Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ma bai tab'a tunanin Zata yi girkin ba tunda yasan ya mata ba dai-dai ba.

Sai da ya kusa cinye duka abincin sabida dadin da ya masa babu Laifi Aliya ta masifar iya girki.


Tasowa yayi ya zauna akan kujerar dake kallon Wanda Aliya ke kwance akai ya d'auki remote ya kamo tashar boom TV yana kallo yana satar kallon Aliya da still idonta a rufe bata nuna tasan yana existing awajen ba.


Wani Masifaffar sha'awa ke damunsa sabida balain sa rai da yayi da zai huta da Zara ayau sai gashi Ameer ya kwapsa masa.


Zaman da yayi yanzu a Palo so yake yasamu fuska daga wajen Aliya ya kashe kishin data taso masa dan ba zai iya kwana haka ba.

Yawu ya had'iye a lokacin da yake bin kwantacen gashin dake k'afar Zara da kallo take ya tuno irin nutsuwar da yake samu da ita hankalinsa ya k'ara tashi.

Buge buge ya fara dan kawai ta bud'e idonta ko zai samu fuska amma ina Aliya na nan a kwance yanda take tari ya farayi da k'arfi amma ina duk abanza duk wani Abu da zaiyi dan ta bud'e idonta ta yi masa kallon rahama bata bud'e ba tunani ya hau yi na yanda zai tareta dan yana da balain girman kai bayajin zai iya sake bata hakuri akan abinda ya mata yana cikin tunanin abun yi yaga ta mik'e ko kallon inda yake batayi ba ta nufi d'akinta kafin ya kai ga wani tunanin yaji ta sa key.


Adnan k'asa sauke girman kai yayi ya bita ya bata hakuri har ya kai ga samun biyan bukatarsa.

D'akinsa ya koma ya d'auki wayarsa yayi dailing number Zara dan ya dan samu nutsuwa dan Zara ta San abubuwan da zata masa ya samu nutsuwan.


Sai da yamata miss call biyar bata d'aga take hankalinsa ya fara tashi yana tunanin ko dai asirin su ya tonu ne shiyasa tak'i d'aga wayarsa da Sauri ya kashe wayarsa gabansa na fad'uwa take ya nemi sha'awar data dameshi ya rasa

A haka ya kwanta yana Dan fargaba da tunanin abinda ya hana Zara d'aukar wayarsa har bacci yayi awon gaba dashi.



Aliya kuwa tana shiga d'aki ta Rushe da kuka dan duk a tunaninta Adnan idan ya dawo zai k'ara bata hakuri yace mata yayi nadamar abinda ya mata amma me sai ma ya shareta ya nuna bai San da zamanta a Palon ba lailai Adnan yayi nisa abokiyar fasikancinsa tayi awon gaba da zuciyarsa da tunaninsa dole ta San abun yi.

bacci bai ga idon Aliya ba aranar sabida kwana da tayi tana addu'ar Allah ya karkato da zuciyar mijinta gareta ya shirye shi ya daina bin matan banza sai gabanin Asuba bacci ya d'auketa akan sallaya.


Ameer kuwa har yazo gida zuciyarsa na masa suya ji yake kamar ya jawo Zara daga gidansu ya mata dan banza duka tabbas badan yana balain jin nauyin Mommy Hauwa ba da babu abinda zai hana ya saketa kuma idan ya saketa ba zai k'ara waiwayarta ba Zara Sam ba matar Aure bace da zakayi tunanin samun zuria da ita dole ya d'auki tsautsauran mataki akanta idan da rabon zasu cigaba da zama dan Sam ba zai jure kwatan hallayenta da rashin hankalin da take masa a gida ba.


Yana k'ok'arin bud'e b'angarensa yaga alamar Leda a bakin k'ofa

Sunkuyawa yayi ya bud'e ledar yaga kula ne aciki da k'aramin note

D'aukar takardar yayi ya bud'e ya fara karantawa kamar haka


*Assalamu alaikum ga abinci nan na ajiye maka a bakin k'ofa tunda matarka bata nan babu mai girka maka na kuma ga ga hakkin mak'otaka tunda na Riga da nasan halin da ake ciki Ameer dan Allah kayi k'ok'ari ka dawo da matarka ka yafe mata kuskurenta ka ajiye min kular a bakin k'ofa gobe da safe idan kafita zan zo in d'auka*

*Mrs Adnan*


Sai da Ameer ya samu minti biyu yana juya takardar a cikin kaso Dari na b'acin ran daya kwaso hamsin ya ware bud'e k'ofar yayi ya d'auki ledar ya shige ciki


Ya Zauna akan kujera tare da jawo kular daga cikin ledar yana bud'e kular ya hadiye wani yawu take yunwar da ta Dade tana cinsa ya k'ara taso masa da k'arfi har da had'awa da kugi

Bai tsaya wani wanke hannu ba ya Ciro k'aramin kular dake sama da miyar ke ciki ya ajiye ya ciro tuwo d'aya ya fara kai loma baki


Ci yake kawai yana lumshe ido yana girgiza kai dan ko ayawon restaurant da yake na siyi abinci bai tab'a shan taushen da ya masa dadi haka ba.


Idonsa ya bud'e a lokacin dayaji yana lalub'en tuwo dan bai San har ya cinye ba dayake mulmule biyu ta sa mishi

Hannunsa ya koma yana sidewa bayan ya cinye duka naman da ta sa a miyar sai da ya shanye miyar tas ya ajiye kular yana gyatsa yana ta shiwa Aliya Albarka yana yiwa Adnan murnar dace da nagartaciyar mace take kuma wani mugun k'unci da tafasar zuciya ta rufeshi da ya tuna tasa jahilar matar da babu abinda ta sani sai dafa shayi da indomie da soya dankali


Tsaki yaja a filli a lokacin da yake tattara kulollin tare da nufar kitchen dasu yace "zan yiwa tufkar hanci insha Allah zan gyara miki zama idan mahaifinki ya kasa baki tarbiyya ni zan baki"

A ranar sai da ya samu katon Ghana must go d'insa dayake zuba litattafansa masu mahimmanci ya juye littattafan ya nufi d'akin Zara ya ringa jiddar kana nan kayanta yana sawa aciki dan duk wardrobe d'inta kusan acike yake da kayanta dake bayyana surarta atamfofi lesuna da material kawai ya bar mata da rigar bacci sai kananan kayan masu dama dama dan ya sha alwashin Zara bazata sake saka mishi irin wanan kayan a gidansa ba wanan din ma zuwa zai yi ya zubar.



B'angaren Zara kuwa tana nan kamar tayi bindiga sabida back'inciki tana kallon wayar Adnan ta k'asa d'agawa Sabida Mommy Hauwa data kafa ta tsare dan har d'akinta ta biyota ta samu gefen gado ta zauna


Ta fara mata Nasiha da wa'azi cikin kwantar da murya tana nuna mata darajar Aure da ladan dake cikin Aure

Tana tsaka da mata wa'azi Adnan ya fara kiranta

Da sauri ta kai hannu zata d'auki wayar cike da zumudi dan arayuwarta babu abinda takesan kasancewa dashi kullum wala a filli ko ta waya Sama da Adnan ta ma manta da wata Mommy Hauwa dake ta sheka mata wa'azi

Ta kai hannu zatayi sliding kenan suka had'a ido da Mommy Hauwa dake binta da kallon tuhuma dan tasan babu yanda za'ayi Ameer ya kirata tayi wanan fara'ar

Zara wurgi tayi da wayar dan tasan idan ta d'aga wayar agaban mommy Hauwa baxa tayi bacci ba yau kila ma ta had'a mata da duka

Tsaki ta fara jerawa akai akai kamar ta zunduma ihu sabida takaici dan kiran Adnan nata shigowa ba dama ta d'aga ji take kamar ta mik'e ta gagaurawa Mommy Hauwa mari ta koreta d'aga d'akinta.


Mommy Hauwa kuwa she is very sensitive tuni ta gane halin da Zara ke ciki na tana da saurayi da aurenta bak'inciki da takaici ne yasa hawaye suka hau zubo mata tana kallon Zara dake mitsinin kanta ita kad'ai alamar tafa takura mata.

Mommy Hauwa sai da ta share hawayen da suka zubo mata ta gyara zamanta tafara magana "Zara ko baki fad'amin ba nasan kina muamalla da wani namijin awaje bayan kina da Aure Zara ina zaki kai wanan Nauyin zunubin da kike dibawa kanki Zara kinsan kuwa halakar da kike ciki kuwa Nan miji ma idan baka bishi sau da k'afa ba ya kake karewa ballantana ka kai ga cin amanarsa Zara ina tausaya miki idan baki tuba kin daina abinda kike yi ba wlh kina cikin masifa idan dai da Aurenki kike kula wani dan Allah dame Ameer ya rageki da kika zabi kiringa cin amanarsa a tunaninki idan kikayi wasa da damarki Ameer ya sakeki zaki samu mai nagartattun hallayensa Zara tambayarki nake kin min shiru"?

Zara shiru tayi tana wani harare harare dan gani take da tana da hali da tuni ta fitar da Mommy Hauwa daga d'akinta

Mommy Hauwa girgiza kanta tayi hawaye masu zafi na k'ara bin kuncinta tana " Zara ban fiye ganin laifinki ba sabida bakida ilimin addini ballantana kisan ya ake zaman Auren har ya kai ki da kisan dokokinsa nayi iya k'ok'arina dan Ku samu ilimin addini sabida kuringa kiyaye dokokin musulunci amma ina mahaifinku ya hana yace na takura muku alhalin bai San gata nakeso nayi muku ba Zara Mahaifinku bai saku akan hanya mai b'illewa ba face halaka Zara ki rufawa kanki asiri gobe na maidaki d'akinki dan aurenki shine rufin asirinki ki daina bari shedan yana kad'a miki ganga har kina kula wani da Aurenki"

Zara mantawa tayi da matsayin Mommy Hauwa a gurinta tace "tab kema naki wasa ne kinsan Allah bazan koma gidan wanan kidahumin mutumin ba da bai San daraja mata ba naji dadi da kika gane akwai Wanda nake kulawa akwai Wanda nake balain So da ya dace dani da ko duk duniyar nan zata had'u wlh bazan rabu dashi ba dan haka Mommy karki fara gigin maidani gidan Ameer matsawar ba takardar sakina zaki k'arbo min ba na samu freedom d'in da nakeso amma idan kika nace akan na koma wlh ke zaki ji kunya babu ruwana idan kinasan Ameer d'in haka ki haifo wata mana ki bashi ko ke ki rabu da daddy ki aure shi haka kawai Dan kina zaman kunci a gidan Daddy kin fisan kowa yaje yayi zaman kunci ina bazai yiwu ba w..."


Mommy Hauwa da ji take kamar kirjinta zai Daka tsalle ya fito sabida irin bugu da raxanar da kalmomin da Zara keyi jikinta ya Ringa wani irin rawa wai yau 'yar cikinta ke gagayawa duk maganar daya fito daga bakinta akan kawai tana gaya mata gaskiya

k'asa cigaba tayi da jin abinda Zara ke cewa ta jawo 'yar yawo dake d'akin ta hau killar Zara dashi

Abunka da Wanda bai iya fushi ba da hannu da bulala tayiwa Zara jinajina bayan ta cire mata attach d'in kanta da hannu baki da hanci jini kawai ke tsiyaya

Zara na ihu da kuka itama mommy Hauwa nayi tana "kinsan kuwa ni na tsuguna na haifeki"

Kuka mommy ke yi sosai Sai da ta tabbatar Zara bata iya motsi kwata kwata ta d'agata ta koma gefe ta fashe da kuka tana "Allah kana kallo banyiwa iyayena abinda 'ya'yana suke min ba ya Allah ka bani ikon cinye wanan jarrabawa..


Tsayar da kukan da take yi tayi cak a lokacin da taji Zara na cewa " Allah ya isa ban yafe miki ba wlh nafisan daddy akanki kuma Sai na gaya mishi yazo ya rama min"....



😡takaici

[21/07, 03:25] Nabila maishanu Fbk Gusau Zamfara: *M🅰K'OT🅰N JUN🅰*


*REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS* *P.M.L*




® REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS

ɯɛ ɖơŋŧ ʝųŞŧ ɛŋŧɛřŧąıŋ ŋɖ ɛɖųĆąŧɛ, ცųŧ ɯɛ ąٳŞơ ŧơųĆɧ ɖ ɧɛąřŧ ơʄ řɛąɖɛřŞ


# WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
# IG PML WRITERS
# https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-08144932303




*Written by*

💅💅💅 *SADNAF*💅💅💅



*Follow me on wattpad @ Sadnaf*



*Wanan shafin na sadaukar dashi ga duka masoyana masu bibiyar novel d'in mak'otan juna ciki kuwa harda.ghost readers masu karancewa suki comment tnx for d support*


*Jiya naga ruwa ruwan comment inda kowa ke fad'ar albarkacin bakinsa inda wasu ke ganin karyane babu yanda za'ayi dan cikinka ya maka rashin kunya har ya kai ga yi maka Allah ya isa tab idan kuwa wayanda basu yarda ba su dage shige da fice zasu ga inda wasu iyayen ke k'ok'awa da yaran da suka Haifa wlh am a witness doki in doka uwa da 'ya kawai dai Addua zamu dage dashi akan Allah ya shiryamana zuria*


*page 11*


Wani irin dum dum kunnen Mommy Hauwa keyi mata taji kamar suma tayi na wucin gadi sakamakon d'aukewar da Numfashinta ke yi babu abinda ke yawo a kunnenta sama da "Allah ya isa"da Zara tace mata

Jikinta kuwa kamar wacce aka sakawa electric shock sabida k'ark'arwar da yake yi kallon Zara kawai take yi dake Jan duwawu ta nufi wajen da wayarta ke yashe ta d'auka still tana Jan Duwawu ta nufi hanyar waje sai kuka take tana Jan majina tana zuba mata harara


Mommy Hauwa k'ark'arwar da jikinta keyi ne yasa ta k'asa motsawa daga inda take wani irin dunkulellen abune ya toshe mata makogaro zuciyarta kuwa kamar an cinna mata wuta


Runtse idonta kawai ta yi tana tuno 'yar data raini a cikinta tsawon wata Tara bacci Mara dadi tashi da mik'ewa sai da dabara wani zubin abinci bazai ciwu ba sabida amai

Ta kwana biyu a asibiti tana nakuda dan halin da take ciki har tana iya jiyo k'amshin lahira tazo ta haihu dak'yar Raino da wahala wani zubin bata isa tayi bacci ba sabida rigima haka zata tashi zaune rarrashi kashi fitsari itace duk wanan wahalar da ta sha a yau itace Wanan 'ya zata yiwa Allah ya isa banda zaginta da tayi

Duk bak'ar wahala da take sha da wulak'anci iri irin da Dr yake mata tun aurensu tana shanyewa ne kawai sabida 'ya'yanta tana gudun ta bar gidan ya Auro wata tazo taci zallin 'ya'yanta amma sai gashi wai akan fad'awa 'yarta gaskiya tace mata Allah ya isa tafisan mahaifinta akanta"


Zuwa wanan lokacin Mommy Hauwa wasu hawayen da kamar an kunna famfo ya fara zubo mata kanta sai juyawa yake

Bud'e idonta tayi da sauri a lokacin da aka b'anko k'ofar d'akin


Dr ne a tsaye sai huci yake Zara tana daga bayansa sai share Hawaye take tana girgiza jiki irin ta samo Wanda zai zo ya rama mata d'inan.


"Ke wacce irin Mahaukaciya ce zaki samu 'yar yarinya ki mata mugun duka har ya kai ki da ki tsitsige mata gashi ke uban waye ya dakeki da zaki mata irin wanan dukan uban mai ta miki haka"

Tunda Ya fara Magana Mommy Hauwa ta kama lebb'enta na k'asa ta dartsa hakoranta a ciki bata damu da lumewa da hakoranta sukayi ba jini ya fara zubowa dan da k'arfi ta danna hakoranta jikinta na wani irin k'ark'arwa tana kallon Dr da Zara dake tsaye


Dr kuwa ganin yanayin da take ciki yasa ya fara slow da fad'an da yake dan tunda ya Aureta bai tab'a ganinta a irin wanan halin ba


Mommy Hauwa kuwa d'aurewa tayi ta mik'e duk da jirin dake d'ibanta still tana cige da lebb'enta idonan nata jajawur kamar an diga jini ta nufi wajen da suke a tsaye

Zara gyara tsayuwarta tayi dan duk a tunaninta idan wani dukan zata k'ara mata Dr zai shigar mata

Dr kuma haka kawai wani d'an tsoro ya shige shi dan a dake ta taho wajensa babu wannan alamar tsoro da girmama shin da take a tattare da ita


Sai da ta tsaya agaban Dr tace Cikin wani irin murya numfashinta Na sama da k'asa "kazo ka rama mata ne"?


Dr wani yawu ya had'iye ya k'asa magana dan ya hango wani k'wantacen bak'inciki da tafasar zuciya a idon Mommy Hauwa

" Karka damu ka dakeni dama tace min zata kiraka ka rama dukan dana mata ka rama mata ka tafi"

Tace tana k'ara matsawa kusa da Dr.


For the first time Dr yaji jikinsa yayi sanyi ya fara tunanin abinda yake yiwa Mommy Hauwa bai dace ba ko ayanayin da ya ganta kawai yanzu yasa yaji jikinsa ya k'ara sanyi dan gwara ta ware murya tayi ta ihu zata ji sa'eda a ranta akan shirun nan da tayi bak'inciki na cinyeta


Mommy Hauwa ganin Dr ya zura mata ido ya k'asa magana ne yasa ta Juya ta kalli Zara dake girgije girgije tana jin Haushin Dr na k'in dukan Mommy Hauwa tun dazu.

"Daddynki ya k'asa rama miki Zara kizo ki rama dukan Dana miki da kanki ki matso ki rama dukan Dana miki Zara"

Zuwa wanan lokacin wanan dunkulellen abun dake makogaron Mommy Hauwa ya narke take Hawaye suka ya hau bulbulowa yana diga a k'asa

Zara harare harare ta cigaba da yi a lokacin da Mommy Hauwa ke kallonta ko ina na jikinta na rawa

Gaban zaran taje ta tsaya ta cakumo wuyar rigarta tana

"Zara ki dakeni nace nasan bani na haifeki ba Zara Zara mai kike jira tunda zu ki rufeni da duka nace Zara wai akan ina gaya miki gaskiya kike min Allah ya isa Zara ni Dana tsugunna na haifeki kikewa Allah ya isa Zara duka ya rage kawai kiyimin ki dakeni nace"

Mommy Hauwa tace Cikin wani irin yanayi tana girgizata


Dr jikinsa ne yayi sanyi a lokacin da yaga Mommy Hauwa ta zube agaban Zara tana ta kuka kamar ranta zai fita

D'aurewa yayi yace "wai mai yake faruwane Zara mai kika mata haka"?

Zara k'asa magana tayi sai girgije girgije take yi

"Ba tambayarki nake ba kika min shiru dan ubanki mai kika mata haka take kuka"?

Dr yace a tsawace

" Allah ya isa tayimin Dr dan ina mata nasiha akan ta koma gidanta Zagina tayi tace ta tsaneni tafi sanka akaina Dr 'yar dana tsugunna na Haifa ce yau take min Allah ya isa akan ina k'ok'arin ceto ta daga halaka ina nusar da ita hanyar daka d'orata akai ba hanya bace mai kyau domin Goya mata baya da kayi yasa take kula wani da Aurenta"


Dr ware ido yayi yana kallon Zaran da take ta zubawa Mommy Hauwa harara tunda ta fara magana


"Zaraaaa dagaske mahaifiyarki take kula wani kike da Aurenki? kina da hankali kuwa da Auren naki kike huld'a da wani namijin"?


Zara tsoro ne ya d'an shigeta ta fara ja da baya dan Dr bai tab'a mata ko da kallon banza ba ballantana akai ga tsawa.


Dr jawota yayi ya fara dukanta yana " dan bakida mutunci mahaifiyarki kike yiwa Allah ya isa dan tana gaya miki gaskiya.


Zara ihu kawai take suna guje guje dashi tana ganin ta nufi hanyar fita daga d'akin ta juyo tana "Allah isa ban yafe maka ba bak'in mugu azzalumi wlh sai na bar muku gidan kai da Mommy bana sanku.

Tunda ta Zara ta fara magana Dr yaji kamar guduma take kwad'a masa kirjinsa kuwa sai dukan goma goma yake kunnensa kawai repeating d'in kalmomin Zara yake kansa na i wani irin juyawa.


K'afafunsa gaza d'aukarsa sukayi har sai da ya kai shi ga zubewa a k'asa zuciyarsa na wani irin harbawa.


Mommy Hauwa itama ta tuni kukanta ya tsaya cak dan bata tab'a tunanin Zara zata iya furtawa mahaifinta haka ba shi da baya San laifinta yake Goya mata baya a duk abinda tayi.




Dr ta kalla da jikinsa ke wani irin rawa gumi na keto masa idanan nasa jawur kamar garwashi.

Babu abinda yake furtawa sai
"Innalillahi wa inna ialhi rajiun" dan ko a mafarki bai tab'a tunanin 'yar daya Haifa zata iya zaginsa ba.


Hawaye ne suka hau zubo masa yana girgiza kai wanan shine karo na farko da tsananin nadama ya rufesa sai ayanzu ya gano illar freedom d'in da ya bawa 'ya'yansa suke abinda suke so baya San ganin laifinsu ko kad'an

Mommy Hauwa kuwa girgiza kai tayi Cikin takaici Cikin raunaniyar murya tace

"Dr kaga irin tarbiyyar da kayiwa 'ya'yanka ko?ka ga sakamakon irin sangarta da gatan da kake cewa kana yiwa 'ya'yanka ko? Dr kaga yau Zara 'yar gwal da baka san a tab'a ko afadi laifinta itace ta bud'e baki ta maka Allah ya isa tace maka Bak'in azzalumi mugu dama nasha gaya maka akwai lokacin da zaka zo kayi dana sanin sangarta yaran nan da kayi nasha gaya maka hanyar daka d'ora yaranan ba hanya bace mai kyau yau ga 'yar cikinmu Na mana Allah ya isa bata yafe ba"


Dr girgiza kansa kawai yake maganar Zara na masa amsaa kuwaa a kunne kamar a yanzu Mahaifiyarsa ke cewa yaje zai gani shima 'ya'yansa sai sun sa shi kuka tunda ya zabi 'yan mata akanta tunda ya zabi ya kashewa 'yan mata kudi akan ya bata naira biyar taci abinci bayan irin abubuwan da tayi dan kawai ya kai matakin da yake kai yanzu amma sai gashi amadadin ya kula da ita a lokacin da bata da k'arfi take bukatar taimakonsa a lokacin zai juya mata baya ya ringa yawo da yan mata a gari yana kashe musu kudi.


Wani irin kuka ya fashe dashi daya tuno abinda Mahaifiyarsa tace gashi is too late ballantana ya nemi yafiyarta


Mommy Hauwa kawai kallonsa take tana mamakin abinda ya sa shi kuka haka to mai abun kuka ai bai kamata yayi kuka ba tunda shine silar lalacewar su.


Dr mik'ewa yayi dak'yar yana Jan k'afa tare da barin d'akin dan shi kadai yasan abinda yake ji.


Zara kuwa dama tana barin d'akin a guje ta fad'a d'akinsu Sadiq ta kulle da mukulli sai kuka take tana kiran wayar Adnan dan bata so gari ya waye tana Cikin gidanan gwara yazo ya d'auketa


Khalid da tunda ta shigo yake tambayarta abinda ya faru dan duk dramar nan da akayi bacci yake.

Ko kula shi bata yi ba ta cigaba da gwada wayar Adnan a kashe.


Dr kuwa bai iya k'arasawa d'akinsa ba ya zube akan kujerar Palo take wani irin zazzabi ya rufe shi.


A takaice sai da Mommy Hauwa ta tsaya akansa sabida mugun zazzabin da ya kama shi duk magungunan da ta bashi yak'i ya k'arba ya sha sai Hawaye yake yana kiran sunan mahaifiyarsa akan ta yafe masa hakkinta ya fara kama shi.



B'angaren Aliya kuwa tana iddar da sallar asuba bata koma bacci ba sai da tayi breakfast ta d'an gyara gidan ta koma d'aki dan Sam bata San had'uwa da Adnan.


Adnan bacci yayi cike da fargaba dan bai San halin da Zara take ciki ba shima tunda yayi sallar asuba ya kasa komawa bacci yana San ya kunna wayarsa yana tsoro.


Ameer kuwa shima da ya iddar da Sallah bai koma bacci ba sabida dattin da gidan yayi

Gyare gyare ya fara yi dan ya tsani k'azanta a rayuwarsa duk da Zara tana da San jiki baya wani saurararta zagewa yake ya gyara ko'ina ya feshe shi da turare girki ne kawai bai iya ba.


Zara kuwa ko sau d'aya bacci bai d'auketa ba dan tsananin tashin hankali da fargaba da take ciki ta lek'a Palo ya kai sau goma dan taga ko Dr da dake rawar d'ari da Mommy Hauwa dake gefensa na mishi sannu sun tashi sun bar Palon amma ina suna nan a palon.

Burinta bai wuce ta bar gidan ba dan bazata sake tsayawa a tab'a lafiyarta ba tunda Dr shima yanzu ya fara dukanta ga zagin da ta mishi har gwara ma ta koma gidan Ameer ta samawa kanta mafita akan ta cigaba da zaman gidan.


A lokacin da khaleed yazo fita massallaci a guje ta nufi band'aki ta kulle dan tana tsoron su biyota su daketa.


Dr kuwa da k'yar yayi sallar asuba kansa kamar ya dare biyu kirjinsa wani irin nauyi yayi masa yana so yayiwa Mommy Hauwa magana amma ya k'asa sabida nauyin da harshensa ya masa.

Mommy Hauwa kuwa kuka kawai take data ga Halin da Dr ke ciki dan bata tab'a tunanin dan Zara ta masa haka zai shiga irin wanan tashin hankalin ba sadiq da Abdulsalam dake shaye shaye suna biye biyen 'yan mata bai damu ba ballantana ya d'aga hankalinsa Sai gashi akan Zara ya tashi hankalinsa ko dan acikin 'ya'yansa yafi Santa ne oho.


Har k'arfe takwas na Safe Dr na kwance baya iya motsi sai Hawaye dake fita ta gefen idonsa

Mommy Hauwa kuwa Sai Sannu take mishi


Mik'ewa yayi a hankali ya zauna Mommy Hauwa tayi sauri ta taimaka mishi


Bud'e bakinsa yayi da k'yar yace "ina Zara"?

Mommy Hauwa Sai da ta share hawayenta tace " tana d'akinsu Sadiq"

Bai ce komai ba ya mik'e yana cije lebb'e sabida nauyin da kansa ya masa


D'akinsu Sadeeq d'in ya nufa yana Jan k'afa

Mommy Hauwa tayi sauri ta sha gabansa ta fara basa hakuri akan ya rabu da ita taje duniya ce itama zata Haifa ai

Dr ko kulata bai yi ba

Please Login or Register in order to submit comment