Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

littafin sadaukarwa ne ga Zahra...
*
U-M-S
*
Idanuwan sarauniya Arya a cike sharkaf da hawaye ta ƙaraso wannan waje. Ta faɗa kan gawar Jalwar da ta Husufa ta fashe da kuka.
Da ƙyar da siɗin goshi, Samudul Ansari da Kusuf suka shawo kanta ta daina wannan kuka.
Samudul Ansari ya baiwa waɗannan dakaru guda ɗari, umarnin ɗaukar yan-uwansu da BES suka kashe.
Ya ɗauki gawar Jalwar akan kafaɗarsa, sannan ya baiwa Kusuf umarnin ɗaukar gawar Husufa.
Nan take suka ɗunguma gaba ɗaya, suka shiga cikin daular Shaha.
Bayan kwanaki uku, aka yi bikin jana'iza aka binne Jalwar da Husufa a waje guda, a bakin wani ƙaramin tafki a cikin gidan sarautar.
Manya-manyan sarakunan duniya da dama saida suka zo gaisuwar jalje wajen Samudul Ansari.
Saboda da yawa daga cikinsu sun sami labarin yadda Samudul Ansari ya turmuza hancin Gorgon a ƙasa.
Duk duniya a wannan zamani, babu inda zaka kewaya baka samu labarin Samudul Ansari ba saboda wannan gagarumar bajinta da yayi.
Bayan cikar watanni huɗu, Samudul Ansari da su sarauniya Arya sun gama jure raɗaɗin rabuwa da su Jalwar.
Samudul Ansari ya baiwa Kusuf umarnin ɗakko kan sarauniya Yilan zasu je daular Gorgon su yi gargaɗi.
Kusuf ya shiga cikin wani daji dake bayan gari, ya haƙo wani rami wanda ya binne wannan dungulmin kai a ciki.
Babu abinda ya sami dungulmin kan tamkar a wannan rana aka sare shi. Kusuf ya cika da tsananin mamaki amma baice komai ba, ya koma fada.
Shi da Samudul Ansari suka je wajen boka Ƙaizadu.
Ƙaizadu ya samar musu da irin waɗannan ingarmun dawakai masu mahaukacin gudu, ya basu.
Samudul Ansari da Kusuf suka haye kan waɗannan dawakai sannan suka zabure su da gudu, suka tasarwa daular Gorgon.
A wannan tafiya sai Kusuf ya lura da cewa, Samudul Ansari yana nuna masa alamun sun kusa rabuwa. Yadda yake magana da yadda yake gudanar da ayyukansa tamkar mai yin bankwana.
Lamarin da yasa Kusuf ya tambaye shi kenan.
"Yau shekaruna ɗari da talati da bakwai a duniya, naci zamani na, bana so na ci na 'ya'yana.
"Tabbas lokacin da zan rabu da ku, ya kusa..."
Cikin tsananin mamaki Kusuf ya dube shi ya ce, "Wanne lokaci kenan, baba?"
Samudul Ansari yayi murmushi ya ce, "Kada ka damu, idan lokacin yazo zaka sani."
Haka dai suka ci gaba da tafiya suna tattaunawa, har suka shigo cikin daular Gorgon.
Duk wani mayaƙin da ya taso musu, yana ganin kan sarauniya Yilan a hannun Kusuf sai kaga yayi mutuwar tsaye.
Kai tsaye, Samudul Ansari suka wuce izuwa babban birnin wannan daula, suka tara dukkan sarakunan daular da masu faɗa a ji.
Samudul Ansari ya karɓi dungulmin kan sarauniya Yilan dake hannun Kusuf ya tsire shi a jikin mashi, sannan ya caka shi a tsakiyar fadar.
Sarakunan daular guda casa'in da takwas suka kewaye su.
Samudul Ansari ya zauna akan karagar sarauniya Yilan ya dube su ya ce.
"Na shigo cikin wannan daula da kaina ne, domin na ja muku kunne kuma nayi muku gargadi akan abinda zai faru da ku, nan gaba."
Samudul Ansari yana gama faɗin haka ya nuna dungulmin kan Yilan dake cake a gabansa ya ce.
"Shin wannan ba kan sarauniyarku bace, wadda kuke ganin kamar tafi ƙarfin kowa a duniya ba?
"Shin ba wannan ce wadda take iya tayar da gawarwakin sarakunan wannan daula tayi amfani da ƙarfinsu ba?"
Waɗannan sarakuna suna jin abinda Samudul Ansari yace, jikinsu yayi sanyi suka rasa abinda ke musu daɗi.
Samudul Ansari ya ci gaba da jawabi, "Sannan ba wai iya sarauniya Yilan ba, hatta waɗannan sarakuna guda ashirin da shida da take kira suna taimaka mata.
"Duk na gama dasu, saboda haka ku nutsu ku ji abinda zan faɗa muku, sannan ku kiyaye..."
Koda waɗannan sarakuna suka ji abinda Samudul Ansari sai mutum goma daga cikinsu suka zaburo zasu afka masa da yaƙi.
Samudul Ansari ya daka musu harara da idanuwansa.
Wannan baƙin hayaƙi ya bayyana, ya kama su ɗaya bayan ɗaya ya tsitstsinka su.
Waɗanda ke zazzaune suna ganin haka, suka sake ruɗewa, suka zazzaro cikin tsananin tsorata.
Samudul Ansari ya daka musu tsawa, suka sake nutsuwa sannan ya ci gaba da jawabi.
"Duk wanda ya sake tunanin tunkarata da yaƙi ko kuma daulata... Wannan baƙin hayaƙi shi ne ajalinsa...
"Daga yau na haramtawa duk wani ɗan ƙabilar Gorgon fita daga wannan daula ta ku.
"Ina da ruhi wanda yake sarrafa TSAFI MATAKI NA SHA-ƊAYA.
"Duk wanda ya karya wannan doka da na kafa muku, a ko'ina nake a faɗin duniya zan gan shi, sannan zan iso inda yake a cikin abinda bai wuce rabin sa'a ba.
"Saboda haka ku bi doka ku zauna lafiya...
"Duk wanda na kama da laifin kashe wani kuwa, zan ƙarar da dukkan danginsa da kowa nasa.
"Duk wanda na kama da laifi daga wannan daula, hukuncin kisa mai muni ne akansa..."
Kafun Samudul Ansari ya ƙarasa rufe bakinsa, wata murtuƙeƙiyar jela ta fito daga cikin wata rijiya dake tsakiyar wannan waje.
Jelar ta kanannaɗe jikin Samudul Ansari sannan ta ɗaga shi sama, ta janye shi izuwa cikin wannan rijiya.
Waɗannan sarakuna guda tamanin da takwas suna ganin abinda ya faru da Samudul Ansari suka bushe da mahaukaciyar dariya, sun san wannan jela ta wacce macijiya ce.
Dukkansu suka zaro takubban Bankai suka kewaye Kusufa a tsakiya zasu afka masa da yaƙi.
Kusufa na ganin haka, ya zaro takobinsa ya zaro takobinsa, ya tsaya a tsakiyarsu yana jira yaga ta ina zasu fara afko masa.
"Kuna tunanin za ku sami nasarar hallaka sarauniya Yilan ce, sannan ku shigo cikin wannan daula tamu. Ku tsira da rayuwar ku?" inji wata murya wadda babu wanda yasan daga ina take.
Wani daga cikin waɗannan sarakuna da suka kewaye Kusufa ya ɗaga murya da ƙarfi ya ce, "Abin kunya ne a gare mu, ace mun yaƙi wannan yaro gaba ɗayan mu. Kamata yayi mu ware mutane goma, su saro mana kansa... Ko ya kuka ce?"
Waɗannan sarakuna suna jin haka, suka ce, kwarai kuwa, mun amince da wannan shawara taka.
Nan take mutum goma daga cikinsu waɗanda suka fi ƙarfi da rauni daga cikinsu, suka turowa su Kusufa.
A fusace sarakuna guda goman, suka ruga da gudu kan Kusufa suka ruguntsume da azababben yaƙi.
****
Samudul Ansari yana buɗe idanunsa ya tsinci kansa a cikin wani tangamemen ɗaki mai girma da faɗin gaske.
Ɗakin yayi masa kama da ɗakin-bauta saboda wasu abubuwa da ya gani a ciki.
A saman wani dogon tudu ya hango macijiya Ziyazilu kwance akan waɗannan jajayen duwatsu ta ƙura masa idanu.
"Kuna tunanin za ku sami nasarar hallaka sarauniya Yilan ce, sannan ku shigo cikin wannan daula tamu. Ku tsira da rayuwar ku?" inji wata murya wadda Samudul Ansari bai san daga ina take ba.
Samudul Ansari ya zaro Saif-Al-Barzaƙ ya ruga da gudu kan macijiya Ziyazilu.
Saura taku uku kacal ta isa inda take, ya daka wawan tsalle sama, ya dira akan wannan tudu sannan ya caka mata takobin.
Wani azababben zogi ya ratsa Samudul Ansari.
Wannan abu yayi matuƙar bashi mamaki, shi ne yayi saran kuma shi ne yaji zogin. Ta ya ya haka zata yiwu.
Sai dai yana dubawa izuwa ƙasa yayi arba da wannan macijiya tana kwance ko motsi bata yi.
Cikin gaggawa ya waiga baya, nan take yayi arba da wani shirgegen aljani mai gangar jiki kamar na maciji.
Daga ƙirjin aljani har zuwa sawayensa duk na maciji ne. Daga sama ne kawai yake aljani.
Yana riƙe da wani zabgegen jan mashi a hannunsa wanda ga dukkan alamu, mashin ya cakawa Samudul Ansari.
"Tabbas ka samu nasarar kashe sarauniya Yilan, amma kaima ka sani cewa, ƙarshenka yazo...
"Babu halittar da aka taɓawa cakawa wannan jan mashin, sannan ta tsira da rayuwarta...
"Komai hatsabibancin mutum, komai ƙarfin sihirin dake jikinsa, indai muka caka masa wannan mashi saiya halaka..."
Samudul Ansari yana jin haka yayi murmushi ya ce, "Koda ka soka min wannan mashi, ko baka soka min ba. Dole wataran zan mutu.
"Na yarda da hakan. Na san cewa wannan jan mashi naku zaiyi ajalina amma ba'a lokaci guda ba...
"Kai kuma daga wannan lokaci, ka gama yawo a duniya... Ba zaka ƙara daƙiƙu ɗari nan gaba ba..."
Kafun wannan aljani ya ankara, tuni Samudul Ansari ya ɓace daga inda yake tsaye.
Cikin abinda bai wuce daƙiƙa biyar ba, sarki Samudul Ansari yasa Saif-Al-Barzaƙ ya fille masa kai.
Kan yayi tsalle izuwa gefe. Jini ya fara malala a ƙasa.
Gangar jikin aljanin ta fara motsawa a hankali, kafun ta daina motsi gaba ɗaya.
Sarki Samudul Ansari ya tunkari wannan ƙaton rami wanda wannan jela ta janyo shi ta cikinta.
****
Ana tsakiyar gwabza yaƙi tsakanin Kusufa da waɗannan sarakuna guda goma.
Kusufa ya ayyana a ransa, SARKIN YAWA YAFI SARKIN ƘARFI.
KOWA A GIDANSA, SARKI NE.
Dukda a wannan lokaci, basu yi masa koda kwarzane ba amma ya soma gajiya saboda tsananin yawansu.
Kusufa ya daka tsalle ya fice daga tsakiyarsu, sannan ya falfala da azababben gudu ya tunkari wannan ƙaton rami wanda aka janye Samudul Ansari cikinsa ɗazu.
Sarakunan guda goma, suka take masa baya da gudu.
Saura ƙiris! Kusufa ya shiga cikin wannan rami, yaga Samudul Ansari ya fito daga cikinsa tamkar harbo shi aka yi.
Cikin gaggawa Kusufa yayi turjiya ta bazato, sannan ya koma bayan Samudul Ansari ya tsaya.
Saif-Al-Barzaƙ dake hannun Samudul Ansari tana ɗigar da wani irin jini kore mai baƙi-baƙi.
Waɗannan sarakuna guda tamanin da takwas suna ganin wannan jini, zuciyoyinsu suka fara bugawa da ƙarfi.
Idanuwansu suka gudun hawaye baƙi ƙirim.
Dukkansu suka durƙushe kan gwiwowinsu, suna cizon yatsun hannunsu cikin tsananin takaici da nadama.
Samudul Ansari ya tunkari karagar mulkin sarauniya Yilan zai zauna akanta.
Nan take yayi arba da waɗansu yara mata guda uku, tsaitsaye a gaban dungulmin kan sarauniya Yilan suna kuka.
Kallo ɗaya Samudul Ansari kawai yayi musu, ya kawar da kai. Yaje kan karagar mulkin ya zauna. Kusufu yazo bayansa ya tsaya.
Samudul Ansari ya dakawa waɗannan sarakuna guda tamanin da takwas tsawa. Dukkansu suka sake dawowa hayyacinsu.
"Na kashe sarki Jiz'Ban!
"Na kashe sarauniya Yilan!
"Na kashe maciji Ziyazilu!
"Wannan ba zai sa ku saduda ba?"
Yana gama faɗin ya miƙe tsaye yazo tsakiyar sarakunan ya tsaya, ya nuna ɗaya daga cikinsu da takobi ya ce.
"Ina fatan kun rubuta waɗannan dokoki da na zayyano muku ɗazu?
"Sannan ina fatan za ku kiyaye su. Saɓawa ɗaya daga cikin dokokina hukunci ne mai tsauri..."
Samudul Ansari yana gama faɗin haka, ya yafito Kusufu da hannu suka tafi.
Wannan shi ne yadda aka yi Samudul Ansari ya karya daular Gorgon a wannan zamani, saboda ya kashe manyan ababen dogaron nasu. Sarki Jiz'Ban, sarauniya Yilan da aljani Ziyazil.
****
Samudul Ansari da Kusuf suna fitowa daga daular Gorgon suka haye kan waɗannan dawakai nasu, suka tasarwa hanyar komawa gida.
Suna cikin tafiya Kusuf yayi arba da ƙaton rauni a gadon bayan Samudul Ansari. Lamarin da yasa hankalinsa ya tashi kenan, ya tambayi Samudul Ansari ina ya sami wannan rauni.
Samudul Ansari yayi guntun murmushi ya ce, "Wannan raunin da kake kallo, irin makamin da aka yi amfani dashi aka kashe Zarifa, da shi aka yi amfani aka yi min shi.
"Babu mahaluƙin da za'a cakawa wannan makami bai mutu ba. Ko shi wane ne?"
Cikin gaggawa Kusuf ya sake duban Samudul Ansari ya ce, "Kenan kaima mutuwa zaka yi, ka barmu kenan..?"
Samudul Ansari ya gyaɗa masa kai ya ce, "Kwarai kuwa. Nima mutuwa zanyi. Sai dai kafun na mutu na cika babban burina.
"Daga yau ba zaku sake fuskantar barazanar Gorgon ba. Saboda na karya duk wani abu da suke taƙama dashi.
"Kafun a ce sun sake dawowa kamar da, aƙalla za'a ɗauki ƙarni goma. Kaga kenan, ba ma zamaninka ba, hatta na jikokinka saiya shuɗe.
"Sanin cewa, komai daren-daɗewa daular Gorgon zasu iya dawowa yasa nayi wani gagarumin aiki..."
Kusuf ya dube shi ya ce, "Baba wanne irin aiki kenan?"
Samudul Ansari ya dafa kafaɗarsa ya ce, "Kada ka damu. Idan muka koma gida zan bayyana maka, kai da mahaifiyarka..."
Daga wannan lokaci, suka ci gaba da tafiya.
Bayan tsahon lokaci, suka iso daular Shaha.
Samudul Ansari bai sanar da sarauniya Arya batun wannan rauni dake gadon bayansa ba, aka ci gaba da tafiyar da komai kamar yadda aka saba.
Bayan watanni biyu kacal! Samudul Ansari ya gayyaci matarsa sarauniya Arya da ɗansa Kusuf domin cin abincin dare.
A cikin wani ƙaton ɗaki aka shirya musu teburin abinci wanda aka cika da abinci kala daban-daban.
Cikin tsananin farin ciki, sarauniya Arya da Kusuf suka shigo cikin wannan ɗaki saboda dama can basu cika cin abinci tare ba.
Suna shigowa cikin ɗakin, suka iske Samudul Ansari zaune yayi shuru fuskarsa cike da jimami.
Nan take jikin Arya da na Kusuf yayi sanyi, suka ƙarasa gefensa suka zauna.
Samudul Ansari ya ɗago kansa ya dube su yayi guntun murmushi sannan ya zuba abinci a cikin farantai guda uku ya miƙawa kowannensu.
Kamar babu abinda ke damunsa, ya saki jikinsa ya fara cin wannan abinci.
Suna ganin haka, su ma suka fara cin wannan abinci. Har dai suka ƙoshi.
Sarauniya Arya ta ɗago kanta ta dube shi ta ce, "Mene ne abinda ke faruwa da kai, mijina?"
Samudul Ansari yayi guntun murmushi. Maimakon ya bata amsar wannan tambaya da ta yi masa, kawai saiya miƙe tsaye ya ɗaga rigarsa ta baya.
Sarauniya Arya da Kusuf suka yi arba da wannan ƙaton rauni da aljani Ziyazil yaji masa. Raunin yana nan kamar yadda yake tamkar a wannan rana aka ji masa.
Hankalinta a tashe ta dube shi ta ce, "Yaushe ka ji wannan rauni, kuma mene ne dalilin da yasa baka nemi magani ba?"
Samudul Ansari ya ce, "Saboda babu maganin da zai warkar da wannan rauni... Mutuwa ce sakamakon duk wanda yaji wannan rauni..."
A gigice sarauniya Arya ta ce, "Kenan ka kusa tafiya ka barmu?"
Samudul Ansari ya koma ya zauna sannan ya dafa kafaɗarta ya ce, "Ki kwantar da hankalinki sannan ki nutsu ki ji abinda zan sanar dake... Mutuwa dole ce akan kowa..."
Sarauniya Arya tana jin abinda Samudul Ansari yace tayi ajiyar numfashi sannan ta gyara zama tana sauraron abinda zai ce.
Samudul Ansari ya dafa kafaɗar Kusuf da hannunsa guda ya ce, "Na bar amanar daular Shaha a hannunka. Ka ci gaba da tafiyar da harkokin mulki kamar yadda na saba.
"Sirrin sabuwar ƙabila zai kare ka da wannan daula daga sharrin duk wani abokin gaba... Dama Gorgon ne kawai nake shakka, amma yanzu nayi musu gargaɗin da ba zasu sake tunanin shigowa Shaha ba."
Idanuwan Kusuf a cike da ƙwalla ya gyaɗa kai, alamar ya karɓi wannan amana.
Samudul Ansari yayi murmushin jin daɗi, ya dubi sarauniya Arya ya ce, "Na kusa tafiya inda masoyiyata Zarifa take...
"Lokacina a duniya ya kusa zuwa ƙarshe.
"Na cimma abubuwa da dama a rayuwata, abinda ya rage min kawai shi ne shiri na ƙarshe wanda zai sake kare wannan daula a karo na gaba koda kuwa daular Gorgon ta dawo..."
Idanuwan sarauniya Arya a cike da ƙwalla ta dubi Samudul Ansari ta ce, "Wanne irin shiri kenan?"
Samudul Ansari ay dubeta cikin nutsuwa ya ce, "Ruhin dake cikin jikina babban sirri ne... Ni kaina har yanzu ban gama gane abubuwa da yawa akansa ba...
"Ruhin baya amfani da ƙarfin sihirin tsafi koda na daƙiƙa. Zallar jarumtaka ne kawai.
"Jikina ya soma gajiya amma wannan ruhi, kullum ƙara ƙarfi yake. Saboda haka dole ne na yiwa na bayana tanadinsa."
Samudul Ansari yana zuwa nan a zancensa yayi gyaran murya sannan ya ƙara ƙarfafa maganarsa.
"ZAN YI TAFIYA IZUWA WANI WAJE MAI HAƊARI A DUNIYA... A WANNAN WAJE ZAN AJIYE WANNAN RUHI A CIKIN WATA KWALBA...
"NAN GABA ZA'A SAMU WANDA ZAI GAJI WANNAN RUHI A CIKIN JIKOKINA...
"FATANA SHI NE WANNAN RUHI, YA SAKE KARE WANNAN DAULA DAGA SHARRIN GORGON A GABA..."
Samudul Ansari yana zuwa nan a zancensa ya dafa kafaɗar Kusuf ya ce, "Kaine sarki wanda zai gaje ni. Ka nutsu ka ji dokokin da zan zayyano maka, wadanda idan kuka bi su wannan daula ta tsira har abada!"
Samudul Ansari yayi shuru ya kama hankalin Kusuf sannan ya ci gaba da bayani.
"DOKA TA FARKO: KADA KU KUSKURA KUYI YAƘI A CIKIN WANNAN BIRNIN!
"DOKA TA BIYU: KADA KU KUSKURA KU BAIWA ƊAN WATA ƘABILA DABAM MULKI A WANNAN DAULA!
"DOKA TA UKU: NA SAN KA KARANCI YADDA NAKE TAFIYAR DA HARKOKIN MULKI. KA CI GABA KAMAR NA SABA..."
Samudul Ansari yana zuwa nan a zancensa ya dafa kan Kusuf ya ce, "Kada ku kuskura ku saɓa doka ta farko... Saboda ku na saɓata zama a cikin wannan birni saiya gagare ku!"
Kusuf ya gyaɗa masa kai, cikin fahimta.
Daidai lokacin ne, wani farin aljani mai fararen tufafi, ya shigo cikin wannan waje. Komai na wannan aljani a lulluɓe yake, yadda su Arya basu iya shaida shi ba.
Samudul Ansari na ganin aljanin ya dube su ya ce, "Ku shirya mana zama gobe a fada da safe, zanzo na naɗa Kusuf sarki sannan nayi bankwana da jama'a na tafi gudanar da aikina na ƙarshe."
Yana gama faɗin haka ya riƙe hannun Kusuf guda sannan yaje gaban sarauniya Arya ya sumbaceta, suka yi sallama ya hau bayan wannan farin aljani ya tafi.
Sarauniya Arya da Kusuf suna kuka tamkar a wannan lokaci ya tafi ne. Tafiya ta har abada.
*****
Yau *24/04/2023*
Babi na gaba zaizo *27/04/2023* da izinin ALLAH.
RUHIN JARUMTAKA!
*
Babi na 116: *Madarul Ansari*
*
***TARIHIN SAMUDUL ANSARI***
*
Wannan littafin sadaukarwa ne ga Zahra...
*
U~M~S
*
Bayan sarauniya Arya da Kusuf sun gama shan kuka, sai suka tashi daga cikin wannan falo. Kowannensu ya koma turakarsa ya kwanta.
A wannan dare dukkansu basu rintsa ba, saboda tunanin maganganun da Samudul Ansari ya faɗa musu.
Tunda asuba sarauniya Arya tasa aka kirawo mata wani hadimi sannan ta bashi umarnin tara dukkan jama'ar dake wannan ƙasa.
Hadimin ya gyaɗa mata kai, sannan ya tabbatar mata da cewa, zaiyi abinda ta umarce shi.
Kafun gari ya gama wayewa tuni wannan hadimi ya cika wannan umarni. Saƙon sarauniya Arya ya isa ko'ina da ina.
Jama'a suka fara hallara izuwa fadar ƙasar. Kan kace kobo ta cika maƙil.
Sarauniya Arya tana zaune akan wata kujera gefen karagar sarki Samudul Ansari, Kusuf yana zaune a ɗaya gefen.
Dukkansu sun yi ado na gani na faɗa, amma jikinsu a sanyaye yake. Lamarin da yasa jama'ar ƙasar cika da mamaki kenan.
Tsahon sa'a biyu, suna zazzaune a cikin fadar, basu cewa komai ba sannan babu wanda ya tambaye su.
Har 'yan majalisar ƙasar sun fara shawarar tambayar sarauniya Arya abinda ke faruwa, kawai sai suka ga sarki Samudul Ansari ya sauƙo cikin wannan fada tare da wani aljani mai fararen tufafi.
Sarki Samudul Ansari ya saki ikonsa ya doki dukkan jama'ar dake cikin fadar, daga kan waɗannan 'yan majalisa har zuwa kan kowa da kowa.
Duk wanda wannan iko ya taɓa sai kaga yayi mubaya'a.
Ba don komai Samudul Ansari ya saki wannan iko ba, sai domin nunawa jama'a ƙarfinsa shi kaɗai ya wuce su yi tunanin yin juyin-mulki koda bayanan.
Sarki Samudul Ansari ya zauna akan karagar mulkinsa, ya dubi dukkan jama'ar dake wannan waje ya ce.
"Mutanen birnin Shaha, daular Shaha. Ina farin cikin sanar da ku cewa, daga wannan rana ta yau: Goma ga watan sha-ɗaya. Mun kubuta daga sharrin Gorgon.
"Ko tunanin sake shigowa wannan daula ba za su yi ba, ballantana su yi tunanin sake kawo muku farmaki.
"Yau shekarata ɗari da bakwai ina mulki a wannan daula. Shin na taɓa muzgunawa ɗaya daga cikin ku..?"
Gaba ɗaya jama'ar dake wannan waje suka yi tsit! shuru babu mai magana.
Samudul Ansari ya ci gaba da jawabi.
"Zamani na ya kusa zuwa ƙarshe. Na cimma manyan burika na. Abu guda da ya rage min shi ne, wanzar da zaman lafiya a wannan daula har na abada.
"Indai nayi wannan abu ku da tashin hankali har duniya ta tashi... Babu barazanar Gorgon, babu barazanar komai.
"Amma dole sai kun bayar da haɗin kai yadda ya dace..."
Samudul Ansari na zuwa nan a zancensa ya miƙe tsaye, ya kamo hannun Kusuf ya tsayar a gaban kowa da kowa.
Samudul Ansari ya fidda hular sarautar dake kansa ya daurawa ita Kusuf.
"Daga yau ga sarkin ku... Ku bashi haɗin kai kamar yadda kuka bani... Kuyi masa biyayya kamar yadda kuka yi min..."
Mutanen dake cikin wannan fada gaba ɗaya, suka risina a gaban SARKI KUSUFU.
Samudul Ansari yayi murmushi ya ce, "Sabon sarki zai bayyana muku, dokokin da za ku kiyaye wajen ganin wannan daula ta sami nasara akan dukkan abokan gabarta..."
Samudul Ansari na zuwa nan a zancensa ya sallami kowa da kowa dake cikin wannan fada. Ya rage daga shi, sai matarsa Arya, Kusufa da kuma 'yan majalisu.
Samudul Ansari ya dubi 'yan-majalisun ya ce, "Fatan dai, wannan hukunci da na yanke yayi muku?"
Cikin haɗin baki suka ce, "Kwarai kuwa!"
Nan take su ma Samudul Ansari ya sallame su. Ya rage daga shi sai Arya da kuma Kusufu.
Samudul Ansari ya zauna kan karagar mulki ya dube su ya ce, "Na gama abinda ya kamata nayi a wannan ƙasa. Zan tafi izuwa kogon dutse [MADARUL ANSARI] inda zan ajiye kayayyaki na.
"Wannan gani shi ne na ƙarshe a tsakanina da ku. Idan na tafi ba zan sake dawowa ba. Ba za ku sake kallona. Na zamo tarihi..."
Sarauniya Arya da Kusufu suna jin wannan batu suka fashe da kuka mai tsuma zuciya, yasa tayi rauni.
"Kada ku damu. Ai indai an haɗu, dole ne sai an rabu... Haƙuri shi ne kawai magani..."
Samudul Ansari ya miƙe tsaye daga kan wannan karaga, sarauniya Arya da Kusufu suka zo suka rungume shi, suna ta kuka.
Kai komai

Please Login or Register in order to submit comment