba hoton yanda na ganki da Adnan yana nan a manne a idona ko mai irin sunanki naji sai yanda na ganku ya fado min Zara zan yafe miki a lokacin da zan iya manta abinda kika min idan kuwa na kasa mantawa hoton yanda naganku namin yawo a zuciya to bazan tab'a iya yafe miki ba dan Zara kinci amanata kin ha'inceni al halin ban rageki da komai ba bakiyi nadama ba tunda Dan iskan kwarton naki na iya cewa kizo ki lankaya min cikinsa ki kuma zo ki lankayamin alhalin banji ba ban gani ba abinda ma kika min yau ya saka min mugun tsanarki Wanda nake tunanin bazan iya yafe mikin ba ki haifi shege lafiya"

Daga haka Ameer ya fice daga Gidan Zara tabi Sawun k'afar sa da kallo hawaye na zubo mata.

Sai data samu minti goma a zaune ta mik'e ta koma ciki.


Gabanta ne yayi mummunan fad'uwa a lokacin data ga Aunty Khadija na rik'e mommy Hauwa akan kar ta tafi Mommy Hauwa na tirjewa shigowarta palon yasa Mommy Hauwa ta watso mata wani irin kallo tana "Zara gwara kisan inda dare ya miki dan nima bazan iya tayaki rainon cikin shege ba Allah ya rufa miki asiri ya miki sutura kika tonawa kanki Zara kinsan hukuncin Wanda yayi zina da Aure kuwa jifansa za'ayi tayi har ya mutu ina tausayinki ne sabida na d'auka da Ciki Ameer ya sake ki Ashe ba nashi bane na shege ne tsinannan kuma yasa kika dawo gida akan ki lanka yawa Ameer cikin dayake ke jahila ce sai kika biye mishi kenan duk tsawon lokacin nan da Ameer ya sake ki kina wajen sa nabi na d'aga hankalina jinina na hawa sai daya gaji dake ya koroki kika dawo gida kenan da bai koreki ba bazaki tab'a dawowa ba ya miki kyau ni kinga tafiyata na Zare hannuna a al amuranki Khadija kema idan kinga bazaki iya ba ki koreta ta san nayi dan yanzu gidana zan koma bazan biye Mata ba Allah yasan babu irin k'ok'arin da banyi akanta ba"


Zara wani mugun ihu ta fasa taje ta kankame Mommy Hauwa tana "Dan Allah karki min haka mommy banida sama dake karki juyamin baya a lokacin danake bukatarki gurin wa kikeso naje idan kema kin gujeni dan Allah ki rufamin asiri kiyi hakuri wlh na gane kuskurena"


Mommy Hauwa bata wani bari maganganun Zara sunyi tasiri akanta ba ta fusge jikinta tayi waje da sauri.

Aunty khadija kuwa ta dafe kanta tare da zubewa akan kujera.


Zara rarrafawa tayi taje ta kama k'afar Aunty khadija tana rokonta akan itama kar ta juya mata baya Aunty khadija kuwa ta fusge k'afarta tare da zuba mata harara tana "kad'an da biyewa san zuciya kenan ai ga irin ta nan kin kai Aunty Hauwa bango ta Zare hannunta akanki sai kije ki karata ke kad'ai dan idan Abban Ummi ya dawo dole kisan nayi Dan bazaki goga min kashin kaza ba"

Daga haka ta mik'e tabar Zara nata kuka tana

Please Login or Register in order to submit comment