Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tsabar rashin hankali da bak'in kishin da ya rufe miki ido zaki dage akan cewar nemanta nake ina cin amanar Aure wlh ki"


Aliya ahaukace tace "Adnan naji ni mahaukaciya ce yau zan nuna maka cewar nid'in mahaukaciya ce har sai na kamaku turmi da tab'arya ka rantse da girman Allah baka aikata zina da Zara ni ganau ce Ba jiyau ba tsabar lalacewa har zuwa take tayi maka oyoyo babu Kunya babu tsoron Allah naga har yanzu da kwarin gwiwarka Adnan naga har yanzu kana da bakin magana tunda ni kafi k'arfina dole ka dakeni ka kuma hanani kuka Ameer fa wlh Hukuma ce zata rabaku dan wlh sai dai idan ba a gidanan zai kwana ba amma matsawar a gidanan zai kwana kamar nagama gaya masa ne kwarto kawai"


Tas tas Adnan ya kwasheta da tagwayen mari yana huci

Aliya kuwa sai da kunnuwanta sukayi season sabida Yanda Marin ya shigeta

Adnan yace "ubanki ne kwarto Mara mutunci wlh wanan kad'an nayi miki try anything stupid and see wlh sai na canza miki kamani gaki ga k'ofar ki gwada fita kigani"


Wani irin zafaffan hawaye ne suka hau sauka a kumatun Aliya ta zubawa Adnan ido Tana "Adnan Mahaifina ne kwarto ni ka Mara akan gaskiya ta"

"Ke d'in Banza na mareki d'in Ashe babu dadi ni kika cemin kwarto"



Aliya a hankali ta sulale ta zube a k'asa ta fashe da wani irin kuka

Adnan kuwa yayi tsaki ya zauna a one seater ya dafe kansa dake bala'in Sara masa ya tsani Aliya imagine daga dawowarta ta had'a masa Zafi tsaki ya ringa jerawa akai akai yana karkad'a k'afa sai hararar Aliya yake duk da ba kallonsa take ba so yake ya shiga d'akinsa ya watsa ruwa sabida wani irin zafi da gumi dayake had'awa amma ina bazai iya ba sabida yasan yana tashi Aliya zata fita waje.


Aliya kuwa kuka kawai take Tana k'ara mugun Dana sanin Auren Adnan wani mugun tsanarsa da bata tab'a ji ba taji yana ratsata Yanda take jin ta idan taga abunda zai kashe Adnan zata iya d'auke kanta.


Sai da suka samu minti 30 ahaka

Aliya na sauke Ajiyar zuciya Adnan na gyangyadi

Horn d'in motar Ameer Aliya ta jiyo ta mik'e da sauri ta nufi k'ofar fita aikuwa k'arar Zare sakatar k'ofar ne yasa Adnan ya bud'e idonsa

Aliya kuwa ta fice aguje dan bata da burin daya wuce ta gayawa Ameer halin da ake ciki idan yaso ko kashe ta ne Adnan yayi duk da tasha alwashin bazata kwana a gidan ba.


Adnan a 360 yabi bayanta hankalinsa a tashe kirjinsa kamar ya fad'o k'asa

Aikuwa Adai-dai lokacin Ameer yayi parking motarsa ya hango Aliya ta nufo motarsa a guje Adnan na biye da ita.


Sallati ya fara yi ya fara k'ok'arin kashe motar dan ya fito aikuwa yaga Adnan ya damketa da k'arfi ya sabata a kafad'a ya juya da ita.


Ita kuwa sai ihu take Tana yafito shi da hannu


Ameer bai tsaya kulle motarsa ba yabi bayansu shi ma da sauri hankalinsa a tashe dan duk ya d'auka Adnan so yake ya daketa shi yasa ta gudo wajensa Adnan kuma ya kamata.


Adnan yana zuwa b'angaren su ya cillar da Aliya ya kulle k'ofar

Aliya ta k'ara mik'ewa ta nufi wajensa dan ta fita waje.

Adnan tureta yayi da k'arfi ta fad'i akan cikinta


Adai-dai lokacin da Ameer yafara kwankwasa k'ofar yana kiran sunan Adnan tare da magiya akan kar ya daki Aliya dan duk ya d'auka dukan Aliya yake


Aliya wani razananan k'ara ta saki sakamakon wani mugun azababben ciwon da bata tab'a ji ba da taji mararta nayi kafin kace me jini ya yanke mata still Marar ta na murd'a mata

Aliya kuwa juya kai kawai take dan azaba Tana yarfa hannuwa.


Adnan da sauri ya nufi wajenta da yaga Yanda jini ke kwararowa ta k'asanta

Jijjigata ya fara yi sakamakon lumshewa dayaga idonta nayi a hankali idon nata ya rufe ruf still jini na zuba kamar famfo.



Adnan Sallati ya fara yi yana kiran sunan Aliya yana jijjigata Ameer kuwa hankalinsa ya k'ara tashi ya cigaba da k'wank'wasa k'ofar da k'arfi.


Adnan kuwa hankalinsa idan yayi dubu ya tashi dan har iskar bakinsa ya ringa hurawa Aliya ko zata tashi tsabar rudewar da yayi yama manta idan mutum ya suma ruwa ake yayyafa masa.


Sai da yaji numfashinsa na Neman d'aukewa sabida Yanda yake hura iskar bakinsa da k'arfi ya tuna da ruwa ake yayyafawa idan mutum ya suma.


Aguje ya nufi kitchen ya d'ebo ruwa ya kwarawa Aliya.

Aliya kuwa taja wani dogon numfashi Still idonta a rufe


Adnan k'ara kwara mata ruwan yayi ta k'ara sauke ajiyar zuciya tare da bud'e idonta a hankali


Azabar zafin da taji marar ta nayine yasa ta rik'e mararta da k'arfi tana sallati tana zata mutu Adnan da sauri ya mik'e yafara k'ok'arin d'agata duk da jinin dake zuba ta k'asanta


Da k'yar ya ciccib'eta ya azata a kafad'arsa yanufi hanyar fita ya bud'e k'ofar aikuwa yaga Ameer a tsaye kana ganinsa kasan hankalinsa a tashe yake .


Ameer sallati ya saki da k'arfi a lokacin dayaga Yanda jini ya b'ata jikin Zara har yana d'iga k'asa


Adnan kuwa ko sauraransa baiyi ba ya nufi wajen motarsa da sauri ya bud'e bayan motar ya saka Aliya aciki tare da rufe k'ofar motar.


Aliya sai sallati take tana juya kai dan har wani gudajan jini ke fad'owa

Ameer kuwa da sauri yasha gaban Adnan dake k'ok'arin bud'e gaban motarsa yafara magana cikin tashin hankalin "Adnan mai kayi mata haka ka fara shaye shayene mai tayi maka kayi mata irin wanan dukan"

Adnan wani mugun kallo ya watsa masa yana "ina ruwanka dani Ina ruwanka da matata kaje kai ma kaji da naka iyalin naga mata ta ce ko kasheta nayi babu abinda ya dameka tunda ni za'a d'aure y do u care ko dai santa kake yi"


"Subhanallahi Adnan kasan mai kake cewa kuwa nikam mai zai had'anii da matarka akan mai zanso matar Aure I just care as a neighbour and nothing else"

"Bana ma san caring naka as a neighbour just stay away from me and my wife or else u would not enjoy wat am going to do to you akan me zaka tashi hankali ka haka akan matata idan ba da akwai wani Abu a zuciyarka ba"


"Subhanallahi Adnan may Allah forgive you for thinking such thing Allah ya tsareni da Neman matar Aure Adnan wlh ban tab'a tunanin kai jahili bane sai Yau Allah ya shiryeka"


Adnan tsaki yayi ya shige cikin motar tare da Jan motar a fusace har yana Neman takewa Ameer k'afa badan ya daka tsalle yayi gefe ba


Har suka b'ace daga gidan yana mamakin Halin Adnan.


Adnan kuwa tafiyar minti goma ne ya kai shi wani k'aramin private hospital da suke zuwa shi da Aliya dayake suna da file awajen basu sha wahala ba aka k'arbi Aliya aka kwantar da ita cikin mintuna da basu wuce goma ba likita da nurse suka rufu akan ta sakamakon yanda take bleeding.


Adnan sai zagaye asibitin yake.


Sai da aka samu awa d'aya likita yafito daga d'akin yana yarfe gumi nurse na biye dashi abaya.


Adnan da sauri ya nufi wajensa yana tambayarsa jikin Aliya


Likita yace ya biyo shi office d'insa suyi magana.


Sai da likita yayi 'yan rubuce rubucensa a takarda ya mik'awa nurse d'in dake tsaye yana "get me this injection I need them right now "

Nurse d'in kuwa ta k'arba da sauri tayi waje.

Adnan kuwa duk yabi ya matsu likita ya fad'a masa abinda ke faruwa Gaza hakuri yayi sai da ya k'ara tambayarsa jikin Aliyar


Kafin likitan ya sauke ajiyar zuciya yace "wife d'inka tayi miscarriage sakamakon buguwa da tayi sosai a cikinta and am sorry to say tana internal injuries sosai da ya k'ara mata ciwon da yawan zuban jinin so yanzu na samu na tsayar da jinin akwai injection da za'ayi mata guda biyu na aika a siyo yanzu for now ta samu bacci she needs to rest sosai we don't want her to be disturbed.

Adnan ajiyar zuciya ya sauke da k'arfi a zuciyarsa yana godewa Allah da cikin ya zube cos he is not ready to be a father.

" dafatan idan ta farka she would be okey"


"Insha Allahu everything would be fine"

"Toh Alhamdulillah zanje gida na dawo Na Riga da nayi settling bills d'in"


"Is OK"

Likita yace a lokacin da sukayi musabiha Adnan ya fice daga office d'in....


*Manage I Neva intend to type today but my ppl out there have to false me to har da masu kira awaya ana idan banyi posting ba yau za'a fad'a rijiya*😁😁😁

*M🅰K'OT🅰N JUN🅰*


*REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS* *P.M.L*




® REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS

ɯɛ ɖơŋŧ ʝųŞŧ ɛŋŧɛřŧąıŋ ŋɖ ɛɖųĆąŧɛ, ცųŧ ɯɛ ąٳŞơ ŧơųĆɧ ɖ ɧɛąřŧ ơʄ řɛąɖɛřŞ


# WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
# IG PML WRITERS
# https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-08144932303




*Written by*

💅💅💅 *SADNAF*💅💅💅



*Follow me on wattpad @ Sadnaf*


*Dedicated to Aunty sis*💖💖💖💖


*Page 17*

Adnan kuwa yana barin asibitin gida ya wuce direct da isarsa ya fad'a band'aki ya sakarwa kansa ruwa tunda ga sama dan har ya kai Aliya asibiti bai daina jin Zafi na shigar sa ko ta ina ba kansa har wani ciwo yake yi sabida d'aga masa hankalin da Aliya tayi.


Sai da ya Samu nutsuwa sosai ya fito daga b'and'aki daga shi sai towel ya zube akan gadonsa yana sauke ajiyar zuciya ahankali ya runtse idonsa yana tunano duk abinda ya faru.


Tsaki yaja a filli daya tuna Zara ce duk ummul aba'isin abinda ya faru idan banda rashin hankali akan me zata ringa mantawa da secret relationship sukayi tunda daga shi har ita suna da Aure ya lura Zara tana zakewa dayawa tana mantawa cewar tana da Aure ya lura she don't give a dam idan asirinsu ya tonu ko wani yasan suna Neman juna dan tariga da tayi nisa akan san da take mishi amma shi fa Sam bai shirya asirinsa ya tonu ba amatsayinsa na Wanda yake Neman matar Aure matar Auren ma matar mak'ocinsa da yanzu tsautsayi yasa Aliya ta gayawa Ameer abinda ke faruwa ina zai saka kansa ina zai kai wanan abun kunyar sai ya d'auki k'wak'waran mataki akan Zara ya ja mata kunne dan ita idan babu sauran kunya a tare da ita shi yana da sauran Kunya.

Tsaki ya k'ara saki a karo babu a dadi ya d'auki wayarsa yafara yiwa Zara message kamar haka-


*Zara kinga abinda kika jawo mana ko meyesa bakya iya controlling kanki wai kin manta da cewa kina da Aure ne ke matar wani ce did u know d consequence idan aka kama mu wane irin mataki kike tunanin mijinki zai d'auka akaina if he get to knw d relationship btwn d 2 of us ko ba mijinki ba da wane ido zan ringa kallan mutanen da suka san cewar ni mak'ocin Ku ne Sanan ina nemanki how could u do that yanzu ace mijinki ne ya kama mu haka mai kike tunanin zai faru duk da nasan kina kaunata baki k'i ki rabu da kowa akaina ba amma ba hakan ne zai sa idonki ya rufe kiyi Abu any how ba batare da tunanin outcome d'in abinda zai faru ba now sabida kar Aliya ta gayawa mijinki halin da muke ciki har miscarriage tayi yanzu haka ta na asibiti Zara pls ki iya takunki I don't want to be caught for now yanzu inaso mu d'an nisanci juna na kwanaki har na Samu na shawo kan Aliya dan ta dage sai ta gayawa mijinki yanzu tunda ta san abinda ke tsakaninmu sai mun canza takunmu pls yanzu just stay away from me bayan kwana biyu zamu had'u ko a hotel ne zan ringa miki text message pls ki iya takunki kar mijinki ya zama suspicious*

Tura mata yayi ya wurgar da wayar ya koma ya kwanta yana cije lebb'ensa sabida ciwon da kansa ke masa gashi yana jin yunwa amma yanda yake ji bazai iya cin abincin ba.


Zara dake zaune a k'asa tana yayamutsa fuska sabida ciwon da ko'ina na jikinta ke mata ga hancinta kamar ba a jikinta yake ba sabida nauyin da hancin ya mata dan tasha naushi awajen Aliya k'eyarta kuwa a kumb'ure yake suntum sabida yanda ya gwaru da bango ruwan Zafi ne agabanta ta ringa tsoma towel aciki tana cirowa tana dannawa a k'eyarta sai cije lebb'e take sabida zafin da yake mata fuskarta kanta a kumbure take bata tab'a tunanin Aliya tana da k'arfi haka ba sai yau uban me ma ya dawo da ita gidan ko dayake bata ga laifin Aliyar kamar yanda taga laifin Adnan ba dan ta Dade tana gaya mishi ya saki Aliyar ya kai mata takardarta yak'i amadadin ma da zai dawo da ita ya sanar da ita ko ta waya ne bai gaya mata ba sai kawai ganinsu Tayi tare da yanzu ya gaya mata ai bazata soma fita waje tararsa ba ballantana tazo taci wanan uban dukan.


Tana cikin daddana jikinta taji alamar message ya shigo wayarta d'aukar wayar tayi da d'aya hannun nata ta bud'e ta karanta message d'in da Adnan yayi mata.


Ranta ne ya masifar b'aci Tayi sauri ta ajiye towel d'in hannunta ta fara masa reply da-

*Adnan abinda zaka cemin kenan I should stay away from you har sai ka shawo kan Aliya u know u love her dat much y do you come for me and da kasan zaka d'auko ta meyesa baka fad'amin Ba ko ta waya ne sai kawai ganinku nayi tare da ka fad'amin ka d'auko ta zan fito ne har ta kama mu is oll your fault kar ka sake kayi blaming d'ina yanzu dubi irin raunin da matarka ta jimin ko'ina na jikina ciwo yake batun I should stay away from you ma bai taso ba Adnan am ready for war in dai akanka ne Ameer kansa ban k'i yasani ba kai ba ma Ameer ba ni kowa ma yasani am happy da matarka ta sani Saura Ameer shima Adnan i don't have control indai akanka ne I can't hide d love I have for you I can even kill because of u bana jin yanda nake jinka araina zan iya kwana biyu batare da ganinka ba so d earlier d better idan kasan bazaka sallami matarka ba kasan yanda zaka yi dani or else idan nayi abun da Ameer yasan muna tare karka ga laifina I miss you so much pls kayi k'ok'ari mu had'u ko gobe ne awani wajen I need you*


Zara tayi mishi sending tana lumshe ido dan agaskiya ba k'aramin so take yiwa Adnan ba.


Adnan da ke dafe da kansa bacci ya fara d'an kwashe shi shigowar message wayarsa ne yasa ya bud'e idonsa ya jawo wayar ya bud'e message d'in ya karanta.


Jikinsa ne ya fara rawa ya hau yi mata reply

*Zara have you gone mad wai kin manta da kina da aure ne ina cikin tashin hankali zaki cemin gobe mu had'u matata fa tana asibiti oll because of you Zara ai nima ina kaunar taki pls kiyi controlling kanki akaina kina da Aure ki rufamin asiri kar mijinki ya gano muna tare dake am begging you ki bani kwana biyu idan komai ya dai-dai ta zamu had'u pls*


Zara tsaki tayi a lokacin da ta karanta message d'in ta wurgar da wayar dan gani take Adnan bai san mai yake cewa ba ta makance ta kurmance akan sa bata k'i komai zai faru ya faru ba.


Ameer kuwa shima tunda ya shiga gidan yayi Alwala yayi sallah Aliya ta tsaya masa arai tausayinta yake ji sosai dan Sam bata dace da miji nagari ba Mai tayi masa haka data cancanci irin wanan dukan aganinsa duk namijin da ya Samu mace irin Aliya ai ya Samu Rabin aljannar duniyar amma kash Adnan bai san irin baiwar da Allah ya mishi ba shi gashi nan bai yi dace da mace tagari ba inama ace shi yasamu Aliya a mata

Da sauri yayi istigifari daya tuna matar wani ce ya gyara kwanciyarsa yana cigaba da tunanin Halin da take ciki dan idan ya tuna yanda ta taho aguje sai tausayin ta ya rufeshi yayi yayi ya cire tunaninta aransa ya k'asa yana so yasan halin da Aliyar take ciki amma yana tsoron irin fassarar da Adnan ya fara masa idan ba hauka da jahilci irin na Adnan ba akan me mai zai kawo zai so matar Aure.

Atakaice ahaka Ameer ya ringa juyi sai bacci barawone ya sace shi.


Adnan kuwa daya turawa Zara text d'in sai da ya tsaya ya jira yaga ko zai ga reply d'inta yaji shiru mik'ewa yayi ya d'auko paracetamol ya sha sabida kansa kamar ya rab'e gida biyu yana kwanciya bacci yayi awon gaba dashi.


Washegari sai K'arfe goma na safe Adnan ya tashi agogo ya kalla yana daga kwance yana ganin k'arfe goma ya duro daga kan gadon ya fad'a band'aki agurguje yayi wanka yayi sallah ya shirya dan ya tafi asibitin dan yaso tun takwas ya tafi asibitin tunda jiya bai samu ya koma ba tashin hankalinsa bai wuce Aliya ta farka ta nemi a sallameta ba ta tafi gidansu dan yasan kad'an da aikinta idan kuwa hakan ta faru yasan kashinsa ya bushe babu abinda zai hana Alhaji Abubakar ya d'aureshi.


Sanye yake cikin farin shadda da bak'in hula ya kuwa yi masifar kyau sai bulbula k'amshi yake

Wajen motarsa ya nufa da sauri

Adai-dai lokacin da Ameer shima ya fito zai tafi aiki dan shi ma ya makara tashi sakamakon baccin da yasha sosai.


Adnan d'auke kansa yayi kamar bai ganshi ba

Ameer kuwa ya girgiza kansa dan yaga k'arfi da yaji Adnan ke san gaba dashi shima d'auke kansa yayi duk da yana masifar san yaji wane Hali Aliya take ciki.

Adnan ne yafara barin harabar gidan

Kafin Ameer ya Mara masa baya.


Zara dake jikin window a tsaye tana kallon Adnan ajiyar zuciya ta sauke a lokacin daya fice daga gidan wani irin k'ullutu ya tsaya mata a wuya sakamakon wani bak'in kishin Aliya dataji ya rufeta dan tasan wanan saurin da Adnan yake yi duk dan yaje ya ganta ne ji take kamar ta Samu wuk'a taje ta cakawa Aliya ta huta Aliya ta zame mata Katanga mai k'arfi tsakaninta da Adnan Aliya tana so ta mata karan tsaye a rayuwarta wai idan dai Adnan na kaunarta akan meyesa ba zai saki Aliya ba mai yasa yake nuna mata yana san matarsa alhalin ita ta Dade da daina san nata mijin ko kallonsa ma bata san yi dan Adanan yana ta hanata ne da tuni ta cakumi wuyan Ameer ya bata takadarta.

Akan kujera ta zube tana tunanin yanda zata mallaki Adnan ita kad'ai dan yanda take kaunarsa bata jin zata jure ganinsa da wata Aliya.


Aliya kuwa tunda ta farka taji marar ta yayi mata wani irin nauyi wani azaba ya ratsa k'wak'walwarta ta runtse idonta da k'arfi tana kiran sunayen Allah.

Nurse d'in dake kula da itace tayi sauri ta matsa kusa da ita tana mata sannu

Sai da ciwon ya d'an lafa mata ta bud'e idonta tana tambayar nurse d'in da mai ya sameta haka take jin irin wanan zafin.


Nurse d'in sai da ta d'an kwantar mata da hankali tace mata b'ari tayi.

Aliya hamdala ta ringa furtawa a filli wani irin farinciki yaringa ratsa zuciyarta dan tunda taji labarin tana da ciki take addu'ar Allah ya kawo sanadin da zai zub'e dan bazata iya zubar wa da kanta ba.

Sai a lokacin ta tuna duk abinda ya faru a daren jiya wasu zafaffan hawaye ne suka zubo mata take taji ranta na b'aci wani mugun tsanar Adnan na k'ara mamaye zuciyarta mai zata yi da mazinacin namiji mai Neman matan aure Wanda babu tsoron Allah a cikin Al-amuransa.

Nurse d'in kuwa ganin tana zubar da hawaye yasa ta fara rarrashinta tana tunanin ko d'an cikinta ya zub'e shiyasa take kuka.



Aliya kallon nurse d'in Tayi tace "Ina Wanda ya kawo ni yake"?

" Tun jiya dai daya tafi gida yace zaije ya dawo har yanzu bai dawo ba"?

Nurse d'in tace tana gyara mata zaman kanta akan pillon data d'ora kanta.

"K'arfe nawa yanzu"?

Nurse d'in agogon hannunta ta duba tace

" k'arfe Tara da rabi "

Aliya lumshe idonta tayi tana tunanin rashin mutuncin Adnan ace tun jiya daya kawota asibiti har yanzu bai waiwayeta ba Alhalin shine sanadiyar kwanciyarta a asibiti.

Bud'e idonta ta k'arayi tace

"Nurse inaso Ku sallameni yanzu"

Nurse d'in waro ido tayi tace "mu sallameki kuma kinsan halin da kike ciki kuwa ai bakiji saukin da za'a sallameki ba dan doctor jira kawai yake ki farka yazo ya baki sauran treatment d'in."

"Nurse nidai Ku sallameni naji sauki ko banma ji sauki ba idan naje gida za'a kira likita yazo ya duba ni banaso na k'ara minti biyar a asibitin nan Ku sallameni kawai"

Aliya tace tana fashewa da kuka dan ko kad'an bataso Adnan yazo ya sameta acikin asibitin bama tasan ganin fuskarsa.


Nurse kuwa ganin ta birkice mata yasa tayi waje da sauri tare da rufe k'ofar taje ta fad'awa likita halin da ake ciki.

Tare suka dawo da Likitan inda suka zo suka tarar da ita a zaune tana kicin kicin cire Karin jinin dake hannunta.

Da sauri likita ya k'arasa gurinta yana tambayarta mai yasa take cire Karin jinin da ake mata.

Aliya tana kuka tace ita dai ya sallameta ta tafi gida batasan zaman asibiti

Aliya birkice musu Tayi sosai tana fusge fusge akan su sallameta


Da k'yar suka shawo kanta akan cewar ta daina fusge fusge zasu sallameta yanzu.

Aliya komawa tayi ta kwanta ta cigaba da kuka dan ko kad'an bataso Adnan yazo yasameta a asibitin tafiso kawai ta tafi gida ya biyota da takadarta.


Likita na cikin had'a allurar maganin baccin da zai yiwa Aliya Adnan ya fad'o d'akin.


Likita fad'a ya rufeshi dashi akan me zai zo ya ajiye matarsa tun jiya bai k'ara waiwayarta ba gari ma da waye sai Yanzu zai zo.

Adnan bai iya tankawa likita ba illa nufar gadon da Aliya ke kwance da yayi dan yaga yanda hawaye ke zubo mata ta gefen fuska duk da idonta a runtse yake .

Adnan zama yayi a gefen gadon yace

"Aliya ya jikin naki"


Aliya da sauri ta bud'e idonta ta watsa masa wani mummunan kallo tace "Ina ruwanka da jikina Adnan cikin mutunci da mutuntawa ka bani takardar sakina yanzu dan ko kad'an banasan ganin fuskarka na godewa Allah da cikin jikina ya b'are dan dama sabida cikin nake tunanin k'ila zan iya zama dakai tunda Yanzu babu cikin ka bani takadata kawai ka tafi can kaje kacigaba da bin matar mutane.


Adnan wani yawu ya had'iye ma tauri yace " Aliya dan Allah ki tsaya tukunna na kisamu sauki sai muyi magana"

Aliya tana k'ok'arin magana likita ya dakatar da ita yana

"Dan Allah ki kwantar da hankalinki ki samu lafiya idan kin warke sai kuyi maganar da zakuyi dan Allah ka d'an fita waje Ina zuwa"


Adnan mik'ewa yayi a hankali yana kallon Aliya dake mishi kallon tsana.

Likita sai da ya mata allurar bacci kafin ya fito daga d'akin.

Likita na fitowa yace
Adnan yazo ya same shi a office d'insa

Adnan mik'ewa yayi yabi bayan likitan

Bayan ya zauna likitan yace "sorry banaso nayi interfering a personal issues d'inku bansan dai mai ya had'aka da matarka ba amma pls try to solve things out saboda matarka tana da hawan jini a stage d'in da take yanzu ba'a san abinda zai ringa b'ata mata rai so ka bita a hankali try oll your best kayi resolving d'in issues d'in da ya taso muku"


Adnan gyad'a kansa yayi yace "insha Allah likita zan k'ok'arta


Likita mik'a masa wani paper yayi akan ya siyo wadanan magungunan ya kuma samo mata Abu taci idan ta farka.


Adnan mik'ewa yayi tare da masa godiya ya fice.


A ranar Adnan ko aiki bai tafi ba yana nan a asibiti yana gading Aliya dan yana tsoron ta farka tana ganin baya nan ta tafi gidansu.


Aliya kuwa data farka da k'yar nurses suka shawo kanta ta shiga wanka ta fito taci abincinta da magunguna.


Ko kwanciya bata yarda Tayi ba tace su sallameta taji sauki zata tafi

Please Login or Register in order to submit comment