Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

sa'adda aka sare ka da wannan takobi tayi maka illa, alhalin saran da aka yi maka da takobin baida wani zurfi?"
Aymanul Faris yayi guntun murmushi ya ce, "Saboda anyi irin waɗannan takubba ne domin su bi umarnin tau'rin ba wai su cutar da shi ba..."
Suka ci gaba da tafiya a cikin wannan kogi har la'asar ta gama yi.
Lokacin ne suka iso tsakiyar wannan ƙaton kogi, wajen da yafi ko'ina zurfi da faɗi.
Ba zato suka ga wata murtuƙeƙiyar jela ta kamo ƙarshen kwale-kwalensu da kuma farkonsa.
Kafun su yi wani yunƙuri tuni an janye su izuwa ƙarƙashin wannan kogi.
A tsakiyar wani waje suka tsinci kansu a ƙarƙashin wannan kogi.
Kasancewar a ƙarƙashin ruwa suke, babu yadda za'ayi numfashi ya shigo musu. Wannan yasa Aymanul Faris yayi amfani da hannunsa guda ya samar musu da waɗansu irin tufafi waɗanda suke basu damar shaƙar numfashi.
Ai kuwa numfashi yana fara zuwa musu suka dawo cikin hayyacinsu suka ƙarewa wannan waje da suke kallo.
Wajen gaba ɗaya a cike yake da shuke-shuken ƙarƙashin ruwa, sannan ƙananun kifaye suna yawo a wajen.
Har sun fara shawarar fitowa daga ƙarƙashin kogi, suka ga jelar wannan halitta da ta janyo su cikin wannan kogi ta soma fitowa daga cikin wani rami.
Aymanul Faris ya zaro takobinsa sannan ya tsaya a gaban Riya ya bata umarnin komawa bayansa.
Jim kaɗan wannan jibgegiyar halitta ta gama fitowa daga cikin wannan ƙaton rami.
Halittar guda ɗaya ce amma tana da jela sun kai guda goma.
Kowanne ɗaya daga cikin wadannan jela nata, yana iya ƙarawa kansa tsaho ko kuma ragewa, sannan masu ƙarfin gaske ne.
Dukda cewa jikinta kore ne amma kana kallonta tunanin baƙin abu zai fara zuwa ranka saboda yanayin nata yafi kama da baƙi.
Tunda su Aymanul Faris suke basu taɓa arba da irin wannan halitta ido-da-ido ba, amma suna jin labarin ta.
Halittar tayi amfani da jelanta guda biyu ta fizgo wadansu duwatsu dake ƙarƙashin wannan kogi ta jefi Aymanul Faris dasu.
Aymanul Faris ya kaucewa waɗannan duwatsu suka wuce, yayi amfani da wannan dama ya ruga kan halittar.
Sai dai kafun ya isa ta sake jefo masa waɗansu jelanta guda huɗu zata kanannaɗe shi.
Aymanul Faris ya sare biyu daga cikinsu sannan ya kaucewa guda biyun.
Dukda cewa a ƙarƙashin ruwa suke, saida suka ji wannan halitta tayi ƙara.
A daidai lokacin wani jibgegen ƙaton kifi yazo wannan waje ta bayan jaruma Riya.
Aymanul Faris ya ga tahowar kifin amma babu ta yadda zai iya sanar da jaruma Riya saboda idan ya ce zaiyi magana a ƙasan ruwa, ruwa zai shiga bakinsa.
Idan kuwa ya ce zai koma inda take tsaye, wannar halitta zatayi amfani da wannan dama ta kamo shi ta jelanta ta matse.
Wannan ƙaton kifi da ya tunkaro Riya bakinsa yana da tsaho da kuma tsini tamkar tsinin mashi. Idan Aymanul Faris bai yi wani yunƙuri na hana wannan kifi isowa inda Riya take ba, akwai yiwuwar ya caka mata wannan baki nasa.
Aymanul Faris yana tsaye yana shawarar abinda ya kamata yayi kenan, wannar halitta ta sake jefo masa jelanta guda uku, sannan abinda ya rage wannan kifi ya riski Riya ɗan kaɗan ne.
Cikin gaggawa Aymanul Faris ya yanke shawarar abinda ya kamata yayi, ya ruga da gudu wajen da Riya ke tsaye.
A ganin Aymanul Faris idan wannan kifi ya caki Riya zata iya mutuwa amma idan waɗannan jela ne suka kama shi, babu wani abu da zasu yi masa.
Kafun tsinin bakin wannan kifi ya caki Riya Aymanul Faris ya isa wannan waje, yasa hannayensa ya tureta gefe guda.
Tsinin ya karci gefen damtsensa, jini ya tsatstsafo.
Waɗannan jela guda uku suka kamo hannayensa biyu da kuma wuyansa wannan halitta ta ja shi inda take.
Jaruma Riya ta juyo cikin tsananin mamaki, lokacin tayi arba da wannan kifi, sannan tayi arba da Aymanul Faris daf da wannan halitta yana ƙoƙarin kwace kansa.
Jaruma Riya ta fusata ta tunkari wannan ƙaton kifi.
Kifin ya sake tunkarota da gudu zai fasata da tsinin bakinsa.
Saura ƙiris su haɗu, Riya ta gwace cikin zafin nama, ta yanki kifin da kaifin takobinta.
Wawakeken yanka ya bayyana a jikin kifin, jini mai yawa ya fara zubowa.
Kafun ya juyo tuni Riya tayi amfani da salon "SIWOD DANS" tayi kaca-kaca da namansa.
Dukda cewa Aymanul Faris yana ɗaɗɗaure a jikin wannan halitta, saida ya sake cika da tsananin mamaki saboda ganin wannan jarumtaka nata.
Jaruma Riya ta sake rugawa kan wannan halitta wadda take ƙoƙarin kakkarya ƙasusuwan Aymanul Faris.
Shima Aymanul Faris saiya dunƙule hannayensa, ya buɗa waɗannan jela da suka ɗaure hannayen da ƙarfi.
Ƙwanjin Aymanul Faris da jijiyoyinsa suka sake kumburowa, koda wannan halitta taji tamkar zai yagata sai ta sake masa hannaye.
Sai dai tana sake masa hannaye ta sake shaƙo wuyansa, wani irin azababben zogi ya sake rufe Aymanul Faris.
Ya sake saka hannayensa ya kamo jelar da ta shaƙe masa wuya, ya fara ƙoƙarin tsinka ta.
Koda wannan halitta ta sake jin wahala sai ta sake wuyan Aymanul Faris.
Yana tsaye yana daidaita wuyansa, wannan halitta tayi wani juyi da dukkanin wadannan jela nata ta doki ƙirjinsa da ƙarfi.
Aymanul Faris yayi tsalle sama sai da ya fice daga cikin kogi sannan ya sake faɗowa ƙarƙashinsa.
Jaruma Riya tana ƙarasowa gaban wannan halitta ta shiga gididdiba waɗannan jela nata cikin zafin nama.
A duk sa'adda wannan halitta ta jefo mata jela, sai tayi amfani da "SIWOD DANS" tayi kaca-kaca da ita.
Kan ka ce me wannan, tuni jaruma Riya ta gama sassare dukkan jelan wannan halitta.
Aymanul Faris yana faɗowa cikin wannan kogi, suka ƙarasa inda halittar take suka hau ta da sara da suka cikin ƙanƙanin lokaci suka ƙarasa ta.
Maimakon jini ya zubo kamar suka yi tsammani, irin wannan baƙin hayaƙi ya sake cika wajen.
Nan take aka yi jifa dasu sama daga cikin wannan kogi, saboda ƙarfin jifan da kuma iskar dake kaɗawa saida dukkansu suka suma.
Bayan Aymanul Faris da jaruma Riya sun farfaɗo sai suka shiga cikin wani ƙaramin kogo, suka yada zango a nan.
Aymanul Faris ya dubi Riya ya ce, "Ya ke matata! A ina kika ƙware a sarrafa "SIWOD DANS" alhalin sa'adda muke yara, ni ne a gaba dake a komai?"
Jaruma Riya tayi murmushi ta ce, "Mijina kenan. Shin ka manta ni 'yar sadauki Jarata ce? Idan ka cire horon da yake bamu a filin horo, idan muka dawo gida yana sake bani na musamman domin na gaje shi.
"Tun ina yarinya ƙarama, babu abinda nafi mayar da hankali akai kamar horon takobi.
"Hakan ne yasa mahaifina ya bani horo mai kyau, sannan ya koya min "SIWOD DANS"
"A halin yanzu don kace, duk wadanda aka bamu horo tare dasu, babu wanda ya kaini ƙwarewa a "SIWOD DANS!" ba kayi laifi ba."
Aymanul Faris ya ce, "Ai ba iya wadanda aka bamu horo tare dasu, duk wani wanda kika san yana da horon SIWOD DANS kin fishi ƙwarewa a kai.
"Tabbas yau naga dalilin da yasa Ranganu ya ce tare zamuyi wannan tafiya. Ina son ki matata!"
Jaruma Riya tana jin haka tayi murmushi ta matso kusa da Aymanul Faris ta zauna ta dafa kafaɗarshi ta ce, "Nagode!"
Aymanul Faris ya rungumeta akan ƙirjinsa. Daga wannan lokaci suka yi ta nunawa junansu soyayya har saida kowa ya gamsu.
Washe gari da safe suka sake yin shiri, suka tunkari daji na ƙarshe wanda daga shi sai kogon Madarul Ansari.
Bayan tafiyar wata da watanni suka fara hango wannan daji daga can nesa.
Dajin daga nesa tamkar nahiyar azaba.
Tsaunika, bishiyoyi, ciyawi da kuma duwatsu na cikin wannan daji duk na wuta ne.
*****
*
*SIWOD DANS = SWORD DANCE*
*
Yau *22/05/2023*
Babi na gaba zaizo *25/05/2023* da izinin ALLAH.RUHIN JARUMTAKA!
*
Babi na 128: *Daular Nehiya*
*
Wannan littafin sadaukarwa ne ga Zahra...
*
U-M-S
*
~Garin Jiminis, ƙasashen Jerawa.
*
Garin ɗan ƙarami ne wanda ba zai wuce ya ɗauki gidaje dubu ba. Idan ka kallo wannan gari daga nesa babu abinda zaka gani face hayaƙi da wuta yana tashi, ga dukkan alamu garin ne yake ƙonewa.
Wannan wuta tafi wata bakwai tana ci a cikin wannan gari, amma har kawo wannan lokaci bata mutu ba.
To, amma idan ka shigo cikin wannan gari zaka fuskanci cewa, jama'a suna ta harkokinsu lafiya, babu wani abu da ya same su.
Kai kace wannan gobara ba daga cikin wannan gari take ba.
Acan bayan garin cikin wani ƙaramin daji, wani mutum ne zaune bisa wata karaga ta mulki.
Mutumin yana sanye da fararen tufafi sannan gashin kansa ya zubo har kan kafaɗunsa.
Yana riƙe da wani ƙaramin mudubi na tsafi, yana ganin abinda ke faruwa.
Abin mamaki idan kasan Barban wanda ke tare dasu Aymanul Faris zaka ga shi ne a wannan waje ba wani ba.
Abinda wannan madubi dake hannunsa ke nunawa kuwa, su sarki Kuffuru ne tare da su sarki Fairaz.
A wannan lokaci su sarki Kuffuru suna daf da ƙarasowa wannan waje da yake.
Wannan gagarumar wuta dake ci a wannan gari, ba ainihin wuta bace.
Barban ne yayi tsafi ya samar da ita a matsayin kafi wadda zata hana su sarki Kuffuru ƙarasowa.
A farkon wannan daji, sarki Kuffuru ne tare da Balwaz, Fairaz da kuma Zayyadu.
Sarki Kuffuru yana tonon wani abu da aka binne a cikin ƙasa da wata zabgegiyar takobi dake hannunsa wadda bamu taɓa kallonsa da ita ba.
Takobin tana da tsaho da kuma kauri, sannan akwai zane-zanen taurari akan ƙarfenta.
Sarki Fairaz na durƙushe a gefen Kuffuru, da zarar sarki Kuffuru ya tono abinda ke cikin rami sai Fairaz yasa hannayensa ya fasa abun, take zai tarwatse.
Abubuwan suna tarwatsewa, wannan wuta dake ci a cikin wannan daji zata soma raguwa.
Boka Balwaz da Zayyadu suna tsaye a gefe suna kallon abinda ke faruwa.
Tun safe sarki Kuffuru da Fairaz suke ta tarwatsa waɗannan kafi amma har kusan azahar basu kammala ba, saboda tsananin yawansu.
Bayan dogon lokaci suna abu ɗaya, sai suka iso wajen wani kafi mai girma kuma shi ne na ƙarshe.
Sarki Kuffuru yayi ta tonowa da takobin dake hannunsa, amma ya gagara samo ainihin tushen kafin.
Saida ya kusan shafe sa'a guda yana tono sannan ya tono ainihin tushen wannan kafi.
Fairaz yayi gaggawar dafa kafin da hannunsa sannan ya rufe idanunsa ya fara ƙoƙarin fasa shi.
Kafin yayi ta ƙanƙancewa a hannun Fairaz yana komawa ɗan ƙarami.
Kafun a jima ya dawo kamar goruba.
Gagarumin farin ciki ya lulluɓe sarki Kuffuru da tawagarsa saboda a wannan lokaci suna daf da samun nasara.
Ba zato ba tsammani wannan kafi ya tarwatse tamkar nakiya, gagarumar wuta ta sauƙa a wannan waje ta lulluɓe su sarki Kuffuru gaba ɗayansu.
Tun da suke a rayuwarsu basu taɓa jin wuta mai zafi kamar wannan ba, kafun a jima sun ruga izuwa cikin wannan daji suna neman wajen tsira.
Sarki Kuffuru ne ya fara faɗawa cikin wani ƙaramin kogi mai sanyin ruwa, wannan wuta da ta lulluɓe shi ta yaye, ya dawo hayyacinsa.
Gefen fuskar sarki Kuffuru ya ƙone, ƙiris ya hana wutar ta taɓa idonsa guda.
Wannan tabo da tayi masa a fuska, ba zai taɓa gogewa ba.
Sarki Kuffuru ya kwarara uban ihu cikin tsananin fusata, zuciyarsa ta fara tafarfasa tamkar zata ƙone.
A wannan lokaci ne, sarki Fairaz, Balwaz da Zayyadu suka shigo cikin wannan kogi.
Sarki Kuffuru na ganin shigowarsu ya haɗe fuska, ya kaiwa iska sara da wannan takobi dake hannunsa sau biyu.
Wasu ƙananun taurari jajaye suka fice daga tsinin takobin, suka tunkari Balwaz da Zayyadu.
Kafun su gama kashe wutar dake ci a jikinsu, tuni wadannan taurari na sarki Kuffuru sun dira a jikinsu.
Nan take taurarin suka juye izuwa takubba sannan suka yi filla-filla da sassan jikin Balwaz da na Zayyadu.
Sarki Fairaz yana gama kashe wutar jikinsa yayi arba da sassan jikin Balwaz da na Zayyadu suna yawo akan wannan kogi.
Cikin tsananin razana ya dubi Kuffuru ya ce, "Ya shugabana! Saboda wanne dalili zaka hallaka waɗannan mutane guda biyu da suka taimaka mana muka iso wannan waje?"
Sarki Kuffuru ya daka masa harara ya ce, "Saboda a wannan lokaci amfaninsu a wajena ya ƙare. Na taɓa ganin hirar da ta gudana tsakanin sarki Darwazu da wannan boka, na ji irin burina yake da, wannan yasa naga bayansa kafun shi yayi tunanin ganin bayana."
Sarki Fairaz yana jin haka ya risina a gaban sarki Kuffuru.
Take suka fito daga cikin wannan kogi, sarki Fairaz ya sakawa Kuffuru magani akan wannan rauni dake kan fuskarsa.
Tarwatsa wannan kafi da suka yi, yasa gagarumar wutar dake ci a wannan gari mutuwa.
A wannan waje suka yada zango, sannan suka kwana.
Washe gari da safe bayan sun yi kalaci, sarki Kuffuru ya fiddo taswirar Barban ya dubata.
Ya dubi Fairaz ya ce, "Barban yana cikin dajin dake maƙwabtaka da wannan, don haka tashi mu kai masa hari."
Sarki Fairaz yana jin haka yayi murmushi, ya miƙe tsaye ya gyara makaman yaƙinsa.
Sarki Kuffuru ya shige gaba shi kuma ya take masa baya.
Sarki Fairaz ya dubi sarki Kuffuru ya ce, "Ya shugabana! Shin kana da bayani akan daular Nehiya?"
"Na dai taɓa jin sunan, amma bani da wani bayani akanta, shin kai kana da ne?" inji Kuffuru.
Sarki Fairaz ya ce, "Daular Nehiya tana ɗauke da masarautu guda tamanin da tara, akwai biranai guda ɗari da arba'in a ƙarƙashin waɗannan masarautu.
"Akwai manyan sarakuna guda ɗari bakwai da tamanin, sannan akwai sojojin yaƙi guda miliyan ɗari tara da ɗoriya.
"Asalin wannan daula matattara ce ta manyan masu laifi na duniya. Mafi yawa daga cikin mutanen wannan daula a zamanin da, ɓarayi ne da 'yan tawaye.
"Kasancewar mutanen banza ne a wannan waje, yasa suka tara dukiya mai tsananin yawan gaske.
"Masana da yawa na ƙasata suna ganin cewa, wannan shine babban dalilin da yasa Hodon ya addabi wannan daula da sata, tun lokacin da yake kan ganiyar ƙuruciya.
"Sannan wannan shi ne babban dalilin da yasa waɗannan sarakuna na wannan daula suke son ganin an kama Barban.
"Damuwar masu wannan daula shi ne, rayuwar Hodon ta wulaƙanta ba wai abinda ya sace musu ya sake dawowa ba.
"Saboda har yayi satar nasa ya gama, bai iya sato kambun-zinari dake ajiye a daular ba."
Sarki Kuffuru yana jin wannan batu ya cika da tsananin mamaki, daga can ya ce, "Shin kana nufin daular Nehiya ita ce zata dawo ƙarƙashin ikona?"
Sarki Fairaz ya gyaɗa masa kai.
"Masarautu tamanin da tara, biranai guda ɗari da arba'in, manyan sarakuna guda ɗari bakwai da tamanin da kuma sojoji miliyan ɗari tara?" inji sarki Kuffuru cikin al'ajabi.
Sarki Fairaz ya gyaɗa kai ya ce, "Bayan wannan rabin sojojin wannan daula, ba mutane bane. Daga sa'adda Barban yayi wannan mummunar ɓarna a wannan daula daga wannan lokaci aka fara ƙirƙirar waɗansu irin dakaru.
"Waɗannan dakaru suna da siffa ta mutane amma sun fi mutane zafin nama da ƙarfin damtse nesa ba kusa ba.
"A wannan daula ana kiransu da suna *UMKAS*"
Sarki Kuffuru yana jin wannan batu gagarumin farin ciki, ya sake lulluɓe shi.
Tabbas idan ya mulki daular Nehiya zai zamo gawurtaccen sarkin da ba'a taɓa yin kamar sa a tarihin duniya ba.
Babu wani abokin gaba da zaiyi shakka, sai dai shi ayi shakkarsa.
Haka dai suka ci gaba da tafiya suna tattaunawa akan wannan daula, sannan lokaci-lokaci suna kawo magana akan abokan gaba.
Bayan ɗan lokaci suka iso wannan daji wanda Barban yake zaune a cikinsa.
Tun daga nesa suka hango Barban zaune akan wannan karaga ya ƙura musu idanu.
Sarki Kuffuru da Fairaz suka zaro takubbansu sannan suka tunkari Barban gadan-gadan.
Kafun su iso Barban ya nuna su da hannunsa guda, take wadansu manya-manyan bishiyoyi da suke kewaye dajin, suka fara juyewa izuwa waɗansu irin halittu masu riƙe da sunguma.
Suka afkawa su sarki Kuffuru da yaƙi.
Nan take su sarki Kuffuru suka tare aka fara gumurzu.
Waɗannan halittu basa jin sara sannan basa jin suka, babu abinda ke tasiri akansu.
Don haka kafun a jima su sarki Kuffuru sun fara galabaita.
Cikin tsananin shammata sarki Fairaz ya zille daga tsakiyar waɗannan halittu, ya koma tsakiyar wannan daji ya fara tonon waɗansu abubuwa da hannayensa.
A duk lokacin da ya tono kamar guda biyar, saiya ɗaga su sama ya doka da ƙasa duk su fashe, sannan ya sake tono wasu.
Fara hakan keda wuya waɗannan halittu dake gwabza yaƙi da sarki Kuffuru suka fara mutuwa, suna zamowa turɓaya suna bajewa a cikin wannan daji.
Barban ya zaro idanu cikin tsananin mamaki. Karo na farko yaga mutumin da yake iya fidda kafi.
Kafun a jima Fairaz ya gama tono dukkan waɗannan kafi dake wannan waje sannan ya ƙone su.
Dukkan dakarun da suka kewaye sarki Kuffuru suka ƙone ƙurmus, babu abinda ya rage a wannan daji idan ba su da Barban.
Sarki Kuffuru yayi murmushi ya ɗaga takobinsa sama, ya ruga da gudu wajen Barban zai kama shi.
Koda ya rage saura bai wuce taku uku ya isa inda wannan karaga take ba, sai ya daka tsalle sama da nufin ya dira akan Barban.
Wata murtuƙeƙiyar bishiya ta lanƙwaso ƙasa, reshenta guda ya doki ƙirjin Kuffuru da ƙarfi, lamarin da yasa ya faɗi acan baya kenan, yana aman jini.
Cikin tsananin mamaki ya miƙe zaune yana goge wannan jini dake zuba daga bakinsa.
Barban yayi murmushi ya kaɗa hannunsa guda, take waɗannan ramuka da Fairaz ya tono waɗannan kafi a cikinsu suka fitar da wani sanyi mai ban al'ajabi.
Kafun a jima sanyin ya cika wannan daji gaba ɗaya, nan take sarki Fairaz yaji jikinsa ya fara mutuwa barci ya fara ƙoƙarin lulluɓe shi.
Cikin tsananin mamaki ya girgije ya miƙe tsaye, ya goge idanunsa.
Wannan sanyi na ci gaba da sauƙa, Fairaz ya bingire a ƙasa ya fara minshari.
Waɗansu gabza-gabzan bishiyoyi dake bayan Barban suka fara tunkaro Kuffuru gadan-gadan.
Sarki Kuffuru na ganin haka, ya ɗaga wannan takobi dake hannunsa, ya kaiwa iska sara da ita.
Manya-manyan taurari jajaye suka fice daga tsinin takobin suka doki waɗannan bishiyoyin da ƙarfi.
Bishiyoyin suka rabe gida biyu amma daga bisani suka sake haɗewa a waje guda, suka ci gaba da tunkarar sarki Kuffuru.
Kafun ya sake kai musu wani harin, tuni sun saka manya-manyan rassansu sun yi masa kyakkyawan duka.
Sarki Kuffuru yayi tsalle ya faɗo acan baya, bakinsa da hancinsa ya fashe, idanuwansa suka yi duhu.
A wannan lokaci Barban ya miƙe tsaye daga kan wannan karaga tasa, ya tunkaro inda sarki Kuffuru ke kwance.
Barban ya nuna Kuffuru da hannu guda ya ce, "Abin kunya ne a gareni ace ragwaye kamar ku, sun yi tunanin kama ni.
"Kuma zan yi muku hukunci bisa hakan,"
To, a lokacin da Barban yake wannan magana wani sarki Fairaz ɗinne a matsayin haske ke tunkaro shi.
Barban da Kuffuru duk basa kallon tahowarsa, har ya iso gaban Barban ya fiddo wata ankwa daga cikin rigarsa.
Fairaz yasa ƙwatar takobinsa ya doki gwiwowin Barban, take Barban ya sulale ƙasa kan gwiwowinsa.
Fairaz ya kamo hannayensa ta baya, ya saka wannan ankwa ya ɗaure su tamau.
Sarki Kuffuru ya dago kansa cikin tsananin mamaki. Baya kallon sarki Fairaz a wannan lokaci.
Wancan sarki Fairaz dake kwance yana minshari ya miƙe tsaye yayi girgiza, take wannan haske na ruhinsa ya ɓace yaje ya shiga cikin jikinsa.
Yazo gaban Barban ya tsaya ya ce, "Tun da kayi kuskure ka hadu da ikon Adbenchan ka shiga hannu, yau ce ranar ƙarshe ta baƙar sana'arka!"
Barban yayi murmushi ya ce, "Sana'ata bata da ƙarshe face na cimma babban burina, ko ina zaku kaini a duniya, hakan ba zai hana ni cimma burina ba..."
Sarki Kuffuru yayi dariyar mugunta ya ce, "Zancen banza kenan, yau zaka ga ainihin shirin mu!"
Sarki Kuffuru yana gama faɗin haka, ya tafa hannayensa sau uku wannan shirgegen aljani nasa ya bayyana.
Nan take ya umarci wannan aljani ya ɗauke su, su uku.
Aljanin ya ɗauke su sannan ya buɗe fuka-fukinsa ya tashi sama.
Bayan doguwar tafiya suka dira a tsakiyar wannan daji wanda magini Gidr ya gina musu.
Sarki Kuffuru yaje bakin ƙofar shiga wannan kurkuku, ya dafa ta da hannunsa guda.
Nan take zanen wasu ɗalasimai suka bayyana a jikin ƙofar suka fara haske, kafun daga bisani tayi ƙara ta buɗe.
Sarki Kuffuru da Fairaz suka ingiza ƙeyar Barban suka saka shi cikin wannan kurkuku, sarki Kuffuru ya sake buɗe wata ƙofa ta ƙarƙashin ƙasa.
Sarki Kuffuru ya tura Barban cikin wannnan ɗaki, sannan ya baiwa Fairaz umarnin rufeta.
Sarki Fairaz ya dafa wannan ƙofa da hannunsa guda, hasken waɗannan ɗalasimai ya fara ɓacewa yana shigewa cikin wannan ƙofa.
Hasken yana gama ɓacewa ƙofar ta koma ta rufe.
"Ka shiga kenan," inji sarki Kuffuru. "Dukda cewa babu mai iya kuɓutar da kai daga wannan kurkuku, zamu turo dakaru dubu suna gadinka..."
Barban yayi murmushi ya ce, "ZAN GIRGIZA DUNIYA,"
Kuffuru da Fairaz suka yi murmushi, suka juya suke fice daga cikin wannan kurkuku, suka kulle ƙofarta ta waje.
Ita wannan kurkuku bata amfani da kwaɗo, ɗalasimai kawai ake amfani dasu wajen kulleta.
Sarki Kuffuru yana amfani da hannayensa wajen buɗeta, shi kuma Fairaz yana amfani da hannayensa wajen kulleta.
A wannan rana sarki Kuffuru da Fairaz suka sami nasarar kama sarkin ɓarayin duniya KILAWUD BARBAN.
Lokacin da suka fito daga cikin wannan kurkuku, sai sarki Kuffuru ya zaro wata takarda mai kauri ya warwareta take hoton sa'adda suke tura Barban cikin wannan kurkuku ya bayyana.
Sarki Kuffuru ya miƙawa Fairaz takardar ya ce, "Kaje daular Nehiya ka nuna musu wannan hoton, sannan ka shaida musu SARKINSU yana zuwa bayan gobe..."
Sarki Fairaz ya risina ya karɓi wannan takarda sannan ya juya zai tafi.
Saida ya ɗan yi nisa kaɗan ya juyo ya dubi Kuffuru ya ce, "Ya shugabana! Ina so ka bani dama idan Barban

Please Login or Register in order to submit comment