Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ruwa ku sha."

Sai lokacin SHAREEF ya ɗago kansa yana sauke wa a kan Momy tare da furta, "Mom Ni ba ki yi min komai ba, su kawai kika yi kewa kenan?"

Wani harara ta narka masa, bata kai ga yin magana ba Dady ya fito yana musu magana,
Hakan ne yasa bata ce komai ba ta wuce kitchen

Dukkan su suka nufe sa suka rungume sa,
Daga bisani ya kama hannun Hanif suka zo har kan sofa suka zauna a tare yana masa congratulations

Momy lokacin ta kawo musu ruwan, sai ta zuba wa Hanif kaɗai ta miƙa masa

Ganin haka ne yasa Sadiq ya dauka ya zuba yana sha tunda ishi yake ji

While SHAREEF kuma sai ya haɗe fuska har yanzu yana a tsayen ya ƙi zama, sai kawai ya juya ya nufi saman benen bai sake cewa komai ba

Maryamu ce kawai ta bi sa da kallo kamar zata zilalar da yawu, tana jin wani irin ƙaunarsa na ƙara mamaye mata zuciya, shi kaɗai take ganin kyawun sa a wurin, farar fuskarsa ta fi komai saka ta nishaɗi

Su Feena da suka kula da ita, suna ganin irin kallon da take yi wa SHAREEF ɗin, abun ya basu mamaki duk da su ma kallonsa ɗin suke yi, musamman ma Amina wacce bata sanshi ba, ita gani take yi kamar ƴan biyu ne da Hanif, baza ta tantance wanda ya fi kyau a cikin su ukun ba, sai dai SHAREEF ya fi kwarjini ne da ɗaukar ido sabida hasken sa mai kyau da dimples ɗin sa da ke bayyana in yayi magana, hakan ke jawo hankalin mutane gare shi; ba ƙaramin kyau yake ƙara masa da haiba ba, sai kuma sassanyar muryan sa ko magana yayi sai ka juya ka kalle sa,
But a zahiri Sadiq ya fi su kyau tunda shi yana da manyan idanuwa masu haske; kuma yana da ɗan fara'a a fuska,
Bata taɓa ganin waɗanda suka bata sha'awa irin waɗannan samarin ba, daga ita har Feena sun kasa sakin jikin su sabida ganin Samarin; kowacce tana jin kunya duk sun takure, ga shi Hanif sai jansu yake yi da hira kamar ya daɗe da sanin su, amma kunya ya hana su zama, dole suka yi musu sallama suka ce zasu tafi

Momy tace, "su je su yi wa Driver magana sai ya kaisu gida."

Tare da Maryamu suka fita har haraban gidan, sai da ta ga tafiyan su sannan ta ɗingisa ƙafa ta dawo ciki,
A wurin Hanif ta zauna suna hira a tare suna ta dariya gaba ɗaya,
Amma ban da SHAREEF don ya ƙi fitowa yana can ɗaki,
Sai da aka kira sallan magriba sannan ya fito suka haɗu da su Hanif suka wuce masallaci

Sai bayan sallan isha'i suka dawo gidan, dukkan su a saman Dinnig suka zauna a tare suka ci abinci yau,
Bayan an gama suka dawo suka ɗan taɓa hira kaɗan,
Shi Hanif tuni ya wuce daki tunda akwai gajiya a jikinsa, sai da ya ɗan jima da shigewa before SHAREEF ya bi bayansa

Dady yace, "kai Sadiq baza ka je ka kwanta bane; ka huce gajiyar?"

"No Dady ba na jin barci, ina nan tare da ku muyi hiran mu, ban jin gajiyar komai."

Murmushi Dady yayi

Ita kuma Momy tace, "mu ma ai ba jima wa zamu yi ba yanzu zamu kwanta, hiran ya isa haka."

"Ita dai daughter tuni tayi barcin ta ta huta, saura mu." Inji Dady yana ɗan muskuta zaman sa

Momy tace, "ai tun ɗazu nake kula da ita tana ta hamma, ban ma farga ba ashe har tayi barcin? Sadiq ko zaka kaita ɗaki?"

Ɗan waro ido yayi yace, "kai Momy wlh bazan iya ba, kina ganin ta nan wasa-wasa nauyi ne da ita."
Sai ya miƙe da ɗan kuzarin sa yana cewa, "nima dai na tafi, bari in je ɗaki in duba books ɗina, good night Mom, Dad."

Sai da ya tafi sannan Momy ta ɗauke ta takaita ɗaki, suka wuce su ma ɗakunan su suka kwanta

A washe gari sai ga su Aunty Najwa da Aunty Zainab sun zo yi wa Hanif murnan kammala karatu,
Dayake Aunty Najwa ita ta taɓa zuwa sau ɗaya time ɗin Maryamu bata da lafiya Momy ta faɗa mata, har ta zo musamman ta gaishe ta,
Aunty Zainab ce bata santa ba, bayan ta ganta take cewa, "kai yarinyar ga ta kyakkyawa kuwa Khadijah, Allah ta shiga raina, anya bazan yi wa Habeeb kamu ba kawai a yi dashi?"

A lokacin Maryamu tana wurin, dariya kawai tayi bata ce komai ba

Bayan tabar wurin ne; Aunty Najwa take cewa, "wannan tuzurun? Ai tayi mishi ƙanƙanta wlh, me ma zata yi dashi? Yarinya ƴar ƙarama da ita beauty a cuce ta."

Aunty Zainab ta ɓata fuska tace, "kai Aunty Najwa gaskiya ban son haka, ina laifin don na ce a haɗa su? Wlh na ga dacewar su Allah ba wasa nake yi ba."

Sai lokacin Momy take cewa, "ai kwanan nan ma zata wuce wurin Surayyya; a can zata ci gaba da karatun ta."

"Haba dai? To sabida me? Bayan ke ma kina buƙatar yarinyar; ke da kike son ƴaƴa mata sai ki bar ta ta koma can?"
Inji Aunty Najwa tana kallon ta

Sai Momy ta ja numfashi; tare da zayyane musu ainihin abun da ke faruwa na auren su da SHAREEF

"Ikon Allah! Wai kina nufin abun nan ya faru amma ba ki sanar mana ba Khadija?" Inji Aunty Zainab tana ɗan ware ido a kanta

"Kuyi haƙuri, na so faɗa muku amma ba yanzu ba, dalili kuwa ita kanta yarinyar bamu so ta tare a ɗakin ta ba tunda kunga yarinya ce, sannan ba ma son ma SHAREEF ya sani a time ɗin, amma yanzu komai ya fito fili har ya nuna ra'ayin ba ya ƙaunar ta sai wata yarinya da ya kawo, gaba ɗaya hankalin mu bai kwanta da ita ba; amma ganin take-taken shi nema yake yi ya bijire mana a kanta shiyasa kawai muka amince, Ni kuma ba na son Maryam ta tare a yanzu ba tare da ta mallaki hankalin kanta ba, tunda SHAREEF ba ya ƙaunar yarinyar sai fama muke yi dashi, idan ta tare akwai cutuwa a wurin ta, kun san halin sa shiyasa nake son tayi nesa da mu ta je tayi karatunta ta samu wayewa ta yanda zata mayar masa da martanin duk abun da yayi mata, ba na son ya cuce ta bare mu mu tauye mata haƙƙin ta."

Aunty Najwa tace, "dama wannan Yaron yana yi da wasu ƙananun idanu ai ba mutunci ne dashi ba, SHAREEF bai da kirki ga shegen jin kai da wulaƙanci, wlh dole zata sha wahala, gwara da kika ɗauki wannan matakin, ba don Ni a nan nake ba ai da na ɗauke ta ta dawo wuri na."

Aunty Zainab ta karɓe zancen tana cewa, "bare Ni da ta fi shiga raina, gudun kawai matsala ne tunda ta zama Matarsa shiyasa bazan ɗauke ta ba, amma da babu igiyar kowa a kanta wlh Yarona zan yi wa kamu tunda shi ba ya so; ai mu muna so ato."

Momy murmushi tayi tace, "shine mu ma abun da ke damun mu, kuma ba ma son raba auren amma da mun haɗa su da Hanif, shi ya fi shi sauƙin kai bazai taɓa bijire mana ba, amma yarinyar itama tana sonshi shine matsalar, shiyasa take bani tausayi wlh, hakan ne yasa muka yi magana da Surayya nace zan kaita can, da mun so sai an yi hutu sai mu kaita ta soma zuwa makarantar, amma tace mu kawo ta kawai yanzu tunda Jarabawa ya rage musu ranan Alhamis zasu fara; sai a kawo ta zata san yanda zata yi ko jarabawar sai tayi ai babu matsala, tunda Hanif ya dawo shi zai kaita ko zuwa jibi tare da driver sai su je."

"To Allah yasa hakan shi ya fi alkhairi." Aunty Zainab tace hakan

Suka amsa da Amin, daga nan suka koma hiran maganar auren SHAREEF ɗin da za a ɗaura da zaran yarinyar ta dawo hutu,
Duk da ransu bai so ba duk sun bada rashin goyon bayan su, a cewar su, "wanne aure ne za a yi yarinya ta tafi wata ƙasa da aurenta babu Miji? Wannan ba yi bane, ai tun farko gwara kar a ɗaura a bari sai ta dawo gaba ɗaya sai a yi bikin."

Momy dai bata da yanda zata yi tunda a so samun ta ne ma kar ya auri yarinyar, amma ba damuwa tunda haka Allah yaso, yanzu abun da ya rage mata kawai ta fahimtar da Maryamu; domin baza ta so ta tafi batare da ta san da maganar ba, ko don gudun wata matsalar.
[27/02, 9:04 am] OumƊahirah نفيسة: 🌱🌱🌱🌱🌱

          *SHAREEF*
               _SexyBoy_
🌱🌱🌱🌱🌱


_Writer: Nafisat Isma'il Lawal_
_Wattpad: UmmuDahirah_

*SARAUNIYAR TSOKANAR PERFECT🧝*



*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞

```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)```

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

       *P.W.A✍️*





*DATA SHARE*

Call, message or whatsap 07065334256

*MTN*
500MB 150
1gb 280
2gb. 560
3gb. 840
4gb. 1120
5gb 1400
6gb. 1700
Verlid for 30 days.












__________
*BOOK1*
_______________*FREE PAGE42to43*
_____Momy ita da kanta ta zaunar da Maryamu tayi mata bayanin tafiyar nata; da suke shirin tura ta Abuja ta zauna a can tayi karatun ta

Maganar ya zo mata a mugun bazata, shiyasa bata yi ƙasa a gwiwa ba tace wa Momy, "don Allah Momy ba na son a kaini can, na fi son zama da ku Momy don Allah."
Sai ga hawaye sharr; domin abu ɗaya yasa ta ruɗe lokacin sabida ganin za a raba ta da SHAREEF, wadda ba ta jin zata iya jure wa, baza ta iya nesa dashi ba, baza ta iya ba

Momy kuma sai ta kama hannunta tana kallonta na ɗan wani lokaci bata ce mata komai ba, daga baya sai tace, "ki yi shiru haka nan ba na son wannan kukan naki, abun da yasa kika ji nace hakan sabida can za ki fi jin daɗin zama ne Maryam, kinga ita tana da Yara sa'annin ki za ki yi karatun ki cikin kwanciyar hankali, ai mu ma ba a son ranmu zamu bar ki ki koma can ba Maryam."

Sai tayi saurin girgiza mata kai tana hawaye sosai a wannan lokacin, yayinda cikin rawan murya take furta, "wlh Momy na fi son zama daku, ba na son na je wani wuri, nan ya fi min can."
Sai kawai wasu zafafan hawayen suka ƙara ɓulɓulowa, taya ya zata iya sanar da Momy baza ta iya zuwa can bane duk saboda SHAREEF? Taya ya zata iya yin nesa dashi? A'a bazai yiwu ba gaskiya. Yayinda take girgiza kanta ba tare da ta san tana yi ba

Inda ita kuma Momy ta bi ta da kallon tausayi, ta san meye a zuciyarta, lokaci guda ganin ta ruɗe shiyasa ta soma rarrashinta tana faɗa mata dalilin da yasa take son tayi nesa da nan, bayan ta gama ta ƙare maganar nata da cewan, "ki yi haƙuri kinji ko Maryam? Na san SHAREEF ne a ranki, amma idan kika yi nesa dashi hakan zai kawo soyayyarki a zuciyarsa, kuma zai rage ƙiyayyar da yake miki, ki je can ki yi karatun ki; ki sauya daga yanda yake kallon ki Bagidajiya ba ki kai ba, duk sanda kika dawo zai ƙaunace ki fiye da yanda kike tunani, kuma idan kika ci gaba da zama a nan baza ki yi karatu sosai yanda ya kamata ba; kinji Ni ko?"

Ita bata fahimci mai Momyn take nufi ba, taya ya tafiyar ta zai kawo canji a kan irin ƙiyayyar da SHAREEF yake mata? Taya ya hakan zai kawo sauyi? Zata tafi ta dena ganin sa ne, zai manta da ita gaba ɗaya bazai sake tuna ta ba, ita bata ga hanyar da zai sa ya so ta ba in har bata zauna a nan kusa dashi ba, sannan ma zuciyarta baza ta taɓa iya jure wa ba, wlh mutuwa zata yi, ko dai-dai da rana ɗaya ba ta son tayi missing ganin fuskarsa, hakan kaɗai yana saka ta farin ciki

Duk yanda Momy ta so ta fahimtar da Maryamu, amma ta kasa gane wa, ta tubure a kan, "babu inda zata je."
Dama Maryamu akwai gardama, don su Momy basu san halin ta bane, tunda ta zo wurin su bata nuna musu ainihin wace ce ita ba

Hakan ne yasa Momyn tayi mata tsiya-tsiya, ta turɓune fuska tace mata, "tana yin komai ne sabida ita, tana son ta mayar da ita Macen da SHAREEF zai kalle ta bai raina ta ba, sannan ma idan ta zauna a nan a banza tunda shi auren sa zai yi; ƙarshe ita za a mayar Bora baza ta taɓa tasiri a gidan sa ba, in ta fi son hakan ya faru sai ta ci gaba da zama tana ƙunsan bakin ciki."

Sai kawai Maryamu ta fashe da kuka jikin ta na wani irin rawa kamar mazari, lokaci ɗaya ta zamo ƙasa ta dunƙule wuri ɗaya tana ihu

Gaba ɗaya Momy ta rikice, domin bata taɓa zaton Maryamun zata tayar da hankalin ta haka ba

Hanif da ke ɗaki kwance yana huce gajiyar makaranta, shiyasa ba ya fita ko'ina tunda ya dawo, babu kowa a gidan sai su kaɗai, yana ɗakin su sama-sama ya jiyo kamar kuka, shiyasa ya tashi ya fito ya ga Momy tana ta rarrashin Maryamu amma ta ƙi yin shiru. Da mamaki ya iso wurin yana tambayar me ke faruwa? Hankalin sa shima ya ɗan tashi sabida ganin yanda Maryamun take kuka sosai ta ƙi yin shiru, lokaci guda ta fita a hayyacin ta

Momy ta kalle sa ta faɗa masa abun da ke faruwa

Haka kawai ya ji tausayin Maryamu ya kama sa sosai, duk da basu fahimci dalilin da yasa take kukan ba, a tunanin su rashin son zuwa Abuja ne, sai ya zauna ya ɗago ta ta koma saman kujera ya soma rarrashinta cikin kwantar da murya

Daƙyar suka samu tayi shiru, amma hawaye sun ƙi tsaya wa a kan face ɗin ta, faɗi take yi, "don Allah Momy kar a yi masa aure, ina sonsa wlh, zan iya zama dashi a haka, ku faɗa masa ina son sa kar ya auri Wata, ina sonsa."
Abun sai ya zame mata kamar taɓin hankali, bata cikin hayyacin ta abun da take ta furta wa kenan

Shi yasa Momy ta soma mata addu'o'i cikin tashin hankali, domin a tunanin su Maryamu ta samu sauƙi daga ciwon da take fama dashi, sai ga shi lokaci guda ta rikice kamar mai aljanu tana surutai mara su kan gado,
To make hankali ai bazai yi wannan abun ba. hakan ya tabbatar wa da Momy har yanzu Maryamu bata samu sauƙi dukka ba,
Addu'o'i ta dinga mata tana tofa mata cikin tsananin tausayin ta, yayinda take salati a cikin ranta

Inda shima Hanif yake bin su da kallo damuwa kwance a saman kyakkyawar fuskarsa, wani irin tausayin ta ne yake ƙara ratsa mishi zuciya, wai yarinya kamar wannan har ta san soyayya? Wannan wanne irin son maso wani ne? Bazai so a ce wani abu ya same ta ba domin yana jin ta tamkar ƙanwarsa da suka fito ciki ɗaya gudan jinin sa, ya san waye SHAREEF. Ya san kuma yanda yake matuƙar ƙaunar Haseena. Haseena ta zama komai nasa a yanzu, tabbas a yanda take gabansa bazai taɓa kallon Maryamu ba, kai ba ma ita kaɗai ba, kowacce ɗiya Mace SHAREEF bazai taɓa kallonta ba a yanzu, amma zai so SHAREEF ya tausaya mata ko don halin da take ciki, kamar ya zubar mata da hawaye haka yake ji. Sai ya buga tagumi yana kallon yanda Momy take ta mata tofi

daƙyar ta samu ta dawo hayyacinta, amma duk da haka bata dena kuka da magiyan, "Momy kar ta bari yayi aure, tana sonshi! Ita kaɗai take son shi baza ta iya rayuwa babu shi ba, su taimaka su roƙa mata shi."

Momy sai da ta zubar da hawayenta, ji take yi kamar ta kurma kuka sabida tsananin tausayin Maryamu, da tana da hali tabbas da ta cire soyayyar SHAREEF a zuciyar ƙaramar yarinyar nan; wadda bata gama sanin duniya ba amma wata mummunan ƙaddara tana shirin faruwa da ita, tabbas da tana da hali da ta canza Maryamu da Haseena a zuciyar SHAREEF; da ta saka shi ya so ta fiye da kowa a duniyar nan, yarinya ce bai kamata a ce ta san wannan soyayyar ba, babu yarinta ko wauta a irin yanda take ganin Maryamu tana ƙaunar SHAREEF, abun har mamaki yake bata,
Sai ta janyo ta jikinta tana sake rarrashinta tare da furta, "ki yi hakuri Maryam, ko so kike yi nima in yi kukan? Ai nayi miki alƙawari SHAREEF zai so ki wata rana; kuma SHAREEF naki ne har abada, auren shi ba shine zai sa bazai so ki ba amma ba na son ki shiga gidan sa ba ya ganin darajar ki kinji ko Maryamu na? Ki yi haƙuri ki dena damuwa da shi wata rana da ƙafafuwan sa zai zo gare ki, amma in kina wannan koke-koken zai raina ki ya ƙara wulaƙanta ki, ko ba haka ba Hanif?"

Kai ya ɗaga yana taso wa a inda yake zaune, ya zo ya kama hannun Maryamu yana cewa, "maza ki share hawayen ki ki dena wannan kukan, Momy ta rarrashe ki amma kin kasa yin shiru, share hawayen." Ya sakar mata hannun yana tsare ta da kallo

Ganin yanda yayi maganar babu wasa shiyasa ta share hawayen nan take, amma wasu ne suke ƙoƙarin fitowa, sai ta kalle sa da jajayen idanunta da suka kaɗa suka yi luhu-luhu, kamar zata fashe da kuka tace, "amma meyasa Yaya SHAREEF shi ba ya so na? Ku kuna so na amma ban dashi, me nayi masa da zafi haka? Kuma meyasa zai auri wata bayan gani Matarsa? Ka faɗa masa ina son sa, idan har bai so Ni ba mutuwa zan yi, zuciyata tana min zafi sosai, Momy don Allah ki taimaka min ki yi ceton rai."
Yanda take wani irin kuka shiyasa ta ƙarisa yin maganar tana kwantar da kanta a jikin Momy

Su kansu sun rasa yanda zasu yi da ita, abun ya soma basu tsoro, gani suke yi kamar Maryamu bata kai ta san wannan abun haka ba,
Dole sai dai Momy ta kira Dady ta sanar masa halin da ake ciki, domin wani irin zazzaɓi ne mai zafi ya kama Maryamun, sai da Momy ta nuna ɓacin ranta sannan ne suka samu tayi shiru, amma kuma sai jikinta ya rikice sun rasa gane kanta

Da sauri Hanif ya nufi ɗaki ya sauya kaya ya ɗauko key ya dawo, yace, "Momy mu je asibiti kawai a duba ta."

Momy ta girgiza kai tace, "ciwon Maryam ba na asibiti bane, ina ganin har da mutanen ɓoyen ta, babu yanda za a yi kamar Maryam ta riƙa wannan abun in har ba su bane, Ni ina kokwanto wlh, mu je kawai gidan Malamin da ke bata magani."

Hakan kuwa aka yi, shi ya ɗauke ta ya dire ta a cikin Mota,
Sanda suka tafi can sai ga kiran Dady,
Haka Momy ta ɗauka tace masa, "sun je gidan Malam ya biyo su can."

Da saurin sa ko zama bai yi ba ya fito suka wuce da drivern sa,
Lokacin da suka isa Malamin duk ya gama mata addu'o'i ya tofa mata, sai sannan suka samu natsuwarta ta dawo dai-dai duk da bata dena hawaye ba

Kiran sunan ta Malamin yayi, sai ta ɗago kai tana kallonsa, yace, "share hawayenki ki dena kuka kin ji Maryam?"

Babu musu ta share hawayen tana duƙar da kanta lokaci guda jikinta sai faman rawa yake yi

Sai ya kalli su Momy yace, "har yanzu mutanen nan suna nan kusa da ita basu rabu da ita ba, amma baza su taɓa cutar da ita ba, domin a bincike na na gane ƙaunar da ke tsakanin su da ita ne shiyasa har yanzu suke tare da ita, da suna son cutar da ita da tuni sun cutar da ita, amma kuyi haƙuri ku ci gaba da yin mata addu'o'i da magungunan da nake bata, itama kanta ku saka ta ta riƙa tsare jikinta da azkar, komai zai daidaita zata ga sauƙin abun, baza su taɓa cutar da ita ba, na tabbata su ne suke wannan haukan son ba ita ba, zaku iya tafiya yanzu ma babu wata matsala."

Godiya suka yi masa sosai, inda Dady ya basa abun sadaka sabida a yi wa Almajirai sadaka, sannan suka yi sallama suka tafi tare da maganar Malam da ya tsaya musu a rai

Har suka koma gida Maryamu bata sake magana ba, duk da jefi-jefi tana share hawaye a ɓoye,
Momy ta riƙo hannunta suka shiga ciki sannan suka zauna a saman kujera

Shima Hanif zuwa yayi ya zauna tare da Dady a kan two seater,
Dady da jikinsa yayi sanyi ya rasa me ke damunsa; sai ya kalli Momy yace, "Maryam ƴata ce da na ɗauko ta daga wani wuri domin ta zauna a tare da Ni, ba na son wani abu ya cutar da ita, sai dai ga shi Allah ya ɗaura mata wata lalura da nake ganin tamkar zai zama gazawata a nan gaba, bazan so a ce in sanar da Iyayenta halin da take ciki ba domin hankalin su zai tashi, yanzu me kika ce Khadija; ya zamu yi da ita?"

Shiru Momy tayi domin ta rasa me zata ce ma, illa kallon Maryamu da take faman yi har yanzu tana sharan hawaye jefi-jefi, sai can kuma bayan ta nisa tace, "duk da mu muka haifi SHAREEF amma bamu da ikon da zamu saka soyayyar Maryam a cikin zuciyarsa, amma mu Iyayensa ne muna da ikon da zamu zaɓa mishi abun da yake so, Maryam." Sai ta kira sunan Maryamun tana kallonta, bata bari ta amsa ba ta ci gaba da cewa, "idan kin fi son ki zauna da SHAREEF a haka ba ya ƙaunar ki kinga za ki iya; shikenan zamu tayar da bikin naku kwanan nan, sai a haɗa rana ɗaya da wacce zai aura, ko?" Ta ƙare tana ɗan shafa kanta

Shiru Maryamu tayi bata ce komai ba, sai dai kishi da baƙin cikin jin cewa zai haɗa su da wata shiyasa sam ba ta fahimtar me suke cewa, amma kuma idan zata zauna da SHAREEF shi ne cikan burin ta,
Shi yasa bayan Momy ta sake mata magana a kan, "ta amince zata tare a hakan?"
Sai ta ɗaga kanta tana faman share hawaye

"To shikenan, tashi ki je ki kwanta ki huta, saura kuma ki ci gaba da kukan naki kinji ko?"

Tashi tayi ta wuce ba tare da ta furta ko kalma ɗaya ba,
Suka bi ta da kallo; kallon tausayi har ta ɓace wa ganin su

Sai Dady ya ja numfashi yana kwantar da kansa jikin kujeran tare da zame hulan kansa

Hanif yace, "Momy gaskiya yarinyar ta bani tausayi, amma ina ganin kamar har da yarinta a lamarin ta, baku san yanda SHAREEF yake son Haseena bace, kuma kun fi kowa sanin wane ne SHAREEF da abun da zai aikata, wannan yarinyar ƙaramar yarinya ce, don Allah ku rarrashe ta kawai tayi karatun ta nan gaba sai ta tare, yanzu tayi ƙanƙanta sabida SHAREEF zai iya cutar da ita."

"Kai kenan da kake ɗan uwansa kake faɗin hakan." Momy ta furta ranta babu daɗi, kawai jinjina kanta take yi zuciyarta na mata zafi a kan SHAREEF ɗin, Yaro ɗaya yana son gagaransu,
"SHAREEF bai gagare mu ba, kuma bazai taɓa gagaran mu ba, Maryam dai mu muka zaɓa mishi haka nan zai yi haƙuri ya zauna da ita, abun da yasa na sauko da zaɓin shi domin kar mu shiga haƙƙin sa da yawa, amma duk ranan da ya muzguna wa Maryam, wlh zan ba shi mamaki, don haka yanzu zamu ci gaba da shirye-shiryen tariyan ta a ranar da za a ɗaura mishi aure, tun da wancan Uwar gantalin ba tarewa zata yi ba, sannan ma babu inda zamu kaita a part ɗin ku zata zauna, muna nan tare babu yanda za a yi ya cutar mana da ƴa."

Dady ya gyaɗa kai da furta, "tabbas hakan yayi, nima abun da nake tunani kenan."

Sun ci gaba da tattauna matsalar, while shi kuma Hanif sai ya miƙe yace musu, "zai je ya dawo."
Direct sai ya wuce ya nufi Companin su ya je ya samu SHAREEF a can

Time ɗin yana cikin office din sa ba ya aikin komai sai waya suke yi da Haseena,
A lokacin shi kansa ya ɗan yi mamakin ganin Hanif ɗin, bare yanda ya gansa fuskarsa babu walwala, sai ya yi wa Haseenan sallama

Please Login or Register in order to submit comment