Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

dubawa yayi arba da takobinsa ta taurari wadda yake yaƙe-yaƙe da ita.
Takobin ta sauya matuƙa ba kamar yadda ya santa ba.
Wani irin sanyi mai ban al'ajabi yana fitowa daga cikin ƙarfenta wanda yake sa wa ɗan kewayen da take gajeren hunturu.
Zane-zanen taurari da suke kan ƙarfenta sun ƙara futowa fili ƙarara, har wani sheƙi suke tamkar sake zana su aka yi.
Gauhan ya buɗe idanuwansa a hankali, ya sake ƙarewa takobin kallo.
Abin mamaki idanuwan Gauhan sun sauya matuƙa. Baƙin cikin ya ɗan koma kore-kore, sannan farin kuma yana bayar da tsoro.
Gauhan ya miƙe tsaye ya ɗaga takobinsa sama, ya wulwula ta sannan ya mayar da ita cikin kufenta.
Sarauniya Yilan tana buɗe idanunta taga takobinta ta Bankais (Bankai 100) da kuma wata nannaɗaɗɗiyar wasiƙa.
Idanuwanta suna arba da wannan wasiƙa, gabanta ya faɗi, tsoro na karon farko ya baibayeta, jikinta ya fara ɓari...
Macijiya Ziyazilu ta ɗago idanuwanta ta kalli cikin sarauniya Yilan.
Idanuwan nasu guda hudu masu kama da juna, suka kalli cikin juna.
Nan take sarauniya Yilan ta fara ganin lokacin da mahaifinta da sarki Samudul Ansari suke gwabza yaƙi.
Ta ci gaba da ganin gumurzun har zuwa sa'adda mahaifinta Jiz'Ban ya ƙaddamar wannan gagarumin hari nasa wanda yayi sanadiyar mutuwar matar Samudul Ansari, Zarifa.
Sarki Samudul Ansari ta gani ya fusata, ya sare kan sarki Jiz'Ban.
Idanuwan sarauniya Yilan suna ganin kan mahaifinta a ƙasa, ta sulale ƙasa sumammiya.
Sai bayan gajeren lokaci sannan ta farfaɗo.
Wasu baƙaƙen hawaye masu yawan gaske suka fara zubowa daga idanunta. Wutar ƙiyayya da ta baƙin nufi ta fara ruruwa a cikin ranta.
Bankai 100 dake ɗaure a gadon bayanta ta fara ɗaukar launin baƙi mai duhu kamar na cikin idanunta.
"KIYI MINI IZINI NA TAFI FARAUTAR WANNAN TSINANNE DA KAINA, YA KE MAI GIRMA..." kalmomin da suka fita daga bakin Yilan ba tare da sanin ta furta su ba.
Ziyazilu ta sake duban sarauniya Yilan da waɗannan idanuwa nata. Idanuwan nasu masu kama da juna, suka sake haɗuwa a waje guda.
Yilan tayi arba da wani ƙaramin filin yaƙi a cikin wani wuri mai kama da duniyar ƙanƙara. Wasu halittu guda goma suna ta yawo a cikin wannan wuri, suna ihu da kururuwa tamkar zasu ci babu.
"Ku je wannan filin yaƙi wanda ke cikin duniyar ƙanƙara ƙusurwar gabas, ku gwada shirin da muka yi muku, akan wadannan halittun...
"Daga nan sai ku dawo nan, mu yi sallama ku tafi birnin Shaha, ku saro mana kan Samudul Ansari..."
Waɗannan kalmomin sarauniya Yilan taji a cikin ranta tamkar zuciyarta ce ta raya mata amma umarni ne daga Ziyazilu.
Sarauniya Yilan tana iya ganin abubuwa wadanda suke ko'ina a cikin duniya, idan idanuwanta da na Ziyazilu suka haɗu.
Ziyazilu tana iya baiwa Yilan umarni, ba tare da waɗanda suke tare da ita sun san anyi zancen ba.
Sarauniya Yilan ta share waɗannan baƙaƙen hawaye dake zubowa daga cikin idanunta, sannan tayi girgiza ta juye izuwa ƙatuwar macijiya.
Macijiyar ta wangame ƙaton bakinta ta haɗiye Gauhan sannan ta haɗiye BES wadanda ke can nesa.
Macijiyar ta faɗa cikin wata ƙatuwar rijiya dake gefen inda Ziyazilu take.
Jikin macijiyar yana nutsewa a cikin ruwan wannan rijiya ta saje da kalar ruwan rijiyan ta ɓace ɓat.
A cikin wata sabuwar duniya ta bayyana wadda komai nata na ƙanƙara ne. Tsaunika, bishiyoyi, koguna, dazuzzuka, garuruwa, tsirrai da komai na cikin wannan daji na ƙanƙara ne.
Wani irin sanyi mai ratsa ƙashi na kaɗawa a cikin wannan duniya, wanda yake daskarar da duk wani baƙon abu da ya shigo cikinsa.
Wannan sanyi bai yiwa wannan ƙatuwar macijiya komai ba, ta fara tsala azababben gudu ta tunkari wani ƙaramin fili dake ƙarshen wani gari.
Bayan doguwar tafiya wannan macijiya ta iso wannan ƙaramin filin yaƙi.
Macijiyar ta amayar da halittu guda biyar dake cikin cikinta, sannan tayi girgiza ta juye izuwa sarauniya Yilan.
Halittun suna dira kan ƙasa, suka juye zuwa Gauhan da kuma BES guda huɗu.
Dukkansu suka yi arba da halittun dake yawo a cikin wannan filin yaƙi.
Halittun ba za su wuce guda goma ba. Gaba ɗaya jikinsu da farin ƙanƙara aka yi shi ko kuma mutum zai iya cewa farin ƙanƙara ne ya lulluɓe jikin nasu.
Siffar jikinsu tana kama da ta dodo, suna riƙe da manya-manyan sunguma na ƙanƙara wadanda suke yaƙi dasu.
Sarauniya Yilan ta zaro takobinta ta Bankai mai mataki na casa'in da tara.
Ta dubi Gauhan da kuma BES guda huɗu ta ce, "Ziyazilu ta bayar da umarnin mu zo wannan waje, mu jarraba ƙarfinmu akan waɗannan halittun, saboda haka kowa daga cikinku ya ɗauki kason sa..."
Sarauniya Yilan tana gama faɗin haka tayi tsalle ta dira a cikin wannan fili, a gaban irin waɗannan halittu guda huɗu.
Gauhan ma yayi koyi da ita ya dira a gaban guda biyu. BES kuma suka ɗauki guda ɗaiɗaiya.
Waɗannan halittu masu kama da dodanni suna ganin baƙin sun dira a inda suke, suka zaro wadannan manya-manyan sunguma nasu sannan suka afka musu da azababben yaƙi.
Ɗaya daga cikinsu ya kaiwa sarauniya Yilan duka da sungumin hannunsa.
Sarauniya Yilan ta ɗaga Bankai ɗin dake hannunta ta tare wannan sungumi. Bankai ɗin tana haɗuwa da jikin sungumin ta tarwatsa shi.
Ɓangarorin ƙanƙara masu yawan gaske suka yi fallatsi daga cikinsa.
Sarauniya Yilan tayi juyi cikin zafin nama ta sari wannan dodo a kafaɗa.
Takobinta tana taɓa kafaɗar dodon, koren-hazo ya lulluɓe shi.
Ai kamar an niƙa jikinsa haka yayi bindiga ya tarwatse.
Sauran na ganin haka, suka yanyamo kan sarauniya Yilan.
Cikin zafin nama ta aikata musu abinda ta yiwa na farkon.
A ɓangaren Gauhan cikin daƙiƙa goma kacal! ya gama da wadannan dodanni.
BES ma haka take.
Ƙarfin su sarauniya Yilan na yanzu ya ninka na baya sau goma.
Idan a da zasu ɓata sa'a guda suna yaƙi da abu, a yanzu ba zai wuce daƙiƙa guda ba.
Wannan shi ne sabon ƙarfin da su sarauniya Yilan a cikin wannan tukunyar sinadarai ta Ziyazilu.
Sarauniya Yilan ta kirawo Gauhan da kuma sauran BES suka dawo gabanta suka tsaitsaya.
"Tsinanne [Samudul Ansari] ya samu nasarar kashe min mahaifina, daga wannan rana ta yau na ƙulla ɗamarar yaƙi da Samudul Ansari.
"Za mu bar wannan daula tamu, zamu tafi har inda yake, nayi rantsuwa da Ziyazilu cewa, ba zan dawo gida ba, ba tare da na sare kan sa ba."
Sarauniya Yilan tana gama ɗaukar wannan alwashin ta kwarara uban ihu, ta ɗaga takubbanta maɗaukaka sama, ta kwarara uban ihu.
Gauhan da BES suka yi koyi da ita.
Nan take dukkansu suka yi girgiza suka ɓace ɓat! daga wannan waje.
***
~Daular Shaha.
***
Sarki Samudul Ansari ne zaune tare da 'ya'yansa tagwaye guda biyu suna tattaunawa. Tagwayen sun girma don sun haura shekaru goma sha-takwas.
Tun suna shekaru bakwai-bakwai sarki Samudul Ansari ya fara ganin abubuwan al'ajabi tattare da su.
Bayan sirrin sabuwar ƙabila dake jikinsu, kowannensu yana da baiwa ta musamman.
Jalwar yana da baiwar ƙarfin damtse.
Waɗannan tagwaye guda biyu ana kiransu da suna - Kusuf da Husuf.
Kusuf yana da baiwar sarrafa takobi da iya yaƙi na gaban misali. A ganin sarauniya Arya sarki Samudul Ansari ne kaɗai zai fishi baiwar iya yaƙi.
Shi kuma Husuf yana da tsananin ilimi da hangen nesa.
Ana ganin cewa, Husuf ne kaɗai ya ɗauko mahaifiyarsu saboda itama tana da hikima da basira.
"Akwai gagarumin shirin da abokan gaba suka yi mana, na tsahon shekaru ɗari. Tun kafun a haifi Jalwar suka fara wannan shiri, a yanzu ina tunanin sun kammala.
"Tun sa'adda na dawo daga daular Irashnur, na ci gaba da baiwa kaina horo saboda nasan shirin abokan gabata bana wasa bane.
"A yadda na ƙudurce a raina, wannan yaƙi da zamuyi na ƙarshe, ba zan fita da ko soja guda ba. Daga ni sai ku 'ya'yana.
"Shin ku na da sha'awar fita filin yaƙi da ma'abota Bankai wadanda mahaifiyarku ta ba ku labari kwanaki?"
Kusuf ya dubi Samudul Ansari ya ce, "Baba! Duk inda ɗan sarki yake, dole ne ya kasance mai ƙarfin zuciya da tsananin jarumtaka.
"A al'adar wannan gida namu babu raggo ko sakare. Duk wanda aka haifa a gidan nan gwarzo ne kuma jarumi.
"Ba mu san tsoro ba, ba'a haife mu a wannan gida domin mu ji tsoro ba.
"Mu kashe ko kuma a kashe mu, wannan ita ce aƙidar mu.
"Ko ya ka ce Husufa?"
Samudul Ansari yayi murmushin jin daɗin wannan batu na Kusuf.
Lallai 'ya'yansa sun samu tarbiyya irin wanda kowanne Yarima ya kamata ya samu.
"Idan kaga an fara kashe mutanen wannan daula, baba. Ka tabbata bama nan a raye. Wannan alƙawari ne, baba." inji Husufa.
Samudul Ansari yayi murmushi ya zaro takubban tau'rin irin wadanda ya baiwa waɗannan dakaru nasa (waɗanda zasu taimaka masa a yaƙi da ma'abota Bankai) ya baiwa Husuf da Kusuf.
Samudul Ansari da waɗannan 'ya'ya nasa suka ci gaba da tattaunawa har tsahon ɗan lokaci sannan suka yi sallama da juna.
Suna tafiya sarauniya Arya tazo wannan waje ta zauna a gefensa.
"Yaushe ne za ku tafi wannan yaƙi?" sarauniya Arya ta tambaye shi.
Samudul Ansari ya ɗago ya dubeta ya ce, "Bayan-gobe da sassafe!"
Sarauniya ta sake cewa, "Saboda wanne dalili ka yanke hukunci fita daga kai sai 'ya'yanka? Shin baka tunanin abokan gaba zasu fi samun nasara akanku idan suka ninka ku a yawa sau ɗari?"
Sarki Samudul Ansari yayi guntun murmushi ya ce, "Abokan gabar mu su shida kacal zasu zo. Sarauniya Yilan, Gauhan Ansari, da kuma manyan sarakunan dake ƙarƙashin ikonta guda huɗu,"
Cikin tsananin mamaki sarauniya Arya ta dube shi ta ce, "Ta ya ya ka gano cewa, su shida zasu zo? Sannan ta ya ya 'ya'yanmu zasu iya ja dasu, ka san cewa sun shekara ɗari suna shan tsumi..."
Samudul Ansari ya dubeta cikin nutsuwa ya ce, "Ashe har kin manta, irin ɓarnar da nayi musu a shekarun baya? Ai a halin da ake ciki a yanzu, idan ba waɗanda aka tsuma a cikin irin wannan tsumi ba, babu waɗanda zasu iya ja da wannan daula tamu.
"Kiyi sani cewa, sakamakon auren da muka yi ni da ke, mun samar da sabuwar ƙabila mai ƙarfin gaske.
"Dukkan 'ya'yanmu suna da baiwa kala daban-daban. Ina da tabbaci a raina, ba zasu bani kunya ba.
"Su ne suka fi dacewa da tarar abokan gaba, ba wai sauran dakarunmu ba."
Sarauniya Arya tana jin abinda Samudul Ansari ya ce hankalinta ya kwanta ainun, ta gamsu da bayanan nasa.
Haka dai suka ci gaba da tattaunawa har tsahon lokaci, sannan Samudul Ansari ya tashi ya tafi izuwa wani ƙaramin filin yaƙi.
Samudul Ansari ya baiwa wani hadimi umarnin kirawo masa 'ya'yansa domin basu horo.
****
Yau *13/04/2023*
Babi na gaba zaizo *15/04/2023* da izinin ALLAH.
RUHIN JARUMTAKA!
*
Babi na 111: *Baƙin Gumurzu*
*
***TARIHIN SAMUDUL ANSARI***
*
Wannan littafin sadaukarwa ne ga Zahra...
*
Barka da shan ruwa, kowa da kowa.
*
U-M-S
*
Tsahon wuni guda cir! Samudul Ansari ya shafe yana baiwa yaransa horo. Tun safe suke cikin wannan filin yaƙi amma saida rana ta faɗi sannan suka fara shawarar komawa cikin gida.
Akan hanyarsu ta tafiya cikin gidan ne, suka hango tahowar waɗansu korayen haske guda shida sun gilma ta cikin gajimare tamkar wucewar taurari masu wutsiya.
Samudul Ansari ya dubi 'ya'yansa ya ce, "Abokan gabar mu, sun ƙaraso. Kowa daga cikin ku yaje ya gama shiri kafun asuba..."
Yana gama faɗin haka suka ƙarasa cikin gidan sarautar. Kowa ya tafi dakinsa.
Washe gari da asuba suka sake haɗuwa a tsakiyar gidan sarautar. Dukkansu su huɗun sun yi gagarumar shiga ta yaƙi mai ban tsoro.
Waɗansu hadimai suka kawo musu ingarmun dawakai guda huɗu, suka haye kansu sannan suka tunkari hanyar da zata kaisu filin yaƙin Ajalin-Abokan-Gaba.
Tuni sun riga da sun yi sallama da sarauniya Arya, saboda haka tafiya kawai ta rage musu.
Jama'ar birnin gaba ɗaya suka taru akan hanya suna yi musu fatan alheri.
Samudul Ansari da 'ya'yansa uku suka ci gaba da tsala azababben gudu suka tasarwa Ajalin-Abokan-Gaba.
Tunda asuba suka fara wannan tafiya amma sai da gari ya gama wayewa, rana ta gama ƙwalewa sannan suka isa can.
A cikin wannan filin yaƙi ne, suka yi arba da macizai guda shida suna ta yawo a cikinsa. Macizan baƙaƙe ne siɗik waɗanda basu da daɗin kallo.
Cikin gaggawa Jalwar, Kusuf da Husuf suka zaro takubbansu zasu afkawa macizan amma sarki Samudul Ansari yayi gaggawar dakatar dasu.
"Ba asalin macizai bane," inji Samudul Ansari. "Sarauniya Yilan, Gauhan Ansari da kuma sarakunanta guda huɗu ne suka juye izuwa macizai."
Ai kuwa yana rufe bakinsa waɗannan macizai suka yi girgiza suka juye izuwa siffofin mutane guda shida.
Sarauniya Yilan, Gauhan da kuma BES.
Dukkansu su shidan suna sanye da korayen tufafi masu kaurin gaske. Kowannensu yana riƙe da takobi tsirara.
A hannun sarauniya Yilan bankai mai mataki na casa'in da tara ne.
A hannun BES kuma bankai mai mataki na casa'in-casa'in ne. Babu wanda a cikinsu su huɗun yake riƙe da mai mataki ƙasa da na casa'in.
A hannun Gauhan kuma, wannan takobi mai zane-zanen taurari ce wadda har a wannan lokaci ba'a ambaci sunanta ba.
Sarauniya Yilan tana tsaye a gaba, Gauhan da BES sun jeru a bayanta.
Idanuwan sarauniya Yilan suna ganin cikin na Samudul Ansari zuciyarta ta soma tafarfasa. Takobin dake hannunta ta fara sauya launi tana ƙoƙarin ƙwacewa ta kaiwa Samudul Ansari sara.
Gauhan ya ƙurawa Jalwar idanu cikin tsananin fusata.
Tsakanin su Kusuf Husufa aka fara hararar juna da BES.
Samudul Ansari ya katse shurun da cewa, "Shekaru ɗari kuna yi min shiri. A yau ga mu ga ku, babu gudu ba ja da baya..."
Sarauniya Yilan ta cije haƙora ta ce, "A yau zan kashe ka, jininka zai yiwa ƙasar dake wannan waje ado. Za mu kama waɗannan 'ya'ya naka a matsayin bayi.
"Zamu ruguje wannan daula gaba ɗayanta, mu ƙone komai da komai. Yadda koda tarihinku ba za'a sake tunowa ba,"
Samudul Ansari ya gyaɗa kai cikin mamaki ya ce, "Ko muna ina duk wannan zata kasance?"
Sarauniya Yilan tayi dariyar mugunta ta ɗaga wannan takobi nata sama, takobin ta fara sheƙi da walwali a cikin hasken rana.
"Lokaci shi zai baka amsa," inji sarauniya Yilan.
Tana gama faɗin haka ta dubi Gauhan da BES dake tsaitsaye a bayanta ta ce, "Bari na gama da waɗannan shashashun,"
Sarauniya Yilan ta ruga da gudu kan su Samudul Ansari tana kwarara uban ihu. Farin hayaƙi na ɓulɓulowa daga ƙarfen takobinta yana tafiya sararin samaniya yana haddasa sabon hadari.
Macizan dake kanta suna ihu da kururuwa suna wangame bakunansu tamkar zasu ci babu.
Samudul Ansari na ganin haka ya juyo ya dubi su Jalwar ya ce, "Kada wanda a cikinku yayi kuskuren shiga yaƙina da wannan shaiɗaniyar saboda tafi ƙarfinku. Ni ne kawai zan iya ja da ita!"
Yana faɗin hakan ya ruga da gudu kan sarauniya Yilan.
Saif-Al-Barzaƙ tana bayar da baƙin haske mai sheƙi. Ɗalasiman da aka rubuta a jikin ƙarfenta suka fara haske suna bayyana.
Samudul Ansari da sarauniya Yilan suna haɗuwa a tsakiya suka kacame da azababben yaƙi mai mugun hatsari.
Suka yi ta kaiwa juna mugayen sara da suka da waɗannan hatsabiban takubba dake hannunsu.
Zafin naman waɗannan jarumai guda biyu yafi ƙarfin a wassafa sai dai abinda idanuwa suka gani kawai.
Amma a cikin daƙiƙa guda suna iya kaiwa junansu sara kamar sau goma-goma.
Kafun a jima tuni wannan waje da suke ya soma turnuƙewa da hayaƙi.
Suka ci gaba da kaiwa juna muggan hare-hare amma lokaci mai tsaho, babu wanda a cikinsu ya samu nasarar koda ƙwarzanar ɗan uwansa.
Lamarin da ya soma fusata sarauniya Yilan kenan. Ta daɗa zage damtse wajen sauƙewa Samudul Ansari muggan hare-hare shi kuma yayi ta karewa.
Koda aka sake ɓata ɗan lokaci ana wannan gumurzu sai wannan farin hayaƙi da ya ɓulɓula daga takubbanta a ɗazu, ya soma taruwa a sararin samaniya yana samar da hadari mai siffar maciji.
Hadarin ya soma bajewa a sararin samaniya yana ƙara girma har ya lullube dukkan filin yaƙin.
Yana gama lulluɓe filin yaƙi ya fara zuƙar wannan hayaƙi dake fita daga takobin Yilan da kuma takobin Samudul Ansari izuwa cikinsa.
Yana gama zuƙar wannan hayaƙi, ya fara komawa kore kamar ganyen maina.
Samudul Ansari da sarauniya Yilan suka sake fuskantar juna, babu wani hijabi da ya tare ɗayansu.
Sarauniya Yilan ta kwarara uban ihu, ta nuna wannan hadari da takobin dake hannunta, sannan ta nuna Samudul Ansari da ita ta ce.
"Kai tsinanne! Yau ce ranar mutuwarka, ƙoƙarinka da mugun nacinka ba zai ƙwace ka ba...
"Addinin Bankai ya tsine ma, abar bautarmu ta tsine ma, tabbas mutuwarka tazo, kuma A HANNUNA TAKE!!!"
Samudul Ansari yana ƙoƙarin mayar mata da martani kenan, yaji tahowar abu da gudu ta bayansa.
Cikin zafin nama ya yi wani irin irin juyawa, amma duk da haka sai da abin ya karci kan damtsen hannunsa.
Samudul Ansari yana dubawa yaga ashe irin wannan jan mashi ne wanda aka yi amfani dashi aka kashe Zarifa da irinsa aka kawo masa hari.
Abinda ya bashi mamaki shi ne, ya ya aka yi kwata-kwata bai ji tahowar wannan mashi ba?
Bayan haka ga su Jalwar dake tsaitsaye a bayansa, meyasa ba su yi arba da wannan mashi ba?
Sarauniya Yilan tana ganin wannan mashi ya karci jikin Samudul Ansari tayi murmushin mugunta, idanuwanta suka ƙara kore mai baƙi-baƙi.
Ta sake nuna sararin samaniya da wannan takobi nata, sannan ta nuna Samudul Ansari da ita.
Faruwar hakan keda wuya wannan waje da suke tsaitsaye ya fara hazo-hazo yana ɓacewa.
Kafun Samudul Ansari yayi wani yunƙuri tuni wannan waje ya ɓace bat! Wani irin abin al'ajabi ya faru.
Wani sabon waje ne ya bayyana wanda komai da komai nasa kore ne. Sararin samaniya koriya, manya-manyan taurari koraye, kai hatta ƙasar da suke takawa koriya ce.
Gangar jikin sarauniya Yilan ya fara bayar da haske kore, idanuwanta suna sheƙi tamkar koren zinari.
A wannan lokaci maimakon takobi guda ɗaya (Bankai 99) dake hannunta, a yanzu guda biyu ne.
Dukkansu suna haske da sheƙi tamkar wanda ke cikin idanunta.
Kai daga ganin wannan waje ka san cewa, wani wuri ne wanda sarauniya Yilan ta samar domin amfani da ƙarfin ikonta kawai.
A wannan waje Samudul Ansari baya iya yin abubuwa da dama.
Baƙin hayaƙin dake ɓulɓula daga takobin Saif-Al-Barzaƙ a yanzu ya ɗauke. Hatimin tau'rin dake zane a bayan wuyansa a yanzu ya goge.
A taƙaice a wannan waje, babu tau'rin babu alamunsa.
Kai kace ƙarfin ikon wajen ne yayi jifa da tau'rin daga jikin Samudul Ansari.
"Tau'rin?" Samudul Ansari yayi masa magana amma shuru bai amsa.
Ya sake maimaitawa har sau uku amma shuru babu amsa, hakan ne ya tabbatar masa da cewa, tau'rin baya wannan waje.
Samudul Ansari ya gyara riƙe Saif-Al-Barzaƙ da hannu biyu.
Ya kamata a san cewa, ko akwai tau'rin ko babu shi, takobin Saif-Al-Barzaƙ zata yi aikinta yadda ya dace.
Tau'rin kawai kamar ya ƙara mata ƙarfi ne akan nata.
Rashin tau'rin a wannan waje, kwata-kwata bai wani ɗagawa Samudul Ansari hankali ba.
Saboda ya san cewa, dole wataran irin haka zata iya faruwa.
Ba kullum ake kwana a gado ba.
A wannan waje da suke babu komai fili ne kawai fetal iya hangenka.
Amma jim kaɗan bishiyoyi da tsaunika koraye jefi-jefi suka fara bayyana. Duk bayan daƙiƙa sai Samudul Ansari yaga waɗannan tsaunika da bishiyoyin sun ƙara girma.
Kafun a jima tuni sun yiwa wajen rumfa, an daina ganin wannan ƙaton fili.
Koren-hazo ya soma sauƙowa daga sararin samaniya wanda ya fara rage ƙarfin Saif-Al-Barzaƙ.
Sarauniya Yilan tayi dariya, tayi tsalle cikin murna sannan ta nuna Samudul Ansari da takubbanta guda biyu ta ce.
"A wannan waje zaka mutu, babu mai ƙwatar ka...
"Wannan waje sashi ne daga kaburburan magabantanmu. Babu abinda zaiyi tasiri a wannan waje, idan ba namu ba.
"Duk bayan daƙiƙa ƙarfinka raguwa yake. Kaga kenan cikin ruwan sanyi zan gama da kai..."
Sarauniya Yilan tana zuwa nan a zancenta ta sake ƙyalƙyalewa da dariya.
Samudul Ansari ya bi ta da kallo kawai, ba tare da ya ce da ita komai ba. Ya sake ƙanƙame takobin hannunsa da hannaye biyu.
Sarauniya Yilan ta daka wawan tsalle sama ta kawo masa wawan sara da takubbanta guda biyu.
Macizan dake kanta suka fara ihu suna zubar da koren-dafi.
Dai-dai inda takubban zasu dira yayi alamar kore-kore.
Samudul Ansari ya fara jin ƙaiƙayi a dai-dai wajen sannan ƙasusuwan wajen suka fara ɓari zasu ɓalle.
A wannan lokaci babu batun rufa-ido saboda an danne ikon Saif-Al-Barzaƙ wanda zai baiwa Samudul Ansari damar amfani dashi.
Kamar walƙiya haka takubban hannun sarauniya Yilan suka ratsa ta cikin hannun Samudul Ansari da kuma kafaɗarsa.
Bankai 99 ta sari kafaɗarsa, Bankai 100 ta sari hannunsa.
Kafaɗar Samudul Ansari ta zaftare wawakeken ciwo ya bayyana, hannunsa wanda takobin Bankai mataki na ɗari ta sara take yayi bindiga ya tarwatse.
Bayan jan jinin dake zuba daga raunikan Samudul Ansari, akwai wani kore-koren sinadarin dake lulluɓe ciwukan nasa a hankali.
Sarauniya Yilan tayi murmushi ta ɗaga takubbanta ta kwarara uban ihu.
Abinda ya ɗaure mata kai shi ne, mene ne dalilin da yasa Samudul Ansari bai tarwatse gaba ɗaya ba.
A saninta dai, saran takobin mai mataki na ɗari yana tarwatsa dukkan ruhin halitta ta zube ƙasa matacciya.
*****
Yau *15/04/2023*
Babi na gaba zaizo *17/04/2023* da yaddar ALLAH.RUHIN JARUMTAKA!
*
Babi na 112: *LESIM*
*
***TARIHIN SAMUDUL ANSARI***
*
Wannan littafin sadaukarwa ne ga Zahra...
*
*Sanarwa ta musamman:- Chapter 113-133 are available on WhatsApp, ga duk mai buƙata ya ɗau wannan numban +2348136093283. Akan farashi mai rahusa - N400 kacal. Ask before payment pls.*
*
U-M-S
*
A ɓangaren su Jalwar da su Gauhan kuwa, kallon-kallo kawai ake. Tsakaninsu Jalwar babu wanda zai ce yasan inda su Samudul Ansari suka tafi, sun dai ga lokaci ɗaya kawai sun yi girgiza sun ɓace.
Tsahon daƙiƙu suna ta muzurai sun gagara afkawa juna, saboda a cikinsu babu wanda shugabansu ya basu umarnin afkawa juna.
Rabin sa'a na shuɗewa Gauhan ya juya ya dubi BES

Please Login or Register in order to submit comment