Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ya ƙi yi bare ya sakar masa fuska, duk da shi SHAREEF ya mara amma ba shi da riƙo ko kaɗan, tuni ya manta abun da ya faru yanzu ransa ya saki sosai, fatan sa kawai komai ya wuce, wlh bai taɓa tunanin zai iya ba shi haƙuri ba a yanda ya san halin SHAREEF, amma sai ya tsinkayi muryansa yana ba shi haƙuri a kan marin da yayi masa,
Tuni Hanif ya miƙe zaune yana kallonsa, sai ya saki murmushi kawai yana furta, "Ni ne nayi maka laifi kuma Ni ya kamata in baka haƙuri Bro, wani lokacin ina manta kai Yayana ne har nake iya furta maka duk abun da ya fito daga baki na, amma bazan sake ba Insha Allahu."

"Kana da right ɗin da zaka sanar min ko ma mene ne, sabida kai ne ɗan uwana kuma Abokin shawarata, na ji dad'i da baka sanar da su Momy abun da ya faru tsakanin mu ba, na san da yanzu Momy ta sake ɗaukar fushi da Ni, ka fi komai a wurina Hanif, ka faɗa min duk abun da kake so bazan taɓa hana ka ba, Ni kaina ban san meyasa na ɗauki zafi har haka ba, amma kayi haƙuri komai ya wuce bazan sake marin ka ba."

Sai kawai Hanif ɗin ya rungume sa cike da farin ciki, yana sake cewa, "kayi haƙuri Yaya."

Janye jikinsa SHAREEF yayi yana ɗan hararansa da wasa, yace, "ba na son Yayan nan fa, wani sai yace na girme ka ne bayan a yanzu ka fi Ni tsawo sosai, let's just live as friends."

Dariya yayi shi kuma, ganin SHAREEF ya miƙe zai fita, sai yace, "ina kuma zaka je yanzu?"

Shiru ya ɗan yi, sai kuma yace masa, "ina zuwa zan sauka ƙasa ne in sha ruwa."
Bai jira cewar sa ba ya fice,
Kai tsaye downstairs ya sauka, ya tsaya yana tunanin inda zai bi ya nemi ɗakin Maryamu, shi kansa bai taɓa sanin ina ne dakin nata ba, amma yau yana buƙatar sani ko don ya dauki mataki a kanta, kai tsaye ɗakunan da suke wurin corridor ya nufa, kusan daki biyar ne a wurin, duk wanda ya taɓa a rufe suke, ɗaya ne kawai ya ji a buɗe, but koda ya shiga babu kowa, babu kaya ma a ciki sai bed, sai ya fito ya taɓa na ƙarshen, nan ma a buɗe yake, sai ya zurma kai ciki, a nan ya hango ta kwance a saman bed ta rufe jikinta da blanket, har da ɗan sauke ajiyar zuciyar sa; tukunna ya nufi wurin kansa tsaye da tunanin abun da yakamata yayi mata.









[02/03, 9:22 am] OumƊahirah نفيسة: 🌱🌱🌱🌱🌱

         *SHAREEF*
             _SexyBoy_
🌱🌱🌱🌱🌱


_Writer: Nafisat Isma'il Lawal_
_Wattpad: UmmuDahirah_

*SARAUNIYAR TSOKANAR PERFECT🧝*



*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞

```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)```

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

       *P.W.A✍️*





*DATA SHARE*

Call, message or whatsap 07065334256

*MTN*
500MB 150
1gb 280
2gb. 560
3gb. 840
4gb. 1120
5gb 1400
6gb. 1700
Verlid for 30 days.












__________
*BOOK1*
_______________*FREE PAGE46to47*
_____Ƙarisa wa yayi gaban gadon, ya tsaya yana faman kallonta; duk da ba ya ganin face ɗin ta kasancewar ta juya baya, tunani yake yi ta yanda zai yi ya tashe ta, cike da mugunta kuma ya saka hannu ya ɗuma mata duka

Lokaci guda Maryamu ta ji wannan dukan har cikin barcin ta, ba shiri ta tashi a firgice tana neman wanda ya duke ta a cikin barci,
A tsaye ta ga Mutum ƙiƙam wanda bata gama tantance wane ne ba, kasancewar akwai duhu ɗakin baza ta iya bambance mutumin da ke tsaye ba, ga kuma barcin ta yayi nisa bata gama wartsake wa ba

Hannu ya sanya ya kifa mata marin da sai da ta hantsala ta dungura kanta a kan gadon sabida azaban zafi; da kuma yanda marin ya zo mata babu tsammani,
Wani irin kuka ta kurma sabida tsananin raɗaɗin da ya shige ta,
Take a nan jikinta ya soma kerma tana shirin ƙara kurma ihun, domin ta gama firgita ta gigice, ba wai don marin ba, sai don tsananin tsoron wanda yayi mata wannan aika-aikan cikin wannan daren,
Sai kuma ta ji saukar hannu mai tsananin taushi da aka ɓame mata baki; hakan yasa sautin kukan nata ya ƙi fita,
Saukar muryansa da ta fito a kausashe ya tabbatarwa da Maryamu wa ke tsaye a gabanta ya aikata mata wannan ɗanyen hukunci, lokaci guda ta sake tsure wa ga tsananin mamakin jin muryansa a kunnenta, a tunanin ta ko mafarki ne, shiyasa ta sake ware idanunta a kansa tana kallonsa da kyau ta cikin ɗan hasken da ya ƙillo a window na farin wata

Shi kuma saboda tsaban mugunta gam ya rufe mata bakin nata har yana haɗa wa da hancin ta, cikin wani irin yanayi da ɓacin ranta ya gama saka shi, yake cewa, "ke dan Ubanki aina kika taɓa ganin na taɓa wasa da ke?"
Ya zazzaro mata ido yana jiran ta ba shi amsa duk da ya ƙi sakin bakin nata

Jikinta sai faman rawa yake yi tana tunanin me tayi mishi, ga shi babu damar ta motsa saboda yanda ya ɓame mata baki da hanci numfashi ma daƙyar take yi, hakan ne yasa tayi saurin ɗaura nata hannayen a kan nasa tana ƙoƙarin cire mishi hannun

Amma sai ya buge mata hannayen tare da ƙara ɓame bakin, ya sanya hannunsa ɗaya ya buga mata a kan kunci, kauu ya kaure ta da wani marin; cikin kausasa murya irin wanda yake cike da tsananin tsana gami da jin haushin ta, yace, "dan Ubanki warning na zo in buga miki, daga yau idan har na sake jin suna na a bakin ki, ko kuma kika nuna Ni kike so a gidan nan, na rantse da Allah duk ranan da kika yi gangancin zuwa cikin gidana a matsayin Matata, sai na illata ki, sai na kashe ki kin mutu murus, banza wawiya ƴar ƙauye kawai, har ke kina da bakin da za ki ce kina so na? Ni sa'an wasan ki ne? Or did I ever play with you? Ƴar ƙarama da ke shegiya ba ki kai matsayin ƴar aiki na ba ma, ki saka a ranki Ni SHAREEF na fi ƙarfin ki har abada, bazan taɓa zama da ke a matsayin Matata ba, I hate you so much, I hate you more than anyone in this world, ba na ƙaunar ki! I don't like to see your ugly black face."
Sai ya sake kifa mata wani marin yana huci tare da buga mata tsawa sabida jin zata yi masa ihu, ya zazzare mata idanunsa da suka kaɗa suka yi ja yake cewa, "har ke za ki shiga tsakani na da Iyaye na; da ɗan uwana? Ba a haife ki ba wlh, duk ranan da kika bari kika kaini maƙura sai nayi miki dukan tsiya a gidan nan, kuma ki sanar da su Momy ba kya so na, kar ki yi gigin shigo min gida sabida bazan taɓa zama da Jaka ƙazamiya irin ki ba." Sai ya tofa mata yawu wanda yayi nasaran kwalɓa mata a fuska,
Ya juya ya fice ko sake waiwayo wa bai yi ba

Maryamu she couldn't move where she was, because she was in shock, almost 3 minutes before ta ja wani irin numfashi at the same time hawaye na ɗiga zuwa kan fuskarta, waɗanda sai a yanzu suka samu nasaran fitowa, wasu hawaye ne masu ɗumi suke gudun tsere,
Hannunta na rawa ta sanya a kan face ɗin ta inda ta ji saukar yawun sa a wurin, sharo wa tayi tana kallon hannun duk da ba ta ganin komai; sabida duhu da kuma ruwan hawayen da suka cika mata ido, kalaman sa suke mata yawo a zuciya wani abu ya zo ya tokare mata a maƙogwaro,
Sai kawai ta kifa kanta a saman gadon ta fashe da wani irin kuka mai ban tausayi, kuka take yi sosai tana jin zafi da tuƙuƙi na ƙaruwa daga zuciyarta, har wani riƙe maƙoshin ta take yi tsaban yanda ta ji wani ƙululun abu mai kama da yaji ya tokare ta,
Tunda take bata taɓa jin tayi matuƙar muzanta irin na yau ba, kalaman sa sun mata ciwo kuma yanda ya wulaƙanta ta ya tofa mata yawu a kan face; hakan ya ƙara saka ta cikin wani yanayi wanda tana jin dama a ce bata fara ba, dama ace bata fara sonsa ba, meyasa take son shi? Mene ne dalili? Wacce ƙaddara ce tasa har ta san shi a duniya? Yau tana dana-sanin sanin sa a rayuwarta, meyasa tun farko ta san shi? Meyasa zuciyarta take azalzalan ta a kansa? Meyasa baza ta iya jure wannan baƙin cikin ta cire sa a ranta ba?
Amma zata iya mutuwa, tabbas zata mutu duk ranan da aka ce ta rasa SHAREEF a rayuwarta, ji take yi kamar baza ta iya numfashi a inda ba ya nan ba, ya zata yi da ranta? Meyasa ba ya sonta? Me tayi masa da zafi haka?
Tuno kalaman sa da yake faɗa mata tace wa Momy ba ta son shi, hakan yasa ta ƙara fashe wa da wani sabon kukan tana ƙanƙame zanin gadon, sai kuka take yi ta kasa yin shiru bare ta saurara wa kanta,
Tun tana yi da iya ƙarfin ta har ta gaza sai hawaye ke fita a idanunta; yayinda wani irin tsananin ciwon kai ya saukar mata, inda jikinta sai faman rawa yake yi lokaci guda ta soma rawan ɗari,
A wannan daren bata runtsa ba sabida kuka ta dinga yi ta kasa koma wa barcin ta, kalaman SHAREEF kawai take tuna wa a ranta, meyasa ita bata zo a Sa'a ba? Don kawai ta kasance a ƙauye shi ne ya tsane ta?
Tana so ta faranta masa rai, bata son ta ci gaba da ganin tsanar ta a cikin idanunsa, tana son ya so ta, tana sonshi baza ta iya rabuwa dashi ba duk wulaƙancin da zai yi mata, tana ganin kamar son sa shi ne ajalin ta, ita nata ƙaddaran kenan son maso wani wanda yake ganin ta a ƙasƙance bata kai matsayin ya so ta ba,
Dole zata tafi tabar masa gidan ko don samun kwanciyar hankalin sa, ko kusa ba ta son ta ci gaba da ɓata masa rai bare ya ci gaba da ganin baƙin ta, ko iya haka tana ji a ranta tayi Nasara, nasaran da ta ceci abun ƙaunar ta a rayuwa, zata tafi tana mai farin ciki a ranta tunda har wani abu daga cikin jikinta yana yawo a jikinsa, wata rana idan ya tuna dole zai tuna da ita, zai san cewa ta taimake sa a rayuwa, ko bai so ta ba baza ta taɓa manta shi a rayuwa ba, ta gummaci ta zauna da auren sa a haka ta ci gaba da rayuwa domin baza ta taɓa son wani bayan shi ba, shi ne duniyar ta, shi take jin zata so har ƙarshen numfashinta

Kafin safe zazzaɓin ya rufe ta sosai, kuma ga tsananin ciwon da ko ɗaga idanunta ba ta iya yi, tana son ta nuna dauriya da juriya ta tashi but ta gaza,
Har garin Allah ya waye tana nan kwance sai rawan sanyi take yi

A haka Momy ta zo ta tarar da ita cikin wani mawuyacin hali, idanunta sun kumbura suntum sun rine alamun ta sha kuka da kuma rashin barci,
Momy ta kiɗime sosai da ganin Maryamu a haka,
Da sauri ta isa wurin ta tana yaye bargon jikin nata, sai ga wani huci mai zafi ya bugo ta, take ta furta kalman Subhanallah..! Tana jero mata tambayoyi hankali a tashe

Sai kawai ta fashe mata da kuka tsaban yanda take jin ciwo mai tsanani yana sukan ta a ƙirji, tamkar ta cire ƙirjin ta yasar saboda yanda yayi mata nauyi; ga wani abu da ya tokare mata wuya har yanzu ya ƙi wuce wa, muryanta kanta ba ta fita tsaban wahala da yanda ta kwana a cikin kuka

Take Momy ta juya ta fita ta kira Dady, sai ga su sun shigo gaba dayansu ban da SHAREEF da suka bari a Falo,
Dukkan su fuskokin su cikin damuwa da tashin hankali suke kallonta

Inda Dady ke tambayarta abun da ke damun ta?

Amma Maryamu ta kasa magana sai rawan ɗari da take yi

Momy ta ɗago ta cike da tsananin tausayinta tana sakin salati, "Allah ya yaye miki abun da ke damun ki Maryam.."
Sai kuma tayi shiru tana share hawayenta da suka fito sabida tsananin tausayin Maryamu, matuƙa tana tausaya mata duba da yanda take ƙaramar yarinya amma kullum tana cikin ciwo, basu san ya zasu yi da ita ba, daga wannan sai wancan

Hanif ne yace, "Momy ina ga fa, kawai mu kaita asibiti kar jikin yayi tsanani, kinga yanda take yi fa alamun zazzaɓi ne mai zafi a jikinta."

Dady yace, "eh abun da ya kamata kenan, sannu daughter Allah ya ba ki lafiya, bari mu tafi asibiti in sha Allahu za ki samu sauki."

Hanif da kansa ya dauko ta suka fito daga ɗakin,
A time ɗin babu SHAREEF ya koma ɗaki zai shirya ya tafi Company

Tare da Dady da Hanif suka wuce asibiti,
Momy ta zauna a gida; shi kuma Sadiq ya wuce nasa ɗakin don shirin school, duk ransu babu dad'i sabida tausayin halin da Maryamu ke ciki

Lokacin da SHAREEF ya gama shirya wa ya fito, bai ga kowa a Falon ba, kuma bai damu ya san me ke faruwa ba in dai a kan yarinyar can ne, sabida a yanda yake jin tsanar ta bai ƙi ta mutu ba, duk ita ta haddasa mishi baƙin ciki, tun zuwan ta gidan komai ya soma jagule masa, musamman da ya ji zancen auren su, yanzu bai san ya zai yi ba, bai san yanda zai yi ya sanar da Haseena yana da wata Matar ba, tabbas sai dai ta dauwama a haka amma bazai taɓa amince wa ta shigo gidan sa ba, bazai taɓa ɓata wa Haseenan sa rai ba, ita ce zaɓin sa ba wannan Bagidajiyar yarinyar ba, to ya kaita ina? Ai sai mutanen da suka sanshi suyi mishi dariya duk sanda aka kalle ta a matsayin Matarsa, duk yanda za a yi sai ya samo hanyar da zai rabu da ita, koda hakan zai ja masa ɓacin rai daga wurin Iyayensa, ya san dole zasu sauko wata rana, amma bazai zauna da ita ba.
***

_____Har suka ƙarisa asibitin; Maryamu kuka take yi kashirɓan sabida yanda jikinta ya rikice, ƙarshe Hanif ya ɗauke ta zuwa office ɗin Likitan

A can Likitan yace, "ya ajiye ta a saman gadon da ke cikin office ɗin."
After ya kwantar da ita sai ya soma duba ta; duk da yana ta bata baki tayi shiru but ta ƙi, azaba ya ishe ta musamman kanta kamar zai tsage, ga jikinta da ke faman kerma

Su Dady suna tsaye a office ɗin duk sun kasa zama, kukan ta na taɓa musu zuciya kamar su zubar mata da hawaye haka suke ji, ko da gani sun san tana jin jiki

Haka Likitan ya ƙoƙarta yana duba ta har lokacin bai dena bata baki ba,
Bayan ya gama sai ya haɗa allura ya zo ya tsira mata ba tare da ta san da zuwan sa ba, zafin ciwo ya hana ta sukuni idanunta a rufe sai jin allura tayi ya lume a hannunta, ko kafin ta buɗe ido tuni ya zare alluran,
Kuka ta sake fashe wa dashi tana murkususu
"Calm down mana Maryam, yanzu me ke miki ciwo?"

Kanta ta nuna masa da hannu alamun nan yake mata azaba, kuma ko buɗe ido sosai ba ta iya yi, duk sun kumbura idanun nata sun fita a hayyacinsu

Wani alluran ya sake haɗa wa, ya gane zazzaɓi ne sosai ya kama ta sakamakon rashin samun hutu da kuma kukan da ta sha, uwa uba fahimtar damuwar da ke tattare da ita, ya san in dai yayi mata wannan alluran zata samu sauƙi in har ta samu tayi barci zata samu relief, haka ya ƙara tsira mata wani alluran,
Kafin mintuna uku kukan nata ya ɗauke, sai kuma barci ya biyo baya

Sai lokacin su Dady suka sauke ajiyar zuciya suna ƙara matsowa inda take

While Dady yace, "ya jikin nata Doctor? Fatan dai babu wata matsala babu abun da ke damun ta?"
Yayi maganar a dame

Shi kuma don ya kwantar masa da hankali yace, "babu komai Alhaji, zazzaɓi ne kawai ke damun ta wanda yayi mata mugun kamu a lokaci guda, irin wannan zazzaɓin dama haka yake da rikitar da Mutum, balle ita akwai damuwa a tare da ita sannan da rashin barci, but komai normal zata wartsake da zaran alluran da nayi mata ya sake ta, sai in baku magungunan da ya kamata ta sha, kar ku damu tana nan ma idan ta tashi sai ku wuce da ita kawai, fatan mu dai ya kamata ta cire damuwa a cikin zuciyarta ta riƙa samun Hutu sosai."

Gaba ɗayan su numfashi suka ja suna sake sakin ajiyar zuciya na jin sanyi a ransu, duk da ba kaɗan ba sun damu da jin zancen Likitan na damuwar da ke damun ta,
Duk sun san cewa bai wuce a kan SHAREEF bane wannan abun,
Musamman ma Dady da ransa ya fi ɓaci da zullumin idan har bai yi wani abu a kai ba zasu iya rasa yarinyar, a wannan lokacin bazai saurara wa SHAREEF ba sai ya ci mutuncin sa wlh idan bai bi umarnin sa ba

Likitan rubuta maganin da zata sha yayi a pepper, sannan ya bama Hanif ya je amso wa,
While su kuma suka zauna suka ci gaba da tattaunawa duk a kan matsalar Maryamun, daga baya suka koma zancen ciwon Dady da yake sanar masa, "maganin sa sun ƙare, shima yana buƙatar a duba sa don kwana biyun nan ya soma jin sauye -sauye a jikin sa."

Hakan ne yasa Doctor ya duba sa,
Ko kafin Hanif ya dawo har ya gama kuma ya rubuta mishi nashi maganin yana ba shi wasu shawarwarin

Hanif ya sake komawa ya amso na Dadyn sannan suka ci gaba da zama suna jiran ta farka,
Tsawon lokaci har Likitan ya samu pation sannan suka tashi suka fita a tare

Dady yace ma Hanif, "ya koma gida shi zai zauna."

Bayan ya tafi babu jima wa Momy ta zo tare da driver, dayake Dady ya sanar mata, "ba gado aka basu ba yanzu zasu dawo da zaran ta farka."
Amma duk da haka sai da ta taho wa Maryamun da breakfast ɗin ta tunda bata ci komai ba

Suna zaune suna jiran ta farka,
Tsawon awanni huɗu tana barcin before ta farka,
Kuma jikin nata da sauƙi ba kamar yanda aka kawo ta ba, garau ta miƙe sai kanta da ke mata ciwon ne kaɗan-kaɗan,
Sun ji daɗin ganin ta a haka sai murmushi suke yi


Likita ya sake duba ta ya tabbatar musu da babu wata matsala, sannan yace, "a bata wani abu ta ci sai ta sha maganin, inyaso sai su wuce gida kawai."
Ganin yanayin jikin nata babu ƙarfi; ya san in aka bata abinci zata samu ƙwarin jikinta sosai, yace, "a hankali shima kan zai dena."
Sai ya fita ya basu wuri

Sai sannu suke mata kamar zasu mayar da ciwon jikinsu sabida yanda suka damu da ita, tamkar ƴar da suka haifa haka suke jin ta a ransu, suna matuƙar tausaya mata,
Momy ta haɗa mata tea a cup, ta soma bata da kanta tana yi mata sannu,
After ta gama sha sai ta ciro maganin; ta bata ta afa a baki, sannan ta ƙarisa da sauran tea,
Cus ta san halin ta a yanzu, ba ta cika son shan magani bane, sai dai a bata da wani abun ban da tsuran ruwa, ta dinga kwarara amai kenan, shiyasa tunda ta laƙanci halin ta sai take dama mata koko ko kunu; ko kuma tea sai ta sha dashi

Bayan sun ga ta samu natsuwa, sai Momyn take tambayar Dady me Likitan yace ke damunta?

Dady bai ɓoye mata komai ba ya sanar mata, da irin ɓacin ran da yake ji a cikin ransa

Ita kanta Momy baƙin cikin hakan take ji, shiyasa ta furta, "wlh Alhaji ina ji a raina idan har wani abu ya samu yarinyar nan; SHAREEF ne sila, komai da ke faruwa da ita shi ne silan komai, kuma duk sabida shi ta shiga wannan halin, kuma ke Maryam sai da na fada miki ki kwantar da hankalin ki in dai SHAREEF ne kin same shi kin gama, mun rigada mun miki alkawarin tarewan ki nan kusa a cikin wannan satin ma ba sai an je da nisa ba, to me yasa baza ki cire damuwa a cikin ranki ba? Kin fi son ki kassara kanki a kan wanda bai damu da ke ba? Kina nan kina haukan sonsa?"

Maryamu da idanunta ke rufe tana sauraron su, dayake ta jingina bayanta da matashin da aka saka mata a bayanta sabida ta ji dadin zama, Momy ta hana ta kwanciya kasancewar yanzu ta gama cin abinci,
Sai da suka gama maganar ta buɗe idanuwanta da suka yi mata nauyi sabida halin ciwo, daƙyar take iya furta maganar nata sabida muryanta ta rigada ta shaƙe ba ta fita sosai, a hankali tace, "Momy Ni yanzu na canza shawara ma, na fi son in yi karatuna tunda na samu dama, ba na son ci gaba da zama a nan ki kaini inda kika ce za ki kaini, ko kuma a mayar dani gida in je in yi karatu na a can, hakan zai fi min kwanciyar hankali."

Shiru suka yi dukkan su, duk da sun ji mamakin maganar nata amma tausayin ta ne ke tasiri a ransu

Ita kuma hawaye ne suke ƙoƙarin fito mata ta sanya hannu tana share wa, yayinda ta hana bayyanan su kan kuncin ta

Dady ya kamo hannunta yace, "Maryam ke ƴata ce halak malak, duk abun da kika nuna kina so ko aina yake in dai bai fi karfina ba zan miki, don haka maganar zancen soyayyar ki da SHAREEF da kuma tarewan ki a gidan sa tana nan daram a yanzu, wannan satin mai zuwa za ki tare a ɗakin shi, ba ki da wata damuwa ki cire komai a ranki kinji ko?"

Girgiza kanta tayi wanda idanunta sun kaɗa sun yi ja kuma ta ƙi yarda ta zubar da hawaye, sai dai ƙwalla da suka taru mata, cikin rauni tace, "Dady Ni dai ba na son in tare yanzu, na haƙura karatu nake so, dama shi ya kawo Ni garin nan shi nake son yi, don Allah Dady ku cika min burina ina son in yi karatu mai zurfi."

"Kin tabbatar hakan kike so? Baza ki saka wani damuwa a ranki ba? Babu wata matsala ko?"

Kanta ta ɗaga mishi alamun eh

Hakan ya yi wa Momy dad'i don wlh kwata-kwata ba ta son Maryamu ta tare tun wannan lokacin bata san ciwon kanta ba, akwai ƙuruciya a kan Maryamu, zata sha wahala a hannun SHAREEF, yanda ba ya sonta ɗin nan kuma ya tsane ta, komai zai iya mata; baza ta taɓa jin daɗin zama dashi ba, itama kuma ba ta son hakan, ta fi so ta zauna da soyayyar SHAREEF, yana sonta tana sonshi wannan shi ne burin ta, tana jin yarinyar kamar ita ta haife ta, musamman yanda take kamanceceniya da ɗanta Sadiq kamar tagwaye, ita kanta suna kama sabida idanunsu da suke kusan iri ɗaya, sai ka ɗauka sun haɗa jiɓi da Momy fiye da Dady ma, sai dai kawai baƙin fatar da take dashi ne amma suna kama sosai, shiyasa soyayyarta take ƙara shiga zuciyarta tana jinta a ranta kamar ƴar cikin ta.
***

          
_____A lokacin Doctor ya zo ya sallame su suka wuce gida, time ɗin jikin Maryamu yayi sauƙi sosai, ita kanta tayi ƙarfin hali wurin ɓoye damuwarta, ta saki jikinta kamar wacce bata yi ciwo ba

Hanif ya ji daɗin ganin ta sai tsokanarta yake yi, yana cewa, "kamar wacce ba ita bace ɗazu ta kusa mace musu, tafiya ma ta kasa sai shi ya ɗauke ta, amma yanzu ta dawo garau da ƙafafuwanta kamar ta fi shi lafiya ma yanzu."

Sai dariya take yi kuwa, ta saki jikinta sosai domin tana jin dad'in yanda Hanif yake wasa da ita, har sanyi take ji a ranta sabida ganin kaman su ɗaya da SHAREEF, tana jin kamar shi ne a gabanta suke magana tare, hakan na saka ta farin ciki

Su kansu sun ji daɗin yanda ta saki jiki tana dariya da raha, kamar ba ita ba, hakan yayi musu dad'i

Koda Sadiq ma ya dawo ya

Please Login or Register in order to submit comment