Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ka ci ka ba."

"Mom Allah zan ci, amma bani da lokaci yanzu, gwara in je can, in na gama meeting zan ci i promise you."

"Did you promise me? I don't want you to disagree with me."

"Allah Mom." Yayi maganar yana marairaice fuska

"Shikenan, but baka manta da maganin ka ba ko?"

Gyaɗa mata kai yayi yana kallonta

"Ok go, sai ka dawo, amma kar ka manta baka ci komai ba SHAREEF na gaya maka, ba a shan magani babu abinci wata matsalar ne kuma. Allah ya bada Sa'a, ya kare ka da dukkan maƙiya masu bin ka da sharri."

Sai a lokacin yayi murmushin sa da ya fito da jerin haƙoransa; kuma ya bayyana dimples ɗin sa masu ƙara matsa tsantsan kyawu, ya kama hannunta yayi kissing, tare da amsa wa da, "Amin Mom, bye." Ya sakar mata hannun yana fice wa da sauri. Da ɗan gudun sa ya taka steps ya sauka ya nufa hanyar fita

Dai-dai lokacin Maryamu ta fito daga nata ɗakin, ta hange sa yana ta zuba sauri, sai ta ɗaga murya cikin zaƙin muryanta da son burge sa tace, "Yaya SHAREEF good moni."

SHAREEF da har ya taɓa ƙofan zai buɗe, sai ya tsinkayi muryanta a cikin kunnen sa, wanda hakan ne yasa shi juya wa don ganin wace ce; since ya manta da akwai baƙuwa a gidan nasu fa

Ɓashe masa baki tayi suna haɗa ido, sai ta ɗaga mishi hannu tana sake cewa, "ina kwana Yaya."

Wani kallo ya sakar mata mai nuni da ƙyamar da yake mata, sama da ƙasa ya kalle ta, sai kuma ya ja tsaki ya juya ya wuce ransa na son ɓaci da ganin wannan baƙar fuskar nata, meye haɗin shi da yarinyar nan da take son raina shi? Har shi zata kira ta gaishe? Lallai kam.. kaɗa kai yake yi yana tunanin ranan da zata shigo hannunsa, yana tunanin sai ya fito mata da ƙwala-ƙwalan idanun nan nata waje, ya taye mata fuskar Magen nan, but yanzu ba shi da ishashshen lokacin ma da zai tsaya jan mata worning.
Motansa ya shiga ya ja ya fice a gidan da gudu kamar zai tashi sama

While Maryamu tana tsaye a wurin sai faman sosa kai take yi tana tura baki gaba, ita ta lura kamar ba ya ƙaunarta ne ma, shiyasa gaba ɗaya ta ji zuciyarta ta soma mata zafi, yayinda take jin tsananin ƙaunarsa na sake huda mata magudanan jininta, kamar ana sake masa halitta ne saboda gani take yi ya fi jiya kyawu da haiba, a ranta take cewa, "Yaya SHAREEF ina sonka, komai naka mai kyau ne." A hankali cike da sanyin jiki ta juya ta koma cikin falon tana zama, yayinda tunanin ta ya bar jikinta ya tafi ga SHAREEF, "Allah ina sonka babu mai raba Ni da kai."

"Ke da wa haka kike magana?" Cewar Momy da ta sauko daga sama, Maryamu bata ji tahowar ta ba

Da sauri ta ɗaga manyan idanunta tana ware su a kanta, sai kuma ta soma soshe-soshe da cewan, "babu kowa Momy, Ni da kaina ne."

Momy da tayi gajeriyar dariya, sai tace, "kin taɓa ganin inda mutum ke magana da kansa Maryam?"

Dariya kawai tayi batare da tace uffan ba, sai kallon Momyn take yi wacce tayi kyau sosai cikin shiganta na farar less mai kama da kamfala, an yi adon shi da sky green color, tayi matuƙar kyau kasancewar ta jawur ce usulin bafulatana

Duk cikin ƴaƴansu ita suka biyo tunda ita ce jawur, so sun biyo hasken ta sosai, musamman ma SHAREEF don shi ya fi ta haske mai kyau tunda shi fari ne tarr, ya bambanta da irin hasken ta. Momy bafulatanan Yola ce, mahaifiyarta da mahaifinta duk ƴan can ne, amma zama ya dawo da su nan tunda suna kasuwanci ne, Allah da ikonsa aka haifi su Momy duk a nan, sai ya zamana gaba ɗayan su a nan suka yi aure, illa Autan su da take aure a Abuja

Mahaifiyar Alhaji Ahmed, wato Hajiya Bilkisu, gidan da tayi aure kusa da na su Momy ne, sanadin da yasa Alhaji Ahmed ya ga Momy har ya aure ta kenan, duk da a lokacin ba ita ya so ya aura ba, ƴar uwanta ce, amma ita tana da wanda take so, sai ta faɗa mishi gaskiya tare da haɗa sa da ƙanwarta, to Alhaji Ahmed bai ja zancen ba tunda a lokacin bai taɓa ganin Momy ba, bayan ya ganta sai ya ga ta fi su kyau ma sosai, tunda a zahiri ita ta biyo iyayenta sak bafulatanan Usul. Sun yi soyayya sosai kafin su yi aure, tunda a lokacin Alhaji Ahmed yana tsaka da karatun sa ne, daga baya kuma ya aure ta bayan ya gama degree ɗin sa, daga nan ya ci gaba da karatu itama tana yi. A yanzu Momy ta gama masters ɗin ta amma ba ta sha'awar aiki, tunda tace, "zaman gidan Mijinta ya fi mata komai." Ita take yin komai na gidanta babu ƴan aiki sai dai masu kula da haraban gidan Maza, duk da daga baya-bayan nan ta so samun masu aiki, amma SHAREEF ya hana su zama, ko an kawo su sai ya kore su, mugun halin da yake nuna musu ma ba ya barin su zama, dole Momy ta haƙura da masu aikin ta ci gaba da ayyukan ta, tunda dama ba ya mata wahala, kawai ta ga yanzu girma ya soma zuwa ne tana buƙatar hutu, ta samu mai yin mata shara da wanke-wanke, shiyasa take yin abun ta da kanta yanzu.
***


      Dayake Momy tace ma Maryamu, "ta je ta shirya zasu fita kasuwa."

Shi yasa ta tashi ta je ta ɗauko gyalen ta tunda har tayi wanka ta saka riga da skirt sababbi, ɗaya daga cikin ɗinkunan da ta zo dasu ne waɗanda suna ɗaya daga cikin wanda Baba yayi musu da Sallan nan, dama duk sababbi ta kwaso kayanta since Birni zasu je. Hoda ta shafa tare da yin ɗigo a goshin ta kamar yanda ta saba yi koyaushe, ya zama ɗabi'ar ta ma, sabida ko bata yi kwalliya ba sai ta ɗiga shi, sai ta ɗauki gyale ta yafa a gefen kafaɗanta tare da zura shegun takalman ta da ba ta rabo da su, masu shegen tsini

Momy sai dariya take mata, sabida ganin yanda take turguɗe wa, tace, "wai baza ki haƙura da takalman nan ba sai sun ka dake ƙasa?"

"Momy ai na saba saka wa, baza suyi min komai ba."

"Yanzu ba ga shi kina ƙoƙarin faɗi ba? Kaii! Anya baza ki je ki canza su ba?" Ta ƙara maganar ganin Maryamun ta kusa zube wa ƙasa, sai ta dafa Momyn tana dariya

"Momy bani da wani fa, kuma wlh na fi jin daɗin su, ko a ƙauyen mu da su nake tafiya duk inda zan je."

Murmushi Momy tayi tace, "to mu je, amma in mun je dole zan siya miki flat shoes ki haɗa, waɗannan sun yi miki tsawo, sai a siya miki ƴan madaidaita."

"To Momy." Maryamu ta amsa mata cikin farin ciki da zumuɗin ta


Haka suka fita driver ya tafi da su Market.
[24/01, 8:09 am] OumƊahirah نفيسة: 🌱🌱🌱🌱🌱

      *SHAREEF*
          _SexyBoy_
🌱🌱🌱🌱🌱


_Writer: Nafisat Isma'il Lawal_
_Wattpad: UmmuDahirah_

*SARAUNIYAR TSOKANAR PERFECT🧝*



*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞

```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)```

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

       *P.W.A✍️*




*NASIHA*
Idan kana fama da damuwa mai tsanani ko wata rashin lafiya da aka kasa gane kanta ko wata bukata da kake so Allah ya amsa maka ita cikin gaggawa, toh ka yawaita abu ukun nan:
1. Sallar dare (ko da raka'a biyu ce)
2. Sadaka
3. Kyautatawa iyaye.










__________
*BOOK1*
_______________*FREE PAGE14*
          Lokacin da SHAREEF ya isa Company, har an taru shi kaɗai ake jira

PA din sa yana bakin hall ɗin yana ta faman duba agogon sa, ga shi SHAREEF ɗin ya ƙi ɗaukar waya bare ya san me ke faruwa har yanzu bai iso ba?
Sai ganin Motan sa yayi ya faka, da sauri ya isa wurin sa yana buɗe masa ƙofan Motan, tare da amsar Jakar hannunsa yana gaishe shi lokaci guda

Bai amsa mishi ba sai da ya fito a natse, tare da kallonsa a fizge ya amsa mishi a takaice cikin isa da taƙama irin nasa, wanda in har ka sanshi a waje baza ka taɓa cewa wancan SHAREEF ɗin bane na gida, kwata-kwata ba shi da fara'a a waje, kuma ba shi da mutunci bare ganin ƙimar mutane

"Sir, kowa ya hallara kai kaɗai ake jira."

Bai yi magana ba, ya soma taka wa zuwa bakin hall ɗin cikin natsuwarsa tamkar ba jiransa ake yi ba, don yanda yake takawan kamar bazai tafi ba

PA na biye dashi a baya sai duba agogo yake yi,
Da sauri yayi gaba yana buɗe masa ƙofan hall ɗin

Shi kuma ya shige ciki yana ƙara gyara daidaituwar rigan sa

Hall ɗin cike yake da manyan mutane a ƙalla zasu kai su ashirin a ciki, gaba ɗaya in ka kalle su manyan mutane ne masu ji da kansu da kuma kuɗin su, duk babu sa'an SHAREEF don gaba ɗaya sun girme shi,
Har da wasu tura wa su uku waɗanda su ne suka bada kwangilar aikin da za a yi musu, na gina katafaren Company a Abuja, tare da haɗakar da zasu samu da companonin su SHAREEF domin samun biyan buƙatar su, shiyasa dole sai an sanya hannun jari da companoni manya-manya don a samu yiwuwar aikin,
Yanzu haka Companin SHAREEF yana ɗaya daga cikin manyan company a nan Kano, shiyasa suke buƙatar amincewar sa domin ya shiga cikin aikin gadan-gadan, tunda zasu samu abun da suke so ba kaɗan ba,
Sai kuma aka samu rashin Sa'a wanda Abokan hamayya suka shiga cikin zancen a kan dole sai an saka Companin su,
Wato Alhaji Inuwa da kuma Honourable Ja'e Ali,
Su ne suka kawo tsaiko a kan harkan, har aka yi kwana biyu ana yin meeting don tsayar da shiyan kowanne a cikin companin

SHAREEF ya ƙi yarda da tayin da suke so a basu, shiyasa yau Turawan suka buƙaci zama a yi taron da su don ganin an samu matsaya,
Tunda idan maganar ta ci gaba da tsawo zasu yi asara babba

Yanzu shigowar SHAREEF shiyasa hall ɗin ta dena hayaniya, wanda duk faman hayaniyar nan ana yi ne a kan SHAREEF ɗin da ya shanya su bai zo ba, har ya ƙara musu mintina 15 a kan lokacin da suka ɗiba,
Suna ganin kamar har da wulaƙanci shiyasa ya ajiye su ya ƙi zuwa a yi magana a gama

"I'm sorry. I was late and did not arrive early." Yayi maganar yana ɗaga musu yatsa ɗaya batare da ya kalli kowa daga cikin su ba, ya samu wuri a inda aka tanadar mishi ya zauna

"Ok, tunda kowa ya hallara kamar yanda ake buƙata, ya kamata a fara gudanar da abun da ya tara mu." Cewar Sharaihu Managern SHAREEF ɗin

Mr. Pitter shi ya soma magana da cewan, "now we should stop at one point, we are listening today and you should make your decision, if the work is possible then tell us because time is running out for us, the reason why we gave you this work is because we know that we will not get it wrong. but you still failed to give us a single solid answer." Ya ƙare maganar yana bin su da kallo

Honourable Ja'e ya yi gyaran murya tare da cewan, "mu bamu da matsala fa, hukunci yana ga SHAREEF idan har ya amince, kowannen mu zai ɗauki kaso ɗaya bisa uku, shi ne tsarin mu. For this work is not his alone."

"Gaskiya ne. Domin shi yake ja mana lokaci, wannan aikin ba companin ka kaɗai suka iya ba, and mu ma dole zamu ɗauki kaso ɗaya bisa uku kowa ya ƙaru, abun da yasa ake ta jayayya domin ku saka naku hannun jarin, don su suna ganin kamar idan sun saka Companin ka a ciki zasu fi ɗaukaka ne, wanda kowa ya san ba haka bane a nan, amma sun dage, kai kuma ka mayar da mu ƙananan mutane kana so ka nuna mana kamar ka fi mu wayon, don haka raba-dai-dai za a yi don shi ne kawai adalci." Cewar Alhaji Inuwa da ya fi kowa jin haushin SHAREEF; kasancewar sa ƙaramin su amma yana taka su son rai

Da yawan mutanen wurin suke ta faɗan, "gaskiya ne wannan, babu shakka."

SHAREEF da ke mirza yatsun sa cikin yanayin ko-in-kula da su, tamkar ma maganar bai dame shi ba tunda babu wanda yake kallo a cikin su, but a cikin ransa maganar nasu ya sosa shi matuƙa har ransa ya ɓaci, amma ya ƙi yayi magana bare su ji ra'ayin sa

Sharaihu yace, "Ni ina ga, ku bi abun nan a hankali komai zai zo ƙarshe, tunda ga su Mr. Pitter a wurin, su zasu yanke hukunci kai tsaye, su zasu san wa zasu ba wa babban shiya."

Mr. Pitter yace, "We have finished speaking, right from the beginning we needed SHAREEF Company, so what he said we will do, we have no choice."

Wani killer smile SHAREEF ya saki, yayinda ya ɗago kyawawan idanunsa ya zuba a kansu, a natse cikin sanyin muryansa tamkar babu abun da ke damun sa yace, "idan na yanke hukunci ba na canza wa, ba wai na dage dole sai an bama Companin mu aikin nan bane, and ban ce dole sai mun saka hannun jari ba, amma su da kansu suka zaɓi namu Companin, don haka a cikin ku babu wanda zai zo yayi mana iko a nan a kan alfarma da kuke biɗa." Ya ƙare maganar yana nuna su Alhaji Inuwa da yatsa, idanunsa har sun soma sauya kala alamun ya soma ƙule wa. "idan baza ku yi aikin bisa tsarin da nake so ba, so sai dai mu cire hannun mu a cikin tsarin nan. I'm done talking, we will take two out of three, anyone who doesn't do it for him, it's not said that he has to do it." Sai ya mayar da idanunsa a kan su Mr. Pitter yace, "If you don't agree, as long as we leave this work, I don't care."

"No, mun yarda, dama aikin ka muke bukata ai." Cewar Mr. Pitter, before kuma ya juya ga ƴan uwan nasa ya soma musu ƙus-ƙus kasancewar su ba sa jin Hausa sosai, kuma tun maganar ma basu furta komai ba

Yayinda su Alhaji Inuwa ransu yayi baƙi sabida baƙin cikin abun da SHAREEF yake son yin musu, su ma sai ƙus-ƙus suke yi suna musayar yawu a tsakanin su

Sai ɗaya Baturen ya ɗago yayi magana a kan, "sun amince, zasu yi aiki da Companin SHAREEF, duk wanda bai amince ba basu gayyace shi ba, amma su ɗaukakar Companin su suke buƙata tunda kasuwanci suke yi, don haka duk wanda zai bi bayan shi suyi aiki tare basu da case da wannan, amma hannun jari gaba ɗaya sun sayar mishi ne, inyaso ya basu wani kaso daga ciki basu da damuwa. Sun tsayar da magana in a three weeks za a fara aiki."

Jin hakan sai SHAREEF ya cije laɓɓansa yana murmushi. Bai ƙara furta komai ba har aka rufe taron kowa ya soma tashi zai wuce

While su Alhaji Inuwa suna zaune sun ƙi tafiya. Suna ganin SHAREEF zai mike sai suka buƙaci magana da shi

Bai ce komai ba ya koma ya zauna a inda ya tashi

Mutane na fice wa, Alhaji Inuwa cikin zafi yace, "Kai SHAREEF yanzu har rashin mutuncin naka ya kai ka wulaƙanta mu a kan wannan kasuwancin da ka san komai ga yanda ake yi? Ko Mahaifin ka ne ya zo nan da kanshi bazai yi mana haka ya kasa amsar tayin mu ba bare kai, and mai kake taƙama dashi kuma nawa kake bukata a wurin mu; mu baka domin ka bamu hannun jarin mu ma? Ba aiki kaɗai muke bukata ba mu ma muna son saka hannun jarin mu a ciki."

"Exactly, don haka ka faɗa mana ko me kake so zamu baka, wannan aikin bazai yiwu a ce muna kallo ka ci kai kaɗai ba, tamkar ɗaukakar ka ne kai kaɗai idan har mun yi aikin nan babu hannun jarin mu, don haka dole mu ma ka bamu kason mu."

Miƙe wa SHAREEF yayi yana bin su da kallon ƙasƙanci, ransa a ɓace yace, "bazan bayar ba, ba Dadyna bane a nan a gaban ku; Ni ne SHAREEF. SHAREEF Ahmad, idan aikin bai yi muku ba kuna da damar ajiye wa tunda mu zamu iya, and babu wanda ya isa yace zai nuna min fin ƙarfi a nan since nima ina da wayon ɗina." Sai ya buga table ɗin cikin huci ya ƙara da cewa, "waye bai son ci gaba? Kuna ɗauka na ban san me nake yi ba? Ku canza tunani."
Ya wuce ba tare da ya sake bi ta kansu ba ya fita daga wurin

Su kuma suka bi bayansa da kallo ransu a ɓace. Alhaji Inuwa da ya fi daukar zafi ya soma faɗin, "wlh sai na koya ma wannan Yaron hankali, bai isa ya ci bulus haka ya tafi ba, aikin da muke jira tsawon lokaci amma a ce shi za a danƙa ma wa? Wlh karya ne sai inda ƙarfi na ya ƙare."

Honourable Ja'e da shima yake cike da ɓacin ran, sai yace, "ka ga mu je, mu bar nan don ba a nan ya kamata mu yi magana ba, ko ma me ke akwai zamu san ya zamu yi, ai ƙwace goruba a hannun kuturu ba abu bane mai wahala, mu je kawai zai san da wa yake yi, mu ne garin fa."
Ya ja hannunsa suka nufi ƙofa suka fice suna baza riguna.
***


              Kai tsaye shi kuma SHAREEF office ɗin sa ya wuce, da Shuraihu da PA suna ciki suna jiran sa,
Shigowar sa sai ya nufi kan kujerar sa kai tsaye yana zama; fuskarsa a matuƙar haɗe babu ko ɗigon walwala a tare da shi

PA ya kasa yin magana don ya san halin sa tunda ya ga ya shiga wannan yanayin, da alamun ran ɗan Maza ya ɓaci, ya lafiyar Kura ma bare tayi hauka?

Shuraihu ne ya soma magana yana cewa, "SHAREEF bai kamata a ce kana nuna ɓacin ranka a kan waɗannan ƙananan alhakin ba, already aikin nan dai mu zamu yi, don haka mu fuskanci abun da ke gaban mu zai fi mana." Sai ya ɗago computern sa da ke hannunsa yana cewa, "Ni yanzu na riga da na fitar da sumfurin building na komai, sai a duba a gani in akwai wata shawara."
Sai ya ajiye computern a gaban SHAREEF yana matso mishi dashi yanda zai gani

Kallo ɗaya SHAREEF ya yi wa fuskar computern yana ɗauke idanunsa; da suka rage haske saboda halin da yake ciki, har yanzu a hassale yake da ɓacin ran su Honourable Ja'e, shiyasa cike da taƙama irin nasa, and kuma cikin sanyin muryansa wacce ko a ɓacin rai yake ba ta sauya wa, sai ma dai ta ƙara sanyi sabida isa da izza ta yanda yake sarrafa ta kamar bazai yi ba, a yatsine yace, "ba na buƙatar wannan zanen, already mun yi magana da Hanif shi zai fitar, abun da nake so da ku." Sai ya ɗago kai ya tsira wa Sharaihun ido yana ƙara wa da faɗin, "kai da Mahmud da PA zaku fara zuwa ku ɗauko mana hotunan wurin gobe, da komai na tsarin wurin." Sai ya janye idanunsa tare da matsar da computern Sharaihun yana ɗaura nasa a wurin, tare da soma daddanna wa ba tare da ya sake ce musu komai ba

While Shuraihu duk yanda ya so ya ɓoye abun da ke ransa ya kasa, ransa suya yake yi da jin hukuncin da SHAREEF ya yanke, wanda har hakan ya bayyana a kan fuskarsa batare da ya sani ba, sai ya kasa haƙura yace, "but sir, na ga Ni nake yin zane idan irin hakan ta kasance, and kuma already na rigada na fitar da zanen tunda sun bamu jadawalin wurin, wannan babban aiki ne fa, idan muka ce zamu fara amfani da sabon zane a hannun wanda bai taɓa yi ba akwai matsala..."

"To and so what? Hanif zai yi wannan zanen ba na son gardama." Yayi maganar bai ɗago da kansa ba yana ci gaba da danne-dannen shi

Shi kuma Sharaihu sai ya haɗiye yawun takaici yana ƙoƙarin danne baƙin cikin sa daga fuskarsa, musamman yanda ya ga PA yana kallonsa

Wanda shi PA ya san dama za a rina, don ba a yi wa SHAREEF gwanin ta, shi dama haushin Sharaihu yake ji yanda yake kane-kane a companin don an ba shi dama, amma ga shi lokaci guda abun mamaki SHAREEF yana son daƙile shi a kan wasu harkokin

"Wannan shi ne sumfurin zanen da Hanif ya tura min, zan tura maka ta e-mail sai ku je dashi ku duba, and ga wanda Mr. Pitter ya tura min." Sai ya ɗan yi shiru yana jan numfashi kaɗan, tare da furta, "make sure today you all check and send me again."

Dukkan su suka amsa mishi, while Shuraihu yana dauke nasa computern tare da duba zanen da SHAREEF ya tura mishi, sai ya miƙe tsaye yana mishi sallama ya fice

"Ka je ka tattaro min files ɗin nan na sabbin ma'aikata, ka kai ma Mahmud ya duba a tantance waɗanda za a ɗauka, kar su gaza mutane biyar."

"Ok sir." Cewar PA cike da girmamawa yana tashi, sannan ya fice daga office din

Shi kuma SHAREEF sai ya ci gaba da latsa computern sa bai sake ɗago kai ba. Like a ten minutes ya ɗauki wayansa yana latsa wa, jima wa kaɗan ya kara a kunnen sa tare da manna wayan da wuyan sa still yana duba computern

Daga can Hanif ya amsa call ɗin yana cewa, "Bro how fer?"

"Fine. And you?"

"Alhamdulillah komai normal."

"Ok, mun gama magana a kan aikin nan nasu Mr. Pitter, zan tura maka iya girman wajen, but zuwa gobe za a sake zuwa a ɗauka gaba ɗaya zan tura maka, sai ka duba Please Do everything for us in one week, everything will be ready."

"Wow! Masha Allah. Did you say that everything is finished? They agreed to give you the shares?"

"Yeah, sai dai waɗannan ƙananun mutanen suna son kawo min cikas, and babu wanda zan raga mishi ciki wlh muddin suka ce zasu taɓa Ni."

Murmushi Hanif yayi tare da cewa, "wooh! Na Haseena, ba da kanka a sare ka je gida ka ce ya faɗi, calm down mana, me zai sa ranka ya ɓaci a kan su?"

Murmushi SHAREEF yayi yana cije laɓɓansa, sai ya ɗan ja numfashi tare da rufe computern, at the time yana ba shi amsa da cewan, "har ka sa zuciyata tayi sanyi, but raina a sama yake tunda muka fito meeting ɗin nan." Sai ya ɗan ja guntun tsaki tare da cewa, "bari in wuce gida, zamu yi waya idan na koma, ina jin yunwa sosai." Ya ƙare maganar yana langaɓe kai kamar zai yi kuka

Hanif da ke murmusawan shima yace, "Ok bro, bari in bar ka nima ina son shiga school now. And stop worrying about these people, since everything is in our hands. Congratulations, fatan nasaran aiki."

SHAREEF smiled and said, "Thank you my brother."

Daga nan suka yi sallama ya katse wayan yana tashi tsaye. Jakarsa ya ɗauka bayan ya mayar da wasu files a ciki, sannan ya nufi ƙofa ya fice yana zura wayansa a cikin aljihun wandon sa. Babu PA a office nasa, shiyasa ya fice kawai yana nufan lifter ya shiga ya saukar dashi ƙasa

Duk inda ya wuce ma'aikata ke gaishe shi, amma ko ci kanku bai ce musu ba. Idan ma da sabo sun saba, ba ya amsa gaisuwar su sai ya ga dama, ko zai amsa sai dai ya ɗaga musu hannu, sosai girman kanshi ya yi yawa da ganin mutane a ƙasƙance, ba ya damuwa da damuwar mutane sai nashi, ba ruwan shi da shiga harkan mutane bare ya san matsalar su, in dai sun yi mishi ba dai-dai bane ko kuma sun shiga gonan shi, yanzu za ka ji ruwan bala'i da masifa, kuma daga ƙarshe ya yi maka koran wulaƙanci; don ba ya iya ba wa mutum dama ta biyu

Motansa ya hau ya figa zuwa gida, a ɗan ƙanƙanin lokaci ya isa gida ya dinga danna horn kamar zai tashi sama

Da sauri mai gadi ya wangale mishi gate ɗin

Please Login or Register in order to submit comment