Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

aka rasa.
"Wannan yasa bayan na tabbatar da an sace abubuwan na gudanar da bincike akan inda suke da kuma waɗanda keda mallakinsu.
"Dukkan waɗannan abubuwa suna rubuce a cikin wani ƙaramin littafina. A hankali a hankali, duk sai mun sake mallakarsu kamar da.
"Bayan na rubuta wadannan abubuwa a cikin wannan littafi ne, na fara tunanin ta ya ya za'ayi na sake mallakarsu?
"Saboda da yawa daga cikin waɗannan abubuwa suna hannun gawurtattun mutane a duniya, sannan bana so na shiga rikici da bil'adama a matsayina na sarkin-aljanu.
"Wannan yasa na fara tunanin waye ya kamata na saka waɗannan ayyuka guda goma domin ya taimaka min, abubuwan da aka rasa su sake dawowa.
"Babban dalilin da yasa nake so a sake samo wadannan abubuwa da sarki Samudul Ansari ya bari shi ne, mafi yawa daga cikin abubuwan ya barsu ne domin na bayansa su yi amfani dasu su ƙetara ta cikin dazuzzukan da za'a ratsa a riski tau'rin.
"Bayan shafe shekaru goma ina bincike, sai idanuwa suka kai kan Barban.
"Sa'adda ya yankewa mahaifinsa aljihu, ina cikin kasuwar ina kallo don a wannan lokaci na shigo ƙauyensu ziyara ne, wai ko zanga idon-sani.
"Ganin cewa yaro kamar Barban a wancan lokaci ya samu nasarar yanke aljihu, ba tare an kama shi ba, yasa na cika da tsananin mamaki.
"Daga wannan lokaci na ɓacewa idanun mutane, nayi ta bin Barban a baya domin ganin abinda zaiyi da waɗannan maƙudan kuɗaɗe da ya sace.
"Bisa mamaki sai naga cewa, rayuwar mahaifiyarsa ya ceta daga cutar dake damunta.
"Daga wannan lokaci naji ya burgeni, nayi ta bibiyarsa har zuwa sa'adda naga mahaifiyarsa ta mutu.
"Lokacin da naga rayuwa ta yiwa Barban ƙunci sai tausayinsa ya kama ni, naga ya kamata na taimake shi, na ɗaga darajar wannan baiwa da yake da.
"Sa'adda sarki Deher yayi shelan wanda zai sato masa Amra (matar sarki Meher), ni ne na kwaɗaitawa Barban abin a zuciyarsa sannan na saka masa ƙarfin zuciya zai iya.
"Sannan ni ne na ribaci zuciyar sarki Deher ya amince ya baiwa Barban wannan aiki.
"Kamar yadda Barban ya baku labari a baya, shi kansa bai san wane ne ɗan-saurayi ba wanda ya taimaka masa a birnin Shaha-Meher.
"To, ku sani cewa, ni ne ɗan-saurayi wanda ya taimakawa Barban.
"Wannan sata da Barban yayi kamar wani gwaji ne nayi masa. Kasancewar naga cewa da taimakona ya sami nasara a wannan aiki yasa ban amince da wannan jarrabawa da yayi ba.
"Hakan yasa na tura shi birnin Sin domin na sake gwada baiwarsa akan sarki Kim Sam wanda ya addabi talakawa da zalunci a wancan lokaci.
"Haƙiƙa na cika da tsananin mamaki bisa ganin irin bajintar da Barban ya nuna a birnin Sin, hakan ne yasa na yarda cewa, zai iya gudanar da wadannan ayyuka guda goma.
"Wannan yasa na ɗauke shi, na bashi ƙarfin sihirin tsafi mai ƙarfin gaske. Na farkar da sirrin dake cikin jininsa irin na Anbalu.
"Na san cewa kun taɓa arba da siffar Barban a cikin ainihin siffar ƙabilarsu ta Aswad.
"Bayan na gabatarwa Barban waɗannan ayyuka guda goma saiya nemi na bashi dama ta tsahon makonni biyu domin yayi tunani da nazari akan ayyukan.
"Na amince da wannan abu da ya nema saboda komai yana buƙatar tunani da kuma nazari.
"Barban na gama tunani da nazarinsa ya tabbatar min da cewa, waɗannan ayyuka ba za su yiwu ba face mun samu gawurtaccen jarumi wanda babu kamarsa.
"Shi Barban yana da tsananin hikima da kuma basira, amma akwai wajajen da hikima da basira ba zasu yi aiki ba dole ana buƙatar jarumtaka.
"Wannan yasa muka fara neman jarumin da zamu baiwa wannan aiki. Mun jarraba jarumai da dama amma duk basu yi nasara ba.
"Daga baya Barban ya ce min, meye zai hana mu jarraba magajin wannan sarki, idan ya haura jarrabawar sai muyi ayyukan tare dashi?
"Barban ya ce, saboda aiki da wannan jarumi zai fi mana sirri sannan kuma kamar horo ne muka bashi.
"Na amince da wannan shawara ta Barban ƙwarai da gaske, na bashi damar zuwa ya gwada Aymanul Faris.
"Barban ya ce ba zai na bayyana kansa a duniya ba, saboda waɗannan ayyuka guda goma da nake so a gudanar suna buƙatar sirri sosai.
"Wannan yasa Barban ya ɗakko hayar ɗan-fashi Rashbir ya bashi umarnin gabatar da wannan aiki.
"Ni ne na baiwa Rashbir wannan mudubi wanda ya nuna ka dashi, sa'adda kuka yi gaba-da-gaba.
"Ka sani cewa, duk waɗannan dakaru dake bayan Rashbir ba mutane bane, hadimanmu ne shiyasa sa'adda ka kashe su, suka ɓace ɓat!
"Sannan kayi sani cewa, wannan macijiya da muka aiko maka ba macijiyar asali bace, samfurin macizan Gorgon ne, saboda mu ga ƙarfin zuciyarka akan yaƙi da ma'abota Bankai.
"Tabbas ka bamu mamaki, bamu taɓa tsammanin jarumtakarka da ƙarfin zuciyarka ya kai haka ba.
"Sa'adda ka yaƙi dakarun sarki Ayubul-Zairiy a saman tekun nan, nayi mamaki matuƙa da ƙaramin yaro kamar kai a wancan lokaci zai tarwatsa dubban mayaƙa.
"Wannan shi ne yadda aka yi muka haɗu da kai, bayan mun yi maka jarrabawa ba tare da kai kanka ka sani ba.
"Bari nayi muku bayanin ayyukan namu dalla-dalla da kuma manufofin mu."
Ranganu yana zuwa nan a zancensa sai yayi shuru.
Aymanul Faris ya cika da tsananin mamaki. Mun ga tun sa'adda yake yaro lokacin da ya gwabza yaƙi da dakarun Rashbir, shi ɗaya jal sannan ya karkashe su.
Mun ga yadda yayi ta mamaki sa'adda yaga gawarwakin dakarun sun ɓace ɓat!
Zaka iya cewa, tun daga wancan lokaci wannan abu ya tsayawa Aymanul Faris a rai amma kasancewar babu wanda zai tambaya yasa yayi shuru.
Tabbas a yau ya samu amsar wannan tambaya.
Yana shirin yin tambaya kenan, Ranganu ya ci gaba da jawabi.
"Jerin abubuwan da muka ɗauko su ne: farin lu'u-lu'u a birnin Askandariyya, zinarin matar sarki Fairaz, Saiful-Shiradu a birnin Kufa, kyawawan furanni a lambun Gorgon, sulken yaƙin sadauki Jarata da kuma makullin taskar Samudul Ansari. Hodon haka ne, ko?"
Barban ya ɗan yi shuru na daƙiƙu, kafun ya gyaɗa alamun haka ne.
"Ayyuka guda shida kenan, saura guda huɗu..." inji Ranganu.
Barban ya gyaɗa kai ya ce, "Kwarai kuwa, haka ka ce."
Ranganu yayi murmushi ya ce, "Bari nayi bayanin manufofin da suka sa muka ɗauko waɗannan abubuwa guda shida, kafun nayi bayani akan dazuzzukan da za'a ƙetare a riski Madarul Ansari."
Ya ɗan yi gyaran murya sannan ya ci gaba, "Dalilin da yasa muka ɗauko farin lu'u-lu'u a birnin Askandariyya shi ne, biyan Samazan ladar hikayar da zai bayar ta sarki Samudul Ansari, sannan wannan lu'u-lu'u asalinsa na attajira Zarshiyya ne.
"Zarshiyya 'yar attajiri Luhes ce, attajiri Luhes ɗan Kabaru ne. In taƙaice muku dai asalin tsatsonta daga birnin Shaha suke. Wannan ya tabbatar da cewa, asalin wannan farin lu'u-lu-u daga gidan sarautar sarki Samudul Ansari yake. Ɗaya kenan.
"Abu na biyu shi ne, sarƙoƙin-zinari na matar sarki Fairaz, Jamriyya.
"Kasancewar waɗannan ayyuka guda goma a hannun Barban suke, yasa na bashi dama domin shima ya rama wani cin mutunci da aka yiwa ƙanwarsa a shekarun baya.
"Sati guda kafun ku haɗu da Barban yaje birnin Faizara ya ɗauko wadannan sarƙoƙi na zinari na ƙanwarsa Hushriba.
"Nayi haka ne domin shima Barban ya ƙaru da waɗannan ayyuka guda goma da za'a gudanar.
****
Yau *06/05/2023*
Babi na gaba zaizo *08/05/2023* da izinin ALLAH.
RUHIN JARUMTAKA!
*
Babi na 121: *Manufar sana'ar Barban (2)*
*
Wannan littafin sadaukarwa ne ga Zahra.
*
U-M-S
*
Ranganu ya ci gaba da jawabi, "Abu na uku shi ne, takobin Saiful-Shiradu wadda muka ɗauko a birnin Kufa.
"Wannan takobi asalinta ta sarki Samudul Ansari ce, mun ji yadda ya sameta a cikin daular Irashnur, sa'adda yasha wannan tsumi wanda sarki Azman ya bashi.
"Babu buƙatar jin dogon bayani akan wannan takobi, kun san ta, kun san komai nata. Don haka ba zamu ɓata wani lokaci mai tsaho akan bayaninta ba.
"Abu na huɗu shi ne, waɗannan furanni wadanda kuka tsinko daga lambun Gorgon.
"Kuyi sani cewa, tsinko waɗannan furanni faɗuwa ce tazo daidai da zama. Saboda a wannan lokaci, muna so mu binciko inda ɓoyayyun Gorgon suke sannan mu nuna musu sabon tau'rin ɗin da zai bayyana.
"Waɗannan 'yan-mata guda uku dake ɓoye a cikin wannan lambu, ƴaƴan sarauniya Yilan ce. Ƙaramarsu sunanta Ileisha, yayunta kuma Laila da Narima.
"Tsinko waɗannan furanni kamar taƙalarsu da yaƙi ne da kuma nuna musu akwai babban bala'i har yanzu a gabansu.
"Shin mene ne dalilin da ya sake shigo da ma'abota Bankai duniya? Dukda cewa Samudul Ansari ya kafa tsari mai ƙarfi wanda zai hana su fitowa daga daular su.
"Babban dalilin da ya fiddo waɗannan ma'abota Bankai daga cikin daularsu shi ne, nemo ISRABIL. Abinda yasa kafin Samudul Ansari baiyi aiki akansu ba shi ne, suna tare da albarkar sarauniya Yilan da kuma ta aljani Ziyazil...
"Shin kun san wane ne ISRABIL?"
Ranganu yana zuwa nan a zancensa yayi shuru ya baiwa su Aymanul Faris damar tunani domin amsa wannan tambaya.
Aymanul Faris ya ce, "ISRABIL shi ne yarima Marganu kamar yadda ka bayyana mana kwanaki, shin yana da wata dangantaka da ma'abota Bankai ne?"
Ranganu ya ce, "Yarima Marganu baida wata dangantaka da ma'abota Bankai, amma ku sani cewa, tun daga zamanin sarkinsu na farko, sarki Sadusa Gorgon ake tattaunawa akan ISRABIL.
"An ɗauki zamani masu tsahon gaske, daular Gorgon tana jiran bayyanar ISRABIL.
"Sarakunanta da dama suna tsoron kada tau'rin ya riga ISRABIL bayyana domin kuwa, idan haka ta faru daular tasu zata iya rushewa.
"Ƙarshe dai, abinda suke tsoro ne ya faru. Wato tau'rin ya riga ISRABIL bayyana.
"Kun ji yadda Samudul Ansari ya ragargaji wancan daula a wancan zamani. Har ta kai ga cewa, ya kashe manyan ababen dogaron nasu har guda uku.
"Daga wannan lokaci, daular Gorgon bata sake samun abun dogaro ba. Hakan yasa suka yi shuru suka daina shigowa duniya.
"Zaka iya cewa, babban abinda daular Gorgon ta shafe fiye da shekaru dubu ne, ya bayyana.
"Ina nufin yarima Marganu. Tuni Marganu da su Ileisha Gorgon sun tattauna harma sun bashi labarin ɓoyayyiyar daular su.
"Abinda kawai ya rage shi ne Marganu ya tafi wannan daula, domin ya taka matsayinsa na ISRABIL.
"Dukda cewa sun sami ISRABIL dole ne zasu yi taka tsan-tsan saboda sun san har yanzu akwai tau'rin."
Koda Aymanul Faris, Barban da Riya suka ji wannan batu na Ranganu sai suka cika da tsananin mamaki.
Ta tabbata dai, Marganu shi ne ISRABIL, wanda dukkan wasiyoyin sarakunan Gorgon suka ƙare akan baiwa jama'arsu umarnin nemo shi.
Zamani bayan zamani, ƙarshe dai, abinda suke daɗe suna jira ya bayyana.
Aymanul Faris ya ce, "Mene ne babban sirrin ISRABIL sannan mene ne zai faru idan ya taka matsayinsa [ISRABIL]?"
Ranganu ya dubi Aymanul Faris ya ce, "Babban sirrin ISRABIL shi ne haske. Abinda zai faru bayan ya taka matsayinsa kuwa, babu wanda ya sani. Za mu sake tattaunawa akan ISRABIL nan gaba, yanzu kafun ya taka wannan matsayi akwai lokaci.
"Abinda ya kamata mu tattauna akai shi ne, manufofin ayyukanmu da kuma dazuzzukan da za'a ratsa a riski Madarul Ansari."
Barban da Aymanul Faris suka gyaɗa kai alamun amincewa.
Ranganu ya ci gaba da jawabi, "Kasancewar Aymanul Faris tare da jaruma Riya zasu yi tafiya izuwa kogon Madarul Ansari yasa muka ɗaukowa Riya sulken-yaƙin da babu kamarsa duk duniya.
"Wannan sulken-yaƙi zai taimaka mata matuƙa a yayin da suke tafiya.
"Abu na ƙarshe da muka ɗauko a cikin jerin wajibabbu shi ne, makullin taskar Samudul Ansari wadda ke ɗaure a wuyan sarki Raja.
"Kuyi sani cewa, in ba don mun tsara yadda zamu farmaki sarki Raja yadda ya dace ba. Da mun rasa wannan mukulli har abada kenan. Idan kuwa babu wannan makulli babu yadda za'ayi a shiga cikin kogon Madarul Ansari.
"A taƙaice dai, duk ayyukan da muka gudanar mun yi su ne domin samun nasarar zuwa inda ruhin Samudul Ansari yake. Da zarar aka ce mun mallaki wannan ruhi, Aymanul Faris zai iya karya kafin dake hana mutane zama a cikin daular ta sake komawa kamar yadda take da.
"Shin akwai mai tambaya a cikinku, kafun mu fara bayanin dazuzzukan da za'a ƙetara aje Madarul Ansari?"
Ranganu ya sake tambayar su Aymanul Faris don a wannan lokaci, ya gama faɗa musu manufofin sana'ar da ya saka Barban.
Aymanul Faris da Hajriya suka cika da tsananin farin ciki da kuma mamaki duk a lokaci guda.
Farkon haɗuwar Aymanul Faris da Barban saida zuciyar Hajriya ta soma raya mata abubuwa iri-iri akan wannan sana'a da suke.
Waye zai so ɗansa ya zamo ɓarawo?
Sau da dama ta so raba Aymanul Faris da Barban amma sai zuciyarta ta hana ta. Bata taɓa tsammanin wannan sana'a da suke tana a manufa mai ƙarfi haka ba sai a wannan lokaci.
Tabbas Barban da Ranganu sun yi abu wanda zai zamo babban dalilin sake kafuwar daular Shaha.
Haƙurin da Hajriya tayi na son hana Aymanul Faris wannan sana'a yayi amfani, ko ba komai zai amfaneta sannan ya amfani dukkan jama'ar da zasu sake zama a daular Shaha.
"Ina da tambaya," inji Aymanul Faris. "Ina sauran jama'ar daular Shaha suka shiga, nasan cewa yaƙi bai shafe su ba... Sannan wannan bala'i ne ya hana su zama a cikin birnin nasan cewa bai hallaka su ba. Ina Hushriba?"
Ranganu yayi murmushi kamar dama yasan cewa Aymanul Faris zaiyi irin wannan tambaya.
"Shin kana da labarin ƙasashen Jerawa?" Ranganu ya tambayi Aymanul Faris.
Aymanul Faris yayi shuru tsahon lokaci, daga bisani ya girgiza kai alamun bai sani ba.
Ranganu ya nuna wani allon haske dake tsaye a jikin bango da hannunsa na hagu. Nan take hoton wata ƙatuwar ƙasa ta bayyana.
Birni ne mai girma da faɗin gaske. Aka nuno jama'ar dake rayuwa a cikin birnin aƙalla zasu kai miliyan arba'in.
"Wannan shi ne ƙasashen Jerawa, garin da ya wanzu bayan an gwabza yaƙi na farko a birnin Shaha tsakanin sarki Meher da sarki Deher."
Ranganu yana gama faɗin haka ya sake nuna wannan madubin tsafi da hannunsa guda. Take hoton wani ƙatoton gari ya bayyana a saman wani tsauni.
"Wannan shi ne birnin Hajarr, shima ya samu ne bayan kammala wannan yaƙi."
Ranganu ya sake nuna musu wani birni dake tsakiyar wani babban teku. Kallon farko suka yiwa wannan birni suka shaida shi domin kuwa ba ko'ina bane face Darul Barban.
"Waɗannan su ne manya-manyan biranai guda uku da na sani, wadanda asalin jama'ar daular Shaha suke rayuwa a cikinsu. Akwai sauran guda huɗu waɗanda ban san a ina suke ba, amma da zarar Aymanul Faris ya mallaki tau'rin zai gano sauran guda huɗun.
"Ƙasashen Jerawa kawai sun juya sunansu izuwa Jerawa ne domin su ɗauke hankalin duniya daga kansu. Haka ma Hajarr."
Ranganu yayi shuru sa'adda yazo nan. Aymanul Faris yayi farin ciki ganin mutanensa har yanzu suna nan a raye, abinda kawai suke jira shi ne sake bayyanar tau'rin.
"Ita kuwa Hushriba, a halin yanzu tana birnin Ranayes garin da Anbalu da mutanensa suka koma, ƙarƙashin kulawar gimbiya Helina..."
Aymanul Faris ya ce, "A taƙaice dai, jama'ar mu har wannan lokaci suna raye sannan duk ranar da muka sake kafa birnin Shaha zasu dawo ciki mu ci gaba da rayuwa?"
Ranganu ya gyaɗa masa kai. "Yanzu bari nayi muku bayanin dazuzzukan dake kan hanyar zuwa kogon Madarul Ansari!" inji Ranganu.
"Kamar yadda kuka sani, hanyar zuwa Madarul Ansari tana cikin dajin Djinn dake yankin ƙasar Hadriyan ta sarki Dujalu.
"Idan mutum ya shigo cikin dajin yayi tafiya mai ɗan tsaho zai iso wata mararrabar hanyoyi guda biyu - ɗaya ta nufi kudu, ɗaya ta nufi arewa.
"Hanyar da ta nufi arewa zata sada mutum da dajin Shiwazu wanda zai kai mutum har saman tsaunin ƙabilar Edwan sannan ya kai mutum dajin Marsas.
"Hanyar da ta nufi kudu kuwa, zata sada mutum da manya-manyan dazuzzuka guda huɗu. Waɗanda kana ƙetare su zaka riski Madarul Ansari.
"Bayan ka kama hanyar kudu, kayi tafiya ta kimanin wuni guda zaka riski wani gabjejen daji wanda Samudul Ansari ya kira shi da suna Husum.
"Kamar yadda kuka karanta a tarihi a wannan daji na farko da ake kira Husum, babu komai face wani shirgegen ƙaton dodo.
"Shi dai wannan dodo ɓarkeken gaske ne sannan yana da ƙarfin damtse har na gaban misali. Ance wani ƙaton sungumi yake yawo dashi a cikin wannan daji, nauyin wannan sungumi inda za'a ajiye shi a ƙasa zai kai nauyin tsaunin Kaulim.
"Babu halittar da wannan dodo zai jibgawa wannan sungumi bai dagargaje ba, komai yawan ayari na mayaƙa ance duka ɗaya kawai yake musu ya kashe da yawa daga cikinsu.
"Sarki Samudul Ansari ne ya samar da wannan dodo domin yayi gadin wannan daji na farko. Jarumai da matsafa masu yawan gaske sun hallaka a cikin wannan daji na farko a hannun wannan dodo.
"Tunda Samudul Ansari ya samar da wannan dodo, ba'a samu wanda ya samu damar ƙetarewa ta cikin wannan daji na farko ba. Duk wanda yayi gaba-da-gaba da wannan dodo hallaka yake.
"Mun san da zaman wannan dodo shiyasa muka tura ka yaƙi da aljanu jinin Rau'an. Yaƙi da jinin Rau'an tamkar horo ne akan yaƙi da wannan dodo. Saboda dukkansu tsafi baya tasiri akansu face tsagwaron jarumtaka.
"Wannan na ɗaya daga cikin dalilan da suka sa muka saka ka a cikin wadanann ayyuka guda goma, wato baiwa kanka horo."
Ranganu yana zuwa nan a zancensa ya sake nuna wannan allon-haske da hannunsa. Take hotunan wadansu sadaukai guda biyar suka bayyana.
Waɗannan sadaukai suna sanye da baƙaƙen tufafi, wani irin hayaƙi mai kaurin gaske na tashi daga jikinsu. Dukkansu suna riƙe da zabga-zabgan takubba baƙaƙe ƙirim.
Babu abinda su Aymanul Faris suke iya shaidawa a jikin wadannan sadaukai, baƙin hayaƙin nan ya rufe komai.
"Mutum-mutumin tau'rin kenan, dole sai mutum ya samu nasara akansu kafun ya wuce izuwa daji na gaba..."
Aymanul Faris ya dube shi ya ce, "Kenan yaƙi da waɗannan halittu tamkar yaƙi da tau'rin ne?"
Ranganu ya ce, "Kusan dai haka, saboda Samudul Ansari bai sanar dani sirrin daji na biyu ba."
Bai sanar dashi ba? To wai shin wane ne ainihin aljani Ranganu?
Ranganu ya sake nuna allon-hasken da hannunsa, take hoton daji na uku ya bayyana.
Wani hazo mai kaurin gaske ya lulluɓe wannan daji, babu wani abinda ake kallo.
Ranganu ya ce, "Babu wanda yasan abinda ke cikin wannan daji, saboda idan zaku tuna, daga sararin samaniya ya jeho ɗalasimansa cikin dajin, don haka babu wanda yasan ajiyar da yayi.
"Shi kuwa daji na huɗu, dajin wuta ne. Komai dake cikin wannan daji na wuta ne, idan mutum bai kai mataki na takwas a sarrafa aljanin-wuta ba. Ba zai iya ƙetare wannan daji ba.
"Wannan shi ne taƙaitaccen bayani akan dazuzzuka guda huɗu da za'a ratsa a riski Madarul Ansari. Yanzu mai tambaya a cikinku sai yayi, kafun na faɗa muku sirrukan wannan daji kamar yadda aka sanar dani."
Aymanul Faris, Barban, jaruma Riya da Hajriya suka yi shuru suna jinjina maganganun Ranganu a ransu.
Daga can Aymanul Faris ya ce, "Ta ya ya za'a yi na taka matsayi na takwas a sarrafa aljanin-wuta?"
"Idan ka ƙaddamar da aljani Nara a matsayin hadiminka, zaka taka wannan matsayi..." inji Ranganu.
Cikin mamaki Aymanul Faris ya ce, "Ance Nara hadimi ne ga duk wanda ya zamo magajin Samudul Ansari, shin mutum zai iya ƙaddamar dashi?"
Ranganu ya ce, "Kwarai ma kuwa. Nara hadimi ne ga duk wani tau'rin, amma idan da zarar mutum yazo shiga wadannan dazuzzuka guda huɗu, akwai buƙatar ya ƙaddamar da Nara."
Aymanul Faris ya ce, "Ta ya ya zan ƙaddamar da Nara a matsayin hadimina?"
Ranganu ya ce, "Dole kaima sai kaje tsakiyar daular Irashnur, ka hau saman tsaunin dutsen-wuta. A nan ne zaka ƙaddamar da Nara..."
Cikin tsananin mamaki Aymanul Faris ya dube shi ya ce, "Ta ya ya zan je daular Irashnur, alhalin ance sai mutum ya shafe shekaru goma bai isa can ba?"
Ranganu yayi murmushi ya ce, "Daɗin abin shi ne, lokacin da Samudul Ansari yaje wannan waje baya tare da Nara amma a halin yanzu kana tare dashi. Aljani Nara zai iya kai ku wannan waje a cikin wuni guda."
"Tafiyar shekaru goma a cikin wuni guda? Ta ya ya haka zata yiwu?" Aymanul Faris ya tambayi Ranganu.
Ranganu ya ce, "Idan baka manta ba, akwai sa'adda Nara yayi amfani da wani ɗalasimi nasa ya tseratar da ku daga sharrin su Ileisha Gorgon..."
Aymanul Faris yayi shuru yana tunani. Lokacin da Aymanul Faris ke fafata yaƙi da Ileisha Gorgon, sa'adda su Laila da Narima suka bayyana mun ga yadda aljani Nara ya fito gabansa ya haƙa rami da hannunsa guda sannan ya juyar gangunan jikinsu izuwa jan-hayaƙi.
Aymanul Faris ya gyaɗa kai a hankali.
Ranganu ya saka hannu a aljihu ya fiddo wata takarda mai kaurin gaske da kuma wata zabgegiyar adda ya baiwa Aymanul Faris ya ce, "Wannan taswira zata kai ka har saman wannan tsauni wanda ke tsakiyar daular Irashnur. Sannan zata kai ka har cikin kogon Madarul Ansari inda ruhin Samudul Ansari yake.
"Wannan adda kuma, ita ce Samudul Ansari yayi amfani da ita ya fara yaƙi da ita a yaƙi da ma'abota Bankai kafun ya sami Saif-Al-Barzaƙ.
"Yau ku tafi kaida Nara izuwa daular Shaha, idan kuka dawo gobe sai ka cika maganar da mahaifiyarka tayi ma, daga nan zan turo a ɗaukeka kai da amaryarka, a kawo ku fadata.
"A nan zamuyi sallama da juna, ku tafi izuwa kogon Madarul Ansari..."
Ranganu yana zuwa nan a zancensa ya risina a gaban Aymanul Faris sannan ya risina a gaban Hajriya, jikinsa ya tarwatse izuwa hoda take ya ɓace ɓat!
Aymanul Faris ya dubi Hajriya ya ce, "Mama, me wannan aljani yake nufi?"
Hajriya tayi murmushi ta ce, "Magana ta da zaka cika guda ɗaya ce ai, AURE TSAKANINKA DA RIYALATU."
"Hmm," Aymanul Faris yayi guntun murmushi. Idanuwansa suka kai cikin na jaruma Riya. Wani irin farin ciki ne har cikin ranta.
"Bari naje daular Irashnur na dawo, zamu ƙarasa sauran" inji Aymanul Faris. "Kuyi tanadin biki da duk wani abinda ya dace."
Yana gama faɗin haka ya risina a gaban Barban sannan ya risina a gaban Hajriya, yaje ya kama hannun Riya guda ya ce, "Mata ta!"
Jaruma Riya tayi murmushi. Jikinsa ya juye izuwa wuta jajawur kafun ya ɓace ɓat daga wannan waje.
*****
Yau *08/05/2023*
Babi na gaba zaizo *11/05/2023* da yaddar ALLAH.RUHIN JARUMTAKA!
*
Babi na 122: *Masoyan Juna*
*
Wannan littafin sadaukarwa ne ga Zahra.
*
U-M-S
*
A gadon bayan Nara Aymanul Faris ya bayyana, bayan doguwar tafiya suka dira a cikin wani ƙaton daji mai yawan yashi. Aljani Nara yasa manya-manyan hannayensa guda biyu ya haƙo wawakeken rami a cikin wannan daji.
Daga bisani ya busa wuta izuwa cikin rami. Gagarumar wuta irin wadda aka daɗe ba'a gani ba, ta fara

Please Login or Register in order to submit comment