Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

cikin takaici.
Marganu ya kwarara uban ihu ya ce, "SAI NI DODON MAZA, MAI SA ƘANANU SU GUDU."
Yana gama wannan ihu, ya juya wannan takobi dake hannunsa, take wannan daji mai yawan duwatsu ya ɓace ɓat!
Fadar daular Gorgon ta maye gurbinsa.
Ileisha, Narima da Laila suna ganin Marganu ya dawo a fusace, suka ruga gabansa suna dudduba shi.
Marganu ya dubi Narima da Laila ya ce, "Birnin Kubwan ya faɗi, ku je kusa a sake gina shi sannan a binne wadanda suka mutu."
Laila da Narima suka zube a gabansa suka ce, an gama, ISRABIL.
Marganu ya dubi Ileisha ya ce, "Ke kuma ki shirya mini gagarumin biki irin wanda ba'a taɓa yi a wannan daula. Lallai a wajen da zan tabbatar cewa da ni ISRABIL ne, a wajen zan auri Firziyya."
Ileisha ta zube ta ce, "An gama!"
Marganu ya shige cikin gidan sarautar, hadimai da dakaru suna ta zubewa a gabansa.
Kafun yaje yankin da aka ajiye gimbiya Firziyya ya faɗa cikin wani ƙaramin tafki yayi wanka, sannan ya saka riga da wando na haske ya tunkari yankin nata.
Yankin ya yiwa Marganu kamar yadda yake so. An ƙawata shi yadda zai yiwa gimbiya kowacce iri ce daidai.
Hadiman yankin suna ganin Marganu ya tunkaro shi, suka fara zubewa a ƙasa suna gaisuwa.
Tun kafun ya iso tuni labari ya riski Firziyya.
Cikin gaggawa tayi wanka ta saka kaya masu tsananin kyawun gaske sannan ta saka bayi suka kunna turare a cikin wannan ɗaki ta ko'ina.
Marganu yana shigowa cikin wannan ɗaki, turare mai ƙamshin gaske ya doki hancinsa.
Yana ɗaga kansa yayi arba da Firziyya tana tahowa riƙe da farantin abinci, tana wata irin tafiya mai jan hankali.
Marganu yayi sauri ya kawar da kansa daga ganinta saboda zuciyarsa zata iya rinjayarsa wanda kuma ba zai iya yin hakan ba, saboda ya yiwa kansa alƙawari.
Marganu ya zauna a tsakiyar wannan ɗaki, Firziyya ta ƙaraso gabansa.
Yana daga zaunen ta sunkuya ta rungume shi cikin tsananin farin ciki.
Marganu yayi murmushi ya nuna mata waje ya ce ta zauna.
A hankali ta zauna a wajen sannan ta fuskance shi.
Gimbiya Firziyya da kanta ta ɗinga bashi abinci har sai da ya ƙoshi sannan ta bashi ruwa mai sanyi yasha.
Marganu ya fara bata labari.
"Na kai farmaki birnin Damashkar inda gimbiya Jaanu take mulki. Na ruguje birnin sannan nayi mata mummunan fyaɗe.
"Alƙawarin da na ɗauka akan gimbiya Jaanu guda biyu ne: na farko nace zan yi mata fyaɗe kuma na cika wannan alƙawari. Na biyu nace zan datse mata wuya wanda shi ne kawai ya rage.
"Babban dalilin da ya hana na kusance ki kuma ya hana na aureki shi ne, na yiwa kaina alƙawari gimbiya Jaanu zan fara sani 'ya mace. Idan ba ki manta ba, farkon haduwata dake, keda kanki kika nemeni amma ban biya miki buƙatarki ba saboda wannan alƙawari.
"To, a yanzu na cika wannan alƙawari, kuma tuni har na bayar da umarnin fara shirye-shiryen bikinmu."
Gimbiya Firziyya tana jin wannan batu gagarumin farin ciki ya lullubeta.
Ta faɗa kan ƙirjin Marganu suka rungume juna cikin tsananin farin ciki.
Lallai Marganu ya yiwa soyayyarta halacci, duk tsananin ƙiyayyar dake tsakaninsa da mahaifinta, ko kaɗan baya nuna mata tsana.
Marganu ya janye jikinsa daga nata ya ce, "NA ZAMO CIKAKKEN ISRABIL! A wajen da zan tabbatarwa wannan daula ni ne ISRABIL a wajen za'a ɗaura mana."
"Na godewa Ubangijin da ya bani masoyi na ƙwarai, tabbas Jaanu tayi babbar asara." inji Firziyya.
"Hmm," Marganu yayi murmushi. "Shekaran-jiya mahaifinki ya kawo min farmaki. A lokacin da ya shigo wannan daula, ina cikin tukunya ina zuƙar sinadarai. Hakan yasa ya samu gagarumar nasara a wannan daula.
"Mahaifinki ya ruguje ɗaya daga cikin manyan biranai na wannan daula amma nayi masa kyakkyawan hukunci, kaɗan ya hana na sare kansa tsinanniyar guguwa ta cece shi."
Gimbiya Firziyya tana jin wannan batu jikinta yayi sanyi ta dubi Marganu ta ce, "Na so ka sare kansa, saboda hakan zai sa zuciyata tayi sanyi.
"Mahaifina ne shi amma baida bambanci da maƙiyi. Tun ina yarinya ƙarama ya rabani da mahaifiyata, a wannan lokaci ba don kazo ka ceceni ba, da tuni nima ya rabani da rayuwata.
"Lallai ina buƙatar faɗuwar wannan mutumi."
Marganu ya ce, "Da sannu lokaci zaizo da zai faɗi... Da sannu lokaci zaizo da zamu samu nasara akansa. Gudunsa da ja da bayansa ba zai amfane shi ba..."
Gimbiya Firziyya ta gyaɗa kai ta ce, "Ya kai masoyina! Mene ne dalilin da yasa baka sare kan gimbiya Jaanu, alhali ka samu nasarar yi mata fyaɗe?"
Marganu ya dubeta ya ce, "Saboda a wannan lokaci ina fafatawa da mahaifinki ne, sannan Aymanul Faris ma yazo domin kawo mata ɗauki.
"Kaɗan ya hana na hallaka Aymanul Faris, baƙin-hayaƙi ya cece shi."
Marganu yana zuwa nan a zancensa ya nuna mata kansa da hannu ya ce, "A yanzu ni DODON MAZA ne mai sa mazaje su gudu. Duk wanda ya gwabza dani sai dai yayi gudun ceton rayuwarsa..."
Gimbiya Firziyya tayi murmushi ta ce, "Wannan haka yake... Amma yaushe zamu kaiwa Jaanu farmaki, saboda na tsani na tuna cewa tana raye. A duk lokacin da na tuno irin abinda ta janyowa rayuwarka sai naji na tsaneta."
Marganu ya ce, "A yanzu farmakar gimbiya Jaanu ba zai yi sauƙi ba, saboda Aymanul Faris ya mallaki tau'rin. Daga baya zanyi tunani akan hakan."
Haka dai Marganu da masoyiyarsa Firziyya suka ci gaba da tattaunawa har tsahon ɗan lokaci, sannan Ileisha tazo ta shaidawa Marganu an gama shirya komai.
Marganu yayi murmushi ya dubi Firziyya ya ce, "Ki kammala shiryawa, nan da cikar sa'a uku za'a ɗaura mana aure."
Gimbiya Firziyya tana jin wannan batu ta sake faɗawa kan ƙirjin Marganu a karo na farko suka sumbaci junansu a baki.
Marganu yayi sallama da ita ya fice daga wannan yanki, sannan yasa Ileisha Gorgon ta kawo masu gyara amarya.
Kafun cikar sa'a uku gaba ɗaya daular Gorgon ta ɗauka.
ISRABIL zai nuna baiwarsa sannan zaiyi aure a wajen da zai nuna baiwar tasa.
Cikin ƙanƙanin lokaci wajen da aka shirya za'ayi wannan biki ya cika ya batse da tarin al'umma.
Iya ganin mutum jama'a ne rututu.
A tsakiyar wajen waɗansu mutane guda goma suka zazzauna, suka kewaye inda za'ayi ɗaurin auren.
Jim kaɗan Ileisha Gorgon ta fito tare da waɗansu 'yan mata guda goma waɗanda suka kewaye Firziyya a tsakiya.
A wannan rana an yiwa Firziyya ado na musamman.
Kyawu idan ya haɗu da ado, abin sai ya zamo abin burgewa ga kowa.
Duk wanda ke zaune a wannan waje bai isa ya yiwa Firziyya kallo ɗaya ya kawar da kai ba, saboda tsananin kyawunta.
Kai da yawa daga cikin waɗanda ke zaune a wannan waje buɗe baki suka fara. Lallai a yau sun ga kyakkyawar da ya kamata ta zamo matar ISRABIL.
Ileisha da waɗannan 'yan-mata suka ƙaraso da Firziyya tsakiyar wannan waje suka zaunar da ita a tsakiyar waɗannan mutane guda goma.
Bayan ɗan lokaci kowa yana zaune zuru-zuru ana jiran zuwan Marganu, kawai sai aka ga wata tauraruwa mai tsananin haske ta bayyana a wannan waje.
Iko na musamman ya fito daga cikin wannan tauraruwa ya doki dukkan jama'ar dake wannan waje.
Nan take kowa ya dawo taitayinsa, sannan aka sake nutsuwa ana jiran zuwan Marganu.
Jim kaɗan Marganu ya bayyana a wannan waje, a cikin shiga mai ban al'ajabi.
Rigar jikinsa alkyabba ce mai ɗan tsaho, sannan ya saka dogon wando wanda yazo har idon-sahu.
Sannan ga wannan hular sarauta akansa mai taken "ISRABIL"
Wannan shiga da Marganu yayi kawai ta tabbatar da waye shi, saboda komai na jikinsa na haske ne.
Gaba ɗaya jama'ar wannan waje suka zube suka yi gaisuwa ga babban sarki.
Marganu ya ƙarasa gefen Firziyya ya zauna.
Waɗannan mutane guda goma suka soma rero baitoci, suna ambaton sunan Marganu da na Firziyya har tsahon rabin sa'a sannan suka kammala.
A wannan lokaci aka ɗaura aure tsakanin MARGANU da FIRZIYYA.
Hadimai suka kawo abinci mai tsananin yawan gaske wannan waje, aka rarrabawa kowa da kowa.
Wannan shi ne al'adar aure a wannan daula, da zarar anyi hakan aure ya ɗauru.
Kwanaki uku cir! aka shafe ana biki sannan aka kammala.
Wata rana da dare Marganu ya shiga ɗakin amaryarsa, inda ya isketa zaune ta sha lulluɓi tana kallon ƙasa.
Marganu ya fidda wannan lulluɓi nata sannan ya tasheta tsaye suka je cikin wani ƙaramin tafki suka fara wanka.
A cikin wannan tafki Marganu ya fara sanin Firziyya 'ya mace, suna kammalawa suka fito, suka kwanta suka yi barci.
Daga wannan rana Marganu ya fara zuwa wannan maɗaukakiyar fada yana zama akan wata ƙatuwar karaga ta mulki wadda aka gina musamman domin shi.
Marganu ya ci gaba da jan ragamar wannan daula a matsayinsa na ISRABIL.
*****
Yau *19/06/2023*
Babi na gaba zaizo *22/06/2023* da izinin ALLAH.
RUHIN JARUMTAKA!
*
Babi na 146: *Ragas*
*
Wannan littafin sadaukarwa ne ga Zahra...
*
U~M~S
*
Aymanul Faris yana ƙarasowa gaban Marganu ya kawo masa wawan sara da wannan takobi.
Marganu ya ɗaga takobin-taswira sama ya juyata a hankali, take wannan waje da suke ya juya.
Aymanul Faris ya juya masa baya, Marganu ya yi guntun murmushi ya kaiwa Aymanul Faris wawan sara da nufin ya yi masa lafcecen sara.
Aymanul Faris ya goce cikin zafin nama, amma dukda haka sai da takobin Marganu ta ɗan yanke shi.
Wani irin zogi da raɗaɗi ya ratsa Aymanul Faris, ya waigo cikin zafin nama na gaban tunani shima ya kaiwa Marganu sara.
Marganu yasa takobin dake hannunsa ya kare saran, takubban nasu na haɗuwa a waje guda.
Alamar yanka ta ɗan bayyana akan ƙarfen takobin Marganu saboda tsananin kaifin BINA-KIL-DEM.
Marganu ya janye takobinsa daga jikin ta Aymanul Faris sannan ya juyata a hankali.
Wannan waje ya sake juyawa, Marganu ya sake kaiwa Aymanul Faris sara a gadon baya.
Kafun takobin ta riski Aymanul Faris ya goce mata cikin zafin nama, ya juyo ya dubi Marganu ya ce, "Ƙananun jarumai ake samun nasara akansu sau ɗaya, sannan a ci gaba da samun nasara akansu kullum. Daga lokacin da kayi amfani da dabarar yaƙi akaina, daga wannan lokaci ta daina amfani.
"Saboda zan ɗauketa ne na gane yadda take, sannan nayi ƙoƙarin kare kaina daga sharrinta. Don haka nake baka shawara da ka sauya salon yaƙi..."
Marganu yana jin wannan batu yayi dariya, bai yarda da abinda Aymanul Faris ya ce ba. Ya sake juya wannan takobi, wannan waje ya sake juyawa Aymanul Faris ya sake bashi baya.
Marganu ya sake kai masa sara, Aymanul Faris ya goce cikin zafin nama.
Dukda haka saida Marganu ya jarraba hakan sau biyar bai sami nasara ba, sannan ya tabbatar da cewa, Aymanul Faris ya gano sirrin wannan takobi.
Babban abinda yake taimakon Aymanul Faris a wannan yaƙi shi ne, tsananin zafin namarsa domin da zarar Marganu ya kawo masa sara ko suka cikin zafin nama yake kaucewa.
Aymanul Faris ya dubi Marganu yayi murmushi, yana lissafi a ransa akan yadda zai rama wannan yanka da Marganu yayi masa a gadon baya.
Jim kaɗan idanuwansa suka kai kan wata bishiyar dabino dake gefen wannan tafki.
Aymanul Faris yana ganin wannan bishiyar dabino, ya juya da baya ya falfala da azababben gudu ya tunkare ta.
Marganu na ganin haka yayi murmushin mugunta, ya bishi da gudu.
A tsammaninsa Aymanul Faris ya tsorata ne, shiyasa ya gudu.
Marganu yana mai ɗaga wannan takobi dake hannunsa, babban burinsa shi ne ya yiwa Aymanul Faris irin raunin da ya yiwa Kuffuru da ita.
Ita dai wannan takobi munji cewa, babban matsafi na daular Nehiya yana cewa, babban illarta shi ne tana ɗaukar taswirar jikin wanda ta yiwa rauni sannan ta mayar dashi kamar gunki.
Kafun ta samu nasarar hakan a jikin mutum ana buƙatan kamar rabin kaifin takobin ya nutse a jikin mutum.
Don haka Marganu yake ƙara azama wajen ganin ya riski Aymanul Faris domin yayi sara wawan sara da ita.
Aymanul Faris yana isowa gaban wannan bishiyar dabino ya juyo ya kalli Marganu, sannan yasa ƙafafunsa ya taka jikin bishiyar dabinon yayi sama.
Marganu yana ƙarasowa Aymanul Faris ya daka tsalle ya dira a bayansa.
Kafun Marganu ya juyo tuni shima Aymanul Faris ya saka BINA-KIL-DEM ya sari bayan Marganu da ita.
Dukda cewa Marganu ya ankara da wuri sannan ya kauce, amma dukda haka sai da wannan takobi ta ɗan sare shi.
Yankan da takobin tayi masa baida zurfi sosai, shi kansa ya raina yanka amma bisa mamaki yaga jini ya fara zubowa daga cikin yankan tamkar yayi zurfi sosai.
Lamarin da yasa Marganu fusata kenan, ya afkowa Aymanul Faris suka ruguntsume da azababben yaƙi mai ban tsoro.
Dukda cewa a jikin kowannensu akwai raunika sannan jini yana zuba daga raunikan, hakan bai rage musu ƙarfi ko zafin nama ba.
Kaiwa junansu sara da suka suke cikin zafin nama. Kai kace jikinsu bai kasance tsoka da jini ba.
BAƘAƘEN MAHAYA da BES suka zubawa wannan gumurzu idanu cikin tsananin mamaki, kuma suka tabbatar da cewa, faɗan da suka yi a ɗazu wasa ne.
Inda takubban dake hannun Aymanul Faris da Marganu basu kasance kimtsatstsu ba, da tuni sun daƙushe sun kakkarye.
Amma saboda hatsabibancin takubban suna nan lafiyarsu ƙalau.
Sai dai a duk lokacin da suka haɗu, tartsatsin wuta yana zubowa ƙasa.
Koda suka sami kamar sa'a guda suna fafatawa, ba tare da ɗayansu ya sami nasara ba, sai suka fusata suka daka tsalle baya sannan suka fara kallon juna cikin nutsuwa.
Kowa daga cikinsu yana tunani da nazarin yadda zai gama da abokin gabarsa farat daya.
Kusan daƙiƙu saba'in suna ta kallon juna, kafun su falfalo da azababben gudu kan juna.
Koda ya rage saura kamar taku bakwai su haɗu, sai duk suka daka tsalle sama.
Suka wuce juna a saman, sannan suka dira acan baya.
Kowannensu ya tsaya, ba tare ya waigo ba, har tsahon 'yan daƙiƙu.
Kawai sai gani aka yi dukkansu sun fara ƙyarma, sannan sun fara layi tamkar zasu faɗi ƙasa.
Hannun Marganu na hagu ya fara jalo-jalo kamar zai faɗi, wani lafcecen sara ya bayyana akan damtsensa, saboda zurfin saran har farin ƙashinsa ake hangowa.
Shi kuma Aymanul Faris wani wawan sara ne ya bayyana akan tumbinsa, saboda zurfin saran har wata jar fata ake hangowa wadda ana fasata kayan cikinsa zasu zube ƙasa.
Babu yadda za'ayi su ci gaba da wannan gumurzu a haka, saboda idan suka ce zasu ci gaba dukkansu mutuwar ragas zasu yi.
A wannan lokaci, da suke tsaitsaye sun yi asarar jini mai yawan gaske daga jikinsu.
Koda yake ISRABIL da tau'rin basa jikin Aymanul Faris da Marganu amma suna tsaitsaye a gefe guda, riƙe da abin rubutunsu.
Cikin tsananin ƙarfin hali irin na asalin manyan jarumai, Marganu ya zaro takobin Tarwatsa-komai ya tunkaro Aymanul Faris da nufin ya caka masa wannan takobi ya yi daga-daga da namansa.
Yana tafe yana tangaɗi tamkar zai kife ƙasa amma a haka ya ƙaraso gaban Aymanul Faris ya ɗaga wannan takobi zai caka masa.
BAƘAƘEN MAHAYA da BES suka kalli Marganu cikin tsananin mamaki, babu wanda ya taɓa tunanin zai iya motsawa daga inda yake balle har ya kai hari.
Sannan idan suka yi izuwa ga raunin da Aymanul Faris yaji kuwa, zasu iya cewa, ƙarshen Aymanul Faris yazo.
Saboda ko motsi mai ƙarfi idan Aymanul Faris yayi, raunin zai iya farkewa kayan cikinsa su zubo ƙasa.
Takobin Marganu tana daf da dira a jikinsa, cikin zafin nama ya zaro Saiful-Shiradu ya tare ta.
Takubban guda biyu suna haɗuwa aka sake kwararo uban tsawa wannan waje, iska mai ƙarfi tayi jifa da su gefe guda.
Saboda munanan raunikan dake jikinsu, dukkansu suka bingire ƙasa suka gagara motsawa.
Jini ya ci gaba da malala daga jikinsu.
Cikin tsananin ɗimaucewa BAƘAƘEN MAHAYA suka ruga suka ɗauki Aymanul Faris, BES suka ruga suka ɗauki Marganu.
A wannan lokaci ko tunanin afkawa juna basu yi ba, saboda idan suka ɓata lokaci kaɗan dukkan waɗannan mutane guda biyu mutuwa zasuyi.
BES suka juya suka nufi hanyar da suka fito, BAƘAƘEN MAHAYA suka tsala azababben gudu suka koma cikin wannan jirgin ruwa wanda suka zo daular Gorgon a cikinsa.
Nan take suka fara shawara akan wanda ya kamata ya yiwa Aymanul Faris taimakon-gaggawa saboda ana jinkirtawa kaɗan zai iya mutuwa.
Kafun su gama yanke shawara likita Laziyya ta bayyana a cikin wannan jirgi ɗauke da kayan aiki.
Ba tare da cewa ɗayansu uffan ba, ta duƙufa akan Aymanul Faris ta fara masa aiki.
****
Kai tsaye BES suka ƙarasa da Marganu cikin gidan sarautarsa. Suka kaishi cikin wani ɗaki na musamman suka kwantar dashi akan gado.
Jim kaɗan babban likita na wannan daula ya shigo cikin wannan ɗaki, ya yiwa Marganu magunguna akan waɗannan raunika na jikinsa sannan ya bashi maganin barci mai ƙarfi yasha.
Saida Marganu ya shafe sa'a huɗu yana sharara barci sannan ya farka.
Yana buɗe idanunsa yayi arba da matarsa Firziyya zaune a gaban wannan gado ta ƙura masa idanu tana kuka.
Marganu ya dubeta cikin tsananin mamaki ya ce, "Matata! Mene ne dalilin da yasa kike kuka?"
Firziyya ta share hawayen idanunta ta ce, "Ni gaskiya wannan doka da ka saka min ta fara damuna. Ya ya ina jaruma zan zauna a gida cikin daula na bar ka, kana shan wahala a filin daga?
"Shin ya ya kake tunanin zan yi da rayuwata idan akace ka riga ni mutuwa?"
Marganu ya yi murmushi ya ce, "Wannan shi ne dalilin da yasa kike kuka? Kwantar da hankalinki, kiyi sani cewa abokin gabar da na kara dashi yau, duk duniya babu wanda ya isa yayi gaba-da-gaba dashi idan ba ni ba.
"Kina son sake fita yaƙi? Na miki alƙawarin za ki sake fita yaƙi amma sau ɗaya..."
Firziyya ta dube shi a nutse ta ce, "Na ji. Yanzu ya jikin naka? Ina fatan babu inda yake maka ciwo ko?"
Marganu yayi dariya ya ce, "Haba na isa! Kaɗan ya hana ya fille hannu gaba ɗaya fa, kuma kwata-kwata yaushe ma aka gyara ciwon?
"Daɗinta dai, shima ya samu mugun rauni a jikinsa wanda yafi nawa muni..."
Firziyya ta dafa hannunsa da nata ta ce, "Ni dai bana so kana yawan magana, ya kamata kayi shuru ka huta sosai. Ko zaka warke da wuri..."
Marganu ya yi murmushi ya ce, "To shi kenan, matata. Zan yi kamar yadda kika ce."
Daga wannan batu suka yi shuru, basu sake cewa komai ba, Firziyya tayi ta yiwa Marganu tausa har barci ya sace shi.
****
A can daular Shaha kuwa, koda aka ga wannan hali da sarki Aymanul Faris ya tsinci kansa a ciki sai hankalin kowa yayi mummunan tashi.
A wannan lokaci Aymanul Faris ya gama tsara daular Shaha izuwa waje mani'imci wanda ko alamun tashin hankali babu a cikinsa balle fargaba ko tsoro.
Bayan wannan albarkar noma a daular Shaha ta sake farfaɗowa fiye da da, gagarumar cibiya ta kasuwa ta kafu a cikin daular.
Attajirai daga ɓangarori dabam-dabam na duniya suna zuwa daular Shaha su sayi abinci sannan su tafi sauran ƙasashe suna sayarwa.
A taƙaice dai, daular Shaha har ma ta ninka da a komai.
Ana shigowa da Aymanul Faris wannan daula, BAƘAƘEN MAHAYA guda ɗari suka kewaye keken dokin da aka kwantar dashi a ciki domin tabbatar da tsaro.
Tun kafun su iso gidan sarauta tuni labari ya riske su.
Gimbiya Jaanu, jaruma Riya da Hajriya sun gagara zaune ko tsaye, suna ta kaiwa da komowa a cikin gidan sarautar.
Kawai suna so su ga halin da Aymanul Faris yake ciki.
Musamman gimbiya Jaanu. Tun sa'adda ta auri Aymanul Faris soyayyarsa a cikin zuciyarta ya ninku sau ba adadi.
Ko wannan tafiya da Aymanul Faris yayi, kullum hankalinta a tashe yake.
Babu abinda take jira kullum kamar dawowarsa.
Ita dai ko ba komai, suna kwana a waje ɗaya tana jin ɗuminsa a kusa da ita.
Daf da azahar aka ƙaraso da Aymanul Faris gidan sarautar.
Cikin gaggawa Jaanu, Riyalatu da Hajriya suka ƙarasa cikin ɗakin da aka kwantar Aymanul Faris.
Jaanu da Riyalatu suka faɗan kan gadon da yake suka rungume shi.
Koda Jaanu tayi arba da lafcecen saran dake kan cikin Aymanul Faris sai ta fashe da kuka.
Saboda wanda bai saba ganin raunika ba, idan yaga wannan rauni na kan cikin Aymanul Faris, zai ce ƙarshen Aymanul Faris yazo kawai.
A wannan lokaci Aymanul Faris yana barci sakamakon maganin barcin da aka bashi yasha.
Saida ya shafe kwanaki biyu yana wannan barci sannan ya farka. Tsahon wannan lokaci kullum idanun gimbiya Jaanu suna kansa.
Lamarin da yayi baiwa Hajriya da Riyalatu mamaki kenan, basu taɓa ganin soyayya irin wannan ba.
Babban abinda ya taimaka shi ne, a cikin waɗannan kwanaki biyu raunin dake kan tumbin Aymanul Faris ya fara haɗewa.
Hakan yasa hankalin gimbiya Jaanu fara kwanciya.
Lokacin da Aymanul Faris ya farfaɗo da sanyin safiya ne.
Jaruma Riya da Hajriya suna can kwance a ɗaki dabam, ita kuwa Jaanu kamar kullum tana tare dashi.
Tana kwance akan ƙirjinsa hannunta guda a cikin nasa.
Kamar a mafarki taji alamun ya motsa, cikin gaggawa ta miƙe zaune. Ai kuwa take tayi arba dashi idanunsa biyu.
Cikin tsananin farin ciki, gimbiya Jaanu ta sumbace shi a goshi.
"Masoyina, ya ya jikin naka?" ta ce.
Aymanul Faris yayi guntun murmushi ya ce, "Ina lafiya, ya kuke ku ma?"
"Muna nan lafiya, shin ka hukunta Marganu?" inji gimbiya Jaanu.
Aymanul Faris yayi guntun murmushi ya shafa gashin kanta ya ce, "Kina maganar na hukunta shi sai kace wani ƙaramin mutum. ISRABIL ne fa, wanda mahaifinki da sarki Kuffuru suka gudu lokacin da suka kai masa farmaki."
Hawaye suka zubowa gimbiya Jaanu ta ce, "Mahaifina ya sake bayyana? A ina?"
Cikin tsananin tausayawa Aymanul Faris ya dubeta ya ce, "Kiyi haƙuri, Ubangiji bai ba ki mahaifi na gari ba. Mahaifinki da sarki Kuffuru ra'ayinsu ɗaya,

Please Login or Register in order to submit comment