Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ta taɓe baki da cewa, "ke kam wahala bai ishe ki ba Alkur'an, ai sai ki yi tayi, kuma wlh ki ɗago ƙafa na gaji fitsari nake ji."

Maryamu da ke ƙara tafiya a hankali don kar ta ƙara turguɗe wa, sai tace, "don Allah mu je gidan Yaya Faisal ki yi fitsarin a can, yau nayi alƙawarin sai na sha mangwaron Haliru Taurin can, sai dai duk abun da zai yi yayi."

"Ƙutt... Wlh babu ruwana ga hanya nan, Ni kinga tafiyana zan yi."

Jawo mata hijabi Maryamu tayi tana marairaice wa tare da faɗin, "haba mana Bintu, wlh bazan jima ba, kuma bazan bari ya ganmu ba ta gidan Yaya Faisal zan tsinka, idan kika koma gida ke kaɗai kin san halin Baba kuma kin san ya dawo, mu je ki raka Ni Ko a waje ne ki jira Ni Please help i." Ta ƙare maganar da shegen turancin ta da bata rabo dashi tunda bata iya ba, amma ta dage sai tayi kamar wata mangofan

Babu yanda Bintu ta iya dole ta yarda zata bi ta, domin ta san Maryamu akwai shegen naci baza ta ƙyale ta ba, sai tayi ƙwafa tace, "Allah yasa ma Yaya Faisal ɗin yana nan inga ƙaryan tsiya."

"Bakin ki ya bi ki, ai Insha Allahu ma bai dawo ba, kin san Allah jiya da mafarkin mangwaron nan na kwana kamar wata mai ciki, dama na sha alwashin in dai muka biyo hanyar nan sai na tsinko."

Suna ƙarisa wa gidan suka buga sallama suka shige

Matar Yayan su Asabe ta amsa musu tana cewa, "ah ah Ƙannina, daga ina haka?"

"Daga school Aunty, me and she just came back and followed here."

"Manyan tura wa, Ni fa ba gane miki nake yi ba, da kin min Hausa da na fi fahimtar ki."

Dariya Maryamu tayi tace, "gwara Yaya Faisal ya mayar da ke makaranta tun kafin ki ba shi kunya wata rana Alkur'anin Allah, amma ace kamar shi ɗan gaye yana zaune da ke, to sanda ya zo da Abokansa na birni ya zai yi?"

Tsaki Asabe ta ja tare da cewa, "ai kuwa kin san ba daga nan yake ba, domin kin san na fi ƙarfin raini tunda shima Faisal ɗin Kyawu na ya ruɗe shi ya aure Ni, meyasa bai je ya auro mai ilmin bokon ba? Ƙaryan banza ƙaryan hofi."

Bintu da fitowar ta daga bayi, tana ajiye buta tace, "kin ji Aunty ki ƙyale ta, in kika biye ta Maryamu Allah kin dinga jin haushi kenan, ki barta kawai."

Ita kuwa Maryamu sai dariya take yi domin har ta yaye hijabin ta tana nannaɗe skirt ɗin ta zuwa sama, sai tace, "ina wai Yaran nan ne ban ji motsin su ba?"

"Su ma basu dawo daga makaranta ba amma yanzu za ki gansu."

"Wai don Allah ki yi sauri mana, wlh idan Yaya ya dawo ya ganmu babu ruwana."

"Me zata yi ne?" Asabe ta tambaya tana kallon Maryamun

Kaɗa kai Bintu tayi tare da cewa, "wai mangwaro zata tsinko."

"Huhh! Ki rufa wa kanki asiri, wlh Haliru tauri na nan a gida, idan kuma kika ce za ki tsinko ke dashi ne domin kin san halin shi, yanzu na gama jin shi da yaran maƙota."

"Sai fa na tsinko, bari ma ki gani, yo Ni da zan tsinka ta gidan ki ina zai ganni?" Sai ta nufi katangan da ya raba gidan dana Haliru tauri, ta kama garu daƙyar tana ƙoƙarin hawa. Sai ta rage murya tana cewa, "Bintu zo ki cinciɗo Ni."

"Sai dai kar ki hau, bazan zo ba."

"Wlh kar ki saka rai kuwa."

Jin hakan yasa Bintu ta je wurin ta taimaka mata, tunda ta san idan ma bata yi ba baza ta bata ba, sai mita take yi sabida nauyin Maryamun, komawa gefe tayi bayan ta gama cinciɗa ta, daga ita har Asabe suka zura mata ido suna kallon ikon Allah

Ita kuwa kamar wata ƙadangaruwa da jan gindi take tafiya a saman katangan, sai da ta isa dai-dai wajen bishiyan sai ta kama ta ɗare ta shige can saman bishiyan ko ganin ta ba a yi

Dai-dai nan Haliru ya fito daga ɗaki yana kakkaɓe takalma, sai ya zauna yana gyara wa yana ɗaure wa da igiya, tare da raira waƙar sa na Mamman shata, batare da ya kula da Maryamu da ke saman kansa tayi ɗare-ɗare ba

Sai da ta cika bujen ta da mangwaron, kuma tayi toking ta tusa su a cikin rigan ta ta cika fam. Sannan ta soma ƙoƙarin sauka, har ta kusa kama bangon, ɗaya ya faɗo ya ƙwandalo wa Haliru a kai. Ya saka salati yana sallallami tare da ɗaga kansa suka yi arba da Maryamu

Ai tuni ya miƙe tsaye yana cewa, "wacce matsiyaciyar ce wannan? Ke.. ke.. ke."

Amma inaa. Tuni Maryamu ta dira ƙasa, kan kace me ta yayimi hijabin ta sun fice a guje ita da Bintu da jikinta sai rawa yake yi, akwai shegen tsoro ne da ita. Suna fita suka hango sa shima ya fito daga gidan riƙe da icce, ai sai suka ɗibi gudu ana artabu daga su har shi ɗin, ya bi bayan su yana ƙunduma musu zagi

Yayinda Maryamu kuwa ta riƙe riganta ƙam don kar mangwaron su zubo, duk da wasu duk sun yi ƙasa amma haka ta ƙwaƙume su ko takalma babu a ƙafanta; tunda bata tsaya ta ɗauka ba suka fece

Haliru tauri na take musu baya a gujen shima da icce a hannu kamar mahaukaci.
[11/01, 9:05 am] OumƊahirah نفيسة: 🌱🌱🌱🌱🌱

            *SHAREEF*
                _SexyBoy_
🌱🌱🌱🌱🌱


_Writer: Nafisat Isma'il Lawal_
_Wattpad: UmmuDahirah_

*SARAUNIYAR TSOKANAR PERFECT🧝*



*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞

```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)```

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

       *P.W.A✍️*





*DATA SHARE*

Call, message or whatsap 07065334256

*MTN*
500MB 150
1gb 280
2gb. 560
3gb. 840
4gb. 1120
5gb 1400
6gb. 1700
Verlid for 30 days










__________
*BOOK1*
_______________*FREE PAGE6*
                Su Umma Jummai suna tsakar gidan suna aiki, sai suka ji didima su Maryamu sun shigo a sukwane kowacce tayi wurin ɓuya

Ɗakin Umma Jumman suka shige gaba ɗayan su, har cikin uwar ɗakar ta kowacce ta shige cikin shirgin kaya suna mayar da numfashi

"Ta.. da alamu sun nemo rigima." Cewar Shatima da yake dariya ƙasa-ƙasa

Kafin ma su yi magana, sai ga sallaman Haliru tauri a waje kamar zai tsaga gidan

"Wa'alaikumus Salam. Shatima je ka duba wane ne?" In ji Inna da ke yafa mayafi a kanta tana shirin fita itama

Da gudu Shatima ya fita, sai ga shi ya dawo yana cewa, "wlh Haliru tauri ne, ya ce a fito mishi da shegun Yaran nan."

Umma Jummai tace, "ai wlh tunda na ga sun shigo da wannan gudun sun nemi wurin ɓuya, to tabbas sun nemo rigima ne, dan kutmar uban ku baza ku fito min a ɗaki ba? Ku fito nace?"

"Ki ƙyale su, bari ki ga in yi maganin su, baza ku jawo mana rigima muna zaune ƙalau ba wlh, wannan mutumin da bai da imani yanzu ma sai ki ga ya shigo gidan, gwara da Allah yasa ku ka yi Baban naku ya dawo, kai Shatima maza ka kira shi a bakin masallaci yanzu ya fita."

"To Inna."

Ita kuma ta wuce kitchen ta ɗauko icce ta fito. Ta nufi ɗakin Umman tana cewa, "wlh idan na shigo baku fito ba kowacce sai ta ji a jikinta tunda ku baku da mutunci."

Tsit suka yi dukkan su suna sake lafewa a maɓoyan su. Maryamu na bayan kabot ɗin Umma Jummai ta maƙale cikin kayan wanki da aka jibge a wurin. While Bintu kuma tana ƙarƙashin gado daƙyar ma ta shiga saboda kaya da aka tula a ƙasa, ƙafafunta a waje. Shi yasa Inna tana shigo wa ta soma hango ƙafafun Bintu, ai sai ta nufi wurin ta rafka mata iccen tana cewa, "fito dan uban ki."

Kuka Bintu ta saka jikinta na rawa, saboda ba kaɗan ba ta ji shigan iccen a ƙafafun ta. Sai ta fara ihu tana cewa, "don Allah Inna kar ki ƙara min wlh zan fito."

"To fito tunda ba na wasa da ke." Tayi maganar fuskarta babu wasa. "Ina ita ɗayan dan uban ta?" Sai ta koma dube-duben ɗakin. Kai tsaye wurin shirgin kayan ta nufa domin ta san baza ta wuce wajen ba tunda ba wani sauran wurin ɓuya a ɗakin. Ilai kuwa ta hange ta tana zazzare idanu

Tun kafin ma ta ɗaga iccen, Maryamu ta fito tana ihun faɗin, "don Allah Inna ki bari, gani nan na fito."

Hannu tasa ta mangare mata kai tana cewa, "tunda ku baku isa a gaya muku magana ba ko? To mu je wajen tun kafin in zane muku jiki yanzu." Ta tasa ƙeyan su suka fito

Tuni Maryamu ta zubar da mangwaron a cikin ɗakin Umman suka fito jiki na rawa

Lokacin Bashir ya shigo gidan yana cewa, "wa ya taɓo Haliru tauri ne?"

"Yauwa. taho ka tasa min ƙeyan su mu je can wajen a yi a gaban shi, tunda sun tono shi can ya ƙare musu."

Sai dariya yake yi yana cewa, "yau akwai kallo kenan, wlh zaku ci uban ku ga Baba da su Yaya Naziru nan a waje."

Bilhaƙƙi da gaske kuka Bintu take yi saboda duk ta gama ruɗe wa, sai rantse-rantse take yi a kan babu ruwan ta

Ita kuma Maryamu ihun kawai take yi amma babu hawaye, itama sai tsalle-tsalle take yi tana cewa, "don Allah Inna ki yi hakuri, wlh bamu yi mishi komai ba. Umma ki saka baki wlh bamu yi mishi komai ba."

"Baku yi mishi komai bane zai biyo ku a gujen nan? Ku dai ba kwa jin magana ko?" In ji Umman tana miƙe wa tsaye daga gaban kwashe tuwon da take yi

Inna kuma tace, "sai sun fita wlh ko tayi musu dukan tsiya."

Bashir sai tara-tara yake musu yana ƙara ruɗa musu ciki da cewa, "yau zaku ci uban ku Alkur'an, ba ku marasu jin magana ba? Yau kashin ku ya bushe." Shi ya riƙe su gam saboda ƙoƙarin guduwa da Maryamu take yi

Ana haka su Baba suka shigo cikin gidan

Dayake Yaya Ashiru yana da saurin fushi, shi ya nufe su da sauri ya amshi iccen hannun Inna yana cewa, "ku dan uban ku uban wa ya kai ku gidan mahaukacin can da har ku ka haye mishi gida?"

"Wlh wlh babu ruwana, Maryamu ce ban dani." In ji Bintu tana kuka sosai

Sai kawai ya haɗa su dukka ya soma rafka musu iccen yana cewa, "wato ku ba kwa jin magana ko? Duk yanda aka yi daku sai kun nemo mana magana? To gobe ku sake zuwa in kun samu ƙafan yawon yau."

Baba ne yayi saurin dakatar da shi yace, "ya ƙyale su." Ganin yanda suka cika gidan da kuka suna ihu. Tsawa ya daka musu yace, "su yi shiru."

Tsit suka yi suna zaune a ƙasa kowacce sai rawan jiki take yi

"Ban san meyasa ba kwa jin magana ba Yaran nan? Amma kuna Mata meye ya kaiku hawa bishiya?"

"Wlh Baba bani bane, Maryamu ce tace in raka ta, amma Ni ban hau ba."

Baba yace, "dama na san sai ita. To gobe sai ku sake kun ji ko tunda dukan kuke so, har yanzu baku san kun girma ba, tunda yanzu mun ba shi haƙuri gobe sai ku ƙara koma wa. Maza ku tashi ku yi alwala ku yi sallah. Kar in ƙara jin kuma kun ƙara wannan sakarcin."

"Ai Baba da ka bari na ci uban su tunda sun ga ana ƙyale su ne, Yara mara su jin magana ba a isa a hana su ba? Daga wannan fitinan sai wannan." In ji Yaya Ashiru ransa a ɓace kamar zai sake kai musu wani dukan

Inna tace, "ai laifin duk na Maryamu ne, ita ce mai kunnen ƙashi, gani take yi ta fi kowa tashin balaga, rashin kunya fal cikin ta."

Yaya Naziru yace, "wlh kuwa Inna, domin yanzu muka haɗu da Jamilu ɗan gidan mai gari yake faɗa min wulaƙancin da tayi mishi ɗazu, wai kawai don ya zo wurin ta zance shine har da kwaɗa mishi Mari, ta ci mishi mutunci har da saka mahaifin shi a ciki, ba ma shi kaɗai ba, majority Mazan ƙauyen nan suna kawo min ƙaran ta."

"Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un..! Mari kuma? Abun naki har ya kai ki mari namiji Maryamu?" In ji Inna cikin al'ajabin maganar har tana dafe ƙirji

Baba shima ransa a ɓace yace, "wato tarbiyyar da muka yi miki kenan Maryamu? Kanki ɗaya kuwa?"

"Wlh Baba ban mare shi ba, ƙarya yake min." Tayi maganar tana yarfe hannu cikin gunjin kuka

"Ni nake miki ƙaryan ko shi?" In ji Yaya Naziru yana amsar iccen hannun Yaya Ashiru zai maka mata

Sai tayi saurin tashi ta je ta ɓoye a bayan Umma Jummai tana kuka wi-wi tana rantse-rantse, "Alkur'anin Allah ƙarya yake min, wlh Yaya karya ya faɗa maka..."

Tsawa ya daka mata yace, "za ki yi mana shiru ko sai na canza miki kamanni a nan? Shegiyar yarinya mara jin magana, dama tara ki nake yi ba na sanar wa Baba, amma yanzu abun naki ya wuce hankali kullum maganar ta ake yi a garin nan."

Baba yace, "ai kuwa zan ɗauki mataki a kanki Maryamu tunda ba ki da kunya, ku ƙyale su mu wuce mu je masallaci tunda an kira sallan."

Haka suka fita a gidan har su Shatima

"Ai kinga gobe ma ki ƙara, dalla sake Ni tunda ana faɗa muku gaskiya amma kuna ganin mu Abokan wasan ku, gwara da suka ci uban ku yanzu."

"Ai laifin duk na wannan yarinyar ne, kuma wlh muddin kika ce za ki ci gaba da wannan ɗabi'ar naki za ki sha wahala, Allah na gode maka ma tunda akwai masu maganin ku, baza ku fi ƙarfin mu ba, ke kuma baza ki tashi ba kin wani langaɓe a wurin?" Ta ƙare maganar tana kallon Bintu da ke zaune dirshan sai ɓarzan kuka take yi

Miƙe wa tayi tana share hawayenta ta nufi hanyar ɗakin su

Itama Maryamu tuni ta wuce ɗakin tana zumɓura baki tare da ƙunƙunai tana zagin Haliru tauri, sai jan Allah ya isa take yi

Babu wanda ya kula ta. Su ma alwalan suka yi suka shige ɗaki yin Sallan

Bintu itama ta fito tayi nata alwalan ta shiga nasu ɗakin. Kallon Maryamu da ke zaune a bakin katifar ta tana duba jikinta inda take jin kamar an karya ta tsaban yanda dukan ya shige ta. "Wlh Allah ya isa na, muguwa azzaluma duk ke kika ja min, tun farko nace bazan je ba amma kika saka Ni na bi ki, ga shi nan ban ci nanin ba nanin ta ci Ni."

Sai kawai Maryamun ta fashe da dariya, duk da a yanzu ɗin hawaye ne kwance a saman kuncin ta, waɗanda basu fito ba sai a yanzu a karan banza, dariya Bintun ta bata shiyasa ta fashe mata da dariya tana cewa, "ai ba Ni za ki yi wa Allah ya isan ba."

"To uwar ki zan yi ma wa?" Tafaɗa a fusace tana hararanta

"Sai dai Uwar ki, son banzan ki ne yasa kika bi Ni, kuma wlh bazan ba ki ko alili ba."

"Shegiya banziya, kar Allah yasa ki bani, kuma wlh bazan taɓa yafe miki ba."

Don ta bata haushi shiyasa ta dinga mata dariya tana cewa, "ai bani za ki yi wa Allah ya isan ba, Yaya Ashiru za ki yi ma wa tunda shi ya dake ki, shegiya da ƙoton kai kamar na Biri."

"Uban ki ne da Ƙaton kan..."

"Wai baza ku dena wannan iskancin naku ku zo ku yi sallah ba? Bari Baban naku ya shigo to." Inji Umma Jummai da ta leƙo ɗakin nasu tana furta hakan

Shi yasa Bintu ta tayar da Sallan bata ce komai ba

"Au ashe ke ce ma ba ki fito kin yi alwalan ba? To zaman me kike yi?"

Baki ta tura tana kwanciya a saman katifar tace, "ba na sallan to."

"Yayi miki kyau ai." Ta furta tayi gaba

Ita kuma Maryamu sai jan tsaki take yi tana ci gaba da ƙunƙunai, tare da alwashin, "wlh sai ta rama, tunda Haliru tauri ya saka aka bige ta sai ta ƙara koma wa, matsiyaci kawai, fatararre, in ban da tsiya ma a kan mangwaron banza sai ya nuna shi matsiyaci ne."
Ta ƙi yin shiru da bakin ta sai zagin shi take yi tana tsine mishi daga shi har mangwaron nasa

Bashir ne ya shigo dakin yana dariya yace, "ah ah, ƴan mata an sha duka kenan? Ya jikin to? Ashe kin san mangwaron na matsiyaci ne kika je tsinkar mishi? Da kin bar mishi kayan shi mana."

Wata uwar harara ta jefa mishi tana miƙe wa a fusace tace, "wlh ka bari, idan ba haka ba Allah zan haɗa ka da Baba."

Zai yi magana, sai ya jiyo muryan Inna tana cewa, "wai Bashir uban me ya kaika ɗakin nan? Neman magana ko?"

Sai da ya taho ya ranƙwashi kan Maryamun, sannan ya fita a guje yana cewa, "wlh a'a Inna, kawai na je duba jikin su ne."

"To ka mayar da hankali tunda ka fi son su raina ka. Ka zo ka ɗauki abincin ka. Ina shi Hallirun ne?"

"Wlh bai dawo ba Inna, ina tunanin yana kan hanya yau yayi dare." Ya bata amsa yana nufan hanyar ɗakin Umma Jummai da aka jera abincin kowa an zuba mishi nashi

Umma Jummai da ta fito itama daga ɗakin nata, ta ɗauko miyan tuwon, sai ta ajiye tana cewa, "nima abun da nake ta zicci-ziccin tambayar ka kenan, na ga yau ka dawo ban dashi?"

"Eh Umma. Yana da sauran gyara ne a garejin shiyasa ya zauna, yace gobe bazai leƙa ba gwara ya ƙarisa yau."

"Tom shikenan. Ɗauki naka ga yi nan ka zuba miyan."

Burum Maryamu ta fito tana cewa, "ina nawa nima?"

Harara ta samu a wurin Inna

Shi kuwa Bashir sai yace, "kin dafa ne kin ajiye?"

"Kai dai ba ka jin magana wlh, ka cika neman tsiwa." In ji Umma

Inna kuma sai tace, "ki bar shi kawai, dama raini yake so."

Dariya shi kuwa yake yi tunda ya saba, akwai shi da neman tsokana, bare dama saƙo da saƙo suke da Maryamun, kullum sai an ji su da ita, su yi ta cacan baki tunda baza ta iya shiru ba. Shi kuma ya samu damar ranƙwashin ta kenan yana faɗin, "ai ta raina shi ne tunda yana faɗa tana faɗa." Haka suka saba koyaushe.






            *********

          Bayan an yi sallan isha'i. Duk sun zauna suna hira a tsakar gidan, har da su Baba tunda haka suke yi

Maryamu da Bintu har sun manta da abun da ya faru tunda dama sabon su ne haka, lokaci ɗaya zasu yi faɗa kuma su shirya, sun matsa gefe sai hira suke yi suna ƙus-ƙus

Baba yace, "ku taso ku dawo nan mu yi magana."

Hakan ne yasa suka taso suka zauna a kan tabarman wanda su Baba suke kai

Ya Kalle su yace, "ke Maryamu da ke zan fara, kina da wanda kike so ne?"

"Baba..." Ta furta tana ɗan zare ido

"Ina jinki faɗa min mana? Domin aure zan muku tunda na gaji da shirun ku, ku ba karatu ba sannan ba aure ba, don haka lokaci yayi da zaku fito da Mazajen da kuke so a yi auren ku a huta, inyaso ma sai a haɗa dana su Naziru kawai, Allah zai hore mana domin hakan zai fi sauki."

Umma Jummai tace, "gaskiya ne Malam, hakan ma yayi wlh, nima abun da nayi tunani kenan, tunda zaman kawai suke yi, duk sa'annin su sun yi aure ban da su, karatun nan dai sun yi iya yin su, auren shi ya kamace su."

Tura baki Maryamu tayi tace, "wlh Baba Ni ba na son aure yanzu, karatu nake so, nima ina son in yi karatu mai zurfi."

"Idan ma za a bar wani yayi karatu ai baza a bar ki ba, a wannan halin naki." In ji Yaya Ashiru yana ban ka mata harara

Sai tace, "to Yaya Ashiru me nayi ne Ni? Wlh ba abun da nayi, kuma ban da saurayin ma ai."

"To ai Ni ina dashi tunda ke ba ki dashi." In ji Baba yana kallonta, tare da cewa, "na faɗa miki babu wani karatu da za ki yi, gwara tun wuri ki nemo saurayi tun kafin in nemo miki. Ke ma haka Fatima gaba ɗayan ku ku fito da Mazajen Aure, in Allah ya yarda Allah ya hore za a haɗa auren ku a huta."

Inna da Umma suka haɗa baki wajen furta, "Allah ya tabbatar da alkhairi."

Ita kuwa Maryamu sai faman zumɓura baki take yi kamar yanda ta saba tana ƙunƙunai, amma ta kasa furta abun da ke ranta

Bashir yace, "ya dai Meramu? Akwai magana a bakin ki fa, ko auren ne ba kya so?"

"Ai ko ba ta so sai an yi shi, don nima na gaji wlh, wata rana sai ta jawo mana abun da ya fi ƙarfin mu in dai wannan yarinyar ce, auren za a yi mata tunda haka ta zaɓa." Innar su tafaɗa hakan cike da jin haushin halin Maryamun da ta fita Zakka a gidan nasu

Itama sai ta tashi tana wuce wa ɗaki tare da cewa, "wlh Ni dai har ga Allah ba na son aure, babu wanda zai min aure sai nayi karatu mai zurfi na zama Shugabar ƙasar ma gaba ɗaya."

Sai maganar nata ma ya basu dariya

Baba yace, "ina ruwan mashirmaciya, kya yi a gidan Mijinki amma ba a nan ba Meramu, nima in ɗana irin na Bashir."

Sai dariya suke yi. Haka suka zauna cikin raha suna ta hira. Daga ƙarshe Samarin ne suka soma zame wa suka shiga ɗaki

Itama Bintu tuni ta wuce ɗakin su, lokacin har Maryamu tayi barci, tunda kasa ce, ba ta tsawon hira sai dai ka ji ta tana jan rago. Rufe musu ƙofan tayi itama ta haye nata katifar ta kwanta.


        Washe gari bayan su Baba sun tafi wurin aiki. Maryamu ta zauna a tsakar gidan tana ta ma su Inna rashin kunyar, "Alkur'an ba a isa a yi mata aure ba, sai dai ta gudu kowa ma ya rasa."

Inna tace, "to in kin fasa dan ubanki, ko akwai wanda zai neme ki ne? Ki tafi mana yanzu tunda ba a ɗaure miki ƙafa ba."

"Na rantse Inna baza a yi min aure ba, kuma kuna ganin wasa ne sai na aikata abun da nace." Ta miƙe tana ɓata rai tare da cewa, "haka kawai, wlh bazan yarda ba, babu wanda zan kawo bare ma a yi min auren."

Umma Jummai tace, "to wai mu ina ruwan mu da kika zo kika tasa mu gaba kina mana rashin kunya iyee?"

"Ki bar ta don Allah, na kusa karyata a gidan nan, kuma billahil lazi in ba ki yi wasa ba sai na saɓa miki kar ki bari mu saka ƙafan wando ɗaya da ke."

Shiru tayi bata ce komai ba sabida ganin yanda Innar take kallonta, ta san tsab zata ci uban ta. Sai ta wuce ɗakin su bata ma bi ta kan Bintu da ke zaune tana tsintan shinkafa ba, Hijabin ta ta ɗauka zata fice

Amma sai Inna tace, "kar ki fita gidan nan Maryam, wlh ƙafan ki ta fita gidan nan za ki ji a jikin ki."

"To Inna Ni fa ba wani wuri zan je ba, gidan Aunty Ummita zan je, dama tace in zo in taya ta gyaran ɗakin ta."

"Baza ki je ba. Tunda yawon kike so ki zo ki wuce ki ɗauki key ki zauna min a shago."

Babu yanda ta iya haka ta wuce ta ɗauko key ɗin. Tana fita kuwa ta zarce gidan Aunty Ummitan batare da ta shiga shagon ba

Tana cikin tafiya tana rera waƙa. Sai turguɗe wa take yi amma hakan bai sa ta cire takalmin ba. Har ta kusa isa gidan Aunty Ummitan sai ganin Jamilu tayi a gaban ta yana kiran ta. Ja tayi ta tsaya tana cewa, "lafiya? Wannan wanne irin halin karnukanci ne da zaka zo kana shan min gaba? Kana da mind?"
 

"Halin karnukancin na zo in nuna miki yanzu kuwa, tunda ke ba ki da mutunci yanzu zan nuna miki kin taɓa wanda ya fi ƙarfin ki, zan yi maganin rashin kunyar ki yanzu".
[12/01, 10:08 am] OumƊahirah نفيسة: 🌱🌱🌱🌱🌱

      *SHAREEF*
          _SexyBoy_
🌱🌱🌱🌱🌱


_Writer: Nafisat Isma'il Lawal_
_Wattpad: UmmuDahirah_

*SARAUNIYAR TSOKANAR PERFECT🧝*



*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞

```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)```

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

       *P.W.A✍️*





*DATA SHARE*

Call, message or whatsap 07065334256

*MTN*
500MB 150
1gb 280
2gb. 560
3gb. 840
4gb.

Please Login or Register in order to submit comment