Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ganta a haka ya ji dad'i sosai, sai murna yake yi domin hankalin sa a tashe yake, ya kasa zama yayi karatun sosai sai da ya kira ya ji ko lafiyarta, ana ce masa an sallamo ta sai ya dawo gida bai tsaya ya ƙarisa lectures din nasa ba

Haka suka taru suna ta sanya ta dariya da barkwancin su, suna zaune sun yi shame-shame a Falon sai hira suke yi har su Dady, shi ne ma gwanin tsokanar yana ta basu labarai lokacin da yake gwagwarmaya a baya yana saurayi,
Har yamma suna wurin Sallah kawai ke ɗaga su, sai kuma abinci da a wurin suka ci suka baje a falon, yau basu zauna a dinning ba

Kamar yanda SHAREEF ya saba dawowa karfe biyar sai ga shi ya shigo gidan

Ganin sa yasa Maryamu ta lallaɓa ta shige ɗaki bata ko kalli inda yake ba, domin ba ta son ta ci gaba da kallonsa tana jin tsananin soyayyarsa a ranta, yanzu dole zata saba wa kanta rabuwa dashi, ada ji take yi zata mutu muddin wata rana aka ce za a raba su, amma yanzu tana jin zata iya jure wa gwara tayi nesa dashi, wataƙil abun da Momy ta sanar mata zai kasance Gaskiya, duk sanda aka ce ta sauya ta zama babbar Mace kuma ya dena ganin ta, ƙila zai ji soyayyarta a ransa,
Amma tana jin ƙunci da baƙin cikin kasancewar wata a ransa ba ita ba, wanda hakan yasa sai da ta kasa jurewa ta dinga kuka a cikin daki, kishi da baƙin ciki ya turniƙe mata zuciya, har yanzu tana jin wannan abun da ya tsaya mata a maƙogwaro ya ƙi tafiyar mata, wurin ya bushe koda ta jiƙa da yawu ba ta jin dai-dai, ta rasa yanda zata yi, tana tunawa dashi sai ta ji hawaye da wani irin zafi a zuciyarta, ga wani nauyi da yake mata kamar tana jin ciwo a wurin

Su kuma su Momy ko kusa basu yi wa SHAREEF maganar Maryamu ba, in fact ma basu nuna mishi komai ba kan face ɗin su ba, asali ma ita kanta Momy yau ya ga sakin fuskarta, shiyasa ya ji dad'i a ransa har ya saki jiki fiye da koyaushe,
Ita kuwa Maryamu bata a cikin ransa, ya san cewa warning ɗin da yayi mata ya shiga kunnen ta baza tayi gigin kuskure abun da ya furta mata ba.
***

   
_____Momy ta so a gobe Hanif ya kai Maryamu Abuja ne,
amma Dady yace, "a'a, a bari zuwa Monday time ɗin jikinta yayi sauƙi sosai."

Momy duk ta kira Surayya ta sanar mata da halin da ake ciki, da kuma irin taimakon da zata yi mata na gyara mata Maryamun; ta zama wayayyiyar yarinya fiye da tunanin mutane, duk abun da ta san zai amfane ta ta koya mata; ita kuma ko nawa ne zata kashe mata

Surayya na dariya tace, "ba ki da matsala Aunty, ko Ni zan bada tawa gudummawar ba dole sai kin biya wani abu ba, ai nima ƴata ce musamman ma da ɗanmu take aure, zan kula da ita fiye da tunanin ki, kuma Insha Allahu sai SHAREEF ya raina kansa wlh."

Momy sai jin dad'i take yi, haka suka ci gaba da wayan, sun jima before suka kammala.



           Ranan Monday aka shirya tafiyar nata, Hanif zai kaita tunda yana son zuwa ya gaishe da Ammeen nasu,
shima sai Sadiq yace, "zai je."
Shi yasa suka shirya gaba ɗaya zasu tafi

Har Dady sai da ya yi wa SHAREEF magana, "ko zai je?"

But yace, "a'a." Sabida ganin har da Maryamu a tafiyan shiyasa ya nuna sam bazai je ba, domin ba ya fata a ce doguwar tafiya ta haɗa shi da wannan bak'ar yarinyar da yake jin tsanarta a ransa, gwara su tafi su kaɗai

Maryamu sai kuka take yi kamar me, duk da kukan nata da biyu ne, na rashin SHAREEF da kuma kewar su Momy, haka suka yi ta rarrashinta kamar zasu goya ta,
Don ma wai tare da su Sadiq zata je shiyasa ta ɗan ji dama -dama

SHAREEF na gefe yana kallon abun mamaki, ji yake yi kamar ya tashi ya nakaɗa mata dukan tsiya, sai kallonta yake yi ransa na ƙara ɓaci saboda jin sautin kukan ta da ya cika masa kunne,
Tsaki ya ja ya miƙe yabar wurin ya koma ɗakin su, ta corridorn sama ya tsaya yana kallon haraban gidan; hannunsa riƙe da goran ruwa da ya ɓalle yana sha sabida jin maƙoshin sa ya bushe,
Yana tsaye a wurin ya hange su sun fito har da su Momy sun raka su bakin Mota,
Yana mamakin yanda suke lalace wa a kan wannan yarinyar, musamman yanda ya ga ta lafe a jikin Momy kamar zata mayar da ita ciki, har lokacin sai kuka take yi,
Daƙyar suka lallaɓa ta ta shiga motan,
Takaici yasa ya kawar da kansa yana kallon wani wurin zuciyarsa na masa zafi da tunanin wani abu a ransa,
To yanzu shi ya zai yi ma da auren ta bayan basu ce masa komai ba?
Ko banza zai ji sanyi a ransa kuma yana ji a jikinsa hakan na nufin sun haƙura da maganar kenan, wannan abun farin ciki ne, jira kawai yake yi suyi masa maganar takardan sakin ta,
Sai kawai ga murmushi a kan kyakkyawar fuskarsa wanda har dimples ɗin sa suna lotsa wa sosai, suka fito da ainihin tsantsan kyawun sa,
Dai-dai sanda ya ƙara kallon Motan still da murmushin kwance a kan face ɗin sa

Karaf suka haɗa ido da ita tana cikin mota itama ta ɗago jajayen idanunta da suka gama rinewa da kuka, bata yi tsammanin ganin sa a wurin ba amma sai ta gansa

Kallon-kallo suka yi wa junan su, inda tuni SHAREEF ya ɗauke murmushin da ke face ɗin sa, kowannen su da irin kallon da suke yi wa juna wanda ya sha bamban

Har Motan ta soma tafiya but Maryamu bata ɗauke ido a wurin ba, domin wani irin sanyi da farin ciki ne ya kawo mata mamaya lokaci guda musamman yanda ta ga kyakykyawar fuskar nan nasa mai cike da haiba da kamala tana fitar da sassanyar murmushi, lokaci guda ta ji wannan abun da ya tsaya mata a wuya ya wuce zuruf, yayinda kaso mafi yawan damuwarta kamar an yaye mata,
Bata damu da irin kallon da yake mata ba, amma har a ranta ta ji dad'i, sai kawai ta sakar masa murmushin da bata san lokacin da ya suɓuce mata ba

Hakan ne yasa SHAREEF yayi saurin ɗauke kansa a ransa yana tunanin wa take yi wa murmushi? Lallai wannan yarinyan bata da hankali, ko giyan wake ya sha zai iya soyayya da ita ne bare har ya ji sonta a ransa? Never, bata kai matsayin ba wlh, ya rasa ma wacce zai so sai ƴar tayin yarinyar nan, ko Haseena da ta girme mata yana ganin tayi masa ƙanƙanta bare wannan ƙaramar yarinyar wacce bata wuce ƴar cikin sa ba, amma ita Haseena ai daban take da wannan, tunda tana da abubuwan kallo fiye da wannan, kuma ta cika Macen da kowanne namiji zai so ta, tana da kwalitin da yake bukata ya samu a kan Mace, ta iya kwalliya, wayayyiya ce ajin farko, wacce ta fito daga gidan Hutu da jin dad'i, babu ƙauyanci a tare da ita, tana da class ta ko'ina zai ina nuna ta a Matsayin girlfriend ɗin sa,
Amma wannan kuma fa? Sai ya ja numfashi yana sakin guntun tsaki tare da jefa hannunsa ɗaya mara riƙe da goran ruwan; a cikin aljihun sa,
In ban da baƙar fata da dogon hanci, sai gwala-gwalan idanunta masu kama dana mujiya, bai san kuma abun da ta ajiye ba, a fili ya furta, "shegiya da wasu idanunta kamar zata yi zawo, in banda Jaka ce ita taya ya zata haɗa kai dani? Ta rasa wacce zata so sai Ni? Lallai ma yarinyar nan ta raina min wayon".
Sai ya juya yabar wurin yana jan guntun tsaki yana sake jin ransa na ƙara ɓaci.
[04/03, 9:00 am] OumƊahirah نفيسة: 🌱🌱🌱🌱🌱

      *SHAREEF*
          _SexyBoy_
🌱🌱🌱🌱🌱


_Writer: Nafisat Isma'il Lawal_
_Wattpad: UmmuDahirah_

*SARAUNIYAR TSOKANAR PERFECT🧝*



*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞

```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)```

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

       *P.W.A✍️*





*DATA SHARE*

Call, message or whatsap 07065334256

*MTN*
500MB 150
1gb 280
2gb. 560
3gb. 840
4gb. 1120
5gb 1400
6gb. 1700
Verlid for 30 days.












__________
*BOOK1*
_______________*FREE PAGE48*
 _____Kusan la'asar su Maryamu suka isa Abuja,
A cikin barikin sojoji gidan da ƙanwar Momy take zaune yake, tunda Mijinta Soja ne kuma babba, gidan su yana farko-farkon layi, gida mai number 4,
Babban gida ne kwatas mai cike da flowers da aka ƙawata gidan

Yanayin anguwar da gidan ba ƙaramin burge Maryamu yayi ba, sai baza idanu take yi har suka shiga gidan

Suna tsayar da Motan; Ammee da Yaranta suka fito tarbar su, yanda ka san Momy haka Maryamu ta ga kamannin su da Matar, suna tsananin kama sai dai Momy ta fi su haske, gaba ɗayan su ma ƴan dakin su in ka kalle su sai ka gane jini ɗaya suke, sai dai Ammee ta fi yanayi da Momy har jikin su da ɗan sirantan su, ga yanda kuma ta tarbe ta shiyasa lokaci guda ta ji Ammeen ta kwanta mata a rai,
Ga Yaranta su Yusaira da Aakifah yanda ka san ƴan biyu kansu ɗaya kamannin su ma ɗaya, sai ƴar Autar su Na'ilah wacce ita bata yi kama dasu ba ko kusa, ita yanda kasan Mahaifinsu yayi kaki ya tofar haka suke kama

Da gudu suka zo suka rungume su Hanif suna murnan farin cikin ganin su

While Ammee ita kuma Maryamu ta tarba bakin ta har kunne sabida ganin yanda Maryamun take, faraɗ ɗaya ta shiga ranta musamman yadda ta ganta ƴar kyakkyawa,
Tana riƙe da hannun Maryamun ne take kallon su Hanif tare da cewa, "Yarana yau an tuna dani ko? Sai yau da dalili ya kawo ku shiyasa zan ga ƙafafun ku?"

Dariya suka yi gaba dayansu

"Ok mu shiga ciki, ku kuma ku sake su kun wani maƙale musu daga zuwa."
Cewar Ammeen tana kallon su Aakifah wadanda sai faman murna suke yi

Cikin gidan tace musu, "su shiga."

Sai suka wuce a tare, while Sadiq ya ɗauki Na'ilah a kafaɗa suna dariya su biyun, musamman ita da sai farin ciki take yi sabida an ɗaga ta sama

Cikin Falon suka shiga a tare suka zazzauna a saman kujera, kana Ammee ta nufi wurin fridge tana kiran sunan Yusaira,
Ruwa ta fito da su tare da juice na kwali ta bata, tace, "takai ta ajiye musu."
Bayan ta gama kwaso wa sai ta ɗauko raguwar ta taho dashi, ajiye wa tayi a saman Centre table inda Yusaira ta jera sauran, ta sake ce mata, "ta je ta ɗauko cups ta kawo musu."
Sannan ta zauna tana kallon su da faɗin, "ina SHAREEF ya ƙi biyo ku ko?"

Hanif yace, "wlh kuwa, yace bazai zo ba."

"Hmm shi ya sani, na san dalili ai; cus Aunty ta sanar min komai before ku ƙariso."
Sai ta kalli Aakifah tace, "Aakifah je ki taho da samosan nan da na ajiye a tray ki kawo musu."

Aakifah amsa mata tayi tana miƙe wa tare da nufan kitchen ɗin

While Ammee ta mayar da hankali kan Maryamu da tayi shiru tana zazaare ido a falon, sai kallon hotunan Falon take yi, "Maryam Allah yasa dai baza ki yi min baƙunta ba? Tunda ga Yara nan sa'annin ki ki saki jikinki sosai kamar kina gaban Aunty Khadijah ne, don kulawar da zan ba ki sai ya fi nata ma."
Tayi maganar tana ƴar dariya

Su ma su Hanif dariyan suka yi, while Maryamu murmushi tayi kawai

Sadiq yace, "nima abun da nace mata kenan Ammee tun a Mota, kin san Momy ita ta cika faɗa wlh shiyasa nima nake son dawowa nan, musamman ma in Uncle yana nan na fi jin daɗin zuwa Abuja."

Hanif ya harare sa yace, "ai kuwa kamar a kunnen Momy."

Dariya Ammee ta fashe dashi Maryamu na taya ta; ganin yanda Sadiq ɗin ya kwaɓe fuska yana yi wa Hanif ɗin magiya

Da Yusaira da Aakifan tare suka dawo daga kitchen, ita Yusaira tana riƙe da cups; Ammee ta bata umarnin ta zuba musu ta basu, while Aakifah kuma ta ajiye samosan tana zama gefen Maryamu wadda suka haɗa ido suka yi wa junan su murmushi

Sai kuma Aakifan ta ɗauki ɗaya cup da kanta ta zuba wa Maryamu drinks tana miƙa mata, tace, "Ammee wlh kyakkyawa ce, muna sonta zamu ji dadin zama da ita."

"Haka nake son ji ai." Cewar Ammee tana murmusawa, "ki zuba mata samosan itama ta ci, bari ina zuwa."
Sai ta miƙe ta nufi kitchen tunda ta ɗaura ferfesun kayan ciki da take musu

Su kuma su Yusaira sun saka Maryamun a tsakiya suna ta hira da su Hanif,
While Maryamu tana kurɓan juice ɗin tana haɗa wa da samosan, ta saki jikinta sosai tunda bata da baƙunta, musamman da ta ga su Yusaira suna janta a jiki suna mata surutu, sai yaba kyawunta suke yi suna ce mata, "tana kama da Kajol Agriwal, don dai ita Black beauty ne amma kamar su ta ɓaci, kuma ita ta fi Kajol ido."

Ita dai Maryamu bata ce komai ba tunda bata san wace ce Kajol Agriwal ɗin ba, amma a yanda suke ta zuzuta kamannin ta har su Hanif suna taya su shirmen, shiyasa take ta jin dadi a ranta tunda akwai ta da son a yaba ta

Hira sosai ta ɓarke a tsakanin su, har sanda Ammee ta dawo ta kammala komai ta kwaso food flakes tana jera wa a dining, sannan tace, "su taso su ci abincin."

Gaba dayansu suka nufi wurin har su Yusaira since su ma basu ci komai ba

Bayan sun kammala cin abincin, sai suka ja Maryamu suka wuce ɗakin kwanan su,
Ammee kuma ta nuna wa su Hanif ɗakin da zasu zauna,
Sannan ta fita ta saka Mai gadin su ya kwaso musu kayan su a Boot, da akwatin Maryamu da aka ciko su da kayanta har biyu,
Bayan ya ajiye a Falo, ita da kanta Ammee ta ja na Maryamu takai ɗakin su Yusaira,
Time ɗin ma Maryamu har ta soma sallah, shiyasa ta cewa su Aakifah, "su haɗu su gyara mata kayanta a wardrobe."

Suka amsa mata da to, sannan suka tashi kowacce ta ja akwati ɗaya suka fara aikin

While ita kuma ta fita ta ɗauki ƙaramar Jakar su Hanif; su ma takai musu dakin su,
Na'ilah na tare da Sadiq sai didima take yi a jikinsa ta samu abun da take so, dama jinta take yi kamar ƙaramar yarinya bare an sangarta ta

Hanif ya shiga wanka; sai Sadiq ɗin da ke kwance a saman gado Na'ilah na jikinsa

Ammee ta harare ta tana cewa, "ke fa ba kya jin magana dama, daga zuwan su kin samu abun da kike so baza ki bar su su huta ba ko? Common zo ki wuce ki barsu su huta ki koma ɗakin su Aakifah."

Kwaɓe fuska tayi tana shirin kuka

Sadiq da ke dariya yace, "Ammee ki barta kawai, doki nake mata but in na gama zata fito."

"Kai baka san halin yarinyar nan bane, haka take yi wa Abee ɗin su sam bata girma, in ka biye nata baza kayi abun da ke gabanka ba, zo ki wuce idan kun kammala kimtsa wa sai ta dawo, ga sallah ma baku yi ba."
Sai da ta tasa Na'ilan sannan ta ƙyale shi, don har kuka ta soma yi, ta ja hannunta suka fice

Sadiq kuma yana faɗa mata, "tayi shiru ya kawo mata tsaraba, idan ta ci gaba da kukan bazai bata ba."

Hakan ne yasa tayi shirun har ta dena turjiya a kan bin Ammeen.
***

         
_____Kwana ɗaya su Hanif suka so suyi, but Ammee ta hana su tafiya sai da suka ƙara kwanan, tace, "tunda ba Abee gwara su zauna su yi mata kwana biyu."

Sai da suka zagaya garin gaba ɗaya har su Yusaira sai jin dadi suke yi, tunda ba a barin su fita, basu da lokacin ma kansu kullum suna makaranta,
Sun ji daɗi sosai da suka fita yawon zagaya wa, ga shi Hanif duk ya kashe musu kuɗi ya siya musu kaya da su chocolates kala-kala yayi musu siyayya sosai

Ranan da zasu tafi ko damuwa Maryamu bata yi ba tunda tuni ta saki jikinta, ko lokacin tunani ma bata dashi tunda su Aakifah sun ɗauke mata kewa kodayaushe suna tare da ita suna mata surutu, shiyasa kamar sun jima da sanin juna sun ƙulle sosai bare kansu ɗaya

Bayan su Hanif sun isa gida sannan Momy ta kira Ammee ta sanar mata, sun daɗe suna waya suna sake tattaunawa a kan matsalar Maryamun, daga baya suka yi sallama

To kasancewar Hutu ake yi a wannan lokacin shiyasa Maryamu bata fara zuwa makaranta ba, amma tuni Ammee ta gama cike mata Form an saka ta makarantar haddan su Aakifah da suke zuwa asabar da Lahadi, sai yamma suke dawowa,
Zuwan Maryamun ne yasa Ammee ta nema musu wurin koyan computer, a ɗan lokacin da suke dashi bayan sun dawo hadda da karfe huɗu, zasu riƙa zuwa sai su dawo ƙarfe shida, driver zai riƙa dauko su,
Amma yanzu da ake hutu shiyasa suke zuwa kullum

Lokaci guda rayuwa ta sauya wa Maryamu, kulawa da komai Ammee tana musu, ba ta barin su lalaci tunda Mace ce mai zafin nama itama kamar Momy, komai na gidan su suke yi, ita take raba musu kowa yayi aikin sa, dayake itama ba zama take yi ba tunda tana aikin ta, shiyasa kafin ta dawo sai dai ta zo ta tarar duk sun yi girki sun gyara gidan, idan ta dawo su kuma sai su tafi wurin koyon computern su, har da Na'ilah suke zuwa tunda itama tana Hutu, kuma idan suka barta a gidan ita kaɗai take zaune, sai su tafi da ita ta zauna a can tana wasa, wani lokacin ma har da ita ake koya mata, don dai tayi ƙanƙanta ne da yawa

Shekara ɗaya ne ake koyon computern sai su yaye mutane, shiyasa Ammee tace, "da zaran sun gama zasu koma wurin koyon kwalliya."

Su Aakifah sai daɗi suke ji domin sun fi son haka, domin yanda suke ƙaunar kwalliya in har suna gida zaka ga sun cakare sun yi makeup a kan face ɗin su, shiyasa tayi musu alkawarin, "da zaran sun gama zata mayar da su can su koya kwalliyar."

Ita kanta Maryamu suna burge ta matuƙa, duk da ba kasafai take son kwalliya ba amma idan sun ce zasu yi mata; haka zata basu fuskarta su zana mata suyi ta yabon ta suna cewa, "tayi kyau sosai."
To itama ganin tana yin kyau shiyasa abun ya soma tasiri a ranta, ta ji tana son itama ta iya, dole ta matsa musu su riƙa koya mata tunda ita dai bata iya ba sai nasu na ƙauye,
Tana yawan yin waya da su Innarta tunda yanzu sun san tana Abuja da zama, yanzu ga shi har bikin su Bintu ya zo saura kwanaki, ta so ta je bikin amma Allah bai yi ba, bata da yanda zata yi, tunda su Aakifah ba sa riƙe waya sai dai ta ari na Ammee ta kira gida suyi ta waya, yawanci sun fi daɗewa da Bintu suna wayan tunda yanzu Mijin da zai aure ta ya siyan mata waya, Maryamu ta samu abun yi; tayi ta zama tana bata labarin Abuja tana gaya mata irin daɗin da take sha da kuma abubuwan da suke koya

Sai Bintu ta ji kamar ita, har so take yi dama ace itama a kaita a fasa auren nan, amma babu hali

Izuwa yanzu Maryamu ta koya wa kanta rayuwa babu SHAREEF, duk da bata taɓa tunanin zata iya rayuwa a wani wuri inda babu shi ba, amma zamanta cikin su Aakifah ta soma saba wa da hakan, duk da yana maƙale a ranta, in dai zata zauna ita kaɗai sai ya faɗo mata a rai, har kuka tana yi a ɓoye sabida a kullum soyayyarsa azalzalan ta yake yi, tana shan wahala matuƙa jurewa kawai take yi domin ta saka a ranta baza ta ƙara ɓata mishi rai ba, kamar yanda ba ya ƙaunar ganin ta a tare dashi itama dole zata yi nesa dashi, a yanzu fata take yi Allah ya cire mata soyayyarshi a ranta tunda gani take yi kamar baza ta iya doguwar rayuwa a inda babu shi ba

Kullum Momy sai ta kira ta itama ta ji lafiyar ta, tana jin daɗi yanda ta ga Maryamun ta saki ranta a yanzu, kuma bata taɓa yin mata maganar SHAREEF ba haka itama bata tambaya ba, iyakan su Yaya Hanif take tambaya, in suna nan ma suna yin wayan tare

Dayake tunda bikin nan ya zo ana gobe Dady yace zasu tafi Zaria,
SHAREEF ya so ya botsare a cewar sa bazai je ba, sabida ganin a ranan asabar Haseena zata dawo ranan bikin kenan, bazai so ya tafi ta dawo ba ya garin ba, amma Dady yayi mishi jan ido yace, "dole sai ya je wlh, sabida ko don auren sa da Maryam iyayenta su sake sanin sa, don haka ya shirya dole su tafi tare."

Ran SHAREEF ya ɓaci jin abun da Dady yace, ashe har yanzu suna nan da maganar basu sauya Shawara ba? Shi a ganin sa lokaci kadan yake jira su ce ya sake ta, ashe har yanzu suna ganin ta a matsayin Matarsa basu canza ra'ayi ba, ai kuwa a haka zasu gaji har su raba auren kamar yanda suka ƙulla, don yanzu lokaci kaɗan ya rage masa ya mallaki Haseenan sa, sanyin idanuwansa; wanda yake jin a duniyar nan ita kaɗai ce farin cikin sa, ita ce jin daɗin sa, a ƙagare yake ta dawo amma ga shi an yi masa cikas, tunda ko ta dawo suna can Zaria, since a gobe zata dawo.
***

         
_____A ranan juma'a misalin ƙarfe biyar suka isa cikin Zaria, a gidan Iya Samira suka sauka, murna wurin ta ba a magana, musamman yanda ta gansu dukkan su suka taho, ta rasa ma inda zata sanya su don murna da daɗi, sai kallon su Hanif take yi domin bata iya gane su ba sai da ta tambaya, "wane ne Mijin nata a ciki?"

Momy ta bata amsa tana nuna mata SHAREEF da kuma Hanif ɗin shine Mijinta

"Lallai! Idan a hanya ne na gansu bazan taɓa gane su ba wlh, ba kwa son zumunci ko kaɗan Yaran nan."

"Wlh kuwa Inna, SHAREEF ma bai so zuwa ba sai da nayi masa jan ido sannan ya biyo mu." A cewar Dady

Iya Samira ta sake kallon SHAREEF ɗin tana washe baki, wanda tuni ya duƙar da kansa yana ta faman latsa waya fuskarsa a ɗaure, tace, "yo ai kai ne zaka zo mu ganka tunda yanzu ka zama Mijin Meramun mu, ai mun yi kewarta wlh ba kaɗan ba, ashe bada ita za a zo ba?"

Murmushi duk suka yi,
Momy tace, "tana can Abuja tana karatu shiyasa, kuma bata daɗe da tafiya ba shi yasa bamu zo da ita ba."

"Ai hakan ma babu komai wlh, wata rana zata zo ai, komai lokaci ne."

Haka suka dinga hira bayan sun yi Sallah sun natsa

SHAREEF tun zuwan su Sallan Asar da yayi musu a hanya, sai yanzu suka samu suka yi, sai ya wuce ɗakin zauren da aka gyara musu yayi zaman sa a can, sai yatsina fuska yake yi kamar ya shiga cikin masai tsaban yanda yake nuna ƙyamatar sa da gidan, jinsa yake yi a takure kamar ya kurma ihu ko ya gudu ya koma gida, wlh ba don ɓacin ran Iyayensa ba babu yanda za a yi ya ci gaba da zama a gidan nan, bare kuma wancan ƙauyen da ya fi tsana

Su Hanif kuwa babu ruwansu suna can sun saki jikinsu ana ta hira, ƴan uwa ma sai zuwa suke yi suna gaisa wa tunda Iya Samira ta je ta sanar musu

Shima Dady yace, "da bata je ba tunda zasu shiga har babban gidan."

Da suka je yin Sallan magriba ne shine suka shiga Babban gidan su Iya Samira aka gaigaisa,
Itama Momy daga baya suka je ita da Iya Samira,
A can suka zauna har bayan sallan isha'i before suka dawo gidan,
Kuma suka sake dasa hira tunda an daɗe ba a haɗu ba,
Dama tuwo Iya Samira tayi, haka nan suka ci don Momy tace, "ba sai an musu wani abincin ba, gwara a ɗumama tunda su ma sun jima basu ci irin wannan tuwon ba."

SHAREEF dai ya ƙi

Please Login or Register in order to submit comment