Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

hannayensu.
Kai babu yadda za'ayi mutum yayi arba da waɗannan mayaƙa bai razana ba, saboda tsananin kwarjininsu da kuma yawansu.
Wani garjejen aljani wanda yafi sauran kwarjini da ban tsoro na tsaye a gaban wannan runduna yana ta sharara uban gudu.
Wani sadauki guda ɗaya jal na zaune akan wannan aljani wanda ko'ina a jikinsa a rufe yake da sulke, hatta kansa a rufe yake a cikin hular yaƙi.
Babu yadda za'a yi ka gane wannan runduna ta wane ne face ka ƙarewa yanayin dakarun kallo.
Gaɓɓan jikinsu irin na mutane ne amma kansu kamar na dodanni haka yake. Idan mutum ya san bayanan UMKAS zai gane cewa su wane ba wasu ba.
Idan kuwa UMKAS ne, to wannan sadauki mai rufaffen jiki dake zaune a gabansu. Ba wani bane illa sarki Kuffuru mai mulkin daular Nehiya.
Ko ina sarki Kuffuru da mayaƙansa suka tunkara?
Bayan dogon lokaci waɗannan aljanu suna ta shawaƙi a sararin samaniya, suka iso saman wata ƙatoton birni a cikin wata daula dabam.
Suna zuwa wannan waje suka tsaitsaya a sararin samaniya, suna kaɗa fuka-fukinsu.
Sarki Kuffuru ya miƙe tsaye a saman wannan aljani ya dubi waɗannan mayaƙa ya ce, "Wannan birni da zamu farmaka sunansa KUBWAN. Yana ɗaya daga cikin manyan biranen wannan daula ta Gorgon.
"Umarni na shi ne, a kashe komai dake rayuwa a wannan birni. Babu batun mutane ko kuma dabbobi hatta gine-gine na wannan daula bana so a ƙyale su. Komai a tarwatsa. Idan ISARBIL ya bayyana kada ɗayanku yayi tunanin tunkararsa."
Sarki Kuffuru yana gama faɗin waɗannan kalamai ya zaro wata zabgegiyar takobi daga gadon bayansa ya kwarara uban ihu. Waɗannan mayaƙa dake bayansa suka amsa masa.
Sarki Kuffuru ya yiwa waɗannan dakaru inkiya da hannunsa guda, sannan ya daka tsalle daga kan wannan aljani da yake zaune akansa ya tsirgo ƙasa.
Waɗannan dakaru nasa suna ganin wannan inkiya su ma suka yi kamar yadda yayi.
Sarki Kuffuru tare da dakarunsa guda dubu ɗaya suka taho ƙasa daga sararin samaniya, tamkar tsuntsaye na sauƙowa ƙasa.
Lafiya ƙalau suka dirƙa a tsakiyar wannan birni mai suna Kubwan.
Sarki Kuffuru ya raba wannan runduna tasa kaso huɗu, sannan ya rarraba su. Wasu suka nufi gabas, wasu arewa, wasu kudu, wasu kuma yamma.
Shi kuma ya tunkari tsakiyar wannan gari.
Kafun jama'ar wannan gari su ankara da zuwan su sarki Kuffuru, tuni dakarun sarki Kuffuru sun fara yi musu mummunar ɓarna.
Waɗannan dakaru na UMKAS basu da imani ko kaɗan, duk wanda suka tarar a cikin wannan gari ko kuma cikin gida sai sunyi masa mugun kisa na wulaƙanci.
Kafun a jima jini ya fara kwarara a cikin wannan gari sannan hayaƙi da wuta ya fara tashi a unguwa-unguwa.
Dakarun sarki Kuffuru na cikin cin karensu ba babbaka kenan, suka jiwo ƙarar busa wani ƙaho.
Ƙarar wannan ƙaho na cika wannan birni, takun sawayen dakaru ya soma yawaita.
Kafun kace kobo, tuni ma'abota Bankai kimanin guda dubu ɗaya sun fito daga cikin sansanin wannan gari sannan sun falfalo cikin garin sun afkawa mayaƙan sarki Kuffuru an fara ɗauki ba daɗi.
Nan take aka kacame da azababben yaƙi tsakanin dakarun sarki Kuffuru da kuma ma'abota Bankai.
Ma'abota Bankai dake wannan gari, gawurtattun mayaƙa ne waɗanda aka baiwa horo mai kyau.
Ana fara wannan gumurzu tsakanin su da dakarun sarki Kuffuru suka fara karkashe dakarun sarki Kuffuru cikin sauƙi.
Kafun a ɗauki lokaci mai tsaho sun fara cin lagon dakarun sarki Kuffuru.
Kasancewar wannan yaƙi a gidansu ake yi, sannan suna riƙe maɗaukakan Bankai masu manyan matakai yasa cikin sauƙi suka yi ta gididdibar dakarun sarki Kuffuru.
Cikin ƙanƙanin lokaci waɗannan ma'abota Bankai suka gama da dukkanin dakarun sarki Kuffuru, ya rage cewa, saura shi Kuffurun kaɗai.
A wannan lokaci sarki Kuffuru yana cikin unguwar da tafi kowacce tarin jama'a a garin, yana ta karkashe jama'a son ransa.
Waɗannan ma'abota Bankai suka haɗu a wata babbar mahaɗa, sannan suka tunkari wannan unguwa da sarki Kuffuru keta ɓarna a cikinta.
Idan muka yi duba izuwa ɓangaren sarki Kuffuru kuwa, zamu ganshi tsaye a tsakiyar wata unguwa riƙe da zabgegiyar takobi mai zanen ɗigo-ɗigon jini akan ƙarfenta.
A duk lokacin da sarki Kuffuru yayi duba izuwa ɓangaren da jama'a suke, sai ya kai sara da wannan takobi dake hannunsa.
A take ɗigo-ɗigon jini zasu fice daga cikin takobin, sannan sun tunkari waɗanda ya kaiwa harin.
Suna isowa gabansu zasu juye izuwa takubba sannan su datse musu kai.
Wannan shi ne babban hari daga cikin hare-haren da su sarki Kuffuru suka taho dasu a yayin wannan farmaki.
Zaka iya cewa, wannan unguwa tafi ko'ina jikkata a cikin garin Kubwan saboda tuni jini ya gama yin ambaliya a cikinta, gawarwaki sun cika ko'ina.
Ma'abota Bankai suna ƙarasowa wannan unguwa, suka ruga wajen da sarki Kuffuru yake suka kewaye shi.
Mutum goma daga cikinsu suka ɗaga takubbansu, suka aikawa sarki Kuffuru harin Bankai-mai-tafiya.
Fai-fai guda goma suka fice daga tsinin waɗannan takubba suka tunkari sarki Kuffuru da gudu zasu gididdiba shi.
Cikin kwanciyar hankali Kuffuru ya ɗaga wannan takobi dake hannunsa ya sari iska da ita.
Ɗigo-ɗigon jini masu yawan gaske, suka fice daga cikinta suka fara yawo akan iska.
"Harin Siwod-del-bulod mai amfani da nau'in jini. Nan da cikar daƙiƙu goma kacal! Waɗannan ɗigo-ɗigon jini zasu ɗauki nau'ikan jininku.
"Ku gaishe da Yilan idan kuka je lahira..."
Sarki Kuffuru yana gama faɗin haka, waɗannan ɗigo-ɗigon jini suka fara ɗaukar nau'ikan jinin waɗannan mayaƙa dake tsaitsaye a gabansa.
Cikin kwanciyar hankali Kuffuru ya kaucewa waɗannan hare-hare nasu na Bankai-mai-tafiya.
Waɗannan dakaru suka buɗe bakunansu cikin tsananin al'ajabi.
Sai dai mamakin dake kan fuskokinsu bai gushe ba, takubba suka fara bayyana akan iska suna hallaka su.
Kan ka ce me wannan, tuni an kashe su gaba ɗaya.
Sarki Kuffuru yayi murmushi ya ci gaba daga inda tsaya.
A wannan lokaci ba wai iya kashe jama'a yake ba, harda bankawa gidajensu wuta.
Cikin rabin sa'a kacal! ya ƙone wannan unguwa gaba ɗayanta.
***
A daidai wannan lokaci da sarki Kuffuru yake ƙoƙarin ƙone birnin Kubwan, acan wani waje a daular Gorgon kuwa, wata ƙatuwar tukunya ce keta zaɓalɓala.
Tsahon daƙiƙu masu ɗan yawa tana ta zaɓalɓala kafun ta tarwatse tayi filla-filla. Abinda ke dahuwa a cikinta ya zubo ƙasa.
Abin mamaki waɗansu irin korayen sinadarai ne masu ɗaukar hankali.
Jim kaɗan bayan zubewar waɗannan sinadarai, suka fara haɗewa a waje guda, wata ƙatuwar tauraruwa ta bayyana a sararin samaniya ta haska wajen da sinadaran suke.
Hasken tauraruwar na dira akan waɗannan sinadarai suka fara haɗuwa da juna cikin sauri.
Cikin daƙiƙu ƙalilan suka haɗu a waje guda suka bayar da siffar wani saurayi, jarumi.
Wannan tauraruwa ta yiwo ƙasa-ƙasa daidai kan wannan saurayi, ta fara haska ƙirjinsa.
Wani abu ya buɗe a ƙirjinsa ya fara zuƙar hasken wannan tauraruwa.
Saida wannan abu ya shafe sa'a saba'in da huɗu yana zuƙar hasken wannan tauraruwa sannan ya rufe.
Nan take wannan abu da ya zuƙi haske a ƙirjin wannan saurayi, ya fara raba hasken izuwa sassa da dama na jikinsa ta hanyar jijiyoyinsa da kuma jininsa.
Haske ya fara yawo a ko'ina da ina na jikinsa, tsahon sa'a uku kafun ya ɓace ɓat!
Bayan ɗan lokaci gangar jikin wannan saurayi ta fara fitar da siffarsa.
Jim kaɗan ya juye izuwa ISRABIL wanda aka fi sani da Marganu.
Wannan Marganun da ya bayyana yana da ban al'ajabi, domin ba kamar na da bane.
Idanuwansa dara-dara na tsaye cak! suna kafiya da rashin tsoro.
Jikinsa ya sake cika da ƙwanji kuma ya murɗe ainun, kallon farko za'ayi masa a gane cewa, gawurtaccen sadauki ne mai baiwar ƙarfin damtse.
An rubuta kalmar "ISRABIL" da alƙalamin haske akan ƙirjinsa.
Dukda cewa a jikinsa babu sutura amma akwai kayan yaƙi na haske da suka lulluɓe tsiraicinsa.
A wannan lokaci takobinsa ta haske, ba wai mariƙin takobin bane, wani irin farin haske mai tartsatsi na tashi a jikinta a matsayin ƙarfen takobin.
Kallon farko kawai mutum zai yiwa Marganu ya gane cewa, cikakken shiryayye ne wanda yafi ƙarfin a gama dashi.
Marganu ya shafi wannan suna dake rubuce akan ƙirjinsa, take kowanne gashi dake jikinsa ya juye izuwa na haske.
Ɗan guntun murmushi kawai yayi, ya zaro wani ruhi daga cikin jakarsa ya danna ruhin a daidai ƙirjinsa.
Wannan rubutu dake damfare akan ƙirjinsa suka juyar da ruhin izuwa haske sannan suka zuƙe shi.
Marganu yayi murmushi ya fara tafiya a cikin wannan waje.
Koda yayi kamar taku arba'in sai ga su Ileisha, Narima da Laila Gorgon sun ƙaraso wannan waje sannan sun zube a gabansa sun sake jaddada mubaya'a.
"NI NE ISRABIL!" inji Marganu cikin kakkausar murya. "An farmaki garin Kubwan, ku zo muje mu ga wanne marar kunyar ne yazo."
Yana gama faɗin haka, ya ɗaga wannan takobi dake hannunsa sama, take wani ingarman doki na haske ya bayyana.
Marganu ya haye kan wannan doki, sannan ya zabure shi da gudu.
Ileisha, Narima da Laila suka take masa baya.
A wannan rana ce, Marganu ya gama farkar da babban sirrinsa na ISRABIL.
A yanzu ya gama zamowa cikakken ISRABIL wanda daular Gorgon ta shafe zamani tana jira.
***
A can birnin Kubwan kuwa, cikin kwana guda da wuni kacal! sarki Kuffuru ya gama ƙone garin gaba ɗaya.
Dukkan jama'ar garin sarki Kuffuru ya hallaka su, abinda ya rage masa kawai shi ne, sarkin su.
Wani mayaƙin basarake mai riƙe da Bankai mataki na saba'in da ɗaya.
Sarki Kuffuru da wannan basarake suka yi ta gwabza yaƙi har tsahon wuni guda sannan Kuffuru ya samu nasarar kashe wannan basarake.
Sarki Kuffuru yayi ta mamakin mene ne dalilin rashin bayyanar Marganu tsahon wannan lokaci?
A wannan rana kawai ya yanke shawarar zuwa babban birnin daular domin acan ne kawai yake kyautata zaton zai samu Marganu.
Yana gama ayyana hakan, yayi girgiza ya tashi sama.
Bayan ɗan lokaci yana shawaƙi a sama, ya dira a tsakiyar wannan birni wanda babu wanda ya kaishi duk daular.
Dirarsa keda wuya, ya fara karo da manyan ma'abota Bankai wadanda suka fi gaban tunaninsa.
Da ƙyar da siɗin goshi yake kashe su.
Koda sarki Kuffuru yaga zasu ɓata masa lokaci, sai ya sake tashi sama ya dira a ƙofar shiga maɗaukakiyar fada ta wannan daula.
A wannan waje ne, yayi arba da BES guda biyar tsaitsaye suna jiran zuwansa.
Sarki Kuffuru ya zaro takobinsa yana shirin afka musu, su ma suka zaro nasu zasu afka masa.
Ba zato sarki Kuffuru yaji wani irin iko ya buwaye shi a wannan waje.
Cikin tsananin mamaki ya ɗaga kansa sama, take yayi arba da wata tauraruwa mai tsananin haske tana yawo a wajen.
BES da duk wani ma'aboci Bankai dake wannan waje, suna ganin wannan tauraruwa suka zube ƙasa suka yi gaisuwa.
Sarki Kuffuru na tsaye cikin mamaki da al'ajabi kenan, yaga waɗansu mutane guda huɗu sun bayyana a wannan waje.
Shi kansa baiga tahowarsu ba, saboda haka zai iya cewa, hasken wannan waje ne ya samar dasu.
Wani saurayi guda ɗaya na tsaye a gabansu bisa ingarman doki na haske, 'yan mata guda uku na tsaitsaye a bayansa.
Kallon farko Kuffuru ya yiwa wannan saurayi ya gane wane ne, saboda tsananin yadda ya san shi.
Abinda ya bashi mamaki shi ne, suturar dake jikin wannan saurayi.
Akwai hular sarauta akansa, sannan akwai gajeren wando a kunkuminsa, amma duk waɗannan abubuwa Kuffuru yasan cewa, ba daga auduga ko fata aka samar dasu ba.
Dukkansu haske suke bayarwa da kuma launin haske.
"Yau babban rana ce a wajen ISRABIL. Na taka babban matsayina sannan ga abokin gabata har gida," inji Marganu.
Sarki Kuffuru yayi dariya ya ce, "Kai yaro karyarka tasha ƙarya. Nazo wannan daula ne domin nayi maka kashedi."
Kafun sarki Kuffuru ya gama rufe bakinsa, Marganu ya fara fusata.
Take jikinsa ya fara bayar da haske, yana kashe idanu.
Marganu ya zaro takobinsa, tartsatsin haskenta ya kashewa sarki Kuffuru idanu.
"Zuwa wannan daular kaɗai, laifi ne wanda ke buƙatar hukunci balle kuma furta kalmomin banza ga ISRABIL!" inji Marganu.
Yana gama faɗin haka ya ɗaga wannan takobi dake hannusa, ya tunkaro Kuffuru gaɗan-gaɗan.
Kuffuru ya dafa ƙarfen Siwod-del-bulod, zane-zanen jikinta suka fara sheƙi suna ɗigar da jini kaɗan-kaɗan daga cikinsu.
"Yau zan nunawa duniya babban sirrin Siwod-del-bulod!" inji Kuffuru.
Marganu yana isowa gaban Kuffuru ya kawo masa wawan sara da takobin-haske.
Duk abinda wannan takobi tasa ta ratsa kafun ta riski sarki Kuffuru sai da ya juye izuwa haske sannan ya ɓace ɓat!
Sarki Kuffuru yasa Siwod-del-bulod ya kare wannan sara.
Takubban nasu guda biyu suna haɗuwa a waje guda, babban sirri irin wanda aka daɗe ba'a gani ba ya sauƙa a wannan waje.
Ƙasa tayi girgiza, iska mai ƙarfi tayi jifa da duk wani mahaluƙi dake gefensu, iya su Ileisha kawai iskar ta bari.
Takobin Marganu ta ratsa ta cikin Siwod-del-bulod sannan ta tunkari Kuffuru gadan-gadan zata sare masa wuya.
Cikin tsananin mamaki Kuffuru ya daka tsalle gefe guda.
Siwod-del-bulod ta fara ɗigar da jini ita kaɗai, dukda cewa babu abinda ta sara.
Ɗigon jini guda talatin na zubowa daga cikinta, sarki Kuffuru ya ɗaga ta sama, ya kwarara uban ihu ya nuna Marganu da ita.
"INFIRONS-DEL-BULOD" inji Kuffuru.
Yana faɗin haka, ɗigon jini guda goma da suka zube a ƙasa daidai wajen da suka ɗige ya fara fitar baƙin haske.
Bayan 'yan daƙiƙu siffofin mutane guda goma sadaukai, suka bayyana a wajen.
Dukkansu suna sanye da baƙaƙen tufafi sannan suna riƙe da takubba maɗaukaka da hannayensu biyu.
Marganu yana ganin haka yayi guntun murmushi.
Waɗannan sadaukai guda goma da sarki Kuffuru ya samar, suka kewaye Marganu a tsakiya.
"Ni ne ajalinka, yaro. Tun da sarauniya Rauziyya ta kasa, Duksum ya kasa. Mutuwarka zata kasance a hannuna ne," inji Kuffuru lokaci da ya tashi saman iska ya tsaya akan Marganu.
Kuffuru ya baiwa Infirons umarnin afkawa Marganu da yaƙi.
Nan take suka afka masa da yaƙi da waɗannan takubba na hannunsu.
Marganu ya tare su suka fara gwabzawa.
Infirons sun kasance sadaukai kuma mayaƙa jaruman gaske. An basu gagarumin horo na yaƙi.
Dukkansu suka yi ta kaiwa Marganu sara da suka cikin tsananin zafin nama, fiye da tunaninsa.
Shi kuwa ya shiga kare kansa iyakar iyawarsa.
A duk lokacin da Marganu zai kaiwa ɗayansu sara ko suka, ya kan tura sinadarin haske izuwa cikin takobinsa domin ya samu nasarar gamawa dasu.
Amma abinda ya bashi mamaki shi ne, yadda takobinsa take dira akan waɗannan sadaukai guda goma amma bata yi musu illar komai.
Sarki Kuffuru yayi dariyar mugunta ya ce, "Shin ko kasan cewa, harin ISRABIL ruhi yake farmaka ba gangar jiki ba?
"Na ziyarci gawar Rauziyya da ta Duksum, naga yadda aka tarwatsa ruhinsu. Hakan yasa nayi maka kyakkyawan shiri, yaro.
"Waɗannan sadaukai dake yaƙarka a yanzu, basu da ruhi, wannan takobi ce take sarrafa su.
"Kaga kenan, tsinannen sirrinka ba zai yi musu komai ba.
"Kaje ka yaƙi Aymanul Faris shi ne tsararka, nikam nayi maka nisa. Babu matsayin da zaka taka a duniya, ka ban tsoro.
"Bari ma ka gani," sarki Kuffuru yana gama faɗin haka ya aikawa Marganu wani ƙatoton dunƙulen jini.
Marganu baida ikon kaucewa wannan dunƙulen jini, domin yana kauce masa, Infirons zasu yi nasara akansa.
Don haka ko kallon wannan dunƙulen jini baiyi ba, har dunƙulen yazo ya kewaye shi.
"Na ɗauki samfurin jininka, yanzu saura na datse kanka!" inji sarki Kuffuru.
Marganu yayi murmushi mai nuna yarda da kai.
****
Yau *17/06/2023*
Babi na gaba zaizo *19/06/2023* da izinin ALLAH.RUHIN JARUMTAKA!
*
Babi na 140: *Shima yayi aure*
*
Wannan littafin sadaukarwa ne ga Zahra...
*
U~M~S
*
Marganu yana gama wannan murmushi ya tsaya cak! A wannan lokaci, hare-haren Infirons na shirin dira a jikinsa, sannan ɗigon jinin da ya ɗauki nau'in jininsa na tunkaro shi zai hallaka shi.
A wannan lokaci tazarar dake tsakanin rayuwar Marganu da mutuwarsa, 'yar kaɗan ce.
Sai dai kafun waɗannan hare-hare su dira a jikin Marganu ya zaro wata takarda mai ɗauke da zanen taswirar wani daji mai yawan duwatsu ya cillata sama.
Taswirar ta tashi sama sannan ta juye izuwa haske, ta zubo ƙasa a wannan waje.
Nan take wannan waje da suke ya fara juyewa izuwa haske, kafun daga bisani ya ɓace ɓat!
Tafkeken daji mai yawan tsaunika ya maye gurbinsa.
A taƙaice dai, Marganu yayi amfani da ɗalasimin-taswira wanda duk duniya Barzas kaɗai ne keda irinsa.
Sa'adda Marganu ke daf da kashe Barzas mun ga yadda ya caka hannunsa a ƙirjin aljanin, ya fiddo dunƙulen wani abu.
To, wannan abu da Marganu ya fiddo shi ne, ɗalasimin-taswira wanda wannan aljani ke taƙama dashi.
A yanzu Marganu zai iya sarrafa wannan ɗalasimi, kamar yadda yayi amfani dashi a yanzu, ya sauyawa Kuffuru muhalli.
Marganu ya dubi Kuffuru ya ce, "Marganun da ka sani na da ne. A yanzu ISRABIL ne!"
Dukda cewa sarki Kuffuru ya cika da tsananin mamaki, amma a hakan ya falfalo da azababben gudu kan Marganu cikin tsananin fusata.
Yana isowa gaban Marganu ya kawo masa wawan sara da Siwod-del-bulod.
Marganu ya zaro wata takobi dabam wadda bata kasance ta haske ko kuma tarwatsa-komai ba amma akwai zanen taswira akan ƙarfenta.
A waje guda kawai muka taɓa ganin wannan takobi, sa'adda Barzas yake fafatawa da Marganu da kalarta yayi amfani.
Marganu ya juya wannan takobi dake hannunsa.
Nan take wannan daji gaba ɗaya ya juya, sarki Kuffuru ya bashi baya kamar yadda ta faru dashi sa'adda yake fafatawa da Barzas.
Marganu ya sa wannan takobi ya danƙarawa Kuffuru sara a gadon baya.
Wani lafcecen yanka ya bayyana a gadon bayan sarki Kuffuru, jini ya fara tsiyayowa.
Sarki Kuffuru bai san sa'adda ya kwarara uban ihu ya daka tsalle gefe guda ba.
Marganu yayi dariyar mugunta ya ce, "Tun da ka kawo kanka ƙasata, sai na sare kanka..."
Sarki Kuffuru yana jin haka ya fusata, matuƙar fusata.
Ya nuna Marganu da Siwod-del-bulod ya ce, "INFIRONS-DEL-BULOD."
Nan take Infirons guda goma suka bayyana a wannan daji, sannan suka afkawa Marganu da mummunan yaƙi.
Sai dai kamar yadda ya yaƙi maigidansu su ma haka ya ɗinga yaƙar su.
Da zarar sun kawo sara ko suka sai yayi amfani da takobin hannunsa, ya juya wannan daji, su bashi baya ya sare su.
Wannan takobi dake hannun Marganu ba mai farmakar ruhi ba ce, asalin takobi ce wadda zata iya yaƙar kowa.
A duk sa'adda ya sari Infirons sai su haɗe fuska alamar sun ji tsananin zogi.
Sarki Kuffuru na ganin haka hankalinsa yayi mummunar tashi, ya tabbatar da cewa, Infirons kaɗai ba zasu iya yaƙar Marganu ba.
Cikin gaggawa ya mayar da Siwod-del-bulod cikin kufe, take dukkansu suka ɓace ɓat!
Sarki Kuffuru ya zaro LESIM sannan ya rugo da gudu kan Marganu.
Take suka sake buɗe wani sabon gumurzu a tsakaninsu.
Suka sake wanzuwa suna kaiwa junansu sara da suka cikin zafin nama na gaban kwatance.
A wannan lokaci Marganu baiyi amfani da wannan takobi ya sauyawa Kuffuru muhalli ba, zagewa kawai yayi suka yi ta yaƙar juna gaba-da-gaba.
Sarki Kuffuru ya cika da tsananin mamaki saboda ganin tsananin horon yaƙin da Marganu yake da.
Kuffuru ya kasance tsohon mayaƙi wanda ya halarci yaƙoƙi da dama a rayuwarsa, a wannan zamani mutum zai iya cewa, kowanne irin horon yaƙi Kuffuru ya san da shi.
Don haka yayi ta ɓullowa Marganu da salon yaƙi kala daban-daban.
Bisa mamaki sai yaga duk wani salon yaƙi da ya ɓullowa Marganu dashi, Marganu ya ƙware ainun akansa.
Lamarin da ya fusata shi kenan, ya daka tsalle gefe guda.
Idan zasu ci gaba da gumurzu a haka, zasu iya shekara arba'in basu sami nasarar komai ba, saboda iya yaƙinsu yazo ɗaya.
Sarki Kuffuru ya nuna Marganu da takobinsa ya ce, "Kai yaro! Yau ce ranar mutuwarka!"
"ISRABIL BA ZAI MUTU BA, FACE YA MULKI DAULOLI GUDA HUƊU..." abin mamaki ba Marganu ne yayi wannan magana ba, sirrin dake cikin ƙirjinsa ne yayi.
Sarki Kuffuru ya sake falfalowa da azababben gudu kan Marganu, yana gudun yana ɗaga takobin dake hannunsa sama.
Saura taku uku ya iso gaban Marganu ya daka tsalle sama ya kawowa Marganu wawan sara a wuya.
Marganu yayi murmushi ya juya wannan takobi dake hannunsa, take wannan daji ya juya Kuffuru ya bashi baya.
A wannan lokaci sai da Marganu ya taƙarƙare ya yiwa sarki Kuffuru wawan sara a kafaɗa, saboda zurfin saran da kuma ƙarfinsa hatta jijiyoyin hannun sarki Kuffuru saida suka tsinke.
Lamarin da yasa ya gagara motsa wannan hannu kenan.
Marganu ya sake ɗaga wannan takobi ya sari Kuffuru a wuya da nufin ya fille masa kai, amma cikin zafin nama Kuffuru ya kauce.
Takobin Marganu ta ɗan kuskuri wuyansa.
Gadon bayan Kuffuru da wuyansa suka fara zubar da jini, ya durƙushe a gaban Marganu.
Marganu ya ɗaga takobinsa zai fillewa Kuffuru wuya.
A daidai lokacin ɗigo-ɗigon jini masu yawan gaske suka bayyana daidai wuyan Marganu, kafun ya ƙarasa sare kan sarki Kuffuru.
Tuni sun haɗe da juna sun bayar da igiya wadda ta kanannaɗe wuyan Marganu, ta shaƙe da ƙarfi.
Marganu yasa hannayensa ya fara ƙoƙarin tsinke igiyar amma kamar ƙara tamketa yake.
Nan fa wannan igiya ta fara wahalar da Marganu.
Cikin ƙanƙanin lokaci ya kusa fita a hayyacinsa.
Sarki Kuffuru ya miƙe tsaye yana layi kamar zai faɗi ya ce, "Mutuwar Kuffuru sai dubu ta taru!"
Yana gama faɗin haka ya doki ƙasa da sahunsa guda, nan take irin wannan guguwa dake bayyana a duk sa'adda Infiron ya kira ɗalasimin sa ta bayyana a wannan waje.
Wannan guguwa ta kanannaɗe sarki Kuffuru sannan tayi jifa dashi sararin samaniya.
Tun Marganu yana hango shi, har sai ya ƙule a sararin samaniya ya ɓace ɓat!
Cikin tsananin fusata Marganu ya tsinke igiyar da ta ɗaure masa wuya, sannan ya kwarara uban ihu

Please Login or Register in order to submit comment