Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

nufi wajensu tana kuka.

Wanda hakan ya karyarwa Mommy Hauwa zuciya Dr kuwa ya hau share hawaye dan duk a tunaninsu Zara ta mutu.


Cikin kuka Aunty Khadija ta kwashe duk abinda ya faru ta gaya musu inda Dr na k'ok'arin magana Likitan dake duba Zara yafito daga d'akin da aka kwantar da Zara yana yarfa gumi.


Da saurinsu suka tare shi dukansu suna tambayarsa Ya Zaran ta farka ko dai ta mutu.

Likitan bai ce musu komai ba yace Dr ya biyo bayansa.


Da sauri Dr yabi bayansa su Mommy Hauwa kuwa suka kara tsurewa.

Suna shiga cikin office d'in Likitan ya gyara zamansa akan kujera yafara Gayawa Dr Halin da Zara take ciki na tsananin damuwa da tunani a matsayinta na mai ciki hakan bai dace da ita ba idan ba so suke su rasa ta ga gabad'aya ko abun dake cikin ta Anan yace su ringa kwantarwa da Zara hankali su daina barin ta cikin damuwa har ta samu ta haifi abinda ke cikinta dan da k'yar suka samu numfashinta ya dawo dai dai.


Dr kad'a kansa kawai yake yana yiwa likitan godiya inda likitan yayi rubuce rubucen magunguna har Dana Karin jini sabida Zara bata da wadatacen jini a jikinta.


Dr da sauri ya k'arba yayi waje inda yaga su Mommy Hauwa sunyi cirko cirko a bakin k'ofar suna jiran fitowarsa.

Hakane yasa ya tsaya ya fara gaya musu yanda sukayi da likitan sanan ya wuce dan ya amso magungunan.

Sai a lokacin hankalin mommy Hauwa ya kwanta inda can k'asan zuciyarta ta ringa godewa Allah da Dr ya sauko daga dokin fushin da yake yi da Zara dan har ya fita shiga tashin hankali.


Ahaka suka zauna suna zaman jiran Zara ta farka inda Aunty Khadija ta koma gida ita da Khalid tayi girkuna kala kala Wanda Duk abincin da tayi Wanda zai Karawa Zara jinine.

K'arfe hud'u da rabi Zara ta bud'e Idonta a hankali tana cije lebb'e sabida nauyin da kanta yayi mata.

A hankali ta fara wurga idonta tana san sanin inda take da kuma mutanen dake zagaye da ita.

Akan Dr ta fara sauke idonta inda ta kura mishi ido tana kallonsa dan duk a tunanin ta mafarki take yi sai data kara rufe idonta ta bud'e ta gasgata ba mafarki take ba daga nan ta maida idonta kan Mommy Hauwa dake gefensa hawaye ne ya hau zubo mata ta bud'e bakinta daya mata nauyi tana "Daddy dan Allah ka yafemin wlh sharrin shaidan ne bazan sake ba idan kuka koreni bansan inda zani ba tunda Ku kadai gareni banida sama daku Nayi nadamar abinda na aikata.

Dr da sauri ya rik'o hannunta yana " Ki bar kukan haka Fateema na yafe miki Allah ma muna mishi laifi mu nemi yafiyarsa ya yafe mana ballantana mu ki bar kukan haka karki jawo kanki wani matsalar kinji mamana"

Zara da sauri ta girgiza kanta ta kalli Mommy Hauwa tana k'ok'arin magana Mommy Hauwa ta dakatar da ita tace "Karki kara magana Zara duk mun yafe miki ki kwantar da hankalinki kinji"

Zara murmushi tayi wani irin farinciki da nutsuwa na shigarta Wanda rabonta da ta tsinci kanta a irin wanan farincikin har ta manta sakayau take jinta sabanin da da take jinta da nauyi yanzu yafiyar Ameer ya rage ta nema daga nan tazo ta dasa sabuwar rayuwa indan Allah ya bata dama.


Wani irin kulawa suka ringa mata kama daga Dr Mommy Hauwa har da yayyenta Wanda take ganin kamar a mafarki iyayen nata ke kula da ita batasan iyaye rahama bane sai a Yanzu da take kwance a gadon asibiti dan tuni dangi suka cika asibitin inda kowa ke iya k'ok'arin sa dan ya kula da ita lura da cikin dake jikinta.

Inda mommy Hauwa da Aunty Khadija suka rufe sirrin cikin da Zara ke d'auke dashi suka ringa fad'awa mutane da ciki Ameer ya saki Zara inda dangi ke ta ganin rashin kyautatawa da Ameer ya musu.


Kwananta uku a asibiti aka sallameta ta koma gida.

Inda Mommy Hauwa ta dage ta ringa kula da Zara acikin sati d'aya Zara tabi ta canja ta murmure nan da nan haskenta yafara dawowa bata da aikin daya wuce ta kwanta tayi bacci dai dai da ruwan wanka kai mata akeyi sallah kawai ke tashinta inda Mommy ta dage ta fara koya mata littatafan addini tana gyara mata duk inda ta kuskure a sallarta dan Zara k'arfi da yaji take so ta gyara hallayenta ta samu ta nemi yafiyar Allah tun tana da sauran lokaci duk dare sai tayi kuka idan Mommy Hauwa tana mata wa'azi ji take inama ace duk rayuwar da tayi abaya mafarki ne babu abinda ke d'aga mata hankali kamar idan ta tuna irin abubuwan da ta aikata da sakamakon Wanda ya aikata irin abinda tayi bata da burin da ya wuce Ameer ya yafe mata ko ta danji saukin tashin hankalin da take ciki haka ma tana bukatar ta nemi yafiyar Aliya Amma Mommy Hauwa ta ce ta bari ta haihu tukunna sai ta nemi yafiyar su duk da ta tsani Adnan ko mai irin sunan shi bata so taji hakan bai sa ta fasa mishi sha'awar ya shiryu ya gane gaskiya tamkar yanda Allah yabata ikon gane abubuwan da ta ringa aikatawa tana nadamarsu duk wankan da take ji take wari take ji yana tasowa daga jikinta sabida dattin zinar dake makale a jikinta.



Ko bacci take bakinta na d'auke da istigifari sosai take nadamar abubuwan da ta aikata.


B'angaren Aliya kuwa kamar yanda Ameer yace ta fad'a a gida akan Asabar zai turo da magabatansa hakan kuwa akayi inda Ameer ya balain basu mamaki dan a shiryensu suka je Neman Auren Aliya ba iya kudi suka kai ba har dasu kayan sa rana da lefe.

Inda ya kashe 'yan uwan Aliya da mamaki dan kaya ya mata na fitar hankali kamar ba bazawara ba k'aramin kudi ya kashe wajen had'a lefen ba duk Wanda yazo Sam barka kawai yake yana rik'e baki dan Ko kayan kanwar Aliya dake buduruwa bai kamo k'afar na Aliya ba mutane kuwa cewa suke Allah ne ya saka mata abinda Adnan ya mata ya musanya mata da Ameer.

Aliya kuwa jikinta ne yayi sanyi data ga uban kayan da ya had'a mata ta ringa jinjina irin san da Ameer yake mata inda ta ringa godewa Allah daya bata miji irin Ameer take kuma adduar Allah ya bata ikon yi masa biyayya.


Sati hud'u aka sa bikin Aliya da Ameer Inda yayi dai-dai Dana kanwarta aka hau yi musu shiri iri d'aya dan tamkar sabon aure Aliya zata yi dan komai da ita ake siya bambancin kawai gyaran da ake mata ya bambanta Dana kanwarta dan na musamman ake mata wani irin san Ameer ne yake hauhawa a zuciyarta sabida Ameer is very caring kullum cikin waya suke da text idan kuwa yazo kamar ba zai tafi ba tsaftaciyar soyayya suke gudanarwa inda ilimi ya tada ilimi komai nasu a tsare.


B'angaren ango Adnan kuwa 🤣🤣



A cikin masifaffan tashin hankali yake yabi yayi wani irin rama sabida rashin kwanciyar hankali idonsa duk yabi ya shige ciki tun yana kuka a bayyane har ya koma yana yin na zuci dan Ajjidde da kawayenta sako shi sukayi agaba suka maidashi sex machine k'arfi da yaji suka ringa tula mishi kwaya yana sha ahaka zasu jeru kamar dabobbi babu kunya babu tsoron Allah yaringa binsu d'aya bayan d'aya yana kuka gabansa duk yabi ya d'aye ya koma jawur ko wando baya iya sawa yanzu sabida tsananin azabar da yake sha yasha yunkurin guduwa Ajjidde nasawa a capko shi har shaketa yayi ya gwada yi mata duka daya rage daga shi sai ita a d'aki amma ta kira a waya aka zo aka masa dan banzan duka ko tausayin shi bata ji ba haka ta ringa haike masa da sunan punishment d'insa kenan.


Sai da sukayi sati ahaka Kafin ta fara d'aga mishi k'afa kawayenta ma haka inda ta b'ullo mishi da sabon salo ta maidashi house boy d'in ta k'arfi da yaji.

Shi yake wanke mata panties d'in ta da undies dinta har Dana kattin dake zuwa tayata kwana haka zata sa shi ya wanke musu gajerun wandunansu wani zubin harda guga a fad'arta tunda bai iya komai ba ragone gwara ya koyi yanda ake wanki wani sa'in idan rashin mutuncinta ya tashi haka zata ce ya tsaya a d'akinta yaga yanda ake harka dan bai iya komai ba agaban idonsa zata yi ta aikata masha'arta har sai sun gama zata ce yafitar mata daga d'aki.

Idan yaga yanda Ajjidde ke wulakanta shi tana sa shi aiki Aliya 'yar Aljanna yake tunawa Aliyar da bata san b'acin ransa Aliyar dake masa biyayya Aliyan da yana cire kaya take wankewa Aliyar da zai b'ata mata rai amma ita zata dawo ta bashi hakuri wai sai gashi wai yau mace ke juyashi tana mishi abinda ranta ke so.

Adnan idan yayi irin wannan tunanin yakan ci kuka ya gode Allah kullum bashida tunanin daya wuce yanda zai bar gidan bai tab'a mugun dana sanin rabuwa da Aliya ba sai a 'yan kwanakin nan daya shiga hannun Ajjidde bai tab'a nadamar abubuwan daya aikata ba sai da Ajjidde ta koya masa hankali take Zara ta fad'o masa inda ya gano dalilin dayasa Ya shiga ukuba da bala'i irin wannan yaci amanar aure yaci amanar matarsa yaci amanar mak'ocinsa ya za'ayi Allah bazai jarrabce shi ba Allah ya jarrabce shi da abinda yafi sab'a masa dashi dan har yanzu baya iya saka gajeran wando sabida tunda su Ajjidde suka sako shi agaba ya daina jinsa dai-dai adduarsa kullum bai wuce Allah yasa basu saka mishi cuta ba yanda yake jinsa ko nan da shekara Ashirin bazai tab'a iya marmarin mace ba ballantana har ya kai ga yayi Tunanin saduwa da mace.


Tuni ya koma ga Allah shima idan ya samu sarari yayi ta sallah yana Neman yafiyar Allah dan yasan Allah ne ya damkeshi abubuwan da ya aikata ne suke bibiyar shi duk dare cikin Nafilfili yake duk da bai yi zurfi a ilimin addini ba d'an surorin da ya sani yake karantawa.

Addua kawai yake Allah ya kawo masa d'auki ya kawo ranar da zai bar gidan.


Ahaka rayuwa ta ringa tafiya Ajjidde abinda zata mishi yau daban na gobe daban bata yarda ko waje ya fita ba aikin wanke panties da undies kawai take bashi duk ranar data rayya mata kuwa Idan kwaratan ta basu zo ba ta kira shi har d'aki ta dura mishi magani yasha suyi ta abu d'aya duk ranar kuwa da ya k'i sai ta kira boys dinta su mishi dan banzan duka ko kuma ta kira kawayenta tace su zo su jona mishi chaji bai iya komai ba.


Adnan zuwa yanzu ya barwa Allah komai Dan sai yanda Ajjidde tayi dashi idan kaga Adnan baka isa ka gane shi ba sabida rama da rashin kwanciyar hankali kullum hannunsa na rik'e da carbi yana Jan istigifari dan mutuwa kawai yake rok'a yazo ya d'auke akan irin rayuwar da yake yi a gidan Ajjidde.


Ahaka ya samu wata d'aya a gidan Ajjidde inda aranar daya cika wata d'aya daddare Ajjidde tazo har d'akinsa ta nuna mishi k'ofa tace ya fitar mata daga gida ta gaji da ganin shi.


Adnan Ji yake kamar ya mata sujada dan farinciki har k'asa ya durkusa ya ringa mata godiya Ajjidde kuwa ko takansa bata bi ba tabar d'akin Adnan kuwa bai tsaya d'aukar komai ba yayi waje da gudu dan karta dawo ta ce ta canja ra'ayinta.


Maigadi bai hana shi fita ba dan anyi mishi umarnin ya bar shi ya fita.


Adnan lumshe ido yayi hawaye suka hau tsere a kumatunsa daya shak'i iska mai tattare da niima wai yau shi yasamu 'yancin kansa.


Bai tsaya b'ata lokaci ba ya fara tafiya da sauri da sauri duk da bashida masaniyar inda zashi amma ko ina zaije yasan sai yafiye masa gidan Ajjidde bala'i.


Sabida farincikin da yake ciki da k'afa yaje gidan Safwan abokinsa ko Nisan shi bai gani ba.


Safwan a lokacin daya yayi tozali da Adnan ba karamin tashi hankalinsa yayi ba ya ringa zuba sallati dan sai da yayi dagaske ya gane Adnan sabida gabad'aya kamar bashi ba.


Adnan kuwa murmushi yayi bai ce masa komai ba ya nufi band'akin gidan yaje ya fara durza jikinsa sabida warin dayaji yana yi sai daya kusa d'aye fatarsa ya fito daga wankan bayan ya d'aura alwala ya fito.


A Palo ya tarar da safwan ya buga uban tagumi yana mamakin yanda yaga Adnan.

Safwan hankalinsa a tashe ya ringa tambayarsa abinda ya same shi dan gani yake kamar Leda Adnan ya ciyo.


Adnan kuwa bai iya ce mishi komai ba in banda Sallaya daya shimfid'a yafara jera salloli yana godewa Allah daya bashi ikon fitowa daga prison.


Sai da ya kwashi kyakyawan awa biyu kafin ya d'aga hannu ya ringa jera adduoi na Neman yafiyar Allah Sanan ya shafa.

Ya kalli Safwan daya matsu ya iddar ya gaya mishi abinda ke faruwa.

Adnan a nutse hawaye na zubo mishi ya fara bawa Safwan labarin duk abinda ya faru dashi babu abinda ya b'oye mishi.


Safwan tsabar mamaki k'asa bud'e baki yayi ya magana gumi kawai ke tsatsafo masa dan bada shi abun ya faru ba amma ya girgiza da jin irin shaidancin Ajjidde tunda yake yawo a bariki bai tab'a jin irin wannan tashin hankalin ba.


Adnab ganin Safwan ya kasa magana yasa yace "Safwan nayi nadamar abubuwan Dana aikata na Dade ina sabawa Mahallicina na biyewa san zuciyata na d'auka mata ababan nishadi da nutsuwa ne na d'auka Neman matan da nake zai sa na ringa jin dadin rayuwa ta Ashe masifa nake janyowa kaina Safwan dak'yar idan Ajjidde da kawayenta basu kashe min gabana ba yau wane riba naci babu na rasa salihar mace mace tagari da kowane namiji zai yi burin Samu na rasa aikina na rasa komai nawa Zina bai amfana min da komai ba sai asara bazaka gane irin abinda nakeji araina ba naga rayuwa safwan duniya ta koya min hankali zanyi amfani da d'an sauran lokacin da nake dashi na nemi yafiyar wayanda na ha'inta na nemi yafiyar Allah Safwan kaima kana da damar da zaka ajiye abinda kake yi yanzu ka nemi yafiyar Allah tun baka tsinci kanka a irin halin Dana tsinci kaina ba"


Adnan kuka yake sosai Safwan na taya shi inda tsoron Allah ya ringa hud'a kowane sashe na jikinsu aranar Sam Adnan bai runtsa ba burinsa gari ya waye yaje ya nemi Ameer da Aliya ya nemi yafiyar su dan wani iri yake ji a jikinsa gani yake mutuwa zata iya daukarsa kafin gari ya waye.


B'angaren Zara kuwa a yau tana zaune tun dare take jin wani irin ciwon Mara a hankali kuma sai ya daina a yanzu da take zaune ji tayi ciwon maran ya had'e mata da bayanta Mararta yayi wani irin rik'ewa sallati ta kwala da k'arfi tana kiran Sunan Mommy Hauwa dake kitchen tana girki.

Aguje Mommy Hauwa ta fito dama tunda Zara ta shiga watan haihuwarta hankalinta yake a tashe cikin tsananin tashin hankali ta fara kwalawa Khalid kira dan Dr baya nan.

Inda Khalid ya fito daga d'akinsa da gudu.

Basu wani tsaya b'ata lokaci ba suka kinkimi Zara suka d'auki hanyar asibiti Zara kuwa sallati kawai take tana Neman yafiyar Mommy Hauwa akan mutuwa zatayi dan tunda take bata tab'a jin irin wannan azabar da take sha ba Mommy Hauwa kuwa kuka kawai take har aka shiga da Zara d'akin haihuwa dan dak'yar aka banbare hannunta daga rukon data mata addua kawai take Akan Allah ya raba Zara da cikin jikinta lafiya .


B'angaren Aliya kuwa A yau ake kamunsu inda Amare biyun ke wani irin kyalli sabida gyaran da suka sha Aliya kuwa wani irin kamshi jikinta ke fitarwa cike da annashuwa aka yi kamu cikin kayatarwa inda aka rufe da wa'azi.

K'arfe taran dare Aliya na kwance idonta a lumshe sabida mugun gajiyar da tayi.

Wayarta dake ringing ne yasa ta bud'e idonta inda ta saki murmushi sakamakon ganin mai kiran nata wato angonta Ameer.

A shagwabe ta d'aga wayar tana turo baki kamar yana gabanta Ameer kuwa yace mata yana waje yana jiranta.

Aliya sai da tayi kunkuni irin rawar kafar da Ameer yake yi akanta kamar bai tab'a aure ba babu yanda batayi ba akan ya hakura kar yazo yau ya bari sai an kawota yak'i.

Doguwar rigarta kawai ta saka da mayafinsa ta fita waje tana turo baki.....


Alhamdulillahi am almost there...💃💃💃💃

*M🅰K'OT🅰N JUN🅰*


*REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS* *P.M.L*




® REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS

ɯɛ ɖơŋŧ ʝųŞŧ ɛŋŧɛřŧąıŋ ŋɖ ɛɖųĆąŧɛ, ცųŧ ɯɛ ąٳŞơ ŧơųĆɧ ɖ ɧɛąřŧ ơʄ řɛąɖɛřŞ


# WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
# IG PML WRITERS
# https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-




*Written by*

💅💅💅 *SADNAF*💅💅💅



*Follow me on wattpad @ Sadnaf*

*Page 36*


Tun daga nesa Ameer ya kura mata ido dan tunda yake da ita bai tab'a ganinta ba dogon Hijabi ba sai yau duk da doguwar rigarta ba matsatsiya bace yana hango baiwar kyau da diri da Allah ya mata.


Aliya kuwa kanta a sunkuye ta k'arasa wajen Ameer Tana d'an murmushi yau wani sabon kunyarsa take ji sabida tunda ta fito ta lura da irin kallon da yake mata sabida akwai wadatacen haske a tsakar gidan nasu tasan kallon nasa na ya ganta ba Hijabi ne dan bai tab'a ganinta ba Hijabi ba kara sunkuyar da kanta tayi tana wasa da yatsun hannunta daya sha bak'i da Jan lalle


Ameer kuwa da k'yar ya amsa sallamar da tayi mishi yana sauke ajiyar zuciya tare da godewa Allah daya Mallaka mishi Aliya dan ba ikonsa ko dabarar sa bace Allah ne yayi ikonsa ya bashi ita.

Lumshe ido yayi yana shak'ar kamshin dake fitowa daga jikinta.


Sai da suka kwashi minti biyar ahaka kafin Ameer yace "Amaryata kinsha kyau kyaun ma har zuba yake dan wlh na ma kasa fassalta miki irin kyaun da kikayi"


Aliya murmushi tayi ta cigaba da wasa da yatsunta.

Ameer kuwa yayi murmushi dan Kunyar Aliya na bala'in burgeshi kamar wacce bata tab'a aure ba.

Hira ya ringa Jan Aliya dashi sosai amma Aliya kuwa ta kasa sakin jiki dashi ya lura kamar a takure take sabida mayafin data fito dashi ya matsu Jibi yayi a d'aura musu aure ya cire mata wanan kunyar da take ji.

Akan dole yayi mata sallama ya tafi dan idan yana tare da Aliya har wani irin nutsuwa da nishadi ke shigarsa a kasan zuciyarsa kuma yana jinjina irin rashin rabon Adnan dan Mara rabone zai k'asa gane baiwar da Allah ya mishi ta Mallakar Aliya.


Mommy Hauwa zagaye asibitin kawai take inda ta ringa sharar kwalla Dr shima tuni ya iso asibitin hankali a tashe haka ma duka yayyen Zara da Khaleed har da Aunty Khadija addua kawai suke akan Allah ya sauke Zara Lafiya dan kusan awa hud'u kenan da aka shiga da ita banda ihun sallatin da take yi babu abinda suke jiyowa.


Dr kuwa Massallacin dake cikin asibitin ya je ya ringa jera nafilolli dan baisan meyesa gabansa ke ta fad'uwa ba.


Har akayi sallar isha Zara bata haihu ba dan ansama ta ruwan nakuda har guda biyu ya kare amma bata haihu ba.


Zuwa wannan Lokacin Mommy Hauwa wani irin zazzabi Zazzabi ne ya ringa shigarta dan haka kawai taji gabanta na mummunan fad'uwa zuciyarta na mata wani iri.


Aunty Khadija ce kawai take da k'arfin halin kwantar mata da hankali.


Zara kuwa bazata iya misalta irin Azabar da take sha ba tunda take arayuwarta bata tab'a jin irin wanan ciwon ba bayanta kamar Sara mata ake haka ma mararta sallati kawai takeyi tsoron Allahn daya Halliceta na shigarta Babu abinda take tunani sai Mommy Hauwa da tayiwa rashin kunya yanzu irin wanan azabar uwa take sha awajen haihuwa yanzu duk Laulayin nan da tayi Ashe nafila ce akan nakuda sunan Allah kawai take iya kira idan azaba yayi azaba ma bata iya kiran sunan Allah a fili sai dai a zuciya.

Likitan dake kan Zara ganin har ruwan nakuda leda biyu ya kare a jikin Zara banda kwayoyin dake tunzura jariri ya fito duk tasha babu alamar haihuwa sai ma bak'ar wahalar da take sha yasa ya fito ya samu Dr yace mishi sai dai ayiwa Zara operation dan Sam bazata iya haihuwa da kanta ba duk da ga kan baby yana hangowa.


Gaban Mommy Hauwa wani irin yankewa yayi ya fad'i haka ma Dr da suka ji abinda likitan yace take Mommy Hauwa ta tuna yayarta data mutu agarin operation.

Mommy Hauwa da sauri tafara girgiza kanta tana "aaa likita ba sai anyi mata operation ba insha Allahu zata haihu da kanta ka bata nan da anjima da izinin Allah zata haihu da kanta"

Likitan da ya riga ya lura tunda ya ambaci operation hankalin Mommy Hauwa ya tashi murmushi yayi yace "Hajiya ki kwantar da hankalinki insha Allahu za'a Ciro mata abinda ke cikinta successfully batare da an samu wata matsala ba tariga da tayi weak da yawa bazata iya haihuwa da kanta ba sai dai a mata operation".

Mommy Hauwa da sauri ta kara girgiza kanta tace " Aa likita kar ayi mata operation insha Allahu zata haihu da kanta"

Dr kuwa kasa ma magana yayi in banda jikinsa dake rawa.

Likita ganin ya kad'a ya rayya akan su bari ayi mata operation sunki yasa ya rabu dasu yaje ya k'ara yiwa Zara 'yan dabaru ko zata iya haihuwa amma ina har k'arfe goma sha d'ayan dare Zara ta k'asa haihuwa sai bak'ar wuyan da take sha.


Mommy Hauwa kuwa sai kuka take Tana jera adduoi.


Nurse d'in dake kan Zara a lokacin da likitan yaje duba sauran patient din Zara ta yafito akan tazo.

Nurse d'in ta matsa da sauri taje saitin kunnenta dan Sam bata jin mai Zara take cewa da k'yar ta iya jiyo mai Zara take cewa

"Dan Allah ki kiramin Ummana kice tazo akwai maganar da zan mata"


Nurse bata tsaya wani b'ata lokaci ba ta fita waje ta samu su Mommy Hauwa tace Mahaifiyar Zara taje Tana san ganinta.


Tun kafin Nurse d'in ta rufe baki Mommy Hauwa tayi saurin nufar d'akin hankalinta a tashe.

Tana turo k'ofar d'akin gabanta ya yanke ya fad'i sabida wani irin dashewar da Zara tayi idonta yayi wani irin fari kamar wacce bata da jini.

Zara kuwa murmushin iya lebb'en baki tayi har Mommy Hauwa ta k'araso gadon da take kwance tana share hawaye.

Sai da ta gwada magana sau biyu muryarta bata fita kafin Tayi magana da iya k'arfinta wani irin azababben ciwo na taso mata.

"Mommy Allah ya saka miki da alheri Ashe haka kika sha wuya akanmu Mommy Dan Allah ki yafemin duk abinda nayi miki daga ranar da kika kawoni duniya har zuwa yanzu danake kwance akan gado Mommy yarinta da rashin Ilimi yasa bansan darajarki ba bansan ciwon ki ba hakika banida abinda zan biyaki dashi inama ina da dama Mommy da na miki biyayya na bauta miki har karshen rayuwata da na gyara kura kuraina da ban bari kin zubar da hawayenki ko sau d'aya akaina ba Mommy inaji ajikina Mutuwa Zanyi Mommy Dan Allah ki yafemin abubuwan da nayi miki"


Cikin matsanacin kukan fitar rai Mommy Hauwa ta rufewa Zara baki da hannunta tana girgiza mata kai tare da cewa "kul Zara bazaki mutu kibarni ba insha Allahu na Dade ina adduar K'ada Allah ya kawo ranar Da zan binne dan cikina dana Haifa sai dai ya binne ni Zara zaki haihu Lafiya zafin nakuda yasa kike ganin kamar mutuwa zakiyi babu abinda da kikayi min sai dai na roki wasu su yafe miki idan kinyi musu ba dai dai ba da izinin Allah zakiyi kyakyawar rayuwa nan gaba za'ayi koyi dake al umma zasu yi alfahari dake zan Goya y'ay'anki a bayana Zara zaki aurar da 'yarki tamkar Yanda na aurar dake dan Allah kibar fadin mutuwa zaki haihu Lafiya insha Allahu"


Zara cije lebb'e tayi cikin tsananin azabar da take sha tace "Ngd Mommy Allah ya biya ki da Gidan Aljanna Mommy Dan Allah ki taimaka min ki kira min Ameer in nemi yafiyarsa dan Allah Mommy ki kirashi kice kina nemansa idan ya yafemin hankalina zai kwanta kullum zuciyata nauyi take min idan na tuna bai yafemin ba Mommy ki kira shi yazo dan Allah"


"Zara

Please Login or Register in order to submit comment