Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

mai kama da ƙonewar wuta na tashi a jikinsu.
Idanuwan aljanin jajazur tamkar garwashin wuta. Lokaci-lokaci hayaƙi yana fita daga bakinsa da kuma hancinsa.
A wannan lokaci yana zaune riƙe da mudubin dutse wanda yake kallon su Samudul Ansari a cikinsa.
Koda yaga Samudul Ansari ya hallaka dakarunsa guda goma, sai ya miƙe tsaye ya ɗaga kansa sama ya kwarara uban ihu, ya daka tsalle ya tumu da ƙasa.
Cikin gaggawa ya shige cikin wani wawakeken rami wanda yayi ƙasa zururu.
Jim kaɗan ya fito daga cikin ramin a cikin mahaukaciyar shiga ta yaƙi.
Ya ɗauko takubba waɗanda aka sassaƙa daga duwatsu guda biyu, sannan ya ɗauko sirarun masu guda uku.
Babu riga a jikinsa amma akwai wani gajeren wando aka haɗa da fatar bijimin kada a kunkuminsa.
Aljanin ya yi kururuwa ya jinjina makaman yaƙinsa sannan ya ruga da gudu ya tunkari ta inda su Samudul Ansari suke tahowa.
****
Samudul Ansari da Zarifa suna tafe suna hira, suka fara hango gagarumar ƙura tana tunkaro daga can nesa.
Samudul Ansari na ganin ƙurar jikinsa ya bashi lallai ba lafiya ba.
Cikin gaggawa yayi amfani da idanun tau'rin domin ganin abinda ke tahowa.
Nan take yayi arba da wannan aljani mai jiki kamar duwatsun ƙanƙara.
Samudul Ansari ya dubi Zarifa ya ce, "Sauƙo daga wannan doki naki, sannan ki hau saman wancar doguwar bishiyar, akwai babban abokin gaba tafe..."
Zarifa tana jin wannan umarni ta sauƙo daga kan dokinta sannan ta ruga ta haye kan bishiyar.
Kafun wannan aljani ya ƙaraso inda Samudul Ansari ke tsaye, ɓoyayyen hadimi ya bayyana a gabansa ya faɗa masa wata magana sannan ya ɓace ɓat!
Ɓoyayyen hadimi yana ɓacewa ɓat! wannan shirgegen aljani ya ƙaraso wannan waje.
Samudul Ansari yayi ido huɗu da cikakkiyar siffarsa.
Sannan jikinsa (duwatsu) suna kama da ɓangarorin ƙanƙara amma maimakon su bayar da sanyi kamar yadda kowa zaiyi tsammani, wani irin mahaukacin zafi ne ke tashi a jikinsu.
Yana riƙe da zabga-zabgan takubba guda biyu a hannayensa, sannan akwai masu guda uku a gadon bayansa.
Bayan ya gama ƙarewa Samudul Ansari kallo sai ya kwarara uban ihu ya ce, "Kai bil'Adama, wane ne kai? Mene ne dalilin shigowar ka daularmu har da zaka kashe mana dakaru?"
Samudul Ansari ya ce, "Ni ne sarkin dake mulkin daular Shaha, ina kira a gareka kayi min mubaya'a, ka ɗauke ni ka kaini tsakiyar daular ku domin na gudanar da wani muhimmin aiki,"
Koda wannan aljani yaji haka sai fuskarsa ta soma gatsinewa, ya taƙarƙare ya kwarara uban ihu.
"Ni sarki Buƙalshiyyu a shigo har yankin ƙasata sannan a nemi nayi mubaya'a, kuma wai nan ma a wajen bil'Adama ba yan-uwana aljanu ba... Kai wannan raini ya kai maƙura..." inji wannan aljani da ya kira kansa da suna Buƙalshiyyu.
Cikin fusata Buƙalshiyyu Djinn ya falfalo da azababben gudu kan Samudul Ansari.
Tau'rin na ganin haka ya yiwa Samudul Ansari tsawa.
"Kada ka kuskura ka kashe wannan aljani, akwai gagarumin aikin da zai yi mana a gaba!!!"
Samudul Ansari na jin abinda tau'rin ya ce, ya gyara riƙe takobinsa bai kaiwa Djinn hari ba.
Djinn yana ƙarasowa inda Samudul Ansari ke tsaye ya kawo masa sara, da waɗannan zabga-zabgan takubba.
Saura ƙiris takubban su dira akan Samudul Ansari ya goce a hankali, dukkansu suka sari iska.
Kafun Djinn ya sake kawo masa wani hari, Samudul Ansari ya juya ƙotar takobinta ya doki jikin Djinn da shi.
Take Buƙalshiyyu Djinn yayi baya taga-taga kamar zai faɗi amma cikin jarumtaka ya turje.
Idanuwa cike da tsananin mamaki, bakinsa a buɗe saboda tsabar mamaki, ya dubi Samudul Ansari ya ce, "Kai wanne irin hatsabibin bil'Adama ne?"
Samudul Ansari yayi guntun murmushi ya ce, "Kayi mubaya'a, Djinn. Har yanzu ƙofa a buɗe take..."
Dukda wannan abin al'ajabi da Djinn ya gani tattare da Samudul Ansari hakan baisa ya saduda ba.
"Da na yiwa bil'Adama mubaya'a gwamma ace ya sare kaina, hakan zai fi min sauƙi..." ya ce.
Yana gama faɗa ya sake rugowa kan Samudul Ansari, yana kwarara uban ihu.
Kafun ya iso Samudul Ansari, ɓoyayyen hadimi ya sake bayyana a gaban Samudul Ansari ya sanar dashi wani umarni wanda su kaɗai kawai suka sani.
Saura ƙiris Djinn ya ƙaraso, Samudul Ansari ya juye izuwa baƙin hayaƙi sannan shige cikin wangamammen bakinsa.
Tsahon daƙiƙa biyar kacal! Samudul Ansari ya ɗauka a cikin cikin Djinn, sannan ya fito.
Duk waɗannan abubuwa dake faruwa Zarifa dake can gefe guda bisa bishiya tana kallo.
Samudul Ansari yana fitowa daga cikin cikin Djinn ya tsaya a gabansa ya nannaɗe hannuwa akan ƙirjinsa.
Abin mamaki Djinn dake cika bakin ba zai yiwa kowa mubaya'a ba, ya ƙaraso gaban Samudul Ansari ya zube ƙasa kan gwiwowinsa.
"Ni Buƙalshiyyu Djinn na daular Irashnur, na yiwa Tau'rin mubaya'a, zan bi dukkan umarninsa, zan gujewa dukkan abubuwan da ya hana ni... Rayuwata fansa ce..."
Yana gama faɗin haka Samudul Ansari yayi murmushi ya ƙaraso gabansa, ya dafa kafaɗarsa ya ce, "Ka kaimu tsakiyar wannan daula, zan gudanar da wani abu..."
Buƙalshiyyu Djinn ya risina ya ce, "An gama ya shugabana..."
Samudul Ansari ya yafito Zarifa dake zaune akan wannan bishiya, cikin gaggawa ta sauƙo sannan tazo inda suke.
Djinn ya shige gaba Samudul Ansari da Zarifa suka take masa baya, suka nausa cikin wannan daula tasu ta Irashnur.
Daga wannan lokaci ne aljani Buƙalshiyyu Djinn ya zamo bawan Samudul Ansari saboda lokacin da Samudul Ansari ya juye izuwa hayaƙi ya shige cikin cikinsa ya ɗebo wani ɓangare daga cikin jinin zuciyarsa sannan ya baiwa ɓoyayyen hadimi shi ya tafi ya gudanar da wani aiki akansa.
Wannan shi ne sirrin yadda aka yi Samudul Ansari ya bautar da aljanin duwatsu - Buƙalshiyyu Djinn.
****
Yau 27/03/2023*
Babi na gaba zaizo *30/03/2023* da yaddar ALLAH.RUHIN JARUMTAKA!
*
Babi na 104: *Hatimai guda biyu*
*
***TARIHIN SAMUDUL ANSARI***
*
UMS
*
*BARKA DA SHAN RUWA, JAMA'A*
*
Wannan littafin sadaukarwa ne ga Zahra.
*
Sarki Samudul Ansari da Zarifa suka ci gaba da bin bayan Buƙalshiyyu Djinn suna kutsawa ta cikin wannan daula ta Irashnur.
Idan suka zo ƙetawa ta cikin ƙananun ƙauyuka sai kaga jama'ar ƙauyukan suna mamaki da al'ajabi bisa ganin yadda sarki Buƙalshiyyu da kansa ke yiwa waɗansu bil'Adama jagoranci.
Da yake waɗannan ƙauyuka a ƙarƙashin ikon Buƙalshiyyu Djinn suke, babu wanda yayi tunanin kawowa su Samudul Ansari hari.
Sarki Samudul Ansari ya dubi Buƙalshiyyu Djinn ya ce, "Bani labari akan ka mana,"
Buƙalshiyyu ya risina sannan ya bari saida suka jera sannan ya soma basu labari.
"Suna na Buƙalshiyyu Djinn. Ni ne wanda ke mulkin gari na farko a wannan daula da ake kira Juluru.
"Babban dalilin da yasa aka bani mulkin wannan gari na farko a wannan daula shi ne, saboda na bayar da tsaro.
"Kaf faɗin wannan daula babu jarumi mai tashe kamata..."
Samudul Ansari ya gyaɗa kai sannan suka ci gaba da tafiya.
Sannu-a-hankali har suka fice daga yankin ƙasar Juluru suka shiga yankin wani sarki dabam.
Samudul Ansari yayi amfani da idanuwan tau'rin ya hanga izuwa wata doguwar ganuwa dake can nesa dasu saman wani dogon tsauni wanda da wuya a samu na biyunsa a wannan daula.
Sarakuna guda biyu ya hango tsaye akan tsaunin, suna amfani da wani abu suna zuƙo hanya.
Gangunan jikin waɗannan sarakuna kamar na sarki Buƙalshiyyu Djinn sai dai sun fishi kwarjini da cika ido.
Samudul Ansari ya sake yin amfani da kunnuwan tau'rin domin jiwo abinda sarakunan suke tattaunawa.
"...na ji ance ya bautar da sarki Buƙal, yanzu haka suna tahowa ƙasata domin su yaƙe mu," shi ne abinda sarki Samudul Ansari ya fara jiwowa.
"Ta ya ya zamu yaƙe shi, don yadda ya yaƙi sarki Buƙal abin akwai ban al'ajabi?"
"Haba ta ya ya zamu haɗa ƙarfi-da-ƙarfe mu biyu, ace yayi nasara akan mu, wannan magana ne..."
Bayan kai-komo Samudul Ansari yaga waɗannan sarakuna sun sauƙo daga saman wannan dogon tsauni sannan suka falfalo da gudu izuwa kan wannan hanya wadda suke kanta.
Samudul Ansari yana ganin haka yayi murmushi ya dubi Buƙal ya ce, "Shin zaka taimaka mana, idan aka kawo mana hari?"
"Rayuwata fansa ce... Na riga nayi alƙawari..." inji Buƙal.
Samudul Ansari yayi murmushi suka ci gaba da tafiya. Zarifa ta dube shi, "Mijina! Shin akwai abokan gabar dake tunkaro mu ne?"
"Kwarai ma kuwa," inji Samudul Ansari. "Gidansu muka zo fa..."
Bayan doguwar tafiya suka sake hango gagarumar ƙura acan nesa tana tunkaro su.
Samudul Ansari ya dubi Zarifa ya ce, "Matata! Kada ki kuskura ki shiga wannan yaƙi da zamu fafata yanzu... Ki koma gefe ki sha kallo kawai..."
Cikin gaggawa Zarifa ta koma saman wata bishiya ta ɓuya sannan ya ƙurawa musu idanu.
Jim kaɗan waɗannan sarakuna guda biyu suka ƙaraso gaban Samudul Ansari da sarki Buƙalshiyyu Djinn.
Bayan kallon-kallo tsakaninsu da Samudul Ansari suka murtuƙe fuska suka dubi Buƙalshiyyu Djinn suka ce, amma dai ka bamu kunya, da ka risinawa wani bil'adama.
Samudul Ansari ya dube su ya ce, "Ku miƙa wuya, ko ruhinanku su isa ƙiyama yau!"
Sarakunan suna jin haka suka dubi juna suka kwarara uban ihu sannan suka falfalo da azababben gudu kan su Samudul Ansari.
Ɗaya daga cikinsu yayi kan Samudul Ansari, ɗaya kuma ya tunkari Buƙalshiyyu Djinn.
Kafun wanda ya tunkari Samudul Ansari ya ƙaraso gabansa, tau'rin ya daka masa tsawa.
"Waɗannan sarakuna su ne manyan sarakuna a wannan daula, idan muka sare kawunansu zamu yi amfani da kawunan nasu wajen ƙwace wannan daula...."
Samudul Ansari na jin haka ya haɗe fuska, ya gyara riƙe Saif-Al-Barzaƙ da kyau.
Wannan basarake wanda ya tunkaro shi yana ƙarasowa ya kawo masa wawan sara da irin wannan takobi wadda ake samarwa daga duwatsu.
Samudul Ansari ya ɗaga takobin Saif-Al-Barzaƙ ya kare wannan sara cikin kwanciyar hankali.
Takubban suna haɗuwa a waje guda, baƙin hayaƙi ya fita daga cikin takobin Saif-Al-Barzaƙ ya shige cikin takobin sarkin ya tarwatsa ta.
Cikin tsananin mamaki ya ja da baya, ya ƙarewa Samudul Ansari kallo.
Kafun daga bisani jikinsa ya soma juyewa izuwa hazo-hazo sannan ya ɓace ɓat!
Kafun Samudul Ansari ya ƙaddamar da idanuwan tau'rin yaga inda aljanin yayi, tuni aljanin ya gabza masa naushi a gadon baya.
Saboda ƙarfin naushin saida Samudul Ansari yayi tsalle sannan ya faɗi a can nesa.
Aljanin ya ɗaga hannayensa biyu ya doki ƙirjinsa sannan ya yi ihu, ya sake rugawa da gudu kan Samudul Ansari.
Yana isowa gaban Samudul Ansari ya sake kawo masa irin wannan duka.
Ya kamata a san cewa, aljanu jinsin duwatsu suna haɗa wani irin ruwan tsumi da hawainiyu.
Indai suka sha wannan tsumi, jikinsu yana zuƙar sinadarin hawainiya yasa su saje da kalar wajen da suke.
Wannan aljani dake gaban Samudul Ansari tuni yasha irin wannan tsumi, wannan shi ne dalilin da yasa gangar jikin wannan aljani tayi hazo-hazo ta ɓace.
Cikin gaggawa Samudul Ansari ya ƙaddamar da idanuwan tau'rin sannan ya yi duba izuwa inda wannan aljani ke tahowa.
Nan take yayi arba da aljanin, saura ƙiris ma ya riske shi.
Aljanin ya sake kawowa Samudul Ansari irin wannan mahaukacin naushi da hannunsa.
Cikin zafin nama Samudul Ansari ya goce aljanin ya naushi iska.
Kafun aljanin ya kawowa Samudul Ansari wani harin, tuni Samudul Ansari ya sare shi da takobin Saif-Al-Barzaƙ dake hannunsa.
Take jikin aljanin ya soma kumbura yana tsatstsagewa, kafun daga bisani ya soma bindiga yana rushewa.
Kafun a ɗauki lokaci, ya gama ruɓurɓushewa ya zube akan wannan farar ƙasa dake wajen.
Samudul Ansari ya sunkuya ya ɗauki ƙoƙon kansa sannan ya tunkari gindin bishiyar da Zarifa ke zaune a kanta.
Yana zuwa ya haye kan bishiyar ya zauna a gefen Zarifa sannan suka ƙurawa Buƙalshiyyu Djinn da wannan sarki dake kewaye juna a wannan lokaci.
Zarifa ta dubi Samudul Ansari ta ce, "Ya kai mijina! Kana da isasshen ƙarfin da zaka iya yaƙar wancan aljanin, saboda wanne dalili ka ƙyale shi da sarki Buƙal?"
Sarki Samudul Ansari ya dubi Zarifa yayi murmushi ya ce, "Akwai wani gagarumin aikin da zan sa sarki Buƙal yayi min, bayan nayi ƙaura. Akwai buƙatar naga ƙarfinsa daga yanzu, idan yana buƙatar ƙari sai na ƙara masa..."
Zarifa ta gyaɗa kai sannan ta ci gaba da ƙura idanu a wannan gumurzu da su sarki Buƙal suke shirin gwabzawa.
Koda suka kewaya juna kamar sau arba'in sai suka afkawa juna da azababben yaƙi.
Sarki Buƙal yana amfani da irin waɗannan takubba wadanda aka sassaƙa da duwatsu guda biyu, shi kuma wannan sarki yana amfani da guda ɗaya sai dai zabgegiya ce.
Koda sarkin yaga Samudul Ansari ya sare kan ɗan uwansa, sannan ya ɗauki kan yaje ya zauna akan bishiya ya saka masa idanu sai ransa ya ɓaci.
Ya kwarara uban ihu ya kaiwa Buƙal sara cikin zafin nama, Buƙal ya goce, sannan shima ya mayar da martani.
Kafun a jima sun kaiwa junansu sara sau tamanin amma babu wanda ya sami nasara.
Samudul Ansari da Zarifa suna can daga zaune suna kallo.
Wannan sarki na ganin cewa, ba zai sami nasara akan Buƙal ba, ya sake fusata.
Jikinsa ya soma yin hazo-hazo yana ɓacewa kamar yadda na wannan sarki na farko yayi.
Kan ka ce me, ya saje da kalar wannan wuri an daina wuri an daina kallonsa.
Buƙal na ganin haka yayi murmushi ya fiddo waɗansu ƙulluka daga cikin aljihunsa ya bibbinne a wannan dajin.
Daga bisani duk ya kunna musu wuta.
Wani irin jan hayaƙi mai ban al'ajabi ya soma tasowa daga cikin wadannan ramuka.
Samudul Ansari da Zarifa suna zaune suna kallo suka soma jiwo tari mai kauri na tasowa daga cikin wannan daji.
Jim kaɗan wannan sarki da jikinsa yayi hazo-hazo ya ɓace ya bayyana, durƙushe akan gwiwowinsa.
Sarki Buƙal yayi dariyar samun nasara sannan yayi tsalle ya fille kansa, ya riƙe kan sannan ya gabatarwa Samudul Ansari shi.
Samudul Ansari yayi murmushi ya sauƙo daga kan wannan bishiya yazo gaban Buƙalshiyyu ya dafa kafaɗarsa ya ce, "A gaisheka namiji, tabbas kayi aiki mai kyau..."
A wannan waje suka ɗauki kan waɗannan sarakuna guda biyu suka nausa cikin wannan daula.
Da wannan Samudul Ansari ya sami nasarar kawar da zalunci a wannan daula, ya kafa adalci.
A da babu inda ya kai daular Irashnur zalunci idan ba Gorgon ba, amma cin waɗannan sarakuna guda uku da Samudul Ansari yayi yasa daular ta dawo ƙarƙashin ikonsa, ya ɗaura wakilansa a daular.
Kai tsaye suka ƙarasa tsakiyar wannan daula, saman wani dogon tsauni wanda yafi wannan wanda Samudul Ansari ya hango waɗannan sarakuna guda biyu akansa.
Samudul Ansari ya fiddo wannan kwalba wadda sarki Azman na duniyar iska ya bashi, ya shanye abinda ke cikinta.
Sinadarin cikin kwalbar, na gama shigewa cikin cikinsa, wani irin baƙin hayaƙi wanda ya ninka asalin nasa a duhu da kauri ya soma ɓulɓula daga jikinsa.
Sannu-a-hankali hayaƙin ya gama cinye jikinsa, ya zamana babu abinda Zarifa da Buƙal suke kallo idan ba baƙin hayaƙin ba.
Wata irin wuta jajazur ta soma tasowa daga cikin wannan baƙin hayaƙi, kai kace gangar jikin Samudul Ansari ce ke babbakewa.
Tsahon rabin sa'a kafun jikinsa ya sake haɗewa ya dawo yadda yake.
Abinda Zarifa ta lura da shi shine babu wani sauyi a jikinsa amma akwai abubuwa guda biyu da suka bayyana wadda a da babu su.
Abu na farko shi ne, wani zane baƙi ƙirim akan gefen ƙirjinsa na dama. Zanen yana da yanayi kamar na aljani amma idan ka ƙura masa idanu yana kama da tau'rin.
Abu na biyu ma, zane ne na wani aljani mai gangar jikin wuta, sai dai shi wannan aljani a ƙasan gashin kan Samudul Ansari yake ta bayan wuyansa.
Kwarjinin sarki Samudul Ansari ya sake ninkuwa sau goma.
Ƙarya ne mutum yayi arba dashi a wannan siffa, sannan ya kalli cikin idanuwansa yayi masa magana yadda yake so.
Samudul Ansari, Zarifa da sarki Buƙal suka sake kewaya wannan daula, suka kafa adalci da ƙarfin mulki wadda ƙarya ne wani ya karya shi, sannan suka kama hanyar komawa daular Shaha.
****
~Daular Gorgon.
****
Wannan rana ita ce cikon shekaru goma sha-uku cir! sarauniya Yilan, Gauhan da kuma BES suna cikin tukunyar macijiya Ziyazilu suna zuƙar sinadarin cikinta.
A duk rana guda jikinsu yana zuƙar sinadari guda miliyan ɗaya zuwa biyu.
Kullum jikinsu ƙara ƙarfafa yake. A kullum sai mahaifin sarauniya Yilan wanda ya kira kansa da suna SARKI JIZ'BAN yazo cikin wannan ɗaki ya duba wannan tukunya.
Yana ficewa daga wannan ɗaki zai koma wannan gida nasa dake cikin daji, ya duba halin da Samudul Ansari ke ciki.
Zaka iya cewa, yana sane da duk wani motsi na Samudul Ansari tun kafun ya fito daga wannan daula tasa.
Sarkin na ganin cewa, Samudul Ansari ya sami nasarar shan wannan tsumi sannan ya bautar da Buƙal sai ransa ya ɓaci zuciyarsa ta soma tafarfasa.
Cikin gaggawa ya sake ɓacewa, ya bayyana a ɗakin bauta inda macijiya Ziyazilu take.
Sarki Jiz'Ban ya ƙarasa gaban wannan macijiya ya sanar da ita abinda ke faruwa cikin yarensu, daga ƙarshe ya nemi izininta domin ya kaiwa Samudul Ansari hari wanda zai ji masa yasa ya dakata da shirye-shiryen tarar su da yake.
Ziyazilu ta amince da wannan ƙuduri nasa, sannan ta bashi umarnin matsowa gaba domin ta saka masa albarka.
Sarki Jiz'Ban ya taka ya ƙarasa har gaban waɗannan jajayen duwatsu waɗanda Ziyazilu take kwance akansu, ya durƙusa a gabanta.
Ziyazilu ya sari jikinsa da bakinta, wani irin jan dafi ya fito daga bakinta sannan ya shige cikin jikinsa.
Wata jar walƙiya ta soma shigewa cikin jikin nasa tana ƙara masa ƙarfi.
Sai da suka shafe sa'a uku, Ziyazilu tana zuba masa wannan dafi sannan ta gama.
Sarki Jiz'Ban ya zube ƙasa kwance saboda ƙarfin sinadaran da suka shiga jikinsa.
Tsaho kwanaki uku cir! yana kwance a ƙasa a cikin wannan ɗaki gaban Ziyazilu, sannan ƙarfin jikinsa ya dawo.
Cikin taƙama da ƙarfi ya mike tsaye, ya kwarara uban ihu.
Irin wannan jan sinadari da ya shiga jikinsa ya soma zubowa ƙasa yana taruwa.
Tsahon daƙiƙu kafun Jiz'Ban ya saka hannunsa cikin sinadarin ya ɗauko wani zabgegen mashi jajawur tamkar wanda aka gasa da wuta.
Sarkin ya sake zubewa a gaban Ziyazilu yayi godiya sannan ya ce, "Tabbas na samu isasshen ƙarfi wanda zai bani damar illata sarki Samudul Ansari..."
Yana gama faɗin haka, ya juye izuwa jibgegen maciji, macijin ya shige cikin wani dogon rami zururu ya ɓace daga cikin wannan ɗaki gaba ɗaya.
****
Samudul Ansari, Zarifa da sarki Buƙalshiyyu Djinn suka ci gaba da tafiya a cikin wannan daula, su kwana nan, su tashi can, har tsahon watanni uku.
Zarifa ta dubi sarki Buƙal ta sake duban Samudul Ansari ta ce, "Ya kai mijina! Shin ta ya ya ka bautar da wannan gagarumin sarki na wannan daula, sannan meyasa ka bautar da shi?"
Samudul Ansari na jin wannan tambaya ya ce, "Yadda aka yi na bautar da wannan aljani shi ne, wani ɓangare daga cikin jinin zuciyarsa na ɗiba na baiwa ɓoyayyen hadimi yaje ya gudanar da wani aiki dashi.
"Dalilin da yasa na bautar da shi kuwa, babu wanda zan bayyanawa kowa a yanzu ba, face lokaci yayi..."
Haka dai suka ci gaba da tafiya suna tattaunawa har tsahon ɗan lokaci.
Ba zato ba tsammani! suka ga ƙasar da suke bisa kanta ta fara tsatstsagewa, wani irin shuɗin hayaƙi ya soma ɓulɓulowa daga cikinta.
Samudul Ansari yana ganin wannan koren-hayaƙi ya shaida shi, saboda ya taɓa kallonsa amma a waje guda.
Cikin gaggawa ya zaro takobin Saif-Al-Barzaƙ, sannan ya dafa wannan hatimi dake bayan wuyansa na aljanin-wuta ya ce, Nara ka shirya...
Samudul Ansari ya dubi sarki Buƙal da Zarifa ya ce, "Ku ruga da gudu izuwa cikin wannan daji, kada ku kuskura ku tsaya a ko'ina, zan zo na riske ku. Djinn idan matata ta gaji, ka goyata..."
Zarifa da Buƙalshiyyu suna jin umarnin sarki, suka ruga da gudu izuwa cikin wannan daji.
Tun Samudul Ansari yana hango su, har sai suka ƙule ya daina hango su.
A daidai lokacin ne kuma, wannan koren-hayaƙi ya gama haɗewa a waje guda, ya bayar da siffar wani garjejen mutum wanda ya fara manyanta.
Mutumin zai fi Samudul Ansari tsaho da kauri, sannan yana da cika-ido.
Fuskarsa a murtuƙe take tamkar bai taɓa dariya ba, yana rataye da zabgegen mashi jajawur a gadon bayansa.
Waɗansu macizai koraye guda huɗu suna yawo akansa a matsayin gashi.
Idanuwansa sun sauya launi, sun koma koraye kamar na sarauniya Yilan.
Kai a taƙaice kallon wannan mutumi kaɗai, razanarwa ne.
To, amma idan mutum yayi duba izuwa ɓangaren Samudul Ansari shima zai fuskanci lallai ya sauya.
Wani irin jan haske mai kama da jar wuta yana kewaye jikinsa ko'ina da ko'ina, kwayar idanuwansa ta sauya izuwa ta wuta.
Gashin kansa ya soma fitar da jan hayaƙi tamkar wuta ke tashi a cikin kansa.
Irin wannan siffa ta Samudul Ansari babu wanda ya taɓa kallonsa da ita.
Wataƙila a cikin wannan tsumi da sarki Azman ya bashi ya sameta.
Waɗannan hatsabiban mutane guda biyu, suka yi kallon-kallo na tsahon daƙiƙu kafun su matso kusa da juna.
Samudul Ansari ne ya fara magana, "Ance ba za ku sake kawo min hari ba, sai bayan shekaru ɗari, shin ko wanne dalili yasa ka kawo min hari yanzu..?"
Sarki Jiz'Ban yayi dariya ya ce, "Yaudara ce kurum yaro, idan ba mun yi maka hakan ba, ta ya ya zan sameka a irin wannan hali da kake yanzu, baka gama kimtsawa ba?"
Samudul Ansari yayi dariya ya ce, "Cikakken mutun kullum a shirye yake, nafi ƙarfin tarkonka ya kama ni... Ko a yanzu ma, ina da tabbaci ba zaka yi min komai ba,"
Sarki Jiz'Ban ya zaro takobinsa ta Bankai mai mataki na casa'in da takwas.
Mutum-mutumi na farar ƙasa guda takwas suka bayyana a bayan sarki Jiz'Ban, kowannensu rataye da zabgegen maciji a wuyansa.
"Anya kuwa, yaro?" inji Jiz'Ban. "da cikakken shirina nazo fa!"
Samudul Ansari yayi murmushi ya ɗaga takobin Saif-Al-Barzaƙ sama, lamarin

Please Login or Register in order to submit comment