Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels

RUHIN JARUMTAKA!
*
Babi na 101: *SARKI AZMAN NA DUNIYAR ISKA*
*
***TARIHIN SAMUDUL ANSARI***
*
Wannan littafin sadaukarwa ne ga ZAHRA...
*
UMS
*
*UBANGIJI YA KARƁA MANA IBADUN MU*
*
Wannan jibgegen tsuntsu yayi ta ketawa da Samudul Ansari cikin gajimare, har suka iso wani waje mai yawan iska.
Komai dake wajen, kama daga garuruwa, dazuzzuka da tsaunika duk akan iska suke yawo.
Sarki Samudul Ansari baida buƙatar a sanar dashi wannan waje ina ne, domin kuwa ya gano cewa ya shigo cikin duniyar iska.
Sannu-a-hankali wannan tsuntsu na tafiya dashi har suka fara isowa cikin garuruwan mutane waɗanda ke ɗauke da irin wannan siffa wadda Samudul Ansari ya gan su da ita a cikin wannan ƙaton jirgin ruwa wanda suka haɗu dashi a daular Gorgon.
Babu wanda ya cewa Samudul Ansari uffan, mafi yawancin lokuta ma jama'ar kallo ɗaya kawai suke yi masa, su kawar da kansu sannan su ci gaba da al'amuran gabansu.
Wannan ko kaɗan bai dami Samudul Ansari ba, ya gyara zama akan wannan tsuntsu sannan ya ci gaba da kallon hanya.
Tsuntsun ya yi ta ratsawa ta cikin biranai daban-daban har tsahon lokaci, sannan suka tunkaro wani babban birni wanda duk faɗin wannan waje babu wanda ya kaishi girma da kawatuwa.
Akwai gagarumar katanga mai girma da faɗin gaske da ta kewaye wannan gari, sannan an yiwa wannan gari ƙofar shiga guda ɗaya tal.
Waɗannan zaratan mayaƙa guda goma na tsaitsaye a bakin ƙofar suna gadi.
Kafun tsuntsun Samudul Ansari ya ƙaraso bakin ƙofar, waɗannan masu gadi suka buɗe masa hanya. Kai kace sun san da zuwan sa.
Sarki Samudul Ansari ya ɗaga musu hannu, lokacin da yazo giftawa ta gefensu.
Cikin wannan gari yana da bambanci sosai da sauran garuruwan da ya ratso, domin anfi ƙawata shi fiye da ko'ina a wannan daula.
Sarki Samudul Ansari ya cika da tsananin mamaki bisa ganin yadda wannan tsuntsu keta sharara uban gudu, amma tsahon lokaci basu iso fadar sarkin Azbin ba.
Bayan shuɗewar sa'o'i wannan tsuntsu ya tunkaro wani ƙatoton gini wanda idan ka ganshi ta sama zaka ga har ya soma shige cikin gajimare wannan duniya, sannan idan ka dubi ƙasan sa kuma, zaka ga har ƙule a cikin wani baƙin hayaƙi wanda ba'a hango ƙarshen sa.
Sarki Samudul Ansari ya raya a ransa cewa, lallai wannan waje shi ne babbar fadar wannan sarki, saboda a ganinsa zai yi wuya a samu wani waje wanda zaifi wajen ƙawatuwa a duk faɗin duniyar.
Tsuntsun nasa na zuwa ƙofar shiga wannan fada, wani badakare mai jajayen tufafi ya bayyana ya tsayar da tsuntsun.
"Kai kaɗai aka baiwa umarnin shiga, saboda kai kaɗai aka gayyato..." inji badakaren.
Shi kaɗai aka gayyato? Yaushe kuma waye ya gayyato shi? A ganin sarki Samudul Ansari ai babu wanda ya gayyato shi, shi ne da kansa ya yanke hukuncin zuwa wannan fada domin sake ganawa da sarkin ƙabilar Azbin.
Dukda haka bai yi wani musu ba, ya sauƙa daga wannan tsuntsu ya tsaya cak! a cikin iska.
Wannan badakare ya shige gaba, sarki Samudul Ansari ya take masa baya, suka shigo cikin wannan fada.
Iya rayuwar sarki Samudul Ansari bai taɓa zuwa ƙawataccen waje kamar wannan fada ba. Komai na fadar ya sha bamban da na sarakunan duniya.
Kai kace wannan fada ita ce, sarauniyar sauran fadodin duniya.
Sarki Samudul Ansari yayi ta arba da kuyangi kala daban-daban suna gudanar da ayyuka iri-iri.
Jama'a suna ta harkokin gaban su, dakaru suna ta kaiwa da komowa a wannan fada.
Duk irin tsananin ƙarfin mulki irin na Samudul Ansari a wannan waje sai da ya fuskanci cewa shi ba komai bane. Ga nan inda sarakuna suke mulki.
Ya ci gaba da bin bayan wannan badakare, suna ta wucewa ta cikin fadodi kala daban-daban har sai da suka wuce ta cikin fadodi ashrin sannan suka shigo cikin wata fada.
A wannan fada babu jama'a sosai, sannan kuyangin da suke aiki a cikinta kyawawan yan-mata ne irin waɗanda Samudul Ansari ya daɗe baiyi arba da irinsu ba.
A wannan waje ne, wani hadimi dabam yazo ya karɓi Samudul Ansari daga hannun wannan badakare sannan suka shiga asalin ƙuryar fadar.
Akan wata ƙasaitacciyar karagar mulki, sarki Samudul Ansari ya hango wannan basarake wanda suka haɗu a cikin jirgin ruwa a shekarun baya.
Sarkin yasha alkyabba wadda aka yiwa ado da jan zinari, wata kyakkyawar budurwa na zaune a hannun damansa.
Wannan hadimi ya kai Samudul Ansari kan wata kujera dake gefen karagar mulkin sarkin, sannan ya bashi umarnin zama akan ta.
Babu musu Samudul Ansari ya zauna akan wannan kujera.
Hadimin ya risina a gaban sarkinsa sannan ya juya ya fice daga cikin fadar.
Fitar wannan hadimi keda wuya, wannan budurwa dake zaune a gefen wannan sarkin ta miƙe tsaye ta ɗauko abinci da ababen sha a cikin wani ƙaramin akwati ta kawo su gaban sarki Samudul Ansari.
Sarkin Azbin ya yiwa Samudul Ansari umarnin cin waɗannan abinci. Babu musu Samudul Ansari ya buɗe kwano ya fara ci, har sai da ya ƙoshi.
Koda sarkin Azbin yaga ya sami nutsuwa sai ya dube shi ya ce.
"Barka da zuwa, duniyar iska. Wani yanki dake cikin sararin samaniya, wanda babu wanda ya san da zaman shi face yan-ƙabilata...
"Mene ne abinda ke tafe da kai?"
Sarki Samudul Ansari ya yi gyaran murya ya ce, "Ya kai wannan sarki mai yawan hikima da basira. Na bi dukkan bayanan da kuka yi min a haɗuwarmu ta farko a daular Gorgon, kuma na samu nasara akan su...
"Kwanaki kaɗan kafun wannan rana, sun sake kawo hari daulata, na samu nasarar ƙarar dasu amma sun bar irin wannan annoba wadda suka haddasa da farko...
"Nazo wajenka ne domin sake samun irin wannan magani, wanda muka yi amfani dashi da farko muka gama da wannan annoba..."
Sarkin Azbin na jin wannan batu na sarki Samudul Ansari yayi shuru ya ƙurawa Samudul Ansari idanu, tamkar wanda ke tunanin wani abu.
Tsahon ɗan lokaci, kafun ya buɗi bakinsa ya ce, "Iya daɗewata a duniya fiye da shekaru ɗari shida da tamanin, ban taɓa ganin gwarzon mutum kamar ka ba.
"Kayi sani cewa, ƙarfin da daular Gorgon take da shi a yanzu, hatta ni kaina ban isa na dakatar dasu ba, amma gashi kai ka iya.
"Mutanen ƙabilar Gorgon duk sun girgiza da lamuran ka, yanzu haka suna wani gagarumin wanda suke tunanin zai kawo ƙarshen ka...
"Wannan shi ne dalilin da yasa na gayyato ka wannan fada tawa, ba wai iya maganin wannan cuta zan baka ba, a'a, zan haɗa maka harda gagarumin tsumi wanda indai ka sha wane Gorgon."
Sarki Samudul Ansari ya ɗan yi shuru, daga bisani ya ce, "Wanne irin shiri mutanen Gorgon suke yi a kaina yanzu?"
Ba tare da ɓata lokaci ba, sarkin Azbin yayi masa bayanin atisayen ƘARSHEN TAU'RIN wanda sarauniya Yilan da mahaifinta suka shirya.
"Gauhan maciyi amana ne, ya haɗa kai da ma'abota Bankai domin kawo ƙarshen daular ku...
"Ban san ya aka yi ba, amma akwai takobin mai darajan gaske a hannun Gauhan.
"A tunanin mu da hangen mu, wannan takobi ce kaɗai zata yi tasiri akan ka a yanzu."
Sarkin na zuwa nan a zancensa ya ɗauko waɗansu manyan kwalabe guda biyu a cikin wani ƙaton akwati ya baiwa su Samudul Ansari.
Kwalba guda tana ɗauke da farin sinadari. Ɗayar kuma tana ɗauke da koren sinadari.
Wadda ke ɗauke da farin sinadari ita ce wannan magani na wannan cuta. Wadda ke ɗauke da koren kuma, ita ce wannan tsumi wanda Samudul Ansari zai sha.
Sarkin ya ce, "Wannan kwalba ita ce, ruwan tsumin da zamu baka. Ana so kaje tsakiyar garin Irashnur ka sha wannan tsumi..."
"Garin Irashnur wannan daula ta aljanu wadda ake cewa, babu waɗanda suka kaisu zalunci a duniya yanzu?" inji Samudul Ansari.
Sarkin ya gyaɗa masa kai.
Samudul Ansari ya ce, "Ai wannan waje yana da tsananin nisa tsakaninsa da daulata, na tabbata koda akan aljani zanyi tafiyar, sai na shafe shekaru goma ban isa can ba...
"A wannan hali da ake ciki, ta ya ya zan yi har tsahon shekaru goma bana nan?"
Wannan sarki na jin haka yayi murmushi ya ce, "Shekaru goma kacal? Ai ba wani abu bane...
"Kayi sani cewa, maƙiyanka shirin shekara ɗari suke yi maka..."
Cikin tsananin mamaki, Samudul Ansari ya ce, "Shekara ɗari - ƙarni fa kenan? Wannan wanne irin shiri ne haka?"
Wannan basarake ya ce, "Kana tunanin ƙarfinka na wasa ne? Ai sun san a yanzu baza su iya da kai ba, shiyasa suka fara wannan shiri wanda a ƙarshensa ne, za'a bambance wanda zaiyi nasara a tsakanin ku..."
Samudul Ansari ya ce, "Idan naje tsakiyar birnin Irashnur na sha wannan tsumi, kenan dawowa zan yi ƙasata na ci gaba da jira har tsahon shekaru tamanin?"
"Ƙwarai kuwa," inji wannan sarki. "Amma a lokacin zaka ci gaba da gwagwarmaya a duniya, ka yaƙi zalunci, ka kafa adalci..."
Haka dai Samudul Ansari da wannan sarki suka ci gaba da tattaunawa tsahon sa'o'i, kafun su yi sallama da juna.
Sarki Samudul Ansari ya ɗauki waɗannan kwalabe guda biyu, ya saka a cikin jakar guzurinsa sannan ya fito daga cikin waɗannan fadodi ya haye bayan wannan tsuntsu, suka juya da baya suka nufi ƙasa.
Sai da suka shafe kimanin tafiyar da suka yi a farko sannan suka iso bakin wannan ƙaton rami wanda boka Ƙaizadu ya haɗa shi da wannan tsuntsu.
Tsuntsun ya sauƙe Samudul Ansari a gefen boka Ƙaizadu wanda ke tsaye yana jiransu.
Samudul Ansari na sauƙa boka Ƙaizadu ya sallami wannan tsuntsu, sannan ya dafa kafaɗar Samudul Ansari suka ɓace a wannan wuri, suka bayyana a tsakiyar fadar bokan.
Samudul Ansari ya kwashe duk abinda suka tattauna da sarkin Azbin ya zayyane masa, a ƙarshe ya nemi Ƙaizadu yayi masa bayanin haɗarin daular Irashnur da wuraren da zai wuce kafun yaje can.
"A yanzu idan ka cire daular Gorgon, babu waje mai haɗari a duniya kamar daular Irashnur, saboda gaba ɗaya halittun dake daular, aljanu ne.
"Aljanun ma, ba wai asalin jinsin aljanu ba. Jikin su da duwatsu aka haɗa shi.
"Bani da bayanai akan haɗarurrukan dake kan hanya amma abinda na sani shi ne, daular Irashnur waje ne mai mugun haɗari, wanda kowa yake tsoro." inji Ƙaizadu.
"Mene ne sunan babban birnin su, wanda ake so naje tsakiyarsa na sha wannan tsumi?" sarki Samudul Ansari ya tambayi Ƙaizadu.
"JEZEN!" inji Ƙaizadu.
Samudul Ansari na jin haka, ya miƙe tsaye daga cikin wannan fada ya dubi Ƙaizadu ya ce, "Ina godiya da gudunmawarka!"
Ƙaizadu ya risina a gaban Samudul Ansari.
Sarki Samudul Ansari ya fice daga cikin wannan fada, ya haye kan dokinsa ya koma birninsa.
Matansa biyu suna ganin ya dawo, suka tare shi, suna masu tsananin farin ciki.
Sarki Samudul Ansari ya baiwa sarauniya Arya wannan magani ya ce, ta tabbatar an saka a kowanne kogi, tekuna da ƙoramu na wannan daula.
Sarauniya Arya ta karɓa sannan ta fice daga cikin fadar.
Da yake Samudul Ansari ya tsara komai da komai na wannan daula. Cikin ƙanƙanin lokaci wannan magani ya gama kewaye ko'ina da ina.
Waɗanda suka kamu da wannan cuta, suka warke, dukda haka saida kaɗan suka mutu.
Bayan an gama jana'izar su, sarki Samudul Ansari ya tara manyan wannan daula da kuma matansa biyu a cikin fadarsa domin su tattauna.
"Da farko, ina jajanta mana bisa rasa mutanen mu da muka yi da kuma asarar dukiya da muka yi a yayin yaƙi da mutanen Gorgon...
"Da izinin Ubangiji, wannan abu yazo ƙarshe, naje har fadar SARKI AZMAN NA DUNIYAR ISKA mun tattauna akan wannan al'amari.
"Sarki Azman ya tabbatar min da cewa, abokan gabarmu ba za su sake farmakar mu ba, daga nan har zuwa tsahon shekaru ɗari..."
Koda mutanen dake zazzaune a fadar suka ji abinda Samudul Ansari ya ce sai gagarumin farin ciki ya lulluɓe su.
A ƙiyasi shekaru ɗari nan gaba masu zuwa da yawa daga cikinsu sun fara manyanta.
Sarki Samudul Ansari na ganin sun cika da farin ciki sai ya haɗe fuska ya ce, "Shin kun san mene ne dalilin da yasa zasuyi shuru har tsahon shekaru ɗari?"
Dukkansu suka girgiza masa kai, babu wanda yasan komai.
"Kyakkyawan shiri zasuyi akan mu wanda zai basu damar zuwa su ruguje daular mu..." inji Samudul Ansari.
Koda suka ji abinda ya ce sai kowa ya dawo taitayinsa.
Abokin gaba ko shiri na wata guda yayi akan ka, dole ne ka razana ballantana ace shekaru ɗari.
Sarauniya Arya ta dube shi ta ce, "Ya shugabana! Shin tsahon waɗannan shekaru zuba musu idanu zamuyi har shekarun su zo, su gama da mu..?"
Samudul Ansari ya ce, "Wannan shi ne dalilin da yasa na taraku a wannan waje, domin nayi muku bayanin shirin da zanje na gudanar nima..."
Yana zuwa nan a zancensa ya fiddo wannan kwalba mai ɗauke da koren sinadari wadda sarki Azman ya bashi.
"Wannan ruwan-tsumi ake so naje tsakiyar birnin Irashnur na sha..."
Duk wanda ke zaune a cikin wannan fada sai da ya zaro idanu cikin tsananin razana.
A wannan zamani, idan ka cire daular Gorgon babu wajen da mutane ke tsoro kamar daular Irashnur, domin jinsin waɗansu aljanu ne masu gangunan jiki na duwatsu.
Babban abinda ya kwantarwa da mutanen dake wannan waje hankali shi ne, jin cewa, Samudul Ansari da kansa zaiyi wannan tafiya.
A wannan lokaci da ake a yanzu, basa tunanin akwai abinda zai kawowa Samudul Ansari matsala a duk al'amuransa saboda ya gama shiryuwa.
"Babu damuwa, zaka iya wannan tafiya. Amma ina neman alfarma a wajenka - nima ina so ayi wannan tafiya tare da ni..." inji Zarifa.
Samudul Ansari ya ɗan yi shuru ya kalli sarauniya Arya.
Daga bisani ya sallami sauran manyan fadar, saboda al'amarin da zasu tattauna akai bai shafe su ba.
Bayan sun gama watsewa Samudul Ansari ya dubi Zarifa ya ce, "Saboda wanne dalili kike so kiyi wannan tafiya mai mugun haɗari, tare dani..?"
Zarifa ta ce, "Saboda na kasance mayaƙiya kamar yadda ka kasance, ni ce yafi dacewa mu ringa tafiya irin wajaje masu haɗari tare da kai, saboda samun nutsuwarka..."
Sarki Samudul Ansari ya gyaɗa kai. Tabbas maganganun da jarumi Zarifa ta faɗa hakane. A matsayinsa na basarake kuma jarumin sadauki, bai kamata yayi irin wannan doguwar tafiya ba tare da mace ba.
Ko domin samun abokiyar hira da kuma biyan buƙatarsa.
Amma a matsayinsa na wanda keda mata guda biyu, dole yana buƙatar yayi musu adalci.
"Ya kika ce?" Samudul Ansari ya tambayi Arya.
"Tsahon wanne lokaci, zaka shafe a yayin wannan tafiya?" ta sake tambayarsa.
"SHEKARU ASHIRIN..." ya amsa a taƙaice.
Samudul Ansari da Zarifa suka ƙurawa sarauniya Arya idanu, suna jiran amsar da zata bayar.
Sarauniya Arya tayi shuru tana tunani.
Duk matar da aka ce tana da miji, rabuwa dashi na wuni guda bata so sai ta kama dole.
Ya ya mace zata ji idan aka ce zai nisanceta na tsahon shekaru ashirin?
Sarauniya Arya mace ce mai tsananin tausayi da ƙaunar talakawanta, tun farkon hawanta karagar mulki munji yadda take yawan fita rangadi domin ganin lafiyar al'ummarta.
Saboda haka wannan abu, ba zai wani ɗaga mata hankali sosai ba, saboda babban dalilin wannan tafiya shi ne ƙwato kimar wannan daula ta su.
Amma idan aka kawo batun auratayya, zamu iya cewa kusan kowa yana da kishi akan abokin tarayyarsa.
"Mene ne abinda zai ɗebe min kewarka, tsahon shekaru ashirin, ya kai mijina?" sarauniya Arya ta tambayi sarki Samudul Ansari.
Samudul Ansari na jin haka jikinsa yayi sanyi, ya dafa hannun Arya guda sannan ya fara yi mata magana cikin tattausan harshe.
"Kiyi haƙuri yake matata. Idan ba ta kama dole ba, bana so na rabu da ɗaya daga cikin ku...
"Wannan tafiya ita ce zata tantance gabar dake tsakaninmu da ma'abota Bankai...
"A matsayin ki na sarauniya yar sarki, zan bar miki amanar mulkin wannan daula gaba ɗaya, har zuwa sa'adda zan dawo...
"Kiyi haƙuri, ki bamu dama muyi wannan tafiya, domin kawo ƙarshen barazana da tsoro na farmakin ma'abota Bankai a kowanne lokaci..."
Sarauniya Arya tana jin wannan batu, hawaye ya zubo daga idanunta ta ce, "Na amince!"
Zarifa tana ganin haka tausayin sarauniya Arya ya kamata, haka shima Samudul Ansari.
A wannan waje Samudul Ansari ya tabbatar mata da cewa, duk kwanakin da zaiyi yana shirye-shiryen wannan tafiya, a ɗakinta zai na kwana saboda ya bata lokacinsa.
Sarauniya Arya tayi farin ciki da hakan.
****
Yau *23/03/2023*
Babi na gaba zaizo *25/03/2023* da yaddar ALLAH.RUHIN JARUMTAKA!
*
Babi na 102: *Ɓoyayyen Hadimi*
*
***TARIHIN SAMUDUL ANSARI***
*
Wannan littafin sadaukarwa ne ga Zahra...
*
*UBAGIJI YA KARƁA MANA IBADUN MU!*
*
UMS
*
Saida sarki Samudul Ansari ya shafe kwanaki goma cir yana shirye-shiryen wannan tafiya sannan ya kammala. A tsahon waɗannan kwanaki kullum a ɗakin sarauniya Arya yake kwana.
Abinda sarki Samudul Ansari ya sake fuskanta shi ne, duk sa'adda alaƙar aure ta shiga tsakaninsa da sarauniya Arya sai jinin jikinsa ya ƙara ƙarfi, ƙarfin tau'rin ya ninninku.
Kafun cikar waɗannan kwanaki guda goma, tuni ƙarfin Samudul Ansari ya sake cika ya tumbatsa.
A ranar kwana ta goman, da sassafe sarki Samudul Ansari ya tara dukkan manyan wannan daula su ɗari uku da uku a cikin wani fadarsa domin yayi sallama dasu.
Sarkin na zaune kan karagar mulkinsa, Zarifa tana zaune a hannun hagunsa tayi irin shigar da yayi wato ta baƙaƙen kayan yaƙi.
Sarauniya Arya kuma, tana zaune a hannun dama ta saka alkyabba irinta kyawawan sarakuna.
Sarki Samudul Ansari ya dubi manyan daular ya ce, "Gagarumar tafiya ta taso wadda ya zamo dole nayi ta, idan muna so wannan daula ta kuɓuta daga sharrin ma'abota Bankai.
"Idan nayi tafiya kafun na dawo, zan iya shafe shekaru ashirin. Saboda haka na tara ku domin mu ajiye magana.
"Ba zai yiwu a mulki babbar daula kamar wannan ba, ba tare da an haɗa kai ba.
"Jiya nayi shawara akan wanda ya dace na barwa mulkin wannan daula, kuma na cimma matsaya.
"Sarauniya Arya matata tun asali, ƙasaitacciyar sarauniya ce wadda ta gaji sarauta a gidansu.
"A shawarar da nayi da zuciyata, sarauniya Arya zan barwa riƙon wannan daula, har zuwa sa'adda zan dawo.
"Shin a cikin ku akwai wanda yake da ƙorafi ko kuma neman ƙarin bayani akan wannan hukunci da na yanke?"
Lokacin da sarki Samudul Ansari yazo nan a zancensa, sai yayi shuru sannan ya ƙurawa waɗannan yan-majalisa idanu ɗaya bayan ɗaya yana jiran abinda zasu ce.
Dukkansu tsahon lokaci suka yi shuru babu wanda yace uffan.
"Ina da magana," inji tau'rin.
Samudul Ansari ya ɗan yi guntun murmushi ya ce, "Ina jin ka?"
"Akwai mutane goma a cikin waɗannan yan-majalisu da suke jin haushin wannan hukunci da muka yanke..." tau'rin ya ce.
Samudul Ansari ya haɗe fuska ya ce, "Indai mutane goma ne, to da sauƙi amma su wane ne?"
"Ba zan bayyana maka su a yanzu ba, amma a duk inda kake a yayin wannan tafiya, zan iya nuna maka abinda ke faruwa a ƙasarka..." Tau'rin ya sake cewa.
Samudul Ansari ya ce, "Na umarce ka a duk lokacin da mummunan abu ya taso a wannan daula a yayin da bana nan, ka nuna min, ni kuma na dawo nayi maganin abin!"
"Zan yi hakan," inji tau'rin.
Kada dai a manta, irin wannan tattaunawa Samudul Ansari da wannan ruhi kaɗai ke jin ta, waɗanda suke tare dashi baza ma su san anyi ta ba, balle su ji ta.
A daidai lokacin Zarifa ta dubi yan-majalisar ta ce, "Ga dukkan alamu, kun amince da

Please Login or Register in order to submit comment