Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

binne.
Saida ya kwana uku a gaban wannan kabari, yana begen Zarifa sannan ya ɗebo duwatsun bakin wannan kogi ƙanana, ya gine kabarin, ya zamana cewa, komai ruwa da iska babu abinda zai yiwa kabarin.
Samudul Ansari ya fiddo wannan ƙaramin kwale-kwale na ƙarfe wanda tau'rin ya samar masa.
Ya shiga cikin wannan kogi, ya fara tuƙa kwale-kwalen, yana tafiya a hankali yana waigowa yana hango kabarin Zarifa.
Tun yana hango kabarin har sai da ya ƙule ya daina hango shi.
Samudul Ansari ya girgiza kai, "Rayuwar duniyar kenan, wataran sai labari," ya faɗa a ransa.
Sai da sarki Samudul Ansari ya shafe shekaru biyar yana tafiya sannan ya isa daular Shaha.
Tsahon wannan lokaci, daidai da wuni guda sarki Samudul Ansari bai taɓa mantawa da Zarifa ba, kullum a cikin tunaninta yake.
Saida ɓoyayyen hadimi da tau'rin suka bashi shawarwari akan ya cire tunaninta a cikin ransa, saboda kada ya sami matsala.
Da ƙyar Samudul Ansari ya samu ya rage tunanin Zarifa saboda tsananin yadda ta shiga ransa.
Sarki Samudul Ansari ya cika da tsananin mamaki bisa ganin yadda babu wani abu da ya sauya a wannan daula kamar yadda ya tafi ya barta haka ya dawo ya sameta, sai dai abubuwa ƙalilan da ba za'a rasa ba.
Tabbas sarauniya Arya ta iya riƙon amana, domin babu wani abu da ya sauya dangane da yanayin tsarin mulkin sarki Samudul Ansari komai yadda yake tafiyarwa haka ta ci gaba.
Samudul Ansari ya kaɗa linzamin wannan doki ya tunkari dajin Ƙaiz wajen Ƙaizadu domin ya tabbatar masa da cewa, ya dawo lafiya.
Bai ɗauki lokaci ba, ya shigo wannan daji na Ƙaiz.
Ƙaizadu ya hango tsaye a ƙofar wannan gida nasa, yana tsaye yana jiransa ya ƙaraso.
Fuskar Ƙaizadu cike da jimami da alhini.
Sarki Samudul Ansari na ƙarasowa gabansa ya zube ƙasa ya kwashi gaisuwa, sannan ya jajantawa Samudul Ansari rashin Zarifa da yayi.
Ƙaizadu ya baiwa Samudul Ansari umarnin shiga cikin wannan gida nasa domin su tattauna.
Samudul Ansari ya take masa baya suka shigo cikin wannan ƙaton ɗaki dake tsakiyar gidan.
Bayan sun sake gaisawa Ƙaizadu ya kawowa Samudul Ansari abinci, ya kimtsa cikinsa. Bayan ya ƙoshi Ƙaizadu ya zaro wata takarda wadda ke ɗauke da zanen hatimai guda biyu a jikinta.
"Jiya sarki Azman na duniyar iska ya aiko min wannan takardar," inji Ƙaizadu. "domin na yi ma bayanin abubuwan da ka samo a daular Irashnur!"
Sarki Samudul Ansari ya matsa kusa da wannan takarda domin ganin abinda ke kanta da kuma fahimtar abinda bokan zai sanar da shi.
Ƙaizadu ya nuna wannan baƙin hatimi wanda keda siffa ta tau'rin ya ce, "Wannan hatimi ɗan-saƙo dake tsakaninka da tau'rin.
"A duk lokacin da ka dafa wannan hatimi, bayanai da manyan amfanin tau'rin zasu bayyana maka. Na san cewa, har yanzu baka san bayanan komai akan tau'rin ba, baka san yadda aka same shi ba, inda yake samun ƙarfinsa da yadda aka yi ya zaɓe ka ba..."
Ƙaizadu ya nuna zanen hatimi na biyu wanda ke ɗauke da aljani mai gangar jiki na wuta - aljanin-wuta.
"Wannan shi ne aljani Nara-ya, ɗan ƙabilar Nara - aljanu jinsin wuta waɗanda ake halittarsu da wuta.
"Wannan aljani a halin yanzu shima ya zamo hadiminka wanda zai na bin dukkan umarninka, sarki Azman ne ya hada ka dashi domin ka ji daɗin yadda zai yi ma aiki.
"Mun san cewa ka ɗan yi amfani dashi a daular Irashnur wajen yaƙar abokan gaba. Kaga manyan illolinsa da yadda zaiyi saurin baka nasara akan abokan gaba.
"A duk lokacin da kake so kayi amfani da Nara sai ka dafa wannan hatimi.
"Wato dai, a taƙaice ina so ka gane cewa, babban dalilin da yasa waɗannan hatimai guda biyu suka bayyana a jikinka shi ne, ana so a samar dasu kamar wata mararraba ta ƙarfinka.
"A duk lokacin da kake so kayi amfani tau'rin, wannan baƙin hatimi mai zanensa zaka dafa, haka ma idan kana so kayi amfani da Nara..."
Samudul Ansari yana gama jin wannan jawabi yayi shuru yana tunani. Daga can ya ɗago ya dubi Ƙaizadu ya ce.
"Idan har wannan shi ne dalilin da yasa aka samar da waɗannan hatimai, hakan yana nufin Nara ya kai Tau'rin ƙarfi kenan?"
Cikin gaggawa Ƙaizadu ya girgiza ya ce, "Ko kaɗan! Aljani Nara ko rabin tau'rin a ƙarfi bai yi ba, saboda idan zaka lura tun da ka fara yaƙi da gorgons da tau'rin kake amfani wajen samun nasara a kansu.
"Sannan idan zaka lura a yayin fafatawarka da sarki Jiz'Ban tsinanne, duk wani hari na Nara da kayi amfani dashi daidai yake zuwa da nasa, hakane?
"Amma kana sako masa ƙarfin tau'rin ka ci galaba akansa..."
Samudul Ansari ya gyaɗa kai cikin fahimta. Lallai wannan jawabi haka yake.
"Ina tayaka farin ciki..." inji Ƙaizadu.
Cikin tsananin mamaki Samudul Ansari ya ɗago kai ya dube shi ya ce, "Na me kenan?"
Ƙaizadu yayi murmushi ya ce, "Idan ka koma gida zaka ga komai,"
Haka dai suka ci gaba tattaunawa a wannan waje, har tsahon sa'a guda da rabi sannan Samudul Ansari yayi sallama da Ƙaizadu ya koma gida.
Tun kafin ya shigo cikin wannan birni, tuni labari ya cika ko'ina. Sarki ya dawo.
Nan take sarauniya Arya tayi hawa na musamman tare da bayi da dakaru suka zo wannan jeji ɗaukar Samudul Ansari.
Sarauniya Arya ta rungume Samudul Ansari cikin tsananin farin ciki, amma ganin cewa, baya tare da Zarifa yasa jikinta yayi sanyi, ƙirjinta ya buga da ƙarfi.
Ba ta ce dashi komai ba, suka shiga cikin wannan ƙasaitaccen keken doki wanda tazo a cikinsa.
A cikin keken dokin ne, Samudul Ansari yayi arba da shayi na alfarma tare da abinci mai kyau.
Sarauniya Arya da kanta ta ciyar dashi wannan abinci.
Samudul Ansari na ƙoshi sarauniya Arya ta dube shi ta ce, "Ina yar-uwata Zarifa?"
Nan take yanayin sarki Samudul Ansari gaba ɗaya ya sauya, jikinsa yayi sanyi, idanuwansa suka kaɗa suka yi ja.
Sarauniya Arya tana ganin haka jikinta yayi sanyi, zuciyarta ta ci gaba da bugawa da ƙarfi.
"Zarifa ta riga mu gidan gaskiya," inji Samudul Ansari. Yana magana a hankali kamar baya so ya tuno abinda yake faɗa.
Hawaye masu zafi suka zubo daga idanun sarauniya Arya, saboda tausayi da kuma baƙin ciki bisa mutuwar Zarifa.
Har suka koma birnin Shaha, babu wanda ya sake cewa ɗan uwansa komai.
Sarauniya Zarifa tana kuka, shi kuma Samudul Ansari yayi shuru yana ta tunanin Zarifa.
Kowa yayi farin ciki bisa dawowar sarki Samudul Ansari lafiya.
Saboda martaba mutuwar Zarifa, saida Samudul Ansari ya bayar da hutun komai da komai na wannan daula tsahon mako biyu.
Malaman addinai daban-daban suka yi tayi mata addu'a.
Dare na rabawa, sarki Samudul Ansari yana zaune a cikin fadarsa bisa karagar mulkinsa, kasancewar da dare ne akwai manyan fitillu na sarauta waɗanda suka haskaka ko'ina.
Sarkin na nazarin wani ƙaramin littafi dake gabansa.
Babu kowa a wannan fada, shi kaɗai ne a cikinta.
Jim kaɗan ya jiwo takun sawayen mutane na shigowa cikin fadar, cikin tsananin mamaki ya ɗaga kansa sama domin ganin wane ne.
A saninsa dai, babu wanda ya umarta ya shigo wannan fada, kuma a ganinsa mutum daya ce kawai zata iya kai tsaye cikin fadar wato matarsa Arya.
To ya aka yi yaji kamar ba takun mutum ɗaya bane?
Ai kuwa yana ɗaga kan nasa yayi arba da matarsa Arya da wani saurayi mai tsananin kama da ita.
Tun daga nesa Samudul Ansari da wannan saurayi suka ƙurawa junansu idanu.
Samudul Ansari ya gagara cewa komai, sannan ya gagara tunanin komai a cikin ransa har Arya da wannan saurayi suka ƙaraso gabansa.
Saurayin ya zube a gaban Samudul Ansari ya kwashi tamkar ɗa da ubansa.
Samudul Ansari ya dubi matarsa Arya yana so ya tambayeta wane ne wannan amma ya gagara buɗe bakinsa.
Sarauniya Arya tana fuskantar haka tayi guntun murmushi ta ce.
"Sa'adda kuka yi wannan tafiya kai da marigayiya Zarifa, Ƙaizadu ya sanar dani cewa, ina ɗauke da juna biyu.
"Bayan tafiyarku da shekara guda na haifi wannan yaron, wanda na saka masa suna Jalwar.
"Jalwar ɗan ka ne na cikinka, na raine shi, na bashi tarbiyya daidai gwargwado.
"Tabbas na cika da tsananin mamaki, saboda Jalwar jarumin gaske ne, ina ganin ko kai ɗinnan ba zaka nuna masa wata jarumta ba."
Samudul Ansari yana jin wannan batu gagarumin farin ciki ya lulluɓe shi. Tunda matarsa Zarifa ta tafi ta barshi yaji gaba ɗaya duniyar ta fita a ransa.
Amma ganin cewa, ya samu magaji yasa zuciyarsa tayi sanyi gagarumin farin ciki ya lullube shi.
Sarauniya Arya tayi sallama da su ta shiga cikin gidan sarautar.
Samudul Ansari ya nunawa Jalwar inda mahaifiyarsa ta tashi ya ce ya zauna a kai.
Jalwar ya risina sannan ya zauna akan wannan kujera.
Samudul Ansari ya dube shi ya ce, "Jalwar! Shin kana da labarin dalilin da yasa nayi wannan gagarumar tafiya wadda tasa aka haifeka, bana nan?"
Jalwar ya ce, "Kwarai kuwa, baba. Mahaifiyata ta sanar dani labarin komai tun daga farkon bayyanar Gorgon..."
Samudul Ansari ya gyaɗa kai cikin jin daɗi ya ce, "Wanne irin salon yaƙi, kafi kwarewa akai?
"Shin kana sarrafa aljanu ko wani makamin yaƙi na musamman?"
Jalwar ya girgiza kai ya ce, "Ko kaɗan, nafi yin imani da zallar ƙarfin damtse da iya-yaƙi... Sarrafa aljanu da makaman yaƙi sam bai dame ni ba,"
Samudul Ansari yana jin haka ya sake yin murmushi ya ce, "Wato, a taƙaice dai, kai jarumi ne wanda ya yarda da ƙarfin dake jikinsa kaɗai?"
Jalwar ya risina sannan ya gyaɗa kai a hankali.
Samudul Ansari ya dube shi ya ce, "Ka je ka kwanta kayi barci, gobe da safe zan jarraba ka..."
Yana gama faɗin haka ya ci gaba da karanta wannan littafi dake hannunsa.
Jalwar yana gama faɗin haka ya risina ya fice daga wannan fada, ya shiga cikin gidan sarautar.
Washe gari da sassafe kuwa, kafun sarki Samudul Ansari ya fita fadarsa, ya tura hadimi izuwa wani ƙaramin filin yaƙi, hadimin ya gyara filin yaƙin domin a nan ne Samudul Ansari zai jarraba Jalwar.
Bayan kimanin sa'a guda wannan hadimi ya dawo ya shaidawa Samudul Ansari ya kammala aikin da ya saka shi.
Samudul Ansari ya gyada kai sannan ya sallami wannan hadimi.
Hadimin yana fita Jalwar da sarauniya Arya suka shigo cikin fadar.
Bayan kammala gaisuwa a tsakaninsu, wata kuyanga ta kawowa sarki Samudul Ansari abincin kalaci mai kyau.
Yana gama cin abincin, suka tunkari wannan filin horo dukkansu.
Suna zuwa wannan filin horo, Jalwar yayi arba da kayayyakin horo kala daban-daban.
Akwai takubba, kwari da baka, masu da garkuwowi.
Samudul Ansari ya nunawa Jalwar wata zabgegiyar takobi ya ce, ya ɗauko ta.
Jalwar yayi murmushi ya tunkari wata takobi dake cake a tsakiyar wannan filin horo.
Yana zuwa cikin raini yasa hannunsa guda zai ɗagata amma ya kasa, saboda tsananin nauyinta.
Jalwar ya ɗan cika da mamaki, yasa hannayensa dukkan biyu ya fara ƙoƙarin ɗagata, nan ma yaji ina ba zata ɗagu ba.
Lamarin da yasa ya fusata kenan, ya tattaro ƙarfinsa gaba ɗaya waje guda ya fara ƙoƙarin ɗaga takobin.
Sarki Samudul Ansari da sarauniya Arya suna tsaye a gefe guda suna kallon Jalwar.
Ƙwanjin hannun Jalwar suka taso, jijiyoyin jikinsa suka yi burɗin-burɗin.
Da ƙyar ya ɗago wannan takobi wadda ke cake a tsakiyar filin horon.
Samudul Ansari ya yi dariya ya nuna masa wani ƙaton gungumin itace ya ce, ya sare shi.
Jalwar ya tunkari wannan gungumen itace, yana jan wannan takobi a ƙasa saboda tsananin nauyinta.
Yana zuwa gindin wannan itace ya ɗaga takobin da ƙyar, yana cije baki ya sareta.
Takobin tana taɓa itacen ta ɓalla shi gida biyu.
Samudul Ansari yayi murmushi ya daka tsalle ya shige tsakiyar wannan filin yaƙi, shima ya tunkari inda irin wannan takobi take.
Yana zuwa yasa hannunsa guda ya zarota daga inda take cake. Sannan ya ɗagata sama, kai kace sillan-kara ya ɗaga saboda tsananin ƙarfin damtsensa.
Ba wai iya Jalwar ba, hatta sarauniya Arya wadda ta san Samudul Ansari sosai sai da ta cika da tsananin mamaki.
A gaban idanunta Jalwar ya gagara ɗaga wannan takobi. Zaka iya cewa, ita ce ya raini Jalwar ya girma har ya kai shekaru ashirin da ɗaya, ta san abubuwan da zai iya da waɗanda ba zai iya ba.
Tabbas a wannan rana ta daɗa sallamawa jarumtakar Samudul Ansari, ta tabbatar da cewa, namijin gaske ne wanda samun magajinsa sai an tona.
Samudul Ansari ya dubi Jalwar ya ware hannayensa biyu ya ce, "Ka afka min da azababben yaƙi... Ka yaƙe ni tamkar kana yaƙi da abokin gabarka..."
Jalwar yana jin haka ya ce, "Haba baba. Ta ya ya zan yaƙe ka a haka? Ka tuna cewa kaine ka haife ni, ta ya ya zan yaƙe ka tamkar abokin gaba ta?"
Samudul Ansari ya murtuƙe fuska ya ce, "Shin baka kasance jarumi bane? Mene ne abinda kake shakka?"
Jalwar yana jin haka jikinsa yayi sanyi, ya rasa abinda ya kamata yayi.
Samudul Ansari yana ganin haka ya yi murmushi ya tunkari inda Jalwar ke tsaye, yana wasa wannan takobi tasa a cikin iska.
*****
Yau *03/04/2023*
Babi na gaba zaizo *06/04/2023* da izinin ALLAH.RUHIN JARUMTAKA!
*
Babi na 107: *Sabbin Abokan Gaba*
*
***TARIHIN SAMUDUL ANSARI***
*
Wannan littafin sadaukarwa ne ga Zahra...
*
Da fatan kowa ya sha ruwa lafiya, Allah ya karɓa mana.
*
UMS
*
Sarki Samudul Ansari yana isowa gaban Jalwar ya kawo masa wawan sara a kafaɗa tamkar ba ɗansa na cikinsa ya kaiwa wannan sara ba.
Koda Jalwar ya fuskanci cewa mahaifinsa da gaske yake, sai ya tattaro ƙarfinsa gaba ɗaya ya ɗaga takobin hannunsa ya kare wannan sara.
Takubban hannunsu na haɗuwa a waje guda, Jalwar ya durƙushe kan gwiwowinsa saboda tsananin ƙarfin damtsen Samudul Ansari.
Kafun Jalwar ya sake wani motsi tuni Samudul Ansari ya juya takobinsa, ya sake kai masa wani wawan saran.
Cikin dakewa da zafin nama, Jalwar ya sake amfani da wannan takobi ya kare saran.
Haka dai Samudul Ansari ya ci gaba da kai masa muggan hare-hare da takobin hannunsa, shi kuma yana karewa iyakar iyawarsa.
Wani lokacin sai ya rage saura ƙiris takobin Samudul Ansari ta yanke shi, sai ya kare da ƙyar.
Kafun a jima tuni Jalwar ya fara haɗa zufa, sannan ya fara haki.
A cikin waɗannan shekaru ashirin da Samudul Ansari ya yi baya nan, Jalwar ya taso gagarumin jarumi a daular Shaha.
Mafi yawancin lokuta saboda yana so ya gwada jarumtakarsa, ya kan fita cikin dazuzzuka daban-daban yayi farauta.
Jalwar ya kan gwabza yaƙi da muggan dabbobin daji, ko kuma wataran idan ya bushi iska sai ya tafi cikin wani dajin daban na wata daular ya gwabza yaƙi da yan-fashi.
Jalwar ya gwabza mummunan yaƙi da dabbobin daji kala daban-daban, ya kashe manyan ƙasurguman yan-fashi.
Amma tun da yake wannan gumurzu, bai taɓa haɗuwa da sadaukin da yayi rabin Samudul Ansari a ƙarfin damtse ba.
Samudul Ansari ya mayar da takobinsa cikin kufe, ya dubi Jalwar ya ce, "Ka ci gaba da kawo min sara da suka ba ƙaƙƙautawa, yau zaka samu gagarumin horon yaƙi, irin wanda baka taɓa saninsa ba."
Jalwar yana jin haka yayi murmushi ya ɗaga wannan zabgegiyar takobi dake hannunsa ya kaiwa Samudul Ansari wawan sara. Kai ka ce ba mahaifinsa ya kaiwa wannan hari ba, saboda ya gama fuskantar wanda ke tsaye a gabansa ba ƙaramin mayaƙi bane.
Cikin kwanciyar hankali Samudul Ansari ya kaucewa takobin Jalwar, ta sari iska.
Jalwar ya sake kai masa wani wawan saran ta ɗaya gefen, Samudul Ansari ya sake kaucewa a hankali, kai kace ya san ta inda saran zaizo da kuma saurin saran.
Haka dai Jalwar ya dake iyakar iyawarsa yana ta kaiwa Samudul Ansari sara cikin zafin nama, amma ko rigar Samudul Ansari bai samu damar samu ba.
Cikin kwanciyar hankali Samudul Ansari yake kaucewa hare-haren nasa, dukda cewa baya riƙe da takobi kuwa.
Sarauniya Arya tana can zaune bisa wata ƙasaitacciyar kujera tana ganin yadda wannan gumurzu yake ta wakana tsakanin mijinta da kuma ɗan su.
Samudul Ansari ya ci gaba da baiwa Jalwar horon yaƙi har tsahon sa'a bakwai, sannan Jalwar ya gaji liƙis ya zube kan gwiwowinsa yana haki.
Samudul Ansari ya yi murmushi ya miƙa masa hannunsa guda, Jalwar ya riƙo hannun sannan ya miƙe tsaye.
Suka tunkari inda Samudul Ansari inda sarauniya Arya ke zaune.
Suna zuwa suka zazzauna akan kujerun dake gefen nata.
Wata kuyanga ta kawo musu wani shayi mai zafi a cikin kofuna.
Samudul Ansari ya karɓa ya miƙawa Jalwar da sarauniya Arya.
Bayan kowannensu ya kurɓa, Samudul Ansari ya dubi Jalwar ya ce, "Tabbas kayi ƙoƙari, wannan horon da na baka, banda dai a samu nasara a kanka da iya-yaƙi, sai dai da ƙarfin sihiri..."
Sarauniya Arya tayi murmushi ta ce, "Ai indai da ƙarfin sihirin tsafi za'a kashe Jalwar zai shekara dubu, ba'a yi masa komai ba..."
Cikin tsananin mamaki Samudul Ansari ya dubeta ya ce, "Meyasa kika ce haka?"
"Saboda tun yana yaro ɗan ƙarami, ya taɓa shiga cikin wani ƙungurmin daji inda ɗan fashi Ƙuzbaru yake.
"Duk faɗin daular Cenziya babu ƙasurgumin ɗan-fashi kamar Ƙuzbaru, sadaukin gaske ne sannan ya tumbatsa da ƙarfin sihirin tsafi.
"Abinda yasa Jalwar ya kai masa hari shi ne, akwai hadiman da muka tura wannan daula su sayo masa jar auduga, a hanyarsu ta dawowa ne suka shiga tarkon Ƙuzbaru.
"Ƙuzbaru ya karkashe hadiman namu amma an samu guda ɗaya daya tsere da ƙyar, shi ne yazo ya bamu labarin abinda ya faru.
"Jin haka yasa Jalwar fusata, ya ɗauki takobinsa ya shiga har wannan daula, ya saro kan Ƙuzbaru ya dawo dashi nan.
"Ance min a yayin fafatawar nasu, ƙarfin damtsensu da iya-yaƙinsu yazo ɗaya, hakan yasa Ƙuzbaru amfani da ƙarfin sihirin tsafinsa.
"Ya watsawa Jalwar muggan hare-hare na wuta da kibbau amma ko ƙwarzane basu yi masa ba, ba wai dan basa samun sa bane.
"Ance suna dira a jikinsa amma basa yi masa koda ƙwarzane.
"Ga dukkan alamu wannan ɗa namu yazo da baiwa ta musamman wanda zata girgiza dukkan duniya."
Samudul Ansari yana jin wannan batu yayi shuru yana tunani, ya ƙurawa Jalwar idanu.
Tsahon ɗan lokaci kafun ya baiwa Jalwar umarnin miƙewa tsaye.
Jalwar ya cika wannan umarni ya miƙe ya tsaya a gaban Samudul Ansari.
Samudul Ansari ya dafa wannan hatimi nasa na aljanin-wuta, sannan ya ɗaga hannunsa sama. Take wata ZABGEGIYAR TAKOBI JAJAWUR ta dira akan hannunsa.
Daga ƙarfen takobin har zuwa mariƙinta jajazur tamkar garwashin wuta.
Cikin zafin nama wanda yafi gaban misali, Samudul Ansari ya zabura sannan ya danƙarawa Jalwar sara da wannan takobi a kafaɗa.
Tartsatsin wuta yayi feshi daga kan kafaɗar Jalwar, bayan komai ya lafa Jalwar ya bayyana lafiyarsa ƙalau.
Samudul Ansari ya buɗe idanunsa cikin tsananin mamaki. Karo na farko a rayuwarsa ya kalli halittar da sihirin aljanin-wuta baiyi tasiri akan ta ba.
Samudul Ansari bai yi gangancin jarraba tau'rin akan Jalwar ba.
Ya kamata a san cewa, tau'rin ba aljani bane. Ruhi ne.
Saboda haka dukkan hare-harensa ba wai gangar jiki suke yiwa illa ba, mafi yawancin lokuta ruhi suke tarwatsawa.
Harin tau'rin baya amfani da ƙarfin sihiri ko kaɗan, gaba ɗayansa zallar jarumtaka ne da ƙarfin iko.
Wannan na daga cikin manyan dalilan da suka sa harin yake yiwa ƙabilar Gorgon illa sosai.
Samudul Ansari da sarauniya Arya suna cikin kallon Jalwar cikin tsananin mamaki kenan, wannan hadimi na Samudul Ansari yazo wajen.
Hadimin ya zube a gaban Samudul Ansari ya kwashi gaisuwa sannan ya ce, "Ya shugabana! Akwai manzon da sarki FARHAMA na birnin Kufa ya aiko, yana can yana jiran ka..."
Samudul Ansari da sarauniya Arya suna jin wannan batu, suka dubi juna cikin tsananin mamaki.
Tun da Samudul Ansari ya karya daular Gorgon a wannan daula, babu basaraken da ya sake aiko masa da wasiƙa.
Mafi yawa daga cikin sarakunan duniya, suna tsoro ne, kada Samudul Ansari ya shafa musu kashin kaji a lokacin da ta kwaɓe masa azo su ma a hallaka su.
Wannan abu bai damu sarki Samudul Ansari da jama'arsa ba, saboda zaka iya cewa, duk wani abu da rayuka suke buƙata na musamman akwai shi a daular Shaha.
Saboda haka rashin hulɗarsu da sauran ƙasashen duniya bai janyo musu wani tangarɗa ba.
Abin tambayar shi ne, mene ne dalilin da yasa sarkin Kufa zai aiko da saƙo, tazarar dake tsakaninsu tana da ɗan nisa.
Bayan haka, tun kafun daular Shaha ta fara yaƙi da ma'abota Gorgon, babu wani abu da ya taɓa haɗa su da birnin Kufa.
Don haka dole ne sarki Samudul Ansari da sarauniya Arya su cika da tsananin mamaki.
Samudul Ansari ya miƙe tsaye, ya tunkari hanyar fada, sarauniya Arya da ɗanta Jalwar suka take masa baya.
Bayan gajeruwar tafiya suka iso cikin fadar ƙasar, inda Samudul Ansari yayi arba da manzanni guda uku zazzaune akan dawakansu.
Manzannin suka risina a gaban Samudul Ansari ya wuce izuwa kan karagar mulkinsa ya zauna. Arya da Jalwar suka zo bayansa suka tsaitsaya.
Ɗaya daga cikin waɗannan manzanni ya sauƙo daga dokinsa, ya taho gaban karagar Samudul Ansari ya sake zubewa ya kwashi gaisuwa.
Daga bisani ya fiddo wata nannaɗaɗɗiyar wasiƙa ya miƙawa maga-takarda.
Maga-takarda ya karɓi wannan wasiƙa sannan ya nemi izini wajen sarki domin ya fara karanta ta.
Sarki Samudul Ansari ya gyaɗa masa kai, alamar an bashi umarnin fara karatun.
Maga-takarda ya warware wasiƙar a hankali sannan ya fara karanta cikin nutsuwa kamar haka:
"Wasiƙa daga sarki Farhama na birnin Kufa, zuwa ga sarki Samudul Ansari mai daular Shaha.
"Ya kai wannan sarki da fatan kana lafiya, ya matanka da ƴaƴanka?
"Kayi sani cewa, a cikin wannan daula taka akwai wani ƙaramin gari da ake kira Julez.
"A wannan gari na Julez akwai albarkar ƙasa sosai a wajen, masana na ƙasata sun tabbatar min da cewa, za'a iya samun ɗanƴen-mai a wajen.
"Kayi sani cewa, babu irin albarkar ƙasar

Please Login or Register in order to submit comment