Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

  
_____Duk da Momy bata so aka tarun mata a gida ba, amma bata da yanda zata yi, dole ta ɗaura girki tunda ƴan uwanta sun zo, wasu ma sai ƙara tururuwan zuwa suke yi duk da duk dangi ne a wurin,
Ana zaune ana ta hira, su Aunty Zainab kuma suna can suna haɗa abincin da za a ci

Ita kuma Momy jin Ammee bata kira ta yau ba, shiyasa ta dauki waya ta kira ta, amma jin yanayin muryanta cikin tashin hankali shiyasa ta miƙe tsam tabar cikin jama'a, ta haura sama ta shiga ɗakin ta, sai da ta zauna a kan gado take ƙara tambayarta tare da cewa, "wai lafiya Surayya duk kin ɗaga min hankali? Me ke faruwa ne?"

"Babu lafiya Aunty, tun asuba nakai Maryam asibiti, jikin babu dad'i."

"Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un! Me ke damun ta; me likitocin suka ce?" Momy ta furta a ruɗe

"To zazzaɓi ne dai Aunty, amma yayi mata mugun kamu don tana jin jiki, sai yanzu ma na samu ganin ta wlh, amma tun ɗazu duba ta suke yi, yanzu ma gani a ɗakin da take tana Barci, sun sanya mata drip har biyu a dukka hannunta."

Momy kamar zata yi kuka ta dinga furta salati cikin tsananin damuwa

"Amma Insha Allahu sun ce da zaran ta tashi jikin zai yi sauƙi, da alamu yanayin jinin ta kenan da saurin ɗaukar ciwo mai zafi, haka suka faɗa, amma sun ce nan da nan zai sauka."

Ajiyar zuciya Momy ta sauke tare da faɗin, "to yanzu ya za a yi? Hankalina ya tashi wlh, bari Dadynsu ya dawo sai in faɗa mishi musan yanda za a yi."

"A'a kar ki tayar masa da hankali, mu bari mu ga yanda hali zai yi, Ni ina tunanin ko ta ji zancen da muka yi ne a yammacin jiya, domin tun jiya jikin nata ya rikice, da har ta samu sauƙi kuma yau da asuba jikin nata ya sake tashi, nan na tarar da ita tana ta sambatu tana kiran sunan SHAREEF, gani nake yi kamar ta san da auren da muka yi magana jiya da ke, sabida furucinta da ta dinga yi."

"Ba mamaki ƙila ta ji ne, mun ƙara tono mata da zancen, kai! innalillahi wa'inna ilaihi raji'un! Wannan wacce irin ƙaddara ce? Wlh na rasa ya zan yi? Taya ya zan sanya SHAREEF ya ƙaunce yarinyar nan? Tana azabtuwa wlh, Ni da da hali wlh sai na cire soyayyar shi a zuciyarta, ban taɓa ganin irin wannan soyayyar na Maryam ba, Allah ya ɗaura mata soyayyar maso wani, ba ki ga yanda SHAREEF yake farin ciki da wannan auren ba, na tabbata hankalinsa ba ya wurin Maryam, bazai taɓa sonta ba."

Cike da damuwa Ammee tace, "kar ki ɗebe tsammani Aunty, na tabbata wata rana zai so ta duk da irin soyayyar da yake yi wa wancan, mu dai taya ta da addu'a domin shi take buƙata a gare mu, Allah ya yaye mata domin ya zame mata masifa da cuta a tare da ita, tana cikin wani hali."

Shiru Momy tayi sabida ta kasa ma furta komai don tsananin damuwa da tunanin halin da Maryamu take ciki

Sai Ammee tace, "Aunty bari zan yi sallah yanzu, wlh tunda muka zo asibitin tun asuba ban samu nayi sukuni ba sai yanzu da na shiga na ga halin da take ciki, hankalina a tashe yake shiyasa ban kira ki ba sai yanzu da na samu sukuni; na ɗauki waya kuma sai ga naki kiran,
bari in yi sallah kar lokaci ya ci gaba da ƙure wa."

"To Shikenan, idan ta farka don Allah ki kira Ni."

Amsa mata tayi sannan suka yi sallama ta kashe wayan,
Miƙewa Ammee tayi ta shiga toilet ɗin ɗakin, alwala ta ɗaura sannan ta fito ta fita cikin ɗakin, ɗakin da ke kusa da su ta leƙa ganin da mutane sai ta shiga ta ari sallaya ta dawo, mayafin ta ta gyara tayi rolling ɗin sa sannan ta kabbara sallan,
After ta idar ta zauna doguwar azkar, ta jima tana zikiri daga baya ta soma addu'ar nema wa Maryamu sauƙi wurin Allah, domin har ga Allah yarinyar tana bata matuƙar tausayi,
Ta jima tana addu'a before ta miƙe ta mayar musu da sallayan, sannan ta zauna ta tasa Maryamun a gaba tana kallonta, ga shi babu halin barin wurin balle ta koma gida ta nema mata abun da zata ci, ita kanta yunwan take ji sosai, shiyasa ta ɗauki waya ta kira driver ta tambaye sa, "ko su Aakifah suna nan basu tafi makaranta ba?"

Ya sanar mata, "tun safe yakai su."

Haka nan ta sauke wayan cike da damuwa, sai kuma ta sauya shawara ta sake kiransa, "ka zo yanzu ka ɗauke Ni ka mayar dani gida."

"To ranki ya daɗe." Ya amsa mata cikin girmamawa

Tana ajiye wayan ta ci gaba da zama tana kallon Maryamu, a tunanin ta zata iya farkawa ma, amma har driver ya zo bata farka ba, shiyasa ta bi shi suka koma gida, cikin sauri-sauri ta haɗa breakfast ɗin a cikin basket; tunda su Aakifah sun yi komai, zuba wa tayi ta fito tace ma drivern, "ya koma da ita."
Allah yasa ma yau bata da aiki, da bata san ya zata yi ba,
Har ta koma Maryamu bata farka ba, shiyasa hankalin ta ya kwanta, zuba breakfast ɗin tayi ta ci nata sannan ta ajiye sauran; tabar ma Maryamu nata a food flakes.



_Finally an yi auren, sai mu jira mai zai faru kuma. Fatan alheri Masoya._
[11/03, 8:14 am] OumƊahirah نفيسة: 🌱🌱🌱🌱🌱

       *SHAREEF*
           _SexyBoy_
🌱🌱🌱🌱🌱


_Writer: Nafisat Isma'il Lawal_
_Wattpad: UmmuDahirah_

*SARAUNIYAR TSOKANAR PERFECT🧝*



*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞

```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)```

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

       *P.W.A✍️*





*DATA SHARE*

Call, message or whatsap 07065334256

*MTN*
500MB 150
1gb 280
2gb. 560
3gb. 840
4gb. 1120
5gb 1400
6gb. 1700
Verlid for 30 days.












__________
*BOOK1*
_______________*FREE PAGE56*
_____Yau dai SHAREEF ya zama Ango already ya mallaki Haseena; kwanyansa ta faɗa. Allah -Allah yake yi ya samu damar da zai keɓe da Amaryansa, domin har ga Allah ba ya jin zai iya jira har wani lokaci, tunda ya mallake ta haka nan zai lallaɓa ta ya rika amsar haƙƙinsa since already ta zama nasa, amma kuma bai samu wannan damar ba a yau, sabida tunda suka tafi yin party ba su suka dawo ba sai gab da Magriba,
Koda suka dawo gida time ɗin duk an watse babu kowa a gidan,
Wanka suka soma yi dukkan su,
Hanif ya soma shirya wa ya fita zuwa masallaci tunda time yayi ana ƙoƙarin kabbara sallah,
Shi kuma SHAREEF sai da ya ɓata lokacin sa kamar yanda ya saba shiryawa, ya tsaya ƙalƙale jikin sa, domin so yake yi daga can ya wuce gidan su Haseena ya ganta, ko fita sai su yi inda zai samu ya huta, shiyasa sai farin ciki yake yi, wani farin yadi ya saka a jikinsa tamkar tissue, kayan sun halittu a jikinsa, bai saka hula ba sai yayi amfani da baƙin takalma sandal, agogon hannunsa kuma fari ne mai kyau da tsada, har wani daukar ido yake yi,
Bayan ya gama ya feshe ko'ina nasa da turarukan sa masu shegen ƙamshi da shiga rai,
Ya zura wayansa a aljihu ya fita ta ƙofan baya zuwa masjid, time ɗin ma an kusa idar wa, haka nan ya jona sallan ya gama sannan ya fito, direct cikin gida ya nufa ya dauki Motansa ya fice,
Wayansa ya ciro ya soma laluban numban Haseena, bayan ya kira ta babu jima wa tayi peaking, ɗaura wa yayi a kunne cike da nishaɗi ya kira sunan ta

Haseena na zaune a gefen gadon ta, fitowar ta kenan daga wanka tana tsane gashin ta da towel, sai ta ji kiran SHAREEF ɗin, hannu ta sanya ta ɗauka tayi peaking, jin ya kira sunan ta sai tayi murmushi tana cewa, "Ango ka sha ƙamshi."

Dariya ne ya kufce masa sabida jin abun da tace, "Wow! Sweetheart, by the way, ban ji daɗin kalman nan ba sai yanzu da naji shi a bakin ki, you didn't feel how happy I am, today I am very happy, kin fi kowa iya faɗa."

Murmushi tayi tana fari kamar yana gaban ta

"Ina kan hanya yanzu zan zo gidan ku, but ki shirya fa don fita zamu yi."

Ɗan waro ido tayi, tace, "ina zamu je?"

Dogon numfashi ya ja, kamar bazai yi magana ba sai ya rage murya kamar wani na jinsa, cikin wani irin shauƙi yace, "just zamu je hotel ne mu ɗan huta, kin san bazan iya jurewa ba dole yau in zama sabon Ango kamar yanda kike faɗa."

Gabanta ne ya faɗi, amma sai ta kanne cikin shagwaɓe murya tace, "dear, Ni yanzu ba na gida fa, mun tafi gidan Uncle ɗin mu, a can zamu kwana, sai dai ka bari idan mun dawo."

"Kina nufin bazan samu abun da nake so ba? And kuma ba ki sanar min ba?"

"I assume baza ka damu ba shi yasa, haba dear." Tayi maganar tana bubbuga ƙafa

"Shikenan, but ko in zo nan?" Yayi maganar kamar zai yi kuka, don wlh bai so hakan ba

"No, don ALLA Ni dai kar ka zo, already yanzu na zama naka, saurin me kake yi? Ka bari idan na dawo sai ka zo mu haɗu."

"Amma ban ji dadi ba sweetheart, any way zan iya jure wa since da yau da gobe duk ɗaya, amma ki faɗa min lokacin da za ki dawo please?"

Haseena tace, "sai yamma dear, cuz ka san tunda na dawo ban samu na je ba, shiyasa Abba yace mu bi su mu kwana."

"Ok, I'll go back home since I won't find what I'm looking for, we'll meet tomorrow and you should prepare, da zaran na dawo aiki by four zan zo in ɗauke ki mu fita, Please sweetheart ki tanadar min kanki da kyau yanda zan ji daɗin ki, You know I love you, tomorrow I want you to show me how much you love me."

Hmm kawai Haseena tace mishi, amma a ranta tana tunanin yanda za a yi ta kufce masa, amma ta san wayon da zata yi masa

Da haka suka ci gaba da wayan har sanda yace mata, "ya kawo gida, zai kira ta daga baya."

Daga nan ta ajiye wayan after ya kashe, shiryawa tayi cikin farar riga na barci har zuwa gwiwarta, mai kwalliyan less a gaban, rigan tana da kauri, hula ta sanya a kanta before ta ɗauki wayanta ta fita ko damuwa da yin Sallah bata yi ba, don yanzu gaba ɗaya ta dena sallah tunda ta hadu da su Nana, sosai rayuwar Haseena ta sauya fiye da baya.






🔆🔆🔆🔆🔆🔆🔆🔆

_____A ranan da daddare aka sallami Maryamu daga asibitin, since jikin ta da sauki sai dai haɗa mata magunguna suka yi kala-kala

Ammee ta ji dad'i sabida dama tunanin kwanan take yi a asibitin,
Kai tsaye gida suka wuce gaba ɗaya since su Aakifah suma duk suna asibitin a tare, tunda suka dawo makaranta driver ya kawo su,
Duk cikin su babu mai walwala sabida ganin yanayin jikin Maryamu, a hakan ma ta samu sauƙi babu abun da ke damun ta sai rashin ƙarfin jiki, da kuma damuwa da ta sanya wa ranta

Likitan da ya duba ta sai da ya sake gargaɗan ta, "ta kula da lafiyarta, ta dena sanya damuwa a ranta domin tana matsa wa kanta da tunani, kuma hakan zai iya haifar mata da babban matsala."
Faɗa sosai yayi mata tunda irin mutanen nan ne masu zafi da saurin faɗa in dai a kan lafiya ne, tunda ya faɗa mata, "in har ta ci gaba da saka damuwa ƙarshe ciwon zuciya zai same ta, since yanzu ma jinin ta ya soma hawa, akwai yiwuwar ta samu bugawar zuciya nan take a irin wannan tunanin da take sanya wa ranta."

Koda suka koma gida sai da Ammee ta zaunar da ita tayi mata nasiha da faɗa sosai, tace mata, "muddin ta naƙasa kanta a banza ne, tunda wanda take yi don shi bai san ma tana yi ba, in zata saki ranta ta koma rayuwarta normal; ta koya wa kanta rayuwa babu shi, ya fiye mata alkhairi, domin duk sanda ta samu ciwo shi babu ruwansa, bai ma san tana yi ba, sannan ma ita ta cuci kanta tunda hakan bazai ƙare ta da komai ba, shi yana can yana rayuwarsa cikin kwanciyar hankali, ita ta kwazzabi kanta ta hana kanta sukuni a kan ɗa namiji, haka zata ƙare rayuwarta cikin wahala tunda Maza haka suke babu tausayi a ransu, idan suka ƙilla ido a kan wata Macen; abu mai sauƙi ne su juya maka baya, bare ita da ba sonta yake yi ba, gwara ta yi wa kanta faɗa."

Kuka ta dinga yi tana sauraron faɗan Ammee ɗin

Daga karshe itama ta koma rarrashinta tana nuna mata muhimmancin lafiyarta, ko babu komai ta cire sa a ranta ko don lafiyarta, idan bata tsira da lafiyarta ba taya ya zata iya yaƙin ƙwato Mijinta? Sosai tayi mata nasiha ta bata shawarwari kala-kala yanda zata taimaki rayuwarta har ta samu sauƙi daga zuciyarta

Tabbas Maryamu ta ɗauki shawarwarin ta, kuma tayi ƙudirin amfani dasu koda hakan zai cutar da ita ne, daga yanzu dole ne ta haƙura da SHAREEF na har abada, domin wannan tana ganin shine ƙaddaran ta, ta sanya wa ranta haƙuri da juriya, dama tun farko ai bata sanshi ba, amma meyasa tayi rayuwarta normal? Sai yanzu da ta sanshi zata saka damuwa a ranta har take tunanin baza ta iya rayuwa ba?
A'a, ta dauki wannan ƙaddaranta ne, soyayyarsa ita ce babbar cuta a gare ta, kuma da sannu zata nemi maganin warakan

Don haka daga rana mai kama ta yau, ta sanya wa ranta baza ta sake zubar da hawayenta a kansa ba, ta yi wa kanta alƙawari, zata koma Jarumar ta wacce hawaye ke wuyan fita a idanunta, in har ta cika Mace tabbas sai ta nuna wa SHAREEF kuskuren sa, da sannu zata yi maganin matsalarta

Shi yasa tun daga ranan ta binne soyayyar SHAREEF a zuciyarta da iya ƙarfin ta, duk wani abun da zai kawo mata tunanin sa ta dena yi, ta fuskanci rayuwarta ɗoɗar babu wani gargada

Dawowa hutun makaranta, hakan ya taimake ta sosai, tunda ana dawowa Ammee ta je ta nema mata makarantar, dayake komai yanzu da kudi ake yi kamar yanda suka faɗa tun farko, shiyasa ba a sha wahala ba aka saka Maryamu ajin su Aakifah, tare da Yusaira da Maryamu SS 1C suke,
Ita kuma Aakifah tana SS 1A

Alhamdulillah makarantar ta yi wa Maryamu dad'i ba kaɗan ba, itama kamar makarantar da ta baro ne, tun safe sai ƙarfe biyar ake tashin su, har Islamiyya ake musu a can,
Tun dama Maryamu mai burin yin karatu ne, shiyasa bata sanya wasa ba a wannan lokacin, nan da nan ta soma gane wa ana tafiya da ita a class din, bare dukkan su aji ɗaya suke shiyasa suke zama suyi ta karatun idan sun dawo, wacce bata gane wani abu ba sai ɗaya ta tuna mata, da haka suke samun sauƙin karatun sosai,
Basu da lokacin kansu ma, da zaran asabar da Lahadi yayi zasu wuce makarantar haddan su, karfe daya in sun yi sallah a can suke dawowa, sai ya zamana yanzu ba sa samun lokacin zuwa koyon computer sai weekends ɗin idan sun dawo daga hadda

Haka rayuwa ta sauya ma Maryamu a ƙanƙanin lokaci, koma in ce ta sauya komai nata a ƙanƙanin lokaci,
Su Ammee sun ji dad'i ba kaɗan ba musamman yanda ta saki jikinta babu sauran wani abu kuma

Momy sai farin ciki, shiyasa jefi-jefi tana kiranta tayi ta bata shawaran abubuwan rayuwa

Kuma tana ɗauka gaskiya, tunda tana amfani da duk wasu shawara da zata bata, shiyasa yanzu take jin daɗin rayuwarta, SHAREEF kuwa da ƙarfi da yaji ta binne tunaninsa da soyayyarsa a cikin ƙasan zuciyarta, tamkar bata taɓa sanin halittar sa ba

Ana haka Abee ya dawo, sai dai bai jima ba ya koma, one week kawai yayi, don dama iyakan yawan hutun nasa kenan, in yayi wuta ne yayi wata ɗaya a gari, ba ya zama sosai

Ita kuma Ammee baza ta iya bin sa ba sabida aikin ta, sannan kuma da makarantar Yaranta ba ta son gantalin nan, ada tana bin shi sosai but tunda suka girma aka saka su a school ta aske wa kanta, ta zauna wuri ɗaya idan ya je ya dawo ya same ta a nan, dalilin da yasa ta nemi aiki kenan; sabida ragewa kai damuwa.






🔆🔆🔆🔆🔆🔆🔆🔆



_____Duk yanda SHAREEF ya so ya angwance da Haseena, abun ya faskara, domin ta ƙi ba shi haɗin kai, yayi nacin but ya hakura tunda ba ya son ɓacin ranta ko kusa, kullum sai sun fita tare sun je Hotel, a can yake hutawar sa, duk yanda ya so yayi mata wayon ya kasa, har fushi yayi da ita ya nuna, "ba ta ƙaunarsa, da tana sonshi baza ta ƙi abun da yake so ba, ta san tsawon lokaci abun da yake jira kenan, amma kuma yanzu gudun sa take yi."

Sai tace mishi, "ita bata shirya ba gaskiya, kuma tsoron ta kar ta samu ciki ne bayan tana tsaka da karatun ta."

Riƙo ta yayi ya ƙara manna ta da jikinsa, cikin sigan rarrashi yake ce mata, "haba Haseena, wanne ciki kuma don kawai za ki bani farin ciki? Kuma idan ma cikin ne ai abun farin ne, ko dai kin dena sona ne? Gaba daya kin sauya kamar ba Haseenan da na sani ba, Na san kin fi Ni bukatar wannan abun, amma yanzu guduna kike yi, kin fi son na mutu ne bayan kin san halin da nake ciki? Please sweetheart help me sau ɗaya fa kacal zan yi, bazan ba ki wahala ba i promise you."

Noƙewa tayi tace, "no Ni dai a'a, Please tashi mu koma gida ka ga dare yana yi, gaskiya bazan iya barin ka ba cus ba na son na samu ciki, after all nayi ma Abba alƙawari kuma daga baya ya zo ya ga ba haka ba, in fact ma yace min in dena fita gudun samun matsala."

Shiru SHAREEF yayi ya rasa ma abun yi, amma sai bai ce komai ba ya miƙe ya mayar da kayansa yace, "ta tashi su je."

Itama tashi tayi ta mayar da nata kayan tare da ɗaukar gyalen ta ta yafa, ta dauki jakarta ta bi bayansa sabida har ya fice, ko kusa bata damu da yanda ya nuna ba, amma don ta nuna mishi kamar ta damu, bayan sun shiga Mota sai ta soma ba shi hakuri har da ƙwallan ta

"Is ok, yanda kike so hakan zan yi, amma idan na mutu Haseena ke kika kashe Ni, ban san meyasa kike son canza min ba, akwai hanyoyi da dama da zamu bi wanda baza ki ɗauki ciki ba, duk hakurin nan da nayi ba kya gani ko?"
Ya kare maganar yana kallon fuskarta kamar zai yi kuka

Hannunta ta daura a saman cinyansa tana mai langaɓe kanta, "I'm sorry dear, Kayi hakuri ba a son raina bane, but kwana nawa ne ya rage zan gama karatun wai? Lokaci fa gudu yake yi please ka kwantar da hankalin ka don Allah."

Bai yi magana ba har ya kaita gida ya dire ta,
Sai dai dole ya saki face ɗin sa sabida yanda ta dame shi har da kukan ta wai, "ba ta son ganin sa a haka."

Shi dai ya rasa yanda zai yi haka nan ya biye mata ya wuce gida abun sa,
Tun daga ranan ya dena ma fitan da ita tunda ba ya samun biyan buƙata, ko sun fita karshe wahala yake sha, domin har ciwo sai da yayi a ɗan kwanakin nan, ya ƙwallafa rai a kan abu amma ya kasa samu, ba ya son ya ɗauki zafi a kanta since ba ya son ɓacin ranta,
Tun yana ɓoye wa Hanif dole ya sanar masa halin da yake ciki

Hanif yayi mamakin abun da Haseena take yi wa SHAREEF, amma gani yake yi son da yake nuna mata ne yasa yake biye mata take yin duk abun da take so, to meye amfanin soyayyar da kuma auren in har baza ta cire shi a wannan ƙangin da yake ciki ba?
Shi yasa ya sanar mishi, "shi fa yana ganin kamar Haseena hankalin ta ya soma barin wurin sa, yakamata su zauna su fuskanci juna idan ba haka ba zai iya halaka kansa."

SHAREEF ya kasa cewa komai don bai san me zai ce ba, domin shi kaɗai yasan iya azabtuwar da yake yi, ji yake yi kamar bazai kai gobe ba in har bai samu abun da yake so ba, amma ya zai yi? Har ga Allah yana sonta ba ya son ɓacin ranta, tun farko shi ya nace mata ya lallaɓa ta har ta amince suka yi auren, ya san idan ya matsa mata kamar ya cuce ta ne

"Ni ga shawara Bro in har baza ka bi wannan hanyar ba, mai zai hana tunda ba ita kaɗai bace Matarka; ka koma wurin Maryam domin biyan buƙatar ka, dama ai gida biyu maganin gobara ne, tunda dama ta ƙi sai ka koma hagu."

Sai da gaban SHAREEF ya buga sabida jin zantukan Hanif, shi har ga Allah ya manta da shafin yarinyar can, tab ɗijam! Tashin hankali kenan, mai zai faru idan Haseena ta gane yana da wata Matar? Tabbas akwai aiki a gabansa kenan

A tunanin Hanif yayi shiru ne yana sauraron sa, shiyasa sai ya ƙara gyara zama sabida son ya samu galaba a kansa, "Ni na san baka son yarinyar, amma mene ne amfanin ta? A irin wannan halin da kake ciki zaka iya samun solution Bro; ba tare da ka ɓata wa ƴar gaban goshin ka rai ba, Maryam zata iya ɗauke nauyin ka, zaka iya mu'amala da ita ba wai dole sai kana sonta ba, zaka iya biyan buƙatarka da ace ka cutar da kanka, kayi tunani Bro, itama Matarka ce halak malak".
[12/03, 9:19 am] OumƊahirah نفيسة: 🌱🌱🌱🌱🌱

       *SHAREEF*
           _SexyBoy_
🌱🌱🌱🌱🌱


_Writer: Nafisat Isma'il Lawal_
_Wattpad: UmmuDahirah_

*SARAUNIYAR TSOKANAR PERFECT🧝*



*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞

```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)```

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

       *P.W.A✍️*





*DATA SHARE*

Call, message or whatsap 07065334256

*MTN*
500MB 150
1gb 280
2gb. 560
3gb. 840
4gb. 1120
5gb 1400
6gb. 1700
Verlid for 30 days.












__________
*BOOK1*
_______________*FREE PAGE57*
_____Wani kallo SHAREEF yake watsa mishi tun soma maganar nasa, tuni ya ɗaure fuskarsa zuciyarsa na tafarfasa da jin kalaman Hanif ɗin, "lallai baka da hankali Hanif, Ni kake nufi zan nemi wannan Jahilar yarinyar baƙauyiya sabida in kau da sha'awata? That will never be possible, because I was stronger than that girl forever, bazan taɓa neman alfarma a wurin wannan ƙasƙantacciyar yarinyar ba, don't do this to me again or you will see my anger again a second time, zan maka abun da baka taɓa tunani ba."
Ya ja tsaki ransa a ɓace yana miƙe wa yabar mishi ɗakin ma


Yayinda Hanif kuwa murmushi yayi yana shafa gemun sa, ko kusa maganar SHAREEF ɗin bai ba shi haushi ba, sai ma taɓe baki da yayi a ransa yana cewa, "akwai ranan ƙin dillaci."
Sai ya ɗage kafaɗa alamun bai damu ba yana mai miƙe wa tare da ajiye wayansa, ya nufi hanyar toilet ya shige.

          Wasa-wasa har hutun su Haseena ya ƙare ta koma school; SHAREEF bai samu abun da yake so ba, amma ya ya iya? Soyayyarta ta rinjayi duk wani abu,
But ya saka a ransa da sannu dole ne ya shawo kanta, ko bai yi nasara yanzu ba zai yi wani lokaci.
***

_____Yau da gobe rayuwa ta ɗaura ta ci gaba da tafiya kamar yadda ta saba, kwanaki na shuɗewa haka ma satikai, yayinda aka ɗaura watanni a kai

Kuma har wannan lokacin soyayyar SHAREEF da Haseena bai canza ba, tun tafiyarta bai samu ya je wurin ta ba, duk da yana ta mata mitan ta ba shi time but ta ƙi, ya lallaɓa ta har ya gaji, shiyasa ya yanke hukuncin zuwan mata a bazata,
Bai samu matsala wurin Iyayensa ba tunda yace musu, "zai je duba Haseena ne."
Ganin Matarsa ce babu wanda ya hana sa, iyakan jan masa kunne da Dady yayi a kan, "bazai riƙa zirya zuwa wurin ta a duk sanda ya so ba, don haka yasan da sani tun wuri dole ya riƙa sanin abun da yakamata, koda Matarsa ce bazai riƙa ziryan zuwa wurin ta a kai-

Please Login or Register in order to submit comment