Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

sari baƙin hayaƙi.
Kafun Aymanul Faris ya sake kawo masa wani harin, tuni ya saka hannunsa guda ya sake gabzawa Aymanul Faris naushi.
Aymanul Faris ya sake yin tsalle baya ya faɗo yana aman jini.
Cikin gaggawa ya sake komawa wajen wannan ruhi ya sake kai masa wani harin. A wannan lokaci ma, wannan ruhi bai kauce ba, harin ya sake dira a jikinsa.
Babu wani abinda yayi masa. Kafun Aymanul Faris ya sake kawo masa wani harin, tuni ruhin ya danƙara masa sara a kafaɗa.
Lafcecen sara ya bayyana akan kafaɗar Aymanul Faris, jini yayi tsartuwa. Lamarin da yasa Aymanul Faris ya kwarara uban ihu kenan.
Hankalin jaruma Riya yayi mummunan tashi, ta rasa abinda ya kamata tayi.
Yadda Aymanul Faris yake gumurzu da wannan ruhi, babu alamun zai samu nasara. Saboda ƙarfin wannan ruhi ya ninka nasa sau babu adadi.
Aymanul Faris ya miƙe tsaye ya yage rigar jikinsa, ya ɗaure wannan rauni dake kan kafaɗarsa.
Jini ya daina zubowa amma dukda haka saida zogi da raɗaɗi suka addabi wannan hannu nasa.
Lamarin da yasa ya daina motsa hannun yadda ya dace kenan.
A wannan lokaci Aymanul Faris bai sake rugawa kan wannan ruhi ba, daga inda yake tsaye ya zaro takobinsa ta Saiful-Shiradu ya ƙaddamar da matakinsa na takwas akanta.
Aymanul Faris ya kaiwa wannan ruhi sara daga inda yake tsaye.
Dutsen wuta ƙatoto ya fita daga tsinin wannan takobi yayi kan wannan ruhi da gudu.
Ruhin yayi murmushi ya dunƙule hannunsa guda, wannan dutsen wuta yana ƙarasowa gabansa yayi masa naushi guda.
Hannunsa yana haɗuwa da dutsen wutan ya tarwatsa shi.
Aymanul Faris yayi murmushin takaici, dama yasan haka zata iya faruwa.
Yadda suka karanta a tarihi hatta hatsabiban takubba irinsu Bankai basa yiwa wannan ruhi komai.
Aymanul Faris yayi shuru yana tunani. Ta ya ya zai sami nasara akan wannan ruhi?
Kafun ya gama tunanin abinda ya kamata yayi, wannan ruhi ya tunkaro inda yake tsaye.
A wannan lokaci ne Aymanul Faris ya sake samun dama ya yiwa wannan ruhi kyakkyawan kallo.
Wannan ruhi daga sama har ƙasa a lulluɓe yake da baƙar alkyabba irinta sarakunan farko.
Akansa akwai hular sanyi. Dukda cewa babu abinda ya rufe masa fuska, amma Aymanul Faris baya iya ganin fuskarsa.
Saboda haka zai iya cewa, wannan ruhi baida fuska. Ko kuma mutum bai isa yayi arba da fuskar sa ba.
Yana ƙarasowa gaban Aymanul Faris ya tsaya cak! Fuskarsa tana tsaye daidai ta Aymanul Faris.
Wani irin iko na musamman ya soma ratsa Aymanul Faris. Shi kansa saida ya sake cika da tsananin mamaki bisa ganin cewa, bai zube yayi mubaya'a ba.
"Wai a hakan ake cewa, kaine magajina?
"Ba zaka iya samun nasara akaina ba, sannan kake tunanin zaka bautar dani?"
Aymanul Faris yana jin wannan batu, cikin shammata ya daka wawan tsalle ya tsallake wannan ruhi sannan ya ruga da gudu ya tunkari cikin wannan ɗaki.
Ruhin ya juyo cikin zafin nama ya bi bayan Aymanul Faris da gudu.
Aymanul Faris bai taɓa gudu irin na wannan lokaci a rayuwarsa ba, amma yana waigowa yaga saura taku uku kacal! wannan ruhi ya riske shi.
Ruhin ya ɗaga wannan takobi dake hannunsa ya danƙarawa Aymanul Faris sara a gadon baya.
Lafcecen sara ya sake bayyana a gadon bayan Aymanul Faris, zogi da raɗaɗi suka sake shiga jikinsa.
Dukda cewa jiri yana ɗibarsa amma a haka ya jure ya ci gaba da gudu.
Wannan ruhi ya sake saran kaurin Aymanul Faris, ƙafarsa ta fashe, jini ya fara malala a ƙasa.
Wani mugun zogi da raɗaɗi ya shige shi, amma a haka ya take ƙafar tasa ya ci gaba da gudu.
Wannan ruhi na ganin haka ya tsaya cak!
A wannan lokaci Aymanul Faris ya shige cikin wannan ɗaki.
Wannan ruhi na ganin haka jikinsa ya tarwatse ya koma wannan baƙin hayaƙi sannan ya saje a cikin hayaƙin dake kaɗawa a wannan waje.
Aymanul Faris yana shigowa cikin wannna ɗaki yayi arba da takobin Saif-Al-Barzaƙ da kuma wannan kwalba ta tau'rin bisa wani tudu.
Idanuwansa suna rufewa da buɗewa ya ƙarasa gaban wannan kwalba ya tsaya.
Aymanul Faris ya ɗaga hannunsa guda, ya ɗora shi akan wannan kwalba.
Wani baƙin hayaƙi ya fito daga cikin wannan kwalba, ya shiga hannun Aymanul Faris, ya ratsa tsoka da fata ta hannun ya shige cikin jijiyoyinsa.
Baƙin hayaƙin yayi ta tafiya a duk cikin jijiyoyin Aymanul Faris har ya gama kewaye dukkan jikinsa.
Hayaƙin ya tunkari zuciyarsa. Yana zuwa cikin zuciyar Aymanul Faris yayi wata ƙara, zogi da raɗaɗi ya rufe shi.
Aymanul Faris ya sulale ƙasa sumamme. Wannan kwalba ta tarwatse ta juye izuwa baƙin hayaƙi, hayaƙin ya lulluɓe Aymanul Faris waɗannan raunika na jikinsa gaba ɗaya suka warke.
Koda jaruma Riya taga Aymanul Faris ya shafe sa'a guda bai fito daga cikin wannan ɗaki ba, sai ta bi bayansa.
Tana zuwa ta iske shi a kwance sumamme.
Jaruma Riya ta watsa masa ruwa, amma bai farfaɗo ba, take ta fara yi masa fifita nan ma bai farfaɗo ba.
Jaruma Riya ta goya Aymanul Faris a gadon bayanta, ta ɗauki takobin Saif-Al-Barzaƙ ta ɗaure a kunkuminta, ta fito daga cikin wannan ɗaki.
Sannan ta nufi ƙofar fita daga cikin wannan kogo gaba ɗaya.
Jaruma Riya tana fitowa daga cikin wannan kogo, ƙofar kogon ta koma ta rufe.
Jaruma Riya ta yada zango a ƙarƙashin wani ƙaramin dutse, ta kafa tanti, ta kwantar da Aymanul Faris a cikinsa, sannan ta zauna a gefensa tana yi masa fifita.
****
Yau *01/06/2023*
Babi na gaba zaizo *03/06/2023* da yaddar ALLAH.RUHIN JARUMTAKA!
*
Babi na 132-133: *Haɗuwar Gwaraza*
*
Wannan littafin sadaukarwa ne ga Zahra...
*
U~M~S
*
~Daular Nehiya.
*
Gari na wayewa sarki Kuffuru ya farka daga barci, ya shiga cikin wani ƙasaitaccen banɗaki yayi wanka sannan ya fito.
Yana fitowa daga cikin wannan banɗaki, wata kuyanga ta lulluɓa masa farin mayafi.
Sarki Kuffuru ya shiga cikin wani ɗaki ya caɓa ado na gaban kwatance sannan ya fito ya nufi ɗakin cin abinci.
Bayan ya gama cin abincin safe ya ƙoshi sai ya fito fadarsa a karo na farko.
Sarki Kuffuru ya ƙarasa kan wannan karagar mulki ya zauna, ya kirawo dukkan 'yan majalisar ƙasar ya tambaye su kowa yayi masa bayanin yadda yake tafiyar da ayyukansa.
Bayan sun gama sarki Kuffuru ya sauƙe wasu daga cikinsu ya ɗaura sababbi.
Azahar nayi sarki Kuffuru ya kirawo waɗannan mahukunta na wannan daula mutum goma, ya basu umarnin shirya masa tafiya rangadi da yamma.
Mutanen guda goma suka zube suka ce zasu yi kamar yadda ya umarce su.
Da yammaci sarki Kuffuru ya fita rangadi izuwa wannan daula domin ganin ƙarfin sojojinta da kuma faɗin ƙasarta.
Saida sarki Kuffuru ya shafe mako biyu yana rangadi a cikin wannan daula sannan ya gama kewaye ko'ina da ina na cikinta. Babu wani lungu ko saƙo da bai je ba.
Sarki Kuffuru yayi arba da dakarun dake tsaron wannan daula kuma sun yi masa kamar yadda yake buƙata.
A ranar cikon mako na biyun ne, ya iso sansani na ƙarshe na wannan daula wanda yayi iyaka da wata daular.
Wannan sansani babu wanda yafi shi girma duk wannan daula.
Sarki Kuffuru ya baiwa bawan dake tuƙa wannan keken doki nasa umarnin shiga cikin wannan sansani.
Bawan ya kaɗa keken dokin ya shiga cikin sansanin.
Sarki Kuffuru yayi ta arba rukunin dakaru kala daban-daban. Babu mutane a wannan sansani gaba ɗayansu UMKAS ne.
A ƙiyasin sarki Kuffuru a wannan waje, za'a iya samun sojoji kamar miliyan arba'in.
Babban sojan dake kula da wannan sansani, ya kai sarki Kuffuru izuwa masauƙi. Yasa aka kawowa sarki Kuffuru abin taɓawa.
Bayan sarki Kuffuru ya ci abinci sai ya dubi UMKAS ɗin ya ce, "Mayaƙa nawa ne a wannan sansani, sannan wanne irin horo suke da?"
UMKAS ɗin ya ce, "Ni sunana Zaili-Zaila, ni ne shugaban duk wani UMKAS dake rayuwa a cikin wannan daula.
"Wannan sansani namu ana kiranshi da "SANSANIN-KARIYA" mune muke kare wannan daula daga duk wani hari dake tahowa daga waje.
"Tunda wannan daula ta kafu, ba'a taɓa samun wanda ya iya ƙetare wannan sansani namu ba, indai da mugun-nufi ya taho.
"Muna da mayaƙa guda miliyan biyar da ɗoriya da kuma makamai babu adadi."
Sarki Kuffuru yana jin wannan batu ya dafa kafaɗar Zaili-Zaila ya ce, "Da kyau, tabbas aikinku yana kyau."
Zaili-Zaila yayi murmushi ya ce, "Horon yaƙin da ake bamu kuwa, hatta sarakunan daular Gorgon basu da irinsa."
Sarki Kuffuru ya sake dafa kafaɗarsa cikin jinjina.
A daidai lokacin Hasamul-Sawaz ya bayyana a cikin haske a cikin wannan ɗaki.
Sarki Kuffuru yana ganinsa ya sallami Zaili-Zaila.
Kafun Hasamul-Sawaz ya buɗe bakinsa ya ce wani abu, kawai sai ya fiddo wani mudubin tsafi na dutse ya shafe shi da hannun hagu sannan ya fara nunawa sarki Kuffuru abinda ke faruwa akan mudubin.
Mudubin yayi haske ya nuno tarin mayaƙa masu tsananin yawan gaske suna gwabza yaƙi da waɗansu halittu guda biyar masu sanye da sutura ta haske.
Sannan suna riƙe da takubba su ma na haske suna ta ragargazar waɗannan dakaru dake ƙoƙarin 'yan'yame su.
Sarki Kuffuru yana ƙarewa dakarun da ake karkashewa kallo sai ya gane cewa, ba wasu bane illa dakarun ƙasar Damashkar saboda ga tambarin ƙasar akan garkuwowinsu da kuma kan sulken dake jikinsu.
Amma ya gagara gane, wadanda keta ragargazar dakarun su wane ne? Don haka ya tambayi Hasamul-Sawaz.
Maimakon Hasamul-Sawaz ya bashi amsa kawai sake shafar wannan mudubi nasa yayi.
Take aka nuno daular Gorgon a wata rana da ta wuce kafun wannan rana.
Marganu aka nuno tsaye a gaban waɗansu 'yan-mata guda biyar riƙe da takobinsa ta haske.
'Yan-matan gaba ɗayansu suna durƙushe akan gwiwowinsu sannan sun sunkuyar da kawunansu ƙasa.
Kallon farko zaka yiwa abinda ke faruwa a wajen, ka gane cewa, hukunci Marganu zai yanke musu.
To amma, abinda zai sake baka mamaki shi ne, ya ya su da za'a sarewa kawuna suke murmushi?
Saboda murmushi ne akan fuskar kowacce daga cikinsu.
Marganu ya ɗaga takobinsa ya bisu ɗaya bayan ɗaya duk ya sare musu kawuna.
Marganu ya sunkuya ya ɗauki kawunan nasu ya saka a cikin wata ƙatuwar tukunya dake gefe guda.
Bayan sun shafe sa'a ashirin da huɗu a cikin wannan tukunya sai sirrin haske ya sauƙo a cikin tukunyar.
'Yan mata guda biyar suka fito daga cikin wannan tukunya.
Wani iko na musamman yana tashi daga jikin wadannan 'yan mata.
"ISRABIL ya sake ƙirƙirar BES nasa na kansa. Ya basu kyautar sirrin haske babban mataki. Zasu zamo tamkar mataimakansa.
"A halin yanzu gangar jikin ISRABIL tana cikin tukunyar tsumi a daular Gorgon tana zuƙan ɗalasiman da zasu farkar da babban sirrinta.
"ISRABIL ne ya turo BES domin su kamo masa Arya su tsare masa ita, hakan zai bashi damar hana Aymanul Faris farkar da babban sirrin dake cikin jininsa.
"A halin yanzu idan bamuyi da gaske ba, ba wai iya Aymanul Faris ISRABIL zai hana Arya hatta mu kanmu zamu rasata.
"Kada kayi tunanin wannan matsayi dake kai a yanzu, dole kana buƙatar wannan ruhi domin yaƙar abokan gabar da zasu sake bayyana a gaba," inji Hasamul-Sawaz.
Sarki Kuffuru yana jin wannan batu yayi shuru yana tunani.
A halin yanzu ba wai yana buƙatar Jaanu bace domin kasancewarta Arya, a'a, ya kamu da tsananin ƙaunarta ne saboda tsananin kyawunta.
"INA BUƘATAR ARYA, MUJE BIRNIN DAMASHKAR DOMIN NA HANA BES ƊAUKARTA!" inji sarki Kuffuru cikin kaushin murya.
Hasamul-Sawaz yana jin wannan batu, ya risina a gaban sarki Kuffuru sannan ya ranƙwafa.
Sarki Kuffuru ya hau kansa, shi kuma ya buɗe fuka-fukinsa ya lulluƙa cikin gajimare.
****
A can birnin Damashkar kuwa, yaƙi ne mai tsananin zafi ke wakana a ƙofar shigowa garin.
'Yan-mata guda biyar ne hatsabiban gaske suna ta sha'aninsu a tsakiyar waɗannan dakaru.
Duk inda suka saka a gaba sai dai kaga dakarun birnin Damashkar suna ta zubewa ƙasa.
Wannan waje gaba ɗaya ya cika da gawarwakin dakarun wannan birni, hatta wajen da za'a taka ya soma yin wahala.
Idan kayi duba izuwa cikin gidan sarautar birnin kuwa, zaka ga dakarun ƙasar manya wadanda aka fi ji dasu kewaye da gimbiya Jaanu domin tabbatar da tsaro.
Dukda cewa ba su suke yin nasara ba, hakan bai sa wani tsoro yazo kan fuskarta ba.
Saura ƙiris a gama da dakarun birnin Damashkar sarki Kuffuru ya sauƙo cikin wannan fili.
Cikin gaggawa ya kai musu sara da takobinsa ta LESIM.
Jajayen taurari guda biyar suka fice daga tsinin takobin suka tunkari BES gadan-gadan.
BES suna ganin haka, suka yi tsalle gefe cikin gaggawa.
Taurarin Kuffuru suka wuce suka doki katangar Damashkar, nan take katangar ta fara rushewa.
BES suna ganin haka, suka ɗauke hankalinsu daga kan tsirarun dakarun Damashkar suka rugo dukkansu izuwa kan sarki Kuffuru suka saka shi a tsakiya.
Sarki Kuffuru ya ɗaga takobinsa sama, suka ruguntsume da azababben yaƙi.
Cikin ƙanƙanin lokaci sarki Kuffuru ya kashe ɗaya daga cikinsu, sai dai tana mutuwa bayan daƙiƙa guda ta sake dawowa.
Suka dubi Kuffuru suka yi masa dariyar mugunta suka ce, ba ma mutuwa, koda sau ɗari zaka kashe mu sai mun dawo!
Sarki Kuffuru yana jin haka ya ɗaga takobinsa sama, ya kaɗata a cikin iska.
Taurari masu tsananin yawan gaske suka sauƙo wannan waje.
Kafun BES su yi wani yunƙuri tuni taurarin sun lulluɓe su.
Kuffuru yayi guntun murmushi ya sake kaɗa takobinsa a cikin iska.
Faruwar hakan keda wuya, waɗannan taurari suka yi jifa da BES izuwa ƙololuwar sararin samaniya.
Sarki Kuffuru ya mayar da takobinsa cikin kufe, ya tunkari ƙofar shiga birnin Damashkar.
Tsirarun dakaru da suka yi saura, suna ganin sarki Kuffuru ne suka fara guduwa suna ɓuya.
Sarki Kuffuru yana shigowa cikin birnin, ya tunkari gidan sarautar Ayubu.
Jama'a da dama suka yi ta leƙowa ta taga suna ganin sarki Kuffuru a yayin da yake tafiya a cikin birnin.
Shin sarki Kuffuru yazo ne domin ya ceci Jaanu? Tambayar da kowa yake yiwa kansa kenan, amma babu wanda ya sami amsa.
Sarki Kuffuru yana ƙarasowa fadar ya tunkari inda aka ɓoye Jaanu.
Dakarun da suka kewayeta suna ganin sarki Kuffuru ne, babban cikinsu ya sanar da ita.
Gimbiya Jaanu ta cika da tsananin mamaki bisa jin cewa, wai sarki Kuffuru ne yazo.
Gimbiya Jaanu ta baiwa wadannan jarumai umarnin buɗa masa ya ƙaraso.
Nan take kuwa suka yi kamar yadda ta ce.
Sarki Kuffuru ya ƙaraso gabanta ya tsaya, suka yi kallon-kallo. Ta risina ta gaishe dashi.
Sarki Kuffuru ya dubeta a hasale ya ce, "Wannan ko kaɗan bai dace da tsarin wannan daula ba.
"Sarakuna da bayar da rayuka aka san su, ba wai ɓuya ba. Yanzu me kike tunanin zai faru, idan ba dan nazo ba?"
Gimbiya Jaanu tana jin wannan batu ta ƙarasa gaban sarki Kuffuru ta ce, "Babu wani abu da zai faru a wannan duniya, wanda ba'a rubuta ba.
"An rubuta zaka zo, ka ceci al'umma, kuma kazo ɗin. Koda baka zo ba, tabbas wani zai zo."
Sarki Kuffuru ya haɗe fuska ya ce, "Me kike nufi?"
Cikin rashin tsoro Jaanu ta dube shi ta ce, "Ko kuma nace me kake nufi? Tun da ka ceci wannan birni namu, sai ka koma ƙasarka kayi fatan kada a sake kawo wani harin a gaba!"
Sarki Kuffuru yayi murmushi. A rayuwarsa babu abinda ke burge shi kamar ganin mace mara tsoro.
"Nazo ne domin na ɗauke ki, na kaiki wajen da ya dace. Barinki a wannan gari babban haɗari ne ga rayuwarki."
Gimbiya Jaanu tayi tunani ta ce, "Babu inda zan je na bar ƙasata. Amana aka bar min. Duk abinda zai samu al'ummata sai dai ya same ni!"
Sarki Kuffuru ya murtuƙe fuska ya dubeta ya ce, "Idan ba ki bar wannan ƙasar ba, za'a iya sace ki a kowanne lokaci."
Gimbiya Jaanu tana jin abinda Kuffuru ta haɗe hannayenta biyu kamar mai roƙonsa ta ce, "Kayi haƙuri ka tafi, ba zan iya barin wannan ƙasar ba."
Sarki Kuffuru ya sake murtuƙe fuska, zuciyarsa ta fara tafarfasa, ya tsani ya bayar da umarni a ƙi abi.
"Ko kizo mu tafi, ko kuma na ɗauke ki da ƙarfi!" inji Kuffuru cikin tsananin fusata.
Dakarun dake kewaye da Jaanu suka zaro takubbansu suka sake kewaye ta a wani salo na bayar da kariya.
Sarki Kuffuru yana ganin haka ya dubeta ya ce, "Za ki tafka babban kuskure, Jaanu!"
Cikin rashin tsoro ta dube shi ta ce, "Ba zan iya bin wannan umarni naka ba, idan kuwa ya zamo dole sai na bi umarnin. Sai dai ka kashe ni sannan ka tafi da gawata."
Sarki Kuffuru yana jin abinda tace ya sake fusata ya zaro takobinsa cikin tsananin fusata ya afkawa wadannan dakaru dake kewaye da ita.
Dakarun suna ganin haka, su ma suka afko masa, dukda cewa sun san yafi ƙarfinsu.
Cikin ƙanƙanin lokaci sarki Kuffuru ya hallaka su gaba ɗayansu, ya rage daga shi sai gimbiya Jaanu a wannan fada.
Sarki Kuffuru ya mayar da takobinsa cikin kufe sannan ya tunkari gimbiya Jaanu yana murmushin mugunta.
"KE TAWA CE, NAZO WANNAN BIRNI NE DOMIN NA ƊAUKE KI, SANNAN NA AURE KI!" inji sarki Kuffuru cikin murya mai kaushi.
Gimbiya Jaanu ta zaro idanu cikin tsananin mamaki.
Wai shin abinda kunnuwanta suka jiwo mata gaskiya ne?
Sarki Kuffuru wanda ke kusan mahaifi a gareta ace ya kamu da ƙaunarta?
To, amma sarki Kuffuru bai bata damar samun amsar wannan tambaya ba, ya tunkarota gadan-gadan zai kamata.
Tun gimbiya Jaanu tana ja da baya, yana matso ta, har saida ta takure a jikin bango.
Ya zamana cewa, babu inda zata motsa dole ne sai sarki Kuffuru ya riske ta.
Gimbiya Jaanu ta rufe idanunta tana jira duk abinda zai faru ya faru.
Sarki Kuffuru yana ƙarasowa gabanta ya miƙa hannunsa guda zai kamo gashin kanta.
Hannun nasa yana daf da taɓa kyakkyawan gashin kanta, aka yi masa wawan duka daga baya.
Saboda ƙarfin dukan sai da sarki Kuffuru yayi sama, sannan ya faɗo acan baya.
Gimbiya Jaanu ta buɗe idanu cikin tsananin mamaki domin ganin wanda ya ceceta.
Yarima Marganu ta gani tsaye a cikin wata siffa mai ban mamaki.
Jikinsa yana bayar da haske da walwali, tamkar ba cikakken mutum ba.
Marganu ya dubi gimbiya Jaanu ya ce, "Babu mahaluƙin da ya isa ya taɓa ki, idan bani ba. Nayi alƙawari ke zan fara sani 'ya mace shiyasa har yau ban taɓa tarawa da wata ba. Duk alƙawarin da na ɗauka sai na cika."
"Ƙarya kake," inji Jaanu. "Baka isa ka sanni 'ya mace ba, mutum ɗaya ne kawai zaiyi hakan, kuma shi na yiwa tanadin kaina."
Marganu yayi murmushin mugunta ya juya wajen da sarki Kuffuru ke tsaye.
Sarki Kuffuru ya gani tsaye riƙe da ƙugunsa cikin tsananin mamaki.
Yau ga shi ga Marganu, ga kuma Jaanu. Mai ƙarfi ya kwaci kansa.
Bisa mamaki sarki Kuffuru ya fara ganin wannan Marganun dake tsaye a gabansa kamar ba cikakken Marganu ba.
Don haka zuciyarsa ta fara ayyana masa anya ba mutum-mutumi Marganu ya turo masa ba kuwa?
"KUFFURU BN GAUHAN!" inji Marganu.
"Mene ne dalilin da zaisa ka shiga faɗan da ba naka ba? A sanadiyar gimbiya Jaanu rayuwata gaba ɗaya ta tarwatse.
"Na turo dakaruna domin su kamo min ita, na yanke mata hukunci kafun na dawo kanka.
"Ina baka shawara da ka tafi ka ƙyaleni da ita. Akwai lokaci da zaizo wanda zanzo har inda kake mu gwabza."
Sarki Kuffuru yana jin wannan batu yayi dariyar mugunta ya ce, "Haba yaro! An faɗa maka na taɓa saka abu a gabana ne, ban yi nasara ba?
"Ka ɗebo babban kashi wanda yafi ƙarfinka. Wannan kyakkyawar budurwar bata dace da mutum irinka ba.
"DA BABBAN SARKI KAMATA TA DACE. NI NE WANDA ZAI MORI WANNAN KYAKKYAWAN JIKI NATA!
"Kafun na sare kanka, ka faɗa min ina tsinanniyar 'yata take?"
Marganu ya zaro takobinsa ta haske ya nuna Kuffuru da ita ya ce, "Surutu a yanzu ɓata lokaci ne! Mu gwabza yaƙi wanda duk yayi nasara ya mallaki wannan budurwar!"
Yana gama faɗin haka ya ruga da gudu kan sarki Kuffuru.
Sarki Kuffuru yana ganin haka shima ya zaro LESIM ya falfala da azababben gudu kan Marganu.
Ai kuwa suna haɗuwa a tsakiya suka ruguntsume da azababben yaƙi mai tsananin ban tsoro fiye da tunanin mutum.
Marganu da Kuffuru suka wanzu suna masu kawowa junansu muggan sara da suka cikin baƙin zafin nama.
A duk sa'adda takobin Marganu ta haske ta haɗu da LESIM sai an kwararo gagarumar tsawa a cikin birnin Damashkar wadda take sa wa garin gaba ɗaya yayi girgiza, gagarumar wuta ta zubo.
Kafun ka ce me wannan, gobara ta kama ci a cikin sassa daban-daban na wannan birni.
Lamarin da yasa jama'ar garin firgicewa kenan, suka fara guje-guje da iface-iface.
A ɓangaren su sarki Kuffuru kuwa, tuni gumurzun ya ɗauki zafi.
LESIM ta gama ɗaukar zafi taurarin dake jikinta sun fito fili ƙarara suna son fitowa daga cikinta su afkawa Marganu amma sarki Kuffuru bai basu dama ba.
Ita kuwa takobin Marganu, tsabar yadda take fitar da haske har kashe idanu take.
Koda dukkansu suka fuskanci babu wata nasara da zasu samu, sai suka daka tsalle baya, suka fara hararar juna.
Sarki Kuffuru ya nuna Marganu da takobi ya ce, "Lallai ɗan zaki ya girma. Wai kamar ni ace na tsaya ɓata lokaci akan Marganu?"
Marganu yayi dariya ya ce, "Da sannu, zan fidda wannan girman kai dake kanka. Ko yanzu ka san cewa nafi ƙarfin ka kashe ni!"
Sarki Kuffuru yana jin wannan batu ya fusata, ya kaiwa Marganu saran takobi-mai-tafiya.
Jajayen taurari guda uku suka fice daga tsinin takobinsa suka yi kan Marganu da gudu.
Marganu ya tsaya cak! har waɗannan taurari suka ƙaraso gabansa.
Cikin kwanciyar hankali ya kauce musu, suka wuce.
Taurarin suka doki gidan sarautar Damashkar, saboda ƙarfin harin da kuma sharrinsa, saida rabin gidan sarautar gaba ɗaya ya ruguje.
Sassan gine-gine suka danne jama'a, manya-manyan ramuka suka bayyana.
Sarki Kuffuru yayi dariyar mugunta ya ce, "Wannan ɗan ƙaramin harina kenan,"
Marganu yayi murmushi shima ya kaiwa Kuffuru irin wannan sara.
Ƙatoton fai-fai na haske ya fice daga takobinsa yayi kan sarki Kuffuru da gudu.
Cikin daƙiƙa biyu kacal! ya iso inda Kuffuru yake.
Ba don Kuffuru yayi tsalle cikin zafin nama ba, da tuni faifan yayi daga-daga da shi.
Wannan hari ma ya zaftare wani ƙaton gini dake bayan sarki Kuffuru, ƙatoton ginin ya faɗo ƙasa ya haddasa girgizar ƙasa da wawakeken rami.
Fai-fan bai tsaya ba, ya wuce izuwa cikin birnin Damashkar duk inda ya ratsa ya wuce saiya zabtare wajen.
Nan take ya soma gagarumar ɓarna a cikin birnin Damashkar domin da ya ratsa ta cikin gini ya wuce, tofa sai ginin ya rushe.
Tun daga gidan sarautar birnin aka yi wannan hari amma saida ya dangana har da ganuwar garin, itama ya rusheta sannan ya faɗa cikin teku ya nutse.
Lallai wannan hari na Marganu gagarumin hari ne.
Sarki Kuffuru ya jinjina kai

Please Login or Register in order to submit comment