Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

love and look at" yace yana nuna mata wandonsa


Aliya bata ce komai ba illa kau da kanta da tayi

Shi kuwa Adnan ya cigaba da janta da wasa ganin bai samu fuska yasa ya mik'e ya nufi band'aki dan yayi wanka


Aliya kuwa tunanin ta hau yi na abubuwan dake faruwa dan tasan Adnan mutum ne mai sha'awa kuma tana iya k'ok'arinta wajen ganin ta jawo hankalinsa gareta dai dai gwargwado tana kyautata masa kwaliyan nan ta nayi amma ba tasan mai yasa bata gabanshi idan dai dagasken yayi mafarki da ita mai yasa bazai neme ta a zahiri ba ko har ta gundure shi ne da can ba haka Adnan yake ba farko farkon Aurensu daga baya taga ya fara canja mata


Ahaka tayi zurfi a tunani har Adnan ya fito ya shirya cikin kananan Kaya ya fice daga d'akin karar rufe k'ofar d'akin ne ya dawo da ita daga duniyar tunanin data tafi


Mik'ewa tayi tafito daga d'akin taga Adnan har ya zauna awajen dining yana waya k'arasawa tayi tayi serving d'inshi itama ta zuba nata ta fara ci batare da ta jira shi ba


Shima yana gama wayar yafara ci batare da ya kalleta ba dan shi yama fisan haka idan tana share shi yafi sakin jiki ya tsula tsiyarsa


Babu abinda kake jin kararsa in banda karar cokula Aliya kuwa kanta a sunkuye suna dab da gama cin abincin Suka ji ana kwankwasa k'ofa kafin Aliya tayi wani yunkuri Har Adnan ya mik'e yace "don't worry let me check who is on the door"

Aliya kuwa abincinta ta cigaba da ci tana tunanin ko mai musu wanki ne dan jiya ta had'a mishi wankin Adnan


Adnan kuwa yana bud'e k'ofar yaga Zara a tsaye ta wani gantsaro kirji tana hamma sleeping dress ne ajikinta doguwar Riga har k'asa mai tsantsi yabi ya lafe ajikinta kana hango komai na jikinta duk da rigar ma mai dogon hannu ne ta saka wani hular net


Adnan wani irin yawu ya hadiya a lokacin dayabi kirjinta dake tsaye carko Carko a tsaye duk da bata kamo Aliya kirji ba


Ita kuwa Zara gaishe shi tayi tana k'ok'arin wucewa ta gefensa

Adai dai lokacin da Aliya ta taso tana so taga waye dan taga yanda Adnan ya kame awaje d'aya


Amir shima adai dai lokacin ya fito dan yatafi office dan ko d'akin Zara bai kalla ba dan mugun haushinta yake ji


Ai kamar cewa akayi ya juya ya kalli b'angaren Su Adnan ya hango Zara na k'ok'arin shigewa a rikice ya juya ya nufi wajen nasu ransa a mutuk'ar b'ace dan baisan rashin hankalin Zara ya kai tafito ahaka ba shi kuma Adnan na tsaye yana kare mata kallo


Da wani irin murya ya kwalla mata kira "Zaraaaa"


Adai dai lokacin da itama Aliya zuciya ya deb'eta ta kwashe Zara da mari sabida takaicin yanda tafito........
[21/07, 03:17] Nabila maishanu Fbk Gusau Zamfara: *M🅰K'OT🅰N JUN🅰*


*REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS* *P.M.L*



*Written by*

💅💅💅 *SADNAF*💅💅💅



*Follow me on wattpad @ Sadnaf*





*Page 3*



"Bansan dabbancinki da tumasancinki da rashin kamun kan naki ya kai ki fito tsirara kizo ki tsaya agaban namijin da ba muharraminki ba ko kishin kanki bakya yi"


Aliya tace tana huci Zara kuwa cikin tsananin mamaki take kallonta hannunta dafe da k'uncinta

Adnan kuwa da sauri ya matsa daga hanya daya hango yanda Ameer ke tahowa idon nan jajjur



Zara dake k'ok'arin magana wani irin finciko ta Ameer yayi daga bakin k'ofa yafara janta da k'asa tana ihu


Aliya kuwa wani irin kallo take bin Adnan da shi

Adnan kuwa dan k'arfin hali ya zabga mata harara ya fice dasauri

Sai daya had'a da gudu ya iya taddo Amir Dan har sun kusa Shiga b'angarensu still yana Jan Zara da k'asa a fusace Dan har gashin kanta ya damka

Shan gaban Ameer yayi da sauri yana " pls Ameer kayi hakuri karka daketa quiet alryt nasan tayi ba dai dai ba Dan Allah kayi hakuri karka hukunta ta acikin wanan halin zaka iya ji mata ciwo am"


"Enoughhhh" Ameer yace a tsawace jijjiyoyin kansa a tattashe idanan a rine ba Zara ba hatta Adnan sai daya tsorata abunka da mai hakuri bai iya fushi ba


"Kace zuwa kayi ka cigaba da kare mata kallo baka gaji da kallonta ba ko kunya bakaji ba ka tsaya kana karewa matar Aure kallo ban tab'a tunanin akuyancin naka zai kai har akan matata ba daga yau babu ruwanka da shiga sabgar data shafeni matata ce idan naga dama na kasheta babu abinda ya dameka"

Daga haka ya Cigaba da Jan Zara a k'asa ya shige tare da rufo k'ofarsa yana shiga ya zare belt d'insa yafara tapkawa Zara tana tsalla Ihu sai zagaye palon suke sai da ya mata lilis ya wurgar da belt d'in ya zube akan kujera yana sauke ajiyar zuciya wani irin tafasa zuciyarsa ke yi dan shi namijine mai balain kishi


Adnan kuwa tunda ya fara jiyo ihun Zara yaji kamar ya b'alle k'ofar ya shige sai da ya daina jin alamar ana bugunta ya nufi b'angarensa yana mai balain jin haushin Marin da Aliya tayiwa Zara



A Palo ya tarar da Aliya tana ta kai da kawowa sai share hawaye take


Adnan kuwa hakan da ya gani ne yasa yaja dogon tsaki ya nufi d'akinsa Dan ya d'auko brief case d'insa ya tafi


Aliya da sauri ta sha gabansa cikin rawar murya tace "Adnan abinda kayi kana ganin ka kyauta Kenan ka zubawa matar aure ido ko kiftawa bakayi saii"


Tsawan da Adnan ya daka mata ne yasa tayi sauri ta hadiye maganar da take yi


"Uban mai nayi an gaya miki kowa irin ki ne kidahuma shikenan Dan tana matar Aure sai na rufe idona ko zaki iya gaya min uban me tayi miki kika mareta sabida ta fito da sleeping dress an gaya miki ita irinki ce macece ita wayaya ba irinki ba ke kiyi ta fama da zani da atamfa kina kunshe kanki a hijabi kina wari"


Jikin Aliya in banda rawa babu abinda yake yi duk kalaman dake fitowa a bakinsa kamar narkakken dalma yake watsa mata hawaye kuwa sai ambaliya yake a kumatunta


Adnan tsaki yayi ya ratsa ta gefenta ya d'auko breifcase d'insa ya fice.

Aliya kuwa durk'ushe tayi a gurin tare da fashewa da matsanacin kuka tana rik'e zuciyarta sabida tsananin zafin da yake mata


Ameer kuwa sai da ya samu nutsuwa sosai ya d'ago da rinannun idonsa ya nufi wajen Zara dake sheme a k'asa tana kuka

Gashin kanta ya damko ta saki wani wahallalan ihu dan muryarta bata fita Sam sabida tsabar ihun da ta ringayi fatar ta tayi rudu rudu


"Wlh daga yau ko k'ofar gida kika k'ara fita ba tare da Hijabi ba wlh dukan da na miki yau kad'an ne shegiya 'yar akuya da bata San martabar Aure ba daga yau ma na k'ara ganin kin saka kananan kaya wlh sai na Lahira yafiki jin dadi useless human being"

Daga haka ya sakar mata kanta tare da hambare ta

"Allah ya isa tsakanina dakai Ameer na tsaneka bana kaunarka ai Auren ba dole bane kabani takardata bazan iya cigaba da zama da mahaukaci da bai San darajar mace ba kuma wlh kananan kaya yanzu nafara sawa sai dai ka kasheni"

Zara tace tana fashewa da matsanacin kuka


Ameer ko kallonta baiyi ba yafice daga palon yaje ya hau motarsa tare da dannawa Adnan dake ta k'ok'arin tada motarsa harara ya fice daga gidan


Adnan kuwa maida kallonsa yayi b'angarensu Ameer bayan Ameer yabar harabar gidan haka kawai zuciyarsa ta ringa raya mishi abubuwa

Yana daga cikin mota ya juya ya kalli b'angarensu ganin k'ofar a rufe kamar yanda yake ne yasa ya fito daga motar ya rufe kansa tsaye ya nufi b'angarensu Amir ba tare da wani tsoro ko shakka ba


A hankali ya tura k'ofar shiga b'angaren yaga ya bud'u dayake ginin iri d'ayane bai sha wahalar gane palon gidan ba tun kafin ya k'arasa yafara jiyo sheshek'ar kukan Zaran da sauri ya shiga palon ya hangota a kwance a k'asa tana ta kuka


Zara da Sauri ta d'ago da kanta sakamakon k'amshin turaren Adnan da taji ya ziyarci hancinta


Aikuwa kuka ta k'ara fashewa dashi da taga alamar tausayinta a kwance a fuskarsa

Adnan kuwa a hankali ya k'arasa kusa da ita ya tsunguna agabanta ya zaro hankici daga Aljihunsa ya mik'a mata yana mata sannu da d'aya hannun nasa


Zara kuwa kukan ta k'ara fashewa dashi ba tare da ta mik'a hannunta ta k'arbi Hankicin ba

Cikin sanyi murya da tausayawa Adnan ya fara magana yana "kiyi hakuri Zara ki tashi ki share hawayenki ban tab'a tunanin Mijinki Jahili bane sai yau Idan ba haka ba banga abinda kikayi da kika cancanci irin wanan dukan ba Wanda bashi da ilimi ai shi yake dukan mace pls bar kukan haka kar kanki yayi ciwo k'arbi ki share hawayenki gani nayi bazan iya tafiya ba tare da naga halin da kike ciki ba"


Tunda yafara magana Zara ta kura mishi ido abubuwa nata mata yawo ajiki muryarshi ba k'aramin sanyi yasa tafara ji aranta ba Adnan shine irin mijin daya dace da ita he is social and a caring type


"Pls k'arbi ki share hawayenki"

Adnan ya k'ara cewa yana mik'a mata hankicin hannunsa


Zara a hankali ta mik'a masa hannunta ya bata hankicin tafara goge fuskarta still hawaye na ambaliya a fuskarta

"Sorry" Adnan yace yana k'yab'e fuskarsa kamar zaiyi kuka

"Thank you"

Zara tace tana zuba mishi ido

Adnan mik'ewa yayi yace "pls kisamu ruwan zafi ki gasa jikinki kinga am not the right person to do all this da ni zan gasa miki jikin naki pls idan kin gasa jikin naki kisamu magani kisha"

Zara ji tayi kamar ta dakka tsalle ta rungume shi sabida wani mugun sansa daya shigeta farat d'aya


Cikin muryarta da baya fita tace "pls ka taimaka min na tashi bazan iya tashi ba"

Adnan mik'a mata hannunsa yayi ta rik'e take su biyu suka ji wani irin shock ya ziyarce su Adnan kuwa ya mik'ar da ita yana karewa kirjinta kallo "thank you am greatfull "

Zara tace tana k'ara kura mishi ido

Adnan murmushi ya sakar mata yace "u are wlcm"

Zaro idonsa yayi a lokacin dayaga yanda fatar jikinta yayi rudu rudu a kumbure dan hatta hannayenta a kukumbure suke


"Subhanallahi yanzu haka Ameer yaji miki ciwo"

Ai tamkar zuga Zara yayi ta fashe da kuka tana "wlh jikina duk ciwo yake min da belt d'insa ya dakeni dubi fa irin ciwon dayaji min"

Zara tace a lokacin da take zame rigarta ta sama

Numfashin Adnan ne ya kusa d'aukewa na wucin gadi sakamakon tozali da yayi da surar Zara ita kuwa Zara kuka ta cigaba da yi tana nununa masa inda Ameer yaji mata ciwo harda d'aga rigarta sama cinyarta ya bayyana Adnan kuwa wani irin yawu ya k'ara hadiyewa dayaga santala santalan cinyarta awaje

(Readers Zara fa bata kamo Aliya a diri da kyau bafa dan tafi Zara komai sai dai Zara ta gaya mata tsayi da haske dan ita fara ce kal kal sabanin Aliya da bata kai ta haske ba amma kuwa duk baiwar da Allah yayi wa matarsa baya gani idan namiji maneman mata ne wlh matarsa ko da gwal aka kerata bazata tab'a burgeshi ba sai dai na haram d'in Allah ya shirya mana mazajenmu wayanda kuma suke Neman matan banza Allah ya shirya mana su)


Cikin stammering Adnan yace "amma bai kyauta ba sorry"

Zara d'agowa tayi tace "ngd bari na shiga toilet na gasa jikin nawa amma fa bansan mai nayiwa matarka ta tsinka min mari ba dazu am really hurt mai dan nafito ahaka did she think am trying to seduce you or wat"?

Adnan cewa yayi " karki damu na d'au mataki akanta kinsan kidahuma ce bata da wayewa ko kad'an"


Zara sai a lokacin tayi murmushi tace "karka damu zan wayar maka da ita" ta wani kanne masa ido d'aya


Adnan ai ji yayi kamar ya fusgota ya rungume sabida ta gama tafiya da imaninsa shima wani kwarton kallo yabita da shi daga sama har k'asa yace "bari na tafi nayi latti a office oll because of you"

Murmushi Zara ta k'ara yi tace "oll d best" ta mik'a masa hannu alamar suyi musabiha

Jiki na rawa ya mik'a mata hannu ta kuwa rik'e gam sai da suka kurawa juna ido na second goma Zara ta janye hannunta tayi mai bye da hannu ya sakar mata murmushi ya juya zai bar palon

"Pls can I have your contact"?

Yaji muryar Zara ta doki kunnensa


Juyawa yayi yace "of course"

Dingisawa tayi ta d'auko wayarta daga d'aki Adnan kuwa sai hadiyar yawu yake dan duk taku d'aya sai mazaunanta sun motsa


Lambarsa ya shigar mata ya mik'a mata tayi saving ta k'ara ce mishi ta gode Adnan ya sakar mata murmushi ya juya ya tafi yana zuwa k'ofar fita daga palon sai da ya k'ara juyowa ya sakar mata murmushin da ya saukar mata da kasala da wani sanyi lokaci guda ya fice yarap ta zube akan kujera ta lumshe idonta tana ayyana abubuwa a ranta ko ciwon da jikinta keyi bata ji


Adnan kuwa sai da ya d'an lab'e ya kalli b'angarensu yaga alamar babu kowa ya nufi motarsa da sauri ya tayar ya fice daga gidan


Aliya kuwa kuka tayi sosai Wanda ya haddasa mata ciwon kai da zazzabi a take


rarrafawa tayi ta shige d'aki ta kwanta duk maganganun Adnan na mata amsa kuwwa a kunne idan ta tuna warin dayace tana yi sai ta kara rushewa da kuka.

Yinin Ranar da tunanin Zara Adnan ya wuni sabida tunaninta ma ya manta da wata Meera sai data kirashi ya tunata duk dokin dayake na su had'u sai yaji baya wani dokin su had'un


Dagawa yayi yace zai kirata nan da k'arfe hud'u


Aikuwa sai da ta k'ara kiranshi ya tuna tsaki yaja yace mata su had'u a Horizon hotel zaije ya musu booking yanzu banza banza ya rage zafi


Karfe biyar da rabi yana kwance a d'akin da ya kama musu daga shi sai gajeren wando yana jiran zuwan Meera


Meera kuwa ba wani Abu bane yasa ta matsu su had'u da Adnan sai dan cikon kud'in ankon kawarta da take nema dan asanadin karya da gasa da San yin ankon masifa ta rasa budurcinta tundaga lokacin indai anko aka fito da shi ko nawane sai tayi inta kama ma tabi maza ukune arana


Room number da Adnan ya gaya mata tashiga ganin Adnan yayi wani rashe rashe daga shi sai gajeran wando yasa ta sakar masa murmushi shima ya sakar mata yana mai kare mata kallo sai yanzu yake hango muninta dan ganin dare ya mata gashi ta sha fente fente


Ba tare da b'ata lokaci suka ci snacks d'in daya musu oda suka kora da mai sanyi daga nan ya janyota yafara mamatseta ita kuwa ganin yana k'ok'awa da rigarta yasa ta rik'e masa Hannu tana "bamuyi ciniki ba zaka apkamin"

"Dama ke karuwace"?

Shine kalmar daya fito daga bakin Adnan

" ni ba karuwa bace amma kasan dai babu yanda zakayi ka hayeni abanza"

"To ai karuwai ke ciniki kafin a dannesu amma karki damu ni ba mitsiyaci bane babu yanda za'ayi na gurjeki a banza ba tare da na miki ihsani ba dafatan ba sai nasa protector ba hope am save"


Yace yana nuna mata condom d'in dake ajiye a bedside d'in d'akin

"Gaskiya kasa dan jiya na gama period"

Meera tace rai a d'an bace dan taji haushin maganar da ya mata


Adnan tab'e baki yayi ya janyota yafara wasani da ita ita kuwa Meera ta ringa nonok'ewa


Adnan kuwa burinsa kawai ya rabata da kayan jikinta da k'arfi ya rabata da top d'in jikinta ya b'alle bra d'inta ya wurgar

Zaro ido yayi dayaga nononta ya kankance himilin cikon da tayi ya fad'o


Ita kuwa Meera kunya ne yabi ya rufeta dan bata da wani diri duk ciko ne daga Bumbum d'in har Hips da nonon....🤣🤣🤣🤣🤣🤣🤣🤣🤣


Wlh Rabin 'yan matan yanzu shape d'in jikinsu fake ne I swear
[21/07, 03:16] Nabila maishanu Fbk Gusau Zamfara: *M🅰K'OT🅰N JUN🅰*
*REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS* *P.M.L*
*Written by*
💅💅💅 *SADNAF*💅💅💅
*Follow me on wattpad @ Sadnaf*
*Wanan shafin nakine ke kadai kiyi yanda kikeso dashi Maman Basheer Ngd sosai da so da K'auna*
*page 4*
Adnan mitsitsika idonsa yayi sosai dan ya ya tabbatar da kwantacen nonon daya gani mai kama da kulin sigan Ashirin
Meera kuwa jikinta ne ya d'an fara rawa ta janyo rigarta tana k'ok'arin kare kirjinta
Adnan kuwa daya zama so shock da sauri ya janye rigar ya k'ara wurgar dashi yace "ke mai wanan? Yasa hannunsa yana kamo tatsitsiyen nononta dake kwance kamar jikakken tsuma sabida tsabar matsar daya sha
Doke hannunsa Meera tayi tace " Wai mai hakane wani rashin mutuncin ne haka"?
"Wane irin rashin mutunci Ameera ya zan kwadaitu da surar jikinki amma Ashe ciko kike yi ba nakin bane ni zaki yaudara karma kice min baya da hips d'in shima cikone"
Ya janyota yana k'ok'arin rabata da skirt d'inta
Meera kuwa data ga Abun Adnan rashin mutinci ne k'ok'awa ta fara yi dashi da hannu d'aya tana rufe kirjinta da hannu d'aya
Adnan kuwa a zuciye ya wanka mata mari ya had'e hannayenta acinyarsa ya zame mata skirt d'in Meera kuwa sai mutsu mutsu take
Bak'in skiny dake jikinta ya zare yaga still akwai wani tight skinny ajikinta aikuwa ya zare shi da k'arfi sai ga linkakkun towels guda biyu data yi hips dashi sun fad'o sai wani form mai zubin pant data saka ya taimaka wajen saka duwawun nata tudu
Adnan sakinta yayi yana sallati dan bai tab'a tunanin Meera is shapeless ba Ashe duk yaudara ce mugun acuci take yi
Meera kuwa kukan takaici ta fashe dashi dan bata tab'a had'uwa da dan iska Mara mutunci kamar Adnan ba dan duk wayanda take bi basa wani damuwa idan suka gano ciko tayi burinsa dai su samu biyan bukatarsu da ita amma sai gashi Adnan ya mata dalla dalla
"Yanzu dama ameera ciko kike yi kike yaudarar mutane da wanan bushashen jikin naki har kike fad'ar baayi ciniki ba amma ban tab'a ganin 'yar iska irinki ba kuma ahaka kike samun masu kusantarki nono kamar lagwani ni ban ma tab'a ganin duwawu Mara tudu kamar faranti ba sai naki"
Adnan yace yana kaiwa duwawunta duka
Meera kuwa babu abinda take yi in banda kuka dan karshen cin mutunci Adnan yayi mata
Mik'ewa tayi a hankali tana share hawaye tabar kan gadon ta nufi inda kayanta ke zube dan ta saka
Adnan da sauri ya duro daga kan gadon yasha gabanta yace "ba tambayarki nake ba uban meyesa kike ciko dan ki yaudari mutane "
Meera kuwa kuka ta fashe dashi sosai ta had'e hannayenta tace "Dan Allah dan annabi ka kyalleni nasaka kayana na tafi cin mutunci ma kawai daka min ya isheni haka dan Allah ka rabu dani daga haka ta fara saka kayanta
Adnan kuwa kame kugu kawai yayi yana kallon ko ina na jikinta da mamaki dan wlh badan ya tub'eta ba ko hadiyar Qurani akayi akace mishi ciko tayi karyatawa zaiyi yanda shape d'inta ya fita
Bra d'inta ta saka ba tare da tasa acucin ba har towel d'in maidasu tayi cikin jakarta tana ta share hawaye
Adnan kuwa ya nufi wajen ta da sauri ya rik'e mata hannun da ta rik'e towels d'in zata sa a ajaka
[21/07, 03:17] Nabila maishanu Fbk Gusau Zamfara: *M🅰K'OT🅰N JUN🅰*


*REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS* *P.M.L*



*Written by*

💅💅💅 *SADNAF*💅💅💅



*Follow me on wattpad @ Sadnaf*



*page 5*



Ameer a Palo ya tarar da Zara tana shafawa tab'on jikinta mai daga ita sai towel Dan bata Dade da fitowa daga wanka ba

Tunda taji karar motar Ameer ta d'aura fuskarta sosai babu alamar faraa a tare da ita


Ameer sallama ya k'ara yi akaro na biyu still bata amsa ba dama yasan zaa rina ko da ba fad'a suka yi ba bata wani damu ta amsa Sallama ba


Ledojin hannunsa ya ajiye yace cikin sanyin murya y "Sannu da gida"

Kamar yanda yayi tunanin bazata kula shin ba ko haka akayi Dan ko d'aga kanta batayi ta kalleshi ba ballantana ta kalli inda ya ke


Kusa da ita ya zauna ya tankwashe k'afarsa ya ruk'o hannunta

Wani irin fusge hannunta tayi tare da sakar masa harara tana "don't u dere touch me Ameer na tsaneka wlh namijin da bai San darajar Mace ba shi yake d'aga hannu ya daketa bazan iya zama da namijin da zai ringa jibgata ba dan haka ka bani takardata kawai na tafi gidanmu"

Tace tana k'ara watsa mishi mugun kallo


Ameer murmushi yayi Dan ko kad'an baiji haushin maganganunta ba he deserve more dan this dan sai a yanzu yaga yanda ya farfasa mata jiki

Cikin Sanyi murya yafara magana

"Zara am sorry pls I know what I did was wrong bai kamata na dakeki ba Amma Zara kinsan idan raina ya b'aci bana iya controlling d'in kaina

Zara kinsan halina ina da bala'in kishi mai yasa zaki fita da sleeping dress har gidan mak'otanmu shi kuma babu kunya babu tsoron Allah ya tsaya yana kare miki kallo Zara dan Allah haka kika ga matarsa ta nayi meyesa bazaki yi koyi da halinta ba

wlh har
yau bansan kamanin matarsa ba sabida yanda take lullub'e jikinta

Zara idan bana sanki babu yanda za'ayi nayi kishinki islamically ma is not right kifita ahaka kina matsayin matar Aure karki manta ko ina na jikin mace Al-aura ce banda fuskarta tafin kafarta da tafin hannayenta am really hurt Dana ganki agaban Adnan atsaye ahaka

Zara ban hanaki kiyi shigar da ranki keso ba wlh Zara ko tsirara ne ma kiyi matsawar dagani sai ke ni zaki yiwa adon nagani naji dadi kisamu lada

ina rok'onki kiji tsoron Allah ki kiyaye dokokin Aure da martab'arsa ki ringa tsare mutuncin kanki ki ringa tayani kishin kanki pls insha Allah zan miki duk abinda kikeso matsawar bai fi k'arfina ba ki ringa koyi da mak'ociyarki pls she is very decent ga kunya wlh ban tab'a ganin fuskarta ba kullum kanta a sunkuye kuma"



Shiru yayi sakamakon wani mugun kallo da Zara ta watsa mishi tace "OK kana nufin am not decent and banida kunya idan hakane mai zai hana kaje ka aureta ni ka sakeni inje in Auri Wanda ya dace dani dan gaskiya bazan b'oye maka ba wlh ina bala'in Dana sanin Aurenka ka takura min ka hanani sakewa ban tab'a ganin ranar data fito ta fad'i batare da kayimin fad'a ba agidanan kullum cikin yimin fad'a kake ban tab'a yin Abu nayi dai-dai ba

Ameer katseta yayi da " ina miki fad'ane cos u are not doing the Right thing Zara babu yanda za'ayi na hau yi miki fad'a kawai ba tare da dalili ba


idan kikayi ba dai-dai ba ban nusar dake naganar dake ba mai amfanina amatsayina na mijinki ke kinfiso na zuba miki ido kawai ki ringa abinda ranki keso yanzu duba Sallar daya zama obligatory akanki bakya San kiyi sai kin ga dama

A times sai na tsaya akanki kikeyi wai Nan da sunan kina cikakkiyar musulma and ahaka zakiyi raising children d'inki suna ganin yanda kike yi Zara marriage is not all about sex and satisfaction u are a woman u have to be a role model to your children abinda kikeyi shi zasu yi koyi da shi amma zaki so ki haifi 'ya'ya suga bakya salla sai kin ga dama ga jin music na tashin hankali ga dressing any how haba Zara ki duba magana ta bawai ina takura miki bane wlh gaskiya nake fad'a miki nan gaba zaki gane hakan

idan kika bi abubuwan danace wlh zamanmu zai yi dadi ni ba mai takurawa bane"

Zara duk maganar dayake ta bayan kunnenta yake shiga yake fita da yake shaidan na mata hudubar Tsiya bala'in haushinsa take ji har wani tsanarsa take ji yana darsuwa a ranta d'agowa tayi tace


"Sheik Ameer kamar yanda na gaya maka gaskiya wlh daga yau bazan yarda ka k'ara takura min ba idan kaga

Please Login or Register in order to submit comment