Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

haka sun yarda ɗari bisa ɗari sai sun same ta.
Dukkansu suka cira masunsu sama sannan suka jefi wannan halittu dasu.
Masu guda tara jajawur suka tafi da gudu zasu cake a cikin wannan halitta mai baƙaƙen tufafi.
Saura ƙiris su dira a jikinta, wani irin baƙin hayaƙi ƙirim ya ɓulɓulo daga jikinsa ya juye izuwa ƙatuwar garkuwa sannan ya shiga tsakaninsu da su.
Masun guda tara suka dira a jikin wannan baƙar garkuwa, take suka zube ƙasa ba tare da sun yi mata kwarzane ba.
Waɗannan mutane guda tara suka zaro idanu cikin tsananin mamaki. Karo na farko a rayuwarsu sun ga abinda waɗannan maɗaukakan masu nasu basu huda ba.
Abinda basu sani ba shi ne, wannan fa ba asalin halittar da zasu yaƙa bane, wannan hoto ne kawai wanda sarkin su ya samar domin gudanar da gwaji.
Wannan sadauki ya tara waɗannan mutane guda tara a gabansa ya ce, "Idan za ku zage damtse, ku zage damtse. Aikin dake gabanmu bana wasa bane. Wannan halitta da kuka gagara samun nasara akanta yanzu, kwafin ainihin halittar da zamu kaiwa hari ne.
"Idan har ƙarfin na bogi ya kasance haka, ya ya kuke tunanin ƙarfin na ainihin zai kasance..?"
Sadaukin na zuwa nan a zancensa ya ware waɗannan dakaru nasa izuwa bibbiyu-bibbiyu sannan ya fara basu sabon horo akan yadda zasu sarrafa wannan jan mashi nasu.
Tsahon kwanaki ashirin da tara cir yana basu wannan horo sannan ya kammala.
A wannan lokaci sun gama zamowa ƙwararrun maharba. Sarki Farhama ya sauƙo wannan waje da fuka-fukinsa.
Sarki Farhama ya buɗe fuka-fukinsa yana yawo a cikin iska, su kuma Kentaurons suna zabga azababben gudu suka tunkari Ajalin-Abokan-Gaba.
****
Yau *08/04/2023*
Babi na gaba zaizo *12/04/2023* da yaddar ALLAH.RUHIN JARUMTAKA!
*
Babi na 109: *Sirrin sabuwar ƙabila: Kuyr*
*
***TARIHIN SAMUDUL ANSARI***
*
Wannan littafin sadaukarwa ne ga Zahra...
*
Da fatan kowa yasha ruwa, lafiya?
*
UMS
*
~Daular Shaha.
*
Sarki Samudul Ansari da Jalwar suna dawowa gida daga wajena suka ci gaba da baiwa kansu horon yaƙi mai kyau. Kullum Samudul Ansari da ɗansa Jalwar suna keɓewa a cikin wannan filin yaƙi su yi ta baiwa juna horo.
Dukda cewa jikin Jalwar a mummurɗe yake amma sai da ya sake murɗewa saboda tsananin horon da yake karɓa a wajen Samudul Ansari.
Jalwar yana da baiwa ta tsananin ƙarfin damtse, iya yaƙi da baƙin zafin nama.
Tun Samudul Ansari yana jarraba ƙarfin damtsensa akan ɗaga irin waɗannan takubba masu nauyin gaske har ta koma ga cewa, Jalwar na iya ɗaga ƙaton dutse wanda sai ƙarti sun taru sannan zasu iya ɗaga shi.
Baya ga wannan, Jalwar ya kware matuƙa a sarrafa takobi, Samudul Ansari ya bashi irin wannan horon takobi na musamman wanda indai mutum yana da shi ba zaiyi shakkar shiga dandazon dubbannin mayaƙa ba.
Samudul Ansari ya cika ya batse da ƙarfin sihiri da na aljanu, shi kuma Jalwar ya cika ya batse da zallar ƙarfin damtse da kuma jarumta.
Tsahon kwanaki ashirin kullum sai sun baiwa kansu horo. Tun sarauniya Arya tana tausayawa Jalwar bisa gagarumar wahalar da yake sha har ta daina.
A ranar da suka cika kwanaki na ashirin ɗin ne, sarki Samudul Ansari da Jalwar suna zaune a fada suna cin abinci.
"Ina da magana," inji tau'rin.
Samudul Ansari ya gyara zama, "Ina jin ka..."
"Baƙin mu suna isowa yau, don haka ku fara shirin tafiya Ajalin-Abokan-Gaba," inji tau'rin.
Samudul Ansari yayi guntun murmushi ya ce, "Sai yau kenan, har na fidda tsammanin zasu zo ai,"
"Kentauron suna da baƙin naci da kuma ƙarfin shiri akan duk abinda suka sa a gabansu, don haka ku kula." inji tau'rin.
Samudul Ansari yayi murmushi sannan suka ci gaba da cin wannan abinci, suna gamawa Samudul Ansari ya dubi Jalwar ya ce, "Ka je kayi shirin yaƙi, sannan kayi sallama da mahaifiyarka, yau abokan gaba zasu ƙaraso.
"Kayi sallama da ita, tamkar wanda zai tafi kabari a yau,"
Jalwar yana jin abinda Samudul Ansari ya ce saiya cika da tsananin mamaki.
Kasancewar tun da yake a rayuwarsa bai taɓa fita gagarumin yaƙi kamar wannan ba, yasa ya ja bakinsa yayi shuru baice komai ba. Ya risina a gaban mahaifin nasa sannan ya fice.
Jalwar yana futowa daga cikin wannan fada ya wuce kai tsaye izuwa turakar sarauniya Arya.
Yana shigowa cikin turakar yayi arba da ita akan gado, tayi shuru tana tunani.
Har Jalwar ya ƙarasa kusa da gadon bata ma san ya shigo ba.
Kai, har sai da ya dafa kafadarta sannan tayi firgigit kamar wadda ta farka daga barci.
Cikin mamaki Jalwar ya zauna a gefenta sannan ya dubeta ya ce, "Ya ke ummina! Tunanin me kike yi wanda har yasa hankalinki kwata-kwata baya nan?"
Sarauniya Arya tana jin wannan tambaya ta ce, "Har yanzu mahaifinka bai bayyana min, yaƙin da za kuje da wanda zaku yaƙa ba. Ta ya ya kake tunanin hankalina zai kwanta alhalin manyan masoyana na duniya zasu tafi yaƙi?"
Jalwar yana jin wannan batu tausayin Arya ya kama shi, ya kama kafaɗunta da hannayensa biyu ya ce, "Kada ki damu yake ummina! Tabbas yaƙi na tunkaro mu ko kuma nace yaƙi ya iso mu. A yau ɗinnan ni da baba zamu je filin yaƙi domin gwabzawa da abokan gaba..."
"Fatan nasara," inji sarauniya Arya lokacin da ta juya masa baya.
Jalwar na ganin haka jikinsa yayi sanyi, ya juyo ta gabanta cikin sauri, ya durƙusa kan gwiwowinsa ya ce, "Kiyi haƙuri yake ummina! Abokan gabar namu suna da tsananin ƙarfi, idan muka ce zamu ringa bayyana shirin da muke da wuya mu sami nasara akansu."
Sarauniya Arya ta dube shi fuskarta cike da murmushi ta ce, "Kada ka damu, ɗana. Ko kaɗan raina bai ɓaci ba. Duk wadda ta kasance matar babban mutum kamar mahaifinka dole ne ta kasance mai ƙarfin zuciya.
"Saboda a kowanne lokaci yaƙi zai taso. Ubangiji ya baku sa'a. Ka yaƙi abokan gaba da dukkan ƙarfin ka..."
Jalwar yana jin wannan batu, wani irin ƙwarin gwiwa ya rufe shi.
Ya sumbaci goshin Arya sannan ya fita daga wannan ɗaki.
Jalwar ya shige cikin ɗakinsa ya saka sulken yaƙi mai tsadar gaske, sannan ya ɗauki takobinsa da kuma garkuwarsa ya tunkari inda Samudul Ansari yake.
Jalwar yana zuwa cikin fadar ya iske tuni Samudul Ansari ya gama kimtsawa shima.
Ba tare da ɓata wani lokaci ba, hadimi ya kawo musu dawakai guda biyu, suka haye dawakan sannan suka tunkari hanyar da zata kai su filin yaƙin.
Babu yadda za'a yi mutum yayi arba da wadannan mutane guda biyu, basu burge shi ba, saboda shigar da suka yi da kuma kwarjininsu.
Bayan doguwar tafiya ta tsahon sa'a uku, suka iso wannan filin yaƙi.
Filin yaƙi ne ƙatoton gaske wanda aka gina a wannan daula musamman domin gwabza yaƙi.
Babu komai a cikin wannan filin yaƙi face ruɓurɓushin ƙasusuwan bil'Adama da kuma jar ƙasa wadda ta zuƙi jini mai yawa.
Samudul Ansari da ɗansa Jalwar suna tsaye a cikin wannan fili yaƙi, suka ji ƙasa ta soma girgiza.
Kafun su ankara tuni sarki Farhama tare da Kentaurons guda goma, sun dira a wannan fili.
Kamar yadda na baiwa su Samudul Ansari labarin waɗannan halittu haka suka gan su. Babu abu guda da ya saɓa.
Bayan kallon-kallo sarki Farhama ya tako sawayensa yazo gaban Samudul Ansari ya tsaya.
Saboda tsananin kwarjinin Samudul Ansari da kuma gagarumar shigar da yayi, sarki Farhama ya gagara cewa komai a gabansa, kawai ya juya ya koma da baya.
Shugaban waɗannan dakaru Kentauron ya dubi Farhama ya ce, "Shin zaka saro mana kansa, ko kuma mu saro da kanmu?"
Sarki Farhama na jin abinda suka ce, ya zaro wata zabgegiyar takobi ya kwarara uban ihu ya ce, "Abin kunya ne a gareni, ace kun shigo har cikin ƙasata, sannan na gagara saro muku kan wani,"
A lokacin Samudul Ansari ya daka masa tsawa, "Yankin ƙasarka? Waye kai tukun?"
Muryar Samudul Ansari na fita da kaushi da kuma iko wanda yasa dole sarki Farhama ya ja bakinsa yayi shuru.
Samudul Ansari ya dafa hatimin aljani Nara. Nan take komai da komai na jikinsa ya sauya.
Wata gagarumar wuta ta fara kewaye jikinsa tamkar hayaƙi.
Samudul Ansari ya dubi Jalwar ya ce, "A wannan rana zan nunawa duniya, na raini ɗan zaki kuma ya girma. Kaje ka baiwa wancan sarki mai rainin hankalin kunya."
Samudul Ansari yana gama faɗin haka ya caka takobin dake hannunsa cikin ƙasa sannan ya zubawa sarki Farhama idanu.
Jalwar ya kwarara uban ihu ya zaro takobinsa sannan ya ɗaga garkuwarsa sama ya ruga tsakiyar wannan fili ya tsaya.
Koda sarki Farhama yaga abinda sarki Samudul Ansari yayi masa sai ransa ya ɓaci. Wato an nuna masa bai kai ba kenan.
Sarki Farhama ya ɗaga zabgegiyar takobin dake hannunsa ya ruga da gudu kan Jalwar.
Jalwar na ganin haka ya gyara tsayuwa, ya fuskanci Farhama sosai.
Sarki Farhama na isowa gabansa suka ruguntsume da azababben yaƙi mai ban tsoro.
Farhama ya wanzu yana kaiwa Jalwar muggan sara da wannan takobi dake hannunsa, shi kuma Jalwar yana karewa.
Farhama ya cika da tsananin mamaki bisa ganin tsananin ƙarfin damtsen Jalwar da kuma zafin namarsa.
Komai ƙarfin saran da Farhama ya kaiwa Jalwar cikin kwanciyar hankali yake karewa, sannan maimakon ya durƙusa ko kuma ya faɗi sai dai ka ganshi a tsaye cak!
Sarki Farhama sadaukin gaske ne, amma bai taɓa haɗuwa da jarumi mai kuruciya kamar Jalwar ba.
Koda aka ɗauki lokaci ana wannan gumurzu sai zuciyar Farhama ta fara tafarfasa, ganin cewa, duk wannan gumurzu da yake yi Kentaurons suna tsaitsaye a baya suna kallonsa.
Duk wanda kake so ku haɗa kai dashi, dole kana buƙatar ka nuna masa ƙarfinka.
Sarki Farhama ya cika musu baki akan zai iya sare kan Samudul Ansari, amma gashi tun daga kan ɗansa ya gagara taɓuka komai.
Lamarin da yasa zuciyarsa ta ci gaba da tafarfasa kenan tamkar zata ƙone.
Sarki Farhama ya daka tsalle baya, ya ƙurawa Jalwar idanu.
Jalwar ma ya tsaya cak! shima ya ƙurawa Farhama idanu.
Ɗan gajeren lokaci suna nazarin juna, kafun su falfalo da azababben gudu izuwa kan juna.
Kafun su haɗu da kimanin taku bakwai, dukkansu suka daka wawan tsalle sama.
Farhama ya kaiwa Jalwar sara a ƙirji, shi kuma Jalwar ya kaiwa Farhama sara a wuya.
Dukkansu suka kaucewa juna, takobin Farhama ta farke sulken Jalwar, take duk sulken ya zube ƙasa.
Shi kuma Jalwar takobinsa ta yanki wani kaso daga cikin gashin kan Farhama.
Dukkansu suka rikito a ƙasa cikin tsananin fusata.
Kafun su sake kaurewa, wannan shugaban dakaru Kentauro ya ƙwalawa sarki Farhama kira ya ce, ya basu wuri tunda babu abinda zai iya.
Cikin ƙunar rai sarki Farhama ya koma da baya, yana hararar Jalwar.
Wannan sadauki ya dubi wani mutumi daga cikin mutanensa ya bashi umarnin saro kan Jalwar.
Mutumin ya yi ihu sannan ya zaro jan mashinsa ya rugo da gudu kan Jalwar.
Jalwar na ganin haka ya mayar da takobinsa cikin kufe, sannan ya gyara riƙe garkuwarsa ya dunƙule hannunsa guda.
Wannan mutumi na ƙarasowa gaban Jalwar ya kawo masa wawan suka da wannan jan mashi na hannunsa.
Jalwar ya saka wannan garkuwa ya tare mashin, jan ƙarfen mashin na haɗuwa da jikin garkuwar ya tsargeta gida biyu.
Ƙiris ya hana ta huda Jalwar amma yayi dungure cikin zafin nama ya koma bayan wannan mutumi.
Kafun mutumin ya juyo tuni Jalwar ya gabza masa wawan naushi a gadon baya.
Duk tsananin ƙarfin damtse irin na Jalwar bai yiwa wannan mutumi komai ba, hasalima hannun nasa lotsawa ciki yayi tamkar buhun auduga ya nausa.
Take maganganun da na sanar dashi suka faɗo masa, waɗannan halittu basa jin duka a ko'ina face ƙirjinsu.
Kafun Jalwar ya samu nasarar sake gabzawa wannan halitta naushi, tuni ta juyo.
Wannan mutumi ya sake kawo masa wawan suka da wannan jan mashi, Jalwar yayi amfani da dukkan zafin namansa ya kauce.
Duk da haka saida wannan jan mashi ya karci wandon ƙarfen dake kunkuminsa, take wandon ya tarwatse ya bi iska.
Jalwar ya bayyana daga shi sai bante wanda ko cinyoyinsa bai gama rufewa ba.
Cikin fusata Jalwar ya shaƙo wuyan wannan mutumi ya matse shi da ƙarfi.
Nan fa suka fara kokawa, halittar tana ƙoƙarin ƙwacewa shi kuma yaƙi sakin ta.
Tsahon ɗan lokaci, mutumin ya fusata yasa hannayensa biyu ya cicciɓi Jalwar sannan ya fara tsala wani irin azababben gudu dashi.
Kai, ko walƙiya ba zata fi wannan mutumi gudu ba.
Haka yaje da gudu ya gwara gadon bayan Jalwar da wata ƙatuwar bishiya dake gefen filin yaƙin.
Bishiyar ta tumɓuko tun daga jijiyoyinta ta faɗi ƙasa.
Jalwar ya saka gwiwar hannunsa ya doki tsakiyar kan wannan mutumi.
Mutumin ya kwarara uban ihu ya ɗaga sawayensa na gaba sama, ya fara tsalle-tsalle tamkar doki zai jefar da Jalwar.
Koda Jalwar yaga wahala ta fara yi masa yawa, sai yayi tsalle daga wuyan wannan halitta ya faɗi gefe guda.
Mutumin yayi kururuwa ya shashshafa wuyansa sannan ya cira wannan mashi dake hannunsa sama, ya jehowa Jalwar shi.
Mashin ya taho da gudu zai caki Jalwar a ƙirji, cikin zafin nama ya goce.
Mashin ya dira akan wani tsauni.
Koda Jalwar yaga babu wannan mashi a hannun wannan mutumi, sai ya falfalo da azababben gudu izuwa kansa.
Yana zuwa suka ruguntume da azababben yaƙi amma hannu da ƙafa.
A nan ma fa, sai da wannan mutumi ya nunawa Jalwar komai sammakonka wani a tafe ya kwana.
Da ƙyar Jalwar yake ƙwatar kansa daga sharrinta.
A cikin daƙiƙa guda tana iya kai masa naushi sau uku ko ma fiye.
Kafun a jima tuni Jalwar ya fara haɗa zufa.
Ana cikin haka ne, wannan halitta ta gabzawa Jalwar wawan naushi a ƙirji.
Take Jalwar yayi tsalle ya faɗo acan baya.
Sarki Samudul Ansari da waɗannan halittu duk suna ganin wannan gumurzu dake faruwa.
Wannan halitta tana ganin ta samu nasarar gabzawa Jalwar wannan wawan naushi, ya daka wawan tsalle ya dira akan Jalwar.
Ya ɗaga lafta-laftan sawayensa sama zai take ƙirjin Jalwar domin ya ƙarasa kashe shi.
Ƙiris ya hana sawayen su dira akan ƙirjin Jalwar, ya mirgina gefe.
Sannan ya daka wani wawan tsalle tamkar wanda aka harba, ya doki ƙirjin wannan halitta da gwiwar ƙafarsa.
Take jikin wannan halitta ya soma ƙanƙacewa yana motsewa. Kafun a jima tuni ya zamo kamar zaki, ya dawo kamar kyanwa, sannan ya zamo kamar ɓera ya yi bindiga ya bi iska.
Waɗannan halittu guda tara da sarki Farhama suka ƙurawa Jalwar idanu cikin tsananin mamaki.
A ɓangaren Samudul Ansari kuwa, murmushi ne kawai yake gilmawa ta gefen bakinsa.
A yau babban sirri ya bayyana - sirrin sabuwar ƙabila wadda ya samar sakamakon aurensa da kuma Arya.
Mutanen duniya kafun bayyanar Samudul Ansari sun fi imani da jarumtaka da ƙarfin damtse akan komai.
Amma bayan juyewar zamani, yanzu sun fi yarda da ƙarfin sihirin tsafi akan komai.
Tabbas samar da sabuwar ƙabila mai ƙarfi kamar na Jalwar abu ne mai kyau musamman ga Samudul Ansari wanda keda abokan gaba masu yawan gaske.
Duk wanda aka ce zai yaƙi hatsabibin halitta kamar Kentauro ba tare da sirrin tsafi koda guda ɗaya ba, tabbas ya zamo abin tsoro wanda zai girgiza duniya.
Jalwar yayi ihu ya dubi waɗannan halittu guda ya nuna su da takobinsa kamar yana so ya ce basu kai ba.
Sarki Farhama baisan sa'adda ya sake falfalawa da gudu kan Jalwar ba.
Su kuma sauran waɗannan halittu guda tara, suka ruga kan Samudul Ansari suna ɗaga masunsu sama.
A wannan lokaci Samudul Ansari yana tsaye a tsakiyar fiin yaƙin, sirrin aljanin wuta yana kewaye jikinsa, takobin wuta tana cake cikin ƙasa.
Halittun suna ɗaga masun hannunsu sama, hasken rana yana ƙara musu ja.
Samudul Ansari ya ɗaga wannan takobi tasa sama.
Jajayen gajimare suka fara bayyana a cikin sararin samaniya.
Suna isowa gaban Samudul Ansari suka fara kawo masa suka da waɗannan jajayen masu dake hannunsu.
Shi kuma ya wanzu yana mai kare saran nasu da wannan takobin wuta dake hannunsa.
A duk sa'adda wannan jan mashi nasu ya haɗu takobin-wuta dake hannun Samudul Ansari, sai gagarumar wuta ta cika wannan waje sannan ta zube ƙasa.
Kafun a ɗau lokaci tuni suturar jikin waɗannan mayaƙa da ta Samudul Ansari sun babbake sannan sun zube ƙasa.
Waɗannan halittu basa son wuta ko kaɗan hakan yasa suka fara baya-baya da Samudul Ansari.
A duk sa'adda ya kawo musu sara, da zarar wannan tartsatsin wuta ya zubo, sai kaga sun yi sauri sun kauce.
Tun kafun Samudul Ansari ya fara yaƙi da waɗannan halittu ya fuskanci cewa, ko kaɗan basa son zafi.
Saboda wannan dalili ne, Samudul Ansari ya fiddo takobin wuta wadda aljanin-wuta Nara ya bashi.
A ɓangaren Jalwar da sarki Farhama abin ya sake ɗaukar zafi. Dukkansu suna kaiwa juna sara da suka cikin zafin nama.
A wannan lokaci sun yanki juna sau uku-uku, jini nata zuba daga jikinsu amma saboda tsananin juriya basu fasa wannan faɗa ba.
Sarki Samudul Ansari ya ci gaba da ƙuntatawa waɗannan mayaƙa guda tara da zabgegiyar takobin da hannunsa.
Ya hana su yin gabas ko yamma, ta ko'ina muggan hare-hare yake kai musu.
Ana cikin haka Samudul Ansari ya samu nasarar saran jikin ɗaya daga cikinsu.
Duk da cewa takobin bata fasa fatarsa ba, amma gagarumar wuta ta kama jikinsa, wadda tasa yayi ihu har ya fita a hayyacinsa.
Koda sauran waɗannan halittu suka ga haka, sai suka fara shawarar guduwa domin su je su ƙaro shiri.
Sanin da suka yiwa Samudul Ansari baida irin wannan gawurtacciyar takobi, saboda haka bayyanarta a wannan yaƙi baiyi daidai da lissafinsu ba.
Jalwar yayi wani wawan tsalle sama ya doki ƙirjin Farhama, saboda ƙarfin wannan naushi saida Farhama ya faɗa da baya sannan ya fara aman jini.
Sarki Farhama na zaune yana aman jini sakamakon mugun dukan da Jalwar yayi masa yaji an ɗaga shi da hannu ɗaya sannan aka yi sama dashi.
Ya duba haka sai yaga ashe waɗannan halittu ne suka kawo masa ɗauki. Suna zabga irin wannan azababben gudu nasu wanda yafi tunanin mutum.
Samudul Ansari ya yi murmushi ya aika musu saran takobi-mai-tafiya da Saif-Al-Barzaƙ.
Ƙatoton fai-fai ya fice daga tsinin takobinsa yayi kan halittun. Fai-fan yana tafe yana tarwatsa iskar dake gabansa.
Duk tsananin gudu irin na waɗannan halittu saida wannan fai-fai ya iso su, sannan ya hallaka biyu daga cikinsu.
Sauran na ganin haka suka sake tarwatsewa suka nemi hanya.
Daga wannan lokaci sarki Samudul Ansari da ɗansa Jalwar suka koma gida, sarauniya Arya tayi farin ciki matuƙa da ganin dawowarsu lafiya.
Sarki Samudul Ansari da Jalwar suka ci gaba da gwagwarmaya suna karya azzalumai suna shimfiɗa adalci a garuruwansu.
Zamani ya ci gaba da tafiya. Sarauniya Arya ta sake haihuwar tagwaye guda biyu; mace da na namiji.
Yaran suka taso da baiwar kyawu da kuma tsantsar jarumtaka.
A haka har shekaru masu yawan gaske suka shuɗe.
Sannu-sannu har waɗannan shekaru ɗari da aka cewa sarki Samudul Ansari shirinsu Yilan zai kammala suka fuskanto.
Duk da cewa zamani mai tsaho ya shuɗe, amma idan kaga Samudul Ansari zaka ɗauka bai wuce shekaru arba'in da biyar zuwa da bakwai ba.
Idan ka dubi sarauniya Arya zaka ce ba zata wuce shekaru talatin da biyar ba.
Akwai wani babban sirri wanda dukkansu suke samu a duk lokacin da suka kusanci juna. Tsakanin nau'in jinin Samudul Ansari da na sarauniya Arya akwai alaƙa mai kyau wadda tasa sirrin rashin tsufa ya shige su.
Tsahon wannan zamani kullum Samudul Ansari ƙara gyara makaman yaƙinsa yake, yana sake baiwa kansa horon yaƙi. Saboda yasan cewa, shiri na shekaru ɗari fa, ba wasa bane.
****
Yau *10/04/2023*
Babi na gaba zaizo *13/04/2023* da yaddar ALLAH.RUHIN JARUMTAKA!
*
Babi na 110: *Sabon ƙarfi*
*
***TARIHIN SAMUDUL ANSARI***
*
Wannan littafin sadaukarwa ne ga Zahra...
*
UMS
*
~Daular Gorgon.
*
Ranar ashirin da biyu ga watan Augusta, gangunan jikinsu sarauniya Yilan, Gauhan da kuma BES guda huɗu suka cika shekaru ɗari a cikin wannan ƙatuwar tukunya ta macijiya Ziyazilu suna zuƙar sinadarin dake cikinta.
Da asuba wannan tukunya ta soma kumbura tana bori, tiririn dake fita daga cikinta ya ninka kansa sau goma.
Tsahon ɗan lokaci tana haka, kafun tayi bindiga ta tarwatse.
Ruwan dake cikinta ya malale a ƙasa, abin mamaki babu su sarauniya Yilan babu alamunsu.
Jim kaɗan waɗansu korayen sinadarai da suka cika wannan ruwa suka soma haɗewa da juna, suna kumbura suna samar da siffofi kala daban-daban.
Siffofin BES guda huɗu suka bayyana, daga bisani gangar jikin Gauhan, kafun gangar jikin sarauniya Yilan ta fara haɗewa.
Dukkan gangunan jikinsu a wannan lokaci koraye ne sharr tamkar korayen-ganyaye. Lokaci-lokaci wani irin tiriri yana fita daga jikin nasu.
BES suka miƙe tsaye su huɗu, suna tafiya sawayensu suna ɗaguwa a hankali, har suka je gaban Ziyazilu suka zube suka yi sujjada.
Ziyazilu ta dube su da waɗannan idanuwa nata masu kama da na sarauniya Yilan, sannan ta jefe su da dafin dake cikin bakinta jajawur.
Jan dafin bakin nata yana taɓa su, suka soma juyewa izuwa ainihin siffarsu.
Suna gama juyewa izuwa ainihin siffofinsu, wani irin mugun jiri ya ɗebe su saboda tsananin ƙarfin dake cikin jikinsu.
Zubewar BES ƙasa keda wuya, wani saurayi mai gangar jiki kore sharr ya shigo cikin wannan ɗaki, yana irin wannan tafiya da suke.
Saurayin ya zube a gaban Ziyazilu yayi sujjada. Kafun ya ɗago wata budurwa ma ta shigo izuwa cikin wannan ɗaki, itama ta zube a gefensa suka yiwa Ziyazilu sujjada.
Su ma Ziyazilu ta jefe su da wannan jan dafi nata, take dukkansu su ma suka zube a ƙasa sumammu.
Sai bayan ɗan gajeren lokaci sannan suka farfaɗo daga wannan suma da suka yi.
Saurayin ba wani bane illa GAUHAN ANSARI... Ita kuwa budurwar ba wata bace illa SARAUNIYA YILAN GORGON.
Dukkansu suka bayyana durƙushe akan gwiwowinsu, kawunansu suna kallon ƙasa, hannayensu guda biyu a buɗe suna kallon sama tamkar waɗanda za'a baiwa wani abu.
Jim kaɗan abubuwa guda uku suka dira akan hannayensu. Gauhan yana

Please Login or Register in order to submit comment