Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

suna ci gaba da waya da Haseena koyaushe, duk da a yanda yake jin matuƙar kewarta a wannan lokacin, shi kansa yana son zuwa ya duba ta since an kwana biyu bai je ba, duk wayan da suke yi da bidiyo call hakan ba ya gamsar dashi, shi kansa yayi mamakin ma yanda bata sake nuna mishi buƙatar son zuwan nashi ba, tunda ya santa in ta fara rigima a kan abu; baza ta bari ba sai ta samu, amma har ita take ce mishi ma, "ya zauna kawai tunda ba shi da lafiya ya huta, ta yafe zuwan nasa."
Shi kuma ya nuna mata ba haka ba, tunda har ga Allah yana matuƙar kewarta, yana buƙatar zuwa su ji ɗumin juna tunda ba ya jin zai iya jure wa, already ya saba da ita, hakan ne kawai yake samun salama daga buƙatar da ke taso masa,
Amma ya san babu yanda za a yi ya bar ƙasar ba tare da sanin iyayensa ba, dole ya soma fitowa waje yana daure wa kamar ya samu lafiya

A ranan da kayan su ya iso ma, har shirya wa yayi ya wuce wurin aiki, tunda so yake yi ya samu damar da zai je wurin Haseena, already ya yanke shawarar da zaran an wuce da kayan gobe, since jibi za a soma aikin, sai ya fada wa Dady, "zasu je Abujan ko two days su yi a can; a fara komai a gaban su."
Shi kuma sai ya samu damar da zai wuce kansa tsaye Australia ba tare da ya je Abujan ba, tunda akwai su PA a wurin ba dole sai ya je ba, zasu faɗa mishi komai abun da ke faruwa,
Wannan tunanin nasa shi ya saka shi shiga farin ciki da walwala, tunda ya samu solution na matsalar sa.
***

_____Yayinda Maryamu tana can tana haukan soyayyarsa bai san ma tana yi ba, tunda ko kallo bata ishe shi ba, in fact ma ko fuska ba ya bata bare ya san Allah ya yi ruwan tsakin ta idan yana wuri,
Amma hakan bai damu Maryamu ba, kullum sake jin matsananciyar ƙaunarsa take ji a ranta, bata damu da halin da yake nuna mata ba tunda ta san yana zuwa wurin ta neman buƙata a cikin dare, kuma bata taɓa hana sa ba duk da sau huɗu kenan abun yana faruwa, tana shiga ɗaki zai zo ya lallaɓa ta yana mata magiyan ta taimaka mishi zai mutu, ita kuma sonshi ya rufe mata ido, burin ta kawai ta faranta mishi kamar yanda yake bukata, tunda tana jin komai nata zata iya ba shi in har SHAREEF zai yi farin ciki, tana mamakin yanda yake nuna mata halin ko'in kula a gidan, amma bata damu ba tunda yana sanya ta farin ciki idan ya kasance tare da ita, tana ganin ko banza dai ta taimake shi a yanda ya raina ta yana ganin ta ba kowa ba

Yanzu kuma abun ya soma damun ta tunda sabida rashin ganin sa da ba tayi a jiya da yau, ko ta kwanta barci ba ta yin mafarkin sa kamar yanda ta saba,
Hakan ya soma damun ta amma babu halin ta nuna,
Tunda da zaran ta canza Momy zata hau tambayarta abun da ke damun ta?

Kullum Sadiq shi ke kaita school ya dauko ta; tunda yana gida a wannan time ɗin,
Kasancewar ya ɗan samu hutu ba ya zuwa school shiyasa yake mata lesson a gida

Ita kuma Momy tana koya mata wasu littafai na addini, tare da hisnul Muslim tana nuna mata muhimmancin yin azkar kodayaushe, kasancewar sun zauna da Dady ta sake mishi bayanin halin da Maryamun take ciki, don ita tana ganin Maryamu tana da aljanu dole sai an taimaka mata, duk da bata ƙara ganin wani alama da zai nuna akwai su a jikinta ba, amma tace wa Dady, "gwara a riƙa amso mata rubutu ana bata tana sha."

Shima Dady ya amince da maganar Momy, tunda akwai malamai a anguwan nasu shiyasa ya yi wa wani malami magana aka soma amso mata rubutun, Sadiq yake zuwa da safe bayan ya kaita school sai ya amso mata, kuma ikon Allah tun daga ranan ne Maryamu bata sake mafarke-mafarken da take yi ba, wanda tana ganin ita a gaske ne, komai da ke faruwa saduwar da ake yi da ita SHAREEF ne yake zuwa wurin ta ba mafarki bane, amma kuma tsaban wauta irin nata bata taɓa ganin alama a jikinta ko na wani abu ba, sai dai ta ga babu kaya a jikinta, hakan yasa ta gasgata SHAREEF ne da gaske yake zuwa wurin ta, kuma dena mafarkin ya jefa ta jin haushin kanta, don bata so hakan ya dena faruwa da ita ba, har tana jin a ranta ko dai zata je ɗakin sa ta ba shi haƙuri ne; wataƙil laifi tayi masa ya dena zuwa, baza ta so ta rasa wannan damar da ta samu ba,
Amma kunya da tsoron abun da zai biyo baya yasa ta haƙura bata je ba


Bata san ma yayi tafiya ba sai yau asabar da Sadiq yake faɗa mata, "SHAREEF yana Abuja, zai yi kwana biyu before ya dawo."

Haka kawai ta ji zafin tafiyan nasa duk da bata da yanda zata yi, shiyasa kwata-kwata ranan bata yi walwala ba

Momy da ta fahimci halin da take ciki, sai ta zaunar da ita tana tambayarta dalilin ɓacin ran yau, sai faman fushi take yi tana kumbura fuska

Maryamu tace, "babu komai, ba ta jin dadi ne."

Momy murmushi tayi tace, "ko dai duk sabida SHAREEF kike wannan fushe-fushen? Ba ki so yayi tafiyar bane?"

Kallon Momyn tayi, sai ga hawaye sun cika mata ido, sai tayi saurin dauke idanun sabida ba ta son Momy ta fahimci halin da take ciki, ta girgiza kanta alamun a'a ta kasa magana, domin in ta buɗe baki tana jin kamar zata fashe da kuka ne


Momy wacce ta gama fahimtar ta gaba ɗaya, har ga Allah tana tausayin yarinyar, ƙanƙanuwa da ita da shiga matsalar soyayya, tana jinjina wanne irin so Maryamu take yi wa SHAREEF da har take kasa ɓoye shi, sai tace mata, "ki je ki kwanta to, in kin tashi sai mu ɗaura karatun."

Da sauri kuwa ta miƙe ta nufi hanyar ɗakinta ta shige

Momy ta raka ta da kallo sannan ta miƙe ta koma ɗakin Dady, a can ta same sa zaune, shiyasa ta faɗa masa shawaran da ta yanke a kan barin Maryamu ba tare da an yi bikin auren su an huta ba, gwara a ba wa SHAREEF Matarsa tunda shi kansa yana bukatar Mata kusa dashi, bata ga amfanin zaman Maryamu a haka da auren ba, tunda itama tana son SHAREEF ɗin, idan ba a kusanta shi da ita ba SHAREEF bazai taɓa sonta ba, ko don yanda suke zaune a gidan babu wani ci gaba gwara a ba shi Matarsa ya san cewa Matarsa ce wataƙil zai haƙura ya ƙaunace ta

Dady da ya gama jin zantukan Momyn, sai yace, "a yanzu dai ba shi da wata matsala gaskiya, yanda ta ga ya dace hakan za a yi, idan SHAREEF ɗin ya dawo sai su faɗa mishi, inyaso a sanya ranan tarewa su zauna a nan."

Ita kanta Momy bata yi tunanin zai canza shawaran nasa ba, shiyasa ta ji daɗi tace, "wlh ban yi tunanin zaka amince ba."

Yana murmusawa yace, "haba sabida me? Ai na san yanda ƴata take son shi nima bazan so in ci gaba da ƙuntata mata haka ba, idan aka yi auren; mu ma sai mu huta tunda na ga alamar ɗan naki shegen taurin kai ne dashi, yana buƙatar auren amma babu Mata a gaban shi, alamu ya nuna ko budurwa tsayayya ba shi da ita, gwara kawai mu faɗa mishi ga Mata a gida mun yi mishi, Allah ya dawo dashi gida lafiya mu ji mai zai ce."

"To Amin, sai mu fara shirye-shirye kenan? Domin za a yi biki sosai ne gaskiya."

Haka dai suka ci gaba da hiran bikin dukkan su suna farin ciki,
Bayan sun gama maganar ne Momy ta fita, sai kuma wayan Dady ta soma ring, yana duba wa ya ga Abokinsa ne Doctor Umar, Mahaifin su Hunaip. Shi ne ya kira sa a kan zancen Hunaip ɗin dayake ya sanar mishi, duk da a waya suka yi maganar kasancewar Hunaip tuni ya koma wurin aiki sabida kiran gaggawa da aka yi mishi, bai ma gama hutun da aka ba shi ba haka nan ya tafi ba da son ransa ba, ya wuce da Maryamu maƙale a ransa, duk da ya so ya bar maganar sai ya sake samun hutu idan ya dawo sai ya sanar da iyayensa, amma zuciyarsa ta azalzala mishi haka nan ya kira Abbansu ya sanar mishi, shi kuma ya kasa hakura sabida farin cikin maganar; shi ne yanzu ya kira Dady yana shaida mishi, "Hunaip ya ga iri a gidan sa yana so."

Dady yayi mamakin maganar, shiyasa ya gyara zamansa sosai yana cewa, "wai kana nufin Hunaip ya ga Maryam ƴar ƙanwata ne?"

"Wlh kuwa, yace min ya ga yarinyar yana so, tunda kwanaki kafin ya tafi shi yake dauko Nafisa daga makaranta, to a can suka haɗu, yanzu yake faɗa min."

"Ikon Allah! Ai kuwa ban san da maganar ba, tunda Momyn su bata sanar min ba, sai dai kuma akwai matsala gaskiya."

Doctor Umar yace, "wacce irin matsala kenan? Ka faɗa min kawai; ai yanzu ba maganar ɓoye-ɓoye muke yi ba."

Nan Dady ya sanar mishi cewan, "tun a can da ya je ɗaukar yarinyar; aka ɗaura auren ta da SHAREEF, yanzu haka da auren SHAREEF a kanta."

"Ikon Allah! To amma shi ne Alhaji Ahmed baka taɓa faɗa min ba? Abun farin ciki haka amma ka ɓoye min?"

"Kayi haƙuri Docta, mu kanmu ka ga maganar ba wai mun sanar da kowa bane, tunda ban so yarinyar ta tare tun yanzu ba, amma yanzu muka gama maganar da mahaifiyar SHAREEF ɗin; muke cewa gwara a miƙa masa Matarsa zai fi, amma kayi haƙuri."

"Babu komai wlh, ai da Hunaip da SHAREEF duk ɗaya ne a wurin mu, abun farin ciki ne wannan, Allah ya sanya alkhairi, shi kuma Hunaip ɗin Allah ya basa wata, zan kira sa sai in faɗa masa yanda muka yi."

Nan Dady ya amsa da Amin, daga nan suka ɗan yi hira nasu na Abokai, before suka kashe wayan.

🔆🔆🔆🔆🔆🔆🔆🔆






_____ *AUSTRALIA*
      *SYDNEY*
Sabuwar rayuwa, sabuwar duniya, ta shigo wa Haseena a lokacin da bata taɓa zato ko tunanin cewa wata rana zata iya faɗa wa irin wannan rayuwar ba, duk da ita ƴar gata ce, ta taso gidan su babu kwaɓa bare takura da hantara, abun da suke so shi suke yi iyayen su basu wani basu tarbiyya mai kyau kamar yanda addini ya shar'anta ba, amma dai-dai gwargwado tana da kamun kai tunda bata taɓa ba wa wani namiji kanta ba, in fact ma bata taɓa yin saurayi ba sai da SHAREEF ya shigo cikin rayuwarta, wadda daɗi soyayya da tsananin ƙaunar da suke nuna wa juna yasa suke tafiyar da soyayyar su bisa tsarin wayewa da ƙetare iyakan addini, rayuwar da suke yi sam bai kamaci ɗan musulmi ya tafiyar da soyayyarsa a haka ba, amma su sun ɗauki hakan shi ne rayuwa a yanzu, ita Haseena tarbiyya da ilimin addini bai ishe ta ba, yayinda take ganin komai dai-dai ne a wurin ta; in har zata ji daɗin rayuwarta,
While SHAREEF dama shi Boko ya rufe mishi ido, ya ɗauki aƙidar yahudawa ya ara ya yafa, zamansa a England lokacin da yayi karatu; sosai halayyarsa ta canza, ya ɗauki ɗabi'un turawa yayi tasiri a zuciyarsa, musamman kasancewar sa Mutum mara son takura da hayaniya, yana rayuwarsa silent ne ba tare da ya shiga shirgin kowa ba; bare shi ya takura wa kansa, hakan ne yasa daga cikin ɗabi'un sa na al'adan bahaushe; ko in ce ɗabi'un da aka san ɗan musulmi da su, ya ajiye su gefe ya ɗauki zamani da wayewar rayuwa ya saka a kansa, abun har ya shafi addinin sa, sallah ma wani lokacin sai lokaci ya gifta yake yin ta

A taƙaice dai; ruɗin duniya yasa Haseena ta faɗa babban bala'in da muke fama da shi cikin rayuwarmu ta yanzu, wato lesbian. Kuma kaso mafi rinjayen laifin Mahaifinta ne, tunda yana ganin shi ɗan boko ne, wayewa ne kuma abun alfahari ne a ce yau ƴaƴansu sun tafi abroad karatu, wanda bai san cewa hakan na taimaka wa da yawan Yaran mu na Arewa su ajiye ɗibi'un su da aka sansu da shi na ƴaƴan Bahaushe; su ɗauki halayen turawa su ɗaura a kansu ba, wasu daga nan tarbiyyar su ta gama gurɓacewa kenan, a can zasu iya haɗuwa da mutane kala-kala masu aƙidu daban-daban, kuma kowanne da zai yi tarayya da ƴaƴan ka akwai gudummawar da zai bada, komin tarbiyyar Mutum da addinin sa, dole ne zai sauya wasu ɗabi'u, idan ma Allah ya tsare sa kenan, amma ana haɗuwa da ɓata gari da dama masu canza wa Mutum alƙibla, ya afka bala'in da bai taɓa tunanin zai riski kansa a ciki ba

Kwatsam Nana ta shigo rayuwar Haseena, kuma tayi tasiri wajen cin galaba tare da sauya mata tunani, ada Haseena SHAREEF shi ne kaɗai namijin da take ganin zata iya ba wa kanta, shi kaɗai take sha'awa wanda take fatan ranan da zasu kasance tare a koyaushe, bata taɓa sha'awar wani namiji ba bayan shi, sai dai kuma tunda Nana tayi amfani da damar ta wajen shayar da ita zuman daɗi da gusar mata da dukkan damuwarta da buƙatarta, sai tayi dana-sanin cewan da tun farko ta san wannan harkan yana da daɗi, babu abun da zai sa bata afka mishi ba, domin tana ganin tamkar hanya ce mai sauƙi ta samu wacce zata biya wa kanta buƙata ba tare da wani namiji ya shigo rayuwarta ba, tunda baza ta taɓa iya kallon wani namiji bare har ta ba shi damar taɓa jikinta ba; Mutum ɗaya ne SHAREEF, matuƙa ta ji daɗin shigowar Nana cikin rayuwarta, kuma ta bata goyan baya ɗari bisa ɗari musamman da ta san cewa tamkar taimakon ta tayi; wajen gusar mata da ƙishin ruwan da ke damun ta,
Wani irin daɗi da farin ciki ne ke gudana a cikin rayuwarta wanda a ɗan kwanakin nan ba ƙaramin sauya wa Haseena tayi ba, lokaci ɗaya ta faɗa ruwa tsundum gaba ɗaya ta makance da tsananin bukatar Nana, burin ta kawai su rika kasancewa tare suna jiyar da junan su daɗi, idanunta sun rufe ita kaɗai take iya hango wa, sun ƙulle sun zama Abokan juna koyaushe Nana tana zuwa gidan ta domin su jiyar da kansu daɗi, har ba sa gajiya duk da Haseena sabon shiga ce amma abun sai ya zo mata a wani irin yanayi, ba ta sukuni in har bata ganta tare da Nana ba, tsawon kwana biyu Nana tana gidan ko koma wa nasu gidan bata yi, gaba ɗaya ta ba wa Haseena lokacin ta tana nuna mata soyayya mai tsaya wa a rai, ko school ba sa zuwa duk da a da Haseena tana gudun fashi, amma yanzu tuni ta biye wa Nana ko labarin makarantar ba ta yi, kasancewar Nanan ta faɗa mata, "basu da matsala da school ɗin, komai zasu iya samu in har tana tare da ita, so ta kwantar da hankalinta."

Shi yasa Haseena itama ta shashantar da labarin school ɗin. Hatta da maganar zuwan SHAREEF da ya sanar mata zai zo shaf ta manta, tana can tare da Nana sun fita tare zata kaita room school ɗin su, daga can zasu wuce wani party ne da aka shirya isu-isu ƴan Lesbian, su Jenifer suna can suna jiran su

Suna kan hanya ne Haseena ta samu kiran SHAREEF, bayan ta amsa call ɗin yake sanar mata da saukar sa, har ya je gidan but ya ga doors a rufe. Ita kanta ta manta ya sanar mata zuwan nasa, shiyasa gaba ɗaya tadaburce tayi saurin katse wayan after ta faɗa masa, "ga ta nan zuwa yanzu."
Sai ta dubi Nana tace, "Please ki sauke Ni a nan, bazan samu zuwa ba, ina son koma wa gida yanzu akwai wanda yake jira na."

Da mamaki Nana take kallonta tace, "I don't understand? Is there someone waiting for you? Who is he?"

Sai da ta ɗan ja numfashi kaɗan tana rufe idonta, ta buɗe su da sauri tana sake duban Nanan tare da furta, "My boyfriend."

"Boyfriend?" Ta maimaita sunan da mamaki, sai kuma tayi shiru tana mayar da idanunta a kan titin tare da ci gaba da mirza sitiyarin cikin ƙware wa

Hakan yasa itama Haseena tayi shiru bata ce komai ba tana jiran ganin Nanan ta faka motan

"Da alamu it is important in your life? The situation you went through showed me that?" Ta furta tana kallonta cike da tsantsan kishi

Smile tayi kaɗan tana gyaɗa mata kai, before ta furta, "It is impossible for me to leave him alone, since he came from Nigeria for me."

"Are you about to get married?"

Ɗan kallonta tayi saboda yanda ta ji tayi maganar, da sauri ta ɗauke kanta tana haɗiye yawun tsoron ta, "No, sai na gama school. But..." Sai tayi shiru kuma

Dakatar da Motan tayi a gefen titi, kafin ta juyo tana kallonta tace, "I will let you go because I don't want your anger, amma bazan iya jure kina sharing ɗina da wani ba, ina da zafin kishi, ba na buƙatar alaƙar ki da kowa, ban damu ba ko me za ki yi; ki bi hanyar da za ki bi domin rabuwa da shi..."

Tun kafin ta ƙarisa zancen ta soma girgiza kanta nan da nan hawaye suka cika mata ido, da sauri ta furta, "No, Bazan iya ba, shi rayuwata ne, idan kika raba Ni dashi kamar kin raba numfashi na da gangar jikina ne. I can't live without him, he's different."

Wani killer smile Nana ta saki, still fuskarta yalwace da murmushin tace, "must be very important in your life, Wow! Har na ji ya burge Ni since ke ma kina sonsa, no problem babe, now go and we'll talk later."

Jin hakan yasa Haseena ta ji sanyi a ranta, sai da Nanan ta gajula ta ta bata good bye kissing before suka yi sallama ta fita. Ta tari Taxi ta hau ya mayar da ita gida.
***

_____Shi kansa SHAREEF ya ga sauyi da yawa a tattare da Haseena, duk da ba ƙaramin farin ciki ya ji ba lokacin da ya ga kyakkyawar fuskarta mai sanya shi farin ciki da natsuwa a zuciya, musamman idan akwai kwalliya a kan face ɗin ta, shi kansa yana manta kowanne irin tunani ne a ransa ya shagaltu da kallonta, ba ƙaramin kyau tayi masa ba musamman kasancewar makeup ɗin da tayi Nana tayi mata, sosai kwalliyar ta ƙara tsatso kyawunta, haka kayan da ta sanya ya fito da ainihin dirin jikinta wanda yasa har SHAREEF ya gaza haƙuri sabida kishi, yayi mata complaint ɗin fitan ta a haka babu ko mayafi kuma ba da Motan ta ba

Murmushi tayi ta manne mishi a jiki tace, "haba dear, daga zuwan ka sai ƙorafi kuma? Maimakon mu fara shiga ciki ka huta sannan ko me zai biyo baya sai ya biyo, ka san dai babu yanda za a yi in yi tarayya da wani bayan kai, You are the only man I see in my eyes, so duk wanda zai kalle Ni sai dai ya ba idanunsa abinci amma na fi ƙarfin sa, balle nan ba irin local ƙasar mu ba ce da zasu damu da shigan da nayi, ko bai yi maka kyau bane? Domin ka nayi fa."

Ba ƙaramin tasiri kalaman ta suka yi a cikin zuciyarsa ba, wanda lokaci ɗaya ya lumshe idanunsa yana ware su a kanta cike da wani irin soyayyarta da yake ƙara tsaga mishi magudanan jini yana shige wa, hannu ya sanya ya kamo nata yana duban yatsun ta da ta maƙala zobe guda biyu kalan ja, wanda Nana ta bata su a daren jiya, ita kanta bata san zoben mene ne bane, kawai ta amsa a matsayin gift ne, kuma ba ƙaramin kyau suka yi mata ba, wanda kyawun da suka yi wa SHAREEF a ido ne; yasa ya kasa yin shiru yana tambayarta, "Aina ta siya?"

Shiru tayi tana tunanin ƙaryan da zata yi masa, sai kuma tace masa, "a super market ta siye su, cuz sun yi mata kyau ne."

Kissing hannun yayi before ya furta, "nima sun yi min kyau sosai, sun ƙara ƙawata hannun ki."
Rungumo ta yayi sosai a jikinsa sannan suka nufi cikin gidan,
Gaba ɗaya SHAREEF ya maƙale mata ya hana ta ko kwaƙƙwaran motsi tayi, wani irin kewa da buƙatar ta ne ke ɗawainiya da shi, haka ya dinga matsa ta yana romance ɗin ta cikin ƙware wa da nuna soyayya

Babu yanda Haseena ta iya dole ta biye mishi, sabida itama har ga Allah tayi kewarsa sosai, sai dai kuma ko kusa ba ta jin sha'awar sa a tattare da ita, ba kamar baya ba, yanzu kamar an cire mata ƙaya sam-sam ba ta jin wata buƙatar sa, kuma kwata-kwata ba ta jin daɗin abun da yake mata, amma ya zama dole ta biye mishi kar ya zargi wani abun; kasancewar ya santa kullum ita ce da ƙorafin ya kusance ta, har kuka take yi in suna tare tsaban yanda take matuwar son su ji daɗi tare, ita kanta tayi mamakin yanda ta ji gaba ɗaya ta sauya sam-sam ba ta farin ciki sosai da zuwan SHAREEF, sabida ta san tamkar takura ce a tare da ita, duk da soyayyarsa bai ragu ko kaɗan a zuciyarta ba, amma kuma ba ta jin sha'awar sa kwata-kwata; daure wa kawai take yi tana biye masa suna shan soyayya, ga shi a wannan lokacin tamkar wani maye yanda ka san chewing gum haka ya maƙale mata, wani sabon salo ma ya tsiro mata dashi ko gajiya ba ya yi da maƙale mata, wuni a ranan suna manne da juna sai da dare ne ta huta time ɗin yayi barci, har ta samu suka yi waya da Nana don ita lokacin ne ta haukace da nata buƙatar, sai da suka yi video call sannan ta samu ta runtsa,
Yayinda ta kwana da tunanin hanyar da zata bi domin samun fita gobe ita kaɗai su haɗu da Nana, don baza ta iya jure halin da take ciki ba, kuma bata san ranan tafiyan SHAREEF ba since bai faɗa mata ba, zuwan sa gaskiya ya zame mata takura wanda daga baya gaba ɗaya farin cikin ta yayi ƙaura, da saƙe-saƙen abun da zata yi ta samu ta fita batare da shi ba; ta kwana a ranta

Sai dai kuma a washe garin ne SHAREEF ya samu waya daga PA ɗin sa, mummunar labari kayan da suka kai Abuja gaba ɗaya sun ƙone ƙurmus. Kayan da ya kai kusan 100 millions wanda ba a san daga ina gobaran ta tashi ba, komai da komai ya ƙone. Tashin hankalin da SHAREEF ya shiga baki ma bazai iya misalta shi ba, lokaci ɗaya ya rikice sabida wannan babban asara ne suka samu, dole ya ruɗe tunda ya san cewa hakan na nufin rasa komai nasu

Ita kanta Haseena hankalin ta ya tashi sosai da ya sanar mata, kuma ta tausaya mishi sabida ganin yanda ya koma duk ya rasa sukunin sa

Nan da nan ya nemi jirgin Nigeria, duk da bai samu ba sai can yamma, ya rasa inda zai saka kansa sai amsa calls yake yi daga ma'aikatan sa suna faɗa masa halin da ake ciki

PA ma har ya sanar masa, "yanzu haka Dady ma yana can wurin, kuma ya tambaye shi amma yace mishi ya koma company sabida kiran gaggawa da ya samu, don haka ya kamata ya san yanda zai yi yayi saurin dawowa tun kafin Dady ya fahimci ba ya ƙasar ma baki ɗaya."

Wani irin sabon rikice wa SHAREEF yayi, har wani zazzaɓi-zazzaɓi yake ji a jikinsa, gaba ɗaya ya rasa ƙwarin jikinsa, kawai tunanin halin da zasu shiga yake yi musamman Dadyn sa, tunda wannan dai ba ƙaramin asara suka samu ba, dole zasu kasance cikin tashin hankali. Ƙarshe airport ɗin ya je ya zauna tare da Haseena, sai da lokacin tashin su yayi sannan ya tafi

Basu kai Nigeria ba sai a washe gari kusan ƙarfe goma na safe, suka sauka a airport na Aminu Kano. Ya rasa ma inda ya kamata ya wuce, don

Please Login or Register in order to submit comment