Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

haske, ƙatoton tauraro guda ɗaya fari ya bayyana ya haskaka wannan daula gaba ɗaya.
Kafun kace wani abu, tuni haske ya gauraye dukkan wannan daula.
ISRABIL ya bayyana.
Idan ka duba cikin wannan keken doki kuwa, zaka ga Marganu da Firziyya suna zaune a cikinsa.
Ileisha, Narima da Laila suna zaune a gabansu Marganu tamkar masu tsaronsu.
Marganu da Firziyya sai leƙa wannan daula suke ta cikin tagar wannan keken doki.
Marganu yana shigowa wannan daula wannan abu dake gefen ƙirjin ya fara haske irin wanda bai taɓa yi ba, domin a wannan lokaci dukda cewa akwai riga a jikinsa amma hasken abun ya ratsa rigar.
Abinda Firziyya ta lura dashi shi ne, su Ileisha suna yawan satar kallon wannan abu sannan suna yiwa abun jinjina a zuƙatansu.
Duk wani ƙaramin ƙauye ko kuma garin da wannan keken doki ya ratsa sai dai kaga mutanen cikinsa suna zubewa ƙasa suna mubaya'a.
Tun sa'adda wannan tauraruwa mai farin haske ta bayyana a sararin samaniya dukkan wani mahaluƙi dake rayuwa a wannan daula yaji babu abinda yake buƙata kamar mubaya'a ga ISRABIL.
Ƙarya ne ɗan ƙabilar Gorgon yayi arba da ikon ISRABIL bai faɗi ƙasa yayi mubaya'a ba.
Saida Marganu dasu Narima Gorgon suka shafe kwanaki bakwai suna tafiya sannan suka iso babban birnin daular inda wannan ɗakin taro yake.
Duk wani gari da suka ratsa a wannan daula saida jama'ar garin gaba ɗaya suka zube suka yiwa Marganu mubaya'a.
Tuni Marganu da Firziyya sun cika da tsananin mamaki bisa ganin girman wannan daula, saboda idan ka kwatanta da girman daular sarki Kuffuru ta da tamkar giwa da kyanwa ce.
Mutanen wannan babban birni suka jeru a sahu-sahu layi-layi suna yiwa Marganu barka da zuwa.
Tun da Marganu yake a rayuwarsa bai taɓa zuwa wajen da aka girmama shi kamar wannan waje ba. Kowa a wajen farin ciki yake da zuwansa.
Bayan ɗan gajeren lokaci suka iso wannan babban ɗakin taro na wannan daula inda wadannan sarakuna guda tamanin da takwas suke jiran zuwan Marganu.
Matuƙin da ke tuƙa wannan keken doki ya ja linzamin dawakan suka tsaya, cikin gaggawa ya sauƙo daga kan keken dokin yazo daidai ƙofar keken dokin ya tsaya, ya fiddo wani abu mai kama da matattakala wanda sarakuna suke amfani dashi idan zasu sauƙo daga keken doki.
Mutumin ya ajiye wannan abu a gaban keken dokin.
Jim kaɗan Marganu ya tako daga cikin keken dokin ya fito waje, gimbiya Firziyya ta take masa baya.
Daga nan kuma sai su Ileisha Gorgon suka fito.
Sawun Marganu yana taka ƙasa, wata babbar tuta dake saman wannan ɗakin taro ta fara haske da walwali.
Sarakunan dake zazzaune a cikin wannan ɗakin taro suka miƙe tsaye dukkansu.
Ileisha, Narima da Laila suka shiga gaban Marganu suka yi masa jagoranci izuwa cikin wannan ɗakin taro.
Marganu ya kama hannun Firziyya ya take musu baya.
Suna shigowa cikin wannan ɗakin taro dukkan sarakunan dake ciki suka sunkuyar da kawunansu ƙasa.
Ƙirjin Marganu ya ci gaba da bayar da haske, ikonsa ya yi musu sallama.
Nan take dukkansu suka zube ƙasa suka yi mubaya'a.
Marganu ya fara kallonsu ɗaya bayan ɗaya har zuwa kan na ƙarshen su. Lokacin da suka je gaban wannan karagar mulki suka tsaya.
Ileisha, Narima da Laila suka haɗa tafukan hannayensu a waje guda suka furta wani babban ɗalasimi.
Faruwar hakan keda wuya, wata hular sarauta ta haske ta bayyana akan tafukan hannayen nasu.
Wannan hular sarauta ta haske ce, an rubuta ISRABIL da yaren wannan daula akan ƙarfenta.
Waɗannan sarakuna duk suka zube akan gwiwowinsu. Ileisha ta baiwa Marganu umarnin zama akan wannan karaga. Nan take kuwa ya zauna.
Ileisha ta baiwa Firziyya wannan hular sarauta tace ta sakawa Marganu akan kansa.
Firziyya ta miƙa hannayenta biyu ta karɓi hular. Abin mamaki hular ta haske ce amma tana da ɗan nauyi.
Firziyya ta taka a hankali tazo gaban Marganu ta saka masa wannan hula akan kansa.
Hular ta zauna daram akan Marganu tamkar dama saida aka gwada kansa aka ƙerata.
Hasken dake ƙirjin ya ƙaru ainun har yana ɗaukewa Firziyya idanu.
Wannan koren haske dake jikin wannan karaga da yake zaune akanta shima ya ƙaru ainun, ya fara kewaya jikin Marganu.
Wani iko na musamman ya sauƙa a wannan daula.
Ileisha, Narima, Laila, waɗannan sarakuna guda tamanin da takwas da duk wani mahaluƙi dake wannan daula (indai jinsin Gorgon ne) sai da suka zube ƙasa suka yi mubaya'a a gaban ISRABIL.
Tsahon daƙiƙa ɗari hudu da biyar dukkansu suna durƙushe a gaban Marganu kafun su ɗago.
"BARKA DA ZUWA, BABBAN SARKI ISRABIL!" wata murya mai kaushi ta yiwa Marganu magana.
A wannan rana Marganu ya zamo babban sarki na daular Gorgon gaba ɗaya.
Waɗannan sarakuna guda tamanin da takwas suka ɗinga zuwa ɗaya bayan ɗaya suna gabatar da kansu da kuma garuruwan da suke mulki a wajen Marganu.
Suna kammalawa suka yiwa Marganu sallama suka fice daga cikin wannan ɗakin taro.
Marganu ya dubi Ileisha ya ce, "Ina so a kawo min taswirar wannan daula gaba ɗaya da kuma rukunin tsaro da ƙarfin makaman yaƙin mu."
Ileisha ta risina a gaban Marganu ta ce, "Dukkanin waɗannan bayanai suna cikin babban ɗakin karatu da bincike na wannan daula wanda kakanmu Jiz'Ban ya bari, ya ISRABIL!"
Marganu yayi murmushi ya ce, "Ina buƙatar sanin waɗannan abubuwa kafun a tsuma a cikin tsumi na musamman!"
Ileisha ta ce, "Ka shirya mu tafi wannan dakin bincike da Jiz'Ban ya bari yanzu."
Marganu ya gyaɗa mata kai ya shirya.
Nan take ita, Marganu da Firziyya suka sake shiga cikin wannan keken doki suka tunkari bayan gari inda gidan sarki Jiz'Ban yake.
A wannan lokaci basu tafi dasu Laila da Narima ba.
Bayan doguwar tafiya wannan keken doki ya iso gidan Jiz'Ban dake saman wani dutse.
Wannan keken doki ya tsaya a gaban gidan.
Marganu, Ileisha da Firziyya suka fito daga cikin keken dokin sannan suka shige cikin gidan.
Ileisha ta kai Marganu cikin wani babban ɗaki wanda Jiz'Ban ya saba gudanar da bincike a cikinsa.
A cikin wannan ɗaki a jikin bangwayensa akwai rubuce-rubuce bisa takardu masu yawan gaske, wasu suna magana akan ƙarfin Bankai wasu kuma Renin-Yilan, da dai waɗansun wadannan.
Idanuwan Marganu suka kai kan takarda ta farko.
Mai rubutun ya fara da cewa;
'Matakan tsaron daular Gorgon guda uku ne: Bankai, Renin-Yilan da kuma BES.
'Bankai: Iko ne da ake sarrafawa a cikin takobi wanda zai bamu nasara akan abokan gaba.
'Renin-Yilan: Iko ne da ake sarrafawa a cikin maɗaukakan idanu da yake bamu damar mayar da abokin gaba gunki.
'BES: Ruhi ne guda biyar da ake samarwa domin taimakawa babban sarki.'
Marganu na gama karanta abinda aka rubuta ya jinjina kai.
Bankai. Renin-Yilan. BES. Yana buƙatar cikakken bayani akan waɗannan abubuwa guda uku.
Idanuwan Marganu suka sake kaiwa kan takardar dake ƙasan wannar. Take yayi arba da bayani da iko akan ISRABIL.
'ISRABIL: Mutum ne wanda haske yake yawo a cikin jinin jikinsa da kuma jijiyoyinsa. Wannan mutumi shi ne aka tattauna akan al'amarinsa tun zamanin sarki Sadusa ƙarni goma da suka shuɗe dukda cewa bai bayyana ba.
'Iya sanin mu dai, matakin takobin Bankai daga ɗaya ne zuwa ɗari.
'ISRABIL zai iya samar da takobin Bankai mai mataki na ɗari biyu zuwa sama.
'Sannan a sanin mu dai, duk wani BES da aka samar yawanci daga koren-dafi ake sarrafa jikkunansu.
'ISRABIL zai iya samar da BES nasa na kansa daga sirrin haske.
'ISRABIL zai iya sarrafa ɗalasimin taswira na Barzas.'
Marganu yana karanta haka ya sake yin shuru yana tunani.
Idanuwan Marganu suka sake kaiwa kan wata takarda wadda aka rubuta, "DANGANTAKAR DAKE TSAKANIN TAU'RIN DA ARYA!"
'Tau'rin yana da ƙarfi na musamman amma ƙarfinsa ba komai bane idan babu Arya.
'Sirrin dake cikin jinin tau'rin ba zai farfaɗo ba face ya haɗu da na Arya.
'Hadimi Gauhan yaso ya hana tsinanne Samudul Ansari kusantar Arya amma baiyi nasara ba.
'Ya ku masu tasowa a bayana, za ku iya dakusar da rayuwar tau'rin idan kuka yi nasarar hana shi tarawa da Arya.'
Ya kamata a san cewa akwai sirruka da dama a wannan waje, Firziyya da Ileisha basa kallo amma Marganu yana gani albarkacin idanuwansa.
Marganu yana gama karanta abinda aka rubuta a jikin wannan takarda ya zauna akan wata kujera dake kusa ya fara tunani.
"Mene ne babban dalilin da yasa waɗannan mutane suka shafe zamani mai tsaho suna jiran bayyanata?" Marganu ya yiwa kansa tambaya.
"Saboda na kare su daga sharrin tau'rin ne!" ya baiwa kansa amsa.
A halin yazo wajen da zai farkar da babban ikonsa irin wanda duniya bata taɓa gani ba.
Tau'rin har yanzu bai sake bayyana ba, balle ya hana shi aiwatar da waɗansu abubuwa.
"Wace ce ARYA!" Marganu ya sake yiwa kansa wata tambayar.
Tsahon ɗan lokaci yana tunani. Abinda ya fara faɗo masa a rai shi ne, amsar da tsoho Aydenlik ya bayar sa'adda suke gasa a garin sarki Wadu kusa da birnin Temisa.
Idan zai iya tunawa bayan Aydenlik ya bayar da wannan amsa, ya tambaye shi bayani akan amsar.
Inda Aydenlik ya shaida masa cewa, ARYA ita ce wadda ya sayar da rayuwarsa akanta wato gimbiya Jaanu.
Kuma idan zai tuna Aydenlik ya sanar dashi cewa, musamman an halicci Jaanu ce domin Aymanul Faris wannan shiyasa bata ƙaunarsa.
Idan kuwa haka ne, ya zamo dole ya hana Aymanul Faris kusantar gimbiya Jaanu.
Tsahon daƙiƙu Marganu yana tunani kafun ya gyaɗa kai ya dubi Ileisha ya ce, "Ina buƙatar cikakken bayani akan Bankai, Renin-Yilan da BES."
Ileisha tazo gaban Marganu ta zauna akan wata kujera sannan ta fara yi masa bayani.
"Ita takobin Bankai takobi ce wadda magabatanmu suka samar. Kalmar Bankai, wani addini ne a wannan daula tamu.
"Bankai mataki-mataki ne. Akwai mataki na ɗaya zuwa na huɗu, akwai biyar zuwa goma, akwai sha-ɗaya zuwa talatin da tara.
"Akwai arba'in zuwa casa'in da tara.
"Akwai ɗari zuwa dubu.
"Mataki na ɗaya zuwa na huɗu, yana sakawa abokin gaba *dafi* a cikin jininsa idan aka sare shi da takobin.
"Mataki na biyar zuwa goma yana fitar *fai-fai* mai ɗauke da sinadarai guda biyu yayin da aka kaiwa abokin gaba sara.
"Mataki na sha-ɗaya zuwa talatin da tara, yana iya samar da *manya-manyan macizai* su afkawa abokan gaba.
"Mataki na arba'in zuwa casa'in da tara, yana baiwa mutum dama yayi amfani da abinda yafi ƙwarewa akai. Wasu walƙiya, wasu hadari, wasu ƙanƙara da dai makamantansu.
"Mataki na ɗari zuwa dubu, yana baiwa mutum dama ya kai abokin gabarsa cikin duniyar-Bankai sannan yayi amfani da ikon duniyar ya gama dashi.
"Wannan shi ne cikakken bayani akan takobin Bankai.
"Renin-Yelin: Waɗansu irin idanuwa ne masu mugun haɗari a duniya. Masana sun ce waɗannan idanuwa suna iya fitar da farin hayaƙi mai ɗauke *sinadarin Aiys*.
"Sarki AIYSMAN na duniyar ƙanƙara shi ne ya bamu kyautar *sinadarin Aiys* a wata yarjejeniya da muka ajiye.
"Amfanin sinadarin Aiys yana iya mayar da gangar jiki izuwa ƙanƙara ta daskare yadda har abada ba zata sake wani amfani ba.
"BES: Mutane guda biyar ne da ake samu a cikin wannan daula tamu, a sadaukar da jininsu ga abin-bauta.
"Idan aka sadaukar da jinin nasu hakan zai sa abin-bauta ya sake dawo mana dasu amma a babban matsayi da kuma iko wanda babu mai irinsa duk daular tamu idan ba sarkinmu ba.
"Wannan shi ne amsoshin da ka tambayeni, ya ISRABIL."
Marganu yana gama jin wannan jawabi ya gyaɗa kai. Tabbas ya samu bayanin da yake buƙata.
Ƙarfin wannan daula zai iya bashi nasara akan kowa.
Marganu ya dubeta ya ce, "Ina son na hana Aymanul Faris kusantar Arya!"
Ileisha ta ce, "Zaka iya yin hakan, idan ka san wajen da Arya take..."
Marganu ya ce, "Na san inda Arya take, sannan zamu iya zuwa wajen."
A tsorace Ileisha ta dube shi ta ce, "Hakan ba zai yiwu ba face anyi maka wannan tsumi. Saboda idan muka yi kuskuren barin wannan daula, tau'rin zai fusata ya turo tsinannen baƙin hayaƙinsa ya gama damu."
Marganu ya fusata ya ce, "Ina Aymanul Faris yake a halin yanzu?"
Ileisha ta ce, "Ance min yanzu haka yana kan hanyar zuwa inda wannan ruhi yake. ISRABIL kada ka sami damuwa, koda ya mallaki wannan ruhi dole yana buƙatar Arya.
"Za mu iya ɗauko Arya kafun ya risketa."
Marganu ya ce, "Muje a tsuma ni a cikin wannan tsumi,"
****
Yau *29/05/2023*
Babi na gaba zaizo *01/06/2023* da izinin ALLAH.
RUHIN JARUMTAKA!
*
Babi na 131: *Ruhin Babban Sarki*
*
Wannan littafin sadaukarwa ne ga Zahra.
*
U~M~S.
*
~Aymanul Faris.
*
Kai tsaye Aymanul Faris tare da jaruma Riya suka tunkari wannan daji na hudu zasu shiga cikinsa.
Suna zuwa farkon dajin wannan hatimin dake bayan wuyan Aymanul Faris ya fara haske da sheƙi, launin wuta jajawur ya bayyana akansa.
Nan take gashin kan Aymanul Faris suka fara ci da wuta, idanuwansa suka juye izuwa na wuta, suturar jikinsa ta juye izuwa baƙa ƙirim ta fara bayar da launin wuta.
Aymanul Faris ya dafa Riya da hannunsa guda take jikinta ya juye izuwa irin nasa.
Salim-alim suka wuce ta cikin wannan daji na hudu babu abinda ya same su.
Suna fitowa daga cikin wannan daji na huɗu suka hango wannan ƙatoton kogo na Madarul Ansari acan gaban su cikin wani ƙungurmin daji.
Gagarumin farin ciki ya lulluɓe Aymanul Faris da matarsa Riya, cikin gaggawa Aymanul Faris ya sake fiddo waɗannan dawakai nasu.
Dawakan suka tsala azababben gudu fiye da na farko.
Aymanul Faris da jaruma Riya sun cika da tsananin mamaki bisa ganin sun shafe kwanaki uku suna tafiya amma basu riski wannan ƙatoton kogon dutse ba.
Lamarin da yasa suka yada zango a gindin wata bishiya kenan, domin su huta.
Jaruma Riya ta yiwa Aymanul Faris shimfiɗa shi kuma ya kwanta akai.
Bayan ɗan lokaci suna tattaunawa, sai suka ga wani aljani ya sauƙo wannan waje.
Babu abinda suke iya shaidawa a jikin wannan aljani saboda komai nasa a lulluɓe yake da farin tufafi.
Babu abinda ya fara faɗowa Aymanul Faris da jaruma Riya a wannan lokaci kamar ɓoyayyen-hadimi wanda aka basu labarinsa a cikin tarihin babban sarki.
Aljanin ya ƙaraso gaban su Aymanul Faris ya tsaya.
Ba tare da ya buɗe fuskarsa ya dubi Aymanul Faris ya ce, "Ashe har ka samu damar da zaka kwanta, ka tsaya hutawa?
"Shin ba ka san cewa, sarki Kuffuru ya karɓi hular sarautar daular Nehiya ba?
"Shin ba ka san cewa, ISRABIL ya taka matsayin sa na daular Gorgon ba?
"Samun sarauta a wajen waɗannan mutane guda biyu, barazana ce ga rayuwarka da kuma matar da zaka aura a gaba, ina nufin Arya.
"Yanzu batun da nake yi maka hankalin Kuffuru da na Marganu ya soma karkata izuwa kan Arya.
"Saboda sun san cewa idan suka hana ka tarayya da ita, hakan zai hana babban sirrin dake cikin jininka bayyana.
"Wannan shi ne dalilin da yasa nazo wajen ka domin na sanar da kai wannan saƙo.
"Idan baka zage damtse kayi yaƙi yadda ya dace ba, zaka iya rasa Arya.
"Da zarar ka mallaki wannan ruhi, kada ka tsaya a ko'ina face birnin Damashkar.
"Idan kaje can ka tara da Arya ko ta hanyar aure ko kuma ta ɗaya hanyar.
"Wannan shi ne saƙona a gareka, magajin babban sarki."
Ɓoyayyen-hadimi yana gama sanar da Aymanul Faris wannan saƙo ya ɓace ɓat!
Hankalin Aymanul Faris ya ɗugunzuma, zuciyarsa ta fusata.
Ba wai kansa yake dubawa ba, ya ya duniya zata kasance idan ƙabilar Gorgon ta sake dawowa ba tare da tau'rin ba?
Tabbas ta kowanne hali ya kamata ya zage damtse ya mallaki wannan ruhi, idan ba haka kuwa, gagarumar matsala ta kusa ta afku.
Sarki Kuffuru ya zamo babban sarki. Marganu ma ya zamo babban sarki.
A halin yanzu shi kaɗai ya rage. Duk waɗannan mutane guda biyu suna da mummunan buri akansa, kuma sun san abinda dogaron nasa a yanzu, wato gimbiya Jaanu.
Aymanul Faris yayi shuru yana tunanin abinda ya kamata yayi.
Bayan ɗan lokaci ya yanke shawarar dole yana buƙatar ya tseratar da rayuwar Jaanu.
A yanzu babu halin ya koma da baya. Mutane guda biyu ne kawai zasu iya tseratar da Jaanu a yanzu: Ranganu da kuma Barban.
Koda ayyana hakan, sai Aymanul Faris ya dafa wannan hatimi dake bayan wuyansa, take aljani Nara hadiminsa ya bayyana.
Nara ya risina a gaban Aymanul Faris cikin girmamawa.
Aymanul Faris ya dube shi ya ce, "Ina so kaje ka sanar da Barban cewa, akwai buƙatar baiwa Jaanu kariya saboda zata iya fuskantar barazana daga kowanne lokaci,"
Nara yana jin wannan batu ya dubi Aymanul Faris ya ce, "Ya shugabana! Ina baƙin cikin sanar da kai cewa, sarki Kuffuru ya samu nasarar kama Barban sannan har ya kulle shi a kurkuku..."
"Meye?!" Aymanul Faris ya dakawa Nara tsawa. "Ka faɗa min gaskiya, kada ka kuskura kayi min ƙarya. Barban ɗin suka kama?"
Nara ya risina a gaban Aymanul Faris ya ce, "Rayuwata fansa ce, da nayi ma ƙarya gwamma na kashe kaina!"
Aymanul Faris yayi shuru yana tunani, "Wanne hali masoyiyata Arya take ciki a yanzu?"
Nara ya ce, "Tana cikin ƙoshin lafiya,"
Aymanul Faris ya ce, "Wai ta ya ya ma aka kama Barban, ina Ranganu yake a wannan lokaci?"
Nara ya ce, "Ya shugabana! Babu wanda ya san wani abu dangane da wannan abu da ya faru. Amma akwai abinda ya bani mamaki,"
Aymanul Faris ya ce, "Me kenan?"
Nara ya dube shi ya ce, "Yaushe kuka rabu da Barban?"
Aymanul Faris ya ce, "Bayan aurenmu da kwana guda,"
Nara yayi murmushi ya ce, "Tabbas Barban zai girgiza duniya. Saboda Barban ɗin da su sarki Kuffuru suka kama, ya daɗe a garin Jiminis yana zaune."
Aymanul Faris ya yi shuru yana tunani. Abinda ya tuno shi ne tattaunawar da suka yi da Barban a cikin fadarsa sa'adda suke tattaunawa akan sato takobin Saiful-Shiradu.
A tunaninsa da kuma abinda Barban ya faɗa masa, a cikin wannan fada dake ƙarƙashin ruwa kawai za'a iya samun Barban.
Ya ya za'ayi ace an kama shi a garin Jiminis?
Aymanul Faris ya yi guntun murmushi, lamarin Barban al'amari ne mai matuƙar rikitarwa.
Babu mai warware wannan al'amari face mai gidan Barban wato Ranganu.
Aymanul Faris ya dubi Nara ya ce, "Ina so kaje wajen sarki Ranganu, ka sanar dashi cewa, rayuwar gimbiya Jaanu tana cikin haɗari..."
Nara yana jin wannan batu ya ce, "Ya shugabana! Ina so ka sani cewa, duk wani abu dake faruwa tsakanin Kuffuru, Marganu da Ayubul-Zairiy Ranganu yana kallo. Saboda haka yasan abinda ke shirin faruwa da Jaanu."
Aymanul Faris ya ce, "Na san da haka, amma dukda haka ina so kaje ka sanar dashi wannan saƙo."
Nara ya risina ya ce, "Zan yi hakan," take ya ɓace ɓat.
Cikin tsananin mamaki Riya ta dubi Aymanul Faris ta ce, "Mijina! Suna nufin an kama maigida Barban kenan?"
Aymanul Faris ya yi guntun murmushi ya ce, "Wataƙila haka ne, wataƙila kuma ba haka bane. Barban mutum mai tsananin lissafi, koda ace da gaske an kama shi nasan wani kyakkyawan shiri yake yi akansu. Idan ba ki manta ba, har yanzu akwai ayyuka guda huɗu da suka rage."
Jaruma Riya ta gyaɗa kai.
Daga wannan lokaci Aymanul Faris da jaruma Riya suka miƙe tsaye suka ci gaba da tafiya.
Duk tsananin ƙarfin gudun waɗannan dawakai, saida suka shafe sati biyu sannan suka isa gindin tsaunin nan wanda kogon Madarul Ansari yake cikinsa.
Kamar yadda Ranganu ya sanar da su haka ƙofar wannan kogo take. Babu ƙofa amma akwai alamun ta na haske, an yiwa hasken siffar ƙwarangwal.
Aymanul Faris ya fiddo wannan makulli wanda suka ƙwato a wajen sarki Raja ya soka makullin a daidai ƙirjin wannan ƙwarangwal.
Makullin yana shiga ƙirjin ƙwarangwal ɗin, jikinsa ya fara haske. Tartsatin wuta ya fara tashi daga jikin wannan mutum-mutumi.
Saida wani haske ya dallare Aymanul Faris da jaruma Riya tsahon ɗan lokaci sannan ya ɓace ɓat!
Ga dukkan alamu jininsu aka gwada, don a tabbatar da jinin Samudul Ansari.
Wannan ƙofa mai siffar ƙwarangol ta tarwatse.
Aymanul Faris da jaruma Riya suka yi arba da wata hanya zururu ta nufi cikin wannan kogo.
Nan take suka sauƙo daga kan wannan doki nasu, suka tunkari cikin kogon.
Aymanul Faris yana riƙe da hannun jaruma Riya, hannunsa guda na hagu yana kan takobinsa.
Suna shigowa cikin wannan kogo suka cika da tsananin mamaki.
Kogo ne mai tsananin girma, faɗi da tsahon gaske. Saboda tsananin girmansa zai iya kai wani ƙaramin gari.
Aymanul Faris da Riya suka sake cika da tsananin mamaki.
Yadda suka karanta a tarihi shi ne, babu komai a cikin wannan kogon dutse, idan ba Saif-Al-Barzaƙ da tau'rin ba.
Amma a wannan lokaci ga tarin dukiya da makaman yaƙi birjik a cikin wannan kogo.
Aymanul Faris da Riya suka ɗauke idanunsu daga kan ganimar dake cikin wannan kogo suka tunkari wani tangamemen ɗaki dake ƙarshen wannan kogo, suna hango shi ɗan ƙarami acan nesa.
Saida suka yi doguwar tafiya sannan suka iso ƙofar shiga wannan ƙaramin ɗaki.
Aymanul Faris yasa hannunsa guda ya buɗe wannan ƙofa.
Wani irin baƙin hayaƙi mai ban al'ajabi ya fara yi musu sallama.
Suna tsaye suna al'ajabin wannan hayaƙi aka gabzawa Aymanul Faris wawan naushi a cikin wannan hayaƙi.
Aymanul Faris yayi tsalle baya ya faɗo acan baya. Bayansa ya doki ƙasa da ƙarfi.
Jaruma Riya tayi tsalle gefe guda sannan ta zaro idanuwanta domin ganin abinda ya yiwa Aymanul Faris wannan duka.
Aymanul Faris ya miƙe tsaye, ya karkaɗe ƙurar jikinsa.
Wani baƙon iko na musamman ya lulluɓe wannan kogo, lamarin da yasa Riya ta zube ƙasa kan gwiwowinta tayi mubaya'a kenan.
Gwiwowin Aymanul Faris suka yi sanyi, yaji kamar ya zube ƙasa shima ya yiwa wannan iko mubaya'a amma sai ya turje.
Aymanul Faris yaji cewa, ba zai iya yiwa wannan iko mubaya'a ba, sai dai wannan iko yayi masa mubaya'a.
Bayan ɗan gajeren lokaci wannan baƙin hayaƙi ya soma haɗewa a waje guda.
Siffar wani garjejen mutum ta bayyana, komai dake jikinsa baƙi ƙirim ne. Babu abinda Aymanul Faris yake iya shaidawa a jikin wannan mutumi.
Wannan baƙin hayaƙi yana kaɗawa a kewayensa.
"KAYI NASARA AKAINA, KA SHIGA!" wannan mutumi yayi magana cikin wata murya mai kaushin gaske.
Aymanul Faris ya dubi Riya ya ce, "Kada ki kuskura ki shigo faɗana da wannan ruhi. Saboda ni ne kaɗai zan iya samun nasara akansa."
Jaruma Riya ta gyaɗa masa kai, alamun zata yi hakan.
Aymanul Faris ya zaro takobinsa (ba Saiful-Shiradu ba) ya tunkari wannan ruhi.
Ruhin ya zaro wata zabgegiyar takobi daga cikin jikinsa.
Takobi ce baƙa ƙirim mai tsaho da kauri. Tana da tsananin kaifi da tsananin tsini.
Ruhin ya tsaya cak! a bakin wannan ƙofa.
Aymanul Faris yana ƙarasowa gaban wannan ruhi ya kai masa wawan sara da wannan takobi ta hannunsa.
Ko alamun kaucewa wannan ruhi bai yi ba, takobin Aymanul Faris ta dira akansa.
Takobin ta ratsa ta wuce tamkar wadda ta

Please Login or Register in order to submit comment