Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da yasa waɗansu jajayen gajimare suka fara bayyana kenan.
Sannu-a-hankali sai da ya samar da guda takwas sannan suka taho saman kansa suka tsaitsaya.
Wani irin jan walƙiya mai kama da wuta ya soma sukuwa daga cikin wannan gajimare izuwa cikin takobin Samudul Ansari.
Idan ka dubi wannan waje daga nesa, zaka ga mutane guda biyu suna fuskantar juna.
Ɗaya yana tsaye, sannan akwai mutum-mutumi da aka halicci jikinsu da irin wannan farar ƙasa wadda suke tsaye a kanta sannan ga macizai rataye a wuyan kowanne ɗaya daga cikin waɗannan mutum-mutumi.
Ɗaya kuma yana tsaye a ƙasan waɗansu jajayen gajimare guda takwas da suke baiwa takobinsa jar walƙiya.
Kai da gani ka san cewa, gumurzun da waɗannan hatsabibai zasu gwabza zai yi matuƙar bayar da mamaki domin duk a cikinsu babu wanda ka isa ka raina.
****
Yau *30/03/2023*
Babi na gaba zaizo *01/04/2023* da yaddar ALLAH.SSSSRUHIN JARUMTAKA!
*
Babi na 105: *Zafin rabuwa da masoyi*
*
***TARIHIN SAMUDUL ANSARI***
*
Wannan littafin sadaukarwa ne ga Zahra...
*
UMS
*
Cikin tsananin mamaki sarki Jiz'Ban ya sake ƙarewa Samudul Ansari kallo. Kafun ya taho wannan tafiya bai taɓa tsammanin Samudul Ansari yana sarrafa aljanin-wuta ba, amma a yanzu idanuwansa sun gane masa haka.
To, amma wannan fitowa da sarki Jiz'Ban yayi, ba ƙaramin gagarumin shiri yayi mata ba.
Zaka iya cewa, ya shiryawa kowanne irin shiri da sarki Samudul Ansari zai zo masa da shi.
Sarki Jiz'Ban ya juya ya dubi waɗannan mutum-mutumi guda takwas dake tsaitsaye a bayansa, ya saka takobinsa ya sassari kowanne ɗaya daga cikinsu.
Sinadarin Reniu, iska, dalma da walƙiya ya shiga jikinsu.
Waɗannan macizai dake rataye a wuyansu suka juye izuwa takubba.
Takubban iska, takubban Reniu, takubban dalma da takubban walƙiya.
Ba tare da jinkirin komai ba, sarki Jiz'Ban ya baiwa huɗu daga cikin waɗannan mutum-mutumi umarnin afkawa Samudul Ansari.
Mutum-mutumin guda huɗu suka kwarara uban ihu, suka falfala da azababben gudu kan Samudul Ansari.
Sai dai kafun su isa, aka ga waɗansu aljanu masu gangar jiki na wuta sun sauƙo daga cikin wannan gajimare sun tari mutum-mutumin.
Nan fa aka fara gwabza azababben yaƙi wanda ya tayar da hankalin wannan waje da suke.
Hadiman Samudul Ansari suna riƙe da takubba ƙerarru daga wuta, su kuma hadiman sarki Jiz'Ban suna riƙe da takubba waɗanda ake ƙera daga sinadaran Bankai.
Nan fa faɗan nasu ya fara ɗaukar hankali, guma-guman wuta da sin adarai kala dabam-dabam suka fara sauƙowa cikin wannan filin yaƙi.
Sai dai kaga kawanyar wuta da sinadaran Bankai suna zubowa cikin wannan fili.
Lamarin da yasa filin ya fara girgiza gagarumar ƙura tana tashi daga cikinsa kenan.
Kafun ka ce kobo, tuni wannan waje ya gama gaurayewa da gagarumar ƙura babu abinda idanu zasu na hangowa idan ba wannan bala'i dake zubowa filin ba.
Amma idan kayi duba izuwa cikin wannan ƙura kuwa, zaka ga mutum-mutumi guda takwas suna gwabzawa.
Sun ware kansu bibbiyu-bibbiyu suna ta gabzar juna.
Gaba ɗaya mutum-mutumin sarki Samudul Ansari suna riƙe da zabga-zabgan takubba waɗanda aka samar daga wuta.
Su kuma mutum-mutumin sarki Jiz'Ban suna riƙe da takubba mabambanta. Wasu takobin walƙiya, wasu takobin Reniu, wasu takobin iska, wasu kuma takobin dalma suka rirriƙe.
A duk lokacin da takubbansu suka haɗu a waje guda, sai dai mutum yaga gagarumar ƙura ta turnuƙe wannan waje gaba ɗaya.
Ba'a ɗau wani lokaci ba, sarki Jiz'Ban da sarki Samudul Ansari suka gane cewa, ƙarfin waɗannan hadimai nasu yazo ɗaya.
Cikin gaggawa suka kaɗa takubban hannunsu, take waɗannan halittu guda goma sha-shida suka bi iska.
A hankali ƙurar wajen gaba ɗaya ta lafa, sarki Jiz'Ban ya sake bayyana gaban sarki Samudul Ansari.
A wannan lokaci babu waɗannan mutum-mutumi guda takwas a bayansa, sarki Samudul Ansari kuma, babu waɗannan gajimarai a saman kansa.
Ga dukkan alamu a wannan lokaci, waɗannan hatsabibai guda biyu suna so su gwabza gaba da gaba, tunda sun gwada ta bayan fage basu sami nasara ba.
Sarki Jiz'Ban ya ɗaga wannan takobi tasa [Bankai 98] sama, lamarin da yasa ƙasar da suke kanta ta tsatstsage kenan.
Dai-dai inda sarki Samudul Ansari ke tsaye ne kaɗai bai tsatstsage ba, irin wannan koren-hayaƙi ya soma ɓulɓulowa daga cikin ƙasa, ya soma cika wajen.
Sarki Samudul Ansari yayi murmushi ya caka takobinsa a cikin ƙasa, lamarin da yasa gagarumar wuta ta soma ƙone wannan koren-hayaƙi kenan, kafun a jima duk ta ƙone shi.
Sarki Jiz'Ban da sarki Samudul Ansari suka bayyana a fili ƙarara, babu wani abu da ya tare gabansu.
Sarki Samudul Ansari ya ce, "Kana ta kawo min hari daga nesa, shin kana tsoron mu gwabza gaba-da-gaba ne?"
Sarki Jiz'Ban ya kurma uban ihu ya doki ƙasa da sahunsa guda ya ce, "Kai yaro! Inda ace ina jin tsoro da ban fito wannan tafiya ba, da ban kawo ma hari ba.
"Wai, ina gwadaka ne naga ko ka kai na fafata da kai gaba-da-gaba... Lallai na fuskanci cewa wuyanka ya kai yanka..."
Sarki Jiz'Ban na gama faɗin haka ya falfalo da azababben gudu kan sarki Samudul Ansari yana tafe yana ɗaga wannan takobi tasa sama.
Koren-hayaƙi ya soma sauƙowa daga sararin samaniya, yana biyayya da ƙarawa wannan takobi ta hannunsa ƙarfi.
A wannan zamani, idan ba takubban dake hannun sarauniya Yilan ba, babu takubban da suka fi na hannun sarki Jiz'Ban ƙarfi.
Wannan koren-hayaƙi da yake yawan bayyana shi ne sirrin wannan takobi, shi ne ikonta sannan shi ne abinda ke ƙara mata ƙarfi.
Bayyanar wannan koren-hayaƙi a wannan waje yana nufin babu wani iko da zaiyi tasiri a wajen, idan ba ita ba.
Saboda wannan dalili sarki Jiz'Ban yana da tabbaci a ransa ɗari bisa ɗari, saiya sami nasara akan Samudul Ansari.
Sarki Samudul Ansari ya tsaya cak! a cikin wannan koren-hayaƙi tamkar hayaƙin ya gama aiki akansa.
Cikin tsananin farin ciki, sarki Jiz'Ban ya ƙarasa gaban Samudul Ansari sannan ya kawo masa wawan sara a kafaɗa.
Tun kafun takobin ta dira akan kafaɗar Samudul Ansari wata alama mai kama da koren-haske ta bayyana daidai inda takobin zata sara.
Faruwar hakan keda wuya sarki Samudul Ansari ya soma jin zogi a wannan waje, hannun nasa ya fara karkarwa, tamkar dama an riga a sare shi.
Sarki Jiz'Ban na ganin haka, yayi murmushin samun nasara sannan ya ƙara taƙarƙarewa wajen ganin saran nasa ya isa.
Sarki Samudul Ansari baiyi motsin komai ba, har wannan takobi ta dira akan kafaɗarsa.
Koren-hayaƙi ya ratsa ta cikin hannun Samudul Ansari, ya ɓalla ƙashin hannun.
Zogi da rawan da hannun keyi, kafun takobin ta sara ya fara aiki akansa.
Sarki Jiz'Ban ya bushe da dariyar mugunta, ya ɗaga takobin hannunsa da nufin ya sake ƙaddamarwa Samudul Ansari wani saran.
Ba zato ba tsammani! yaji hannunsa ya fara karkarwa sannan ƙashin hannun yayi ƙara ya ɓalle.
Cikin tsananin mamaki, ya duba hannunsa ai kuwa sai yayi arba da irin abinda ya faru da sarki Samudul Ansari shi ne ya faru dashi.
Cikin tsananin mamaki ya sake ɗago kansa ya dubi sarki Samudul Ansari, abinda ya gani shi ne ya girgiza shi.
Sarki Samudul Ansari ya gani tsaye cak! lafiyansa ƙalau babu abinda ya same shi.
"Ƙarya ne," inji sarki Jiz'Ban cikin ƙaraji. "Ni za'a yiwa rufa-ido?"
A wannan lokaci idanuwan sarki Samudul Ansari suna tsaye akan wannan littafi wanda marigayi mayaƙi Nurbas ya bashi, wanda ke ɗauke da bayanan takobin Saif-Al-Barzaƙ.
'Na daga cikin babban amfanin takobin Saif-Al-Barzaƙ: Rufa-ido. Zaka iya tsayawa a gaban abokin gabarka, hannunka guda na hagu na riƙe da takobin Saif-Al-Barzaƙ har wannan abokin gaba naka, ya ƙaddamar ma da hari.
'Abinda zai fuskanta na gaba shi ne, juyewar wannan hari izuwa kansa. Wannan shi ne ɗalasimi na musamman da kakana ya saka a cikin takobin,'
Waɗannan su ne abubuwan da Samudul Ansari ya karanta a cikin wannan littafin, sannan shi ne yadda aka yi ya yiwa sarki Jiz'Ban rufa-ido.
Cikin gaggawa sarki Jiz'Ban ya fiddo irin wannan batta, wadda suke ɗaurewa a kunkuminsu domin gudun kada ɓacin-rana. Ya shanye abinda ke cikinta.
Hakan ne ya bashi damar farfaɗowa daga mugun dafin dake yawo a jikinsa.
Fuskarsa a cike da tsananin mamaki ya ƙarewa Samudul Ansari kallo, sannan ya ɗaga kansa sama ya kwarara uban ihu, koriyar walƙiya tayi feshi daga cikin bakinsa.
Baƙaƙen hawaye suka fara zubowa daga cikin idanunsa.
Sarki Jiz'Ban yasa hannunsa guda ya shafi daidai ƙashin da ya ɓalle, hakan yasa ƙashin ya koma kamar da amma har a wannan lokaci yana jin zogi.
Samudul Ansari yayi murmushi ya ce, "Na fi ƙarfin ku, ku fita daga sha'ani na, ba za ku taɓa samun nasara akaina ba..."
Sarki Jiz'Ban ya sake kurma uban ihu ya ce, "Ƙarya kake yaro! Ziyazilu ta rubuta yau a matsayin ranar da zan yi nasara akan ka, kuma tabbas sai nayi nasara akan naka..."
Yana faɗin haka ya sake ɗaga takobinsa sama, koren hazo ya soma sauƙowa wannan waje.
Hazon ya danne ƙarfi da ikon Samudul Ansari ya zamana ikon sarki Jiz'Ban ne kaɗai ke aiki a wajen.
Maimakon sarki Jiz'Ban ya kaiwa Samudul Ansari irin harin da ya kai masa ɗazu, sara kawai ya iska.
Wani zabgegen fai-fai wanda zai kai girman kamu goma ya fice daga tsinin takobinsa, ya tunkari Samudul Ansari.
Samudul Ansari ya sha yin arba da saran Bankai-mai-tafiya ba sau ɗaya, ba sau biyu ba.
Kai ya taɓa yin arba da harin ɗaya daga cikin BES ma, amma bai taɓa kallon sara mai hatsari da ƙarfi kamar wanda sarki Jiz'Ban ya aiko masa ba.
Fai-fai ne kore sharr, yana tafe yana juyar da iskar dake taɓa shi izuwa kore-kore, sannan wani huci mai zafi da sanyi duk a lokaci guda na fita daga cikinsa.
Ba don Samudul Ansari cikakken shiryayye bane, bai isa yayi ido-huɗu da wannan fai-fai ba tare da ya fara karkarwa ba.
Sarki Jiz'Ban ya mayar da takobinsa cikin kufenta sannan ya zaro wannan jan mashi wanda ke ɗaure a gadon bayansa, ya falfalo da azababben gudu ya rako wannan faifai.
Niyyar sa ita ce, sarki Samudul Ansari yana mayar da hankali wajen kaucewa wannan fai-fai zai yi amfani da wannan dama wajen caka masa wannan mashi.
Maimakon sarki Samudul Ansari ya bari wannan koren fai-fai ya iso inda yake, kawai shima ya kaiwa iska sara da Saif-Al-Barzaƙ.
Wani bishiya jajawur ta tsiro daga cikin kasa ta tsaya a gaban wannan koren fai-fai.
Faifan yazo da gudu ya doketa, nan take tartsatsin wuta da koren hayaƙi ya cika wannan waje.
Babu abinda idanu zasu kalla idan ba wannan koren hayaƙi da wuta ba, babu sautin da kunnuwa zasu ji idan ba hargagi da ƙara tamkar fashewar nakiya ba.
A cikin wannan hali ne, sarki Samudul Ansari ya kalli sheƙin wannan jan mashi dake hannun sarki Jiz'Ban na tunkaro shi.
Saurin da gudun wannan mashi yafi ƙarfin ya kauce masa, saboda abinda ya rage mashin ya soke shi a wannan lokaci ɗan kaɗan ne.
Saboda wannan dalili babu yadda za'ayi sarki Samudul Ansari ya kaucewa wannan mashi, ko ya zaiyi sai ya soke shi.
Cikin tsananin farin ciki sarki Jiz'Ban ya ƙara ƙarfin gudun wannan mashi nasa, saboda yasan dole sai ya caki Samudul Ansari.
Samudul Ansari ya rufe idanunsa yana jira yaji wannan mashi ya huda shi, shima sarki Jiz'Ban ya rufe da idanunsa saboda yana da yaƙini mashin ya huda Samudul Ansari.
Jim kaɗan dukkansu suka ji ƙarar mashin ya huda jikin mutum.
Cikin tsananin farin ciki sarki Jiz'Ban ya buɗe idanunsa domin ganin yadda mashin ya huda Samudul Ansari.
Shima sarki Samudul Ansari cikin tsananin mamaki ya buɗe idanunsa domin ganin wanda wannan mashi ya huda, saboda yana da tabbaci ɗari bisa ɗari, ba jikinsa wannan mashi ya caka ba.
Dukkansu suka yi arba da kyakkyawar budurwa fara kamar mudubi tsaye a tsakanin Samudul Ansari da wannan mashi.
Ga wannan jan mashi soke a gefen ƙirjinta na dama.
Jikin sarki Samudul Ansari ya soma karkarwa saboda tsananin razana, fuskarsa ta fara gatsinewa saboda tsananin fusata, kansa ya fara sarawa yana kallon duhu-duhu saboda wadda ya gani ta ceci rayuwarsa.
Ba wata bace illa matarsa jaruma Zarifa.
Saboda ƙarfin dafin wannan mashi, tuni jikinta ya soma juyewa izuwa kore-kore kamar waɗannan mutane waɗanda wannan annoba ta kashe a baya.
Idanuwan Zarifa suka rufe, jikinta ya daina motsawa, ta taho a hankali ta jingina da jikin Samudul Ansari.
Samudul Ansari ya kwantar da ita a hankali, sannan ya fara dudduba ta ko tana da sauran numfashi amma babu.
Sarki Jiz'Ban ya bushe da dariya ya kaɗa hannunsa guda, take wannan jan mashi ya fito daga ƙirjin Zarifa ya dawo kan hannunsa.
Fitar mashin daga jikinta yasa ta ja dogon numfashi sannan ta buɗe idanunta ta kalli Samudul Ansari.
Wani murmushin ƙarfin hali yazo kan fuskarta, ta dubi Samudul Ansari ta ce.
"Zan kasance mai tsananin farin ciki, idan na mutu akan hannayenka, mijina.
"Ruhina zai yi barci cikin aminci a kabarina, saboda na bayar da rayuwata na kuɓutar da taka daga hallaka.
"Tabbas ba zan mutu koda da baƙin ciki guda ba, saboda nayi kyakkyawar ƙarshe a hannun mijina.
"Ka yaƙi Gauhan da ahalinsa, saboda shi ne wanda ya cutar da rayuwata fiye da komai. Wannan ita ce wasiyyata a gareka, kayi rayuwar farin ciki kai da Arya!!!"
Zarifa tana zuwa nan a zancenta idanuwanta suka kafe akan fuskar Samudul Ansari suka daina motsawa, jikinta gaba ɗaya yayi sanyi.
Wannan ya tabbatarwa da Samudul Ansari, matarsa Zarifa ta riga mu gidan gaskiya.
Dafin wannan jan mashi yayi ajalinta, ta rasa rayuwarta a dalilin ceton nasa.
Duk faɗin duniya, babu wanda za'a cakawa wannan jan mashi bai mutu ba, saboda daga dafin macijiya Ziyazilu aka samar dashi.
Ko ita kanta sarauniya Yilan aka cakawa wannan mashi sai ta mutu.
Saboda wannan dalili yasa sarki Jiz'Ban yayi ta baƙin ciki da bai samu nasarar cakawa Samudul Ansari wannan mashi ba.
Samudul Ansari ya rungume gawar matarsa, jikinsa ya ci gaba da tsuma, ya gagara miƙewa koda tsaye balle ya afkawa sarki Jiz'Ban.
Zuciyarsa a wannan lokaci ta gama karaya.
Sarki Jiz'Ban na ganin haka yayi murmushin jin daɗi, ya ɗaga wannan jan mashi ya jefowa Samudul Ansari da ƙarfi.
Mashin ya taho da azababben gudu tamkar walƙiya ya tunkaro Samudul Ansari zai tsire shi.
Tau'rin ya dakawa Samudul Ansari tsawa.
"Kai sarki ne, an san sarakuna da manyan zuƙata, duk abinda ya faru da masoyanka dama can an riga an rubuta.
"Kayi haƙuri da duk halin da rayuwa tazo maka da ita.
"Kai sarki ne, ba'a san sarakuna da karayar zuciya ba, a kullum zuƙatansu a ƙarfafe suke.
"Ka tashi ka yaƙi wannan abokin gaba naka, wanda yake so ya sanyawa zuciyarka rauni..."
Samudul Ansari yana gama jin abinda tau'rin ya ce ya miƙe tsaye a fusace.
Miƙewarsa tsaye tayi daidai da zuwan wannan mashi wanda ƙiris ya hana ya tsire shi.
Cikin kwanciyar hankali da nutsuwa Samudul Ansari ya kaucewa mashin a hankali, mashin ya wuce da gudu.
Sarki Jiz'Ban ya cika da tsananin mamaki domin kuwa a tarihin wannan mashi, ba'a taɓa kai hari dashi bai sami nasara ba.
Da farko ya kaiwa sarki Samudul Ansari hari, matarsa Zarifa ta shiga tsakani ta tare harin wanda yayi sanadin ajalinta.
A yanzu kuma, Samudul Ansari ya kaucewa wannan hari cikin kwanciyar hankali, kai kace gama-garin mashi aka aiko masa.
Samudul Ansari ya sake fiddo Saif-Al-Barzaƙ ya tunkari Jiz'Ban.
Saif-Al-Barzaƙ tana sauyawa izuwa sinadaran wannan takobi kala shida: Sinadarin Jeeish [ƙarfen dutse], sinadarin iska, narkakkiyar dalma, ƙanƙara, jini da kuma ruwa.
Kafun Samudul Ansari ya riski Jiz'Ban Saif-Al-Barzaƙ ta sassauya kamar sau arba'in da takwas.
Sarki Jiz'Ban ya ɗaga hannunsa sama, wannan jan mashi dake yawo a sararin samaniya ya dawo da gudu ya dira akan hannun.
Samudul Ansari yana isowa ya kaiwa sarki Jiz'Ban wawan sara da takobin Saif-Al-Barzaƙ, a wannan lokaci takobin ta juye izuwa Jeeish [sinadarin dutse]
Jiz'Ban yasa wannan mashi ya kare saran, Saif-Al-Barzaƙ ba tai wa wannan jan mashi dake hannunsa komai ba, amma saboda ƙarfin saran da kuma nauyin takobin saida ya durƙusa kan gwiwowinsa.
Sarki Samudul Ansari ya janye takobinsa daga jikin jan mashin JizBan sannan ya sake kai masa wani saran.
Takobin ta sake juyewa izuwa ƙanƙara, a wannan karon ma, Jiz'Ban ya sake amfani da wannan mashi ya kare kansa.
Ƙanƙarar ma ba tai wa wannan mashi nasa komai ba, amma wani irin azababben sanyi ya fice daga takobin ya doki ƙirjinsa.
Ƙasusuwan ƙirjinsa, zuciya da huhu suka daskare suka daina aiki, hakan ne yasa sarkin ya fita a hayyacinsa.
Samudul Ansari ya juyar da Saif-Al-Barzaƙ izuwa iska sannan ya sari kan sarki Jiz'Ban da ita.
Wannan shi ne karo na farko da sarki Samudul Ansari yayi amfani da sinadarin iska dake cikin Saif-Al-Barzaƙ.
Macizan dake kan sarki Jiz'Ban suna ta ihu suka fara tsalle suna barin kan nasa, ba wai don suna so bane, sai domin wata gagarumar iska dake fitowa daga cikin kan tana jifa dasu.
A daidai lokacin ne, ƙanƙarar da ta riƙewa sarkin ƙirji ta narke, ya farfaɗo.
Maimakon yayi farin ciki da wannan farfaɗowa da yayi, kwarara uban ihu ya fara, saboda sinadarin iska dake cikin kansa.
Kowanne ƙofa ta jikinsa iska ce ke fita, saboda haka bai san sa'adda ya sake fita a hayyacinsa ba.
Samudul Ansari ya juya izuwa inda gawar Zarifa ke kwance, ya ganta kwance bata motsi.
Zuciyarsa ta ci gaba da tafarfasa ya ɗaga takobi zai sare kan Jiz'Ban amma ya fasa.
Gani yake idan ya yiwa Jiz'Ban kisan farat ɗaya ba zai huce takaicin da sarkin ya ƙunsa masa ba.
Ya sake juyar da takobin izuwa ta dalma ya cakawa Jiz'Ban a tsakiyar kai, ƙofofin jikin Jiz'Ban dake fitar da iska a wannan lokaci suka fara fitar da tafasashshiyar dalma wadda tana fitowa tana ƙone masa fata.
A wannan lokaci saboda tsananin azaba, sarki Jiz'Ban gagara yin ihu yayi. Saboda dalma ce ke zubowa daga idanun nasa, bakinsa da hancinsa.
Sarki Jiz'Ban ya durƙushe a gaban Samudul Ansari, saboda tsananin azabar dake ratsa shi ba zai iya tsayawa akan ƙafafunsa ba.
"Duk wanda ya kashe min ahali, hukuncin kisa ne akansa!!!" inji Samudul Ansari. Muryarsa na fita da kaushi da iko irin na sarakunan farko.
Ya rintse idanunsa sannan ya fille kan sarki Jiz'Ban.
Baƙin hayaƙi ya ɓulɓulo daga takobin, ya kama wuyan sarki Jiz'Ban ya tsinke shi sannan yayi jifa da kansa gefe guda.
Samudul Ansari ya mayar da takobinsa cikin kufe, ya kwarara uban ihu ya dubi inda gawar Zarifa ke kwance, ya ruga da gudu inda take ya rungume ta.
Zarifa ita ce budurwa ta farko da Samudul Ansari ya fara ƙauna a rayuwarsa, na daga cikin dalilan da suka sa ta shiga ransa sosai, saboda ya tabbatar da gaske take ƙaunarsa.
Dukda cewa Arya tafi Zarifa a komai, hakan bai sa Samudul Ansari ya ƙaunaceta fiye da Zarifa ba.
Saboda wannan dalili Zarifa ita ce gimbiya a zuciyar Samudul Ansari, rashinta zai taɓa wani bangare na rayuwarsa.
*****
Yau *01/04/2023*
Babi na gaba zaizo *03/04/2023* da yaddar ALLAH.
RUHIN JARUMTAKA!
*
Babi na 106: *Baba da mama*
*
***TARIHIN SAMUDUL ANSARI***
*
Wannan littafin sadaukarwa ne ga Zahra...
*
UMS
*
Samudul Ansari ya ci gaba da rungume gawar matarsa Zarifa a ƙirjinsa, yana jimami da alhinin rabuwa da ita.
Tsahon daƙiƙu kafun ya fara jiwo manyan takun sawaye na tahowa ta bayansa. Jin sautin takun da yadda suke tahowa ya tabbatar masa da wane ne tafe.
Jim kaɗan, aljani Djinn ya ƙaraso wannan waje, jikinsa a sanyaye yana tafiya kamar baya so.
Djinn yana ƙarasowa gaban Samudul Ansari ya durƙusa kan gwiwowinsa sannan ya rufe idanunsa ya ce, "Zartar min da hukunci, ya shugabana. Duk abinda faru da matarka laifina ne, ni ne na ƙyaleta ta dawo filin yaƙin nan..."
A fusace Samudul Ansari ya miƙe tsaye zai sare kan aljani Djinn, amma a daidai lokacin ɓoyayyen hadimi ya bayyana.
Ɓoyayyen hadimi ya sake tunatar da Samudul Ansari maganar da ya faɗa masa ta farko, wadda babu wanda yasan abinda suka tattauna face su.
Samudul Ansari ya mayar da takobinsa cikin kufe, ya nunawa aljani Djinn kan sarki Jiz'Ban ya ce, "Ɗauki kan wannan sarkin, ka kaishi tsakiyar daular Gorgon ka jefar..."
Djinn ya risina ya ce, "An gama, ya shugabana."
Ya ruga ya ɗauko kan sarki Jiz'Ban sannan ya faɗa cikin wani ƙaton teku, ya ɓallo dutse mai fai-fai daga jikin wani tsauni yayi amfani dashi a matsayin kwale-kwale ya nausa a cikin wannan teku.
Samudul Ansari ya samar da wannan baƙin hayaƙi sannan ya shige cikinsa, ya fito tare da akwatin ƙarfe da kuma farin likkafani.
Samudul Ansari ya nannaɗe gawar Zarifa a cikin wannan likkafani, sannan ya saka ta a cikin wannan akwati.
Ya doki ƙasa da sawunsa guda, waɗannan baƙaƙen dawakai guda biyu da Ƙaizadu ya basu, suka ratso ƙasa suka fito.
Samudul Ansari ya ɗaura wannan akwati akan doki guda, sannan ya haye ɗaya ya kaɗa linzamin dawakan ya tunkari hanyar komawa gida.
Sai da ya shafe kwanaki uku cir! yana gudu a cikin dazuzzuka sannan ya iso bakin wannan ƙaton kogi wanda zai shafe watanni bakwai yana tafiya a cikinsa.
A bakin wannan kogi ne, Samudul Ansari yaja linzamin dokinsa ya tsaya cak! ya ƙurawa ruwan kogin idanu yana tunani.
Shin ya binne Zarifa a gaɓar wannan kogi ne ko kuma ya shiga cikin kogin da ita?
Wannan ita ce amsar da ya rasa.
Matsalar kogi shi ne babu ruwansa da ƙarfinka da ƙarfin ikonka, ko kai waye zai samu nasara akanka.
Kada ya shiga cikin wannan kogi da ita, raƙuman ruwa su ƙi bashi haɗin kai jirgin ta kife ya rasa gawar gaba ɗaya.
Da wannan shawara yayi amfani, ya sauƙo daga kan dokinsa, sannan ya sauƙo da wannan akwati wadda gawar Zarifa ke kwance a cikinta.
Samudul Ansari ya haƙa kabari madaidaici sannan ya fiddo gawar Zarifa daga cikin wannan akwati, ya buɗe daidai fuskarta ya yi mata kallon bankwana na ƙarshe sannan ya mayar ya rufe.
Samudul Ansari ya ɗaga gawar ya saka cikin wannan kabari, idanuwansa cike da kwallah ya tura ƙasa ya

Please Login or Register in order to submit comment