Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

faɗo a gaban su Darwazu tamkar wadda ta suma.
"Idan kuka gama yanke hukunci, ina jiran amsar ku!" inji Ranganu.
Yana gama faɗin haka, ya koma cikin birninsa. Waɗannan masu gadi guda huɗu suka mayar da ƙofa suka rufe.
Darwazu da Hubbazu suka dubi junansu cikin tsananin mamaki.
"Wai shin mene ne asalin shirin sarki Kuffuru, me yake nufi da mu ne?" inji Darwazu.
Hubbazu yayi murmushin takaici ya ce, "Wa ya sani? Sarki Kuffuru ya turo mu wannan birni ne, domin yaga ko zamu samu nasara akan sarki Ranganu. Idan muka samu nasara akan Ranganu zai dawo mu ci gaba da tafiya, idan kuwa Ranganu ya hallaka mu. Shi kenan babu ruwansa."
Darwazu ya gyaɗa kai ya ce, "Wannan shi ne asalin yaudara kenan. Wacce shawara zamu yanke akan abinda sarki Ranganu ya ce?"
Hubbazu ya sake yin murmushin takaici ya ce, "Wacce shawara kuma zamu yanke banda mu koma da baya? Abinda sarki Kuffuru da kansa ya ji tsoro, shi ne zamu tunkara?"
Darwazu yayi gajeren tunani kafun ya gyaɗa kai, ya amince.
Nan take suka fara yiwa Rauziyya fifita domin ta farfaɗo su ci gaba da tafiya.
Tsahon ɗan lokaci suna tayi mata fifita amma ta ƙi farfaɗowa. Bayan gajeren bincike suka gano cewa, irin wannan suma ta sake yi wanda ake amfani dashi ana sanar da ita abubuwan da suke faruwa.
Jikin boka Hubbazu ya soma kyarma saboda tsananin razana. Babban abinda yake tsoro shi ne, kada Barzasa ya sanar da ita cewa, wannan jini da ta yanka masa a matsayin na Marganu ba na Marganu bane.
Shi kansa Darwazu saida ƙirjinsa ya soma dukan uku-uku saboda tsananin firgita. Shirin da suka daɗe suna yi a yanzu ya wargaje.
Hubbazu ya dubi Darwazu ya ce, "Mene ne abin yi?"
Darwazu yayi kamar bai san duk wani abu da ya faru ba. Ya ce, "Ai ba wata damuwa, dama akan jinin Marganu ne kuma mun riga da mun yanka masa!"
Hubbazu ya cije yatsa, gumi ya fara keto masa. Yana tsoron ya sanar da Darwazu yaudarar da yayi kuma Rauziyya ta farfaɗo ba magana akan abin zata yi ba. Hakan yasa yayi shuru bai sanar da Darwazu ba.
Darwazu yasan abinda ke faruwa amma ganin cewa Hubbazu bai kawo masa maganar ba, yasa shima yayi shuru. Kada Hubbazu yaga kamar yana gano sirrukansa.
Wannan shi ne babban kuskuren da Hubbazu yayi a rayuwarsa domin kuwa ya manta cewa, ƙabilar Adbenchan ƙabilar su Darwazu su ne kaɗai suke iya sarrafa su Rauziyya a duniya.
Rauziyya tayi attishawa sau uku sannan ta buɗe idanuwanta a hankali. Hubbazu ta gani ya sunkuyar da kansa ƙasa ya gagara ɗagowa yaga fuskarta.
Sarki Darwazu ne kawai yake iya ganin fuskarta.
Fuskarta ta sauya matuƙa baƙin cikin idanunta ya ƙaru ainun ya har kusa rufe cikin idanun. Gashin kanta ya koma jajawur. Fatar jikinta ta ƙara fari da duhu-duhu.
Cikin tsananin shammata Rauziyya ta zaro wata ƙatuwar wuƙa daga gadon bayanta ta cakawa Hubbazu a ƙahon zuciyarsa.
Hubbazu yayi ihu da ƙarfi sannan ya fara kakarin mutuwa, kafun a jima tuni ya riga mu gidan gaskiya.
Rauziyya ta zaro wannan wuƙa daga ƙirjinsa ta ɗagata sama zata cakawa Darwazu amma sai ta tuno sa'adda ya ceto rayuwarta, nan take ta fasa.
Darwazu ya taɓo sirrin Adbenchan ya dafa kafaɗar Rauziyya ya ce, "Mene ne abinda ke faruwa, saboda wanne dalili za ki hallaka Hubbazu?"
Babban sirri da iko yayi amfani akan Rauziyya ta ɗan nutsu ta dubi Darwazu ta ce, "Maigidana ya sanar dani cewa, wannan jini da na yanka masa ba na Marganu bane.
"Kuskuren da nayi na bashi wani jini dabam ba na ISRABIL ba, yasa yayi fushi dani. Ya bani daga nan zuwa kwanaki biyu, na nemo masa Marganu ko kuma yayi fushi dani har abada."
Darwazu yana jin haka yayi shuru yana tunani. Dama yasan dole irin haka zata iya faruwa. Wannan yasa kwata-kwata bai amince da yaudara ba.
Rauziyya ta ɗaga hannunta sama, wata sabuwar taswira ta bayyana akan hannun.
Ta warware taswirar ta nunawa Darwazu tsakiyar wani ƙaton daji wanda yayi kore. Wani ƙaramin haske jajawur aka nuno a tsakiyar dajin.
"Yanzun nan maigidana ya samar min da wannan taswira - wannan jan hasken inda ISRABIL yake kenan...
"Ya zamo dole naje wannan waje a yanzu, sannan na kama shi da rai, naje na yankawa abin bautana jininsa."
Rauziyya tana gama faɗin haka, ta bude fuka-fukinta zata tashi sama.
Cikin gaggawa Darwazu ya ce, "Dakata uwar matsafa. Duk inda za kije tare zamuje, ban bar birnina domin na koma babu komai ba. Tun da sarki Kuffuru ya yaudare mu, daga yau na ƙulla ɗamarar yaƙi dashi.
"Mu haɗa kai mu yaƙe shi sannan mu gaje daularsa."
Rauziyya tayi shuru tana tunani. Tun daga fitowarta daga gida babu wanda zata yarda dashi kamar Darwazu ya sayar da rayuwarsa ya ceci nata, sannan akwai babban sirri a jikinsa wanda yake sawa tana jin daɗin zama dashi.
Nan take ta amince da wannan shawara da yazo da ita. Rauziyya ta buɗe fuka-fukinta ta tashi sama, Darwazu ya fiddo dardumar tsafinsa ya take mata baya.
Suka ƙyale gawar Hubbazu da tarwatsatstsen jikin Infiron a wajen.
****
A can cikin wani daji kuwa, Marganu ne tare da Firziyya tafe. Ita tana zaune akan doki, shi kuma yana bisa ƙafafunsa.
A wannan rana sun shafe kwanaki uku suna tafiya a cikin wannan daji.
Jikin Firziyya wanda ya galabaita a kurkukun azaba-uku ya soma komawa kamar da.
Gimbiya Firziyya ta dubi Marganu ta ce, "Ya kai masoyina! Shin ba zaka bani labarin abubuwan da suka faru da kai, bayan wannan guguwa mai ƙarfi tayi jifa da kai ba?"
Marganu yayi murmushi ya ce, "Bayan wannan guguwa mai ƙarfi tayi jifa dani. Na tsinci kaina a cikin wani ƙasaitaccen lambu mai ban al'ajabi. A cikin wannan lambu na hadu da waɗansu irin halittu da ake kira Gorgon.
"Waɗannan halittu sun shaida min cewa, suna da babbar daula wadda al'umarsu ta mamaye, sannan babban dalilin shigowarsu cikin duniya shi ne NEMO WAYE ISRABIL.
"Bayan na tattauna da su sai muka gano cewa, ai ni ne ISRABIL ɗin wanda suka zo nema.
"A yanzu haka waɗannan halittu sun ba ni wani mudubi wanda zanyi amfani dashi nayi musu magana, a duk lokacin da naga buƙatar tafiya daularsu tazo."
Gimbiya Firziyya tayi shuru tana tunanin maganganun da Marganu ya faɗa mata.
Mahaifinta Kuffuru ya taɓa bata labarin wannan ƙabila yace yayi amfani da sunan ƙabilar ya yaudari sarki Hasanul Jalwar sa'adda yake zuwa ƙauyen Gazwar ta'addanci.
Mahaifinta ya ce mata, zamanin da wannan ƙabila take da ƙarfi sai da suka gagari kowa a duniya. Babban abinda ya ƙwaci jama'a a wancan lokaci shi ne wani ruhi mai sirrin baƙin hayaƙi.
A tsammanin Firziyya an shafe tarihin wannan ƙabila gaba ɗaya daga duniya. Bata taɓa tsammanin zasu sake wanzuwa ba.
To, amma mene ne dalilin da zai sa babbar ƙabila kamar Gorgon zata fito da kanta neman ISRABIL (Marganu)?
Wannan ita ce ta tsayawa Firziyya a rai. Don haka sai ta tambayi Marganu.
Marganu ya ce, "Idan kin taɓa jin tarihin ƙabilar Gorgon za ki ji cewa, akwai wani babban ruhi wanda ya gallabe su ya hana su sakat!
"A wancan zamani sun rasa yadda zasu yi da wannan ruhi. Ance sun yi wani gagarumin shiri irin wanda ba'a taɓa yi ba a duniya amma dukda haka basu sami nasara ba.
"Abu ɗaya ne kawai zai ƙwace su. Abu ɗaya ne kawai abinda suka yi imani dashi tun daga na farkonsu har zuwa na ƙarshensu.
"WANNAN ABU SHI NE "ISRABIL" NI KENAN. NAN GABA ZAN ZAMO BABBAN SARKI A WANCAN DAULA."
Firziyya tana jin wannan batu gagarumin farin ciki ya lulluɓeta. Idan Marganu ya zamo sarki tamkar ita ce saboda a wannan lokaci bata da wani bambanci da matarsa.
"Masoyina! Shin mene ne abinda kake jira?" ta tambaye shi.
Ka tsaye Marganu ya ce, "Ina so na sare kan sarki Kuffuru kafun nan, saboda idan Kuffuru ya samu nasarar kashe Ranganu tamkar ya kama Barban ne. Idan kuwa ya kama Barban tamkar ya mulki masarautu guda tamanin da uku ne.
"Yaƙi da sarki mai mulkin masarautu tamanin da uku, ba ƙaramin aiki bane."
Wasu hawaye suka zubowa Firziyya har ta buɗi baki zata ce wani abu, amma sai ta fasa.
Suka ci gaba da tafiya a cikin wannan daji.
Bayan kwanaki uku, suka iso wani waje mai yawan gajerun duwatsu da ƙananan bishiyoyi.
Ba su daɗe da shigowa wajen ba, Marganu ya fara ganin wadansu irin baƙaƙen shaho suna yawo a saman kansu.
Ganin haka yasa Marganu ya tsayar da dokin Firziyya sannan ya zaro wata wuƙa mai kaifi ya bata. Ya nuna mata wani kogo mai faɗi yace ta shiga ciki ta ɓuya, kada ta kuskura ta fito.
Ba tare da gardamar komai ba, Firziyya ta ruga cikin kogon ta ɓoye. Daga ciki tana hango abubuwan dake faruwa a waje.
Jim kaɗan waɗannan shaho dake shawaƙi a wajen suka soma ihu suna tashi sama suna barin nahiyar dajin.
Marganu na ganin haka ya ɗaga kansa sama, ya yi amfani da idanuwansa na haske ya hanga.
Nan take yayi arba da waɗansu mutane guda biyu a cikin gajimare suna sauƙowa ƙasa.
Kallon farko ya yiwa macen ya shaidata saboda ba zai taɓa manta wulaƙanci da barazanar da aka yi masa a birninta ba. Wanda ke tsaye a gefenta ne bai gane wane ne ba.
Marganu ya gyara tsayuwa yana jira su sauƙo.
Daƙiƙu kaɗan na shuɗewa. Sarauniya Rauziyya da sarki Darwazu suka sauƙo a cikin wannan daji.
Rauziyya tana riƙe da wannan zabgegiyar takobi wadda ta kashe Hubbazu da ita. Shi kuma Darwazu yana riƙe da zabgegiyar takobinsa.
Marganu bai taɓa ganin Rauziyya a cikin wannan shaiɗanin siffa ba.
Baƙin cikin idanunta ya kusa ya cike farin idanun. Harshen bakinta ya koma baƙi. Fatar jikinta ta sauya launi izuwa fara mai duhu-duhu.
Waɗannan idanuwa nata na tsaye cak! akan yarima Marganu tamkar an halicce su ne kawai domin neman Marganu.
Zuciyarta tana tafarfasa, jikinta yana ɓari. Kai da gani ka san cewa, a wannan rana ba zata taɓa barin Marganu ba.
Marganu ya duba gefe da gefenta sannan ya ce.
"INA SARKI KUFFURU!!!" muryarsa babu wasa ko alamun zai raga musu.
Sarauniya Rauziyya ta kwarara uban ihu ta nuna Marganu da tsinin takobinta ta ce, "Yau zan kashe ka. Yau zan ƙarasa aikin da maigidana kullum yake jira. Yau ce ranar da darajar ƙabilarmu zata ɗagu a idon duniya."
Tana gama faɗin haka ta rugo da gudu kan Marganu. Takobin dake hannunta tana kartar ƙasa tana fasa duwatsun dake can gefe.
Marganu na ganin haka ya zaro takobin tarwatsa-komai. Ya wulwula takobin a cikin iska, wasu tsaunika guda uku dake gefe suka tarwatse tamkar an fasa su da nakiya.
*****
Yau *13/05/2023*
Babi na gaba zaizo *15/03/2023* da yaddar ALLAH.RUHIN JARUMTAKA!
*
Babi na 124: *Babban Sirri*
*
Wannan littafin sadaukarwa ne ga Zahra.
*
U-M-S
*
Saboda wani dalili wanda babu wanda ya sani, Marganu baya amfani da takobinsa ta haske. Tun sa'adda ya gano cewa, shi ne ISRABIL daga wannan lokaci ya daina amfani da komai da ya shafi sirrinsa.
Rauziyya tana ƙarasowa gaban Marganu ta kai masa wawan sara da takobin hannunta.
Cikin kwanciyar hankali Marganu yasa takobinsa ya kare saran. Ta sake kai masa wani saran, ya sake karewa.
Kafun a jima ta kai masa wajen sara ashirin, duk yana tarewa da takobinsa ba tare da ya mayar da martani ba.
Cikin tsananin fusata Rauziyya ta daka tsalle baya sanna ta ƙurawa Marganu idanu cikin tsananin mamaki.
Karo na farko da ta haɗu dashi, cikin ƙanƙanin lokaci ta galabaitar da shi har tayi masa yanka masu kyau.
Amma gashi yanzu, kare kansa kawai yake ba tare mayar da martani ba, amma ta gagara yi masa komai.
Rauziyya ta ɗaga hannunta guda sama, ta karanto ɗalasiman tsafi.
Nan take wata zabgegiyar takobi ta dira a hannunta, ta haɗa takubba guda biyu ta sake rugowa kan Marganu.
A wannan lokaci ne Marganu ya motsa, suka fara azababben yaƙi.
Tana kai masa sara da suka da wadannan takubba guda biyu, shi kuma yana karewa gami da mayar da martani.
Wannan baƙuwar takobi da ta dira a hannunta ba ƙaramar hatsabibiya ba ce. Tana da tsananin nauyi fiye da tunanin mutum.
Da zarar ta kaiwa Marganu sara da wannan takobi sai wani sirri na nauyi ya sauƙa a wannan waje.
Da ƙyar Marganu yake kaucewa takobin a lokacin da nauyin yake daf da ɓaɓɓalla masa ƙasusuwa.
Ɗaya takobin dake hannunta kuwa, tana da babban sirri na kaifi. Idan aka kaiwa mutum sara da ita, koda bata sami nasarar saran jikin mutum ba, wajen da aka yi niyyar saran sai yayi alama.
Kafun a jima rigar jikin Marganu ta fara yagewa saboda sharrin wannan takobi.
Amma a duk sa'adda takobin Marganu ta haɗu da ɗaya daga cikin takubban hannun Rauziyya sai ƙara mai kama da aradu ta sauƙa a wannan waje.
Lamarin da ya fusata Rauziyya kenan, tayi wata irin alkafira tayi tsalle ta tsallake Marganu. Kafun ya juyo ta yanke shi a gadon baya.
Jini ya zubo daga gadon bayan Marganu, wani irin zogi ya ratsa shi.
Rauziyya ta caka wannan takobi nata a ƙasa, babban sirrin nauyi ya sauƙa a cikin wannan waje.
Duwatsu suka soma farfashewa. A wannan lokaci ba wai iya inda Marganu ke tsaye bane kaɗai, dukkan wannan daji ne sirrin ya shafa.
Wani irin azababben nauyi ya fara sauƙa akan Marganu. Ƙasusuwan kafaɗunsa da na gadon bayansa suka fara amsawa.
Nauyin ya fara danne shi izuwa cikin ƙasa.
Marganu ya taƙarƙare ya miƙe tsaye. Dukda cewa baya ganin abinda ke danne shi amma a haka ya cije ya ƙi yarda yayi ƙasa.
Rauziyya tayi murmushi ta fiddo fuka-fukin dake gadon bayanta, ta tashi sama tamkar tsuntsuwa tazo ta gifta ta gefen Marganu.
Tana wucewa wani lafcecen yanka ya bayyana akan damtsen Marganu, jini yayi feshi.
Wani mugun jiri ya ɗebi Marganu ya faɗi ƙasa, lamarin da yasa sirrin nauyi dake wannan waje amfani akansa kenan.
Ƙasusuwan ƙirjinsa suka soma ƙara tamkar sun kusa ɓallewa.
Jini ya fara zubowa daga bakin Marganu da kuma hancinsa.
Rauziyya tayi murmushin samun nasara, ta rugo kan Marganu ta ɗaga wannan takobi dake hannunta sama ta caka masa a ƙahon zuci.
Takobin ta nutse a cikin ƙirjin sannan ta ɓullo ta baya.
Abinda ya baiwa Rauziyya mamaki shi ne, ga shi dai takobin ta nutse a ƙirjin Marganu amma jini ko ɗigo bai fito ba.
Inda ace abin iya nan ya tsaya, to da da sauƙi. Amma take ƙarfin takobin nata ya fara kumbura yana haske kafun daga bisani ya tarwatse.
Ƙirjin Marganu ya bayyana sumul babu wani abu da ya same shi.
Rauziyya ta ja da baya cikin tsananin mamaki. Karo na farko a rayuwarta taga mutumin da takobinta ta KAIFI ta gagara yin tasiri akansa.
Babban abinda ya firgita shi ne a wannan lokaci Marganu baya cikin hayyacinsa balle a yi tunanin yayi amfani da wani ɗalasimi ya kare kansa.
Marganu da sumamme basu da wani bambanci sa'adda ta caka masa takobin.
Rauziyya ta zaro takobin-nauyi dake cikin ƙasa tayi amfani da ita ta sake cakawa Marganu.
A wannan lokaci ma, babu wani abu da ya faru. Ƙarfen takobin yayi haske ta tarwatse.
Rauziyya ta ja da baya mamaki wanda yafi na farko na shimfiɗe akan fuskarta.
Wannan takobi ta nauyi tana daga cikin manyan makaman yaƙin sarauniya Rauziyya. Mun ga yadda tayi amfani dasu a baya ta yaƙi sarki Kuffuru.
To wai shin mene ne a jikin Marganu wanda yake hana wannan takobi tasiri akansa?
Marganu ya buɗe idanuwansa a hankali sannan ya miƙe tsaye, ya tsaya cak! a gaban Rauziyya.
Rauziyya ta sake ɗaga hannunta guda sama, wata zabgegiyar takobi ta sake dira akan hannun.
Sirrin nauyi mataki na biyu ya sake sauƙa a wannan waje.
A wannan lokaci nauyin ba wai fasa abubuwan dake wajen yake ba, nutsar da abubuwan yake cikin ƙasa.
Abinda ya sake razana Rauziyya shi ne, ko kaɗan wannan nauyi baya yiwa Marganu komai.
Yana tsaye cak! tamkar babu wani abu dake sauƙa a wajen.
Rauziyya ta daka tsalle ta kai masa suka a tsakiyar ƙirjinsa.
Marganu bai motsa ba, har wannan takobi ta sake nutsewa a cikin ƙirjinsa.
Wannan sirri ya sake tarwatsa takobin. Lamarin da yasa kan sarauniya Rauziyya sarawa kenan.
Cikin gaggawa ta ja baya sannan ta ƙurawa Marganu cikin tsananin mamaki.
Babu wani sauyi akan fuskar Marganu tana nan kamar yadda ta santa.
Sai dai abinda ya tsaya mata a rai shi ne, mene ne dalilin da yasa Marganu yake tsaye cak! tamkar gunki?
Rauziyya ta daka tsalle ta gabza masa naushi da hannunta guda a ƙirji. Hannun Rauziyya ta lotsa ƙirjin Marganu ciki.
Jikin Marganu da fuskarsa bai nuna alamun yaji zafin wannan naushi ba, dukda cewa yana da ƙarfin gaske kuwa.
Tamkar mutum ya ɗaura hannunsa akan garwashi, haka Rauziyya ta janye hannunta da sauri daga jikin Marganu.
Ta sake daka tsalle ta koma baya.
Har a wannan lokaci Marganu na tsaye cak! bai motsa ba.
Rauziyya ta haɗe gira. Makaman yaƙinta ba zasu yi tasiri akansa ba. Ƙarfin damtsenta ba zaiyi tasiri akanta ba.
Ta ya ya zata gama dashi?
Bayan gajeren tunani, Rauziyya tayi irin wannan baƙin tsafi wanda ta taɓa yinsa sa'adda take fafatawa da sarki Kuffuru a cikin kurkukun-mutuwa.
Waɗansu ƙwallayen haske guda huɗu baƙaƙe suka faɗo cikin wannan daji, lamarin da yasa dajin gaba ɗaya yayi girgiza kenan, ƙura ta gauraye ko'ina.
Waɗannan baƙaƙen ƙwallaye suka haɗe a waje guda, suka bayar da siffar gunki Barzasa a gaban sarauniya Rauziyya.
Nan take ta zube a gaban wannan gunki tayi sujjada ta tsahon daƙiƙa goma kacal sannan ta miƙe.
Gunkin ya sake rikiɗewa ya koma waɗannan baƙaƙen kwallaye guda huɗu suka shige cikin jikin sarauniya Rauziyya.
Nan take ta bayyana a cikin waɗansu irin baƙaƙen tufafi masu sheƙi da walwali. Gashin kanta ya ƙara tsaho da baƙi sosai, wata irin bezar gashi ta bayyana a idonta wanda ya ƙara mata kwarjini matuƙa.
Sarauniya Rauziyya ta nuna Marganu da ɗan yatsa guda, nan take ƙananun bishiyoyin dake bayansa suka tarwatse suka zube ƙasa.
Koda ganin haka sai ta bushe da dariya ta ce, "Bani da niyyar amfani da ƙarfin jinin ƙabilata amma sai da ka kaini bango, don haka a sauƙa lafiya." Tana gama faɗin haka ta juya ɗan yatsanta, wannar baƙar guguwa ta sake bayyana ta kanannaɗe jikin Marganu sannan ta cilla sama cikin gajimare.
Sarauniya Rauziyya tayi murmushin samun nasara, ta juya da baya wajen da sarki Darwazu ke tsaye.
Cikin tsananin ɓacin rai ta tsaya cak! Tabbas tayi babban kuskure a raye take buƙatar Marganu.
Ta ya ya idanunta suka rufe zata yi amfani da babban ɗalasimi tayi jifa dashi?
Idan yaje wani wurin ya hallaka fa?
A gaggauce ta juyo wajen da Marganu yake domin ta tashi sama ta bi bayansa.
Bisa mamaki sai tayi arba da Marganu tsaye a inda yake, lafiyarsa ƙalau babu wani abu da ya same shi.
"Ƙarya ne!" inji sarauniya Rauziyya lokacin da take ja da baya cikin tsananin mamaki.
Duk faɗin ƙabilar Edwan sarauniya Rauziyya ce kaɗai take iya kiran waɗannan manya-manyan ƙwallaye guda huɗu.
Waɗannan manya-manyan ƙwallaye guda huɗu su ne asalin ƙarfin aljani Barzasa. Babu halittar da za'ayi amfani dasu akanta ba'a sami nasara ba.
Sun jarraba hakan ba sau ɗaya ba, ba sau biyu ba.
Hatta gawurtattun mutane irinsu sarki Kuffuru wannan ɗalasimi yayi tasiri akansu.
Shin mene ne sirrin da ya hana wannan ɗalasimi tasiri akan Marganu?
Wannan ita ce tambayar da ta sake tsayawa Rauziyya a rai.
A wannan lokaci Marganu ya motsa. Ya tunkaro Rauziyya.
Wani haske wanda bata taɓa kallo ba, ya soma tashi daga wannan waje.
Marganu ya zaro takobinsa ta haske, haskenta ya sake cika wannan waje gaba ɗaya.
Dukda cewa tsakiyar rana ce amma saida hasken ya ninka na da.
Sarauniya Rauziyya tana ganin haka, ƙirjinta ya soma dukan uku-uku. Ta san halittar da aka halitta da irin wannan sirri na haske.
A daidai lokacin kalmar ISRABIL ta faɗo mata.
Mene ne dalilin da yasa Barzasa ya bata umarnin nemo jinin ISRABIL?
A binciken sarauniya Rauziyya ta gano ma'anar wannan kalma guda uku.
Ma'ana na farko da na biyu ta same su a cikin tsofaffin littatafa ne. Ma'ana na uku kuma a wajen wani taƙadarin tsohon aljani ta samu.
Aljanin ya ce mata, "ISRABIL: Mutum ne wanda haske yake yawo a cikin jinin jikinsa da kuma jijiyoyinsa."
Daga ina jini yake samuwa a jikin mutum? Zuciya ce.
Kenan sirrin haske dake jikin Marganu daga zuciyarsa yake samuwa?
Rauziyya ta tambayi kanta. Nan take taga akwai buƙatar tabbatarwa.
Rauziyya ta zaro waɗannan baƙaƙen idanuwa nata, ta yiwa Marganu wani kallo.
Nan take ta kalli har can cikin ruhinsa. A gefen zuciyar Marganu tayi arba da wani abu tamkar dunƙulen zuciya amma na haske ne.
Abin yana bugawa tamkar zuciya, sannan yana furta wata kalma guda ɗaya wadda bata san abinda take cewa ba.
Kafun ta gama sauraron abinda kalmar take cewa tuni Marganu ya ƙaraso gabanta.
Bisa dole Rauziyya ta dakata sannan ta ɗaga hannayenta sama, take waɗannan takubba guda biyu suka sake dira akan hannayen nata.
Kafun Marganu ya kai mata hari ta fara kai masa sara da waɗannan takubba guda biyu.
Ɗaya a kafaɗa, ɗaya kuma a tumbi.
Marganu ko alamun kaucewa bai yi ba, har waɗannan takubba guda biyu suka ratsa shi.
Abinda ya faru daga farko dai, shi ne sake faruwa. Sirrin dake cikin jikin Marganu ya tarwatsa takubban.
Daga wannan sashe dake cikin jikin Marganu gefen zuciyarsa, wani sirrin haske ya bayyana ya taho cikin hannun Marganu wanda ke riƙe da takobi.
Sirrin haske ya haɗe da takobin hannun Marganu. Take takobin ta fara tartsatsin haske.
Marganu ya sari hannun Rauziyya

Please Login or Register in order to submit comment