Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

rashin tausayin mutum, idan yaga yadda masoya ke kukan rabuwa da masoyansu sai zuciyarsa tayi sanyi.
Saida suka shafe sa'a guda suna ƙanƙame da juna, sannan suka janye jikinsu daga nasa.
Samudul Ansari ya dafa kafaɗar Kusufu ya ce, "Ina maka fatan nasara, sabon sarki."
Kusufu ya goge hawaye idanunsa ya durƙusa a gaban Samudul Ansari yayi godiya.
Samudul Ansari ya sake rungume sarauniya Arya a ƙirjinsa ya ce, "Nagode bisa yadda kika kula da mahaifina tun farkon haɗuwar mu.
"Nagode da yadda kika amince kika aureni, lokacin da nake ba'a komai ba. Kika mayar da ni komai.
"Labarin soyayyata da ke abun tunawa ne ga 'yan baya. Ba zan taɓa mantawa dake ba. Koda kuwa ina kwance a cikin kabarina ne..."
Yana zuwa nan a zancensa ya sumbaci Arya a goshi, sannan ya juya ya tunkari inda ɓoyayyen hadimi ke tsaye.
Sarauniya Arya da Kusufu suka bishi da kallo kawai, suna ta kuka.
Har Samudul Ansari ya kusa isowa inda ɓoyayyen hadimi ke tsaye, saiya tsaya ya juyo ya kirawo Kusufu.
A guje Kusufu yaje inda yake tsaye. Samudul Ansari ya zaro takobin Saiful-Shiradu ya baiwa Kusufu ya ce, "Hadiman Shiradu da aljani Nara zasu ci gaba da tayaka tafiyar da harkokin mulki. Fatan alheri, ɗana."
Idanuwan Kusufu a cike da hawaye ya karɓi wannan takobi, yayi godiya.
Samudul Ansari ya dubi sarauniya Arya yayi mata murmushin ƙarshe, sannan ya haye kan ɓoyayyen hadimi. Nan take ɓoyayyen hadimi ya tashi sama da shi.
Tun su Arya da Kusufu suna hango shi, har saida ya ƙule a cikin gajimare.
Hawaye suka ci gaba da zubowa daga cikin idanuwansu.
****
Ɓoyayyen hadimi da Samudul Ansari suka ci gaba da tafiya a cikin gajimare, lokaci mai tsaho sannan suka sauƙo a cikin wani ƙaton daji mai yawan manya-manyan itatuwa.
Samudul Ansari ya sauƙo daga kan ɓoyayyen hadimi sannan ya fiddo takobin Saif-Al-Barzaƙ ya cakata a tsakiyar wannan daji sannan ya binne waɗansu ɗalasimai.
Faruwar hakan keda wuya, wani narkeken dodo baƙi ƙirim ya bayyana a cikin wannan daji.
Samudul Ansari na ganin haka yayi murmushi ya sake hawa bayan ɓoyayyen hadimi, suka bar wannan daji gaba ɗaya.
Bayan shafe wata doguwar tafiya suka sake dira a cikin wani daji.
Samudul Ansari ya sake caka wannn takobi tasa a cikin ƙasa, sannan ya zana ɗalasimai.
Waɗansu halittu guda biyar masu kama da tau'rin suka bayyana a cikin dajin.
Samudul Ansari ya sake hawa bayan boyayyen hadimi suka bar dajin.
Bayan watanni uku, suna tafiya Samudul Ansari ya zana ɗalasimai akan hannunsa sannan ya sake su suka faɗo cikin wani daji.
Wannan shi ne dajin da Samudul Ansari yayi ajiya a cikinsa wanda kuma bai sauƙo a cikinsa ba.
Suka ci gaba da tafiya tsahon watanni sannan suka sake sauƙowa cikin wani daji.
Abin mamaki wannan daji komai nasa na wuta ne.
Gaba ɗaya bishiyoyin dajin da tsaunikan cikinsa duk wuta ce keta cin su tamkar gobara ake, amma haka yake kuma haka ya wanzu.
Samudul Ansari ya sake yin ajiyarsa, sannan suka wuce.
Daga wannan waje, ba'a sake kallon Samudul Ansari ba sai a cikin wani ƙaton kogon dutse dake ƙarƙashin ƙasa.
Idan kaga girman wannan kogon dutse da kuma abubuwan dake cikinsa zaka iya cewa, ƙaramin gari ne kawai.
Samudul Ansari da ɓoyayyen hadimi suka ƙarasa cikin wani ɗaki wanda babu kamarsa a duk cikin kogon.
A cikin wannan ɗaki ne aka nuno wata baƙar kwalba da kuma wani baƙin kufe.
Samudul Ansari ya fiddo wata wasiƙa ya baiwa ɓoyayyen hadimi, sannan ya fara magana da tau'rin.
"Lokaci yayi. Nazo wajen da aka umarce ni da zuwa!" inji Samudul Ansari.
"Ka tafiyar da komai yadda ya dace... Fatan alheri a rayuwarka ta gaba..." inji tau'rin.
Nan take Samudul Ansari ya durƙusa a gaban waɗannan abubuwa guda biyu (kwalbar nan da kuma kufen takobi).
Hayaƙin baƙi ƙirim ya fara sauƙowa wannan waje. Ɓoyayyen hadimi ya daina ganin komai.
Bayan cikar sa'a uku wannan baƙin hayaƙi ya yaye. Ɓoyayyen hadimi yayi arba da gangar jikin Samudul Ansari ta juye izuwa gunki wanda aka ƙera da zallar dutsen Zaijan.
Fuskarsa na ɗauke da murmushi a haka ya riga mu gidan gaskiya.
Ɓoyayyen hadimi ya risina ya yiwa Samudul Ansari sujjada, sannan ya juya ya fice daga cikin kogon Madarul Ansari.
****
Daga wannan rana sarki Kusufu ya ci gaba da mulki a birnin Shaha.
Wata guda bata kewayo ba, sarki Kusufu ya tara dukkan jama'ar ƙasar ya sauya sunansa daga *KUSUFU* zuwa *KUSUFUL JALWAR* domin a dinga tunowa da Jalwar saboda jarumtakar da yayi ta bayar da rayuwarsa da yayi ya ceci Kusuf lokacin da sarauniya Yilan take daf da caka masa takobi.
Daga wannan lokaci ya ci gaba da tafiyar da harkokin mulki kamar yadda mahaifinsa sarki Samudul Ansari ya umarce shi.
Sarki Kusuful Jalwar yayi aure ya haifi yara shima.
****
****
****
Lokacin da tsoho Samazan yazo nan a labarinsa sai yayi shuru, ya dubi Aymanul Faris, jaruma Riya da Barban yaga duk sun sunkuyar da kawunansu ƙasa, suna ta zubar da hawaye saboda tsananin tausayi.
Samazan ya ce, "Wannan shi ne cikakken tarihin Samudul Ansari wanda mutane da dama a duniya suke burin saurara..."
Barban ya ce, "Yau shekaruna tamanin da bakwai a duniya. Na saurari hikayoyin manya-manyan sarakuna, aljanu da jarumai. Amma ban taɓa jin hikaya mai taɓa zuciya kamar wannan ba.
"Akwai abubuwan al'ajabi, jarumtaka, gagarumar soyayya da tausayi duk a cikin wannan hikaya. Amma ka manta abu guda!"
Cikin tsananin mamaki Samazan ya dube shi ya ce, "Me kenan?"
Barban ya ce, "Baka faɗa mana hukuncin da aka yankewa Gauhan Ansari ba, tunda mun ji cewa ikon duniyar sarauniya Yilan ya danne shi, sannan lokacin da Samudul Ansari ya fito daga cikin duniyar har da shi."
Aymanul Faris da jaruma Riya suka dubi juna cikin tsananin mamaki. Dukkansu basu kawo wannan a ransu ba. Lallai a wannan rana sun tabbatar da hikimar Barban da ake magana akai.
Samazan yayi murmushi ya ce, "Shin ba ku ji ance an tsuma Gauhan da wadannan BES guda huɗu a cikin tukunyar tsafi ba?"
Barban, Aymanul Faris da jaruma Riya suka gyaɗa kai, "Haka ne!"
Samazan ya ce, "Babban sirrin waɗannan sinadarai da gangunan jikinsu suka zuƙa yana cikin jikin sarauniya Yilan. Duk lokacin da aka kashe sarauniya Yilan, su ma mutuwa za su yi.
"Don haka sa'adda Kusuful Jalwar ya sare kan sarauniya Yilan, a dai-dai lokacin shima Gauhan ya mutu. Akwai wata tambayar?"
Jaruma Riya ta dube shi ta ce, "Mene ne dalilin da yasa Samudul Ansari bai baiwa ɗansa Kusuful Jalwar takobin Saif-Al-Barzaƙ ba?
"Kuma mene ne dalilin da yasa bai umarci wannan ruhi ya shiga jikin Kusuful Jalwar ba?"
Samazan ya ce, "Takobin Saif-Al-Barzaƙ da tau'rin tare suke tafiya. Tau'rin zai iya rayuwa babu Saif-Al-Barzaƙ amma Saif-Al-Barzaƙ idan babu tau'rin ƙarfinta baida yawa.
"A cikin duniyar Gorgon babu tau'rin, wannan yasa takobin Saif-Al-Barzaƙ ta ƙi tayi tasiri a cikin duniyar.
"A duk lokacin da tau'rin ya taɓa Saif-Al-Barzaƙ ƙarfinta yana ninka kansa sau dubu.
"Bayan wannan waɗannan dazuzzuka da Samudul Ansari yayi ajiya a cikinsu, dole saida takobin Saif-Al-Barzaƙ zaiyi ajiyar shiyasa bai baiwa Kusuful Jalwar ita ba.
"Sannan batun wannan ruhi kuwa, idan ba ku manta ba, ance shi kansa Samudul Ansari jininsa ne da na Arya ya haɗu shiyasa suka yi aure.
"Idan babu mai irin jinin Arya, shi kansa Samudul Ansari ba zai mallaki wannan ruhi har ya sarrafa shi ba, fatan kin fahimce ni?"
Jaruma Riya ta gyaɗa masa kai cikin fahimta.
A wannan lokaci ne Aymanul Faris yasa baki a cikin maganar.
"Shin tun daga wancan zamani, daular Gorgon bata sake wani motsi ba?
"Ya ya batun Kentaurons wadanda aka turo cikin wannan duniya musamman domin su tarwatsa wannan ruhi?"
Samazan yayi murmushi kusan duk tambayoyin da suka yi babu wadda ta burge shi kamar ta Aymanul Faris.
"Tun daga wancan lokaci daular Gorgon basu sake fitowa daga daular su ba.
"Zaka iya cewa a wancan zamani abubuwan dogaron nasu guda huɗu ne.
"Abu na farko shi ne aljani Ziyazil, abu na biyu sarki Jiz'Ban, na uku sarauniya Yilan, na huɗu addinin Bankai.
"Duk waɗannan abubuwa da na lissafo muku, Samudul Ansari ya gama da su.
"Kentaurons?
"Tun daga wannan lokaci da Samudul Ansari yayi musu barazana suka gudu daga wannan duniya, suka koma wajen sarkin da ya aiko su.
"Sarkin na jin abinda suka sanar dashi, duk yasa aka karkashe su, sannan ya sake zaɓo zaƙwaƙurai daga cikin mutanensa. Ciki harda ɗansa guda.
"Sarkin ya turo su cikin wannan duniya, amma suna zuwa suka iske tau'rin baya nan.
"Wannan na daga cikin hikimomin da suka sa Samudul Ansari ya ƙi baiwa Kusuful Jalwar wannan ruhi domin za'a iya raba shi dashi tunda baya tare da jinin Arya a jikinsa."
(Ƙarin bayani: Akwai bambanci sosai tsakanin samu da kuma haɗuwa. Samudul Ansari asali jininsa ne da na Arya ya haɗu, shiyasa ya samu gagarumin ƙarfi. Saboda haka 'ya'yansu zasu iya samun jinin Arya ko kuma na Samudul Ansari, ya danganci yanayin ƙwayoyin haihuwa.)
Aymanul Faris ya sake cewa, "Shin mene ne Samudul Ansari ya rubutawa ɓoyayyen hadimi a cikin wannan wasiƙa? Sannan wane ne ɓoyayyen hadimi?"
Caraf Barban ya tari numfashin Aymanul Faris ya ce, "Za mu amsa maka wannan tambaya, amma ba a wannan waje ba... Idan babu wata tambayar zamuyi sallama da Samazan mu tafi!"
Aymanul Faris ya cika da tsananin mamaki amma baice komai ba.
Bayan gajeren lokaci, suka yi sallama da Samazan. Suka gode masa ƙwarai da gaske.
Shima yayi godiya.
Barban ya dafa su. Nan take jikinsu ya ɓace daga cikin wannan kogo.
****
Yau *27/04/2023*
Babi na gaba mai suna *DAWOWAR MARGANU* yana nan tafe ranar *29/04/2023*
****
Ba mu sharhinka/sharhinki dangane da TARIHIN SAMUDUL ANSARI?RUHIN JARUMTAKA!
*
Babi na 117: *Dawowar Marganu*
*
Wannan littafin sadaukarwa ne ga Zahra...
*
UMS
*
~Ɓangaren Yarima Marganu.
*
Aljani Isika ya tsaya cak! a inda yake har saida aljani Djinn yazo daf da shi. Djinn ya ɗaga waɗannan takubba guda biyu na hannunsa waɗanda aka sarrafa da zallan duwatsu, ya kawowa Isika sara dasu.
Takobi ta farko kan Isika ta nufa zata fille, ta biyu kuwa, gangar jikinsa ta tunkara zata tsinke gida biyu.
Isika bai yi wani motsi ba, sai da takubban suka zo daf da shi zasu tsarge shi, sannan jikinsa ya saje da kalar hasken wannan wuri ya ɓace ɓat!
Hare-haren aljani Djinn suka sami iska. Kafun ya juyo tuni Isika ya bayyana a bayansa.
Cikin gaggawa Isika ya dankara masa sara akan kafaɗa da wannan sunduƙi na haske dake hannunsa.
Jan haske wanda ke jikin wannan sunduƙi ya shige cikin hannun Djinn, tun ana hango hasken har sai da ya ƙule.
Cikin tsananin fusata Djinn ya sake juyowa inda Isika yake, ya sake kai masa irin waɗannan hare-hare, jikin Isika ya sake sajewa da kalar hasken wajen ya ɓace ɓat!
Ga dukkan alamu kamar yadda Djinn ya daɗe yana yiwa Marganu shiri, haka shima Isika ya daɗe yana yi masa shiri.
Tun da dai gashi Isika yazo har gidansa, amma ya gagara yi masa komai.
Djinn ya tsaya cak! yana tunani da baƙin cikin rashin samun nasara akan Isika.
Tsayawar da yayi ne ta baiwa Isika dama, ya ɓace ya bayyana a daidai inda Marganu ke ɗaɗɗaure.
Isika ya dafa wannan hatimi na haske wanda ke kan damtsen Marganu.
Take jikin Marganu ya tarwatse ya juye izuwa ɗigo-ɗigon haske waɗanda suka zube a ƙasa, sannan suka narke a cikin ƙasa.
Djinn ya caka waɗannan takubba dake hannunsa guda biyu, ya ɗaga kansa sama ya dubi rana, ya kwarara uban ihu.
Kai, wannan ihu da aljani Djinn yake yi a wannan lokaci, yafi ƙarfin kunnuwan bil'Adama domin babu abinda za'a kwatanta shi dashi face ƙarar sauƙar aradu.
Djinn yana gama wannan ihu, ya juyo ya dubi Isika.
Idanuwansa sun juye izuwa jajazur tamkar garwashi, wani irin tiriri mai mugun zafi na fita ta hancinsa da kuma bakinsa.
Yana shirin sake afkowa Isika kenan, hannunsa na hagu ya fara yi masa ƙaiƙayi.
Cikin tsananin mamaki Djinn ya duba hannun domin ganin abinda ke faruwa.
Abin mamaki babu komai akan hannun, ga dukkan alamu wannan ƙaiƙayi daga cikin hannunsa yake fitowa.
Djinn ya zaro idanu sannan ya fara ja da baya, tamkar yana shakku akan wannan abu dake faruwa ko kuma yana kwakwanto akan anya jikinsa ne kuwa?
Duk faɗin daular ƙabilar su Djinn, ba'a taɓa jiwa ɗayansu rauni ba, basu da jini sannan basa rashin lafiya.
Indai kaga an hallaka ɗayansu, sai dai idan da ƙarfin sihiri aka yi amfani.
Kai sihirin ma, idan ba irin na daular baƙaƙen fata ba, bai cika aiki akansu sosai ba.
Saboda wannan dalili, dole Djinn ya girgiza kuma ya cika da tsananin mamaki.
Amma inda ace abun ya tsaya iya ƙaiƙayi to da sauƙi, jim kaɗan hannun nasa ya fara haske yana tartatsi.
Wani irin zogi wanda tunda Djinn yazo duniya bai taɓa ji ba, ya soma ratsa shi.
Kaɗan ya hana ya kwarara ihun wahala amma sai ya daure.
Tsahon lokaci hannun nasa yana ta haske kafun ya tarwatse yayi bindiga.
Djinn bai san sa'adda ya kwarara uban ihu ba. Hannunsa guda ya guntule ya faɗi ƙasa.
Djinn na ganin haka ransa ya ɓaci, ya ɗaga zabgegiyar ƙafarsa guda ya doki ƙasa.
Ƙasar ta rufta wani wawakeken rami ya bayyana. Djinn yayi tsalle ya faɗa cikin wannan ƙaton rami.
Ƙasar wajen ta koma ta haɗe kamar da.
Isika yayi murmushi sannan ya nemi waje ya zauna, ya ɗakko tukwanen tsumin Djinn duk ya ƙona su.
***
A wani waje a cikin wata duniya kuwa, Marganu ne kwance akan wani ƙaramin gado, yayin da wata tsaleliyar budurwa ke duba shi.
Abin mamaki Marganu yafi wata guda a cikin wannan duniya yana kwance.
Wannan duniya da Marganu yake ciki, wani yanki ne da Isika ya samar da ƙarfin ikonsa.
Wannan waje musamman Isika ya samar dashi domin yana hutawa ko kuma jinyar jikinsa, idan gumurzu bai yi masa daɗi ba.
Wannan duniya tana da bambanci sosai da ainihin duniya. A wannan duniya kwana guda daidai yake da daƙiƙa talatin na ainihin duniya.
Wannan shi ne dalilin da yasa Isika ya turo Marganu wannan duniya, domin likita ta duba lafiyarsa.
Kasancewar yayi wata guda a cikin duniyar, tuni wannan raunika da Djinn yaji masa sun gama warkewa, jikin Marganu ya dawo sumul tamkar a wannan lokaci ya fito daga gida.
A wannan rana ne, wannan likita take so ta sallame shi saboda ya gama samun sauƙi.
Marganu na kwance akan wannan gado, tunanin abubuwan da suka faru a rayuwarsa suka fara dawowa kansa.
Ya sadaukar da rayuwarsa akan samun gimbiya Jaanu, bai same ta ba.
Sarki Kuffuru ya kama shi ya kulle a kurkuku, an wulaƙanta shi.
Gimbiya Jaanu ta furta cewa bata son sa, hakan ya janyo fusatar mahaifinsa.
Sarki Kuffuru ya ɗauki gagarumar runduna, sun je sun gwabza yaƙi da mahaifinsa.
Sarki Kuffuru ya sare kan mahaifinsa sannan ya nuna masa kan don wulaƙanci.
Marganu na zuwa nan a tunaninsa ya miƙe zaune a gaggauce, sannan ya kwarara uban ihu.
Jin ihunsa yasa wannan likita rugowa da gudu domin ganin abinda ke faruwa.
Tana ganin Marganu a zaune tazo ta dafa kafaɗar sa ta ce, "Yi haƙuri, ya shugabana! Yau zaka koma ainihin duniyarku, domin kaiwa mai gidanmu ɗauki..."
Marganu na jin abinda likitar ta ce ya haɗe fuska ya ce, "Wace ce ke? Wannan wajen ina ne?"
Likitar ta risina a gaban Marganu ta ce, "Ya shugabana! Wannan waje shi ne duniyar iska wadda maigidana hadiminka Isika ya samar domin jiyyar marasa lafiyansa da kuma hutawa idan buƙatar hakan ta taso.
"Ni ce wadda keda alhaƙin kula da wannan duniya. Suna na Ailuri."
Marganu na jin wannan batu ya cika da tsananin mamaki.
Wannan wanne irin iko ne? A ce an samar da duniya wadda za'a na kula da marasa lafiya, sannan ace abokan gaba basu san da zamanta ba?
"Ailuri. Tsahon wanne lokaci na shafe a wannan wajen, kina jiyyata?" Marganu ya tambayeta.
Ailuri ta ce, "Wata guda da kwana uku!"
"Ah haba, wannan magana ne," inji Marganu. "A wannan yanayin da nake ciki, za ki ajiye ni har tsahon wata guda? Kin kyauta kuwa?"
Ailuri ta zube a gaban Marganu ta ce, "Har yanzu ana fafatawa tsakanin shugabana Isika da aljani Djinn..."
Marganu ya sake haɗe fuska ya ce, "Tsahon wata guda suna gumurzu har yanzu basu gama ba..?"
Ailuri ta sake risinawa a gabansa ta ce, "Ya shugabana! Wannan duniya tana da bambanci sosai da sauran duniya.
"Wata guda a wannan duniya, bai wuce sa'a guda na ainihin duniyarka ba."
Marganu yana jin abinda tace yayi shuru yana tunani. Tsahon lokaci kafun ya ɗago kansa ya ce, "Na samu sauƙi a yanzu, mayar da ni asalin duniyar mu..."
Ailuri tana jin abinda ya ce, ta zube ƙasa cikin biyayya. Ta taso tazo gabansa sannan ta dafa kafaɗarsa, take jikin Marganu ya sake juyewa izuwa ƙananun dunƙulen haske.
***
Isika yana zaune a cikin wannan daji kuwa, ba zato yaga daidai inda aljani Djinn ya faɗa ya fara tsatstsagewa, wani irin tiririn zafi da sanyi duk a lokaci guda na fesowa.
Jim kaɗan ƙasar wajen ta tarwatse tayi sama, siffar wani aljani ta bayyana.
Aljanin dogo ne sannan kakkaura ne. Gaba ɗaya sassan jikinsa da duwatsu aka halicce su.
Duwatsun suna bayar da launin ƙanƙara amma maimakon a ji sanyi a tattare dasu, wani irin mugun tiriri ne ke fita.
Idanuwan aljanin jajawur ne tamkar garwashi.
Yana riƙe da zabgegiyar takobi wadda aka ƙera da zallan dutse.
Wannan aljani shi ne, SARKI BUƘALSHIYYU DJINN a cikin ainihin siffarsa wadda hatta sarki Kuffuru bai taɓa ganinsa da ita ba.
Ga dukkan alamu a wannan rana, an gama fusata shi.
Isika yana ganin aljani Djinn a cikin wannan siffa, gagarumin farin ciki ya lulluɓe shi, ya fara zana ɗalasimai akan ƙasa da wannan sunduƙi dake hannunsa.
Djinn yayi ihu, duwatsun wannan daji suka amsa masa, ya falfalo da azababben gudu kan Isika.
Sawayensa suna dira akan ƙasa suna haifar da gagarumar girgiza wadda take kaɗa bishiyoyi da kogunan dake gefe.
Kafun ya iso gaban Isika, tuni Isika ya gama zana wannan ɗalasimi.
Wani irin farin haske ya fara ɓullowa daga cikin ɗalasimin, yana kashe idanun halittun dake cikin wannan daji.
Djinn yana ƙarasowa gaban Isika ya kai masa wawan sara da wannan sabuwar takobi da ya bayyana tare da ita.
Isika ya saka wannan sunduƙi nasa ya tare saran, makaman yaƙin nasu na haɗuwa a waje guda, takobin Djinn ta raba sunduƙin Isika gida biyu sannan ta wuce zata sare wuyansa.
Cikin zafin nama Isika ya ɗan goce, takobin ta sare shi a kafada.
Nan take yaji wani irin azababben nauyi ya danne shi, tamkar ƙaton tsauni guda aka aza masa.
Djinn yayi dariya ya sake amfani da hannunsa guda wanda baya riƙe da takobin, ya gabzawa Isika bahagon naushi a ƙirji.
Saboda ƙarfin wannan naushi sai da Isika yayi tsalle ya fado acan nesa.
Isika yana faɗowa ya gagara miƙewa koda zaune, saboda har a wannan lokaci wannan nauyi na ci gaba da danne shi, yana ƙoƙarin nitsar dashi ƙasa.
Djinn ya yi dariya yayi ihu, ya ɗaga kansa sama yayi kirari, ya ɗaga wannan takobi ya tunkari inda Isika ke kwance zai ƙarasa shi.
Kafun ya isa wajen ne, yaga wannan ɗalasimi wanda Isika ya zana, ya ci gaba da haske.
Siffar wani saurayi ta bayyana a saman ɗalasimin.
Saurayin yana riƙe da zabgegiyar takobi sannan babu riga a jikinsa.
Djinn yana ganin wannan saurayi ya shaida shi. Ba wani bane illa Yarima Marganu.
Marganu yana riƙe da takobin Tarwatsa-Komai ta sadauki Gayawa-Jini wadda ya ɗauko a garin Temisa.
Idanuwan Djinn suna ganin wannan takobi a fili, kansa ya fara sarawa. Kai kace ragon layya ne yayi arba da wuƙar da za'a yanka shi da ita.
Djinn ya sake kwarara uban ihu ya ruga da gudu kan Marganu, yana ɗaga wannan takobi ta dutse dake hannunsa.
Yana isowa gaban Marganu ya kaiwa Marganu wawan sara a kafaɗa.
Cikin zafin nama Marganu ya goce, to, sai dai ai wannan dama ita ce Djinn yake buƙata.
Yana ganin Marganu ya kaucewa saran takobinsa, yasa hannunsa guda ya naushi ƙirjin Marganu.
Marganu ya hantsila can baya, takobin Tarwatsa-Komai ta suɓuce daga hannunsa.
Gangar jikin Marganu tana dira a ƙasa, Djinn yayi tsalle ya caka masa takobi a gefen ƙirji.
Takobin bata gama huda jikin Marganu ba, yayi amfani da hannayensa biyu ya riƙeta.
Wani irin nauyi mai kama da sauƙar jibgegen tsauni ya sauƙo wannan waje, ya danne Marganu ya gagara motsi.
Takobin Djinn ta ci gaba da ratsa cikin ƙirjinsa tana hudawa, jini ya fara tsatstsafowa a hankali, kafun ya fara zubowa da yawa.
Saura ƙiris takobin ta gama lumewa cikin ƙirjin Marganu, aka yiwa Djinn wawan duka daga bayansa.
Duk tsananin ƙarfinsa da dakewar jikinsa, sai da yayi baya-baya kamar zai faɗi.
Aljani Isika ya bayyana a bayansa riƙe da wani sabon sunduƙi na haske.
Marganu ya miƙe tsaye cikin tsananin jarumtaka, jikinsa yana ƙyarma saboda raunin dake kan ƙirjinsa.
Marganu ya kwance wani farin yanki dake kansa, ya ɗaure ƙirjinsa dashi domin tsayar da jini.
Kafun Djinn ya gama dawowa hayyacinsa, Marganu ya falfala da azababben gudu ya ɗauko takobin Tarwatsa-Komai sannan ya juyo wajen Djinn.
Niyyarsa ita ce ya cakawa Djinn takobin kafun ya juyo.
Yana zuwa ya daka wawan tsalle ya kaiwa Djinn suka da takobin.
Saura ƙiris ta taɓa jikin Djinn, Djinn yayi wata irin juyowa cikin zafin nama ya sake cakawa Marganu wannan takobi tasa a kwiɓin cikinsa na dama.
Dama shammatar Marganu yayi domin ya yi masa irin wannan bazata.
Marganu ya faɗo ƙasa a gaban Djinn,

Please Login or Register in order to submit comment