Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yayi dari ya tashi matsawa yayi kusa da ita da sauri ya kankantar da muryarsa yana cewa bashida kudi 50k ne kawai a Aljihunsa.

Ajjidde ko dagowa batayi ta kalleshi ba har ta gama kwasar abinda zata kwasa ta nufi inda ake biya bayan tace Adnan ya biyota.

Adnan kamar ya saki fitsari ya d'iba da gudu dan yasan ya gama shan kunya Ajjidde bai kamata tayi masa haka ba tunda tasan bashida da kudi.

Cikinsa ne yayi wani irin kullewa dayaji bill d'in kayan da ta siya dubu dari biyar da hamsin.
Wani irin gumi ne ya hau keto masa.

Ajjidde kuwa ta juya fuskarta d'auke da murmushi tace yayi settling bill d'in

Adnan ido ya gwagwalo yana kallonta ya kasa ko motsawa.


Ajjidde kuwa ganin yanda Adnan ya tsure ya gigice yana narka gumi yasa ta saki murmushi duk hakoranta suka fito ta sa hannu a Jakarta ta Ciro ATM card d'inta ta mik'a musu suka ciri kudin.


Ta kwashi ledoji biyun da aka saka mata kayan a ciki tayi gaba Adnan ya bita abaya jiki asanyaye yana tunanin meyesa tayi mishi haka ko Dan ta nuna masa bazai iya aurenta bane tafi k'arfinsa


Ahaka ya ringa binta abaya har suka karasa inda yayi parking motarsa ta ajiye kayan akan motarsa ta juyo tana kallonsa da wanan murmushin nata.

Adnan shima kallon nata yake yi jiki ba kwari dan yasan zaginsa zatayi sabida ya kasa biya mata idan ba ganganci irin nasa ba ina shi ina Ajjidde.


Ajjidde ce ta katse masa tunanin da yake yi tace "nace ka fita dani ne sabida idonka ya gane maka irin luxurious life danakeyi this is how I spend money on perf and cream I used a rana bana kashe k'asa da dubu dari can u still marry me"?


Adnan yawu ya hadiye mai kauri dan ya jika makoshinsa daya bushe jikinsa ya fara rawa


Ajjidde kara tambayarsa tayi tace " zaka iya aurena ka cigaba da hidimanta min kamar yanda na saba"?

Adnan shiru yayi ya cigaba da kallonta sai da ta k'ara tambayarsa akaro na uku Adnan ya bud'e bakinsa dak'yar yace

"Ajjidde ba laifina bane dan na kamu da matsanacin sanki nasan nima na yaudari kaina idan nace zan iya aurenki dan nasan kinfi k'arfina am no body I have nothing but ya zanyi zuciyata bata min adalci ba with wat u just said nasan nasan bazan iya auranki ba banida kudin da zan iya meeting need dinki"

Adnan yace muryarsa na cracking kana ganin Cikin idonsa zaka hango tsantsar tashin hankalin da yake ciki na rasa Ajjidde.


Ajjidde murmusawa tayi tana tunanin hukuncin kawai da ta yanke na Auren Adnan at least bai kamata ace rayuwar da kanzel da Nura sukayi ba aure ace itama tayi irin wanan rayuwar ba kamata yayi ita kuma ta Auri irin Adnan ta ringa juya shi San ranta tana cigaba da barikinta dan dama auran mai kudi zai hanata tayi abubuwan da takeso but auren Adnan da bashida komai zai sa ta cigaba da abubuwanta dan bashida powern da zai hanata cigaba da sana'arta da wanan tunanin tace "I know nafi karfin aurenka na girmi ajinka but ba hakane zai sa naki auranka ba but on just on one more condition".

Adnan jiki na rawa da d'an hope d'in bazai rasa Ajjidde dayake jinta tamkar fitar numfashinsa ba yace " am ready for any condition indai bazai sa ki k'i aurena ba"

Ajjidde girgiza kanta tayi tace "inka Aureni zan cigaba da sana'ar danakeyi cos da sana'ar da nake yi kagani a Wanan stage d'in kuma har na baka sha'awa kaji kana sha'awar aurena 2 aurena bashi yake nufin zaka mik'a k'afa kayi tunanin ka samu inda zaka huta ba Sam kaje ka cigaba da Neman kudinka kuma idan anyi Auren gidana zaka zauna sabida bakada gidan da zaka iya ajiyeni lastly babu ruwanka da samun ido acikin al amurana i do wat Eva I want idan ka yarda fine zan yarda ka aureni idan baka yarda ba zaka iya hakura da aurena"


Adnan duk da dokokin sun mishi tsauri amma tunda dai ta yarda zata Aure shi bai tsaya wani dogon tunani ba ballantana har yayi tunanin irin sana'ar da take nufi yace mata ya amince jiki na rawa.

"Duk lokacin da ka shirya zaka iya zuwa a d'aura mana Auren I dont need anything from u"


Daga haka ta kwashi ledojinta ta shige cikin mota Adnan ya zagaya ya shige Cikin tsantsar farincikin aurensa da Ajjidde tace zatayi.


Sai da ya sauketa a gida yana jera mata godiya inda ita kuma tayi shigewarta ta bar shi awajen.

Adnan tsabar murnar cikar burinsa da dubu hamsin dinsa da baiyi ciwon kai ba sai da ya tsaya a hanya ya siyi kaji da tsire har dasu yoghurt ya nufi hanyar gida.

Karfe goma dai dai ya k'ara so gida da wake wakensa ya shiga gidan sabida murnar dayake ciki inda ya Tarar da Zara a zaune a Palo ta had'a manja da yaji tana ta lassa sabida kawai kwadayin da takeji.

Adnan kusa da ita ya zauna yana ta murmushi ya ajiye ledar agabanta yace "yarinya gashi kici ki ture burina ya cika na samu abinda nakeso"


Zara da kamshin da tajiyo yasa taji tsohon yunwar da takeji ya taso mata wani irin damka ta kaiwa ledar ta Ciro takardar kazar ta bud'e ta fara yaga tana kallon Adnan tana zabga murmushi Adnan kuwa kallonta kawai yana kallon yanda jikinta ke rawa kamar bata tab'a cin kaza ba.

Sai da taci iya cinta har ta rasa wajen turawa ta hakura ta ture takadar gefe ta fara zabgawa Adnan godiya tana Allah ya k'ara cika masa burinsa.


Ameen Adnan yace ya kira sunanta yace "Zara aikin da nake nema a Maiduguri na samu nan da wata da zai kama zan koma can da zama gabadaya dan haka kafin watan ya kama kisan yanda zakiyi ki koma gidanku Ki daidaita da iyayenki zan baki kudin da zaki kula da abinda zaki Haifa kafin na yi balancing na dawo inyaso idan nazo sai muyi Auren amma idan kuma kika k'i to babu ruwana dan babu abinda zai hanani tafiya ta idan kuma kudin hayan ya kare sai kisan yanda zakiyi amma dai ki kara shawara da zuciyarki kigani ya kamata kije ki sami iyayenki ki nemi yafiyarsu tun lokaci bai kure miki ba"

Wani irin zufa ne ya hau ketowa Zara hankalinta yayi mugun tashi cikinta yayi wani irin dunkulewa.



Idan nasamu lokaci xanyi posting gobe insha Allahu idan kuma bansamu dama ba sai bayan sallah amma I would try na kusa dai kammallawa na huta insha Allahu..

*M🅰K'OT🅰N JUN🅰*


*REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS* *P.M.L*




® REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS

ɯɛ ɖơŋŧ ʝųŞŧ ɛŋŧɛřŧąıŋ ŋɖ ɛɖųĆąŧɛ, ცųŧ ɯɛ ąٳŞơ ŧơųĆɧ ɖ ɧɛąřŧ ơʄ řɛąɖɛřŞ


# WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
# IG PML WRITERS
# https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-




*Written by*

💅💅💅 *SADNAF*💅💅💅



*Follow me on wattpad @ Sadnaf*


*TUNATARWA*


*ARAFAT DAY*

*monday 20th august 2018*

*ASSALAMU ALAIKUM*
*'Yan uwa mata da mabiya addinin* *musulunci ga k'aramin tunatarwa,ranaku goma na cikin watan dhul hajj na d'aya daga cikin kwanaki goma uku da su kafi kowanne* *muhimmanci da albarka a rayuwan ko wani halitta, don haka ne ma ake azumtar su ake kuma kwad'aita mana yawan ayyuka na gari,toh a yau Allah ya kusa kawo mu ranar ARAFAT wanda ubangijin mu ne dakan sa yake saukowa ya amshi bukatunmu ,a ranar akwai wani lokaci mai mutuk'ar daraja da ake so muyi amfani dashi (lokacin shine:DA YAMMA i.e daga fad'uwar rana zuwa lokacin magrib) don ANNABI S.A.W ya sanar da mu addu'a bata fadi kasa wannan lokaci,kuma ya sanar damu cewa zaifi dacewa mai gida ya tara iyalansa ko uwargida ta tara iyalanta ayi addu'oi tare.cewar sa Annabi s.a.w mai daraja,Alokacin Allah yana matuk'ar jin dadin hakan,sannan in har ka roki abu wajen Allah baka samu daga abunda ka tambaya ba, to ba shakka bai dace da kai ba ne ,don kowane addu'a ba makawa karb'abb'iya ce a lokacin,matan gida mu muka fi kowa bada gudumawa a rayuwa yanzu, mu d'aure pls duk da da ma lokacin na ayyukan gida ne ki ajiye aikin gefe zaki iya yinsa daga baya ki tara iyalinki waje d'aya idan kuma maigidan na nan Alhamdulillah haka aka fiso kiyiwa ya'y'anki addu'a kiyiwa mijinki kiyiwa iyayenki kiyiwa mak'otanki kiyiwa al ummar musulumai gabaki d'aya this is an golden opportunity don't miss it 5 minutes can change your life entirely ALLAH YASA MUNA DA TSAWON RAN GANIN WANAN RANA HAPPY SALLAH IN ADVANCE TO YOU OLL*


*Dis page is oll urs Surrayhams stay blessed*



*page 29*



Kallon Adnan kawai take hawaye na zubo mata

Adnan kuwa tab'e baki yayi yafara k'ok'arin mik'ewa dan bashida wani matsala yanzu tunda zai Auri sanyin idaniyarsa Ajjidde.

Zara da Sauri ta ruk'o hannunsa adai-dai lokacin data fashe da wani irin kuka tace "Haba Adnan ya za'ayi ka tafi ka barni a cikin wanan halin da nake ciki ina ma laifin ka tsaya na haihu kafin ka tafi Maidugurin daga ina zan fara idan ka tafi karka manta cikinka ne ajikina duk halin danake ciki a yau Kaine sila bazan iya zuwa gida da cikin nan ba idan naje da ciki nace musu me ince musu cikin waye ajikina"


Zara tace tana sakin hannunsa tare da kara fashewa da kuka


Adnan da sauri ya koma ya zauna a gefenta da wani tunani ya fad'o masa da Sauri yace "na samo shawara indai kika koma gida iyayenki zasu k'arbeki da hannu biyu kuma zamuyi Auren mu cikin kwanciyar hankali ba tare da mun fuskanci wani matsala ba kinaji "

Zara da sauri ta gyad'a masa kai

Adnan kuwa ya K'ara gyara zamansa yana tunanin mai yasa duk wanan tsawon lokacin wanan tunanin bai fad'o masa ba sai yanzu.

"Gobe ki shirya da magriba na kai ki gidanku da kaina idan kinje karki shiga gidan kai tsaye kisa ayi miki magana da Mahaifiyarki idan ta fito ki fad'a jikinta ki fashe mata da kuka sai kin yi kuka mai isarki kin tabbata da hankalinta ya tashi sai kice mata tunda Ameer ya sakeki kike tsoron zuwa gida sabida kinsan korarki zasu yi wajen wata mata mai siyar da abinci kika zauna kike tayata aikace aikace take baki abinci kike ci kina kwana a gidanta babu waya a hannunki ballantana ki kirata ki gaya mata halin da kike ciki Sanan ga wahalar da kika ringa sha sabida sakinki da Ameer yayi da ciki ahaka kika ringa shan wahala kinje gidan Ameer yafi a kirga amma yana korarki shine jiya wacce kike yiwa aiki tace miki zata koma garinsu da zama yau babu Yanda bakiyi da ita ba akan ta barki ki zauna tace aa sai kin bar mata gidanta ahaka ta koreki yau dinan kika ringa Neman wajen da zaki koma ki zauna amma babu shine kikace bari ki gwada zuwa gida ko zasu amsheki kinsan kinyi kuskure dan Allah ta yafe miki bakida wajen zuwa karta manta bakida sama da ita Kinga sai ki lanka yawa Ameer cikin kice da ciki ya sake ki ni nasan zasu karbeki kinga idan kin haihu zasu d'auka d'an Ameer ne nan kuwa nasan d'ana ne bakida wani tashin hankali kinga idan naje na samu abinda nakeso sai na dawo na aureki cikin kwanciyar hankali na nuna musu zan rik'e abinda kika Haifa Kinga shikenan d'anmu ya dawo gabanmu" Adnan yace yana sakin murmushi rabuwa da k'aya ya huta


Zara kallon Adnan kawai take dan tasan wayo kawai yake so ya mata guduwa zai yi ya barta amma ya zata yi hakan shine kawai zai zame mata ma fita idan ba haka ba idan bata koma gidansu ba ya zata fara rayuwa idan ya koma garinsu idan dai iyayenta suka amsheta basu Koreta ba zata zauna ta haifi abinda ke cikinta ta kuma raineshi ta bar Adnan da Allah.


Adnan ne ya katse mata tunanin da take yi yace "ya kika yi shiru ko shawarar bata yi ba Nifa tausayinki nakeji Zara dan wlh idan na tafi zan Dade ban dawo ba kuma kinga zaki shiga gararin rayuwa sabida haka gwara kawai kibi shawarata"


"Idan kuma suka kira Ameer suka tambayeshi fa akan dagaske cikinsa ne ajikina yace ba cikinsa bane bafa"?




Adnan da Sauri yace "haba sai kace ba mace ba ai tub'urewa zakiyi kice wlh cikinsa ne zarginki kawai yake ke baki tab'a sanin wani d'a namiji ba ni nasan idan kika dage da kuka da komai dole zasu yarda"


Zara ajiyar zuciya kawai ta sauke ta mik'e Hawaye na zubo mata magana ta fara yi cikin karyayar murya tana "Adnan nasan so kake na koma gida kawai dan nabar rayuwarka nasan so kake ka gudu kabarni Bawai dan ka samu aiki a Maiduguri ba nasan nid'in ce baka so Karka damu Adnan zanje gida zan kuma bar rayuwarka zan lanka yawa Ameer cikin dake jikina duk da nida kai munsan cikin ba nashi bane nakane amma inaso ka sani zan raini abinda muka Haifa har ya girma inaso duk inda ma zaka gudu kaje ka tuna kana da d'a awajena idan baka neme shi ba ni zan sa ya neme ka wlh nayi dana sanin biye wa san zuciyata nayi dana sanin biye maka yanzu gashi tun ba'aje ko'ina ba ina girb'ar abinda na shuka Allah ya rufa min asiri na tonawa kaina Allah ya min niima ya bani salihin miji mai kaunata amma dayake banida rabo shaidan na kad'an min ganga haka na biye maka muka ringa watsewa babu komai idan na koma gida iyayena suka yafemin bayan na haihu zan nemi Ameer in nemi yafiyarsa Adnan ngd da irin sakayyar da kayimin Insha Allahu tun a gidan duniya Allah zai sakamin abinda kayi min Allah ya kaimu goben zanje gida da kaina ba sai ka kaini ba"

Zara tace ta juya tare da nufar d'akinta

Adnan duk maganganun da tayi babu Wanda ya tab'a shi ko kad'an hasali shi Allah Allah yake gari ya waye Zara ta k'ara gaba yana ganin babu Wanda zai kai shi jin dadi.


Ido kawai ya zuba mata har ta shige d'aki tana zubar da hawaye tab'e baki yayi ya shige d'akinsa yana kiran Layin Ajjidde ya mata misscall yafi a kirga amma bata d'aga ba ahaka ya kwana yana kiran layinta inda a karshe yaji ta kashe wayan gabad'aya da tunanin Ajjidde yayi bacci har dasu mafarkinta.


Zara kuwa fargaba ne yabi ya cikata dan batasan mai zata tarar ba goben idan taje gida.



B'angaren su Ameer kuwa washegarin ranar da yamma yana barin office gidansu Aliya ya nufa da d'an confidence d'in shawarwarin da Hajiya Ameena ta bashi.

A k'ofar gidansu yayi parking ya d'auko wayarsa yana k'ok'arin kiran Aliya.

Adai-dai lokacin motar Alhaji Abubakar yayi parking a k'ofar gidan inda Adnan yayi Sauri ya maida wayarsa cikin Aljihunsa ya mik'e yana sunkuyar dakai daya hango Alhaji Abubakar ya fito daga motarsa fuskarsa d'auke da fara'a.


Ameer da Sauri ya k'arasa ya tare shi kafin ya iso wajensa ya zub'e a k'asa yana gaishe shi.

Alhaji Abubakar cikin fara'a ya amsa gaisuwarsa tare da cewa ya taso su shiga daga ciki akan me zai tsaya a waje ai shi na gidane.

Ameer cikin tsananin farinciki ya mik'e yabi bayansa wani irin farinciki na ratsa shi dan ji yake tamkar har an bashi auren Aliya.


A palon saukar baki Alhaji Abubakar ya sauke shi suka kara gaisawa dashi yana tambayarshi mutanen gidan inda bayan sun gaisa Alhaji Abubakar ya mik'e da zumar ya shiga daga ciki dan yaga Ameer din kunyarsa yake ji.

Ameer da Sauri ya d'ago yana Sosa kai ya fara magana cikin 'in'ina yana Cewa dama wajensa yazo.

Alhaji Abubakar komawa yayi ya zauna yace Allah yasa lafiya duk da yariga da yasan abinda ke tafe dashi amma gwara yaji dai daga bakinsa.

Ameer kara sunkuyar da kansa yayi a hankali ya fara gayawa Alhaji Abubakar abinda ke tafe dashi akan san Aliyar da yake da kuma Aurenta da yakeso yayi ba wasane ya kawoshi ba.

Tun kafin ya gama magana Alhaji Abubakar ya washara baki yana Mai jin wani irin farinciki dan kowane uba zai so yarsa ta samu miji irin Ameer.


Alhaji Abubakar ce masa yayi babu komai Allah ya tabbatar musu da alheri su fahimci juna shi da Aliyar duk lokacin daya shirya yazo kawai a tsaida magana.


Ameer godiya ya fara zabga masa tamkar har an d'aura masa aure da Aliyar inda Alhaji Abubakar ya mik'e yace masa bari ya turo masa Aliyar daga haka ya fice daga palon fuskarsa d'auke da fara'a.


A Palo ya Tarar da Hajiya Rukayya da Aliya da Sumayya suna kallon tashar Arewa 24

Shigowarsa palon yasa suka mik'e suna masa sannu da zuwa

Alhaji Abubakar amsawa yayi ya dakatar da Aliya dake k'ok'arin barin palon yace ta dawo ta zauna.

Aliya cikin fad'uwar gaba ta koma ta zauna tana kallonsa dan ta d'auka wani laifin Tayi.

Gyaran murya yayi yafara magana yana "Aliya yanzu dana dawo na tarar da Ameer a k'ofar gidanan yazo nemana akan yana sanki da aure yana neman izinina akan zai fara zuwa wajenki dan Ku fahimci juna dashi ya kuma ce ba wasa ya kawo shi ba ban tsaya naji ta bakinki ba sabida munriga da munyi magana dake na kuma baki shawara nace mishi na amince mishi akan ya ringa zuwa kuna fahimtar juna kafin magana Tayi k'arfi Aliya ga Ameer can ban yarda ki wulakanta Shi ba dan godiya ya kamata kiyi wa Allah daya baki Wanda yafi wanan tsohon mijin naki dan haka gashi can a palon bak'i yana jiranki maza kije ki same shi.


Aliya mik'ewa tayi jikin ta asanyaye ta nufi d'akinsu taje ta saka hijabinta ta nufi palon bak'i gabanta na d'an fad'uwa bazata iya cewa ga abinda take ji ba game da Ameer ita dai tasan zata ringa kula shi kawai dan tayiwa iyayenta biyayya amma idan ba haka ba ta Dade da kulle zuciyarta bata jin akwai wani d'a namiji da zata bud'ewa Zuciyarta.

Ahaka ta k'arasa wajensa fuskarta babu yabo babu fallasa.


Ameer kuwa shigowarta yasa ya mik'e ya tsaya sai da ta zauna ya koma ya zauna shima.


Aliya gaishe shi Tayi kanta a sunkuye.

Ameer ya amsa yana lek'a fuskarta sai dai suka samu minti biyar ahaka kafin yace "Aliya kiyi hakuri nasan na takura miki ba laifina bane zuciyata ce ta kamu da mugun kaunarki da har nake ganin bazan iya rayuwa batare dake ba nasan u would find it difficult to trust and love again but ina rokonki ki bani dama nashiga rayuwarki na zama abokin rayuwarki I promise u bazaki tab'a Dana sani akaina ba"


Aliya ita dai kanta a sunkuye yake bata d'ago ba ballantana Tayi yunkurin magana

Sai da Ameer yace "kinyi shiru baki ce komai ba Aliya i don't want to false u idan dai kina ganin bazaki iya samar min waje a zuciyar ki ba pls ki fad'a min bazan ji haushi ba dan komai yin Allah ne duk inda nakai da kaunarki idan Allah yayi bazan aureki ba dole na hakura"

Aliya sai a lokacin ta d'ago suka had'a ido tayi Sauri ta maida kanta k'asa tace murya na rawa "Allah ya zaba mana abinda yafi alheri"


Ameer cikin tsananin farinciki yace "meaning am accepted kenan"?

Aliya kai kawai ya gyad'a masa

Ameer ya saki ajiyar zuciya yana ta zabga hamdala a filli hakane yasa Aliya d'an sakin murmushi dan ba k'aramin Dariya ya bata ba.


Ameer hira ya ringa janta dashi duk dan ta saki jiki dashi duk da amsarta ee ko aa ne bashi ya bar gidan ba sai da Magriba bayan ya dire mata siyayyan da ya mata da sakon da Hajiya Ameena ta bashi ya bata da bai samu ya bata a jiyan ba.


Washegari da sassafe Adnan ya kara dira kan wayarsa yana kiran Ajjidde dan kwana yayi yana mafarki da ita shi kansa har tsoron irin san da yake yiwa Ajjidde yake haka ya ringa kiran wayar Ajjidde har sai da yagaji dan yana ta ringing taki d'auka tagumi ya buga kamar Wanda akayiwa rasuwa dan ji yake idan baiji muryarta ba zai iya mutuwa wanan wane irin azababben so ne haka yake yiwa Ajjidde haka ya wuni a gidan tamkar Mara lafiya wayarsa rik'e a hannunsa yana san zuwa gidan Ajjidden yana tsoron zuwa.


Zara kuwa a ranar da sassafe ta had'a kan kayanta da basu fi kala biyar ba bayan kukan dataci ta koshi har wani fad'awa Tayi sabida fargaba aranar ko abinci ta k'asa ci a d'aki ta wuni tana jiran magriba tayi ta tafi gidansu.


Ana kiran sallar magriba tafito daga d'akinta da turtsetsen cikinta hannunta rik'e da ledar kayanta.

Ko kallon inda Adnan daya buga tagumi yana kallon waje d'aya batayi ba ta nufi hanyar waje.


Adnan wucewarta ne yasa ya dawo daga tunanin da ya tafi tun safe bai sata a idonsa ba sai yanzu da sauri ya mik'e yabi bayanta yana "Ki tsaya nazo na kai ki mana"


Zara ko tsayawa batayi ba ta fice daga gidan.

Adnan kuwa ya tab'e bakinsa ya koma ciki dan shi wani zazzabi zazzabi ma yakeji sabida rashin jin muryar Ajjidde.


Zara kuwa bata sha wahalar samun tricycle ba ta nufi gidansu gabanta na balain fad'uwa hawaye kawai take sharewa.

Daga nesa da gidan tace a sauketa ana sauketa ta tsaya cak tana kallon gidan gabanta kamar ya fad'o dan cikin ta kuwa sai motsi yake sabida abincin da bata ci ba tun safe.


Sai da ta samu kusan minti talatin tana tunanin abinda ya kamata tayi dan wani irin tsoro takeji.

Ahaka ta d'aure jikinta na rawa ta nufi k'ofar gidan ta fara kwankwasa wa kirjinta kamar zai fado k'asa sabida fargaba

Takun takalmi ta jiyo alamar za'a zo a bud'e k'ofar ta ja da baya da sauri tana dafe cikinta dan ji take kamar dan zai fad'o.

Ana bud'e k'ofar ta maida hannunta kirjinta ta dafe ta gwalalo ido.

Khaleed da k'arfi yace "Aunty Zara kece ko mafarki nake"

Zara cikin rawar baki da jiki hawaye na zubo mata tace "Khaleed nice dan Allah jeka kirawo min Mommy"


Khaleed a 360 ya koma ciki da gudu dan yasan burin Mommy Hauwa da mafarkinta kenan taga Zara.


Zara kuwa zubewa tayi a k'asa sabida k'afarta dake rawa wani irin kuka ta fashe dashi.

Adai-dai lokacin da Mommy Hauwa ta fito kamar wacce aka hankad'o daga gidan tabi ta rame kamar ba ita ba.

Ido kawai ta zubawa Zara hawaye na zubo mata inda Zara itama ta zuba mata nata idon tana sheshek'ar kuka.


Mommy Hauwa cikin rawar murya tace "Zara kece"?

Zara cikin matsanacin kuka da numfashinta dake seizing tace " Nice Mommy Dan Allah ki yafemin...........

*M🅰K'OT🅰N JUN🅰*


*REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS* *P.M.L*




® REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS

ɯɛ ɖơŋŧ ʝųŞŧ ɛŋŧɛřŧąıŋ ŋɖ ɛɖųĆąŧɛ, ცųŧ ɯɛ ąٳŞơ ŧơųĆɧ ɖ ɧɛąřŧ ơʄ řɛąɖɛřŞ


# WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
# IG PML WRITERS
# https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-




*Written by*

💅💅💅 *SADNAF*💅💅💅



*Follow me on wattpad @ Sadnaf*


*HAPPY SALLAH TO ALL MUSULIM UMMA ALLAH YA MAIMAITA MANA*



*Page 30*



Mommy Hauwa kallonta kawai take hawaye na zubo mata kukan Zara na karya mata zuciya babu abinda yafi d'aga mata hankali kamar Dr da batasan ya zasu kwashe dashi ba idan yaga Zara.


Zara kuwa ganin Mommy Hauwa a tsaye tak'i motsawa ballantana tayi magana yasa ta rarrafa ta k'arasa wajen Mommy Hauwa ta rik'e mata k'afa tana k'ara fashewa da kuka tana "Dan Allah Mommy kiyi magana ki yafemin nasan ban cancanci yafiyarki ba sabida abubuwan da nayi miki banida sama dake Mommy dan Allah ki yafemin nasha wahala bayan da Ameer ya sakeni da ciki Mommy maganar da nake ma Yanzu ko abinci banci ba tun safe"


Mommy Hauwa da sauri ta durk'usa agaban Zara hankalin ta a tashe ta ruk'o kafad'ar Zara tana "Zara dama da ciki Ameer ya sakeki? Meyesa tsawon lokacin nan baki zo gida ba?


Zara katseta tayi tana " Mommy da ciki Ameer ya sakeni babu irin zuwan da banyi wajensa ba ina rokonsa akan ya maidani d'akina ko dan cikin dake jikina yak'i ina tsoron zuwa gidane sabida nasan korata zakuyi duk tsawon

Please Login or Register in order to submit comment