Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ya san idan yace zai je gida yanzu akwai matsala, dole can Abujan zai wuce, tsaya wa yayi gefe ya nemi layin PA ya danna masa kira, a nan ya soma tambayarsa halin da ake ciki

PA ya faɗa masa, "har yanzu suna can har Dady suna wurin, dukkan su a can suka kwana, an samu damar kashe wutan tun jiya amma wurin yana nan cike da hayaƙi, su Mr. Pitter ma sun samu zuwa yau, kuma suna ta tambayar ina yake?"

Runtse idanu SHAREEF yayi yana tare mai Texi, ba tare da ya jira ƙarisan abun da PA zai ce mishi ba, sai yace, "ga shi nan zuwa yanzu."
Katse wayan yayi yana shiga Motan yace mishi, "ya wuce dashi Abuja drop zai yi, zai biya sa ko nawa ne."

Jin haka babu musu mai Texi ya kunna mota ya figa hanya, a murnan sa tunda kallo ɗaya ma da ya yi wa SHAREEF ya san cewa akwai maiƙo a wurin

SHAREEF wanda yake duban hanya yana ganin tamkar ba ta sauri Motan, sai yace mishi, "ya tuƙa da gudu sosai, ba ya son delay."

Ai kuwa sosai mai Texi ya ƙara wa mota gudu, kawai figan Motan yake yi kamar zai tashi sama

Amma shi SHAREEF gani yake yi kamar ba a sauri, gajen haƙuri irin nasa ya kasa yin shiru haka ya ƙara damun sa, "ya ƙara gudu fiye da wannan, don yana buƙatar su isa Abuja cikin ƙanƙanin lokaci."

Mai Texi yace, "gaskiya Oga sai dai kayi haƙuri, wannan gudun ma da nake yi ya isa haka nan in ba so kake yi mu tashi sama ba, ai komin saurin ka dole kayi haƙuri mu isa a hankali kar mu samu matsala."

Kasancewar wayan SHAREEF ɗin ta soma Ring, shiyasa bai saurari mai Texi ɗin ba, sai ma jan dogon tsaki da yayi yana ƙoƙarin amsa call ɗin wanda ya ga sunan Hanif ya fito ɓaro-ɓaro

A dai-dai nan kuma mai motan ya shige wa tirela da nufin wuce ta tunda ta kare musu hanya, amma sai aka yi rashin Sa'a ya gogi tirelan; ƙuuuuuu! Wani ƙara mai sauti ya biyo baya nan da nan murfin Motan da ke side ɗin drivern ta fice fit tare da na baya. Hakan ya ɗaga wa mai Texi hankali, wanda yayi ƙoƙarin ya kawar da motan tare da matsa wa daga jikin tirelan, amma halin ruɗe wa da ya shiga ya kasa, take motan ta haɗe da tirelan har ta kusa shige wa ƙasan ta, lokaci ɗaya suka yi mummunar hatsari a wurin.
[16/02, 9:47 am] OumƊahirah نفيسة: 🌱🌱🌱🌱🌱

      *SHAREEF*
          _SexyBoy_
🌱🌱🌱🌱🌱

_Writer: Nafisat Isma'il Lawal_
_Wattpad: UmmuDahirah_

*SARAUNIYAR TSOKANAR PERFECT🧝*



*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞

```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)```

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

       *P.W.A✍️*





*DATA SHARE*

Call, message or whatsap 07065334256

*MTN*
500MB 150
1gb 280
2gb. 560
3gb. 840
4gb. 1120
5gb 1400
6gb. 1700
Verlid for 30 days.












__________
*BOOK1*
_______________*FREE PAGE33*
_____Tashin hankali! Bazan iya misalta muku irin tashin hankalin da iyayen SHAREEF suka shiga ba, sakamakon riskar su da labarin hatsarin sa ya je kunnen su. Dole Dady a ranan ya dawo Kano ya bar su PA a can da su Shuraihu, ya dawo wurin ɗansa hankali a tashe, duk da har lokacin ba a basu wani result na sakamakon abun da ya same su ba, amma an tabbatar drivern take ya mutu ko shura wa bai yi ba

Momy da Sadiq suna asibitin cikin tsananin tashin hankali, kallo ɗaya kayi musu ma ka san cewa sun yi kuka har sun gaji, kowanne a cikin su idanunsa jawur,
Har wasu daga cikin ƴan uwan Momy Maza sun zo wurin ana ta jira a ji me Likitan zai ce tunda har yanzu basu fito ba

Shi kansa Dady da ya iso wurin ya kasa natsuwa sabida ganin halin da iyalansa suke ciki, kallo ɗaya da yayi musu sai da zuciyarsa ta karye domin yana ji a jikinsa tamkar ya rasa ɗansa ne, tunda ya gama jin labarin irin mummunar hatsarin da suka yi, har an rasa drivern ma

Hankali fa ya tashi, sai dai kuma zuwan Doctor da bayanin da suka samu shi ya kwantar musu da hankali har suka iya jin sanyi a ransu, sakamakon bayyana musu da yayi, "SHAREEF yana raye har yanzu, sannan ba wani ciwo sosai ya ji ba Allah ya tsare shi gaskiya, kansa ne kawai ya bugu sai targaɗe da ya samu a hannu, sai kuma ƙananun ciwuka da ya ji a ƙafafunsa, amma jikinsa da sauƙi ko zuwa anjima zai farfaɗo."
Sai ya keɓe da Dady kuma ya sanar masa, "gaskiya da yiwuwar a sauya wa SHAREEF ƙodan nan da gaggawa tun kafin a samu matsala, because of this accident that caused the place to be slightly damaged, inda hali kafin a sallame shi a jinyar nan kawai a yi aikin a huta hakan zai fi."

Dady da ke cikin wani yanayi da jin abun da Likita yace, sai ya ja numfashi yace, "shikenan Doctor, yanzu ya kake tunanin zamu yi? Ko za a duba namu kidney ɗin ne sai a cire wanda zai yi?"

"No Alhaji, ai kai kana fama da kanka zai fi kyau dai a samo wani sai a cire nasa, kana fama da ciwon sigar and your wife also has high blood pressure, it would be better to find someone else and get tested, idan kuma za a samo na siya ka san akwai matsaloli irin wannan, sannan sai an kashe kuɗi sosai."

"Duk da muna cikin wani hali, kuɗi ba damuwa bane Doctor, a jaraba samo wa in zamu dace, ko nawa ne zan bayar, then I will go and see if we can find it at our place and you will hear Me."

"Ok no problems." Daga haka ya basa hannu sannan suka rabu.
***

_____Ƴan uwa da Abokan arziki suna ta zuwa duba SHAREEF duk da har yanzu bai farfaɗo ba, amma ana shiga duba sa, su Momy ma suna tare da shi ita da Aunty Najwa da ta zo tun da abun ya faru bata tafi ba

Sai da hayaniyar ya ɗan yi yawa ne sannan aka dena barin mutane suna shiga, sai suka dawo haraban ɗakin aka shimfiɗa tabarma su Momy suka zauna a wurin, a nan suka wuni har yamma suna wajen

Maryamu kuwa tana can makaranta bata san me ke faruwa ba, kuma lokacin tashin su yana yi Sadiq ya tafi ɗauko ta since Momy ta tuna masa, "in time yayi ya je ya dauko ta, ya wuce da ita gida."
Hakan kuwa yayi, kuma bai sanar mata da komai ba sai da suka koma gida ganin babu kowa yasa ta dame shi da tambayar inda Momy ta tafi?
Ce mata yayi, "ta je ta canza kayan ta ta ci abinci sai ya faɗa mata inda Momyn ta tafi, zai kaita can ne."

Cikin sauri kuwa ta gama kimtsa wa suka ci abincin tare tunda shima tun safe bai saka komai a cikin sa ba, sai yanzu ne da ya ɗan samu natsuwa shiyasa ya ci. Bayan sun gama yace mata, "Momy tana asibiti, Yaya SHAREEF ba ya jin dad'i, shi ne aka je duba sa."

Duk da bai faɗa mata ainihin mai ke faruwa ba gudun tashin hankalin ta, since ya san yanda SHAREEF yake a wurin ta, amma hakan bai hana ta rikice masa ba, sai ga hawaye sun soma gudu a kan fuskarta cike da rawan murya take cewa, "Yaya Sadiq, dama bai da lafiya ne? Don Allah me ke damun sa ka sanar min?"

"Calm down mana Maryam, ba fa na faɗa miki bane don ki tashi hankalin ki ba, SHAREEF yana cikin ƙoshin lafiya kin san dai ciwon da yake fama da shi; shi ne ya ƙara taso mishi aka kai shi asibiti a duba sa."

Shiru tayi tana hawaye, sai kuma ta sake duban sa tace, "to amma an ce ciwon ƙoda ba a warke wa, kenan zai mutu ya bar Ni? Wlh bazan iya rayuwa babu shi ba ina sonsa."

Ƴar dariya Sadiq yayi yace, "da can da kike rayuwa babu shi fa ya kika yi? Ki dena wannan sakarcin Maryam komai da kika ga yana faruwa muƙaddari ne daga Allah, har yanzu ke yarinya ce ba ki san so ba bare ki ce baza ki iya rayuwa babu shi ba, don haka babu wanda ya san gawan fari mu dashi gaba ɗaya, kuma ciwon da yake yi ana warke wa da zaran an yi masa aiki an canza mishi ƙoda zai samu lafiya bazai sake ciwo ba."

Jin abun da yace yasa tayi shiru ta kasa magana, yayinda jikinta yayi sanyi, sai ta kifa kanta a saman kujerar tana shashsheƙa zuciyarta na zafi tare da wani irin harbawa kamar zata faso ƙirjinta, gaba ɗaya jikinta ba ya mata dad'i har wani irin rawa yake yi

Shi kansa Sadiq yana mamakin yanda Maryamun take nuna soyayyarta a wurin Yayansa, gani yake yi kamar har da ƙuruciya har yanzu Maryamu yarinya ce bare ta san irin wannan soyayyar, amma kuma ganin halin da take ciki sai ya koma yana rarrashinta yana faɗa mata kalamai masu dad'i tare da bata tabbacin, "SHAREEF bazai taɓa mutuwa ba."

"Don Allah ka kaini in gansa, ina son ganin sa."
Ta furta tana fashe wa da wani irin kuka da ya kufce mata, "don Allah ka kaini wurin sa."

"Ki yi shiru mana, I told you jikinsa da sauƙi, su Momy ma suna can, ki zauna a gida idan ya dawo sai ki gansa zai fi."

Kuka ta ci gaba da yi ta kasa yin shiru, duk yanda ya so ya rarrashe ta amma ta ƙi amince masa ita tana son ganin sa

Shi yasa yace, "to ta je tayi sallan magriba tunda an kira, shima zai yi sai ya dawo su tafi, maybe ma kafin lokacin su Momy sun dawo."
Da haka ya samu tayi shiru har ya fice ya barta

Ita kuma ta shiga ɗaki da sauri don yin Sallan kafin ya dawo, har yanzu jikinta sai rawa yake yi kamar mazari, wani irin sara wa kanta yake yi ga wani irin yanayi da ke riskan ta duk a kan SHAREEF ɗin, har a ranta tana matuƙar tausayin SHAREEF, baza ta taɓa samun sukuni ba har sai ta gansa sannan hankalin ta zai kwanta, domin yanda zuciyarta take buga wa tana jin kamar akwai abun da ya same sa.
Alwala tayi ta fito, a time ɗin ta ji kamar an shigo da mota tun tana toilet, shiyasa tayi saurin fita don a tunanin ta su ne suka dawo,
Amma tana fita sai ta hangi Dady ne ya shigo falon ya nufi wurin steps ya tsaya yana amsa call,
Wurin sa ta nufa ba tare da shi ya ganta ba

Yayinda shi kuma ya ci gaba da wayan yana sanar da Doctor Umar yanda suka yi da Doctor kan ciwon SHAREEF

Tsab ta gama jin komai, hankalinta ya ƙara tashi, sai a lokacin ta fahimci cewan ashe hatsari yayi, kuka ta saka sosai a lokacin

Yayinda Dady ya juyo a rikice yana kallonta, don bai yi tsammanin ta a wurin ba, "daughter."
Ya kira sunan ta yana kamo ta hankali a tashe, "what's wrong with you? Wa ya taɓa ki yi shiru haka nan, ki yi shiru nace ki sanar min me ke damun ki kike kuka?"

Shiru tayi tana shashsheƙa but ta gaza yin magana, sai rawa da jikinta ke faman yi

Ganin yanayin da take ciki, sai ya kamo ta zuwa cikin falon ya zaunar da ita, tare da furta, "ina Sadiq ɗin? Ya aka yi ya bar ki ke kaɗai?"

"Dady ya je yin Sallah." Ta furta tana ci gaba da shashsheƙan kukan

Yace, "to ya isa, fada min me aka yi miki kike kuka? Ko tsoro kike ji?"

Girgiza kanta tayi tana sake matso wasu hawayen, a hankali ta furta, "Dady Yaya SHAREEF."

Sai a nan Dady ya gane musabbabin kukan nata, shiyasa cikin kula wa da tausayin ta yace, "SHAREEF yana nan lafiya zai samu sauƙi daughter, ba abun da zai same sa, yanzu haka jikinsa very easy har ya farka ma, kinji ki kwantar da hankalin ki ko zuwa gobe za ki je ki duba sa."

Kallonsa tayi idanunta jawur tace, "Dady amma ka ce sai an yi mishi aiki? Na ji kana faɗa a waya za a sauya mishi Ƙoda, don Allah Dady a saka mishi nawa ba na son Yaya SHAREEF ya mutu ya bar Ni."

Da mamaki Dady yake kallonta, sai yace, "Maryam ba yanda za a yi a cire miki ƙoda a saka mishi, ke yarinya ce ƙarama ki dena tayar da hankalin ki a kan wannan matsalar, ba wai an rasa ƙodan bane za a samu kuma za a saka mishi zai warke kamar kowa ya tashi kina jina? Kin yi sallah ma?"

Kanta ta girgiza mishi, sai kuma cike da sanyin murya tace, "don Allah Dady a saka mishi nawa wlh na amince zan ba shi nawa ƙodan, ai shi Mijina ne ina da damar da zan iya taimaka masa a rayuwa."

"Maryam ba ki da hurumin da za ki iya bada ƙodan ki ba tare da sanin iyayen ki ba, in fact ma ke amana ce a wuri na bazai yiwu haka kawai a cire miki ƙoda a saka wa SHAREEF ba. Ko kina da damar taimaka masa sai da sanin iyayenki. Ki bari zamu ga abun da hali zai yi, in ba a samu ba sai a cire naki a saka mishi, hakan yayi miki?"

Da sauri ta ɗaga mishi kai cikin farin ciki

Sai yayi mata murmushi yace, "yauwa to, je kiyi sallan ki dawo sai mu wuce asibitin ma ki duba sa."

Kafin ma ya rufe bakin; har ta amsa mishi ta tashi ta wuce da sauri

Yayinda ya raka ta da kallo yana mai ci gaba da mamakin yarinyar; da kuma wani irin tausayinta da ya kama shi don ya san cewa yanda take ƙaunar SHAREEF har zuciyarta; shi ba ya mata haka, dole zata sha wahala yarinyar, bai san meyasa SHAREEF ya tsane ta ba, kuma shi ba wata budurwa ce da shi ba bare yayi tunanin hankalin sa yana a kanta ne, amma koma dai mene ne bazai taɓa barin SHAREEF ya wulakanta ta ba, ko yana so ko ba ya so sai ya zauna da ita, auren su mutu ka raba ne babu saki a tsakani, Maryamu ita ya zaɓa wa ɗansa SHAREEF

Mike wa yayi ya wuce saman da sauri yayi alwala, sannan ya fito ya wuce masallaci

A tare suka dawo da Sadiq suka tarar da Maryamu tana faman jiran su, shiyasa Dady yace, "su wuce gaba ɗaya zuwa asibitin."

Bayan sun je lokacin Momy ne kaɗai a wurin sa, itama idar da sallanta kenan tana zaune tana lazimi,
Shi kuma SHAREEF ɗin yana kwance a saman gado, sai dai idanunsa biyu amma ya rufe su, jin shigowar su Dadyn ne ya buɗe idon yana kallon su

"My son, ya jikin naka?"
A cewar Dady yana bin sa da kallo tare da shafa masa kai

Murmushi yayi yace, "alhamdulillah Dady."

Sadiq shima ya jikin yayi masa yana ƙara matsowa kusa dashi

Ya amsa cikin kula wa yana kallonsa, har yanzu da ɗan guntun murmushin sa

"Taho nan daughter ki yi masa sannu da jikin, Sadiq janye jikinka tunda ka gaishe shi." Cewar Momy tana kamo hannun Maryamu da ke bayansu

Tunda SHAREEF ya ɗaura ido a kanta sau ɗaya bai sake kallonta ba

Yayinda ita kuma ta matso sosai wurin sa, duk idanunta sun kaɗa sun yi jazur kowa ya kalle ta ya san tayi kuka, muryanta ma a raunane take yi wa SHAREEF ɗin sannu

Amma bai amsa ba sai da Momy tayi masa magana sannan ne ya amsa ta a daƙile. Dukkan su sun fahimci yanayin da ya amsa mata tamkar ba ya so, sai dai ba wanda yayi magana a cikin su, sai Momy ne da ta koma tambayar Maryamun dalilin yin kukan nata sabida ganin yanda idanunta suka yi

Sadiq yace, "ai Momy tunda na sanar mata ta tayar da hankalin ta tana ta kuka wai sai na kawo ta." Ya ƙare maganar yana ƴar dariya
      

Ita kuma ta harare sa tana cewa, "to wa yace ka faɗa mata don ƙaniyar ka? Cewa nayi fa ka ɗauko ta a school ba wai ka sanar mata halin da yake ciki ba, yanzu ga shi nan ka saka min ita kuka." Sai ta ƙara kallon Maryamun da a yanzu take shirin yin wani kukan, don har idanunta sun cika da hawaye ta kasa jure wa, "kar dai a ce wani kukan za ki sake yi? Ya isa haka Maryam ba ki ga ya samu sauƙi bane?"

Gyaɗa kanta tayi tana saurin saka hannunta; tare da share hawayen da har sun sauka a kan fuskarta

While SHAREEF kamar ya maƙure yarinyar haka yake ji; sabida yanda ya ga iyayen nasa sun raja'a a kanta suna bata baki, nufin ta kenan don shi take kukan? Tsaki ya ja a ransa yana lumshe idanunsa tare da sake jin haushin ta sosai,
Allah ya gani ya tsani yarinyar wlh, bai san meyasa ba duk idan ya kalle ta haushi da ɓacin rai; gami da zallan tsanar ta yake ƙara tasiri a zuciyarsa, in so samu ne ya dena ganin ta gaba ɗaya a cikin rayuwarsa, don shi ba ya son abun da zai takura sa bare ya saka mishi damuwa a tare da shi, har yaushe ma wannan ƙanƙanuwar yarinyar da yake ganin ta ƙaramar alhaki; har yaushe ta san soyayya?

Bayan sun gama rarrashinta ne Momy take sanar da Dady zuwan Hanif da ya dage sai ya dawo, "don haka gwara ya kira sa yayi mishi magana don ita ta hana shi amma yace sai ya dawo."

Dady yace, "ok zan kira shi, ai bai kamata ya dawo ba since jikin SHAREEF ɗin da sauki, zan kira sa muyi magana, bari in je wurin Doctor in dawo."

Daga haka ya fita ya bar su a ɗakin. Sadiq ya zauna a gefen ƙafafun SHAREEF

Ita kuma Maryamu tana saman kujera wacce Momy tace ta zauna a kai. Sai kallon SHAREEF ɗin take yi zuciyarta cike da tsananin tausayin sa, musamman yanda ta ga bandage na kansa da aka sanya mishi duk ya jiƙe da jini, wani yawu ta haɗiye mai kauri tana lumshe idanunta, jin wasu hawayen suna shirin fito mata shiyasa tayi saurin buɗe idon don ba ta buƙatar Momy ta sake fahimtar tana kuka. Karaf idanunta suka shige cikin nasa da shima ya buɗe ya aza a kanta,
Wani irin kallo ya watsa mata wanda yasa lokaci ɗaya ta ɗauke nata idon a kansa, sosai take jin bugun zuciya kamar ana zare mata laka daga jikinta, bata sake ɗago kai ta kalle sa ba bare tayi magana, wani irin kuka ne yake son kufce mata, bata san meyasa Yaya SHAREEF ba ya ƙaunarta ba, amma me tayi masa a rayuwa? Hakan na saka ta ta ji zuciyarta tana mata zafi sosai, tana son tayi abun da zai so ta sosai, tana son tayi rayuwa dashi, baza ta iya jure wannan yanayin ba, ba ta son yana nuna mata tsana, tana son ya kasance kusa da ita domin samun farin ciki a zuciyarta, ko kallonsa yanzu ya hana ta yi, tsoron kallonsa take yi don kar ta ɓata mishi rai, amma ya zata yi?

Har suka tashi tafiya ta kasa sakin jikinta a wurin, sabida da zaran ta ɗago kanta sai sun haɗa ido dashi yana sakar mata mummunar kallon nan nasa da ke faɗar mata da gaba, har tsoron kar ya furta wani abu a kanta take yi don ta san tsab zai iya zagin ta ko yace tana kallonsa, shiyasa duk ta kasa sakin jikinta,
Har suka tashi tafiya aka bar Sadiq a wurin sa tunda shi zai kwana dashi,
Daga nan suka wuce gida

Basu tsaya wani hira ba Momy tace, "ta je ta kwanta."
Haka nan babu yanda ta iya dole ta tafi ɗaki ta kwanta, duk da tana jin barci bazai taba zuwan mata ba saboda halin damuwar da take ciki, da kuma tunanin SHAREEF da ya gallabe ta

Dady kuma bai ɓoye wa Momy komai ba halin da ake ciki, a kan zancen Doctor tunda bata san da maganar ba, yanzu dole sai dai su tashi tsaye da yin masa addu'a don ganin an dace an yi aikin nan lafiya, sannan ya faɗa mata abun da Maryamu tace duk da bai ɗauki maganar nata da wani muhimmanci ba

Haka zalika itama Momy, don ta san bazai yiwu a ce Maryamu ce zata bada ƙodan ta bA, ko ma dai mene ne zasu san yanda za a yi a samu kafin kwana biyu da doctor ya ɗiba musu

Amma kuma me? yanda Maryamu ta ga rana haka ta ga dare a ranan, gani take yi kamar in tayi wasa bata taimaki SHAREEF ba zata iya rasa shi a duniya, gani take yi tana da hanyar taimaka masa, wataƙil ma idan aka cire wani abu a cikin jikinta aka sanya mishi zai ƙaunace ta, domin ta sha jin labarin irin hakan, idan aka cire wani abu daga cikin mutum aka sanya wa wani, to jinin su zai haɗu su ji suna ƙaunar juna matuƙa, hakan ya bata ƙwarin gwiwa da tunanin dole sai dai a cire nata ƙodan a saka mishi, baza ta taɓa bari a saka mishi na wani ba tunda ita take sonshi, kuma ta tabbata in har aka sanya mishi zai ji a ransa yana sonta sosai, ko bai san ita ta ba shi ba zai iya ƙaunarta. Don haka da safe ƙin shirya wa tayi ta tafi makarantar, ta sami Dady har da kukan ta a kan, "a cire nata don Allah a saka mishi, wataƙil zai so ta in wani abu nata yana yawo a jikinsa."

Su kansu mamaki ne ya kusa kashe su da zancen Maryamu, don gani suke yi tamkar bata da hankali akwai wauta a tare da ita, don an cire ƙoda an saka wa SHAREEF ba hakan ke nufin zai so ta ba, duk yanda suka so su fahimtar da ita amma ta ƙi gane wa; kuka sosai take musu sun rasa yanda zasu yi da ita

Wannan wanne irin soyayya ce Maryamu take yi wa SHAREEF? Dady yace, "Maryam ko ba ki ba shi ƙodan ki ba ke Matar SHAREEF ne, babu mai raba ku sai mutuwa, don haka ki kwantar da hankalin ki za a yi mishi aiki ba sai an taɓa lafiyar ki ba."

Kuka ta fashe da shi tare da furta, "don Allah ku taimaka min ku saka mishi nawa, wlh zan fi samun farin ciki muddin ƙoda na ta shiga jikinsa, ina matuƙar sonsa, bazan bari a saka mishi na wani ba, Ni ce Matarsa zan iya taimaka masa Ni dai na amince a saka mishi ƙoda na, Ni ba sai kun sanar da iyayena ba wannan sirri ne daga Ni sai shi, ba na son kowa ya sani ku taimaka min kar ya mutu, idan ya mutu nima mutuwa zan yi."

Yanda ta fita hayyacin ta tana musu kuka kamar ranta zai fita, dole suka amince a kan sun yarda da maganar ta, sannan fa suka samu kanta, sun rasa ma yanda zasu yi da ita, duk da basu so hakan ba amma gani suke yi soyayyar da Maryamu take yi wa SHAREEF yayi yawa, sannan ma kasancewar ta Matarsa basu da yanda zasu yi tunda ta matsa sosai, ga halin da take ciki duk ta haukace musu

Bayan Dady ya je wurin Doctor ya sanar mishi da samun kidney ɗin, amma yayi masa bayanin, "ƙaramar yarinya ce in da wata matsalar da za a samu ya faɗa masa, yarinyar ce ta nace dole sai nata za a saka tunda Mijinta ne, baza ta yarda a saka mishi na wani ba."


Shi kansa Doctorn yayi mamakin yarinyar musamman da ya ganta, duk da babu wata matsala don har ya sanya musu ranan da za a yi aikin nan da gobe insha Allahu, tunda an samu baza a tsaya wani jira ba.
  
[18/02, 7:18 am] OumƊahirah نفيسة: 🌱🌱🌱🌱🌱

          *SHAREEF*
            _SexyBoy_
🌱🌱🌱🌱🌱


_Writer: Nafisat Isma'il Lawal_
_Wattpad: UmmuDahirah_

*SARAUNIYAR TSOKANAR PERFECT🧝*



*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞

```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)```

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

       *P.W.A✍️*





*DATA SHARE*

Call, message or whatsap 07065334256

*MTN*
500MB 150
1gb 280
2gb. 560
3gb. 840
4gb. 1120
5gb 1400
6gb. 1700
Verlid for 30 days.













__________
*BOOK1*
_______________*FREE PAGE34*
_____A

Please Login or Register in order to submit comment