Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

jefawa cikin wannan tafki.
Ranganu da Hodon suna wurge a ƙasa, kamar baza su iya wani motsin kirki ba.
Ana gama watanda da naman wadannan bayi aka tunkaro Ranganu da Hodon su ma za'a kaisu wajen shugaban dakaru.
Koda yaga su ne sai ya jefar da wannan adda dake hannunsa, ya zaro sabuwa wadda tafi ta farkon kaifi da kauri nesa ba kusa ba.
Saura ƙiris a damƙawa wannan mutumi su Ranganu, Ranganu ya zaro wata ƙaramar wuƙa sannan yayi amfani da ita cikin zafin nama ya cakawa dakarun dake riƙe dashi.
Dakarun suka yi ihu sannan suka zube ƙasa matattu. Ranganu ya sake amfani da wannan adda ya cakawa waɗanda ke riƙe da Barban su ma suka sulale ƙasa matattu.
Wannan shirgegen sadauki na ganin haka ya daka tsalle ya dira a gaban Ranganu sannan ya kawo masa wawan sara da wannan adda.
Ranganu ya goce cikin zafin nama, sannan ya doki ƙirjin sadaukin da ƙafarsa.
Sadaukin yayi tsalle ya faɗa cikin wannan tafki, kafun yayi wani yunƙuri ya nutse a cikin tafkin.
Ranganu ya juya a fusace ya karkashe dukkan dakarun dake wannan waje, sannan shi da Hodon suka daka tsalle suka faɗa cikin wannan tafki.
Saida suka yi tafiya ta kusan kamu tamanin a cikin ƙasusuwa da gurɓataccen jini sannan suka iso ƙarƙashin wannan tafki inda yafi ko'ina tsafta.
A wajen wannan tafki kuwa, akwai dakaru dake bisa dogwayen ganuwowi sun ga dukkan abubuwan da suka faru.
Cikin gaggawa suka busa ƙaho, sarkin dake kula da wannan waje gaba ɗaya ya ƙaraso.
Nan take suka sanar dashi abinda ya faru.
Sarkin dakarun yayi dariyar mugunta sannan yasa aka kawo masa dakarun da suka fi kowa iya nutso ya basu umarnin shiga wannan tafki, su ɗauko masa waɗannan bayi ku su ko kuma gawarwakinsu.
Dakarun suka daka tsalle suka nutse a cikin tafkin.
Ranganu da Hodon suna tsaitsaye kawai suka ga dakaru guda biyar sun diro a gabansu.
Ranganu yayi murmushi dama abinda yake jira kenan, cikin gaggawa yasa takobinsa ya sare su duk suka mutu.
Nan take ya guntulewa mutum biyu daga cikin kawuna, sannan ya cire kayan jikinsa ya yiwa ɗayansu musanya.
Ya baiwa Hodon ma, wannan umarni.
Hikimarsa a nan ita ce, idan aka ga gawarwakin da kayan bayi za'a ɗauka su ne suka mutu.
Ranganu yayi girgiza ya juye izuwa ƙatoton kifi, sannan ya haɗiye Hodon yayi nutso izuwa can ƙarƙashin wannan tafki ya fara tsala azababben gudu fiye da tunanin mutum.
Ranganu da Hodon sun sami nasarar ɗauke wannan hular sarauta, sannan wannan shi ne karo na farko da Hodon yayi sata bai ajiye wannan hatimi nasa ba.
Babu wanda yasan dalili face shi da kuma Ranganu.
*
Sa'a guda na shuɗewa shugaban dakarun dake tsaron wannan yanki yaga gawarwakin dakarun da ya tura ɗauko wadannan bayi ta taso saman ruwa.
Ransa ya ɓaci yana shirin shiga cikin tafki, yaga gawarwaki guda biyu sun taso daga cikin wannan tafki sanye da kayan bayi amma dukkansu basu da kai.
Yana ganin haka yayi dariya ya ce, "Na san cewa, tun da suka yi kuskuren shiga wannan waje sai sun hallaka. Wannan waje shi ne kogin jini, kogin halaka."
Yana gama faɗin ya tunkari ginin tsohuwar husumiyar nan, zai ɗauko hular sarautar babban sarki domin mayar da ita cikin sabon gini.
Yana zuwa ya buɗe ƙofar shiga ya shiga cikin husumiyar ya tunkari hular da yake hangowa daga nesa.
Sai dai yana zuwa gaban hular ya miƙa hannu zai ɗauketa amma bisa mamaki sai yaji hannunsa ya wuce ta cikinta tamkar haske ya shafa.
Sadaukin ya cika da tsananin mamaki ya duba hannunsa da kyau, ya sake taɓa hular amma sai yaji babu komai a wajen.
Ya taɓa abinda ke gefenta yaji ya taɓa. Nan take ya tabbatar da cewa, lallai wannan hula an saceta.
Sadaukin ya taƙarƙare ya kwarara uban ihu wanda ya cika wannan gidan sarauta gaba ɗaya, ya durƙusa kan gwiwowinsa yana kuka.
Cikin tsananin baƙin ciki da fusata ya zaro takobinsa ya cakawa kansa ita, ya kashe kansa. A ganinsa wannan hanya ita ce kaɗai zai ceci kimarsa saboda an sace abinda yafi komai daraja a ƙarƙashin tsaronsa.
Kafun a jima sarki Kuffuru ya ƙaraso wannan waje a guje.
Bayan nazari da bincike sarki Kuffuru ya dubi wadannan mahukunta guda goma ya ce, "Duk yadda aka yi Marganu ne ya sace wannan hula. Tun da Hodon yana tsare a hannunmu, babu yadda za'ayi ya sace wannan hula.
"Kuma idan kuka yi duba, zaku ga cewa da zallar jarumtaka kawai aka yi amfani wajen wannan sata."
Mutanen guda goma suka gyaɗa kai, alamun haka zancen yake.
******
Yau *12/06/2023*
Babi na gaba zaizo *15/06/2023* da yaddar ALLAH.RUHIN JARUMTAKA!
*
Babi na 138: *Komawa Daular Shaha*
*
Wannan littafin sadaukarwa ne ga Zahra...
*
U~M~S
*
Sai da Aymanul Faris da jaruma Riya suka sake shafe kwanaki goma suna tafiya sannan suka iso birnin Darul Barban.
Aymanul Faris ya tara dukkan jama'ar wannan gari, ya sanar dasu saƙon babban sarki.
Nan take hankalin kowa dake garin ya tashi, Aymanul Faris ya bayar da umarnin fara shirye-shiryen komawa daular Shaha.
Daga nan suka wuce izuwa gidan Hajriya, inda suka hangota zaune a tsakiyar wani falo tare da gimbiya Jaanu suna tattaunawa.
Gagarumin farin ciki ya lulluɓe Aymanul Faris, tun daga nesa suka ƙurawa juna idanu, shi da gimbiya Jaanu.
Yana ƙarasowa wannan waje ya rungume mahaifiyarsa cikin tsananin farin ciki.
Aymanul Faris ya bata labarin yadda suka karya duk wani kafi dake birnin Shaha da kuma yadda suka ziyarci Jerawa da Hajarr suka sanar dasu umarnin babban sarki.
Ya sake shaida mata cewa, dukkan waɗannan garuruwa guda biyu a halin yanzu suna ta shirye-shiryen komawa daular Shaha, kuma a cikin abinda bai wuce mako biyu ba zasu koma.
Cikin tsananin farin ciki Hajriya ta dube shi ta ce, "Lallai kayi ƙoƙari, ɗana. Idan ka farkar da sirrin dake cikin jininka, ina so ka ɗauke ni, ka kaini daular Shaha domin na binne ɗalasiman da nayi gado a wajen mahaifina na sirrin noma."
Aymanul Faris yayi godiya sosai ga mahaifiyarsa. Babbar daula kamar Shaha tana buƙatar sirrin noma na musamman kamar wanda suke dashi a baya.
Koda Hajriya ta fuskanci cewa, kamar Aymanul Faris yana so yayi magana da gimbiya Jaanu kuma yana kunyar idanunta, sai ta miƙe tsaye. Ita da jaruma Riya suka fita daga cikin wannan falo, ta ce bari ta kawo musu abinci.
A wannan rana, gimbiya Jaanu doguwar riga ta saka wadda ta ɗan wuce cinyoyinta da kaɗan.
Jaruma Riya da mahaifiyar Aymanul Faris suna fita daga cikin wannan falo, Jaanu ta miƙe tsaye ta faɗa kan ƙirjin Aymanul Faris ta fashe da kuka.
Hankalin Aymanul Faris yayi mummunan tashi ya shiga lallashinta, da ƙyar ya samu ya shawo kanta.
Cikin sheshsheƙa ta dube shi ta ce, "Marganu ya cuceni, ya cutar da rayuwata. Ba don ina tare da kai ba, da tuni na kashe kaina. Saboda wannan cin mutuncin da yayi min, shi ake yiwa mace na ƙarshe a rayuwarta wadda yafi kowanne ciwo."
Aymanul Faris yana jin haka tausayinta ya kama shi ya ƙanƙameta a ƙirjinsa ya ce, "Kiyi haƙuri, masoyiyata. Tabbas zai fuskanci hukuncin da ya dace akan wannan laifi da ya aikata. Wanne irin hukunci kike so, muyi masa?"
Gimbiya Jaanu ta ce, "Babu wani hukunci da za'a yi masa a duniya wanda zai sa na huce wannan abin takaici da yayi min, zanyi tunani akan hakan."
Aymanul Faris ya ce, "Ko domin taɓa min ke da yayi, sai na hukunta shi. Fatan dai, jikin naki yayi sauƙi yanzu?"
Gimbiya Jaanu tayi guntun murmushi ta ce, "Jikina yayi sauƙi. Kowanne lokaci daga yanzu, za'a iya ɗaura mana aure..."
Aymanul Faris yana jin haka gagarumin farin ciki ya cika ransa.
A duk sa'adda jikinsa yake jin ɗumin na gimbiya Jaanu, wani irin aminci na musamman na zuwa ransa.
"Mun kusa mu yi aure domin shiga sabon babi na rayuwa..." inji Aymanul Faris.
Haka dai Aymanul Faris da gimbiya Jaanu suka yi ta tattaunawa cikin soyayya har tsahon ɗan lokaci.
Jaruma Riya da Hajriya suka sake dawowa cikin wannan falo, cikin gaggawa Aymanul Faris ya janye jikinsa daga na Jaanu sannan ya matsa kusa da Riya lokacin da take saka musu abinci a cikin faranti.
Nan take dukkansu su huɗun suka haɗu a waje guda, suka ci abincin.
Bayan sun kammala Aymanul Faris ya shaidawa Hajriya cewa, gimbiya Jaanu ta samu lafiya kuma za'a iya wannan aure a kowanne lokaci.
Farin ciki a wannan falo dai, ba'a cewa komai.
Jim kaɗan, Barban da Ranganu suka bayyana tsulum a cikin wannan falo.
Aymanul Faris yana ganinsu ya cika da tsananin mamaki ya dube su ya tambaye su daga ina suke?
Kafun Ranganu ya ce komai, kawai sai yasa hannunsa a cikin rigarsa ya fiddo wannan hular sarauta wadda suka ɗauko a daular Nehiya.
Ya ajiye wannan hular sarauta a tsakiyar wannan ɗaki.
Duk da cewa akwai hasken rana sosai a wannan lokaci, amma saida hasken wannan hula ya sake dallare wajen.
Tun da su Aymanul Faris suke a duniya, basu taɓa ganin abu mai daraja kamar wannan hular sarauta ba.
Kallonta kawai idan mutum yayi yasan cewa, bata ƙananun sarakuna bane.
Irinta manyan sarakuna ne masu mulkar duniya.
Ranganu ya dubi Hajriya ya ce, "Wannan ita ce asalin hular sarautar Samudul Ansari wadda daular Nehiya suka sace a shekarun baya.
"A yanzu mun samu nasarar ɗaukota, kuma zamu damƙata ga sabon sarkin da zai mulki daular Shaha. Ina nufin Aymanul Faris."
Koda jin wannan batu sai Aymanul Faris da Hajriya suka yi ta yiwa Ranganu godiya.
"Babu komai," inji Ranganu. "Gobe zamu ɗaura aure tsakanin Aymanul Faris da gimbiya Jaanu. Ko a wannan gari namu, babu wanda zamu bari yasan anyi auren, saboda tabbatar da tsaro."
Hodon ya tari numfashin Ranganu ya ci gaba, "Saboda bama so a sake samun matsala. Idan Aymanul Faris ya farkar da jininsa, zamu koma birnin Shaha domin sake kafa birnin."
Bayan ɗan lokaci suna tattaunawa sai suka yi sallama da juna suka watse daga wannan waje.
Jaruma Riya da Hajriya suka shirya gagarumin biki a cikin wannan gida nasu, ba tare da labari ya fita waje ba.
Tsahon wannan dare Aymanul Faris da gimbiya Jaanu shafe lokaci suka yi, suna ta nunawa junansu soyayya.
Washe gari da sassafe aka tashi da wani irin baƙon yanayi a wannan gari.
Rana ta fito amma akwai wani abu baƙi-baƙi kamar gajimare da ya tare haskenta.
Hadimai suka dafa abinci a cikin gidan su Aymanul Faris.
Jaruma Riya da kanta ta yiwa gimbiya Jaanu ado na gaban kwatance.
Daf da azahar aka ɗaura auren AYMANUL FARIS da gimbiya JAANU a cikin wannan gida.
Idan ba hadiman gidan da kuma su Aymanul Faris ba, babu wanda yasan ma anyi auren.
Aka daura aure a bisa tsarin al'ada irinta Banu Kuyuru.
Bayan la'asar Hajriya da kanta ta yiwa Jaanu gyara na musamman irin na amare, sannan ta duba ƙasan gimbiya Jaanu da kyau, ta tabbatar da cewa koda mijinta ya kusanceta ba zata sake samun matsala ba.
A taƙaice dai, wajen ya warke sannan wannan gyara da aka yi mata yasa wajen ya koma kamar da.
Ana magariba jaruma Riya da kanta ta kaiwa Aymanul Faris gimbiya Jaanu cikin wani ƙasaitaccen ɗaki na musamman wanda aka tanadar musu musamman domin wannan rana ta daren farko.
Jaruma Riya ta zaunar da Jaanu akan wani katafaren gado ta dubeta ta ce, "Ƴar-uwa ki nunawa masoyinmu soyayya a yau."
Gimbiya Jaanu tayi murmushi ta sunkuyar da kanta ƙasa.
Nan take suka yi sallama da juna, jaruma Riya ta fice daga cikin wannan ɗaki.
Aymanul Faris yana tare da su Hodon suna yi masa bayanin yadda abubuwa zasu kasance.
"Ka san wani ya taɓa shigarta, don haka kada kayi mata da ƙarfi!" inji Hodon.
Aymanul Faris ya gyada kai, alamun zaiyi hakan.
Nan take yayi sallama da su Hodon, ya bar wannan falo da suke ya tunkari wani ƙaramin banɗaki.
Aymanul Faris ya shiga cikin wannan ƙaramin banɗaki ya watsa ruwa, sannan ya tunkari ɗakin amarya daga shi gajeren wando.
Yana shigowa cikin ɗakin yayi arba da gimbiya Jaanu zaune akan gado ta sunkuyar da kanta ƙasa.
Ga abinci wajen kala ashirin a jere a gabanta.
A hankali ta ɗago kanta ta kalle shi.
Take tayi arba da murɗaɗɗen jikinsa wanda a wannan lokaci yake bayyane babu abinda ya rufe shi.
Gimbiya Jaanu tayi murmushin jin daɗi, abinda ta daɗe tana jira kuma tana mafarkin samu, yau gashi yazo.
Aymanul Faris ya zauna a gefen wannan gado sannan ya ɗaura hannunsa guda akan nata.
Wani irin abu ya ratsa su duk su biyun, cikin gaggawa suka ɗago kai suka kalli juna.
Aymanul Faris ya fara magana da cewa, "Ina farin ciki da zuwan wannan rana. Tun sa'adda nayi arba dake, bani da burin da yafi ace na mallake ki.
"Godiya ta musamman,"
Yana gama faɗin hakan ya ɗauko farantin abinci guda, ya fara bata da hannunsa har sai da ta ƙoshi.
Koda ya fuskanci abinci ya isheta sai ajiye farantin a gefe, sannan ya rungumeta a ƙirjinsa.
A hankali, a hankali Aymanul Faris ya tuɓe mata dukkan wani sutura dake jikinta.
Tana bayyana haihuwar uwarta sai da ya miƙe tsaye ya koma gefen wannan gado, ya ƙurawa kyakkyawar surarta idanu yana al'ajabi a ransa.
A wannan lokaci tana kwance akan wannan gado, idanuwanta a lumshe.
Gashin kanta mai kyakkyawan launi na tarwatse akan gadon, kyawawan hannayenta na dafe akan ƙirjinta ta rufe su.
Aymanul Faris ya kashe wutan wannan ɗaki, ya koma kan gadon yaci gaba.
Sa'adda ya samu nutsuwa da ita kuwa, sai wani gagarumin duhu wanda ya ninka na cikin wannan ɗaki ya lulluɓe wajen.
Tsahon daƙiƙu talatin, kafun wannan duhu gaba ɗaya ya yaye. Wani irin farin haske ya gauraye ɗakin gaba ɗaya.
Gimbiya Jaanu tana kwance lulluɓe da wani farin bargo, ta buɗe idanuwanta a hankali.
Aymanul Faris ta hango durƙushe a tsakiyar wannan ɗaki ya haɗe hannayensa a waje guda, sannan yana furta wata kalma guda ɗaya wadda bata san ma me yake cewa ba.
Gimbiya Jaanu ta ci gaba da kallon abinda ke faruwa cikin tsananin mamaki.
Jim kaɗan wani irin iko na musamman ya sauƙo cikin wannan ɗaki.
Gimbiya Jaanu ta gagara motsa koda ɗan yatsanta, saboda ƙarfin wannan iko.
A hakan ta daure ta ci gaba da kallon abinda ke faruwa.
Aymanul Faris ya miƙe tsaye, lokacin da wani baƙin hayaƙi ya soma sauƙowa a cikin wannan ɗaki.
Gimbiya Jaanu tana fara kallon wannan baƙin hayaƙi, ruhinta ya soma girgiza tamkar zai tarwatse.
Cikin gaggawa ta miƙe tsaye sannan ta zube akan gwiwowinta tayi mubaya'a, saboda wannan abu shi ne kawai zai ƙwaceta.
Wannan baƙin hayaƙi na gama cika wannan ɗaki, siffar wani zabgegen mutum ta bayyana a cikinsa.
Wannan mutumi baya numfashi, baya baƙin ciki, baya farin ciki, kai zaka ce baya motsi ma, saboda kamar gunki haka yake tsaye shirim a gaban Aymanul Faris.
A wannan lokaci, asalin surarsa ta bayyana yadda mutum zai iya ƙare masa kallo.
Mutumin dogo ne sosai, fasali da zubin jikinsa tamkar na Aymanul Faris.
Abinda ya bambanta su da Aymanul Faris shi ne, wannan halitta bai da kamanni kamar na mutane.
Komai na jikinsa a lulluɓe yake da baƙin hijabi.
Daga sama har ƙasa wata doguwar baƙar alkyabba ce a jikinsa mai samfurin kayan yaƙi.
A kansa kuma, wata irin hular sanyi ce mai zubin hular ƙarfe amma da auduga mai kauri aka ɗinka ta.
Wannan hular sanyi ta zamo tamkar shingen-tsafi wadda ta ɓoye fuskar sa.
Gimbiya Jaanu ta samu damar yiwa wannan halitta kallo na tsahon daƙiƙu biyar kacal, kafun ruhinta ya ci gaba da girgiza zai tarwatse.
Bisa dole Jaanu ta sake zubewa ƙasa ta sake yin mubaya'a.
"NI ARYA 'YAR HARUN NAYI MUBAYA'A GA TAU'RIN!" shi ne kawai abinda ya fita daga bakinta.
Ga dukkan alamu itama kanta bata san ta furta waɗannan kalmomi ba.
Aymanul Faris da wannan mutumi suka yi kallon-kallo, kafun mutumin ya zube a gaban Aymanul Faris ya yi mubaya'a shima.
"AN HALICCE NI DOMIN NAYI BIYAYYA [A GARE KA]
"NUMFASHINA SHI NE BIYAYYA [A GARE KA]
"ABINCINA SHI NE BIYAYYA [A GARE KA]
"RUWAN SHA NA SHI NE BIYAYYA [A GARE KA]
"BARCINA SHI NE BIYAYYA [A GARE KA]"
Wannan mutumi ya furta waɗannan kalmomi a cikin wata irin murya.
Muryar bata da kaushi, bata da taushi, bata nuna farin ciki sannan bata nuna baƙin ciki. Akwai iko na musamman a cikinta wanda yake sawa dole mutum ya nutsu ya saurareta.
Wannan mutumi na gama faɗin waɗannan kalmomi ya sake juyewa izuwa baƙin hayaƙi, sannan ya cikin jikin Aymanul Faris ta idanuwansa.
Aymanul Faris yayi shuru tsahon daƙiƙa ɗari da arba'in, har wannan baƙin hayaƙi ya gama shigewa izuwa cikin jikinsa.
Nan take gaba ɗaya jikinsa ya sauya.
Murɗewar jikinsa a yanzu ta ninka na da sau uku.
Ƙarfin damtsensa na yanzu ya ninka na da sau arba'in.
Wani kwarjini ya bayyana a gare shi wanda duk sarakunan duniya babu mai rabinsa.
A wannan siffa da Aymanul Faris yake, babu wanda ya isa ya tsaya a gabansa su yi cacar baki.
Babban sarki ne, wanda bin umarninsa ya zamo dole.
Gimbiya Jaanu ta sake buɗe idanunta cikin tsananin mamaki, ta ƙurawa Aymanul Faris idanu.
Karo na farko a rayuwarta taga mutumin da ko sarkin aljanu na duniya, bai isa ya kaishi kwarjini ba.
Aymanul Faris ya tako sawayensa a hankali ya tunkarota.
Yana tafiya a cikin wannan ɗaki amma duk wata halitta dake rayuwa a ɗakin tana yin biyayya ga ikonsa.
Idan ka cire ɓangaren gimbiya Jaanu, kowa dake rayuwa a birnin Darul Barban a wannan rana saida ya farka.
Ikon tau'rin ya kewaye dukkan wannan gari, ya yiwa jama'a sallama.
Aymanul Faris yana ƙarasawa gaban gimbiya Jaanu ya rungumeta a ƙirjinsa, yana mai tsananin godiya a gareta.
"KA SAMU CIKAKKEN ƘARFI NA," wata murya ta yiwa Aymanul Faris magana wadda yake da yaƙini a ransa, shi kaɗai yaji abinda take faɗa.
"TUN DA ISRABIL YA BAYYANA AYYUKA GUDA UKU NE A GABAN MU," muryar ta ci gaba da jawabi.
"AIKI NA FARKO - MAYAR DA BIRNIN SHAHA, BIRNIN AMINCI.
"AIKI NA BIYU - FARMAKAR ISRABIL.
"AIKI NA UKU - CIKA BURIKAN SARKI SAMUDUL ANSARI.
"IDAN KA KAMMALA WAƊANNAN AYYUKA GUDA UKU, ZAN ZAUNA A JIKINKA HAR ZUWA ƘARSHEN RAYUWATA!"
Aymanul Faris yana jin wannan batu ya kwantar da Jaanu akan wannan gado sannan ya yi shuru yana tunani.
"Shin zaka yi min bayanin kowanne daga cikin wadannan ayyuka guda uku, tau'rin?" Aymanul Faris ya tambaye shi.
"Zan kasance mai sanar da kai kowanne aiki a lokacin da zaka aiwatar dashi. Yanzu aikin dake gabanmu shi ne mayar da birnin Shaha, birnin aminci.
"Hakan ba zata yiwu ba, face an farfaɗo da albarkar noma sannan an sake samar da dakaru na musamman wadanda zasu kare wannan birni daga sharrukan maƙiya.
"Mahaifiyarka zata iya farfaɗo da albarkar noma, kai kuma zaka iya samar da dakarun da zasu kare daular."
Aymanul Faris ya ce, "Haka ne. Abinda ban gane ba shi ne, ta ya ya zan samar da waɗannan dakaru waɗanda ƙarfinsu zai kai na ma'abota Bankai da kuma UMKAS?"
"Abu ne mai sauƙi. Mutum dubu kacal zaka ware, ka bamu sunayensu, na rubuta a allon-ruhi.
"Da zarar nayi hakan, zasu fara sarrafa baƙin hayaƙi, babban sirrina."
Aymanul Faris yana jin haka ya ce, "Zan yi hakan,"
Yana gama faɗin haka ya ƙarasa kan wannan gado, ya rungume Jaanu.
"Gobe zamu koma asalin daular mu ta Shaha." inji Aymanul Faris.
Gimbiya Jaanu tayi murmushi ta ce, "Gaskiya nayi dacen samun namiji."
Aymanul Faris ya mayar mata da martanin murmushi mai taushi ya ce, "Ko meyasa kika ce haka?"
"A bar maganar kawai," inji ta.
Haka dai Aymanul Faris da matarsa Jaanu suka ci gaba da tattaunawa cikin soyayya har dare ya gama rabawa, dukkansu suka yi barci.
Washe gari tun da sassafe Aymanul Faris, Hajriya, jaruma Riya, Jaanu da kuma su Hodon suka gama shiryawa domin zuwa daular Shaha.
Nan take dukkansu suka tunkari birnin bisa aljanun su.
Bayan ɗan ƙanƙanin lokaci suka iso birnin'
Tun a ƙofar shigowa wannan birni, Hajriya da Aymanul Faris suka fara ziyartar manya-manyan dazuzzuka na wannan daula tana binne wadansu abubuwa.
Aymanul Faris ya lura da cewa, a duk dajin da ta binne waɗannan abubuwa damshi da albarkar noma na sauƙa a cikin dajin.
Tunda safe suka fara wannan aiki, amma sai bayan la'asar suka kammala.
Wata iska mai kama da ta tsakiyar damina ta fara kaɗawa a cikin daular Shaha.
"Albarkar noma irin wanda aka samu a zamanin Samudul Ansari ya sauƙa a wannan daula. Ubangiji ya tayaka riƙo," inji Hajriya.
Aymanul Faris yayi murmushin jin daɗin wannan addu'a da tayi masa.
"Adalci zai sake shimfiɗa a wannan daula. Zan kare daular Shaha daga sharrin ISRABIL da duk wani abokin gabarta. Zan karya zalunci, na kafa adalci!" inji Aymanul Faris.
Hajriya tayi murmushi ta ce, "Waɗannan burika ne masu kyau. Fatan mu shi ne ka cika su."
Haka dai Aymanul Faris da Hajriya suka ci gaba da tafiya suna tattaunawa har suka iso cikin birnin Shaha.
Lokacin da suka iso gidan sarautar Shaha sai Aymanul Faris da matansa guda biyu suka fara kewaya gidan sarautar suna ganin tsantsar kyawunta.
Hodon ya shaidawa su Aymanul Faris cewa, nan da cikar kwanaki uku kacal! dukkan jama'ar wannan birni zasu ƙaraso.
*****
Yau *15/06/2023*
Babi na gaba zaizo *17/06/2023* da izinin ALLAH.RUHIN JARUMTAKA!
*
Babi na 139: *SIWOD-DEL-BULOD*
*
Wannan littafin sadaukarwa ne ga Zahra...
*
U~M~S
*
~Daular Gorgon.
*
Runduna ce ta manya-manyan aljanu keta shawaƙi a sararin samaniya ɗauke da tarin mayaƙa masu tsananin yawan gaske.
Dukkan mayaƙan suna sanye da sulken-yaƙi ruwan ƙasa da mahaukatan makaman yaƙi rirriƙe a

Please Login or Register in order to submit comment