Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

sorry

Cikin sanyin murya ya kira sunanta yana "Aliya bansan mai zance miki ba amma am sorry bazan sake ba I promise you am a human being akwai abinda zanyi iya resisting d'inshi akwai abinda bazan iya ba most especially wen it comes to women but i would change all I need is your prayers am sorry pls"

Aliya wani kukan ta kara fashewa dashi dan ji tayi kamar zuciyarta zata fad'o sabida nauyin da ya mata tunda Adnan ya bud'i baki ya bata hakuri lailai ya Dade yana cin amanarta awaje tunda gashi ya fad'a da bakinsa

Wani tsanarsa taji ya darsu aranta atake ta cire hannunsa daga jikinta ta mik'e ahankali ta fita daga d'akin.

Wani wawan ajiyar zuciya Adnan ya sauke yana dafe kansa ya mik'e daga tsugunan da yake ya kara kallon mudubi yana bin inda Jan bakin Zara ya kwanta a jikinsa Sosa kansa yayi yana ta blaming kansa akan meyesa bai tsaya ya dubi mudubi ba kafin ya shigo cikin gidan sai da ya samu minti goma a tsaye kafin ya iya Jan k'afarsa ya nufi band'aki dan yayi wanka.


Aliya kuwa tana fitowa daga d'akin Adnan d'akinta ta shige ta kulle kanta ta cizgi kuka San ranta dan shi kad'ai ne zai rage mata nauyin da kirjinta yayi take wani irin ciwon kai ya rufeta da zazzabi dan ko yaya ta runtsa idonta sai zuciyarta ya ringa mata picturing abinda Adnan yaje ya aikata

Har Adnan yayi sallah yaje ya ringa kwankwasa k'ofarta ko motsi batayi ba tana dafe da kanta ko kad'an bacci bai ga idonta ba.


Adnan kuwa daya koma d'aki yana hawa watsapp yaji duk wani nauyi da yakeji ya kau zuciyarsa wasai dan Zara wasu irn zafaffan kalmomi taringa tura mishi na yanda warmth d'in lips d'insa yasa tayi loosing control she wish dat moment will last forever he is one of d best thing dat Eva happen to her a karshe ta tuttura masa pic d'in ta kusan half naked dan da k'aramin towel tayi d'aura kirji

Adnan kuwa juyi kawai yake wani irin farinciki na ratsa shi dan skin d'in Zara na notikan kansa ya kunce tuni ya manta da wata Aliya suka hau musayar kalmomi shima ya tura mata yanda yayi erecting sabida yanda kalmominta da jikinta suka tsuma shi.



Ameer kuwa tunda ya kai Zara gidansu ko sau d'aya baiyi danasanin hukuncin da ya yanke ba dan Zara Sam ba matar zama bace matsawar bata gyara halayyenta ba idan kuma yana so ya hararo yanda yake so ta zama idan ta nutsu tayi hankali sai zuciyarsa ta ringa hararo mishi kyaun halin Matar Adnan he wish Allah ya sa ta gyara halinta ya zama irin na Aliya ko da ba duka hallayen nata ta d'auko ba kasancewar yasan babu mace a gidan gidansu yaje yayi zamansa suka d'an tab'a hira da mahaifiyarsa dan Mahaifinsa ya rasu sai wajen sha biyun dare ya koma gida dan cewa mahaifiyarsa yayi Zara ta tafi biki gidansu yana kuwa shiga gida peaceful sleep yayi babu wani b'acin rai dan mai b'ata masa ran bata nan amma ko yaya ne yayi feeling rashin presence d'inta.



Mommy Hauwa kuwa tunda ta shiga d'aki itama ta tunano irin rayuwar dabbancin da akeyi a gidanta taci kuka ta gode Allah abinda ta saba yi na tayi Alwala tazo ta duk'ufa agaban Mahallicinta tayi ta adduoi tana rok'awa 'yayanta shiriya har mijinta dan tasan Allah ma'aji rok'on bawansa ne wataran zai amsa mata addu'arta ko ba jima ko ba Dade tana kan sallaya har taji lokacin da Zara ta shigo gidan inda tayi sauri ta kalli agogon d'akin dan taga lokacin da ta shigo

Hawayene ya k'ara zubo mata da tuna matsayin Zara na matar Aure ta fita kusan tsirara ta kuma dawo mata kamar wanan lokacin.

tunanin matakin daya kamata ta d'auka akan Zara ta fara yi dan babu yanda za'ayi ta zuba ido Zara tana ta fad'awa halaka dan idan ta Dr aka bi bai d'auki hakan amatsayin wani Abu ba.


sai da ta kai ukun dare tana tunane tunane inda a k'arshe ta yanke shawarar kiran wayar Ameer idan gari ya waye akan yazo ya d'auki matarsa su koma zata canja da izinin Allah inyaso sai ta k'ara yiwa Zara fad'a sosai.


Adnan sai wajen 8:30 ya tashi sabida yanda yayi baccinsa cikin nishadi tare da mafarkan Zara

Da sauri ya duro daga kan gadon yaje yayi wanka yayi alwala yayi sallah ya shirya dan ya tafi office d'an akwai meeting da zasuyi a office k'arfe 9:30.

Sai da yafito Palo ya kalli d'akin Aliya ya tuna abinda yayi mata lailai ba k'aramin fushi tayi ba dan bata tab'a kulle kanta tak'i fitowa ba sai yau tunawa da ayanzu ne ma zai sakata ya wala ba takura ne yasa ya fasa zuwa ya kwankwasa mata k'ofa yayi ficewarsa .


Yana rufe k'ofa Aliya ta share hawayen daya zubo mata dan tasan Adnan ya Riga da yayi nisa

yayi mata irin wanan laifin amma bai San ya biyota ya bata hakuri ba ba dan adduoin da ta kwana tanayi ba Daren jiya damuwar da take ciki ta d'an ragu da k'ila zuciyarta ta Dade da bugawa.


Wanka ta shiga tayi ta fito ta samawa kan ta abinci taci idon nan nata yayi luhu luhu sabida kukan da tasha

A kujerar palon ta kwanta tana ta tunane tunane inda duk tunanin da zatayi na ta hararo buduruwar da ta d'aukewa Adnan hankali awaje sai ta ringa hango fuskar Zara take kuma sai kallon da Adnan ya ringa mata ranar da ta shigo b'angarensu da sleeping dress sai ya fad'o mata

Tsintar kanta tayi da mik'ewa da sauri ta sako hijbanta dake Jan k'asa ta nufi b'angarensu Zara Dan akwai abubuwa da dama da takeso ta gaskata.

A hankali take k'wank'wasa k'ofar gabanta na d'an fad'uwa dan bata San wane irin tarb'a Zahran zata mata ba tunda ta wanka mata mari bata k'ara sata a idonta ba

Ameer da adai dai lokacin ya gama shirinsa tsaf zai fita aiki


"waye" yace yana d'an daga murya

A hankali tace "nice" kamar wacce bata San magana

Ameer kuwa ji da yayi ba'ayi magana ba yasa ya nufi k'ofar dan yaga waye

Da sauri Aliya ta Gaidashi tana k'ara sunkuyar dakai data ga shine ya bud'e k'ofar


Ameer amsawa yayi shima yana so yaga fuskarta dan har yau bai San ya kamaninta yake ba sabida tsabar kamun kai

"Zara na nan kuwa"?

Aliya tace dan duk a takure take

" wlh bata nan tana gida tun jiya"

Da sauri Aliya ta d'ago da kanta for d first time da Ameer ya fara ganin fuskarta

"Tabarakallah masha Allah ya tsinci kansa da cewa a zuciyarsa yayi sauri yayi isitigifari dan bai kamata ya yabi kyaunta ba amatsayinta na matar wani

" Lafiya dai ta tafi gida"?

Aliya tace tana kallonsa

Ameer Sosa kansa ya fara yi yana tunanin abinda zai ce mata sai kuma yake ganin gaya mata zai d'an sa ya samawa kansa mafita yanda idan Zara ta dawo zata ringa d'orata akan hanya

Gyara tsayuwarsa yayi yafara cewa "wato Aliya mun d'an samu sabani da Zarane na kaita gidansu duk ke mak'ociyarta ce nasan zaki iya sanin wasu abubuwan da Zara take yi da bai dace ba amatsayinta na matar Aure

duk da ina iya k'ok'arina dan na ganar da ita.

wasu abubuwan
bazan iya fad'a miki ba amma Zara tana min abubuwa da hakuri kawai nakeyi da ita a musulunce kinsan yanda ya kamata ace matar Aure ta ringa suturta jikinta amma babu wanan a tsarin Zara wani shigar ma idan tayi ko buduruwa bazata yi ba ballantana ita da take da Aure shigar da taga dama kawai takeyi, duk da tasan bamu kadai ne a gidan ba.

yanzu kamar ranan kinga irin shigar da tayi ta taho b'angarenku ta kuma tsaya agaban mijinki da tasan haramune ya ganta a hakan bayan Wanan akwai abubuwa da take min da dama shiyasa nikuma da naga nayi mata wa'azin nayi mata nasihan duk abanza jiya na maidata gidansu dan iyayenta su koya mata zamantakewar Aure ko zata San darajar Aure.


Tunda ya fara magana Aliya kanta a sunkuye yake tana jin abinda yake cewa inda duk maganganun da ya ringa yi a nutse cikin ilimi da hankali ta fara hararo mijinta da bashi da burin ma daya wuce ita ta fidda tsiraicinta idan zasu fita acikin maganganun da Ameer yayi ta hango tarin ilimi da sanin ya kamata atattare dashi sai taji inama haka Adnan yake da ilimi da kishin iyali

Da sauri ta kau da tunanin da take Tafara magana "Ameer ba abinda zan iya cewa sai dai na baka hakuri ka kuma cigaba da hakuri da itan maidata gidansu da kayi ba mafita bace ka dawo da ita ka cigaba da yi mata nasiha zata daina insha Allahu nima zan ringa nusar da ita idan ta dawo"

"To shikenan Aliya ngd sosai agaida Adnan d'in"

Aliya da sauri ta juya tana zaiji


Ameer kuwa ya bita da kallo har ta fice yana assuming ina ma haka Zara take da ya more ko k'afar Aliya baka hangowa sosai sabida yanda hijabinta ke sharar k'asa yana cikin kulle k'ofar dan ya tafi wajen aiki yaji wayarsa na ringing.

Zaro wayar yayi daga Aljihunsa yaga bai San Lambar ba

D'agawa yayi tare da kara wayar a kunnensa yayi sallama


Mommy Hauwa amsawa tayi kafin tagama amsawa Ameer ya hau gaisheta dan ya gane muryarta

Bayan sun gama gaisawa Mommy Hauwa tace yazo tana San ganinsa idan ya gama abinda yake yi.

Cikin girmamawa yace insha Allahu idan ya baro office zai zo daga haka sukayi sallama ya katse wayar.


Mommy Hauwa babu Wanda ta gayawa ta kira Ameer dan tasan Zara zata iya bijire mata Dr kuma ya hana tafiso kawai yana zuwa ya tafi da ita.

Zara kuwa moment d'in da ta yi da Adnan kawai take tunawa tana daga d'aki har yanzu tana jin bakin shi cikin nata komai na Adnan yayi mata gashi he is romantic agaskiya yau zata tambayeshi idan sun had'u akan zata kashe Aurenta ya aureta dan yanda take jinta she can not do without him.

Wuni sukayi suna waya dan tama fi kiranshi awaya inda Adnan yace ta shirya K'arfe 9 zai zo suje suyi dinner daga nan su d'an yi catching fun


Zara ai ji take kamar lokaci baya tafiya she 'is earger ta k'ara sa Adnan a idonta ta tsotsi Wanan lips d'in nasa mai dadi kamar swt.


K'arfe 9 Dai dai Ameer yayi parking a k'ofar gidansu Zara ya fito daga motarsa ya jingina da jikin motarsa ya Ciro wayarsa daga Aljihunsa dan ya kira Mommy Hauwa yace mata ya k'ara so

A dai dai lokacin shima motar Adnan ya karyo kwana tare da parking a opposite d'in motar Ameer yana jiran fitowar Zara Dan Sam bai ma lura da motar dake kallon motarsa ba ballantana har ya lura da Ameer dake tsaye


Zara dayake tun kafin Adnan ya k'ara so ya kirata data fito ya k'ara so

Shiri tayi sosai da wani gown mai bud'dden kirji ya bayyana duk wani sura da Allah ya mata ko bra bata saka ba aganinta Bra na hana Adnan yayi wasa da albarkatun kirjinta wani mugun hill tasa ka da sirirrin mayafi sai bulbula kamshi take.

Cike da yauki da yanga tafito daga d'akinta aikuwa luckily babu kowa a palon dan Mommy Hauwa bata Dade da shiga d'aki dan ta watsa ruwa a jikinta ba.


Sa sauri ta fice ta nufi k'ofa tana wani irin cat walking ko wane taku d'aya sai ko ina na jikinta ya girgiza


K'arar b'ude gate d'in gidan ne yasa Ameer daya k'ara waya a kunnensa yana ta jiran yaji an d'aga

ya d'aga kansa ya kalli k'ofar gate d'in gaban Ameer yayi wani irin mummunan fad'uwa ya zubawa Zara ido kamar bai tab'a ganinta ba.


Zara itama turus tayi jikinta ya fara rawa a lokacin da taga Ameer a k'ofar gidansu.


Adnan da shima tunda ta fito ya zuba mata ido ganin ta k'ame waje d'aya tana kallon wani waje yasa ya juya dan yaga mai take kallo


Wani irin kululu cikinsa yayi take yaji wani mugun fitsari na Neman zubo mishi dan Ameer yasan kalar motarsa da plate number d'insa tunda ma awajensa ya siyi motar........dan dan dashhhhh😨😨😨😨😨




Hewe Adnan en Zara are in trouble oooo🙆‍♀🙆‍♀🙆‍♀🙆‍♀🙆‍♀
*M🅰K'OT🅰N JUN🅰*


*REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS* *P.M.L*



*Written by*

💅💅💅 *SADNAF*💅💅💅



*Follow me on wattpad @ Sadnaf*


*DUK reader da bata karanta Abokai ba na marubuciya Shauty ta bar dadi dan littafine mai k'unshe da tsantsar darasi kuje Ku nema Ku karanta Nima karatun shi ya hana ni typing jiya*

*SHAUTY NA JINJINA MIKI DA WANAN FASAHA DA KIKA BAJE A WANAN LITTAFIN NAKI ABOKAI MORE INK TO UR SPARKLING PEN*


Page 9


Zara jikinta ne ya d'au rawa ko ta ina cikinta ya ringa murd'awa Dan Duk da bata da burin da ya wuce Ameer ya saketa amma ta tsorata da ganinsa


Ameer kuwa tun daga kanta zuwa k'afarta kawai yake bi da kallo zuciyarsa na masifar harbawa ko kad'an bai kifta idonsa ba dan so yake ya tabbatar da abinda idonsa ya gane masa Zara cikin shigar banza duk da akwai tazzara a tsakaninsu yana hango yanda kirjinta ke tsaye bai ma lura da motar Adnan ba dan bayaso ya d'auke idonsa daga kanta jikinsa sai rawa kawai yake zuciyarsa namasa wani Zafi.

wani Mugun tsanar Zara ya fara mammaye shi.


Adnan kuwa ganin Hankalin Ameer na kan Zara yasa yayi kicking motarsa cikin zafin nama tare da reverse ya kashe fitilar motar bai damu da ya kalli ko akwai wani abayansa ba gudun kar ya take shi yayi reverse da gudu duk da pole d'in wuta da motarsa ta daka glass d'in bayan motarsa ta fashe bai damu ba ko kad'an burinsa kawai kar Ameer ya ganshi


Ameer yanda Adnan yayi reverse ne yasa yayi sauri ya juya yana kallon motar amma bai iya ganin komai ba ballantana ya gane Wanda yake cikin motar sabida fitilar motar a kashe kuma wajen da d'an duhu

Take k'wak'walwarsa ta basa abinda ke faruwa wato wani ne yazo wajen Zara shine tayi wanan kwalliyar Wanda ya bayyana tsiraicinta ta fito ta sameshi.

take jikinsa ya fara rawa idon nan nasa ya kad'a yayi ja Kirjinsa kamar ya bindige sabida Azabar kishi da tsanar Zara.

Zara kuwa tana Ganin Adnan yayi reverse Ameer bai gane shi ba ta saki wani Wawan ajiyan zuciya had'e da dafe kirjinta dan yau da Ameer yasan Adnan ne yazo wajen ta da kashinta ya bushe

Juyawa tayi da sauri ta shige gidan

Ameer ya bita da gudu Wanda hakan ya sa itama Zaran ta kwasa a guje


Tana dab da shiga palon ya kamota ya kwashe ta da wasu zafaffan mari biyu daya sa taga stars

Wani mugun Ihu ta k'walla daya sa Dr Mommy Hauwa da Khalid dake zaune a palon suka yo hanyar waje da gudu.

Inda suka Tarar da Zara a durk'ushe ta dafe kumatunta

Ameer kuwa sai wani irin huci yake jikinsa na rawa dan da ace yau daga shi sai Zara ne mai k'watarta a hannunsa sai ya shirya


Dr Ware idonsa yayi sosai dayaga Ameer a tsaye

Zara kuwa ta tafi da gudu ta rungume shi cikin kuka tace Ameer ne ya zo har gida ya rufeta da duka kuma shi yace mata ta fito ta same shi a waje.

Ameer mamakin karyar da Zara tayi ne yasa ya saki baki yana kallonta

Dr kuwa ya zame Zara daga jikinsa yana "dan baka da mutunci dukan daka mata a gidanka bai isheka ba sai ka biyota har gida da kazo gidanma kasa ta fito ka rufeta da duka how there you"

Dr yace yana shararawa Ameer Mari ya k'ara d'aga hannunsa da zumar ya k'ara masa

Mommy Hauwa tayi sauri ta rik'e masa hannu cikin tsananin b'acin rai ta wancakalar da hannunsa tace


"Dr kaji kunya arayuwarka wlh 'yar cikinka ta tsara maka karya ka hau kai ka zauna dubi shigar dake jikin 'yarka da sunan tana da Aure tazo kuma tace mijinta ne yace tazo ya hau dukanta data fita Wanda karya take yi ni na kirashi nace yazo na sassantasu amma ta shirga maka irin wanan karyar ba bincike ba komai ka hau kai ka zauna.


" Dr a tunaninka akwai Wanda zai iya jure halin Zara ya zauna da ita idan ba Ameer d'in ba har ta kwaso k'afa tazo gida kayi supporting d'inta ta zauna a gida tana janyo maka balai.


"Wai yaushe zaka gane hanyar daka d'ora 'ya'yanka akai ba hanya bace mai kyau"?


Zara da haushin Mommy Hauwa ya gama cikata cewa tayi " nidai kawai yabani takkadata bazan zauna da mahaukacin da bai San darajar mace ba Abu d'aya biyu duka na tsane shi bana San komawa gidansa Daddy kasa ya bani takardata wlh bazan koma gidan ba.

Daddy wani mugun kallo yake bin Mommy Hauwa dashi tunda ta fara magana "ke ai dama dakikiya ce bakisan mai kikeyi ba aci zarafin 'yarki dayake bakida hankali kika hau shigar masa to bari kiji na gaya miki am giving u last warning babu ruwanki da shiga sabgar 'ya'yana ban yarda a takurawa 'ya'yana ba kinji na fad'i miki,Mr Man out of my house duk ranar da ka k'ara gigin tab'a Zara aranar zaka San koni waye"

Daga haka ya koma Palo tare da banko k'ofar.




Ameer tsabar bak'inciki da takaicin sirikinsa da bai San darajar kansa ba ballantana yasan na mutane girgiza Kansa kawai yayi ba dan yana Auren 'yarsa ba kuma a haife ya haife shi ba da babu abinda zai hanasa Zaginsa.

Wani mummunan kallo mai tare da tsantsar tsana ya watsawa Zara da idonta ke barazanar fitowa sabida harara

Ya juya ya nufi hanyar waje

Zara tayi sauri ta sha gabansa ta rik'e kugu tana " dalla bani takardata nagaji da zama da kai"


Mommy Hauwa tunda Dr ya zageta agaban Ameer hawaye masu zafi suka hau sintiri a fuskarta zuciyarta kamar ta fashe dan bakin ciki

Jin abinda Zara tace ne yasa ta tsayar da Hawayen da take cikin tashin hankali ta nufi wajensu tana

"Ameer Dan Allah kayi hakuri karka saketa batasan mai takeyi bane zan mata fad'a Dan Allah zan nemeka da kaina am sorry for oll dat happened.

Ameer duk da yana balain jin nauyin Mommy Hauwa sai dayace " Mommy ni aganina rabuwar mu shi zai fi min alheri Zara ba matar zama bace ki dubi shigar dake jikinta mommy nan da sunan da igiyar Aurena akanta kuma ahaka wani ne yazo wajenta ta fita waje zata je ta same shi shine tagani badan kin kirani Nazo ba da ahaka zata je ta same shi Mommy da Aurena fa akanta take muamalla da wasu mazan.
Alhamdulillah naji dadi da kuka ganewa kanku irin shigar fidda tsiraici da Zara keyi Mommy haka nake fama da ita sallah sai taga dama takeyi bata wani girmamani a matsayina na mijinta

Mommy
Zara gaskiya bata San darajar Aure ba bata San ciwon kanta ba ina iya kan k'ok'arina Dan in nusar da ita gaskiya amma ina gani take ina takura mata dan haka Mommy nima nagaji da ita gwara kawai na saketa"

"Uban me kake jira ka sakeni mana da wanan dogon bayanin da kake yi"


Zara tace tana jifansa da wani mugun kallo dan burinta bai wuce ya saketan ba ta samu freedom ta wataya San ranta and kuma tasan Adnan zai Aureta


Tagwayen Marin da batayi expecting a wajen Mommy Hauwa ba taji ya sauka a fuskarta dayasa ta kurmance na sakanni.

"Shasha Mara mutunci ina tausaya miki idan kika rasa Ameer dan ba zaki tab'a samun irinsa ba Shaidan nata kad'a miki ganga kina abinda ranki keso wlh idan bakiyi wasa ba wlh sai kinyi kuka da kanki kinyi Dana sani Mahaifinki dake d'aure miki gindi wlh ba gata yake miki ba Dan shi ya Riga da yagama nasa rayuwar kefa idan kina da tsawon rai yanzu kike mataki na farko arayuwa".



" Ameer Dan Allah kayi hakuri nasan kana hakuri da Zara ba kowane namijine zai jure halinta ba amma kayi taimakon musulunci idan ka saketa yanzu k'ara lalacewa zatayi ta k'auce hanya ka cigaba da aikin lada kana mata nasiha da wa'azi zata gyara insha Allah Ameer tamkar d'ana na d'aukeka wlh ni kadai nasan irin jarrabtar da Allah yamun akan yaranan a sanadinsu na kamu da hawan jini daddare bana iya bacci yanzu idan ka saki Zara ta dawo gabana da zama Allah kad'ai yasan halin da zan shiga kayi hakuri goben nan zan dawo maka da ita tana so ko bata so"



Tausayin Mommy Hauwa ne kawai yasa Ameer ya k'asa magana ballantana ya musa mata amma kam da ta shi ne yau zai wurgar da kwallon mangaro ya huta da kud'a ganin Mommy Hauwa na Hawaye tana jiran taji mai zaice yace

"Ba komai Mommy Allah yasa ta gyara"

Da sauri ya juya ya fice daga gidan sabida kallon Zaran da yake yi zuciyarsa nata ingizarsa da ya rufeta da mugun duka yana jiyo kururuwar Zara tana rantsuwa da ita bazata koma gidansa ba.

A fusace ya bar unguwar dan har yanzu zuciyarsa tafasa take yana tunanin wane k'aton dan iska ne yazo wajen Zara Al halin yasan tana da Aure kenan Zara tana muamalla da wasu mazan Awaje indan kuwa hakane ba k'aramin sa mata ido zaiyi ba dan yanzu zai ringa bincikar wayarta.


Adnan kuwa a tamanin ya k'arasa gida bai gama parking ba sosai yafito aguje sakamakon wani mugun gudawa data matso shi dan ayau kam ya tsallake rijiya da baya

Aliya dake kwance a palo tana tunanin rayuwarta da Mafita

Gani tayi ya shigo aguje tun a Palo ya cire wandonsa ya nufi band'aki da gudu


Bata ko damu da abinda ya dawo dashi ba cigaba da tunaninta.

Adnan sai da ya samu minti Ashirin a band'aki yana sharce zufa dan ya d'auka asirinsa ya gama tonuwa Ameer ya gane shi.

Dak'yar ya fito waje still yana share zufa

Ya nufo Palo kamar Wanda kwai ya fashewa a ciki ya kalli Aliyan dake kwance abinta tana kallon ceiling har d'an fad'awa tayi daga jiya zuwa yau.

Wajen dining ya nufa yaga ko ta masa girki aikuwa kafin ya k'arasa yajiyo karar motar Ameer.

Taku biyu yayi ya shige d'aki jikinsa na rawa dan gani yake Ameer zuwa gida yayi yaci ubansa yasan shine yaje wajen Zara ......

Make una manage biki tnzzzz yaseen kila Sunday or monday
*M🅰K'OT🅰N JUN🅰*


*REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS* *P.M.L*




® REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS

ɯɛ ɖơŋŧ ʝųŞŧ ɛŋŧɛřŧąıŋ ŋɖ ɛɖųĆąŧɛ, ცųŧ ɯɛ ąٳŞơ ŧơųĆɧ ɖ ɧɛąřŧ ơʄ řɛąɖɛřŞ


# WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
# IG PML WRITERS
# https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-08144932303


*Written by*

💅💅💅 *SADNAF*💅💅💅



*Follow me on wattpad @ Sadnaf*


*page 10*


Aliya tashi tayi Zaune tana mamakin abinda ya tsorata Adnan

A hankali ta mik'e taje bakin window ta d'aga labule dan taga ko dai wani ne ya shigo gidan taga babu kowa sai Ameer dake kulle motarsa.

Tab'e baki tayi ta koma ta kwanta dan yanda take jin zuciyarta bata jin zata iya yiwa Adnan hidindimu da take mishi idan ya dawo dan daga yanzu sai ta k'aurace masa har sai taga alamar ya shiga hankalinsa.


Adnan kuwa sai da yasamu minti Ashirin a zaune jikinsa na d'an rawa kafin ya fara samun nutsuwa tare da godewa Allah da Ameer bai gane shi ba.

Yunwar dayake balain ji ne yasa ya fito d'aga d'aki ya nufi wajen dininng bayan ya gama satar kallon Aliya dake kwance idonta a rufe tana k'ark'ad'a k'afa.

Ajiyar zuciya ya sauke a lokacin da ya bud'e kulollin yaga hadaddiyar tuwon shinkafa da miyar taushe ga wani kunun Aya mai sanyi agefe

Juyawa yayi ya k'ara kallon Aliya da bata motsa ba tana nan yanda take duk da taji motsin fitowarsa inda Dane sai ta zo ta zuba mishi abincin ta tabbatar da yaci ya koshi ahakan

Please Login or Register in order to submit comment