Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tashi a cikin wannan rami.
Nara da Aymanul Faris suka daka tsalle suka faɗa cikin wannan rami. Gangunan jikinsu suna shigewa cikin wutar, jikinsu ya saje da kalarta.
Wani jan hayaƙi mai ban al'ajabi ya fara tasowa sama daga cikin ramin, hayaƙin yayi ta tafiya a cikin gajimare.
Bayan tafiya ta kimanin sa'a ashirin da huɗu wannan jan hayaƙi ya dira a saman wani tsauni, wanda idan kana zaune a samansa har fararen gajimare zaka na gani suna wucewa ta gefenka.
Hayaƙin na dira ya fara ƙatantanwa, yana juyewa izuwa Nara da Aymanul Faris.
Jim kaɗan siffar Nara da Aymanul Faris ta bayyana a saman wannan tsauni.
Abin mamaki wannan tsauni da suke kansa, ya gama juyewa izuwa jajawur. Sassa da dama na jikinsa sun tsatstsage. Kallo ɗaya zaka yi masa ka tabbatar da cewa, ya kusa yayi bindiga.
Aymanul Faris ya dubi Nara ya ce, "A saman wannan tsaunin zan ƙaddamar da kai? Ta ya ya? Idan ya tarwatse kafun mu gama, ya ya kenan?"
Nara yayi murmushi ya ce, "Ni aljanin wuta ne, kuma ni ne hadiminka. Wannan waje shi ne yafi dacewa da ƙaddamarwa!"
Nara yana rufe bakinsa wannan tsauni ya soma rugugi zai tarwatse, cikin gaggawa Aymanul Faris ya ƙaraso gabansa ya tsaya.
Nara ya dubi Aymanul Faris ya ce ya ɗaga hannunsa na hagu sama, sannan ya rufe idanunsa.
Cikin gaggawa Aymanul Faris yayi abinda Nara ya umarce shi. Ai kuwa yana yin hakan, wata ƙara mai cika dodon kunne ta sauƙa a wannan waje.
Tsaunin da suke tsaye akansa yayi bindiga, wata irin laba (lava) mai ban tsoro tayi feshi. Jikin Aymanul Faris da na Nara gaba ɗaya ya narke a cikin wannan ruwan-wuta wanda ke tsananin gudu tamkar ruwan kogi.
Ruwan ya ci gaba da gudu a cikin wannan daji, yana narkar dukkan ƙananun dabbobi da kuma bishiyoyin da suka shigo gabansa, har yaje ya shige cikin wani kogi mai tsananin sanyi.
Sa'adda wannan ruwan-wuta ya taɓa Aymanul Faris sai yaji wani irin azababben zogi da raɗaɗi ya shige shi, amma a haka ya daure. Bai bude idanuwansa ba.
Har sai da Nara ya bashi umarnin buɗe idanun nasa. Ai kuwa yana bude su, ya tsinci kansa a cikin wani waje wanda babu komai a cikinsa face wuta. Kai ka ce wannan daji ne wanda yake kan hanyar zuwa Madarul Ansari.
Aymanul Faris yayi arba da Nara durƙushe a gabansa, wannan ruwan-wuta ya soma narkar da jikinsa.
Narkakken jikin Nara yana tafiya a hankali yana shiga jikinsa.
Sannu-a-hankali wannan ruwan-wuta ya gama narkar da jikin Nara, sannan Nara ya shige cikin Aymanul Faris gaba ɗaya.
Faruwar hakan keda wuya wani irin zafi mai kama da narkakken laba (lava) ya ziyarci Aymanul Faris. Tunda Aymanul Faris yake rayuwa a duniya, bai taɓa jin zafi mai kama da wannan ba.
A ɗaya ɓangaren kuwa, gangunan jikin Aymanul Faris da na Nara suka sake haɗuwa a cikin wannan ƙaton kogi mai tsananin sanyi.
Ba tare da jinkirin komai ba, suka yi iyo suka fito daga cikin kogin.
Nara ya rikide izuwa halittar aljani mai jikin wuta, ya caka hannunsa guda a cikin cikin Aymanul Faris.
Yin hakan keda wuya, siffar Aymanul Faris ta sauya ƙwarai da gaske.
Kayan jikinsa suka juye izuwa baƙaƙe ƙirim, suna sheƙin jar wuta. Ƙwayar idanuwansa ta fara ci da wuta. Gashin kansa ya fara cire hayaƙi jajawur.
Idan kaga Aymanul Faris a wannan siffa zaka iya cewa, yayi kama da mahaifinsa Hasanul Jalwar sa'adda yayi mugun-gamo da sarki Kuffuru a saman teku.
Bambancinsa da Hasanul Jalwar shi ne yafi Hasanul Jalwar kwarjini a wannan lokaci sannan jar wutan tafi ta Hasanul Jalwar ban tsoro.
Nara ya zube a gaban Aymanul Faris yayi mubaya'a, ya furta waɗansu kalmomi a cikin wani irin harshe wanda daga shi sai Aymanul Faris suka san abinda yake cewa.
Tsahon 'yan daƙiƙu kafun jikinsa ya juye izuwa jar wuta sannan ya shige cikin Aymanul Faris ta cikin wani sabon hatimi da ya bayyana a bayan wuyansa.
Wannan jar-wuta na gama shigewa cikin Aymanul Faris wani sabon zogi da raɗaɗi wanda ya ninka na farko ya sake lulluɓe shi.
A wannan rana, a wannan lokaci Aymanul Faris ya ƙaddamar da aljanin wuta Nara-ya a matsayin hadiminsa.
Lamba takwas a cikin wani yare wanda bamu taɓa gani ba ta bayyana akan goshin Aymanul Faris. Tsahon daƙiƙu goma kacal kafun ta ɓace ɓat!
Nara ya sake bayyana durƙushe a gaban Aymanul Faris cikin biyayya ya ce, "Daga yau na zamo babban hadiminka... Zaka iya amfani da ƙololuwar fasahata ta wuta wadda hatta shi kansa Samudul Ansari baiyi amfani da ita ba."
Aymanul Faris yayi murmushi ya ce, "Mu koma birnin Darul Barban, ina so ayi aurena da Riya cikin gaggawa..."
Nara yayi murmushi. Maimakon a wannan lokaci ya sake amfani da wannan ɗalasimi kamar wanda yayi amfani dashi lokacin da zasu taho wannan tafiya, kawai jikinsa ne ya juye izuwa wuta ya ɓace.
Aymanul Faris yayi murmushi ya gogi wannan sabon hatimi da ya bayyana a bayan wuyansa, take jikinsa shima ya juye izuwa wuta ya ɓace daga wannan waje.
****
A can birnin Darul Barban kuwa, tuni shirin biki ya fara yin nisa. An shirya wajajen taro masu yawan gaske. An dafa abinci mai tsananin yawa.
A tsakiyar birnin aka gina wani ƙaton gida wanda za'a ɗaura auren a ciki.
Wasu ƙwararrun mata aka samo waɗanda suke yiwa jaruma Riya kwalliya da kuma yi mata gyara irin na amare.
Kafun kace wani abu, tuni gagarumin biki ya fara tashi a wannan waje.
Kowa da kowa ya gama hallara, amma banda ango.
A lissafinsu Barban da asuba Aymanul Faris zai dawo amma gashi har gari ya gama wayewa bai dawo ba.
Hakan ne yasa suka fara tunanin ko'ina ya tafi.
To, idan kayi duba izuwa birnin Damashkar kuwa, zaka ga kyakkyawar gimbiya wadda zaka rantse idanuwanka basu taɓa kallon mai rabinta a kyawu ba, tana zaune bisa karagar mulki tana gudanar da harkokin mulki.
Ta saka kaya ruwan-ƙasa waɗanda suka ƙara fiddo tsantsar kyawunta.
Abin mamaki, idan ka san gimbiya Jaanu masoyiyar Aymanul Faris zaka fuskanci wannar ba wata bace sai ita. Amma kallon farko shakku zai zo ranka saboda yadda kyawunta ya ninka na da sau goma.
Da yawa daga cikin jama'ar dake zazzaune a wannan fada, suna zuwa ne kawai domin arba da wannan kyakkyawar sura wadda kallonta kaɗai ya isa ya cirewa mutum takaici.
Jaanu tana zaune bisa karagar mulkin amma tayi shuru kamar wadda take tunani ko kuma wani abu ke damunta.
Zaka yi matuƙar mamaki idan aka ce ma, kyakkyawar budurwa kamar wannan tana shiga damuwa ko kuma tunani akan wani.
A wannan rana tunda asuba ta tashi da wani irin yanayi wanda hatta ita kanta, bata san na mene ne ba.
Wani lokacin sai taji kamar damuwa a ranta, to amma mene ne ke damunta?
Wani lokacin kuma sai tayi ta tunani, tunanin Aymanul Faris ya faɗo mata, tunanin mahaifinta ya sake faɗo mata.
Wannan shi ne halin da ta tsinci kanta a ciki a wannan rana.
Bayan gajeren lokaci, wani irin iko ya ziyarci wannan fada. Dukkan jama'ar dake zaune a cikin fadar, suka daina ganin komai.
Ba wai sun daina motsi bane, ba wai kuma an taɓa tunaninsu bane. Kawai wannan iko ya hana su ganin dukkan abinda ke faruwa a wannan wajen ne.
Jaanu tayi ajiyar zuciya, dama tunda ta tashi da wannan yanayi tasan cewa, akwai yiwuwar a wannan rana zata yi baƙo.
To, amma wane ne?
Mafi yawancin lokuta, idan Aymanul Faris ne zaizo a cikin lambunta suke haɗuwa. Ko sau ɗaya bai taɓa zuwa fada ba.
Jim kaɗan bayan bayyanar wannan sabon iko, wani kyakkyawan saurayi mai murɗaɗɗen jiki ya bayyana a cikin wannan fada.
Saurayin na sanye da baƙaƙen tufafi a jikinsa, gashin kansa a kwance yake, idanuwansa na bayyanar da kamala da kwarjini irin na manyan sarakuna.
Kallon farko Jaanu ta yiwa wannan saurayi, taji wani sanyi a ranta.
Abinda ta daɗe tana jira ne yazo, wanda take tunaninsa kullum da ko da yaushe.
Ba wani bane illa, masoyinta Aymanul Faris.
Aymanul Faris ya kaɗa hannunsa guda, wata karagar mulki ƙerarriya daga wuta ta bayyana a bayansa ya zauna akanta.
Tun da ya bayyana a wannan waje, idanuwansa da na Jaanu na haɗe a waje guda, suna yiwa juna kallon soyayya da bege.
Duk jama'ar dake wannan fada, basu san da bayyanar Aymanul Faris ba, ballantana ma su yi tunanin wane ne shi.
Babu mai kallonsa a wannan fada, idan ka cire gimbiya Jaanu.
Lallai Aymanul Faris ya samo babban matsayi a wajen aljanin-wuta wanda ya bashi ƙarfin iko.
"Wacce shawara kika yanke a zuciyarki, ya ke Arya?" Aymanul Faris ya tambayeta.
Lokaci na ƙarshe da suka rabu, mun ji cewa Jaanu ta buƙaci ya bata lokaci domin tayi tunani akan maganar da yazo mata da ita, na amincewa ta zamo matarsa ta biyu bayan jaruma Riya.
Gimbiya Jaanu tayi guntun murmushi ta ƙura masa idanu, kamar tana tunanin wani abu.
Ƙirjin Aymanul Faris ya soma dukan uku-uku. Wannan murmushin da take na mene ne?
"BA ZAN TAƁA CANJAWA BA, AIKINA GUDA ƊAYA NE A DUNIYA - SHI NE ƘAUNARKA. BABU ABINDA ZAI RABA MU, KOMAI WUYA, KOMAI RINTSI NI TAKA CE!!!" inji Jaanu.
Abin mamaki a wannan lokaci muryarta ta amsa kuwwa daga kowanne bangare na wannan fada. Kai kace ba ita kaɗai ce ta furta waɗannan kalmomi ba.
"Na gode," inji Aymanul Faris cikin murmushi. "Na zo ne na sanar dake yau ake ɗaura aurena da jaruma Riya. Kada ban sanar dake ba, hakan ya zamo laifi a nan gaba..."
Gimbiya Jaanu ta girgiza kai ta ce, "Ba zaka taɓa aikata min laifi ba. Duk laifin da zaka aikata min a nan gaba na yafe maka. Fatana shi ne Ubangiji ya nuna min auren mu, wanda shi ne babban burina..."
Aymanul Faris yayi murmushi. Zuciyarsa ta cika maƙil da mamaki. Bai taba tsammanin soyayyar da take masa ya kai haka ba.
"Da yaddar Ubangiji auren mu ya kusa. Idan na auri Riya, zamu tafi izuwa kogon Madarul Ansari domin ɗauko tau'rin. Idan muka ɗauko tau'rin abu na gaba da zamu gudanar shi ne, aure tsakanina da ke.
"Da zarar an ɗaura mana aure, zan farkar da babban sirrin dake cikin jinina.
"Idan na farkar da babban sirrin dake cikin jinina, zan zamo babban sarki.
"Daga wannan lokaci, zamu koma daular Shaha mu ci gaba da tafiyar da harkokin mulki kamar yadda magabantanmu suka yi.
"Shin kin amince?"
Gimbiya Jaanu tayi murmushi ta ce, "Ɗari bisa ɗari!"
Haka dai Aymanul Faris da masoyiyarsa Jaanu suka ci gaba tattaunawa a cikin soyayya har tsahon ɗan lokaci sannan suka yi sallama da juna.
Akan cewa, Aymanul Faris zai dawo ya bayyana mata ranar aurensu da kuma wajen da zasu gudanar.
Aymanul Faris yayi girgiza jikinsa ya juye izuwa wuta, take ya ɓace ɓat!
Wannan iko da ya lulluɓe wannan waje ya yaye, kowa ya dawo hayyacinsa. Mutane suka ci gaba da gudanar da ayyukansu tamkar babu wani abu da ya faru.
****
A can birnin Darul Barban kuwa, koda su Barban suka ga azahar ta fara kawo jiki, Aymanul Faris bai dawo ba sai suka fara shawara akan abinda ya kamata su yi.
Wasu su ce Barban ya bi bayan Aymanul Faris, wasu kuma su ce a bari zuwa dare idan bai dawo ba, sai a san abinda ya kamata a yi.
Bisa dole dai, aka ajiye magana akan cewa, zuwa dare idan bai dawo ba za'a yanke hukunci.
Rana na daf da faɗuwa, aka ga unguwar Barbanul Kuyr ta soma cika da wani irin jan hayaƙi.
Jaruma Riya da Barban suna ganin wannan jan hayaƙi suka soma murmushi saboda sun gano na wane ne.
Jim kaɗan hayaƙin ya soma curewa a waje guda yana samar da siffar wani kyakkyawan saurayi wanda yake sanye da baƙaƙen tufafi.
Cikin gaggawa jaruma Riya ta ruga ta rungume shi.
Bayan rana ta faɗi aka ɗaura auren Aymanul Faris da jaruma Riya a cikin wannan ƙatoton gida.
Aka yi aure kamar yadda aka saba gudanarwa a al'adar ƙabilar Kuyuru.
Bayan mahaifiyar Aymanul Faris ta gama saka musu albarka, sai Aymanul Faris ya kama hannun matarsa suka nufi ƙawataccen ɗakin da aka gina musu musamman domin more amarci.
Suna shigowa cikin wannan ɗaki, suka yi arba da kuyangi sun shirya ababen ci da sha.
Kuyangin suna ganin shigowarsu suka miƙe suka basu waje.
Aymanul Faris ya zaunar da jaruma Riya a gaban wadannan abinci.
A wannan rana Aymanul Faris da kansa ya ciyar da Riyalatu abinci saida ya tabbatar ta ƙoshi, sannan shima ya bata umarnin ciyar dashi.
Nan take kuwa ta cika wannan umarni.
A wannan dare Aymanul Faris da jaruma Riya suka yi ta nunawa junansu soyayya, kowa yana so ya burge ɗan uwansa.
Bayan ɗan lokaci, Aymanul Faris da Riya suka shiga cikin wani ƙaramin banɗaki suka yi wanka.
Suna fitowa daga wankan, suka hau kan ƙasaitaccen gadon da aka shirya musu.
A wannan lokaci, mu'amalar farko ta shiga tsakanin Aymanul Faris da Riya tun daga tasowarsu har zuwa wannan lokaci.
Sa'a huɗu na shuɗewa suka sauƙo daga kan gadon, suka sake yin wanka, sannan suka koma suka kwanta.
Washe gari da safe, suka yi ado suka je wannan falo a tare.
Barban suka tarar tare da Hajriya suna tattaunawa. Tana kallonsu tsananin farin ciki ya cika ranta.
Wannan rana ita ta daɗe tana jira. Ranar da zata ga auren ɗanta da jaruma Riyalatu.
Bayan sun gama gaisawa, Hajriya ta ce, "Ya ya daren ku na farko?"
Dukkansu suka yi murmushi suka gagara bayar da amsa.
Barban ya dubi Aymanul Faris cikin nutsuwa ya ce, "Babban jarumi, yau ne maigirma Ranganu ya ce kuje wajensa domin yin sallama ta ƙarshe. Shin wadanne tsare-tsare ka tsarawa kanka, ka san cewa da zarar ka mallaki tau'rin kana buƙatar Arya?"
Aymanul Faris ya ce, "Ɓangarena da ɓangaren ARYA babu wata matsala. Har i zuwa wannan lokaci, mahaifinta bai bayyana ba. Ya mutu ko yana raye, babu wanda ya sani."
Tsahon ɗan lokaci duk suka yi shuru.
Daga can sai Aymanul Faris ya ce, "Ya ya labarin sarki Kuffuru da sadaukai-uku wadanda suke shirye-shiryen kama ka? Shin ISRABIL ya kusa kashe Kuffuru?"
Barban yayi guntun murmushi ya ce, "Na kusa na girgiza sarki Kuffuru da tawagarsa. Ka bari sai mun dawo kan waɗannan abubuwa guda huɗu da suka rage, duniya gaba ɗaya sai ta girgiza.
"ISRABIL? Har yanzu basu haɗu da sarki Kuffuru ba. Watan da ta wuce ne, wani aljani ya kawo min labarin wai ISRABIL ya kashe hadimin-duwatsu Buƙal."
Aymanul Faris ya jinjina kai cikin fahimta. Sarki Kuffuru, sarki Ayubul-Zairiy da yarima Marganu su ne abokan gabarsa, yana da kyau a wannan lokaci yana tambayar labarinsu.
Barban ya ce, "Idan ka shirya, ya kamata ku tafi wajen Ranganu domin tafiya izuwa Madarul Ansari..." Aymanul Faris da jaruma Riya suka gyaɗa kai, daga bisani suka zo gaban Hajriya suka kwashi gaisuwa.
Hajriya ta saka musu albarka tare da fatan nasara.
Aymanul Faris ya dafa jaruma Riya take suka ɓace ɓat! daga wannan waje.
Barban da Hajriya suka ɗan yi shuru na lokaci, kafun ta dube shi ta ce, "Ta ya ya kake cewa, zaka girgiza duniya alhalin su sarki Kuffuru sun kusa kama ka?"
Barban yayi guntun murmushi ya ce, "Babu wanda zai san wannan tsare-tsaren face ni da maigidana... Amma duniya zata girgiza..."
Haka dai suka ci gaba da tattaunawa har tsahon lokaci, sannan shima yayi sallama da ita ya tafi.
****
Yau *11/05/2023*
Babi na gaba zaizo *13/05/2023* da yaddar ALLAH.RUHIN JARUMTAKA!
*
Babi na 123: *Babban Kuskure*
*
Wannan littafin sadaukarwa ne ga Zahra.
*
U-M-S
*
*Sanarwa ta musamman: Za mu dawo ɗaura muku wannan littafi da rana, kamar yadda aka saba kafun azumi.
*
~Birnin Jai'zin, daular Zas.
*
Birni ne ƙatoton gaske wanda da wuya a samu wanda zai kaishi girma a wannan daula.
Gine-ginen cikin birnin sun tashi sama, wasu har sun fara ƙulewa a cikin gajimare.
Anyi amfani da wani irin tubali wajen gina wannan birni, tubalin yana kama da na kwarin Jekish.
Gaba ɗaya garin a kewaye yake da wata ƙatuwar katanga wadda ta shige har cikin gajimare.
Ƙofar shiga guda ɗaya jal! kawai aka yi masa ta ɓangaren yamma.
Waɗansu dakarun-aljanu guda uku kacal! suna tsaitsaye a bakin garƙamemiyar ƙofar suna gadi.
Suna sanye da farin sulke mai ratsi-ratsin baƙi-baƙi. Kansu na rufe a cikin hular-sulke, iya idanuwansu kawai ake kallo.
A tsaye zasu kai bishiyar dabino biyu tsayi, kaurin jikinsu kuwa tamkar bishiyar kuka.
Dukkansu suna riƙe da zabga-zabgan takubba, masu kauri da tsananin nauyi.
Wannan shi ne birnin Jai'zin, birnin da sarki Ranganu yake mulki.
Idan kayi duba izuwa ƙofar shigowa wannan gari, zaka yi arba da waɗansu mutane guda huɗu tsaitsaye sun yi cirko-cirko a gaban waɗannan masu gadi.
Biyu daga cikin waɗannan mutane zaratan-mayaƙa ne, ɗaya kuma gawurtacciyar matsafiya ce, ɗaya kuma hatsabibin boka ne.
Idan ka san rundunar SADAUKAI-UKU 'yan-baiwa da kuma boka Hubbazu zaka fuskanci su ne a ƙofar shiga garin Jai'zin ba wasu ba.
Sarki Kuffuru (Infiron) na riƙe da zabgegiyar takobinsa, haka ma Rauziyya da kuma Darwazu. Shi kuwa Hubbazu yana tsaye a bayansu riƙe da isgar tsafi.
Kasancewar sun yi arba da dakaru guda uku kacal! yasa gagarumin farin ciki ya lulluɓe su.
Saboda sun tabbatar da cewa, ta kowanne hali sai sun yi nasara akansu yau. Ko domin ƙarfin shirinsu kuwa.
Masu gadin na ganin baƙin mutane a gabansu, suka yi kamar basu gansu ba ko kuma zaka iya cewa tamkar sun san da zuwansu.
Sarki Kuffuru, sarki Darwazu, sarauniya Rauziyya da boka Hubbazu suka ƙarasa kusa da waɗannan mayaƙa guda uku, suka tsaitsaya.
Sarki Kuffuru ya daka musu tsawa ya basu umarnin buɗe masa ƙofa.
Masu gadin suka yi shuru tamkar basu ji wannan umarni da ya basu ba.
Lamarin da yasa sarki Kuffuru fusata kenan, ya ɗaga takobinsa ya ruga da gudu kan wadannan masu gadi.
Sarauniya Rauziyya da sarki Darwazu na ganin haka, suka yi koyi dashi. Shi kuwa Hubbazu saiya tsaya a baya yana gyara isgar tsafinsa.
Abinda ya baiwa su sarki Kuffuru mamaki shi ne, kwata-kwata waɗannan masu gadi basu damu dasu ba. Kai kace ba su aka tunkaro ba.
Su sarki Kuffuru suna ƙarasawa gabansu suka fara kai musu muggan sara da suka cikin baƙin zafin nama.
Waɗannan masu gadi suka wanzu suna masu kakkaucewa hare-haren su sarki Kuffuru cikin kwanciyar hankali.
Tsahon ɗan lokaci ana ta abu ɗaya; su sarki Kuffuru basu samu nasarar saran jikinsu ba, sannan su kuma ko sau ɗaya basu mayar da martani ba.
Koda sa'a guda ta shuɗe su sarki Kuffuru basu sami nasarar komai ba, sai suka daka tsalle baya suka tsaya cirko-cirko.
"Hmm," wata murya mai kaushi da ikon gaske tayi murmushi, amma su sarki Kuffuru basu ga mai ita ba.
Masu gadi suna jin murmushin suka yi gaggawar buɗe wannan ƙatuwar ƙofa dake rufe.
Sarki Kuffuru, sarki Darwazu, Rauziyya da Hubbazu suka tsaya ƙyam, suna jiran su ga wane ne zai fito daga cikin wannan birni wanda ga dukkan alamu shi ne yayi wannan murmushi.
Ƙofar tana gama buɗewa, siffar wani basaraken aljani ta bayyana cikin fararen sulke da zabgegiyar farar takobi.
Dukda cewa a cikin shigar yaƙi yake amma fuskarsa na bayar da tsantsar buwaya da kamala. Kai kace wani babban mai bayar da karatu ne.
A hankali ya ƙaraso gaban su sarki Kuffuru ya tsaya, suka fara kallon-kallo.
Duk cikin su sarki Kuffuru babu wanda ƙirjinsa bai soma dukan uku-uku ba, saboda tsananin kwarjinin sarkin.
Wannan basarake shi ne sarki Ranganu wanda ke mulkin daular Zas gaba ɗayanta.
Kuma shi ne wanda su sarki Kuffuru suka zo hallakawa domin su samu damar kama Barban cikin sauƙi.
Sarki Kuffuru ya daka tsalle ya dira a gabansa, sannan ya kai masa wawan sara a kafaɗa.
Cikin kwanciyar hankali Ranganu ya kaucewa saran, sannan ya cafko wuyan sarki Kuffuru ya ɗaga shi sama, yana reto a hannunsa tamkar wanda ya riƙe kyanwa.
Darwazu, Rauziyya da Hubbazu suka zaro idanu cikin tsananin mamaki, a duk cikin tawagarsu babu sadauki mayaƙi kamar Kuffuru amma gashi a hannu tamkar kyanwa.
Ranganu yayi murmushi ya dube su ya ce, "Kada ku ga kamar na kama abin dogaron naku, ba shi bane. Yaudararku sarki Kuffuru yayi. Ku mahaukata ne, shin kun manta ance KOWA A GIDANSA SARKI NE!"
Koda Rauziyya, Darwazu da Hubbazu suka ji wannan batu na Ranganu sai suka cika da tsananin mamaki.
Cikin rashin tsoro Rauziyya ta dube shi ta ce, "Ƙaryarka tasha ƙarya. Wannan mutumin sarki Kuffuru ne. Kada kayi tunanin don ka kama shi farat ɗaya, zaka yi amfani da hakan ka yaudare mu.
"Kowa da ka gani a cikin wannan runduna tamu da cikakken shirinsa yazo. Ko akwai sarki Kuffuru, ko babu shi. Hakan ba zai rage mana komai ba..."
Rauziyya tana gama faɗin haka, ta ɗaga takobinta sama tayi ihu. Waɗannan fuka-fuki dake fitowa daga gadon bayanta suka bayyana.
Nan take ta buɗe fuka-fukin ta tashi sama tamkar tsuntsuwa ta fara yawo a cikin iska a wannan waje.
Ranganu yayi murmushi ya gyaɗa kai, ya ɗaga wannan sarki Kuffuru dake hannunsa ya doka shi da ƙasa. Take gangar jikin mutumin ta tarwatse, wani irin baƙin abu mai kama da ƙonannen dalma ya cika wajen.
A razane Hubbazu da Darwazu suka ja da baya cikin tsananin mamaki. Basu taɓa tsammanin sarki Kuffuru zai yaudare su ya bar musu mutum-mutumi ba.
Sarauniya Rauziyya tana gama tashi sama, ta yiwo ƙasa sannan ta fara kaiwa Ranganu sara da suka.
Ranganu bai kauce ba, sannan bai zaro takobinsa ba. Hare-haren sarauniya Rauziyya suka yi ta dira kansa, amma basa yi masa komai tamkar dutse take sara.
Ranganu ya dube su ya ce, "To, ku yanzu wanne hukunci kuke so na yanke muku?"
Dukkansu suka yi shuru tsahon ɗan lokaci, basu bashi amsa ba.
Ranganu yana gajiya da jira yasa hannunsa guda ya make Rauziyya wadda ke kawo masa sara da suka.
A galabaice Rauziyya ta

Please Login or Register in order to submit comment