Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da bani da a ƙasata ta Kufa face wannan ɗanyen-mai.
"Wannan yasa ɗanyen-mai yayi ƙaranci a cikin ƙasata sosai, sannan yayi tsada fiye da tunanin mutum.
"Saboda wannan dalili na rubuto maka wannan wasiƙa akan mu yi cinikin wannan ƙaramin gari na Julez..."
Sa'adda maga-takarda yazo nan a karatun wannan wasiƙa sai yayi shuru sannan ya ɗago kansa ya dubi Samudul Ansari.
Samudul Ansari ya gyaɗa masa kai, alaman ya ci gaba.
"...ka sakawa garin kuɗi, ni kuma zan saya.
"Kai sarki ne, kayi tunanin irin halin da jama'a zasu shiga idan suka rasa ɗanyen-mai a ƙasarsu.
"Saboda haka nake so, ka sayar min da wannan gari ya zamo ƙarƙashin ikona..."
Samudul Ansari na gama jin abinda wannan wasiƙa ta ƙunsa, yayi shuru yana tunani.
Gaba ɗaya cikin wannan wasiƙa babu magana ɗaya ta hankali. Dukkan abinda ke cikin wannan wasiƙa rainin-hankali ne kawai da kuma raini.
Tun da ake a duniya an taɓa sayar da gari, idan ba rainin hankalin sarki Farhama ba?
Samudul Ansari yayi shuru yana tunanin amsar da ya kamata ya baiwa wannan sarki.
A matsayin sa na sarki yasan dukkan tuggun sarakuna. Mafi yawancin lokuta idan kaga irin wannan wasiƙa tana nuni da neman tsokala ne domin janyo yaƙi.
Me sarki Farhama yake taƙama dashi da zaiyi tunanin kawowa daular Shaha wargi?
Daular da hatta Gorgon ma, basu share ba da suka shigo ta?
Samudul Ansari ya bayar da umarni aka kawo masa jemammiyar fata da alƙalami, ya rubutawa sarki Farhama amsa sannan ya baiwa waɗannan manzanni guda uku ya ce su kaiwa sarkinsu.
Babu wanda yasan abinda Samudul Ansari ya rubuta a cikin wannan wasiƙa domin bai bari wani ya gani ba.
Manzannin suna fita ya dubi sarauniya Arya ya ce, "Daga gobe, za ki ci gaba da riƙe daular nan, zamuje wani waje ni da ɗana Jalwar..."
Yana gama faɗin haka, ya miƙe tsaye ya fice daga cikin wannan fada.
Ya bar sarauniya Arya, Jalwar da dukkan jama'ar dake zazzaune a wannan fada cikin duhu.
****
A can wani ɓangare na duniya kuwa, a cikin wani tafkeken teku wanda manya-manyan duwatsun ƙanƙara suka cika da ta ko'ina.
Wani hamshaƙin basarake ne zaune bisa wata kujera, ya saka jar alkyabba.
Waɗansu irin halittu guda biyu na tsaye a gefensa, ga dukkan alamu tattaunawa suke.
Waɗannan halittu guda biyu suna da ban al'ajabi.
Daga kunkuminsu yayi sama - gangar jikin mutum ne. Daga ƙugunsu yayi ƙasa - siffar ingarman doki ne wanda ke harbin iska.
Dukkan waɗannan halittu da wannan basarake idanuwansu na tsaye cak! akan wani faifan ƙanƙara wanda ke nuna musu abinda ke faruwa a birnin Shaha.
Koda suka ga sarki Samudul Ansari ya baiwa waɗannan manzanni wasiƙa sai suka cika da tsananin mamaki.
A zatonsu da imaninsu idan suka kaiwa babban sarki kamar Samudul Ansari irin wannan wasiƙa mara-kan-gado zai fusata ya sare waɗannan manzanni sannan ya ɗebo gagarumar runduna ya fito farautar su.
Wannan sarki shi ne sarki Farhama wanda wasiƙarsa ta isa wajen sarki Samudul Ansari a wannan rana.
Farhama ya taɓa yin arba da baƙin hayaƙin tau'rin a cikin wani mafarki da yayi.
Ƙarfin iko da ƙamshin sarautar da yaji a cikin wannan baƙin hayaƙi yasa dole yayi mubaya'a.
Farhama na farkawa ya garzaya wajen babban bokansa yayi masa bayani.
Bokan Farhama ya tabbatar masa da cewa, bayan sarki Samudul Ansari akwai yiwuwar shima wannan ruhi ya sake zaɓansa saboda babu wanda ya taɓa irin wannan mafarki duk duniya, idan ba Samudul Ansari ba.
Babban matsalar da ya fuskanta ita ce, ba zai taɓa mallakar wannan ruhi ba, matuƙar aka ce Samudul Ansari yana raye.
Saboda wannan dalili bokansa ya tabbatar masa da cewa, yana da kyau ya naɗe hannayensa ya jira zuwa sa'adda Samudul Ansari zai mutu.
Farhama yana matuƙar son mulki saboda haka ba zai iya haƙurin jira ba, wannan yasa ya fara bincike akan yadda zai ɓullowa Samudul Ansari ya gama dashi ya ƙwace wannan ruhi.
Duk ta inda ya ɓullo sai yaga lamarin ba zai yiwu ba, saboda Samudul Ansari ya riga yayi ƙarfi.
Har Farhama ya fara tunanin haɗa kai da ma'abota Bankai domin ganin bayan Samudul Ansari, amma a kwanakin da suka wuce yaga abinda ya faru dasu.
Ma'abota Bankai ba zasu iya ja da Samudul Ansari ba, saboda ƙarfinsu yayi kaɗan.
Sarauniya Yilan ce kaɗai yake tunanin zata iya taɓukawa Samudul Ansari wani abu, albarkacin wannan takobi [Bankai 100] dake hannunta.
Sarauniya Yilan tana da ƙarfin mulki da ji-ji da kai ba zata taɓa amincewa ta haɗa kai dashi ba.
Wannan yasa sarki Farhama tunanin mafita, domin ɓullowa wannan al'amari.
Shi kam tun sa'adda yaji ƙarfin ikon tau'rin yayi rantsuwa akan sai ya mallaki ruhin.
Watarana ya samu labarin irin waɗannan halittu masu jiki kala biyu a bakin wani bafatake da ya faɗo cikin irin wannan teku nasu, ya tsira da ƙyar.
Farhama yayi doguwar tafiya izuwa birnin Sin wajen masanin Kimiyya - Sin-Baihar.
Sin-Baihar ya yiwa Farhama cikakken bayani akan waɗannan halittu.
Wannan yasa Farhama yin kasada ya shigo wannan teku nasu wanda ke ɗauke da ƙanƙara kala daban-daban domin su haɗa kai.
Waɗannan halittu bayin wani gagarumin sarki ne wanda baya rayuwa a wannan duniya gaba ɗaya.
Babban dalilin shigowarsu wannan duniya shi ne, TARWATSA RUHIN TAU'RIN domin sarkinsu yaji daɗin mulki a wannan duniya.
Koda suka ji Farhama yana daga cikin waɗanda suka taɓa arba da wannan ruhi, sai suka yi gaggawa suka amince zasu taimaka masa.
Amma basu bayyana masa babban dalilin da yasa suka shigo wannan duniya ba, kada ya gane manufarsu ya ƙi amincewa su haɗa kai.
Koda suka ga sarki Samudul Ansari ya tashi ya fice daga cikin fadarsa ba tare da bayar da wani umarni na yaƙi ba, sai suka sake cika da tsananin mamaki.
Waɗannan sarakuna guda biyu suka baiwa Farhama umarnin zuwa wajen waɗannan manzanni ya karɓo wasikar da Samudul Ansari ya basu.
Farhama ya kaɗa wannan jar alkyabba tasa, take ta juye izuwa manya-manyan fuka-fuki ya kaɗa su ya tashi sama ya lulluƙa a cikin gajimare ya ɓace ɓat!
**
Waɗannan manzanni guda uku suna tafe a cikin ƙungurmin daji, suna tattaunawa akan yadda aka yi suka tsira daga sharrin Samudul Ansari dukda cewa wasiƙar rainin hankali suka kai masa.
Ba zato suka ga saman wani ƙaramin dutse dake gabansu ya fara haske.
Cikin gaggawa suka zaro makaman yaƙinsu sannan suka tsaitsaya.
Sarki Farhama suka gani ya sauƙo saman wannan dutse, cikin gaggawa suka risina a gabansa.
Farhama ya tambaye su, ina wannan wasiƙa wadda sarki Samudul Ansari ya basu?
Babban cikinsu ya zaro wasiƙar daga cikin aljihunsa ya damƙawa ita Farhama.
Farhama ya karɓi wannan wasiƙa ya warwareta ya duba
"Mu haɗu a filin-yaƙin Ajalin Abokan Gaba a duk lokacin da ka gama shiryawa!" shi ne kawai abinda aka rubuta a jikin wannan wasiƙa.
Sarki Farhama na karantawa ya gane cewa, sarki Samudul Ansari ya gano shirinsa da ya daɗe yana yi.
Cikin gaggawa ya buɗe fuka-fukinsa ya tashi sama, ya koma cikin wannan teku inda waɗannan halittu suke.
Koda ya sanar dasu abinda ke cikin wannan wasiƙa, ba su yi wani mamaki sosai ba.
A wannan waje suka ajiye yarjejeniyar zasu kaiwa Samudul Ansari hari, bayan wata guda.
A cikin wata gudan zasu yi ƙoƙari su yi ta shirye-shirye saboda karo da ma'aboci Saif-Al-Barzaƙ sai cikakken shiryayye.
*****
Yau *06/04/2023*
Babi na gaba zaizo *08/04/2023*RUHIN JARUMTAKA!
*
Babi na 108: *Kentaurons*
*
***TARIHIN SAMUDUL ANSARI***
*
Wannan littafin sadaukarwa ne ga Zahra...
*
BARKA DA SHAN RUWA, KOWA DA KOWA.
*
UMS
*
A birnin Shaha har gari ya waye sarki Samudul Ansari bai sake cewa komai ba.
Sarauniya Arya da Jalwar tunanin abin ne ya hana su kwanciya su rintsa har gari ya gama wayewa.
Washe gari tunda safe, sarki Samudul Ansari ya shiga cikin yankin da ɗakunan sarauniya Arya da Jalwar suke.
Bisa mamaki sai ya iske su zazzaune sun yi jugum-jugum, sun gagara rintsawa. Lamarin da ya yi matuƙar bashi mamaki kenan.
Samudul Ansari ya haɗe fuska ya dube su ya ce, "Shin ko zan iya sanin dalilin da ya hana ku kwanciya, ku yi barci? Don ga dukkan alamu jiya da dare ba kuyi barci ba."
Sarauniya Arya ta ɗago ta dube shi ta ce, "Tayaya zamu kwanta muyi barci alhalin baka ce damu komai ba? Wane ne wannan sarki Farhama wanda ya aiko ma da wasiƙa, sannan amsar me ka rubuta masa..?"
"Hmm," Samudul Ansari yayi murmushi. "Akwai idanuwa sosai a kaina, babu yadda za'a yi na bayyana abubuwan da zan gudanar daga yanzu."
Yana faɗin haka yazo gaban sarauniya Arya ya dafa kafaɗarta da hannunsa guda ya ce, "Kada ki sa damuwar komai a ranki, kamar yadda a yaƙi da ma'abota Bankai ban ba ki matsala ba, nayi miki alƙawari a wannan yaƙi ma babu abinda zai faru!"
Sarauniya Arya ta dafa hannunsa guda ta ce, "Yaƙi kuma? Da su waye kenan?"
"Kada ki damu," inji Samudul Ansari. "Za ki samu bayanan wajen da zamu je ni da ɗanmu a cikin wasiƙar da na bar miki akan gado..."
Yana gama faɗin haka ya kama hannun Jalwar suka fice daga cikin wannan ɗaki.
Suka koma cikin ainihin gidan sarautar suka yi shiga ta yaƙi mai ban al'ajabi sannan suka hau ingarmun dawakai guda biyu suka fice daga gidan sarautar gaba ɗaya.
Sarauniya Arya tana tsaye bisa wata doguwar baranda tana ganin tafiyarsu, tun tana hango su har sai da suka ƙule.
Wasu hawaye masu zafi suka zubo mata, ta juya ta nufi cikin turakarta inda sarki Samudul Ansari yace ya bar mata wasiƙa.
Sarki Samudul Ansari da Jalwar suka ci gaba da tafiya a cikin daular Shaha, suna zabga azababben gudu har suka fice daga cikin daular gaba ɗaya suka shiga daji.
Tun da suka fara wannan tafiya babu wanda ya ce uffan a cikinsu.
Tsahon lokaci suna ta wannan tafiya amma basu tsaya ba. Abinda ya baiwa Jalwar mamaki shi ne, waɗannan dawakai da suke kansu kwata-kwata basa gajiya, tafiya suke tamkar zasu tashi sama.
Samudul Ansari ya dubi Jalwar ya ce, "Ina tunanin amfanin jarumtakarka da ƙarfin damtsenka ya kusa ya fara amfani..."
Jalwar ya juyo ya dube shi ya ce, "Baba, ko meyasa kace haka..?"
Samudul Ansari ya ce, "Idan muka je wajen masanin Kimiyya Samazan zai yi mana bayanin komai, amma ina tunanin amfaninka ya kusa zuwa..."
Wannan shi ne yadda aka yi Samudul Ansari da ɗansa Jalwar suka kawo min ziyara a karo na farko a cikin wannan kogon dutse.
Wannan shi ne kuma yadda aka yi ya zamo cewa, ni ne kaɗai nake da cikakken hikayar Samudul Ansari duk faɗin duniya, hatta iyalansa da mutanensa basu san abubuwa da yawa da na sani akansa ba.
Lokacin da Samudul Ansari da Jalwar suka iso cikin wannan kogon dutse nawa, nayi musu tarɓa mai kyau sannan na basu abinci da abinsha na alfarma.
Bayan sun gama cin abinci sun gama samun nutsuwa sai na tambaye su, abinda ke tafe dasu.
"Shin ko kana da bayanin halittu jinsin Kentaurons? Saboda an ce min a wajenka ne kaɗai zan samu bayanin duk wasu halittu da nake so..." inji Samudul Ansari.
Koda naji abinda ya tambaya sai nayi shuru, ɗan gajeren lokaci ina tunani, kafun na ɗauko wani ƙaton littafi nawa wanda manyan masana na zamanunnuka daban-daban suka rubuta.
Na buɗe shafin farko na wannan littafi, kafun na buɗo shafi na ɗari da saba'in da tara.
A wannan shafi akwai babi guda da yayi magana akan waɗannan halittu jinsin Kentaurons.
Bayan gudanar da gajeren bincike na ɗago kai na dubi Samudul Ansari da ɗansa Jalwar na ce.
'Waɗannan halittu asalinsu ba daga wannan duniya suke ba, dakaru ne na wani babban sarki dake rayuwa a wata duniya.
'Masana na ƙarni na biyu sun yi saɓani sosai akan ainihin jikin waɗannan halittu.
'Wasu sun ce da ƙanƙara aka ƙirƙire su, wasu sun ce da tsoka da jini aka yi su, wasu sun ce da zallar tsoka aka yi su.
'Zance mafi rinjaye shi ne, sinadarin Ulwein aka sarrafa aka samar da waɗannan halittu.
'Sinadarin Ulwein wani irin sinadari ne da ake samun sa a jikin wani ƙaton kifi dake rayuwa a can ƙarƙashin teku.
'Saboda tsananin nisan zurfin wajen da wannan kifi yake rayuwa, babu wanda ya taɓa arba da shi face mutane masu nutso sosai a cikin ruwa.
'Sinadarin Ulwein yana da ban al'ajabi, domin tamkar roba haka yake.
'Duk abinda ya sare shi ko kuma ya doke shi, maimakon ya fashe ko ya tsage, lotsawa ciki yake yi.
'Bayan daƙiƙu sai ya koma kamar yadda yake a da.
'Wannan shi ne zance mafi rinjaye duba da cewa, tun da muke bincike bamu taɓa ganin gawar Kentauro wadda takobi ko wuƙa tayi ajalinta ba.
'A duk sa'adda muka tsinci gawarwakinsu sai dai mu fuskaci cewa, ƙasusuwan wuyansu aka kakkarya wanda zai sa jijiyoyin dake baiwa kansu jini su tsitstsinke, su mutu.
'Kentauron suna da ban al'ajabi. Kasancewar ƙirƙirarsu aka yi hakan yasa aka tsara musu siffa mai ban tsoro wadda zata baiwa dukkan wani abokin gabarsu tsoro.'
Ina zuwa nan a zancena na buɗo shafi na ɗari da tamanin wadda aka zana cikakkiyar siffar Kentauron akanta.
Kentauron: Halitta ce mai siffa guda biyu; rabin jikinta na mutum, rabi kuma na ƙaton ingarman doki.
Daga kunkuminsu yayi sama, gangar jikin mutum ce. Daga kunkuminsu yayi ƙasa kuwa, siffar ingarman doki ce.
Kana ganin wannan halitta zaka tabbatar da cewa, zata yi ƙarfin damtse har na ban mamaki.
Na nuna wani jan mashi dake hannun wannan halitta wadda ke kan wannan shafin littafi na ce.
'Wannan jan mashi shi ne babban makamin waɗannan halittu, duk wani gumurzu da yaƙin da suke fita da irin wannan mashi suke amfani.
'Babu wani abu a wannan duniya da wannan jan mashi ba zai huda ba, komai ƙarfin sihirin abu da taurinsa kuwa.
'Ko tau'rin aka cakawa wannan jan mashi sai yayi nasara akansa.
'Wannan na daga cikin manyan illolin Kentaurons wato wannan jan mashi, wanda suke tahowa dashi daga can duniyarsu.
'Ba mu san wanne irin sinadari aka sarrafa aka haɗa wannan mashi ba, shiyasa har gobe bamu gano makarinsa ba.
'Shawarar da duk masana Kimiyya suke bayarwa akan wannan jan mashi shi ne, kada wani ya kuskura ya bari wannan jan mashi ya caki jikinsa.
'Masana Kimiyya sun tabbatar da cewa, babu halitta mai ƙarfin gudu bisa doron ƙasa kamar Kentaurons.
'Ɗaya daga cikinsu na da ƙarfin ingarman doki guda bakwai.
'A duk sa'adda ake gwabza gumurzu dasu, da zarar gumurzun bai yi musu daɗi ba, suna iya juyawa su falfala da azababben gudu. Kafun abokin gaba ya ankara sun tsere da tazara mai nisan gaske.
'A hasashen masana, saran takobi-mai-tafiya ne kaɗai zai iya kamo su.'
Ina zuwa nan a zancena na buɗo shafi na gaba wanda aka yi bayani sosai akan fatar Kentauron.
'Fatar Kentauron tana da taurin gaske, sihirtattun makaman yaƙi da dama baza su yi nasara akansu ba.
'Takubba guda biyu ne ake tunanin zasu yi nasara akansu - Saif-Al-Barzaƙ da takobin Bankai.
'A wannan zamani da muke, babu takubba maɗaukaka kamar waɗannan takubba guda biyu.'
Koda nazo nan a zancena sai nayi shuru sannan na rufe wannan ƙaton littafi dake hannuna.
Samudul Ansari da Jalwar suka yi shuru suna tunanin waɗannan bayanai nawa.
Tsahon ɗan lokaci. Samudul Ansari ya ɗago kansa ya dube ni ya ce, "Idan jikinsu ya kasance kamar roba, ta ya ya takobin Saif-Al-Barzaƙ da Bankai zasu yi nasara akansu?"
Ina jin wannan tambaya tasa nayi murmushi na ce, "Takobinka ta Saif-Al-Barzaƙ tana samar da baƙin hayaƙi wanda kayi amfani da shi ka datsewa sarki Jiz'Ban wuya.
"Lokacin da aka samar da Saif-Al-Barzaƙ bata samar da irin wannan baƙin hayaƙi, daga lokacin da tau'rin ya dafata da hannunsa wannan sirri ya shiga.
"Wannan baƙin hayaƙi daga jikin tau'rin yake futowa, abinda yasa yake datse wuya shine, yana zuƙar sinadarin Jeeish dake jikin Saif-Al-Barzaƙ ya ƙaddamar da hari dashi.
"Kamar yadda ya zamo dole, in dai aka cakawa mutum jan mashin ma'abota Kentauro saiya mutu, haka shima wannan baƙin hayaƙi mai amfani da sinadarin Jeeish.
"Duk abinda wannan baƙin hayaƙi ya taɓa sai ya datse shi.
"Saboda haka wannan baƙin hayaƙi mai amfani da sinadarin Jeeish zai iya datse gangar jikin Kentaurons.'
Ina zuwa nan a zancena na buɗo shafi na casa'in da bakwai a cikin wannan ƙaton littafi nawa.
A cikin wannan shafi akwai wani babi da yayi magana mai taken 'KOREN-HAZO'
Koren-hazo: yana samuwa ne daga takobin Bankai mai mataki na casa'in zuwa sama.
Koren-hazo yana danne kowanne irin iko dake waje ya hana shi aiki, ya zamana cewa iya ikon ma'aboci Bankai ne kaɗai zaiyi aiki a wajen.
Mun ga yadda cewa, koren-hazo ya danne hatta ikon tau'rin ya hana shi aiki.
'Koren-hazo idan ya sauƙa a wajen da Kentauron zai hana su motsi, hakan zai baiwa ma'aboci Bankai damar ƙaddamar musu da sara.
'In dai ya sare su, a ƙarƙashin wannan koren-hazo tamkar ya samu nasara akansu ne.
'Wannan shi ne taƙaitaccen bayani akan sirrin takubba guda biyu da zasu yi nasara akan Kentaurons.'
Sa'adda nazo nan a zancena sai naga Jalwar ya dubi Samudul Ansari cikin tsananin mamaki ya ce, "Ya kai abbana! Ta ya ya jarumtaka da ƙarfin damtsena zasu yi tasiri akan waɗannan halittu, wadanda hatta takubbanku maɗaukaka ma daƙyar zasuyi tasiri akansu?"
Kafun Samudul Ansari ya baiwa Jalwar amsa, sai na dafa kafaɗarsa da hannuna guda nace, "Magaji! Mun tattauna ne akan makaman yaƙin da zasu yi tasiri akansu amma bamu tattauna akan yadda ƙarfin damtse zaiyi tasiri akansu ba."
Jalwar yana jin abinda nace naga ya gyara zama, yana sauraron abinda zan ce.
Na sake buɗo wannan shafi wanda ke ɗauke da hoton wannan halitta. Na nunawa Jalwar daidai ƙirjin wannan halitta inda ke ɗauke da zanen wani jan hatimi nace.
"Wannan waje shi ne, daidai inda ruhin waɗannan halittu yake. Ko ya ya aka gabzawa wajen naushi ya ɓurma, halittun mutuwa zasu yi.
"Babbar matsalar ita ce, idan mutum bai kasance sadauki mai tsananin ƙarfin damtse ba, ƙarfinsa zaiyi wuya ya ɓurma ƙirjin, sannan zasu iya cakawa mutum wannan jan mashi na hannunsu su hallaka shi.
"Wannan yasa ba'a cika bayyanawa jarumai wannan lago nasu ba, saboda da yawa daga cikin jarumai sun hallaka..."
Jalwar ya gyaɗa kai alamun fahimta.
Daga wannan lokaci muka ajiye batun Kentaurons a gefe. Muka fara tattauna akan duniya.
Sai da Samudul Ansari da Jalwar suka kwana uku a wajena, sannan muka yi sallama da juna, suka haye dawakansu suka tunkari hanyar komawa gida.
Sa'adda Jalwar ke kwance yana barci, mun sha tattaunawa da Samudul Ansari waɗanda hakan suka sa Samudul Ansari ya bani yardarsa har yasa na wakilta hadimi wanda zai na ɗauko min abubuwa da dama da suka faru a rayuwarsa yana rubutawa domin mu samu tarihinsa.
***
A can bisa wani tsibiri kuwa, wanda manya-manyan duwatsun ƙanƙara suka kewaye ta ko'ina waɗansu Kentaurons ne guda goma tsaitsaye sun yi sahu-sahu.
Kowannensu na riƙe da irin wannan jan mashi wanda na gama yiwa su Samudul Ansari bayani akansa.
Wani garjejen ƙato wanda yafi sauran girma da faɗi na tsaye a gabansu riƙe da zabgegen mashi.
Gaba ɗaya waɗannan halittu su goma ne kacal sarkinsu ya turo cikin wannan duniya domin su yi masa aiki.
Wannan garjejen ƙato dubi yan-uwansa guda tara ya ce, "Babban dalilin da yasa muka haɗa kai da sarki Farhama shi ne, akwai yiwuwar shi ne magajin wannan baƙin ruhi wanda sarki ya ce zai jawo masa matsala idan ya shigo wannan duniya.
"A halin yanzu kafun mu raba sarki Samudul Ansari da wannan ruhi zamu sha baƙar wahala, saboda ruhin ya gama shiga jikinsa, ya samu sinadarin da yake buƙata a cikin jinin yar ƙabilar Arya.
"Sarki ya ce, dole ne mu cakawa sarki Samudul Ansari wannan jan mashi namu a tsakiyar zuciyarsa, hakan zai sa wannan ruhi ya fice daga jikinsa.
"Ruhin na fita daga jikinsa, sarki Farhama zaiyi iya bakin ƙoƙarinsa wajen ganin ya kamo shi.
"Muna ganin sarki Farhama ya kamo wannan ruhi, zamu kashe shi sannan mu kama wannan ruhi mu kaiwa sarki ya fasa shi da hannunsa."
Wannan sadauki na zuwa nan a zancensa ya ɗaga sawayensa na gaba masu kama da na doki, ya kwarara uban ihu.
Sauran waɗannan mayaƙa suka yi koyi dashi.
Daga wannan lokaci, yayi tafiya mai nisa bisa wannan tsibiri ya ɗakko duwatsun ƙanƙara kala daban-daban ya ajiye a nesa da inda suke.
Sadaukin ya tsaya a nesa kaɗan da waɗannan mutane nasa guda tara, sannan ya fara kiransu ɗaya bayan ɗaya.
Na farko yazo, sadaukin ya nuna wani dutsen ƙanƙara dake can nesa bisa wani tudu ya ce, ya jefe shi da mashin hannunsa.
Mutumin yayi ɗaga sawayensa sama, ya cilla wannan mashi sama ya cafe sannan ya jefi wannan dutse.
Saura ƙiris, mashin ya goce amma a haka ya samu wannan dutse.
Dutsen yayi tsalle gefe guda sannan ya dagargaje tamkar niƙa shi aka yi.
Sadaukin yayi murmushi ya ce ya tsaya a gefe.
Mutumin ya koma gefe guda ya tsaya.
Sadaukin ya sake kiran na biyu, shima harinsa ya kusan zuwa daidai da na farkon.
Haka dai yayi ta kiran waɗannan mutane nasa, wasu su kusan rasa abin harinsu amma sai su same shi.
Mutum ɗaya ne kacal ya samu abin-hari daidai yadda ake buƙata.
Mutum hudu kuma suka saɓa saiti.
Sadaukin yayi murmushi ya nuna wata ƙaramar bishiyar ƙanƙara dake bisa wannan tsibiri da hannunsa guda wanda ke riƙe da wannan jan mashi.
Take bishiyar ta juye izuwa kamannin tau'rin.
Tau'rin na sanye da baƙaƙen tufafi waɗanda suke ɓulɓular da baƙin hayaƙi wanda ke sanyawa wajen da yake duhu.
Sadaukin nan ya dubi mutanen nasa guda tara ya ce, "Dukkanku ina so ku jefi wancar halittar a lokaci guda..."
Mutanen nasa suka jin wannan batu suka yi murmushi, dukkansu babu wanda keda kwakwanto a ransa ba za su sami waɗannan halittu ba.
Tazarar dake tsakaninsu da wannan halitta babu nisa sosai, saboda

Please Login or Register in order to submit comment