Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ihun ayafe mata.



Ameer kuwa yana barin gidansu Zara kafin ya k'arasa gida yaga misscall d'in Aliya guda biyu har da text message dan hankalinta ba k'aramin tashi yayi ba data ga da asuba bai kirata tayi sallah kamar yanda ya saba ba har wayewar gari bata ga kiransa ba Wanda hakan yasa hankalinta kasa kwanciya dan tun kafin ma ya furta Santa yakeyi yake tashinta da asuba rashin ganin kiransa yasa hankalinta tashi sai da ta kira shi ganin bai daga ba yasa tayi mishi message dan take ta rasa mai ke mata dadi.

Wani irin farinciki ne ya rufe Ameer take ya manta da wani b'acin ran da Zara ta saka mishi bayan ya karanta message d'in da Aliya tayi mishi ya juyar da kan motarsa ya nufi gidansu Aliyan yana isa ya kirata a waya.

A lokacin Aliya na kudundune a d'aki tana rik'e da wayarta a hannu ta kurawa wayar ido ko kiran Ameer zai shigo wayarta aikuwa wani irin mik'ewa tayi jiki na rawa ta d'aga wayar Ameer.

Ameer kuwa yace mata yana waje.

Durowa tayi daga kan gadon ta fad'a bandaki da sauri ta wanke fuskarta ta saka farin hijabinta tayi waje ita kanta har mamakin yanda ta kamu da san Ameer take lokaci guda.


Ameer kuwa tunda ta fito yake ta washe baki dan ko ba'a fad'a masa ba yasan yasamu karb'uwa awajen Aliya tunda har ta damu dashi haka.


Aliya kanta a sunkuye ta k'araso wajensa tana d'an kare fuskarta da Hijabinta tare da gaishe shi.

Cikin fara'a ya amsa ya ringa tsokanarta da Ashe haka itama ta damu dashi bai sani ba.

Aliya ita dai murmushi kawai take tana k'ara sunkuyar da kai sai da Ameer ya gama tsokanarta ya gyara tsayuwarsa ya kwashe duk abinda ya faru ya gaya mata babu abinda ya b'oye mata.

Aliya ba ta tab'a kallon Ameer cikin ido na minti biyar ba sai gashi ta zuba mishi ido tana kallon shi tsananin mamakin labarin daya gama bata dan bata tab'a tunanin shaidancin Zara da Adnan ya kai haka ba kullum acikin godewa Allah take daya kawo sanadin rabuwarta da Adnan da Yanzu tana nan tana kunsar bak'in cikinsa sai da Ameer ya tafa hannuwansa tayi sauri ta kau da kanta tana Allah ya shirya.

Ce mishi Tayi tana zuwa ta koma ciki ta had'a mishi abun karyawa ta kai palon saukar baki.

Ta koma wajensa tace yazo su shiga daga ciki.

Ameer bai ce komai ba yabi bayanta suna shiga ta fara zuba mishi soyayyan dankali da kwan ta zuba mishi kunun gyad'a tace ya karya kafin ta dawo ta mik'e tana k'ok'arin barin palon

Ameer da sauri ya tsayar da ita yace bazai ci ba indai ta tafi gwara ta tsaya yaci agabanta akan dole Aliya ta koma ta zauna kanta a sunkuye Ameer yafara ci yana janta da hira.

Ameer ba shi ya bar gidan ba sai wajen Sha biyun rana dan badan anata kiransa a office ba da babu inda zaije da Aliya ta saki jikinta dashi sosai suna hira inda a hirar tasu yace ta gayawa Alhaji Abubakar akan zai turo manyansa a satin nan asa ranarsu dai-dai dana kanwarta Sumayya.


B'angaren Adnan kuwa yana tashi da sassafe yaje ya nemo masu siyan kayan gidan.

Inda yayi gwanjon komai na gidan ya siyar ko cokali bai bari ba kayansa na sawa kawai ya zuba a cikin sabon akwatinsa da siyo sai wajen k'arfe biyu na rana ya kira Ajjidde a waya shima sai daya mata misscall uku kafin ta d'aga yace mata k'arfe hud'u zai taho da walliyinsa.

Ajjidde kuwa tace masa sai yazo dan itama tana nan tana shirye shiryenta ta ma tanada masa kayan da zai sa daga haka ta kashe wayarta.


Adnan wani irin farinciki ne ya ringa ratsa shi dan kamar a mafarki wai shi ne zai mallaki Ajjidde.


Waya ya buga wani Dauda da ba shi da aikin da ya wuce zaman majalisa duk da ya manyanta babu Wanda yake huld'a dashi acikin unguwar sai shi yana d'agawa Adnan ya kora mishi jawabi akan yanaso yazama walliyinsa zai bashi dubu ashirin ya shirya k'arfe uku da rabi zai biyo su tafi.

Dauda kuwa jiki na rawa yace bari ya shirya tun yanzu ya taho sai su wuce daga nan Adnan yace to sai yazo yana jiranshi.


Dama tun safe ya Ciro kudin Sadakin Ajjidde ya saka a wani sabon k'aramin akwatin daya siya sabo lokaci kawai yake jira ya tafi dan har wanka yayi ya kuma saka yar tsadaddiyar shaddarsa light blue bakin takalmi da agogo ba k'aramin kyau yayi ba dan har sabon waya ya siya babu abinda yake sai murmushi yana hango yanda zai sarrafa lallausan jikin Ajjidde.


K'arfe hud'u dai-dai suka iso gidan Ajjidde acikin adai daita sahu shi da Dauda.


Mamakine ya rufe Adnan dayaga manya manyan motoci a k'ofar gidan Ajjidde kid'a nata tashi daga gidan dan tun daga nesa suka fara jiyo kid'a gate d'in gidan ma a bud'e yake cikin gidan yasha decoration har waje.

Adnan k'asa saukowa yayi daga cikin adaidaita sahun Dauda kuwa ya saki baki da hanci yana kallon gidan .

Adnan wayarsa ya zaro daga Aljihunsa ya kira layin Ajjidde bugu d'aya ta d'auka tace yana ina

Adnan yace gashi awaje

Ajjidde da sauri tace ya tsaya kar ya shigo ya bata kunya agaban kawayenta ya koma ta bayan gidan zata turo wani da kaya ya saka za'a tuko shi har cikin gidan daga haka ta kashe wayar.

Adnan yabi wayar da kallo yana hadiyar yawu tare da kara kallon jibga jibgan jeep din dake pake a k'ofar gidan.

Mai adai-dai ta sahun yacewa su koma ta bayan gidan ya sauke su yana ajiyesu ya sallameshi ya tafi ya tsaya shi da Daudu da akwatin kayan Adnan agaba.

Tsayuwarsu da minti biyar sai ga wata katuwar Jeep ruwan toka yaji decoration din flowers da balloons ya parker agabansu.


Daudu jikinsa ne ya fara rawa Adnan kuwa yawun bakinsa ya k'afe

Zubawa motar ido sukayi bayan k'ofar motar ta zugee a hankali wani matashi yafito daga cikin motar yace su shiga ciki.


Jiki ba kwari suka shiga cikin motar jikinsu na rawa matashin saurayin nan kuwa ya saka musu akwatin a bayan motar Adnan Lumshe ido yayi sakamakon sanyi Ac da kamshin daya d'aki hancinsa.

A hankali ya dofana duwawunsa akan kujerar daudu kuwa ya zubawa plasmar dake cikin motar ido yana had'iyar yawu.


Matashin mutumin wani Leda ya janyo daga gefensa ya mik'awa Adnan akan ya saka ya d'auki d'aya ledar ya mik'awa Daudu shima akan ya sa


Cikin minti biyar matashin Saurayin nan ya taya Adnan shiryawa a cikin wani arnen gezner mai kyalli kamar mudubi ash colour hula takalmi da agogo ma Ash kana ganin shirgar jikin Adnan zaka san naira tayi kuka tsaf kayan suka masa kamar telan yasan measurement d'insa ba k'aramin kyau da had'uwa Adnan yayi ba inda Adnan ya ringa shafa kayan sabida kyaun da suka masa turarruka masu mugun tsada matashin ya fito dashi ya fara fesawa Adnan Inda Dauda da shima aka hada shi da farin shadda mai kyau da tsada har da babbar Riga hular kuwa tayiwa kansa yawa sabida k'aramin kai gareshi washe hakora kawai yake yana kallon jikinsa yana addu'a Allah yasa su bar mishi kayan.


Adnan ji yayi kansa yayi wani irin girma a lokacin da matashin ya koma gaba yana jansu shi da Daudu daga baya.

Adnan dayake yasan komai na gayu tuni ya d'ora k'afarsa d'aya kan d'aya yana wani yatsine yatsinen fuska ala dole irin mai kudinan.

A hankali motar ta shiga harabar gidan Adnan kuwa ya fara kallon yanda akayi decorating wajen da za'ayi walimar ga masu serving abinci a gefe ga manya manyan Alhazawa masu ji da kansu kid'an 'yan shu'uwa kawai ke tashi.


Matashin saurayin nan yana parking ya fita daga motar yaje ya fad'awa Ajjidde akan sun k'araso tace masa ya shigo da Adnan da walliyinsa.


Inda Matashin Saurayin yayiwa Adnan da Daudu iso har wani Palon da Adnan bai san dashi ba.


Wani mutum suka tarar a palon da wata matashiyar buduruwa tana zaune a cinyarsa tayi shigar lafayya itama kanta kyakyawa ce ba laifi.


Adnan kansa ne ya d'an daure dayaga mutumin ahaife zai haifeshi amma katuwar buduruwa a cinyarsa.

Haka ya maze ya samu waje ya zauna shi da Dauda zamansu da minti goma sai ga Ajjidde ta fito da wani irin shiga kamar ta indiyawa kayan sai kyalli suke rigar iya kirjinta ya rufe sai bud'edd'en skirt d'inta da bai kai k'asa ba wajen kugunta da duwawunta kuwa wani irin jigida ne mai kyallin gaske kamar mudubi ta jerashi tunda ga wajen cibiyarta har zuwa duwawunta duk taku d'ayan da tayi sai yayi k'ara.


Gashinta kuwa yasha gyara ta baje shi a kafadarta sai kyalli yake ba ko mayafi ajikinta.

Adnan zuba mata ido kawai yayi numfashinsa na shirin d'aukewa har ta k'araso wajen Adnan ta zauna a cinyarsa tare da sakar masa murmushin dake narkar da zuciya.

Adnan k'asa maida mata martanin murmushin yayi sabida mazaunanta da yaji ajikinsa da kamshin dake fita ajikinta ido kawai ya zuba mata yana kallon ta.

Ajjidde kuwa ta d'auke kanta ta kalli wanan mutumin da har yanzu buduruwar nan na cinyarsa bata d'aga shi ba tace "Mamman nur gashi ya k'araso a d'aura mana Auren lokaci yana tafiya kasan yau kwana zamuyi muna chasu"


Adnan mamakine ya rufeshi ya zubawa sarautar Allah ido yana kallon ikon Allah inda Wanda aka kira da Mamman Nur ya ya d'aga buduruwar daka kansa ta zauna a gefensa yace to "Bismillah"

Ajjidde cikin murmushi ta juya ta kalli Adnan tace "ina Sadakin"?

Adnan cikin 'inina yace " yana cikin mota"

Ajjidde kuwa ta kalli matashin da tunda suka shigo ya kame a bakin k'ofa kamar wani soja tace " jeka kwaso duk abinda yazo dashi "


Cikin minti biyar ya dawo d'auke da akwatin kayan Adnan dana sadakin Ajjidde Inda Ajjidde tace ya mik'o mata k'aramin akwatin dan tana kyautata zaton aciki kudin sadakinta suke.


Matashin ne ya bud'e akwatin Ajjidde ta sauko daga kan cinyar Adnan ta fara kirga rafar dubu dubu dake ciki akwatin.

Adnan shi dai sakin baki yayi yana kallon ta inda Daudu shima ya bud'e baki da hanci yana kallon sabon salo.

Ajjidde murmushi Tayi ta rufe akwatin ta kalli Mamman nur tace "kudin sun cika zaka iya daurawa ka matsa kusa dashi ku d'aura muna kallonku"


Ajjidde tacewa Daudun da yawu ke neman zubo masa sabida kallo da saurinsa ya matsa kusa da Mamman nur yana kallon sabon salon daurin aure.


Ajjidde kuwa ta koma kan cinyar Adnan tana shafa mishi Saje tana sakar masa murmushi.


Abun mamaki Mamman Nur sai da yafara gindaya sharrud'an da Ajjidde ta gindayawa Adnan tace ya zama shaida sannan yayi sallati ya karanta fatiha yace shima daudu yayi sallati ya karanta fatiha Daudu kuwa ya karanta kamar yanda ya umarce shi Mamman Nur kuwa ya shafa fatiha yace shikenan an d'aura Auren Ajjidde da Adnan sun zama miji da mata


Daudu mamakine ya rufe shi ya juya ya kalli Adnan da shima ko ba'a fad'a ba mamakin sabon salon da suka zo dashi yake inda take wannan buduruwar dake gefen Mamman Nur ta saki wani irin gud'a Ajjidde kuwa ta rungume Adnan tana murmushi.


Adnan kamar soko haka ya zama yana kallon ikon Allah Dan Ajjidde tana cika shi ta mik'e ta fara wani irin rawa tana kad'a kugunta tare da ruk'o hannun Adnan suyi waje.



Adnan binta kawai yake abaya kamar soko ganin sun nufi wajen da akayi decoration inda manyan manyan Alhazawan ke zaune yayi sauri ya rik'e hannunta yana "Haba Ajjidde ba dai haka zakije wajen Mazan can ahaka ba kinga fa komai na jikinki awaje ko kin manta ke matar aure ce dan Allah muje ki canja kaya"


Wani irin kallo Ajjidde tayiwa Adnan tace "ka biyoni"?

Daga haka Tayi gaba Adnan ya fara binta abaya.


Tundaga nesa da mai kid'an garinsu ya hango Ajjidde ta taho ya saki wani irin kid'a yana zabga gud'a kamar mace.


Ajjidde kuwa da rawa ta k'arasa tsakiyar filin ta fara wani irin rawa tana gantsaro kirjinta tana kad'a kugunta.

Aikuwa Alhazawan nan d'aya bayan d'aya suka fara tasowa suna mata liki inda Hankalin Adnan yayi balainy tashi dan duwawun Ajjidde suke kaiwa duka suna matsewa da hannu suna zuba mata ruwan kudi ita kuwa sai tura musu duwawun take Inda wasu kuma suka ringa zubawa kirjinta shafa da liki wasu har da d'an rungumeta.
Wai ahaka da sunan sun zo tayata murna Auren da tayi suke

Wasu mata goma ne suka fito daga wani k'ofa sun sha shigar lafayya da manya manyan jakankuna suka zo suka zagaye Ajjidde suka tsugunna suna kwasar kud'in da ake likawa Ajjidde.


Ajjidde kuwa kamar zata balle ta cigaba da taka rawa dan likin da suke mata shine tamkar gudunmawarsu



Adnan cikin tsananin tashin hankali yashiga tsakiyar filin yajawo Ajjidde da k'arfinsa sabida wani mugun kishi daya rufe masa ido Ajjidde kuwa ta juyo ta zabga mishi mari........

*M🅰K'OT🅰N JUN🅰*


*REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS* *P.M.L*




® REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS

ɯɛ ɖơŋŧ ʝųŞŧ ɛŋŧɛřŧąıŋ ŋɖ ɛɖųĆąŧɛ, ცųŧ ɯɛ ąٳŞơ ŧơųĆɧ ɖ ɧɛąřŧ ơʄ řɛąɖɛřŞ


# WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
# IG PML WRITERS
# https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-




*Written by*

💅💅💅 *SADNAF*💅💅💅



*Follow me on wattpad @ Sadnaf*


*WANAN SHAFIN NAKINE HABIBA LV MY LOVE FOR U HAS NO LIMITATIONS BEENAF STAY BLESSED*


*YAN GRP DIN HABIEBA LV INA YINKU SOSAI DA SOSAI NGD DA KAUNARKU AGARENI*


*page 33*


Adnan dafe kumatunsa yayi cikin tsananin mamaki da Al-ajabin Marin da Ajjidde ta zabga mishi

Ajjidde kuwa ta ringa zabga mishi wani mummunan kallo Tana huci cikin tsantsar b'acin rai ta nuna shi da yatsa tana "ka shiga hankalin ka bazan yi tolerating nonsense ba abokaina ne suka zo tayani murna juya da kyau kagani dalolli suke lik'a min banda rashin hankali irin naka awane dalili zaka jawoni wlh ka shiga hankalin ka kar kaga an d'aura mana aure yanzu nan zan koreka ka kara gaba dan sai da ka amince da sharud'an Dana gindaya maka na yarda na aureka dan haka karka sake ka kara yunkurin yin wani Abu har agama taron nan ka wuce muje idan kuma bazaka iya ba ga waje can ka zauna"


Daga haka ta juya tabar Adnan baki a sake cikin tsananin mamakin Ajjidde.


Ajjidde kuwa da tsallenta ta koma cikin filin ta cigaba da rawa Alhazawan Na matseta suna zuba mata ruwan kudi.


Adnan kuwa yana dashe awaje d'aya zuciyarsa Na k'unna yama rasa kalar tunanin da ya kamata yayi idan yaga Yanda Alhazawan ke rungume amaryar da aka d'aura mishi aure da ita yanzu sai yaji kamar kirjinsa ya fad'o

Jikinsa ne ya fara bala'in rawa dayaga Ajjidde Na turawa wani Alhaji duwawunta yana murzawa yana zuba mata uwar kudi

Wani d'an banzan kishi yaji ya rufe shi yaga bazai iya jurewa ba ya nufi wajenta a zuciye dan har wani kiss Alhajin ke kai mata a duwawu duk wai da sunan liki taku biyu ya rage ya isa wajenta Ajjidde ta jefo masa wani mugun kallo ya tsaya cak jikinsa Na k'yarma dan a kallon da ta masa ya gane warning ta zuba mishi.

Ajjidde d'auke kanta tayi ta cigaba da rawar ta inda wasu daga cikin 'yan matan suka nufi wajen Adnan dake Neman zub'ewa k'asa sabida mugun bak'inciki.

'Yan matan zagaye shi sukayi suka fara rawa wasu daga cikin Alhazawan kuwa suka nufi wajensu suka fara lik'a mishi kudi.

Adnan kamar statue kallonsu kawai yake ko motsawa baiyi ba.


Inda Ajjidde itama ta nufi wajensu bayan wani Alhaji ya mata rad'a a kunne.

Matsar da 'yan matan tayi gefe ta tsaya a gaban Adnan ta jawo hannunsa ta zagaye kugunta dashi ta juya masa bayanta tare da had'a duwawunta da jikinsa.


Alhazawan suka saki wani irin ihu suna tafi.

Ajjidde kuwa ta fara sama da k'asa ajikinsa tana shafo gabansa kamar dai a club.

Adnan waro idonsa yayi cikin tsananin mamakin Ajjidde jikinsa Na rawa dan bai tab'a ganin irin wannan rashin kunyar ba take ya wulla duniyar tunanin san sanin wai wacece ma Ajjidde yana tsoron tunaninsa ya tabbata yana tsoron ace Ajjidde karuwa ce dan duk abinda takeyi kamar rik'akk'iyar 'yar bariki Hannunta da yaji Na k'ok'awa da tazugensa tana Neman tsince masa wando yasa yadawo daga duniyar tunanin daya fad'a hankalinsa a mugun tashe ya rik'e mata hannu.

Alhazawan da 'yan matan kuwa suka ringa kurma ihu suna wasa Ajjidde.


Ajjidde kuwa doke hannunsa tayi ta cusa hannunta a wandonsa tare da saka hannunta a gajeran wandonsa tana k'ok'awan d'aga mishi Riga dan har wandonsa yayi k'asa.

Ganin Abinda Ajjidde ke shirin yi masa ta hanyar fito da tsiraicinsa waje yasa ya doke hannunta da gudu tare da w'ular da hannunta cikin tsananin tashin hankali ya kwashi wandonsa a hannu ya saka gudu.

Alhawazawan kuwa suka kwashe da Dariya suna mai ihun "Ashe angon ragone".

Ajjidde kuwa cikin tsananin takaici ta bishi da kallo har sai data daina hango shi.

Mik'ewa tayi a fusace ta jawo wani daga cikin Alhazawan ta fara mishi wani irin rawa aka saka ihu ana mata yayyafin kudi.


Adnan kuwa can bayan gidan yaje ya tsaya jikinsa Na masifar rawa har yanzu mamakin abinda Ajjidde tayi mishi a cikin mutane yake tunda yake bai tab'a ganin irin wannan tashin hankalin ba duk da yayi yawon club club yayi iskanci iri iri amma iskancin Ajjidde yafi k'arfinsa a bainar jama'a take Neman fito mishi da jikinsa to me take shirin yimasa.

Sallati yasa yana dafe kansa dake Sara mishi saka wandonsa yayi ya zub'e a k'asa zuciyarsa Na rayya masa da Ajjidde yar bariki ce lamba d'aya amma san dayake mata na Neman hana shi ganin haka danganta abinda tayi kawai da k'ila aladarsu ce haka ko yaya ya runtse idonsa sai ya hango irin rawar da take yi agaban Alhazawan nan kirjinsa Na bugawa.

Kansa dake sarawa ya dafe ya wula duniyar tunanin matar Auren sa da yake aure duk alamomin da yake nuna Ajjidde 'yar bariki ce duk a bayyane suke yaga wasu da idanuwansa ko daga yanayin rawar da take Alhazawan na kai mata runguma da matsa amma san dayake wa Ajjidde na hana shi ganin haka shi kuwa wane irin so ne haka yake wa Ajjidde haka wani irin makahon so ne wannan anya Ajjidde bata fi k'arfinsa ba wane irin masifar yake Neman jefa kansa ne tunda ga wajen d'aurin Auren ya gane Ajjidde ba matuniyar arziki bace idan bahaka ba ina aka tab'a d'aura aure babu shaidu babu siga Wanda ma ya d'aura Auren mace na daga gefensa inama ace irin halin Aliya ne da Ajjidde da yafi kowa jin dadi sai a yanzu yake ganin irin salihancin Aliya sai a yanzu ya san Aliya mace ce mai kishin kanta Bawai kauyanci ne da ita ba sai a yanzu yasan Ashe Aliya wayayyar mace ce me ake yi da wayewa irin ta Ajjidde mace da aka sani da kunya amma Ajjidde Sam bata dashi har yanzu mamakin abinda tayi masa yake yi to wai da bai gudu ba mai take shirin yi masa ne?runtse idonsa yayi yana yana fargabar sabuwar rayuwar da zai soma yi da amaryarsa da bai san wacece ba daga inda yake yana jiyo ihun Alhazawa da 'yan matan suna ihun kiran sunayen Ajjidde ko bai lek'a ba yasan Ajjidde tana can tana watsewarta da sunan rawa wai meyesa so zai masa haka matar da yake aure ma tafi k'arfinsa bai isa ya sata ba ballantana ya hanata a ranar aurensu ta kwashe shi da mari wai wane irin rayuwa ne wanan take Aliya ta fado mishi aransa iya tsawon zamansu Aliya bata tab'a mishi rashin kunya ba ballantana har akai wai data d'aga Hannu ta mareshi wai sai gashi Ajjidde ta mareshi acikin bainar jama'a tabbas ba dan san dayake mata ba da babu abinda zai hana ya mata dan banzan duka ya kwashi kayansa ya k'ara gaba dan ba sai ya saketa bama aurensu ma bai d'auru ba.


Gashi daga d'aurin aure ta fara cewa zata Kore shi sabida kawai gidanta ne yana cikin tsaka mai wuya dan ko da ta koreshi bashida wajen zuwa akan ta ya siyar da komai nashi yanzu abinda ke cikin account d'insa bai fi dubu dari biyu da ashirin ba.

Cije lebb'ensa yayi yana tunano masifar dake tunkuro shi bai san adadin awanin daya kwasa awajen ba yana tunani har sai da d'aya daga cikin 'yan matan Ajjidde tazo tana girgiza shi.


A firgice Adnan ya mik'e yana kallonta tare da kalle kalle yana mamakin yanda akayi dare yayi haka Dan garin yayi duhu sosai.

Maida kallonsa yayi kan buduruwar dake cije lebb'e tana shafo kirjinta tare da mai signa

Adnan ya ware idonsa yana kallonta.

Sai data wani zaro harshe ta kad'a shi tace masa "kaje Amaryarka na kiranka tun dazu take nemanka Ashe Anan kazo ka b'uya haba angwan mu akan za'a fito mana da lollipop muga yanayin shi zaka gudu da ganinka fa zakayi zaki dan Allah kabani numberka gobe mu hadu ka lassamin dadi"


Tace tana wani lumshe ido.


Adnan mamakine ya rufe shi jikinsa ya fara rawa

Shi dai yau yana ganin tashin hankalin da bai tab'a gani ba bai Ankara ba yaji ta rungumoshi tare da chapko wandonsa.

Adnan k'ok'arin tureta yake yi da iya k'arfinsa sai ga Ajjidde ta bayyana agabansu tana ture buduruwar daga jikin Adnan tana "Ubanki Summy angon nawa kike Neman haikewa tun bamu yi komai dashi ba Dalla ware daga nan"

Summy da sauri tabar wajen tana jifan Adnan da kallon mayyata.

Adnan kuwa yace "nashiga uku na lalace yau naga ta kaina"

Ajjidde murmushi ta sakar masa ta jawo hannunsa tana "bangane ka shiga uku ka lalace ba mai akayi maka nidai banji dadin kunyar daka bani ba agaban kawayena inaso na nuna musu cewar mijina namijin duniya ne ba rago ba kawai sai ka saka gudu wlh ba karamin kunya kabani ba kasa sai tsokanata suke sai kazo muje daga ciki dan inaso na tabbatar musu da cewar ba ragon miji na aura ba"

Daga haka Ajjidde ta fara Jan hannunsa suna tafiya.

Adnan sallati yayi ya fusge hannunsa hankali a tashe yace "Ajjidde kinsan mai kikeyi kuwa mai haka ni Wlh kin fara bani tsoro mai kike nufi dani ne"?


Ajjidde murmushi tayi tace " Haba Adnan karka manta yau aka d'aura mana aure kai mijina ne ni matarka yau ranar farincikine agaremu ahaka kamar a waye kake amma kuma alamomin da kake nunamin kamar irin daga kauyen nan kake banaso na kara jin komai daga wajenka ka wuce mutafi"


Daga haka ta k'ara rik'e hannun Adnan tafara ja

Adnan binta kawai yake yana sallati dan lamarin Ajjidde sun girmama tunaninsa.

Palonta suka shiga inda warin shisha ya bugi hancinsa Alhazawan nan ne a zazaune kowane da mace a cinyarsa kowane da abinda yake yi.


Suna ganinsu suka fara ihun ga amarya ga Ango.

Adnan kuwa numfashinsa ne ya ringa gudun tsere yana k'ok'awa da numfashinsa dan yau kam yana ganin tashin hankali arayuwarsa.

Ajjidde hannu ta d'ad'aga musu taja hannun Adnan suka shige d'aki ta cika masa hannu tare da kulle d'akin.


Adnan zuwa yanzu tsoron Ajjidde ne ya lullub'eshi ya kame a waje d'aya yana kallonta.

Murmushi ta sakar masa tace ya shiga ya watsa ruwa yazo yaci abinci.


Adnan sallati ya ringa yi a zuciyarsa wai k'arfi da yaji Ajjidde ta zama namiji ya zama macen dan a iya tunaninsa amarya kunya gareta ranar data kebb'e da angonta idan ba mantawa yayi ba sai da ya kai ruwa rana kafin Aliya ta iya shiga tayi wanka aranar da aka kai masa ita aranar ma sai da suka kwana suna dambatuwa da Aliya kafin ta yarda dashi dan kusan sumewa ma tayi daya rabata da kayan jikinta sai gashi wai Ajjidde ce ma take cewa ya shiga wanka.

Hulan kansa da Ajjidde ta cire shi ya dawo dashi daga tunanin daya tafi.

Ta fara balle mishi links d'in rigarsa.

Adnan shi dai ido kawai ya zuba mata har ta gama cire masa kayan jikinsa ya rage daga shi sai gajeran wando da vest ganin ta kai hannu zata cire masa gajeran wandon yasa yayi sauri ya rik'e mata hannu ita kuwa ta d'ago tace "Adnan wai me hakane da kayan zaka shiga wanka ka tsaya In tayaka cirewa mana mai kake b'oyemin mai bansani ba ka bari na ga girman abuna"

Kafin ya ankara har ta sutalle masa wandon k'asa.

Adnan cikin tashin hankali

Please Login or Register in order to submit comment