Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

gida.

Nurses d'in kuwa ganin ta tub'ure musu yasa suka fita suka kira Adnan dake kan benci a zaune gabad'aya ya rasa mai ke masa dadi yana ganin kiran mai gidansa ya k'asa d'agawa dan bai san mai zai ce masa ba ga Zara itama data dame shi da kira da messages ya rasa inda zai saka kansa ga Aliya itama ta dage akan ya bata takadarta ta tafi gida a gaskiya idan ta matsa mishi takadarta zai bata kawai.


Bayan nurses d'in yabi ransa a b'ace dan ba k'aramin haushin Aliyar yake ji ba.


Suna had'a ido da Aliya
Aliya ta sakar masa harara tana "Ka bani takardata zan tafi gidanmu"


Adnan fuskarsa a d'aure yace "Aliya nima sakin naki shine zai fiyemin kwanciyar hankali tunda kin dage ki bari ki k'arasa warware wa sai muje gida ki kwashi kayanki daga nan sai na baki takadarki"


Aliya da sauri tace "babu ma abinda zai maidani gidanka kuma babu ruwanka da na warke ko ban warke ba ka sallameni kawai na tafi gida kuma dan na tafi gidan wlh bashi zai hana in gayawa Ameer cin amanar sa da kuke ba"


Adnan tsaki yayi yace "kin Dade baki fad'a masa ba sabida ke na rasa abubuwa da dama kin d'auka bazan iya rabuwa dake bane ki dai bari ki warware d'in kar wanan uban naki yazo ya ringa min haushi idan ya ganki ahaka"


Aliya kallon mamaki ta bishi dashi dataji yace mahaifinta zai mishi haushi wani hawaye mai zafi ne ya zubo mata ta cigaba da kallon Adnan dan bata tab'a sanin bayan iskancin da yake bai da mutunci ba.

Aliya share hawayenta Tayi tace "Naji ka sakeni ahaka babu ruwanka da na tafi ahaka ko kar na tafi ahaka"


Adnan wani mugun tsaki yaja dan yafa zo wuya cewa yayi "kije na sake ki saki d'aya kuma idan kinje ki fad'awa iyayenki ke kika nemi in sake ki kar Wanda ya nemeni haba tun jiya kin sakoni agaba in banda asara babu abinda kike janyomin idan ke 'yar gwal ce na hakura dake"

Daga haka Adnan yaja dogon tsaki tare da barin d'akin.



Aliya ko kad'an bata ji haushin sakin daya mata ba dan ta bala'in tsanarsa wani ma sanyi taji daya saketa.

Komawa Tayi ta kwanta tacewa nurse gobe ta rubuta mata takadar sallamar ta.


Nurse d'in dai bata iya cewa komai ba sabida mamaki da al ajabin abinda ya faru.


Adnan kuwa yana barin asibitin ya nufi company su hankalinsa a tashe dan bai san mai zai cewa ogansa ba dan kwana biyun nan yana ta masa laifi


A lokacin da ya isa bai samu ogan nasu ba inda ya nufi office d'insa dan yayi cike ciken takardu da ogan nashi ya bashi tun shekaran jiya ya cike.


Turus yayi a lokacin daya ga kwado a jikin k'ofar

Sallati yayi da k'arfi yana add'uar Allah yasa kar ya rasa aikinsa Allah yasa ogansa ba korarsa zai yi ba.


Adnan sai da ya samu minti ashirin a tsaye kafin ya iya barin wajen ya nufi motarsa yana ta sak'e sak'e babu wacce yake bala'in jin haushin ta sama da Aliya dan duk ita ta janyo masa wanan masifa kud'in ma kawai daya kashe a asibiti yaji ajikinsa ......

*M🅰K'OT🅰N JUN🅰*


*REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS* *P.M.L*




® REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS

ɯɛ ɖơŋŧ ʝųŞŧ ɛŋŧɛřŧąıŋ ŋɖ ɛɖųĆąŧɛ, ცųŧ ɯɛ ąٳŞơ ŧơųĆɧ ɖ ɧɛąřŧ ơʄ řɛąɖɛřŞ


# WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
# IG PML WRITERS
# https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-08144932303




*Written by*

💅💅💅 *SADNAF*💅💅💅



*Follow me on wattpad @ Sadnaf*


*dedicated to Aunty sis*


*page 18*


Har ya isa gida jikinsa ya sanyaye yake bai ko kalli b'angarensu Zara ba kamar Yanda ya saba idan ya dawo ya nufi b'angaren su.

A Palo ya zub'e ya Zaro wayarsa ya fara kiran Layin ogansa.

Sai da ya masa miss call yafi goma bai d'aga ba hankalinsa idan yayi dubu sai da ya k'ara tashi dan bai san ta yaya zai fara rayuwa ba idan aka Kore shi a wajen aiki dan dai-dai da gidan da suke ciki na company ne gashi ko fili bai siya ba ballantana akai ga yayi gidan kansa duk kud'in da yake samu awajen 'yan mata yake karewa account d'insa ma ba wani nauyi yayi ba da zai juya yayi kasuwanci ballantana har ya siyi gida.


Kansa yaji ya fara Sara mishi dan idan har korarsa ogansa zaiyi ya shiga uku.


Mik'ewa yayi ya nufi d'akinsa yana mai tsinewa Aliya dan duk ita ta jawo masa rashin fita aiki yau.


Adnan Bayan ya iddar da Sallar isha addu'a ya ringa yi sosai akan Allah ya d'ora shi akan ogansa Allah yasa kar ya Kore shi daga wajen aiki.

Palo ya dawo ya zauna bayan ya dafa indomie da zai ci ya k'unna kayan kallo ya kamo tashar da yake so.


Wakar da ake yi ya fara bi a hankali wani farinciki da nutsuwa suka fara rufeshi dan arayuwarsa Indai zai ji waka to kome akayi masa zaiji sanyi a zuciyarsa.


Wayarsa ne ya fara ringing yayi sauri ya d'auka dan duk a tunaninsa ogansa ne ya biyo bayan kiran da ya mishi.

Siririn tsaki yaja a lokacin daya ga Zara ce ke kiransa dan shi fa yanzu ba dai-dai yake ba.

D'agawa yayi ya k'ara wayar a kunnensa

Lumshe ido yayi a lokacin da yaji Zara ta mishi muryar da take k'unna shi

"Ina ka shiga ne yau ina ta kiranka baka d'auka ba kasan Yanda rashin jin muryarka yake Neman samun zazzabi kuwa?"

Adnan lumshe idonsa ya k'ara yi dan har Zara ta fara tayar masa da hankali dan magana take in a sexy way tana wani Jan numfashi tare da saukewa.

"Kayi shiru Ko dai kana gaban Aliya ne"?

Tsaki Adnan yayi yace

" Wacce Aliya kuma"?

"Kai wacce Aliya kuwa wacce ta wuce matarka"


Zara tace Tana zaro ido tamkar Tana gabansa

"Dan Allah rabani da zancen wanan matar dan na rabu da k'aya na huta"

Zara dake kwance wani irin mik'ewa tayi har Tana Neman hantsilawa tace

"Adnan bangane ka rabu da ita ba"


Adnan tsaki yayi yace mata Ya saketa and ya saketa ne sabida dukan da Aliya Tayi mata ya sharara mata karya.


Zara da ji take kamar akan gajimare take sabida Yanda Kalmar ya masifar saka ta cikin farinciki tsalle ta fara yi kamar wata yarinya tace

"Adnan yanzu sabida dukan da Aliya Tayi min jiya ka saketa ooh my God Adnan ina zan saka kaina dan dadi Adnan i love u bansan yanda zan nuna maka irin kaunar da nake maka ba".

Murmushi Adnan yayi tamkar yana gabanta yace " I can fight d world for you Karki damu ya jikin naki"

"Adnan am fine wanan news d'in daka bani yanzu ya k'ara sawa naji garau is now my turn goben nan zan saka Ameer agaba akan ya sakeni kaga shikenan burinmu zai cika na mallakar juna Adnan I miss you I really want to be with u I miss everything about you most especially ur soft touch"

Tace tana wani lashe lebb'e tare da lumshe ido

Adnan shima tuni yaji ta k'unna mishi duk channels d'in jikinsa ya narke a jikin kujera yana fidda numfashi da sauri da sauri yace


"Zara I need you now kin d'aga min hankali"


Zara tuni ta mik'e dan itama tuni taji bata da burin da ya wuce taje gurin nasa she need him too

"Adnan Ameer bai dawo ba bari nazo yanzu am on my way"

Katse wayar Tayi da sauri ta suri k'aramin mayafinta Tayi b'angarensu Adnan.

Adnan tana ce mishi gata nan zuwa yayi sauri ya rage kayan jikinsa dan hankalinsa ya kai kololuwa wajen tashi a bakin k'ofa ya tsaya yana jiran zuwanta.


Aikuwa tana shigowa ya sureta yayi bedroom da ita tun kafin su shiga d'aki suka dakumi juna kamar zasu shige jikin juna.


Adnan sarrafata yake tamkar ya samu matarsa ta sunna inda itama ta saki jiki take mai da masa martani ta na bulo masa da sababin salon da yake k'ara harzuka shi yama manta a duniyar dayake ballantana ya tuna yanada wata matsala a gabanshi Nisan da yayi bai sa ya tuna Ameer zai iya dawowa a kowane lokaci ba.

Haka zalika Zara ta ma manta da ita matar Aure ce ballantana har ta tuna Ameer zai iya dawowa a kowane lokaci.


B'angaren Ameer kuwa bai iya tab'uka komai ba tunda yaje office haka kawai Yanda Aliya ta taho wajensa a guje ya ringa yawo a idonsa tausayinta yake ji sosai aransa ya hango abubuwa da yawa a idonta jiya jinin daya gani a jikinta jiya ya masifar d'aga masa hankali ba zai iya manta mutuncin da ta masa ba da Zara bata nan ta kawo mishi abinci har da bashi hakuri akan ya dawo da Zara.

Mai tayiwa Adnan haka da ya mata irin wanan dukan har tana Neman mai taimakonta duk da ganinta kawai yake yi basu tab'a tsayawa sunyi magana mai tsayi sosai ba yasan Aliya mace ce da ta san mutuncin kanta tasan darajar Aurenta ko daga Yanda take suturta jikinta mai yasa Adnan bai san baiwa Allah ya mishi da ya bashi mace irin Aliya ba.


Yana so yasan halin da Aliya take ciki ko d'an mutuncin da ta masa amma ta yaya zai san halin da take ciki bayan mijinta yana zarginsa sabida bak'in kishin sa.


A ranar Ameer da tunanin halin da Aliya take ciki ya wuni inda har ya ringa san yakice tunanin nata a zuciyarsa a matsayinta na matar aure shi yasan babu wani Abu a zuciyarsa game da ita amma yanaso yasan halin da take ciki.

Aranar da wuri ya bar office da zumar yaje gidansu Batula yace mata bazai samu zuwa daddare ba sai dai gobe zai zo dan Yanda yake jinsa ba zai iya zance ba.


Gabansa ne ya ringa dukan uku uku a lokacin daya k'arasa k'ofar gidansu Batula ya hangota agaban motar wani tana zance sai kyalkyala Dariya take yi.


Kansa wani irin Sara mishi ya ringa yi ya cigaba da binta da kallo dan Sam bata lura dashi ba bama wanan ne ya saka kansa sarawar ba sai mayafin daya gani a jikinta.


tunda yake da ita bai tab'a ganinta da mayafi ba Yanda ma take k'yalk'yale Dariya tana dukan cinyarta bata tab'a irin wanan dariyar agabansa ba sai dai tayi murmushi.

Jikinsa ne ya fara wani irin rawa zuciyarsa na bugawa fiye da Yanda ya kamata ya ringa bugawa.

Numfashinsa ne ya nemi d'aukewa a lokacin dayaga Batula tana b'oye wani Abu a bayanta shi kuma yana k'ok'arin k'arba har hakan ya kaisu ga k'ok'awa still suna kyalkyala Dariya.


Batula kuwa Sam bama tasan da zuwan Ameer ba dan tasan daddare yake zuwa shiyasa take zancenta da yamma da Saurayin da take bala'in so sai dai shi yace ba yanzu zai yi Aure ba sai dai suyi soyayya kawai dan yama fito ya nuna karta jira shi an Dade da mishi mata.


Hakane yasa ta rik'e Ameer da hannu bibiyu sabida kar tayi biyu babu tunda shi aurenta zai yi kuma ba laifi tana san shi.


Ameer yafi k'arfin minti Ashirin yana kallonsu kamar numfashinsa zai d'auke dan tsananin bugun zuciya dan bayan k'ok'awa har cakulkuli ya ringa mata har yana d'an tab'a kirjinta.

Sha'aninsu kawai suke batare da sun lura dashi ba.

Ganin ba zai iya cigaba da kallonsu ba yasa yafito daga motarsa a zuciye ko ina na jikinsa na wani irin rawa wasu rud'u rud'un jijjiyoyi sun firfito masa a goshi ko rufe motarsa baiyi ba ya nufi wajen su yana wani irin tak'u k'asa na amsawa.


Har ya isa wajen motar babu Wanda ya lura dashi har sai daya bud'e side d'in da Batular take yayi wani irin fincikota.

Ruk'on daya mata kamar zai karya mata hannun

Batula firfito da idanuwa tayi cikin masifaffen fad'uwar gaba cikinta yayi wani irin k'ullewa data yi tozali da Ameer da ya zame mata tamkar zaki.

Cikin wani irin murya Ameer yace "Batula dama haka kike? Batula dama fuska biyu gareki ni zaki yaudara kiciwa Amana?


Batula tamkar gabanta zai fad'o haka takeji ga wani mugun fitsari dake Neman k'ubce mata dan ko a mafarki bata tab'a tunanin Ameer zai zo gidansu da yamma ba dan tasan zuwan dare yake yi kuma ko yau da su kayi waya sun yi dashi akan daddare zai zo to mai ya kawo shi da yamma.


Ameer ganin ta k'asa magana numfashinta sai sama da k'asa yake yi yasa yace

" Batula ban tab'a tunanin haka kike ba Alhamdulillahi na godewa Allah daya nuna min wacece ke da sai dai na k'ara kwasar Zara ta biyu na kai gidana kanki kika cuta bani ba Batula dan"?


Saurayin Batula ne yafito daga motarsa yana

"Batul wai waye wanan"?


Wani irin kallo Ameer ya watsa mishi ya cikata yana " ba sai kasan koni waye ba"


Daga haka ya juya ya nufi wajen motarsa.

Batula hankali a mutuk'ar tashe tabi bayansa tana " Ameer dan Allah ka tsaya ka saurareni wlh ba saurayina bane mutunci muke yi dashi karkayi min haka"tace tana rik'e murfin motarsa dan har ya shige.

Ameer bai iya ce mata komai ba sabida abinda ya tsaya masa a wuya ya finciki murfin motarsa Daga hannunta yaja motarsa da gudun tsiya kamar zai take mata k'afa dan badan tayi zafin naman daka tsalle ba da babu abinda zai hana ya taka mata k'afa.


Batula hannu ta d'ora aka tana fashewa da kuka dan duk samarinta Ameer ne yazo mata dagaskiyar zai Aureta sauran duk yan holewa ne ciki kuwa har da Ismail saurayinta da Ameer yazo ya gansu tare.


Ismail kuwa tunda Batula tabi Ameer da gudu yayi tsaki ya shige cikin motarsa shima yaja ya tafi.


A guje Batula ta shige gida tana rusa kuka tana ta shiga uku ta lalace Ummanta ta taimaketa.


Ummanta dake tuk'a tuwo a kitchen a guje ta fito tana sallati tare da tambayarta abinda ya sameta.

Batula kuwa ko magana bata iya yi sai kuka.

Ameer yana barin gidansu Batula gidansu ya nufa direct ko motarsa bai tsaya rufewa ba ya shige cikin gidansu ransa a mutuk'ar b'ace.


Fuskarsa kawai Hajiya Ameena ta kalla ta fara sallati dan ko sallama bai yi ba ya zube akan carpet d'in palon idonsa jajjawur jikinsa sai rawa yake.


Hajiya Ameena addu'a ta fara yi a filli tana "Allahuma lah sahla illa "

Da sauri Ameer ya cafe ya k'arshe ya cigaba da maimaitawa dan shap ya manta bai yi addu'a ba tunda ya shiga tashin hankali

A hankali yaji ya fara samun nutsuwa hankalinsa ya d'an farawa kwantawa.


Hajiya Ameena ido kawai ta zuba mishi har sai data ga fuskarsa ta d'an saitu ba kamar dazu ba ta mik'e ta d'auko masa ruwa mai dan banzan sanyi.

Sai da ya shanye tas kamar zai had'a da k'ofin sabida zab'alb'alan da zuciyarsa keyi tunda ya k'afa kai yaji zuciyarsa ta fara sanyi.

A hankali ya kwanta akan carpet d'in palon yana sauke ajiyar zuciya.

Hajiya Ameena kuwa ta cigaba da binsa da kallo sai da suka samu minti Ashirin a haka kafin Hajiya Ameena ta tambayeshi mai ya same shi haka.

Sai da ta maimaita tambayar sau uku kafin ya bud'e idonsa da su kayi ja kamar garwashi ya kwashi komai ya gaya mata.


Tsananin mamaki ya hana Hajiya Ameena magana sai nannata sunan Batula take dan gani take kamar bazata aikata abinda Ameer ke tuhumarta dashi ba.


Maganar Ameer ne ya dawo da ita hankalinta

"Hajiya mai yasa banida sa'a a rayuwata ne mai yasa nake had'uwa da watsatsun mata Ina murna na had'u da salihar mace abokiyar rayuwar arziki Ashe itama tamkar Zaran take ba dan kince kar nayi gaggawa ba in bari mu fahimci juna sosai da tuni na aureta batare da nasan halin ta ba wanan wane irin abune Hajiya yaushe zan dace da macen kwarai Saliha mai kamun kai data san mutuncin kanta"

Zuwa wanan lokacin Muryar Ameer rawa yake kawai hawaye na zubo masa


Hajiya Ameena hannunsa ta rik'o ta kwantar da k'ansa akan cinyarta tace "Ameer karka karaya zaka dace da macen kwarai insha Allahu wanan yana cikin jarrabawar ka karka damu ka d'auka Allah ya kaddara Batula ba abokiyar rayuwar ka bace babu Yanda Allah baya ikonsa Zara matarka Allah zai iya shiryata ta nutsu fiye da tunanin mai tunani koda bata nutsu ba Allah zai iya had'a ka da macen da zaka yi alfahari da ita har ka koma ga mahallicinka kayi hakuri ka barwa Allah yinsa ka cigaba da rok'onsa shi maji rok'on bawa ne zai amsa maka addu'uar ka insha Allahu.


Ameer ji yayi kalmomin Hajiya Ameena sun kwantar masa da hankali sosai acikin kashi d'ari na b'acin ran daya kwaso 60 ya ragu.


Hajiya Ameena cigaba tayi da kwantar masa da hankali har akayi sallar isha'i yana gidan dan har abinci tasa yaci sosai.

Wajen k'arfe Tara ya mik'e yace mata zai tafi ta rako shi har bakin gate sai data ga tafiyar sa ta koma ciki.


Adnan kuwa suna gama aikata masha'arsu bacci mai nauyin gaske yayi awon gaba dasu har Ameer ya dawo basu sani ba.


Ameer kuwa daya shiga b'angarensu ko kallon d'akin zara bai yi ba ballantana yasan bata nan dan kwana biyu kenan bai ma sata a idonsa ba bama ya san ganinta sabida tsanar da ya mata shi yasa baya damuwa yasan halin da take ciki in ya dawo.

D'akinsa ya shige ya fara watsa ruwa ya d'aura alwala yazo yayi 'yan nafilfilinsa ya kwanta dan yayi bacci amma me Sam bacci yak'i d'aukansa tunanin abinda Batula tayi mishi kawai yake


Take ko ina na jikinsa a hau zafi gumi ya hau k'eto masa ji yayi kamar Ac d'akinsa ma zafi yake hurowa

Mik'ewa yayi daga shi sai dogon wando da farin vest d'in jikinsa yayi waje

A Palo ya zauna amma ina ji yayi still palon na masa zafi hakane yasa ya fita waje ya nufi wajen motarsa ya hau kan bonet d'in motar ya kwanta ya lumshe ido sabida iskar daya fara shiga ko'ina na jikinsa

Idonsa a lumshe Aliya ta fad'o masa aransa take ya bud'e idonsa ya kalli b'angarensu ya dawo da kallonsa kan motar Adnan ina ma yana da hali dayaje ya tambayi Adnan halin da Aliya take ciki.


Adnan kuwa juyi yayi da zumar gyara kwaciyarsa yaji hannunsa ya sage sabida kwanciyar da Zara tayi akai

Bud'e idonsa yayi a hankali ya sauke idonsa akan Zara dake kwance tsirara tana fidda mumfashi a hankali sabida dadin baccin da take yi.


Juyawa yayi da sauri ya kalli agogon bangon d'akin yaga 10:25


Wani irin mik'ewa yayi hankalinsa a tashe ya kai mata duka a cinya

Aikuwa ta mik'e zumbur tana mitsitsika ido

Adnan da sauri yace "Zara yi sauri kisaka kayanki ki tafi kafin Ameer ya dawo"


Zara mik'a tayi tana hamma ta fad'a jikin Adnan tana "dan Allah kazo mu kwanta muyi bacci ba sani zai yi ba na nan ba ni anan zan kwana"

Adnan durowa yayi daga kan gadon yana "Zara kina hauka ne kinaso asirinmu ya tonu ne akan me zaki kwana anan dan Allah kiyi sauri ki saka kayanki ki tafi tun kafin ya dawo.


Zara k'ok'arin magana take Adnan ya fusgota ya fara k'ok'arin zura mata doguwar Rigarta ita kuwa sai hamma take sabida baccine a idonta sosai.


Ko pant bai bari ta saka ba ya bata mayafinta yana hankad'ata akan ta tayi sauri ta tafi.


Har k'ofar palon ya bud'e mata sai data fice ya rufe k'ofar sa

Ameer kuwa da sauri ya juya dayaji karar k'ofar b'angarensu Adnan

Aikuwa ya hango Zara na nufar b'angarensu tana zabga hamma rigar nata ma abaibai yake


Wani mugun bugu k'irjinsa yayi ya k'ara ware ido yana kallonta dan Sam bata kallo inda yake ba sai zabga hamma take.


Mik'ewa yayi a hankali daga kwance da yake ya cigaba da kallonta har ta shige b'angarensu

Ameer rik'e kansa yayi gam sabida bindigar da yake shirin yi dan yana so ya matsawa kan nasa yayi tunani amma ina ya k'asa tambayoyi ne fal aransa ya rasa Wanda zai kama

Mai Zara taje yi b'angarensu Adnan uwar haka?

Aliya taje dubawa da ta dawo daga asibitin ko kuwa mai taje yi?

Ya akayi tafito a hargitse rigarta abaibai?

Ko dai wajen Adnan taje data ga Aliya bata nan?


Wani irin bugawa kirjinsa yayi jikinsa ya fara rawa dan haka kawai zuciyarsa Ke hararo masa Zara wajen Adnan taje.

Tuni ya duro daga kan motar har yana zubewa a k'asa dan k'afafunsa kamar bazasu d'aukesa ba da kuwa ya mik'e b'angarensu Adnan kawai yake kallo yana sake sake.

Tuni hankali da tunaninsa ya rabu gida uku biyu na zargin Zara daga wajen Adnan take d'aya nacewa Aliya taje dubowa

Kai to idan Aliya taje dubowa mai zai sa ta kai dare haka a b'angarensu duk da tasan Adnan ya dawo yana gida?


Gabansa ne ya k'ara fad'uwa a hankali yaga ya nufi b'angarensa dan yana bukatar yayi tunani da bincike inta kama ma ya saka Zara agaba yau ta gaya masa mai taje yi b'angarensu Adnan daddare haka sai ya ta mishi bayani.


Jiki na rawa ya nufi d'akin Zara kirjinsa na wani irin bugawa....


*Washhh Allah na Yaseen na gaji anya bazan tafi yajin aiki ba kuwa*🤪🤪🤪

*M🅰K'OT🅰N JUN🅰*


*REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS* *P.M.L*




® REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS

ɯɛ ɖơŋŧ ʝųŞŧ ɛŋŧɛřŧąıŋ ŋɖ ɛɖųĆąŧɛ, ცųŧ ɯɛ ąٳŞơ ŧơųĆɧ ɖ ɧɛąřŧ ơʄ řɛąɖɛřŞ


# WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
# IG PML WRITERS
# https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-




*Written by*

💅💅💅 *SADNAF*💅💅💅



*Dedicated to Aunty sis*💖💖💖






*Follow me on wattpad @ Sadnaf*



*page 19*

A hankali ya tura k'ofar d'akinta da bai gama rufuwa ba haka kawai gabansa na azabar fad'uwa dan he is afraid ya gaskata abinda yake zargi dan idan kuwa hakane he is afraid yayi rayuwa a prison cos zai iya kashe Zara.


A hankali ya d'an shiga d'akin dan Zara a kwance take tayi rub da ciki k'afafunta a ware da alama tana shiga d'akin ta fad'a kan gadon sabida baccin dake idonta

A hankali yafara wurga idonsa yana examining d'inta tun daga kanta har zuwa tafin k'afarta


Wani irin bugawa k'irjinsa yayi kansa yayi wani irin nauyi kamar zai fad'o sakamakon ganin Zara datayi wawan kwanciya kana hango komai nata babu ko wando a jikinta dan Yanda ta ware k'afarta hakan ya bashi clear view d'in gurin.

A hankali ya matsa kusa da inda take kwancen ya sunkuya tare da d'aga rigarta duk fitar numfashinsa sai kirjinsa ya buga

K'asanta ya zubawa ido jikinsa na wani irin rawa dan ga semen nan a jikinta sosai mai zai had'ata da semen idan ba saduwa tayi da namiji ba.

Ji yayi d'akin na juya mishi har yana Neman fad'awa kanta zanin gadon ya damka da hannu biyu sabida kar ya fad'i

Yayi baya a hankali tare da zub'ewa a k'asa kansa kuwa kamar guduma ake k'wad'a masa take hancinsa ya fara jini dan Ameer irin mutanen nan da idan ransu ya kai k'arshe wajen b'aci sai hancinsu ya fara zubda jini.


Flat yayi a k'asa sakamakon numfashin dake mishi wahalar shak'a kirjinsa sai sama da k'asa yake yi

K'asa bud'e baki yayi yayi addu'a sabida nauyin da bakin ya masa sai kawai ya fara addu'a a zuciyarsa hakan kuwa ya taimaka sosai wajen dai-daituwar numfashinsa jikinsa dake rawa kamar an sa masa shocking ya fara rage rawa

Sai da yasamu minti Ashirin ahaka kafin ya dawo dai-dai.

Zara kuwa baccinta kawai take sha bata san abinda ke faruwa ba.

Ameer kuwa da taimakon addu'ar da ya ringa yi yasamu nutsuwa sosai a hankali ya lumshe idonsa ya fara hango ranar da Zara ta fita da sleeping dress ta tsaya agaban Adnan Adnan ya zuba mata ido kamar zai lasheta.

Kenan intentionally Zara ta fita ahaka dan taja hankalin Adnan wajenta

Tun yaushe Zara da Adnan suka fara cin amanarsa batare da yasani ba.

Ko dai Adnan ne yaje gidansu Zara ranan dayaje.


Adnan runtse idonsa ya k'ara yi da k'arfi zuciyarsa na k'awata masa Yanda Zara da Adnan ke cin amanarsa kenan shiyasa kullum Adnan yake Riga shi dawowa gida.

To Aliya tana ina suke cin amanarsu.

Ameer mik'ewa yayi a hankali daga kwancen dayake ya zauna tare da zubawa Zara ido abubuwa da yawa na mishi yawo arai.

Ji yake kamar ya tashi ya shak'e Zara har sai ta daina numfashi

Please Login or Register in order to submit comment