Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ya miƙe yana nufan ƙaramin falon nasa

Lokacin Maryamu tana tsaye ta kasa shigowa ciki sosai saboda ganin babu kowa, kuma ta ƙi magana sai kallon tsarin falon take yi tana buɗe ƙofofin hancin ta tare da shaƙar ƙamshin SHAREEF da ke ratsa mata har cikin ƙwanya, wani irin daɗi na ratsa ta, har wani lumshe idanu take yi tsaban farin ciki

"Kee."

Muryan SHAREEF ɗin ne ya dawo da ita hayyacinta, firgigit ta dawo da kallonta gare shi, yanda ya tsare ta da kallo babu kaya a jikinsa, da sauri ta kawar da kanta sabida wani irin yanayi da ya riske ta, wani yawu ne mai ƙauri ta haɗiye yayinda ta kasa furta ko kalma ɗaya

"Me ya kawo ki nan? Kin tsaya kamar wata munafuka; ban miki gargaɗin shigo min ɗaki ba? I don't like to see this black face. get out."
Ya daka mata tsawa muryansa alamun a ɓace

Hakan ne yasa ta ɗago manyan idanunta ta zuba mishi, maimakon ta fita kamar yanda yace, sai kawai ta saki wani murmushi wanda sai da dimples ɗin ta suka fito sosai, ya ƙayata kyakkyawar fuskarta, ba komai ne yasa ta yin murmushin ba, sai tuna kamar ba shi ne jiya ya zo wurin ta da buƙatar sa ba, amma yanzu kuma yana ɗaure mata fuska, hakan ne ya bata dariya har ta murmusa tana sake bin jikinsa da kallo kamar zata haɗiye shi

Hakan ne ya fusata SHAREEF, tare da mamakin ganin yanda ta kifa masa manyan idanun nan nata kamar wata mayya kuma tana masa dariya, takowa yayi ya nufo inda take,
Kafin ya ƙariso har ta ruga zata fice cikin ɗakin, amma sai yayi caraf ya cafke ta yana mayar da ƙofan ya rufe, "ke kina da hankali da za ki shigo har ɗaki na kina min dariya? Mene kika gani a jikina da ya ba ki dariyan? Oya tell me ko in kakkarya ki."

"Wlh babu komai Yaya SHAREEF, ba da kai nake yi ba, wani abu na tuna."
Ta furta tana runtse idanunta ganin tayi kusa dashi wadda yasa ta kasa kallonsa

Tura ta yayi yana yatsina fuska, tare da furta, "shashshan banza, fitan min a daki ko in ci ubanki, idan kika sake gigin shigo min ɗaki a karo na uku, sai na canza wa mumun fuskar nan taki kamanni, Oya tashi ki fita mana."

Tashi tayi tana fice wa da sauri kamar ana hankaɗa ta, sai da ta fita sannan ta sauke ajiyar zuciyar tsoro, dantsen hannunta ta kama tana shafa wa, dai-dai wurin da ya kama mata, yayinda take jin wani sanyi da farin ciki a zuciyarta, komai nasa abun kyau ne, kwata-kwata ba ta jin haushin abun da yake mata, a fili ta furta, "ina sonka wlh, koda yanka Ni kake yi haka nan zan jure, domin in rayu da kai, kai kaɗai ne farin cikina a yanzu, Allah zan iya bada raina sabida kai."
Sai ga tagwayen hawaye sun fito daga idanunta sun sauka a saman kuncin ta,
Jin motsi kamar ana taho wa, shiyasa tayi saurin share hawayen; ta nufi hanyar downstairs da saurin ta; tana kaɗa kanta.
[13/02, 10:12 am] OumƊahirah نفيسة: 🌱🌱🌱🌱🌱

      *SHAREEF*
          _SexyBoy_
🌱🌱🌱🌱🌱


_Writer: Nafisat Isma'il Lawal_
_Wattpad: UmmuDahirah_

*SARAUNIYAR TSOKANAR PERFECT🧝*



*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞

```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)```

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

       *P.W.A✍️*





*DATA SHARE*

Call, message or whatsap 07065334256

*MTN*
500MB 150
1gb 280
2gb. 560
3gb. 840
4gb. 1120
5gb 1400
6gb. 1700
Verlid for 30 days.












__________
*BOOK1*
_______________*FREE PAGE30*
_____Yau ma bayan an tashi daga school, Feena tace ma Maryamu, "ta zo su ajiye ta a hanya."

Sai tace, "a'a baza ta bi su ba, ta san za a zo ɗaukar ta."

Duk yanda Feena ta so ta biyo su but ta ƙi, sai da ta wuce ta shiga Motan, Hunaip ya tambaye ta; take sanar mishi yanda suka yi

Shi da kansa ya sauka ya ƙarisa wurin ta, ya tsaya yana kallonta fuskarsa ɗauke da murmushi yace, "haba friend, ya za a yi mu tafi mu bar ki a nan bayan ba a zo ɗaukar ki ba? Ki zo mu sauke ki tunda mu ba baƙi bane a wurin ki."

Ɗago kai tayi ta ɗan kalle sa kaɗan tana dauke idanunta a kansa, sai ta haɗe fuska da cewa, "gaskiya bazan bi ku ba tunda jiya an min faɗa, ku tafi kawai za a zo ɗauka ta, Momy sai da tayi min gargaɗi za a aiko driver."

Murmushi yayi jin zancen nata, yana ɗan shafa gemun sa a yanzu yake kallonta cike da burge wa, komai nata mai kyau ne har yanda take maganar tana yatsina fuska alamun tsiwa a tattare da ita, tsab ya ƙare wa halittar ta kallo yana jin a ransa gaskiya ya samu Mata, yarinyar tayi masa duk da ƙarama ce sosai, amma har a ransa ta kwanta masa, shiyasa ya ɗan ƙara kwantar da murya tare da furta, "don Allah kar ki yi min katanga ga hana Ni taimakon tsaleliyar budurwa kamar ki, haba taya ma zan bar ki a nan wurin in tafi? Please ki taimaka ki biyo mu tunda har yanzu drivern bai ƙariso ba, Ni zan shiga da kaina in yi wa Momyn bayani tunda na san bata fahimci motan da kika hau bane."

Yanda yake mata maganar raɗa-raɗa cikin kwantar da murya, da kuma jin abun da yace, shiyasa ta sake kallonsa kaɗan tana dauke idonta, ba wai don ta yarda da maganar nasa bane, sai don ganin girmansa da tayi, kuma ga shi sai wani lallaɓa ta yake yi da wasu kalaman da ta kasa gane musu, baza ta iya masa musu ba tunda babban Mutum ne, shiyasa ta gyaɗa kanta alamun ta amince

"Yauwa ko ke fa, har na ji sanyi a raina, mu je in bude miki ƙofan."
Ya nuna mata hanya alamun ta wuce

Babu musu tayi gaba duk da har ranta tana mamakin yanda yake nuna mata a yanzun ɗin, musamman yanda ya saki jikinsa har yana mata murmushi, bata dai kawo komai a ranta ba ta shiga Motan bayan ya buɗe mata

Ita kuwa Feena daɗi ne sosai ya ratsa ta ganin yanda Babban Yayan nasu yake yi wa Maryamu, da alamu ta soma gane Hunaip yana son Maryamun ne, kuma hakan yayi mata dad'i, don tayi mamakin ma yau da yace mata, "ta jira sa zai zo daukar ta." Ashe da biyu ne, ta riga da ta harbo jirgin, sai ta ji farin ciki da wannan haɗin, duk da basu daɗe da Maryamu ba amma ta shiga ranta since tana da kyawun da kowace zata so ƙulla alaƙa da ita

Tunda suka shiga Motan Maryamu bata ce uffan ba, yau ma tana zaune a gidan baya tana jin shi yana yi wa Feena magana tana basa amsa, daga ƙarshe ne ya sanyo ta a cikin zancen nasu yana cewa, "meyasa ba ta son yin magana kamar kurma?"
Murmushi kawai tayi bata ce uffan ba still, a ranta tana jinjina yanda yake faɗin, "wai daga ganin ta shiru-shiru ce babu ruwan ta, kuma alamu ya nuna bata da hayaniya, don haka zai ja kunnen Feena kar ta riƙa jan ta da surutu a class don ya san halin ta."
Taɓe baki kawai tayi tana mayar da hankalin ta a kan hanya, ita tunanin SHAREEF ma ya fiye mata jin hiran nasu, tana can ta faɗa duniyar soyayya da tunanin farin cikin nata, har ba ta sanin sanda take zuba murmushi ita kaɗai abun ta; tsaban tunanin yana jefa ta cikin nishaɗi

Kamar yanda Hunaip yace zasu shigo ciki ne, shiyasa yana yin packing ɗin motan, yace wa Feena, "ta fito su shiga ciki su gaisa da su Momy."

Tare suka shiga, suna gaba yana bin su a baya sai kallon Maryamu yake yi ko ɗauke ido ba ya yi a kanta, fuskarsa ɗauke da murmushi, har ransa yana jin yanzu ya samu Matar aure, duk da kusan shekaru biyar kenan da mutuwar Matarsa bai taɓa saka wata Mace a rai da sunan yana sonta ba, sai Maryamu, lokaci guda ta shiga ransa kuma tayi dai-dai da zaɓin zuciyarsa, don haka ba ya tunanin zai yi sanya a wannan karon, kafin ya koma bakin aikin sa zai sanar da Abbansa a zo a nema masa iznin neman ta, a jiya bai samu ya runtsa ba saboda tunanin Maryamu, duk da yana ganin yarinyar ƙarama ce sa'ar Autar su Feena, amma zai iya jira koyaushe ne in har za a ba shi...
Ɗan numfashi ya ja yana fitar da hucin bakin sa, tare da bin bayansu zuwa cikin Falon kasancewar har sun shige su

Momy suka samu a falon, don itama zaman ta kenan; ta shiga kaiwa SHAREEF kunun gyaɗa da ta gama dama mishi,
Ganin fuskokin su Hunaip ya sanya ta faɗaɗa fara'an ta tare da furta, "kai! Yanzu su wa nake gani haka kamar Hunaip da Nafisa? A gida na?"

Dukkan su dariya suka yi

"Ku ƙariso ku zauna, lale marhabun, ah! Lallai yau muna da manyan baƙi, barkan ku da zuwa."

Bayan sun zauna ne Hunaip ya soma gaishe ta yana murmushi

Ta amsa cikin kula wa tana cewa, "Hunaip ashe kana gari? Saukar yaushe?"

"Shekaran jiya Momy."

"Ikon Allah! to ya aikin fatan komai lafiya?"

"Alhamdulillah Momy, komai lafiya wlh."

"Momy ina wuni?" Feena itama ta gaishe ta

Sai ta harare ta tana cewa, "No, ke bazan amsa gaisuwar ki ba, tunda ga baki ga hanci amma ba ki san ki zo gidana ba, i know ma yanzu haka Hunaip yace zai zo kika biyo sa."

Duk dariya suka yi, har Maryamu da ke zaune gefen Feena itama tana jin su

While Feenan tace, "Laa wlh Momy a'a, ina son zuwa school ne ya ɓoye Ni, amma yanzu zan riƙa zuwa."

"Wai ko dama motan ku Maryam ta hau jiya take faɗa min Yayan class mate din ta ne?"

Hunaip da ke murmusawa yace, "gaskiya ne, yanzu ma tace baza ta hau bane shiyasa nace zan shigo in yi miki bayani, that's the reason da ta hau."

"Allah Sarki! To tashi mana ki dauko musu drinks su sha Maryam, ki shiga Kitchen ki duba freezer za ki ga cakes a ciki ki zubo musu."

"Momy Allah da kin bar shi, zamu wuce ne yanzu, but Dady ba ya nan ne?" Cewar Hunaip yana ɗan kallonta

Tace, "eh ba ya nan, tun safe ya fita a kan wasu kaya na Company da suka samu matsala, ina tunanin ma maybe sai gobe zai dawo, amma duk da haka baza ku wuce ba sai kun taɓa wani abu. Bari ta kawo muku."

"Ina SHAREEF yana nan kuwa?" Ya sauya maganar da furta hakan, tunda ya san ko yace zasu tafi, baza ta bar su ba sai sun sha drinks din

A nan ta faɗa mishi, "yana ciki a kwance ba lafiya ai, but jikin da sauƙi dai."

"Subhanallah.. amma bamu ji labari ba? Ko Abba bai da labari ina tunanin?"

"Eh, ai dayake jiya ne jikin nasa ya tashi, kuma da sauki gaskiya."

"To Allah ya ƙara lafiya, bari mu duba sa Momy kafin nan."

"To." Tace tana tashi tare da sake furta, "mu je sai in raka ku."

Wuce wa suka yi saman har Feena

Time ɗin Maryamu ta gama ajiye musu komai a saman Centre table, shiyasa ta wuce dakin ta don ta sauya kaya tunda ta san ɗakin SHAREEF suka tafi

Su kuma bayan sun shiga, Momy ta shiga har bedroom ta taso shi, har tana mishi faɗan, "ta ajiye masa Kunun ashe bai taso ya sha ba? Da bata sake shigowa ba haka zai bar shi ya ƙandare."

Sai murmushi su Hunaip suke musu,
Bayan Feena ta gaishe shi da jiki, sai suka fita da Momy suka bar su

Hunaip ya sake mishi ya jiki yana cewa, "ashe an taɓa file ne Kanina?"

Smile SHAREEF yayi yana cewa, "wlh kuwa Yaya Hunaip, amma jiki Alhamdulillah baka ga yanda na koma ba? har ƴar ƙiba nayi."

"Exactly na ga alama ai, haka ake so shiyasa na ga har tara ƙwanji kayi."

Tare suka yi dariya gaba ɗaya

"Ina Hanif da Sadiq ban gansu ba?"

"Hanif yana England, shi kuma Sadiq i think bai dawo school ba shima."

"Oh! Har yanzu Hanif bai gama karatun nan ba ashe?"

"Wlh kuwa, ya bar min aiki Ni kaɗai ina ta fama, amma ya kusa gama wa just few months ai."

"Ok Allah ya taimaka, Ni bari in zo in wuce. Sai mun yi waya duk da ba son zumuncin kake yi ba, ɗan gwara Hanif da kai; kwanakin baya ina ganin kiran sa, amma kai kuwa."
Sai ya ɗan girgiza kansa yana miƙe wa

Shi kuma SHAREEF murmushi yayi yace, "sorry Babban Yaya, na san nayi laifi amma zan gyara."

Ɗan ɗage kafaɗa yayi yana cewa, "da dai ban san hali bane, get well soon Ƙanina, sai kuma na sake kewayo wa before na tafi."

"Ok thanks."

Hannu ya basa sannan ya fice ya koma Falon,
Suna zaune gaba dayansu har Feena ta soma taɓa abun da aka kawo musu,
Sai yace, "Mom zamu wuce mun gaishe ku."

"A'a, ba fa zaka tafi ba sai ka taɓa wani abun, tunda na sa aka kawo sai kun ci."

"Mom Allah ina sauri akwai inda zan je, amma bari in sha ruwa."

"Hmm shikenan tunda baka yi ninya ba, ku gaishe da Maman taku, insha Allahu nima zan leƙo kwanan nan tunda na jima ban zo ba, yaushe zaka koma Abujan? Ko an ɗiba mana hutun da yawa za a riƙa leƙo mu?" Ta furta tana ƴar dariya

"Uhm Momy wannan ma hutun da ya ya na samu? One week ne kawai sannan zan wuce, amma zan sake zuwa insha Allah tunda bamu haɗu da Dady ba."

Daga nan dai sallama suka yi suka fita, Maryamu har bakin farandan gidan ta raka su suka sake sallama da Feena

Shi kuma Hunaip tuni ya wuce wurin Motan yana waya, duk da sai da ya juya ya sake kallon Maryamun har ta shige, sannan shima ya shiga Motan yana jiran Feena

Motan su na fita gidan wata motan ta shigo, Babbar Mace ce a cikin Motan, Yayar Momy ce duk da ba Uwa ɗaya suke da ita ba, Uba suka haɗa, Hajiya Salma kenan

Maryamu ce kadai a falon tana cin abinci, while Momy kuma ta wuce ɗakin ta,
Shi yasa da Hajiya Salman ta shigo tana doka sallama, Maryamu ta amsa mata tana kallonta

Haka itama Hajiya Salma kallonta take yi tana ɗan yatsina fuskarta, sai tace, "ba ki iya gaisuwa bane kin kafe Ni da ido? Haka ake yi?"

Kawar da kai Maryamun tayi ta ƙi cewa komai, sai ma ci gaba da cin abincinta tayi

Hakan ya fusata ta tace, "Kee, ba da ke nake yi ba?"

"Ai ban san dani kike yi ba." Maryamu tayi maganar tana tura baki, sai da ta yatsina fuska kafin tace, "ina wuni?"

"Au iyee? Lallai ne ma, wato Khadija fitsararriya ta ajiye a gidan ta?" Ƙwafa tayi tana sake kallonta tace, "ina Matar gidan take?"

"Tana ciki." Ta bata amsa batare da ta sake ɗago kanta ba

"Lallai yarinya, tabbas kafin in bar gidan nan ina tunanin zan yi maganin rashin kunyar ki, don daga gani fitsararriya ce ke ko a ƙauyen naku, ai wannan masifa aka ajiye wa Khadija a gida, amma ki kuka da kanki."
Ta buga mata yatsun ta alamun warning tana wuce wa saman benen

Yayinda Maryamu ta raka ta da kallo tana ƙunƙunai har da jan guntun tsakin ta, "wai zata yi magani na, mai magani na sai ya shirya, don kin zo a lokacin da nayi sanyi ne amma ba na ɗaukar raini wlh, ga ki nan fitsararriya mai ruwan ƴan duniya, tana yi tana wani baza ɗuwawu kamar faranti wai ga ta ƴar fi'ili, to Ni digree ne dani a fi'ilin, tun daga Nahawu na farko har na ƙarshe sai da na sauke ."
Ta sake jan dogon tsakin cike da haushin Matar saboda kallo ɗaya har ranta ta ji Matar bata yi mata ba, ko meye ruwanta da ita da zata ce dole sai ta gaishe ta?

Ita kuma Hajiya Salma ɗakin Momy ta shiga, ta same ta ta fito daga toilet

Da fara'a Momy ta tarbe ta sabida bata yi expecting ganin ta ba, ta bata wuri suka zauna ta fara gaishe ta tana cewa, "ina son zuwa gidan ma tunda na ji wayanki ta mutu kwana biyu ba na samu, ashe ke ma kina hanya?"

Taɓe baki tayi tace, "eh ina hanya, nan maƙotan ku na zo shiyasa na ce bari in ƙariso nan mu gaisa, Hajiya ma ta faɗa min SHAREEF ba lafiya dalilin shigowa ta kenan."

"Wai har sun sani? Sai da na cewa Aunty Najwa kar ta sanar musu, don na san zasu ce zasu gaishe shi, jikin da sauki wlh."

"To ai sai in faɗa musu, don nima daga nan gidan zan yi, ba zama ya kawo Ni ba, gobe za a kawo kaya shiyasa nace bari in zo mu ƙarisa maganar tunda ban san da me- da me za ki siya ba? Wayata ta samu matsala ce shiyasa ma ba ki ji Ni ba."

Momy tace, "kayan ai ba nawa bane, na Maryam ne, dama nayi mata siyayya ne kuma kinga yakamata a zaɓa mata har da su atamfofi, shiyasa nace bari in miki magana, ki zaɓa mata kala biyar masu kyau ƴan 10k, sai materials da less su ma guda biyar biyar ɗin, waɗanda dai zasu yi wa bak'ar Mace kyau, ko kuma bari in kira miki yarinyar sai ki ganta don ba na son a samu matsala, ki haɗa kuɗin da lissafin mayafan da na ɗauka kwanakin baya."

"Wai kina nufin waɗannan kayan duk yarinyar nan za ki siyan ma wa? Ai na ganta ba sai kin kira ta ba, yarinyar da ta nemi min rashin kunya idanu a tsatstsaye ko gaisuwa babu?"

Da mamaki Momy tace, "rashin kunya kuma Aunty Salma? Ita Maryam ɗin?"

"Eh ita fa, ai wlh ina mamakin ki Khadijah, a ce har dangin Miji sun fi miki mu ƴan uwanki, nan nace miki Mubeena zata dawo wurin ki da zama tunda ba ki da ƴa Mace, ko ƴan aikace-aikace ta riƙa taya ki dashi, zaman ma zai fi miki daɗi tunda Yaran nan Maza ne ba zama suke yi ba, amma kika watsa min ƙasa a ido kika ƙeƙashe kika ce ba kya so, dama aka ce in baka yi Sharan masallaci ba zaka yi na coci wlh, ga shi nan an jajibo miki ƴar ƙauye an kawo miki, wannan yarinyar kuma sai kin yi aiki da ita daga ganin ta, don wlh idanunta suna gama buɗe wa da jin daɗi da sanyin AC, ke kanki sai ta gagare ki."

Baki sake Momy take kallon Hajiya Salman yadda take ta rattafo zance, duk da ta san cewa hali ne, mai hali ba ya fasa wa, amma ita kanta baza ta iya jajibo Mubeena ƴarta ta kawo ta gidan nan ba tunda ta san yarinyar bata da kunya ko kaɗan, ita kuma tana da ƙattin Maza baza ta iya haɗa su gida da wannan yarinyar ba, dama laifi tudu ne; ka taka naka ka hango na wani, ita bata ga halin yarinyar ta ba sai na Maryam wacce tana jin cewa haka kawai Maryam baza ta yi wa Hajiya Salma rashin kunya ba, sai dai in faɗa tayi, kuma yanzu Maryam ai daban take tunda tana auren ɗanta, duk da ba wai sun sanar da kowa bane zancen sun bar shi a tsakanin su ne, sai lokacin da Maryam zata tare a ɗakin ta sannan Momy take tunanin sanar da kowa a dangin su, duk da ta so ko Aunty Najwa Yayarta ta sanar mata,
Ɗan numfashi ta ja tare da kallon Aunty Salman da har yanzu take tsiyan ƙin amincewar zuwan ƴarta Mubeena gidan, don ta ji haushi ba kaɗan ba, shiyasa Momy tace, "to ki yi haƙuri Aunty Salma, Ni wannan yarinyar fa babu yanda za a yi in kore ta ko in hana ta zuwa, tunda gidan Ubanta ne, Alhaji ya fi Ni iko da gidansa zai kawo duk wanda yake so ya kawo gidan sa, amma Ni sai da amincewar sa, bani da hurumin koranta tunda shi ya je ya dauko ta."

"Ai dama haka za ki ce, dole dai sai kin nuna wata kusar ta fi wata, wlh na tabbata da ace Aunty Najwa ce ko Zainab; su suka ce zasu kawo nasu gidan nan, baza ki ƙi amince wa ba, tunda sun fi mu a wurin ki."

Cikin rashin jin daɗin maganar Momy tace, "a'a Aunty Salma kar ki ɗaura min Jakar tsaba Kaji su bi ni, mene ne abun magana a cikin nan? Ni a wuri na baku da bambanci da su tunda ɗaya na ɗauke ku, shikenan tunda kin faɗi haka idan Alhajin ya dawo zan yi mishi magana; kinga in ya amince ki dawo da ita Ni babu abun da ya shafe Ni, wurin zama ai akwai su birjik tunda ba a kaina zata zauna ba sai ki kawo ta."

Sanin cewa ta gaya mata magana ne, tunda ta san halin Momy ba a faɗa mata tayi shiru in har tana da yanda za tayi sai ta rama, shiyasa sai Aunty Salman ta miƙe tsaye tana cewa, "ina kuwa ƴata zata zo tunda tun farko ba a yi ninyar zuwan ta ba? Ko ta zo yanzu ma babu amfani, Ni kinga tafiyana, kuma na manta ban faɗa miki ba; jibi za a wuce Katsina ba ki kawo gudummawar ki ba, in kuma da ke za a je to?"

"A'a ba dani za a je ba, na kira ta a waya nayi mata Barka, sai ki ɗauki atamfa ɗaya da kayan jarirai guda biyu na sanyi ki bata nawa gudummawar, Allah ya raya."

"Amin." Hajiya Salma ta furta cikin jin zafin abun da Momyn ta bayar, wai duk wannan tulin dukiyar da take ciki, ga ƙaton gida amma ta rasa me zata ba wa ƴar ƙanwarta sai wannan tsiyar, amma ta san da ƴar wacce suka fito ciki daya ne baza ta basu wannan kaɗai ba, tun ba yau ba ta gama kula da Momy maƙon tsiya ne da ita, ƴan ɗakin su kaɗai ta sani in dai a alheri ne, dole sai ta nuna su ɗin ƴan Uba ne. Ƙwafa tayi a ranta take cewa, "matsiyaciya, da kin bar tsiyar ki ma, ai mun fi ƙarfin wannan."

Momy kuwa wacce ta taso domin ta raka ta, bata san ma tana yi ba, sai cewa tayi, "mu je Aunty na taka miki zuwa wajen, ki gaishe da su Hajiya in kin je gidan."

"Zasu ji."
Ta amsa mata tana yatsina fuska tare da yin gaba, sabida ba kaɗan ba a yanzu ta sake ƙule wa da halin Momyn, musamman yanda ta barta hannu rabbana sai gaisuwa da ta aike ta dashi ta kaiwa su Hajiyar su, kuma gani take yi don kawai babu Uwarta a ciki ne, amma da tana a raye baza ta ƙi bata wani abun takai musu ba,
Dama wanda yasa rai a abun wani dole zai sha wahala, wanda take yi don ita bata san ma tana yi ba

Koda suka sauka Falo ma babu Maryamu a wurin, ta shiga ɗaki ɗauko littafin ta domin Sadiq ya duba mata assignment ɗin da aka basu

Sadiq kaɗai suka tarar, shima sauri yake yi yana afa abinci sabida yunwar da ya dawo dashi sosai, ga shi har an soma kiran sallah yana son cinye wa ya wuce masallaci,
Bama su kula dashi ba tunda yana kan Dinnig ne, sai shi ne ya ɗaga murya yana gaishe da Hajiya Salman

"Ah... ah! Sadiq, ashe kana nan? Na shigo ban ganka ba?"

"Ina nan Aunty, yanzu na dawo school, ina wuni?"
Ya sake gaishe ta kasancewar bata amsa wancan gaisuwar ba

Ta amsa da fara'a tana tambayar sa school ɗin?

Yace, "Alhamdulillah."

Bayan sun gama gaisa wa ne suka fita da Momy, ta raka ta har bakin Mota sannan ta juya cikin gida.


[14/02, 9:30 am] OumƊahirah نفيسة: 🌱🌱🌱🌱🌱

      *SHAREEF*
          _SexyBoy_
🌱🌱🌱🌱🌱


_Writer: Nafisat Isma'il Lawal_
_Wattpad: UmmuDahirah_

*SARAUNIYAR TSOKANAR PERFECT🧝*



*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞

```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)```

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

       *P.W.A✍️*





*DATA SHARE*

Call, message or whatsap 07065334256

*MTN*
500MB 150
1gb 280
2gb. 560
3gb. 840
4gb. 1120
5gb 1400
6gb. 1700
Verlid for 30 days.












__________
*BOOK1*
_______________*FREE PAGE31to32*
_____Kwana biyun da suka wuce, duk SHAREEF yana gida babu inda yake zuwa sabida rashin lafiya da yake fama dashi, duk da dasauki but Dady ya hana sa zuwa wurin aikin, sai dai ya duba ayyukan a cikin computern sa

Gefe guda kuma

Please Login or Register in order to submit comment