Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

wai meyesa kike irin wanan maganar ne kina karyamin zuciya Zara ki bari idan kin haihu zan kirashi da kaina in rokeshi ya yafe miki"


"Mommy nasan mai nake cewa Mommy ni naci amanarsa dan Allah ki kiramin shi dan Allah nace"

"Innalillahi wa inna ilahi rajiun Zara yanzu dare yayi kusan sha biyun dare ki bari gobe sai na kirashi nasan kafin nan kin haihu insha Allahu"


"Mommy ki kira shi yanzu kice yazo da sassafe dan Allah Mommy na rokeki da girman Allah"


Mommy Hauwa kallon Zara kawai take Hawaye na zubo mata

Wayarta dake rik'e a hannunta da tunda zu sabida irin kiran da aka ringa mata ana tambayarta Zara ta haihu ta d'auko tayi dailing number Ameer tasa a handsfree taji yana ta waya dan call waiting kawai yake sa mata.


Adai dai lokacin da Ameer suke ta soyewa da Aliya ta waya ba k'aramin mamaki yayi ba dayaga kiran Mommy Hauwa wajen sha biyun dare bai d'aga ba sai dayaga kiran nata shigowa gabansa ya d'an yanke ya fad'i yana tunanin mai zai sa ta kira shi awanan lokacin mai kuma hadinshi dasu Aliya yacewa yana zuwa ya d'aga wayar Mommy Hauwa tare da Sallama.




Mommy Hauwa ce ta fara gaishe shi da sauri
Ameer shima ya gaisheta tare da bata hakuri akan k'in daga wayar da yayi daga farko

Mommy Hauwa cewa tayi "Ameer dan Allah Dan annabi wani alfarmar nake nema duk da nasan zan takura maka ka dubi girman Allah kayimin wanan alfarmar"

"Subhanallahi Mommy ya kike ta had'a ni da girman Allah haka ai tamkar Mahaifiyata kike kin wuce duk wani alfarma a wajena idan Kinga kin tambayeni Abu banyi ba to Sai dai idan bani dashi Karki ga wai dan mun rabu da Zarah kiyi tunanin zan daina girmamaki ko mutuncinki zai ragu a idona ko d'aya wlh fatana Allah ya bani ikon yi miki abinda kike Neman"

Zara lumshe ido tayi hawaye masu dumi na biyo kuncinta dan a hands free tasa wayar.

Mommy Hauwa kuwa tace "Ameer dan Allah idan da Hali inaso gobe da sassafe kazo ka sameni a standard hospital dan Allah"


"Subhanallahi Mommy waye ba lafiya"

"Ameer ka dai kawai sai kazo ka kwantar da hankali ka ba wani Abu bane"

Ameer ajiyar zuciya ya sauke duk da hankalinsa bai kwanta da abinda tace ba yace "toh insha Allahu Mommy zan zo da sassafen"


"Yauwa Ameer ngd kwarai sai naganka"

Daga haka Mommy Hauwa ta kashe wayarta tare da kallon Zaran da idonta ke lumshe tace "toh na kira shi Zara kuma kinji Yanda mukayi dashi Zai zo da sassafe"


Zara bud'e idonta tayi da d'an murmushi a fuskarta tace "Ngd Mommy kinsan kuma wani abun mamaki wlh Kinga ciwon ya koma sakayau nake jina"
Mommy Hauwa da d'an mamaki tace "Ciwon ya koma kamar yaya kin daina jin Nakudar"?

Zara girgiza mata kai tayi tace " eee wlh nakudar ya koma"

"Ikon Allah ya akayi nakudar ya koma bari na kira likita dai ya dubaki dan bangane kin daina jin Nakuda ba"


Daga haka Mommy Hauwa ta fice waje da sauri.

Fitarsu da minti biyar sai gashi sun dawo da likitan

Inda likitan ya dudduba Zara yace "ta koma 4cm shiyasa ta daina jin nakuda amma zai kara sa mata ruwan nakuda kila ta haihu kafin gari ya waye"

Sai da ya saka mata ruwan ya bar d'akin.


Mommy Hauwa kuwa ta zauna a gefenta tana kallonta har bacci ya kwashe Zaran.

Zara baccinta tasha har akayi Sallar asuba bata ko motsa ba inda Mommy Hauwa ko kad'an batayi gyangyadi ba a kasan ranta kuma tana mamakin Yanda akayi Zara ta daina nakudar.
Likita kuwa ya dawo ya duba Zara yafi sau biyar amma har lokacin baccinta kawai take yi.



Bakwai na safe Ameer yafara shirin zuwa asibitin standard dan Sam bacci bai wani kara d"aukarsa daya samu kuwa bacci yayi awon gaba dashi Mafarkin Zara ya ringa yi tana ta Neman yafiyarsa a mafarki.

Haka ya tashi sukuku yana mamakin Mafarkin da yayi ahaka ya shirya kafin ya fito daga gida ya kira Aliya awaya dan su gaisa kamar dai Yanda suka saba.


Gaisawa sukayi ya tsokaneta kamar dai Yanda ya saba jin da yayi kamar a bakin titi suke yasa ya tambayesu suna ina ne yajisu a bakin titi.

Aliya ce mishi tayi Hajiyarsu ce ta aikesu tarauni zasu karbo mata sako.


Ameer murmushi yayi yace mata ai hanyarsu d'aya ma shima zaije asibiti bari yazo sai ya kaisu daga nan.

Cikin minti biyar ya k'arasa layinsu Aliya inda yagansu a tsaye da wata 'yar uwarsu data zo daga Jos

Aliya tana sanye da doguwar Rigar atamfa da farin Hijabi kal mai hannu hijabin har gwiwarta ya kai mata babu kwalliya a fuskarta amma ba k'aramin kyau tayi ba.


Ameer k'asa d'auke idonsa yayi akanta har suka shigo cikin motar inda Aliya ta zauna agaba 'yar uwarta ta zauna a baya.


Ameer kunyar Yar uwar Aliya ne yasa bai mata santin kyaun da tayi ba yaja motar suka d'auki hanyar asibitin dan sai an fara zuwa asibitin za'aje gidan da aka aiki su Aliya.

Yana karya kwanar da zasu shiga asibitin Ameer yace musu "Dan Allah bari na duba Mara Lafiya anan kunga kuma zaku samu lada".
Kusan atare sukace babu komai.

Adai dai lokacin da ya shigar da kan hancin motarsa a harabar asibitin yayi parking ya fito yace Su Aliya ma su fito su shiga ba dadewa zasu yi ba.

Fitowa sukayi suka jeru da Ameer ita kuma 'yar uwar Aliyar na binsu abaya.

Ba k'aramin dacewa sukayi ba inda kana ganin Aliya kasan Amarya ce sabida Yanda take kyalli k'unshin hannunta yafito rad'au.

Ameer wayar Mommy Hauwa ya kira adai dai lokacin da Zara ta bud'e idonta sakamakon wani azababben ciwo Mara daya tasheta.


Sallati kawai take tana kiran sunan Mommy Hauwa Inda Mommy Hauwa ta rude tayi waje da gudu dan ta kira likita.

Kafin ta k'arasa office d'in likitan taga Ameer a tsaye yana ta danna wayarsa da alama ita yake ta kira.

Ameer ganin Mommy Hauwa na sauri kamar zata tashi sama sai kuka take Ameer sallati ya saki ya nufi wajenta adai dai lokacin da ta shige office d'in likitan.

Inda suka k'ara fitowa da likitan.

Likitan yayi d'akin da aka kwantar da Zara

Mommy Hauwa kuwa ta tsaya cikin tsananin tashin hankali ta gaya mishi halin da suke ciki tun jiya da kuma Neman da Zara take mishi dan ta nemi yafiyarsa.


Ganin Yanda Mommy Hauwa keta kuka yasa Ameer ya hau kwantar mata da hankali akan insha Allahu Zara zata haihu lafiya lau.


Sai a lokacin Mommy Hauwa ta Lura dasu Aliya tacewa Ameer "Wadanan kanenka ne"?

Ameer murmushi yayi yana d'an Sosa kai cike da jin nauyin Mommy Hauwa yace " aa ai tunda zu suke ta gaisheki bakiji ba Mommy Wannan sunanta Aliya itace matar da zan Aura gobe za'a d'aura mana aure Wanan kuma kanwarta".


Mommy Hauwa Aliya ta zubawa ido tana yaba kyaunta da nutsuwarta tana kuma mata murnar samun miji kamar Ameer da Sauri Mommy Hauwa tace musu Allah ya sanya alheri ta nufi d'akin da Zara take dan har lokacin Likita bai fito ba.

Tana barin gurin Aliya tacewa Ameer "Allah sarki Ameer wanan ce Mahaifiyar Zara"

Ameer girgiza mata kai yayi Aliya tace "Allah sarki Ashe Zara haihuwa zatayi ita kazo dubawa kenan"


Yana k'ok'arin magana Dr dasu Aunty Khadija suka nufo wajen da suke.

Dr awajen Ameer ya tsaya dan duk a tunaninsa shima Yaji labarin haihuwar da Zara zatayi shiyasa yazo.

Kadaran kadahan suka gaisa da Ameer dan Dr yayi laushi sosai duk wanan zafin kan babu.

Inda Aunty Khadija tayi wajen d'akin da sauri .

Aliya wajen Ameer ta nufa dan tace mishi ita zata tafi kar ayi musu fad'a dan haka kawai taji wani kishi kishi ya rufeta data ga Yanda Hankalin Ameer d'in ya tashi akan Zara kenan har yanzu yana san matarsa .


Tana k'ok'arin yi mishi Magana Adnan ya shigo asibitin Khaleed na biye dashi abaya dan tunda asuba yabaro gida dan Safwan shawara ya bashi akan yafara zuwa ya nemi yafiyar Zara yaga halin da take ciki kafin ya nemi su Aliya dan Zara tafi bukatarsa inda ya d'auki shawarar Safwan ana iddar da asuba yafito daga gidan rashin abun hawa yasa sai da gari yafara wayewa yasamu abun Hawa ya nufi gidansu Zara.


Sai daya sha wahala kafin ya samu Wanda zai aika ciki dan akan idonsa su Dr suka fita tsoro ne yahana shi zuwa yayi musu magana inda sai da suka tafi ya samu wani yaro ya aike shi ciki akan ayi mishi sallama da Zara.


Khaleed dashi kawai aka bari a gida shi yafito dan yaga wanda yake Sallama da Zara dan duk a tunaninsa Ameer ne.


A bakin gate ya tsaya yana kallon Adnan dan bai san shi ba

Adnan kuwa ya k'arasa wajensa da Sauri ya mik'a mishi hannu tare da gaishe shi bai tsaya b'ata lokaci ba ya fad'awa Khalid Zara yake nema dan Allah ya kira mishi ita.

Khalid ganin Yanda yake magana kamar hankalinsa ba'a jikinsa yake ba yasa ya fad'a masa Zara na asibiti tun jiya taje haihuwa har yanzu kuma bata haihu ba shima so yake yayi wanka yaje.

Adnan cikin tsananin tashin hankali ya rik'e k'afar Khalid yace dan Allah ya raka shi asibitin yaga Zara ya taimaka mishi.

Khalid mamakine ya rufe shi dayaga Yanda yake had'a shi da Allah Dan har hawaye ne ya fara zubo mishi yana so ya mishi tambaya amma Adnan bai bashi dama ba sai had'a shi yake da Allah akan dole yaje ya shirya suka taho asibitin.

Aliya da Ameer Adnan suka zubawa ido da gashi ya cika wa fuska yabi ya zama wani siririr kamar mai cutan kanjamau babu abinda kake hangowa sai dogon wuyansa da idonsa daya shige ciki.

Ameer da Aliya ko kad'an kasa d'auke idonsu sukayi akan shi dan suna kwokwanton anya ma shine dan har carbi suka gani a hannunsa.

Adnan kuwa ko kad'an bai ma lura dasu ba dan bashida burin daya wuce yasan halin da Zara take ciki sai zabga sauri yake kamar zai tashi sama.

Haka kawai gaban Aliya ya yanke ya fad'i ta cigaba da kallon Adnan daya kusa isowa wajen da suke a tsaye.

Adai dai lokacin Adnan ya kallo inda suke a tsaye inda numfashinsa ya nemi d'aukewa sakamakon tozali da yayi da Hadaddiyar Aliya da kyaunta ke zuba sabida gyaran da ta sha bai yarda ita bace sai da ya k'ara Murza idonsa ya ga tabbas ita d'in ce dan itama bata d'auke idonta daga kan shi ba haka zalika Ameer dake gefenta.


A slow Adnan ya fara takawa inda suke a tsaye har lokacin bai kalli Ameer ba dan hankalinsa na kan Aliya.


Agaban Aliya ya tsaya hawaye Na sauko mishi bakinsa sai rawa yake sabida yana so ya furta sunanta.

Aliya kuwa cikin tsananin tsoro da mamakin Yanda Adnan d'in ya koma yasa ta juyar da kanta da sauri Tana "Ameer mu tafi"

Adnan da sauri ya kalli gefenta yaga Ameer ne daya zama First class Alhaji gentle guy ya zuba mishi ido yana mishi shima kallon mamakin Yanda ya zama.


Adnan kasa d'auke idonsa yayi akan Ameer ya Kalli Ameer ya juya ya kalli Aliya data Kau da kanta.


Aliya magana ta kara yi akan Ameer yazo ya maidasu gida ta fara k'ok'arin ratsa gefen Adnan ta wuce.

Adnan ya zube agabanta ya fashe da kuka yana "Aliya dan Allah Dan Annabi ki yafemin wlh nayi nadamar abinda nayi miki Aliya kinga Yanda na koma Aliya ki rufamin asiri ki yafemin dan Allah Dan annabi wlh bansan Yanda zan yi ba idan baki yafemin Na nasan an cutar dake na zalunceki amma ki bani dama dan Allah Dan annabi Na gyara kuskurena"


Aliya a kyamace ta zabga mishi harara ta ja da baya tace "kai da wa Allah ya kiyaye mai zanyi dakai Adnan ai ka Riga da ka makaro dan sai dai ka nemi wata kuma bani ba dan gobe insha Allahu za'a daura mana aure da angona Ameer Allah ya saka min abinda kayi min ya bani nagartacen miji Ameer ai baka ga komai ba Adnan ba dai bariki kasa agaba ba Kaje ka cigaba da yi ai baka ga ribar bariki ba tukunna"

Adnan tunda tace angonta Ameer ya maida kallonsa kan Ameer dake kallonsa shima yana tab'e baki kirjinsa wani irin bugawa yake kamar ya fad'o kasa wai Aliyarsa ce zata Auri Ameer mak'ocinka.


Hawaye ne suka cigaba da sauko mishi yana daga tsugunan Aliya kuwa taja tsaki tare da ruk'o hannun Ameer abinda bata tab'a yi ba.

Adnan runtse idonsa yayi sabida wani irin Abu daya sokeshi a kirji Ameer kuwa Yaji wani irin shock har kwakwalwarsa sabida taushin hannun Aliya.


Yana k'ok'arin bin bayan Aliya ya jiyo Mommy Hauwa Na k'walla mishi kira Tana wani irin kuka yana zabga sallati.


Ameer a kidime ya kwace hannunsa ya nufi wajen Mommy Hauwa inda Aliya itama ta rufa mishi baya Adnan kuwa yayi saurin mik'ewa hankalinsa a tashe dan yama manta dan Zara yazo asibitin sabida ganin Aliyar da yayi.


Mommy Hauwa cikin tsananin kuka tacewa Ameer yazo inji Zara daga haka ta koma d'akin da sauri


Ameer yabi bayanta Aliya da Adnan ma haka

Dan haka kawai Aliya taji hankalinta ya tashi data ga Yanda Mommy Hauwa ke kuka.

Zara kuwa tunda ta farka azabar da take sha yake karuwa tun Tana sallati da k'arfi har tazo ta kasa sai gwallo ido take awaje.

Likitan shi kansa hankalinsa a balain tashe yake dan bai kuma wani sauraran su Mommy Hauwa ba yafara processing yanda za'ayi mata operation Zara kuwa ganin zaa shiga da ita d'akin theatre yasa tacewa Mommy Hauwa ta kira mata Ameer ta nemi yafiyarsa.


Ameer jikinsa ne ya fara rawa dayaga Zara a kwance kamar ba ita ba yana had'a ido da ita gabansa ya fadi dan ansaka mata kayan operation d'akin kawai za'a kaita ta hana tace sai taga Ameer.


Adnan cikin masifaffan tashin hankali ya matsar da Ameer daya k'asa k'arasawa wajenta ya k'arasa bakin gadon yana

"Zara dan Allah ki yafemin abinda nayi miki nagane kuskurena yanzu na dawo gareki idan kin haihun za'a d'aura mana Aure kinji dan Allah ki yafemin Abubuwan danayi miki"

Tunda ya k'ara so bakin gadon Zara ta rufe idonta Dan Sam bata san ganin Adnan dan shine silar shigar ta masifar data jefa kanta.

Bud'e idonta tayi ta sauke shi akan Ameer da Aliya da suka zuba mata ido wani abun mamaki wani irin k'arfi ne yazo mata ta bud'e bakinta hawaye na zubo mata tace "Ameer dan Allah ka k'araso gareni kai da Aliya na nemi yafiyarku"

Kamar wayanda ake turawa haka suka k'arasa wajenta inda haka kawai Aliya ta fara zubar da hawaye na tausayin Zara.


Ameer kuwa shima tausayin Zara ne ya rufe shi ya zuba mata ido

Zara kuwa ta cijje lebb'e ta sabida wani azabar ciwon daya taso mata magana ta fara yi tana "Ameer dan Allah ka yafemin abinda nayi maka ka dubi girman Allah ka yafemin ko da zanji saukin azabar da nake ciki Ameer na cuceka ma hainceka naci amanarka alhalin kana iya bakin k'ok'arin ka dan kaga ka faranta min dan baka rageni da komai ba amma dayake shaidan da san zuciya na dawainiya dani haka na butulce maka naci amanarka da mak'ocinka na keta alfarmar aure Ameer dan Allah Dan annabi ka yafemin nasan da wuya ka manta abinda nayi maka dan Allah ka yafemin ka dubi halin danake ciki"


Ameer da Sauri yace "karki damu Zara na yafe miki Allah ya yafemu gabaki d'aya kiyi ta Neman yafiyar Allah Dan shi kika sab'awa dan ya hane mu da mu aikata zina Kiyi ta neman yafiyarsa shi gafurur rahim.ne mai yawan gafara ne zai yafe miki tunda har kika gane abinda kikayi ba dai dai bane ni dai na yafe miki har ga Allah sabida Allah ya Riga da ya musanya min da abinda yafi alheri ta hanyar bani Aliya"


Zara murmushin k'arfin hali tayi tace "Ngd Ameer Allah yasaka da alheri dan Allah ko da na mutu ka ringa tuna alherina kana bina da addua"


Ameer da Sauri ya girgiza kansa yace "insha Allahu bazaki mutu ba Zara Zafin nakuda ne kawai"


Zara murmushi tayi ta maida kallonta kan Aliya dake ta share hawaye tace "Kawata Aliya dan Allah ki yafemin sharrin shaidan ne kinsha yimin nasiha akan in gyara halina nikuma sai nake ganin baki waye ba yar kauye ce ke Ashe kece wayayyar dan akan hanya kike nikuma na kauce hanya kawata dan Allah ki yafemin abinda nayi miki ki dubi irin zaman da mukayi abaya kafin shaidan ya fara kad'a min ganga"


Aliya da Sauri ta matsa kusa da Zara ta rufe mata baki cikin tsananin tausayin Zara tace "na yafe miki kawata Allah ya yafemu gabad'aya"

Ameen Zara tace ta kalli inda su Mommy Hauwa suka tsaya cirko cirko suna share hawaye tayi murmushi tace "Mommyna Daddyna pls Ku yafemin abinda nayi muku kuyi min addua naji dadi araina"

Mommy Hauwa kasa magana tayi sabida kukan dayaci karfinta Dr kuwa ya daure cikin zubar hawaye yace "Na yafe miki 'yar albarka Allah ya yafemu gabad'aya Allah ya miki albarka ya saukeki lafiya insha Allahu bazaki mutu ba mamana zafin nakuda ne"

Zara murmushi tayi ta kalli yayenta ta kalli Khalid da Aunty Khadija ta sakar musu murmushi ta maida kallonta kan Adnan dake ta kuka kamar zai shidde dan bai san meyesa wani irin tsoro ke shigarsa ba duk Kalmar dake fitowa daga bakin Zara tsoratashi yake dan tamkar mutuwa zatayi sunan shi data kirane yasa yayi Sauri ya sunkuya kusa da gadonta yace "Zara pls ki daina irin wanan maganar bazaki mutu ba insha Allahu zamu raini abinda muka Haifa tare zamu haifi wasu 'yayan kin manta kinsha cemin dani kika dace Aliya da Ameer ta dace kinga yanzu aure zasuyi kema idan kin haihun sai a d'aura mana aure pls karki tafi ki barni a lokacin danakeso mu gyara rayuwarmu muyi tsarkakkakiyar rayuwa.


Zara cijje leb'enta tayi cikin tsananin azaba tace " Adnan munyi kuskure daga ni har kai kayi ta istigifari kana neman yafiyar Allah na yafe maka sabida nima inaso Allah ya yafemin idan na mutu kayi ta min addua ka fad'awa abinda na Haifa kaddara ce tasa yazo duniya ta wanan hanyar karka manta dani a adduarka naji dadi da kaima ka gane gaskiya kamar Yanda nagane gaskiya"


Sallati tasa sakamakon wani azabar ciwon marra daya murd'ota gadan gadan taji kan baby ya taho inda Likita ya koresu gabad'aya daga d'akin Mommy Hauwa kuwa ta k'afe akan bazata fita ba.


Likitan yana k'ok'arin saka hand glove Zara tayi nishi da k'arfi kan baby yafito.

Da Sauri likita ya taimaka mata ya fito da babyn inda Babyn ya fito ba rai sabida wahalar da shima ya sha aciki.


Zara kuwa wani irin jini ne ya yanke mata mai gudaje manya manya kafin a Ankara Jini yafara biyo wa ta kasan gadon.

Likita a. Rude ya mik'awa nurse gawan baby boy d'in yayi kan Zara dan ya tsayar da jinin amma ina sai bulbulowa yake .

Zara sallati kawai take Mommy Hauwa na sallati a gigice.

Likita a rude ya aiki nurse akan ta hado mishi allurai inda kafin Nurse din ta bar d'akin Zara ta fara wani irin jijjiga.

Mommy Hauwa aguje taje ta rik'eta Tana sallati.

Zara kuwa ta rik'e mata hannu gam Tana Sallati a can ciki a hankali ta fara rage rukon da tayi mata a hankali Mommy Hauwa kuwa ta ware idonta Tana kallonta cikin tsananin fad'uwar gaba.

Zara murmushi tayi mata tace "Mommy zan sha ruwa"

Aguje mommy Hauwa ta bar d'akin dan ta d'auko ruwan inda fitowarta yasa gabad'aya su Dr suka mik'e suna tambayarta abinda ya faru ta haihu kuwa.

Daga Ameer Adnan har Aliya a rude suke.

Mommy Hauwa bata tsaya kulasu ba ta kinkimi ledan pure water guda tayi d'akin da gudu.


Kasa hakuri sukayi suka bi bayanta dukansu .

Inda dai dai lokacin da Mommy Hauwa ta shigo d'akin likita yaja Zani ya rufewa Zara fuska.

Dukansu sai da kirjinsu ya buga suka zubawa likitan ido.

Mommy Hauwa kuwa ta saki ruwan ta nufi wajen Zara a guje ta bud'e zanin.

Wani irin Razanann k'ara Mommy ta sa tare da kiran sunan Zara.

Adnan kuwa ya zub'e a k'asa a sume.

Dr shima zubewa yayi a kasan .

Inda gabad'aya aka rude da sallati.

Likitan kuwa yayi sauri yabar d'akin sabida tausayi.

"Innalilahi wa inna ilahi rajiun watarana haka zamu tafi inda Zara ta tafi ko yau ko gobe ka shirya baka shirya ba dole ka tafi Domin Kulli nafsi za'ikatul maut pls dis page should increase our iman Allah yasa mudace duniya da lahira ameen.


2nd to d last page

*M🅰K'OT🅰N JUN🅰*


*REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS* *P.M.L*




® REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS

ɯɛ ɖơŋŧ ʝųŞŧ ɛŋŧɛřŧąıŋ ŋɖ ɛɖųĆąŧɛ, ცųŧ ɯɛ ąٳŞơ ŧơųĆɧ ɖ ɧɛąřŧ ơʄ řɛąɖɛřŞ


# WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
# IG PML WRITERS
# https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-




*Written by*

💅💅💅 *SADNAF*💅💅💅



*Follow me on wattpad @ Sadnaf*

*Page 37*


*JAN HANKALI*

*Zanyi Jan hankaline ga wayanda sukayi k'orafi akan page d'in da Zara ta mutu inda wasu suka ce littafi bai had'u ba sabida na kashe Zara wasu kuma suka ce na b'ata littafin harda wayanda zasu daina bin Novel d'in Sadnaf dan na b'ata musu rai Allah sarki Sadnaf bata ji haushi ba dan sai mai kaifin basira zai gane sakon da littafin yake d'auke dashi Karku manta Mutuwa na wuyan kowa duk inda ka kai ga ka gujeta dole sai ta d'auke ka Idan lokacin tafiyarka yayi na Riga da na lura da abu d'aya Novel ba'a fiye mutuwa ba zallar soyayya ne ko kudi Wanda a zahirin gaskiya kullum cikin mutuwa ake haka ma haihuwa a novel ne zaa fara rayuwa mai dadi agama da dadi batare da wani tangarda ba which a reality abubuwa na faruwa ga kowane dan Adam ta fanin kaddara Wanda idan kaga kayi rayuwa tundaga lokacin da aka haifeka girman ka aurenka kai har zuwa lokacin tsufanka baka tab'a fuskantar wani jarrabawa na Allah ba kaje ka tuhumi kanka da kyau kaje ka binciki kanka kagani yana da kyau a duk inda muke a kowane Hali muringa tunanin Zamu mutu zanyi misali kad'an duk soyayyarku da Zara akan karta mutu a yanzu data tuba ya yakamata tafara tsafatataciyar rayuwa Allah yafiku santa daya dauketa dan Alhamdulillahi Zara ta samu damar da wasu basu samu ba cikin kankanin lokaci Allah ya ganar da ita taringa neman yafiyar Allah har wayanda ta zallinta Karku manta wanan rayuwar novel ne Wanda hakan na iya faruwa a zahiri ina zaku kai matar da ta rasa mijinta a tsakiyar lokacin da take bukatarsa ina zaku kai Yaran da suka rasa iyayensu a lokacin da basu da kowa sai su in real life 2014 bazan manta ba wani Friday mata tayiwa iyalinta girki sunci tare yaranta maza uku da Allah ya bata sunci wanka sun saka kaya iri daya da mahaifinsu zasu tafi Sallar juma'a ta rakosu har K'ofar gida suka tafi last born d'in ta nada 3yrs haka suka ringa d'aga mata hannu har suka tafi ta koma ciki dawowar da basu ba kenan sakamakon bomb daya tashi dasu acikin massallaci ta rasa mijinta da yayanta lokaci guda aka jera mata gawansu agabanta inaso Ku saka kanku a takalminta akai abinda ya kai wanan tashin hankali kuna ganin dan Allah baya santa ya k'arbi mijinta da yayanta so inaso kugane Mutuwa na kan kowa da kuma a yanayin da zai zo mana fatan mu Allah yabamu ikon cikawa da kyau da imani ameen*


Aunty Khadija da sauri ta nufi wajen Mommy Hauwa data kankame Gawan Zara bayan ta bud'e mata fuska tana "Zara ya zaki min haka Ashe mutuwa zakiyi shiyasa kikace min ruwa zaki sha Mutuwa meyesa baki d'aukeni kin bar Zara ba"

Kuka take sosai tana jijjiga Zara tamkar wacce take Bacci fuskarta Tayi fayau da haske.


Aliya kuwa kamar sumewa tayi na wucin gadi dan Gawan Zara kawai ta zubawa ido Hawaye na zubo mata gani take kamar Zara bata mutu ba dan idonta har wani gizo yake mata kamar Zara tana numfashi.


Ameer kuwa sallati kawai yake jikinsa na rawa daga inda yake tsaye take ya fara tuno lokacin da ya had'u da Zara da irin Soyayyar da sukayi da fara'arta dan bazai manta ba Auduga abokanansa ke ce mata sabida yawan fara'ata ko kad'an tunanin mugayan Halin Zara basu darsu a Zuciyarsa ba illa ma kyawawan Halinta daya rinjiyeshi ya aureta

Please Login or Register in order to submit comment