Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da yasa sarkin mu fusata kenan, yasa aka kirawo mu ya shirya mana gasa.
"Gasar ita ce, mu saro kan wata ƙatuwar macijiya dake rayuwa a tekun birnin Sin mu kawo masa. Sarkin ya ce, duk wanda ya kawo kan wannan macijiya shi za'a aurawa Rosnil.
"Ni da tau'rin muka yi shiri muka je wannan teku. Bayan mun sha baƙar wahala, sai muka gane cewa, ba fa zamu iya kashe wannan macijiya da ɗaiɗaya ba dole ne mu haɗa kai, mu gama da ita.
"Idan ba haka ba kuwa, zata gama damu. Bisa dole muka ajiye ƙiyayya a gefe muka haɗa kai, muka kashe wannan macijiya.
"Bayan mun sare kanta na dubi tau'rin na ce, yanzu ya za'ayi, waye a cikinmu zai ɗauki kan wannan macijiya?
"Tau'rin ya zare takobinsa ya ce, mu yaƙi juna kawai, duk wanda yayi nasara a cikin mu saiya ɗauki kan macijiyar.
"Cikin gaggawa na amince da wannan shawara tasa domin ita ce daidai.
"Muka afkawa juna da yaƙi, amma sai da muka shafe kwanaki goma, ba tare da mun sami nasara ba.
"Tau'rin ya shammace ni, yayi min wani wawan duka wanda yasa nayi tsalle baya na fada cikin ruwan teku, na nutse a ƙarƙashinta.
"Daga wannan lokaci ban sake sanin abinda ke faruwa ba, ina dawowa birninmu bayan mako guda na samu labarin an ɗaura auren tau'rin da Rosnil kuma da dare zasu tare.
"Raina yayi mummunan ɓaci, saida na bari dare yayi na lallaɓa na shiga gidan da amarya Rosnil take.
"Na karkashe dukkan dakaru da bayin dake cikin gidan, sannan na afka mata.
"Ina tsakiyar more rayuwata da ita ne, aka sare kaina da wata takobi.
"A wannan waje na mutu amma saboda jinin jikina yana haɗe da babban jini, yasa ruhina bai gudu ba. Ruhin ya rikiɗe izuwa haske sannan ya ɓace daga wannan waje.
"Waɗannan abubuwa da suka faru na samun ƙarfin ikona suna da nasaba da jinin Rosnil da kuma takobin da aka sare ni da ita.
"Tun daga wannan lokaci, ruhina ya koma duniyar haske ya tare. Kullum zuƙar haske nake har saida ta kai ga cewa, ruhina ya zamo haske, sannan zai iya bayar da ita.
"Kuma na kai babban mataki a haske, wanda babu mahaluƙin da ya taɓa kaiwa a wancan lokaci, kai harma a gaba.
"Wannan shi ne yadda aka yi nake samar da haske, sannan shi ne tarihin tsananin gabar dake tsakanina da tau'rin."
Marganu ya dubi wannan ruhi dake zaune a gabansa cikin tsananin mamaki ya ce, "A da can kuma mutane ne kamar mu? Ya ya aka yi babu wannan tarihi kwata-kwata a duniya, abinda kowa ya sani shi ne, ISRABIL ƙarfin iko ne, shima tau'rin ƙarfin iko ne..."
Wannan ruhi dake zaune a gaban Marganu ya sake duban Marganu ya ce, "Kaso casa'in na abubuwan da suka faru a duniya, babu su a tarihi. Ba'a jima da fara rubuta tarihi ba, wannan shi ne dalilin da yasa babu tarihin rayuwata sa'adda nake mutum..."
Marganu ya dube shi ya ce, "Shin da wacce takobi aka sareka wadda take da nasaba da sake bayyanar ruhinka, sannan wane ne ya sareka? Ya ya akayi tau'rin ya samu ƙarfin ikonsa?"
Wannan saurayi ya sake duban Marganu ya ce, "Ni kaina ban san wane ne ba. Amma a hasashena sarkinmu ne, saboda yana da wata takobi wadda ban san bayanan komai akan ta ba. Ina kyautata zaton da takobin ya sare ni.
"Yadda aka yi tau'rin ya samu ƙarfinsa? Ban san komai akan haka ba, amma abin yana da nasaba da auren Rosnil."
Marganu yana jin wannan batu yayi shuru yana tunani. Daga can ya ɗago kai ya dubi wannan saurayi ya ce, "Na ji wannan tarihin, faɗa min abinda ke tafe da kai..?"
Wannan ruhi da ke zaune a gabansa yana jin haka yayi murmushi a karo na farko tun bayyanar sa.
"Sa'adda kuke gwabza yaƙi kai da Aymanul Faris na ɗauki dukkan bayanan Aymanul Faris da abubuwan da yake taƙama dasu.
"Kayi sani cewa, a yanzu faɗa tsakaninka da Aymanul Faris gaba-da-gaba yazo ƙarshe.
"Duk kuskuren da ya sake haɗa ku faɗa gaba-da-gaba, za ku iya mutuwar kasko.
"Kaga abinda ya faru sa'adda nake ƙoƙarin tarwatsa ruhinsa da hannuna a lokacin da kuke fafatawa a garin Jilliza.
"Na ɗauki bayanan Aymanul Faris sannan na gudanar da bincike na musamman akansu.
"Abubuwan da Aymanul Faris yake taƙama dasu su ne: tau'rin, Saif-Al-Barzaƙ, Saiful Shiradu da kuma takobin BINA-KIL-DEM..."
Marganu yana jin wannan batu yayi shuru yana jinjina su a ransa. Tau'rin. Saif-Al-Barzaƙ. Saiful Shiradu. BINA-KIL-DEM.
Marganu yana cikin wannan hali, wata nutsuwa ta rufe shi. Ya ɗago kansa a hankali ya kalli wannan saurayi.
A wannan lokaci Marganu yana cikin tsananin nutsuwarsa, babu kalma guda ɗaya da za'a faɗa masa a wannan lokaci bai haddace ta ba.
"Hanyoyin da zamu bi wajen tarwatsa Aymanul Faris koda bamu sake haɗuwa gaba-da-gaba ba, guda uku ne:" inji ISRABIL.
"Hanƴa ta farko kawar da Saiful Shiradu daga doron duniya!
"Ta ya ya zamuyi hakan?
"Asalin takobin Saiful Shiradu mallakin wani gawurtaccen sadaukin aljani ne, wanda ake kira Shiradu.
"Aljani Shiradu ɗan ƙabilar Nar ne. Shi ne aljanin da ya ƙirƙiri wannan takobi daga wuta.
"Sa'adda aljani Shiradu ya cika shekaru dubu ashirin da uku a duniya, ya saka wata ƙa'ida tsakanin ruhinsa da wannan takobi.
"Ƙa'idar ita ce, duk sa'adda ya mutu wannan takobi zata ladabtar da hadimansa guda goma masu irin halittarsa.
"Waɗannan hadimai guda goma su ne, ƙarfin wannan takobi, su kuma da ikon Shiradu suke amfani.
"Saiful Shiradu ba zata taɓa daina tasiri ba, face an ɗauko ruhin Shiradu an ajiye shi akan tsaunin Maudum.
"Ruhin Shiradu yana ajiye a cikin birnin Naru-wal-nara a gindin wani dutsen wuta.
"Birnin Naru-wal-nara yana kewaye da wata babbar katanga wadda aka ginata da zallan dutsen-wuta wanda a kowanne lokaci mugun zafi yake fitarwa.
"Idan ba aljanu 'yan ƙabilar Nar ba, babu halittar da ta isa ta shafe rabin sa'a a cikin birnin Naru-wal-nara, ba tare da sassan jikinta sun zagwanye sun zamo ruwa ba. Saboda tsananin zafin dake cikin wannan gari.
"Idan ka ɗauko wannan ruhi na Shiradu zaka kaishi saman tsaunin Maudum sannan ka ajiye shi akai.
"Tsaunin Maudum yafi kowanne abu a wannan duniya tamu sanyi. Idan aka ajiye ruhin aljanin akan tsaunin, zai sa ruhin ya daskare wutar dake ci a cikinsa ta mutu.
"Hakan zai sa takobin Saiful Shiradu ta daina aiki a duk inda take.
"Wannan shi ne bayanin aiki na farko da zaka aiwatar. Wato ɗauko ruhin Shiradu daga birnin Naru-wal-nara ka kaishi saman tsaunin Maudum ka ajiye."
Marganu yana jin wannan batu ya cika da tsananin mamaki. Kafun daga bisani zuciyarsa ta fara rawa akan anya wannan aiki zai yiwu kuwa?
"Tayaya zan je birnin Naru-wal-nara ba tare da na ƙone na zamo toka ba? Ta ya ya zan ɗauko ruhin sarkinsu, cikin nasara? Sannan ta ya ya zan hau saman tsaunin Maudum ba tare da nima na daskare ba?"
"SIRRIN ISRABIL!" inji ISRABIL. "shi ne amsar tambayoyinka. Zafi, sanyi, ruwa, iska, guguwa da komai, basa yiwa haske komai. Hakane?
"Zaka iya juyar da jikinka izuwa haske, ka shiga garin Naru-wal-nara ba tare da ka ƙone ka zamo toka ba. Amma zaka fafata mummunan yaƙi da dakarun dake tsaro a garin.
"Yadda zaka ɗauko ruhin Shiradu? Dabara da basirarka su ne zasu ƙwace ka, amma wajen akwai mugun tsaro. Saboda tunda sarkin ya mutu aka gina masa kabari a cikin gidan sarautarsa, daga wannan lokaci ake bashi tsaro yadda ya dace.
"Shi kuwa tsaunin Maudum, bincike ya tabbatar min ba'a wannan duniya yake ba. A cikin duniyar ƙanƙara yake. Shima idan ka juyar da jikinka izuwa haske babu abinda zaiyi ma..."
Marganu yana jin wannan batu yayi shuru yana tunani, daga can ya dubi ISRABIL ya ce, "Shin wanne tasiri takobin Saiful-Shiradu take da akaina da shan wahala sannan na ɓata lokaci sosai akanta?"
"Akul!" inji ISRABIL. "Duk makamin da ka gani a hannun Aymanul Faris gawurtaccen makami ne... Shin ka manta cewa da takobin Saiful-Shiradu aka hallaka sarauniya Yilan?
"A wancan lokaci bata ɗauki takobin Saiful-Shiradu a bakin komai ba, wannan yasa suka yaudareta da takobin. Samudul Ansari ya shammaceta ya soka mata takobin, tayi ajalinta.
"Saboda haka ba zamu yi ganganci irin wanda Yilan tayi ba.
"Duk wani makami dake hannun Aymanul Faris zamuyi ƙoƙari mu raba shi dashi."
Marganu yana jin wannan batu jikinsa yayi sanyi, ya tabbatar da abinda ISRABIL yake faɗa masa gaskiya ne.
Shi kansa ya cika da tsananin mamaki da ya karanta tarihin gumurzun sarauniya Yilan da Samudul Ansari, saboda ƙarfin sarauniya Yilan yafi na Samudul Ansari amma a ƙarshe shi ne yayi nasara.
Tabbas a yanzu ya samu amsar dalilin da yasa Samudul Ansari ya samu nasara akan sarauniya Yilan.
Ko shi kansa a gumurzun da suka gwabza da Aymanul Faris ya cika da tsananin mamaki da takobin dake hannun Aymanul Faris wadda bata kasance Saif-Al-Barzak ko Saiful Shiradu ba, amma ta samu nasarar yi masa mummunar illa.
Saboda wannan dalili ba zai yi wasa wajen tarwatsa komai na Aymanul Faris ba.
"Zan yi dukkan abinda ka ce, zan tarwatsa Aymanul Faris..." inji Marganu.
ISRABIL yana jin wannan batu yayi murmushin jin daɗi sannan ya ci gaba da baiwa Marganu bayanan.
"Zaka iya tarwatsa takobin Saif-Al-Barzaƙ kaɗai, idan ka ɗauki ruhin sadaukin da ya ƙirƙiro takobin ka kaishi saman tsaunin Maudum ka ajiye.
"Sadaukin da ya ƙirƙiro Saif-Al-Barzaƙ sunansa Hasnalu.
"Kabarin Hasnalu yana cikin birnin Sheshen.
"Tuni teku ya cinye garin Sheshen, yanzu haka a ƙarƙashin ruwa garin yake. Ba mu san masifu da bala'in dake ƙarƙashin wannan teku ba, amma mun tabbatar da cewa kabarin Hasnalu yana cikin wannan gari.
"Ya zamo dole kaje wannan gari, ka kamo ruhin Hasnalu shima ka kaishi saman tsaunin Maudum.
"Idan ka tarwatsa Saiful Shiradu da Saif-Al-Barzaƙ zan sanar da kai hanyar da zaka bi wajen tarwatsa tau'rin wanda shi ne babban abin dogaron Aymanul Faris...
"Kayi tunani..." inji ISRABIL.
Nan take jikinsa ya saje da kalar hasken wannan waje, sannan ya ɓace ɓat.
Sannu-a-hankali gaba ɗaya ya gama disashewa daga cikin wannan ɗaki.
Gimbiya Firziyya ta ɗago kanta a hankali ta kalli Marganu. Koda taga wannan iko ya kau, sai ta rugo kansa ta sake rungume shi.
"Akwai gagarumin aiki a gabana," inji Marganu. "Dole ne na kawar da Aymanul Faris daga duniya, indai ina so na ci gaba da rayuwa..."
Gimbiya Firziyya ta dubi Marganu ta ce, "Ta ya ya zaka kawar da Aymanul Faris alhalin wannan yaƙi da kuka gwabza kwanaki ƙarfinku yazo ɗaya? Kada ka manta kaɗan ya hana kuyi ragas."
Marganu ya dubeta cikin nutsuwa ya ce, "Wannan shi ne dalilin da yasa ruhina ya bayyana yanzu domin ya sanar dani, hanyar da zan bi na kawar da Aymanul Faris koda bamu sake haɗuwa gaba-da-gaba ba.
"Idan komai ya gama daidaita zan fara wannan tafiya mai mugun haɗari. Zan je garin Naru-wal-nara sannan naje birnin Sheshen na ɗauko waɗansu ruhi guda biyu..."
Gimbiya Firziyya ta dubi Marganu cikin tsananin mamaki. Kafun ta buɗi baki ta ce wani abu, Ileisha ta shigo cikin wannan turaka nasu riƙe da wata wasiƙa.
Marganu da Firziyya suka ƙura mata idanu, tun kafun ta ƙaraso inda suke.
"Wasiƙa ce aka kawo daga daular Nehiya, daga hannun sarki Kuffuru..." inji Ileisha Gorgon.
******
Yau *08/07/2023*
Babi na gaba zaizo *10/07/2023* da yaddar ALLAH...RUHIN JARUMTAKA!
*
Babi na 150: *Ƙarfin BES*
*
Wannan littafin sadaukarwa ne ga Zahra.
*
U~M~S
*
Marganu da Firziyya suna jin abinda Ileisha ta ce suka cika da tsananin mamaki. Marganu ya miƙe tsaye daga kan wannan gado ya sauƙo sannan ya karɓi wasiƙar daga hannun Ileisha.
Firziyya ta matso kusa dashi domin karanta abinda ke kan wannan wasiƙa.
*Wasiƙa daga sarkin sarakuna, sadauki uban sadaukai. Sarki Kuffuru ɗan Gauhan na daular Nehiya.
*Ya kai watsatstsen jarumi wanda ya ƙarar da rayuwarsa akan haukan soyayya, kayi sani cewa saƙonka ya riske mu kuma tuni zuciyoyinmu suka harzuƙa.
*Muna sanar da kai cewa, za mu zo ƙasarka ranar ashirin ga wata mai kamawa, domin fidda ji-ji da kai da kuma girman kai dake damunka.
*Haka kuma, wannan zuwa da zamuyi zan shigo har cikin ƙasarka na kama tsinanniyar 'yata na yanke mata hukunci bisa abinda ta aikata min.
*Ba wai iya ni ba, harda sarki Ayubu mahaifin Jaanu zaizo wannan yaƙi domin yi maka hukunci bisa abinda ka yiwa 'yarsa.
*Kayi shirin gwabza yaƙi, ranar ashirin ga watan Yuni.
*MARGANU MAI KARAMBANI DA CIKA BAKI, mu haɗu acan.
Koda Marganu yazo wannan waje a karatun wannan wasiƙa saiya yayyaga ta cikin tsananin fusata.
Ya dubi Ileisha ya ce, "A kirawo BES da manyan sadaukai na wannan daula. Zamu fara shirin wannan yaƙi da wuri, domin yau talatin da ɗaya ga watan Mayu."
Ileisha ta risina a gabansa sannan ta juya ta fice daga cikin wannan ɗaki.
Gimbiya Firziyya ta ƙaraso gaban Marganu ta tsaya suka ƙurawa juna idanu. Daga bisani ta ce, "Wannan yaƙi dake tunkaro mu babban yaƙi ne, da manyan sarakuna guda biyu zamu gwabza.
"Sarki Kuffuru da sarki Ayubu dukkansu cikakkun shiryayyu ne, ya kamata mu nutsu sosai mu tsara yadda zamu ɓullo musu a wannan yaƙi. Idan ba haka ba kuwa, akwai gagarumar matsala..."
Marganu ya dafa kafaɗarta ya ce, "Kada ki samu karaya ko kaɗan a cikin ranki, babu abinda zai faru a wannan yaƙi. A yanzu ni babban mutum ne a duniya, matsayin da na taka sarki Ayubu bai taka shi ba.
"Ko kaɗan ba zanyi shakkarsu ba. Idan da ace ni ɗaya ne suka tunkara da yaƙi, da zasu iya nasara amma a yanzu daular Gorgon kanta suka tunkara da yaƙi.
"Addinin Bankai ba zai bari suyi nasara akan mu ba. Kada ki samu damuwa."
Marganu yana zuwa nan a zancensa wata nutsuwa tazowa Firziyya a ranta, ya kama hannunta suka fice daga cikin turakar.
Kai tsaye Marganu da Firziyya suka ƙarasa cikin wani babban ɗaki dake kusa da fadar ƙasar.
A cikin wannan ɗaki suka yi arba da Ileisha, Narima, Laila, BES da kuma waɗansu sadaukai guda goma zazzaune a gaban wata ƙatuwar karaga.
Marganu ya ƙarasa kan wannan karaga ta mulki ya zauna. Firziyya ta koma bayansa ta tsaya.
Marganu ya bi waɗanda ke zazzaune a cikin wannan fada da ɗaiɗaya ya ƙare musu kallo.
Ileisha ta fara magana, "Daular Nehiya ta aiko mana da wasiƙar-yaƙi wadda tayi kurari sosai a cikinta. Ko zamanin sarki Samudul Ansari wanda ya kashe mana mahaifiyarmu ba'a samu daular da ta taɓa aikowa Gorgon wasiƙar-yaƙi ba.
"Saboda wannan dalili zamu zage damtse a wannan yaƙi, mu ladabtar da Nehiya mu nuna musu basu kai ba..."
Marganu ya tari numfashinta ya ce, "Ina so a wannan yaƙi mu karya daular Nehiya... Duk wanda yazo wannan filin yaƙi da niyyar yaƙarmu, ina bayar da umarni a kashe shi. Ku barni da sarki Ayubu da sarki Kuffuru, ni kaɗai zan gama da su.
"A fita wannan yaƙi da sojoji dubu ɗari bakwai, sarakuna talatin da kuma BES. A je a fara shirye-shiryen gwabza yaƙi..."
Marganu yana gama wannan batu ya miƙe tsaye ya kama hannun Firziyya suka tunkari ƙofar fita daga cikin wannan ɗaki.
Har sun iso ƙofar fita daga cikin wannan ɗaki, Marganu ya tsaya ya juyo ya dubi Ileisha da BES ya ce, ku sameni a filin horo.
Yana gama faɗin haka ya fice daga cikin ɗakin.
Gimbiya Firziyya ta dubi Marganu ta ce, "A ina za'a gwabza wannan yaƙi?"
Marganu ya dubeta ya ce, "Filin yaƙin Shizis dake garin Nayet, a wajen sarki Kuffuru da rundunarsa zasu dira."
Yana gama faɗin haka ya ci gaba da tafiya, gimbiya Firziyya ta dube shi kamar tana so tace wani abu amma sai ta fasa, har suka ƙarasa wannan filin horo.
Tafkeken fili ne wanda aka gina a cikin wani ƙaramin yanki dake cikin gidan sarautar Marganu.
An sassaƙa gumaka daban-daban a cikin filin domin gwada makaman yaƙi.
Marganu ya ƙarasa tsakiyar wannan fili ya tsaya a gaban ƙaton gunki. Gimbiya Firziyya tazo gefensa ta tsaya.
"Ina takubbanki?" Marganu ya tambayeta.
Gimbiya Firziyya tayi murmushi ta ce, "Suna nan..."
"Je ki ɗauko su," inji Marganu.
Firziyya ta matso gabansa cikin sauri ta ce, "Ka amince min, zan fita wannan yaƙi?"
Marganu ya gyaɗa mata kai a hankali, "Wannan yaƙi zai iya kasancewa yaƙi na ƙarshe a rayuwata. Im ma dai nayi nasara ko kuma a yi nasara akaina. Dama na miki alƙawarin za ki sake fita yaƙi sau ɗaya, ina so wannan yaƙi ya zamo cikon alƙawarina.
"Dole muna buƙatar kawar da sarki Kuffuru domin mayar da hankali sosai akan Aymanul Faris..."
Gimbiya Firziyya tana jin wannan batu ƙirjinta ya buga da ƙarfi, ta rungume Marganu ta ce, "Babu abinda zai faru da kai a wannan yaƙi. Mu ne zamuyi nasara."
Marganu ya yi guntun murmushi ya ce, "Shi yaƙi kamar tafiya haka yake. Kafun ka fita ne kake da shi, amma da zarar ka fita shi ne yake da kai...
"Komai zai iya faruwa a wannan yaƙi. Sarki Kuffuru da sarki Ayubu gawurtattun mayaƙa ne, sannan bamu san ƙarfin dakarun da zasu zo dasu ba.
"Wannan yasa nake so na kirawo BES wannan filin horo domin naga ƙarfin da kowannensu yake da. Kin san cewa, BES suna riƙe da Bankai mai mataki sama da na casa'in, wannan zai basu damar amfani da ƙarfin iko na musamman."
Gimbiya Firziyya ta gyaɗa kai cikin fahimta ta ce, "Tabbas wannan dabara ce mai kyau. Muna buƙatar sanin ƙarfin dakarun mu, kafun fita wannan yaƙi. Na yi maka rantsuwa da ruhin mahaifiyata, ba zan baka kunya a wannan yaƙi ba. Tabbas zaka yi alfahari dani a filin yaƙin."
Marganu yayi murmushi ya janye jikinsa daga nata ya ce, "Ina fatan hakan,"
Gimbiya Firziyya tayi sallama dashi ta bar wannan filin horo ta nufi cikin gidan sarautar.
Tana tafiya BES da su Ileisha suka ƙaraso wannan filin horo rataye da maɗaukakan takubban su.
Dukkansu suka zo gaban Marganu suka risina.
"Ina so kowa ya nuna min ƙololuwar ƙarfinsa da abinda yake sarrafawa," inji Marganu.
Ileisha, Narima, Laila da BES dukkansu suka zaro Bankai ɗinsu, sannan suka tunkari wadannan gumaka da aka sassaƙa a tsakiyar wannan fili.
"Da ɗaiɗaiya nake so, kowa ya nuna min ƙarfinsa," inji Marganu. "Daga BES sai Laila, Narima sai kuma Ileisha."
Suna jin wannan umarni suka tsaitsaya a inda suke.
Ɗaya daga cikin BES ta juyo ta dubi Marganu ta ce, "Suna na Yelila Gorgon. Abinda nafi ƙwarewa akansa a matakin Bankai shi ne sarrafa ƙanƙara. Ina da nasaba da hadiman dake zuwa duniyar ƙanƙara wajen sarki Aiys'man."
Wannan budurwa mai suna Yelila tana gama bayanin kanta, ta ɗaga takobinta sama ta kaiwa gunkin dake tsaye a gabanta sara.
Wani farin haske ƙatoto ya bayyana akan ƙirjin gunkin, cikin daƙiƙu biyu kacal! Marganu yaga wannan gunki ya daskare ya zama ƙanƙara.
Abin bai tsaya iya kan wannan gunki ba, take wani sanyi mai ratsa ƙashi ya fara kaɗawa a wannan waje.
Marganu ya dubeta cikin jinjina ya ce, "Wannan ƙarfi naki yayi yadda ya dace, ta gaba..."
Yelila Gorgon ta koma baya ta tsaya. Wata tsaleliyar budurwa ta matso gaba.
"Suna na Shedima Gorgon. Abinda nafi ƙwarewa akansa shi ne sarrafa ƙarfin damtse wato sinadarin Reniu. Akwai kaso tamanin da biyar na ƙarfin damtse a cikin Bankai ɗina, kaifin dake cikinta kaso goma sha biyar ne kawai."
Wannan budurwa mai suna Shedima tana gama bayanin kanta, ta ɗaga Bankai ɗin dake hannunta ta kaiwa gunkin dake tsaye a gabanta sara.
Wani ƙatoton dunƙulen hannu ya fice daga tsinin takobinta ya doki ƙirjin gunkin.
Gagarumar ƙara ta sauƙa a wannan waje, gunkin ya tartwatse yayi filla-filla.
Marganu ya gyaɗa kai cikin jinjina, "Ta gaba..."
Wata budurwa ta sake matsowa kusa, "Suna na Ishana Gorgon. Abinda nafi ƙwarewa akansa shi ne, sarrafa dalma. Addinin Bankai ya hore min dalma fiye da kowa a wannan daula..."
Tana gama faɗin haka ta kaiwa gunkin dake tsaye a gabanta sara, ruwan dalma yayi feshi daga cikin takobinta yazo saman wannan gunki ya tsaya kamar hadari.
A hankali ya ɗinga zubowa kan gunkin yana narkar dashi, har saida komai na jikin gunkin ya zagwanye izuwa wannan dalma.
Marganu ya dubeta cikin al'ajabi ya ce, "Tabbas kina da ƙarfi na musamman. Amma abinda nake son sani, iyakar girman ruwan da za ki iya sauƙewa kenan?"
Ishana ta ce, "A'a. Ina samar da hadarin mai girman gaske wanda zai iya yiwa mutane dubu rumfa, sannan nasa yayi ruwan wannan dalma ya narkar dasu gaba ɗaya..."
Marganu ya gyaɗa kai ya ce, "Ƙarfinki yayi yadda ya dace, ta gaba?"
Ishana ta koma gefensu Shedima ta tsaya. Wata budurwa ta matso gaba.
"Suna na Kubwana Gorgon. Abinda nafi ƙwarewa akansa shi ne, samar da walƙiya. Ni ce wadda ta gaji Aiyni Gorgon wadda sarki Samudul Ansari ya kashe."
Budurwa Kubwana tana gama faɗin haka ta kaiwa gunkin dake tsaye a gabanta sara. Walƙiya tayi feshi daga takobinta ta tarwatsa wannan gunki izuwa filla-filla.
Marganu yayi murmushi ya ce, "Fatan kema kina iya samar da babbar da'ira ta wannan walƙiya?"
Kubwana ta gyaɗa kai, "Kwarai kuwa."
Marganu ya gyaɗa kai ya ce, "Ta gaba?"
Nan take wata tsaleliyar budurwa ta matso kusa.
"Suna na Zainila Gorgon. Babban abinda nafi ƙwarewa akansa shi ne dafi. Ina iya gurɓata ruwan teku komai girmanta. Dafin dake cikin jikina mai ƙarfin gaske ne, a cikin sa'a guda rak yake gama tasiri a jikin mutum, ya kashe shi."
Zainila tana faɗin haka ta kaiwa gunkin tsaye a gabanta sara. Wani siririn layi ya bayyana akan iska, yaje ya caki ƙirjin gunkin.
Nan take jikin gunkin ya soma komawa kore-kore, alaman dafin yana shiga jikinsa.
Marganu ya tafa hannayensa sau huɗu alamar dukkansu ya yi musu jinjina.
Bayan yayi gajeren tunani ya ƙarasa gaban Zainila ya tsaya, ya dubeta yadda har suna jin numfashin juna ya ce, "Ba zamu je dake wannan yaƙi ba..."
Zainila ta dube shi cikin tsananin mamaki ta ce, "Ya shugabana! Saboda wanne dalili?"
Marganu ya ce, "Ina so ki haɗa min cuta mai ɗauke da babban mataki na dafi wanda zai iya shafe

Please Login or Register in order to submit comment