Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Adnan akan ya bata kudi ce mata yake bashi da ko biyar cikinta na shiga wata shidda ta shirya da kanta ta fara zuwa asibitin gwamnati awo inda Anan ta fara samun saukin laulayin da take yi cikinta ya daina mata tsurfar zaban abincin da zata ci dan kome ta samu yanzu sai taci


B'angaren Ameer kuwa tunda Aliya ta gama idda ya fara nuna mata yana santa duk da bai fito ya fad'a mata kai tsaye ba amma yana ta nuna mata alamomin amma ina Aliya ma nuna masa take batasan abinda yake nufi ba dan idan yaje bai fiye samun fuska a gurinta ba Rabin hirar shi yake yi eee da aa kawai ne amsar ta fuskar da bai samu ya sa ya kasa fitowa ya gaya mata abinda ke ransa game da ita ga wani irin kaunarta dake dawainiya dashi dan zai iya cewa tunda yake bai tab'a yiwa mace irin san da yake mata ba haka ya cigaba da zuwa wajenta indai zaije sai ya tafar mata da wani abun.


A yau ya kuduri niyyar gaya mata abinda ke zuciyarsa bayan ya dawo daga office ya shirya cikin wani lallausan yadi coffe color daga hula har takalminsa duk kalar yadin ne yayi kyau ba karya sai da ya kalli kansa a mudubi ya kara gyara zaman hulansa ya sakarwa kansa murmushi dan yasan yayi kyau mukullin sabon motarsa da ya siya kwana uku da suka wuce ya d'auka yayi hanyar waje.

Motar tasa kuwa sai kyalli take sai da yafara shiga main house d'in yacewa Hajiya Ameena zai tafi wajen Aliya tayi mishi addua Allah yasa ta k'arbeshi da hannu biyu Hajiya Ameena murmushi tayi ta mishi adduar Allah yasa su daidaita daga nan ta mik'e ta shiga d'aki ta had'o kayan kwalliya turaruka masu kamshi da turmin atamfa ta kawo wa Ameer tace ya bawa Aliya tace injita.


Ameer cikin farinciki ya amshi ledar tare da mata godiya.

K'arfe biyar da rabi ya isa gidansu Aliyan ya kirata a waya yace mata gashi nan awaje.
Aliya dake kwance kanta akan cinyar Hajiya Rukayya tsaki tayi tace "gaskiya nikam wlh Ameer ya fara takuramin"



Hajiya Rukayya murmushi tayi tace "Ummm anya nidai zaryar da yaron nan yake yi akanki ba sanki yake yi ba"?

Aliya da sauri ta mik'e tana " Haba Hajiya ya zakice sona yake yama zai soma tunanin haka Mak'ocinmu ne fa"


"To haramune kijiki da wani magana Allah ma yasa ma san naki yake ai da kin dace da nagartacen miji kinsan yanda Abbanku yake kaunar yaron nan kuwa yake yabon kyawawan halinsa"


Aliya tashi tayi daga zaunen da take ta mik'e tana "ni ba abunda zanyi da Ameer wlh ni bana ma san Auren yanzu sai na huta sosai na nutsu fatana dai ki kara rok'ar min Abba ya barni dan Allah in cigaba da degree d'ina"

Hajiya Rukayya murmushi tayi tace "kije ki sameshi kin bar shi waje tundazu zaki cigaba da Degree d'inki a d'akin mijinki insha Allahu"


Aliya d'akinsu ta shige ta sako bakin hijabinta mai hannu ta d'an fesa Turare ko hoda bata shafa ba tayi hanyar waje tana mai d'an daura fuskarta dan tunda Hajiya Rukayya tace kila santa yake yasa ta shirya mishi kora da hali.


Ameer tun daga nesa ya zuba mata ido yana hadiyar yawu sabida mugun kyau Da Aliya tayi mishi dan fatarta wani irin glowing yake duk da babu make up a fuskarta har tunani yake idan zata yi kyau a cikin hijabi haka ya kyaunta zai zama idan babu Hijabi zai so ya ganta babu Hijabi yasan sai tafi haka kyau a fili.

Har ta k'araso wajensa kanta a sunkuye yake cikin siririn muryar ta Tayi mishi sallama

Ameer ya amsa jikinsa a sanyaye dayaga yanda ta d'aura fuska.

Bayan sun gaisa shiru sukayi dan Ameer ji yayi gabad'aya ya nemi kuzarinsa ya rasa wani sashe na zuciyarsa na ingiza shi akan ya gaya mata kawai a wuce wajen wani sashe na zuciyarsa na hana shi.

Aliya kuwa kanta a sunkuye yake tana wasa da k'asan Hijabinta sau d'aya ta d'ago ta kalleshi duk da yayi bala'in kyau hakan bai sa ya wani burgeta ba.


Sai da suka samu minti goma sha biyar ahaka Aliya kuwa ganin yak'i magana ya sa ta d'ago tace "ina girki ne fa zan koma ciki dan kar girkin nawa ya k'one"


Ameer fitowa yayi daga motar dan tunda tazo yana zaune a ciki k'afafunsa kawai ya zuro waje.



Gyara tsayuwarsa yayi yana kallon Aliya bayan ya tattaro duk wani kwarin gwiwarsa yace

"Aliya akwai wani magana danake so na fad'a miki duk da bansan ya zaki amshi maganar tawa ba barin kashi a ciki baya maganin yunwa so gwara yau dai na fito na gaya miki abinda ke cikin zuciyata game dake Aliya a gaskiya Allah ya jarrabceni da so da kaunar ki na Dade ina Adduar Allah yabani mace mai irin halayenki mace da zata zamo uwar ya'yana da kuma dukan alamun kece macen da Allah ya zaba min lura da kaunar ki da na wayi gari dashi dan Allah Aliya kisa min wuri a zuciyarki dan nasan da wuya ki iya kuma yarda da wani namijin amma inaso kisan ba'a taru an zama d'aya ba insha Allahu bazaki yi nadamar aurena ba"


Tunda ya fara magana gaban Aliya ya fara fad'uwa dan bata tab'a tunanin Ameer zai Ce yana santa ba dan aganinta ma duk da sun rabu da Adnan shima ya rabu da Zara idan yace yana santa tamkar sunci amanarsu ne"


Sai da suka samu minti goma yana jiran yaji mai Aliya zata ce yaji tayi shiru ta k'i magana

Sai da ya k'ara mata magana ta d'ago tace "Ameer a gaskiya kayi hakuri bazan iya auranka ba dan gani nake kamar munci amanar Zara ni yanzu ma ba aurene agabana ba makaranta zan koma dan Allah kayi hakuri Allah ya baka wacce tafini"


Daga haka ta juya da sauri ta nufi cikin gidan.


Ameer binta yayi da kallo har ta shige cikin gidan inda hankalinsa yayi masifar tashi dan duk fitar numfashinsa sai San Aliya ya linku a ransa.


Sai da ya samu minti goma a tsaye yana tunanin abinda ya dace yayi kafin ya shige cikin motarsa ya tafi.....

*M🅰K'OT🅰N JUN🅰*


*REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS* *P.M.L*




® REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS

ɯɛ ɖơŋŧ ʝųŞŧ ɛŋŧɛřŧąıŋ ŋɖ ɛɖųĆąŧɛ, ცųŧ ɯɛ ąٳŞơ ŧơųĆɧ ɖ ɧɛąřŧ ơʄ řɛąɖɛřŞ


# WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
# IG PML WRITERS
# https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-




*Written by*

💅💅💅 *SADNAF*💅💅💅



*Follow me on wattpad @ Sadnaf*


*HABIEBA LV THANKS FOR D LOVE EN CONCERN I LOVE U SO VERY MUCH*


*THIS PAGE IS OLL URS SAWWAMATA U ARE D CINGUM OF MY HRT* 😍😍😍



*page 26*


Aliya kuwa tana shiga ciki ta zube akan kujera tana sauke ajiyar zuciya kamar wacce tayi tseren gudu.


Hajiya Rukayya dake zaune mik'ewa tayi tana "ke lafiyarki kuwa mai haka kika shigo kina haki kamar wacce ta sha gudu"?

" Hajiya nida Ameer ne mana wlh ya bani mamaki wai kiji sona yake zai Aureni ko kunya baiji ba salon ace dama can soyayya mukeyi dashi"


"Laillaha illallahu Aliya mai abun kunya aciki dan yace yana sanki mai kika ce masa?

Aliya zumb'ura bakinta tayi tace " hakuri na basa nace yayi hakuri dan Gaskiya bazan iya aurensa ba"

"Amma ke kuwa anyi sokuwar yarinya wlh Allah ya saka miki abinda Adnan ya miki ta hanyar baki Salihi kamar Ameer kice bakya so anya kina ma da hankali kuwa ke daya kamata ace kinfi kowa murna kinsamu hanyar da zaki cusawa Adnan bak'in ciki dan ni nasan idan yaji labarin Ameer zaki Aura sai yafi kowa shiga tashin hankali da bak'in ciki shine zakice bakya sansa to bari Alhaji ya dawo na fad'a masa zakiga yanda zaki kwashe dashi kullum sai ya min maganar Ameer akan yana San ya mashi maganarki amma yanzu Allah yasa ya kawo kansa kince bakyaso"

"Haba Hajiya ya zaki gayawa Alhaji Dan Allah kiyi hakuri ni idan Auren ne ma kukeso kuyi Min ku samo min kowaye banda Ameer dan Gaskiya bazan iya aurensa ba"


"Idan na tashi gayawa Alhajin anjima sai kizo ki matse bakina"

Hajiya Rukayya tace tana zabga mata harara tare da nufar d'akin ta.

Ameer kuwa yana isa gida ya zube akan cinyar Hajiya Ameena dake cin abinci


Hajiya Ameena kuwa ta d'ago shi da sauri da d'aya hannun nata tana tambayarsa mai yafaru.


Ameer a hankali yace "Hajiya tace bata sona wai bazata iya aurena ba inyi hakuri Allah ya bani wacce ta fita"


Yanda yayi maganar kamar Mara lafiya ne yasa Hajiya Ameena sakin murmushi

Wanda hakan yasa Ameer k'ara daura fuska yace "Haba Hajiya kinji kuwa mai nace kike murmushi cewa nayi miki fa Aliyar tace bata sona"


Murmushi Hajiya Ameena ta k'ara yi tace "najika sarai Ameer ai Dariya kabani ne dan bansan yaushe ka zama ragwon namiji ba da tun ba'aje ko'ina ba za kabi ka karaya haba dan Allah kamar ba Ameer d'ina ba ai ba'ayi macen da zata ce bata sanka ba"


Ameer shagwabe fuska yayi yace "Hajiya dan Allah kibar batun wasa wlh hankalina ya tashi bana San na rasa Aliya dan wlh Allah ya jarrabceni da santa bazan iya jure rasa ta ba Aliya irin macen dana Dade nake fatan ta zamo uwar 'ya'yana ce dan wlh halinmu yazo d'aya da ita ina aureta na samu Aljannar duniya"


Hajiya Ameena tagumi tayi tace "oooo yanzu Ameer kafisan Aliyar nan akaina kenan"

Tayi maganar tana matse matsen ido aikuwa Ameer Dariya ya kyalkyale dashi Wanda hakan yasa itama Hajiya Ameena sakin murmushi dan dama abinda take so kenan

"Karka damu Ameer insha Allahu Aliya zata soka za kuma ta aureka karka wani karaya dan dama dole kafin ta aminta da kai sai an kai ruwa rana lura da yanda namiji yaci mata amana kaga kuwa yanzu kafin ta kara yarda da wani namijin za'a d'an dau lokaci Dan haka karka wani damu kanka
nace mata zaka yi ka cigaba da zuwa ni nasan insha Allahu wataran zata kaunace ka"


"Hajiya anya bake zakije min gidan ba ki roketa kila taji nauyinki ta yarda ta Aureni"


"Ooo ni Ameena wai gaggawan na menene Ameer kabita a hankali mana ni nasan zata soka wlh"


"Aaa nidai Hajiya ina tsoron wani ya rigani gwara dai kije min dan Allah"


"Ka dai cigaba da zuwa Ameer idan naga alamar bazata saurarekan ba sai naje gidan nasu da kaina kaji babana maza wanke hannunka muci abinci dan dama nasan baka wani ci abincin rana ba sabida dokin zuwa wajen Aliya ooo ni kam zanso naga wanan Aliya data susutar min da d'a"


Ameer murmushi yayi yana wanke hannunsa yace "Hajiya Bazaki gane ba Aliya ta had'u ko ta ina shiyasa nace miki tsohon mijinta bashida rabon duniya Dan Wlh Aliya macece da kowane namiji zaiyi fatan ya sameta a mata shiyasa kika ga na dage dan tana da tarbiyya sosai ga kunya wlh ban tab'a ganinta babu Hijabi ba"

"Allah sarki ai ana samun irinsu wlh idan kaga haka gidansu an Gina shi akan tarbiyya ne ba kamar waccar kwashashiyar da mahaifinta ma tarbiyya tayi mishi karanci ba dan ko a lokacin daka dage sai ka aureta babu yanda zanyi dakai ne dan Sam ba'a fadi kyawawan halin 'yan gidansu ba daga dan iska sai dan shaye shaye kuma ance Mahaifinsu ne ya lalatasu haka"


Ameer hadiye loman tuwon da ya kai bakinsa yayi yace

"Allah sarki har kin tuna min da Mahaifiyarta wlh Dan shekaranjiya ma ta kirani tana tambayata ko naji labarin inda take nace mata wlh ni ban ma kara zuwa unguwar nan ba ballantana naji labari yarinyar nan sai tayi nadamar abinda tayiwa Mahaifiyarta dan bakiga wulakancin data mata ba Hajiya har zaginta tayi amma ki duba kiga yanda ta damu da ita ko ina ta shiga oho yarinyar nan tayi nisa wlh"


Hajiya Ameena tab'e baki tayi tace "gwara ma ta manta da ita idan ba haka ba bak'in ciki yayi ajalinta dan wanan kam tayi Nisan da bazata ji kira ba sai dai idan duniya ta koya mata hankali"

"Allah ya shiryeta idan tana da Rabon shiryuwa"


"Ameen bari a karo maka tuwon naga ka kusa cinyewa"


Hajiya Ameena tace ta mik'e tare da nufar kitchen.


Aliya a zaune take agaban Alhaji Abubakar tana ta matse hawaye sabida yanda yake zabga mata fad'a kamar zai daketa dan yana gama cin abinci Hajiya Rukayya ta kwashe komai ta gaya masa

"Banda rashin hankali da tunani awane dalili zakice bakya San sa ko har yanzu wanan Dan iskan mijin naki kikeso"


Aliya da sauri ta d'ago ta fashe da kukan bak'inciki dan ko kad'an bata so ma taji sunan Adnan ballantana akai ga ace tana San sa cikin kuka tace "ni wlh bana sansa ko sunansa bana San ji"


"To idan bakya sansa awane dalili zakice bakya San Ameer yaron dan mutunci da yafito daga gidan tarbiyya dan har mahaifinsa ya rasu wajen shekara biyar kenan har yanzu ana yabon kyawawan halinsa idan ba Wanda bashida rabo ba babu Wanda bazai so ya had'a zuria da 'yan gidan ba yaro nagartace irin Ameer kice bakyaso abinda godewa Allah ya kamata kiyi da ya saka miki da abinda wancan dan iska manemin matan ya miki ta hanyar baki Wanda ya fishi nesa ba kusa ba yaron da kullum cigaba yake arayuwarsa yana k'ara samun matsayi awajen aikinsa sabida kyawawan dab'iunsa wancan kuwa dan iskan tsohon mijin naki shi k'ara tab'ewa yayi ya lalace dan Yanzu aikin DJ yake yi"


Hajiya Rukayya da Aliya a tare suka ce "Djjj"?



Alhaji Abubakar yace "kwarai kuwa DJ fa dan yanzu duk inda ake bad'ala a garin nan shi ake kira yayi DJ shekaranjiya Alhaji Saminu ke bani labari dan a unguwarsu yake ance har mace ya ajiye a gidan mai cikin shege"

Hajiya Rukayya zaro ido tayi tana
"Subhanallahi kace yaron ya K'ara nisa ooo Allah mungode ma da Aliya bata had'a zuria dashi ba da ya zamuyi"


Aliya kuwa runtse idonta tayi tana mai k'ara jin tsanar Adnan aranta

Alhaji Abubakar kuwa yace "Dan haka ki gayawa 'yarki Ameer Alherine agareta gwara ta amshe shi hannu bibiyu dan kowane uba zai zo 'yarsa ta Auri irinsa idan kuma ba San tsohon mijinta take ba"


Aliya kuka ta k'ara fashewa dashi tace "ni wlh bana kaunarsa ko sunansa bana San ji"

"To idan hakane ki ringa sauraran Ameer a hankali zaki so shi dan idan zan samu ne ma na had'a aurenki dana kanwarki sumayya nan da sati biyar masu zuwa kiringa kula shi karki sake ki kara wulakanta shi kinji mai nace ko"?


Aliya gyad'a kanta tayi a hankali tana share hawayen fuskarta Alhaji Abubakar yace ta tashi ta tafi.


Ta mik'e ta nufi d'akinta tana zuwa ta zub'e akan gado tana tunanin yanda zata soma ma San Ameer ballantana har ya kai da ta aure shi.



Kid'a ne yake ta tashi a wani k'aton hall da ake bikin wasu Amare biyu.


Adnan shine Djn da aka kira awajen bikin yayi shigar bak'akk'en kananan kaya yayi masifar kyau dan tunda ya fara harkar DJ yake wani irin gayu yana ajiye saje

Kai idan ka gansa kaga Wanda yake masifar ji da kansa


Yana daga zaune agaban manyan speakernsa ya k'afa head phone a kunnensa yana cacanza wakokin da ake yayi acikin system D'in dake gabansa 'yan mata nata ihu da shewa.

Girgiza kansa kawai yake yi yana Dan rawa da jikinsa jefi jefi sai ya d'ago ya kalli yanda 'yan mata ke dancewa a tsakiyar Fillin.

Wak'ar Kizz Daniel yasa "Baba"

'Yan matan suka saki shewa da ihu hakane yasa shi d'agowa da murmushi asaman fuskarsa aikuwa idonsa ya sauka akan wata kyakyawar hallitar data kusa sa numfashinsa d'aukewa.


Kyakyawa ce idan aka ce kyakyawa irin first class d'inan

Adnan hadiye yawu yayi ya k'ara ware idonsa yana kallonta fara ce tas mai d'auke da doguwar fuska da dogon hanci idonta yafi ko'ina kyau dan irin lumsassun idonan ne da ita farare tas gasu manya kallo d'aya zaka mata kasan ta had'a jini da 'yan shu'uwa.


Adnan wani yawun ya k'ara hadiye ya kai idonsa kirjinta da take girgizawa a hankali na fulaninta na lek'owa waje sabida girmansu

A hankali ya kai idonsa kan hips d'in ta ya k'ara hadiyar wani yawu sabida makoshinsa dayaji ya bushe dan yanda cikinta yake so flat hips d'in ta kuma mai fad'i ko ba'a fad'a masa ba yasan ba ciko tayi ba dan tsabar sanin matan da yayi da muamalla da yake dasu yanzu yana iya tantance jiki mai acuci.


A hankali ya k'ara maida kallonsa kan fuskarta murmushi take yi ta d'aga hannuwanta sama tana rawa tana juya hips d'in ta dimples d'in ta ya lotsa sosai.


Adnan wani irin harbawa kirjinsa ya fara yi a karo na farko dayaji yaji mace ta kwanta masa da ya aure ta a karo na farko dayaji yana yiwa mace wani irin so daga kallo d'aya.


Mik'ewa yayi yasa yaransa dake taya shi entertaining mutane idan sun fita yace su cigaba da saka wakokin yana zuwa.


Kujera ya samu ya zauna ya cigaba da kallonta.


Ajidde dake ta tikar rawa kiran daya shigo wayarta ne yasa ta tsayar da rawar da take yi ta daga wayar da hannunta dake sanye da zobunan gwal tayi hanyar waje.



Adnan da sauri ya mik'e yabi bayanta har yana tuntub'e


Adnan waje ya samu ya tsaya daga d'an nesa da ita ta juya masa baya tana waya haka kawai jikinsa yayi sanyi dan shigar jikinta kawai ya nuna masa babbar yarinya ce dan ko takalmin k'afarta kawai zai yi dubu Ashirin.


Juyowar da tayi ne yasa gabansa wani irin fad'uwa jikinsa ya d'au rawa adai-dai lokacin da ta nufo wajen da yake tsaye dan ta koma cikin hall d'in.

K'afeta yayi da ido jikinsa na cigaba da rawa har tazo zata wuce shi.


Gabanta yasha da sauri Wanda Saura kiris suyi karo.


Ajjidde kuwa tayi sauri ta ja da baya ta zubawa masa idonta dake ji kamar ya narke.


Cikin wani irin siririn murya tace "Lafiya kuwa ya zaka zo kasha gabana"


Adnan tattaro duk wani jarumtarsa yayi ya sakar mata murmushin da yasan yana sace zuciyar 'yan mata yace "u are very beautiful"

"I know u are not the first person that says so do u just cross my way to say am beautiful"?


Adnan murmushi ya k'ara sakar mata fararren hakoransa suka bayyana

Ajjidde kuwa itama ta zuba masa ido tana karewa hallitar fuskarsa kallo dan ba karya Adnan din ma ya had'u.


" ko d'aya ban tsayar dake dan nace kinada kyau ba na tsayar dake ne sabida kaunar ki danake"


Ajjidde wal tayi da idanuwanta ta saki murmushin dake Neman kayar da Adnan k'asa tace "OK then try your luck am Ajjidde by name nyc to meet u"

Tace tana mik'a masa hannunta

Adnan shima mik'a mata hannunsa yayi yana mai d'an mamakin yanda tayi saurin sakin jikinta da shi lumshe idonsa yayi da yaji taushi da sanyin hannunta yace " Am Adnan nyc to meet u too hope am accepted"?


"Eee to bansani ba tukuna just have my contact and call me tomorrow"

Adnan da sauri ya Ciro Samsung d'insa daga Aljihunsa ta karanto mishi lambarta ya kirata tayi saving daga nan ta shige ciki ta bar shi a tsaye.

Adnan bayanta yabi da kallo yana hadiyar yawu wani irin santa na ratsa masa zuciya.

Hall d'in ya nufa sukayi kicibis dashi ta kuma fitowa tana amsa waya murmushi kawai ta sakar masa ta wuce shi.


Adnan kuwa ya juya yana kallonta.


Wani katon bakin jeep daya shigo Harabar wajen yaga ta nufa ta bud'e gaban motar ta shige.


Adnan kirjinsa ne yayi wani irin bugawa hankalinsa yayi bala'in tashi har suka bar wajen yana tsaye kamar Wanda aka dasa shi tunani ya fara da Allah yasa Ajjidde bata fi k'arfinsa ba dan shi bill haki so yake ya aureta.



Kuyi manage insha Allahu zan ringa kokari ina posting kullum dan yanzu labari zai d'auko dadi dan Adnan ya zai d'ebo ruwan dafa kansa zai haka ramin da zai binne kansa tun lokacin mutuwarsa baiyi ba more comment long typing ooooo🧐🧐🧐🧐

*M🅰K'OT🅰N JUN🅰*


*REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS* *P.M.L*




® REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS

ɯɛ ɖơŋŧ ʝųŞŧ ɛŋŧɛřŧąıŋ ŋɖ ɛɖųĆąŧɛ, ცųŧ ɯɛ ąٳŞơ ŧơųĆɧ ɖ ɧɛąřŧ ơʄ řɛąɖɛřŞ


# WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
# IG PML WRITERS
# https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-




*Written by*

💅💅💅 *SADNAF*💅💅💅



*Follow me on wattpad @ Sadnaf*


*page 27*

*AJJIDDE*



First class olosho tankwarariyar karuwa datayi gadon karuwanci a wajen Mahaifiyarta Nura inda itama Nuran gadonsa tayi wajen Mahaifiyarta Kanzel asalinsu 'yan shu'uwa ne Neman kudi ne ya fara kawo kanzel Nigeria inda a lokacin babu Wanda ya kaita kyau da diri hakan yasa manyan masu kudi da siyasa suke ringa rububinta suna kashe mata kudi a ciki wani Wanda bata San kowaye ba sabida yawan mutanen da take mua'amalla dasu ya mata ciki ta haifi Nura Inda itama Nura ta yo gadon kyaunta babu inda ta barta ahaka ta taso a hannun Kanzel inda tana da shekara 12 customers d'in Kanzel suka fara komawa kan Nura inda ita kuma Kanzel tayi retire sabida cutar sanyin data kwasa awajen wani bature sai ta d'ora Nura akan harkar tana samun mahaukatan kudi dan sai ka dire manyan kudi zata sallama maka Nura.


Nura itama sai data zo ta ninka Kanzel a karuwanci dan ita har k'asar Saudiya take zuwa Anan ta had'u da wani Balarabe da ya biya ta mahaukatan kudi akan ta huta dashi har na tsawon shekara d'aya batare da ta kula wani ba a cikin shekara d'ayan ta haifo 'yarta Ajjidde datayi gadon kyau da kyau wajen uwa da uba inda Balarabe da Nura ta gama shekara d'ayarta ya mata babban sallama ta k'ara gaba ahaka ta cigaba da zama a saudiya tana kula da Ajjidde.


Ajjidde tun tana da shekara shidda a duniya zaka ga irin baiwar kyau da diri da Allah ya mata Wanda ya kai ya kawo Nura sai da ta koma Sanya mata hijab sabida gudun kar ayi mata fyad'e.


Tun Ajjide nada shekara goma Nura ta fara mata wani irin gyara da tsumi sabida yanda Manyan alhazawa suka fara kai mata hari suna rokonta akan zasu bata ko nawa takeso indai zata basu Ajjidde

Nura kuwa hakane yasa itama ta fara tunanin lokacin ritayanta yayi sabida itama tana fama da cutar sanyi yanzu bata da kwarin da zata iya cigaba da hark'ar.


Ajjidde nada shekara goma sha biyu Nura ta bada ita ga wani Alhaji da ya dire mata makudan kudade da gwalagwalai inda shi ya fara amshewa Ajjidde budurci daga nan kuma Ajjidde ta zame mata source of income dan tamkar ita kad'ai ce mace duk da kankantar ta rububinta ake yi dan har su Dubai England Nura tura ta take yi ta samo musu kudi.


Ajjidde nada shekara goma sha shidda Nura ta rasu bayan rasuwarta da shekara d'aya Ajjidde ta tattara duka dukiyar da suka mallaka ta dawo gida Nigeria wajen Kanzel a lokacin Kanzel ta tsufa sosai tana fama da wani irin cuta sabida kudin da suke dashi yasa ake mata kula na musamman ana siya mata magunguna.



Kanzel kamar jiran dawowar jikarta take itama ta amsa kiran Mahallici bayan ta damkawa Ajjidde dukan dukiyarta.

Tunda Ajjide ta duro Nigeria 'yan bariki da Manyan Alhazawa suka kyallara ido suka ganta suka fara layi akanta.

Ajjidde ba kowa take kulawa ba sai Wanda ya tada Kai sosai dan wayayya ce ta tashin hankali.


Shekarata hud'u kenan da dawowa Nigeria inda take buga runs d'inta da isassu kudi ne da ita kamar su kasheta banda dukiyar da Nura da kanzel suka bar mata.


Ita kad'ai ke zaune a wani makekken gidan data gina da kudinta bata yarda tabi kowa sai dai ka biyota har gidanta kayi abunda ya kawoka ka bata kudinta.wanan kenan


*ADNAN*



Adnan sai k'arfe d'ayan dare ya koma gida Ajjidde na masa gizo duk fitar numfashinsa sai San Ajjidde ya linku a ransa koyaya ya d'an runtse idonsa sai ya hango yanda ta zuba masa lumsassun idonta tana kashe shi da murmushi Allah Allah kawai yake

Please Login or Register in order to submit comment