Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

zata cakawa Kusuf, cikin gaggawa Jalwar ya tsitstsinke sarƙoƙin da suka ɗaɗɗaure shi sannan yayi tsalle ya shiga tsakani.
Takobin Yilan ta fasa ƙirjinsa, nan take shima ya shiga irin yanayin da Husufa ya shiga.
Sarauniya Yilan ta zare takobinta ta sake yunƙurawa zata cakawa Kusuf amma sai ta jiwo ihun Gauhan daga bayanta, yana mata nuni da ta kauce.
Cikin gaggawa sarauniya Yilan ta daka tsalle zuwa gefe, sannan ta waiwayo cikin zafin nama.
Nan take tayi arba da wani irin baƙin fai-fai mai kama da irin wannan baƙin hayaƙi dake shawaƙi a wajen.
Sarauniya Yilan tayi murmushi saboda ta san cewa, tunda wannan fai-fai bai sameta ba, zai samu waɗanda ke bayanta wato su Jalwar.
Lallai ko ma wane ne ya aiko wannan hari, baiyi la'akari da hakan ba.
Bisa mamaki taga wannan baƙin fai-fai ya juyo izuwa kanta da gudu tamkar makami mai linzami wanda indai aka harba shi dole saiya sami abin harinsa.
Sarauniya Yilan ta kaiwa fai-fan sara da Bankai 100 domin ta kare kanta.
Fai-fai kore sharr ya fice daga takobinta.
Kamar an yanka tuffa haka fai-fan Samudul Ansari ya tsarge na sarauniya Yilan sannan yayi kanta gadan-gadan zai hallaka ta.
Cikin zafin nama na gaban kwatance sarauniya Yilan ta sake daka tsalle sama ta kaucewa wannan fai-fai.
Baƙin fai-fai ya sake yiwo kwana ya juyo kanta.
Sarauniya Yilan ta tsaya cak! a inda take tsaye ta fuskanci wannan fai-fai dake tunkaro ta.
A wannan lokaci ne, sarauniya Yilan ta samu damar juyawa da baya ta yiwa wanda ya aiko mata wannan hari kyakkyawan kallo.
Samudul Ansari ta gani tsaye a cikin cikakkiyar kamala wanda bata taɓa ganin wani da rabinsa ba.
Baƙar alkyabba irinta manyan sarakunan farko ta bayyana a jikinsa. Takobin Saif-Al-Barzaƙ dake hannunsa ta juye izuwa baƙa ƙirim.
Gashin kansa ya ƙara baƙi ainun fiye da kowanne lokaci. Gashin girarsa sun ƙara yawa da kauri suna bayar da kamala.
Irin wannan baƙin hayaƙi yana ta kewaye jikinsa.
Ƙwayar idanunsa tana ci da wuta wadda take nuna alaƙar dake tsakaninsa da Nara.
Hatimai guda biyu maɗaukaka sun sake bayyana a jikinsa.
Kai, ganin Samudul Ansari a cikin wannan siffa yasa sarauniya Yilan ja da baya cikin tsananin tsorata.
Gauhan bai ma san abinda ke faruwa ba, saboda ƙarfinsa bai kai ya iya tsayawa a gaban ikon Samudul Ansari ba.
Samudul Ansari ya juya a hankali, ya yi duba izuwa inda su Jalwar suke.
Tuni ya gansu durƙushe akan gwiwowinsu, baida tabbaci akan suna raye ko sun mutu.
Cikin tsananin fusata ya dakawa sarauniya Yilan wani irin harara.
Sarauniya Yilan ta caka takobinta a cikin ƙasa, sannan ta durƙusa kan gwiwowinta ta fara karanto wasu ɗalasimaia a cikin ranta.
Faruwar hakan keda wuya, wannan waje da suke tsaye akansa ya fara komawa hazo-hazo yana ɓacewa.
Kafun daga bisani ya gama ɓacewa gaba ɗaya. Wannan koriyar duniya wadda muka ji sarauniya Yilan ta ambaceta da kaburburan kakanninsu ta maye gurbin inda suke.
A wannan waje, ga Samudul Ansari ga sarauniya Yilan. Har da su Gauhan da su Jalwar saida suka bayyana.
Amma idan Samudul Ansari zai lura dukkansu a kwakkwance suke saboda ƙarfinsu da yake raguwa a cikin wannan duniya.
Ƙarfin sarauniya Yilan ya fara yin sama, wannan waje sirri ne na ƙarfin sarakunan Gorgon.
Abinda sarauniya Yilan ta sake fuskanta shi ne, kwata-kwata a wannan lokaci babu abinda wannan waje yake yiwa Samudul Ansari.
Ƙarfinsa da ƙarfin ikonsa yana nan kamar yadda yake a wajen wannan duniya.
Sarauniya Yilan ta haɗe gira cikin tsananin mamaki.
Indai mutum da ƙarfin sihiri yake taƙama, dukkan ƙarfinsa zai ɓace a cikin wannan duniya.
Mene ne dalilin da yasa ƙarfin Samudul Ansari baya raguwa?
Shin Samudul Ansari bada ƙarfin sihiri yake aiki ba?
Canji guda da sarauniya Yilan ta gani tattare da Samudul Ansari shi ne, sauyawar ƙwayar idanunsa.
A wajen wannan duniya, idanuwansa na wuta ne amma a cikin wannan duniya sun zamo kamar yadda suke a da.
"HUKUNCIN WANDA YA TAƁA IYALAN GIDANA SHI NE: KISA!!!
"KU NISANCI WANNAN DAULA TAWA, NA FI ƘARFIN KU...
"DAGA YAU, YAƘI TSAKANINA DA KU YAZO ƘARSHE...
"ZAN SARE KANKI, SANNAN NAJE HAR DAULAR TAKU NAYI MUKU GARGAƊI...
"DUK GANGANCIN DA YASA KUKA SAKE KAWOWA DAULATA HARI, NAYI RANTSUWA DA ƘARFIN RUHINA ZAN RUGUJE DAULAR TA KU..."
Samudul Ansari ya furta waɗannan kalmomi cikin murya mai kaushi da nuna cikakken iko.
Sarauniya Yilan ta ɗaga takubbanta sama, tayi ihu ta wasa gashin kanta sannan furtawa ɗalasiman tsafi guda ashirin da shida.
Nan take tsofaffin kaburbura suka bayyana a bayanta, saboda daɗewa har wasu daga cikinsu sun fara shafewa.
Cikin zafin nama, sarauniya Yilan ta bi waɗannan kaburbura ɗaya bayan ɗaya ta caccaka takubbanta akai.
Tana kammalawa, kaburburan suka fara tsagewa, waɗanda ke kwance a cikin kaburburan suka fara fitowa.
Tun daga kan sarki na farko na wannan daula da aka taɓa binnewa har zuwa kan sarki Jiz'Ban saida suka fito.
Ba wai ruhinsu ya dawo bane, a'a, sun zo ne domin taimakawa Yilan.
Basa numfashi sannan basa motsi. Ikon wannan duniya ne kawai yake sarrafa su.
Dukkansu suna sanye da baƙin likkafani, fuskokinsu a lulluɓe da baƙin rawani.
Sarakunan suka taru a bayan sarauniya Yilan sannan suka zazzauna. Cikin haɗin murya suka fara rero ɗalasiman tsafi.
Wani hazo kore mai kaurin gaske ya bayyana a wannan waje, ya soma shiga cikin jikin Yilan.
Kan kace kobo, ƙarfinta ya fara ninkuwa sau dubu-dubu a duk bayan daƙiƙa.
Samudul Ansari yayi murmushi ya janyo baƙin hayaƙinsa cikin wannan waje, baƙin hayaƙin ya bayyana ya fara kewaye jikin Samudul Ansari yana sawa ikonsa yana buwaya.
Samudul Ansari ya ɗaga Saif-Al-Barzaƙ sama, ya tunkari inda sarauniya Yilan ke tsaye.
Sarauniya Yilan ta ɗaga takubbanta guda biyu sama, ƙarfin ikon wannan waje ya fara kwarara jikinta itama ta tunkari Samudul Ansari.
*****
Yau *20/04/2023*
Babi na gaba zaizo *22/04/2023* da yaddar ALLAH.RUHIN JARUMTAKA!
*
Babi na 114: *Shirin Samudul Ansari*
*
***TARIHIN SAMUDUL ANSARI***
*
Wannan littafin sadaukarwa ne ga Zahra...
*
BARKA DA SALLAH.
*
U-M-S
*
Samudul Ansari da sarauniya Yilan suna haɗuwa a tsakiya suka ruguntsume da azababben yaƙi, wanda yafi ƙarfin kallon idanuwan bil'adama sai dai a wassafa musu kawai.
A duk lokacin da Samudul Ansari ya kaiwa sarauniya Yilan sara da takobinsa ta Saif-Al-Barzaƙ, sai kaga baƙin hayaƙi ya tunkareta da gudu zai lulluɓeta amma sai ta gwace cikin zafin nama.
Kafun ta juyo yake sake kai mata wani saran cikin zafin nama, sannan ita kuma ta goce.
Tsahon daƙiƙu suna ta gwabza wannan gumurzu, amma ko sau ɗaya sarauniya Yilan bata sami nasarar mayar da martani ba, sai ma ƙoƙarin kare kanta kawai.
Lamarin da yayi matuƙar girgiza ta sannan ya bata tsoro kenan.
Wannan waje da suke yaƙi a cikinsa, ɓangare ne daga cikin kaburburan sarakunan daular Gorgon waɗanda suka shuɗe.
Musamman suka samar da wannan waje domin su jawo abokin gabarsu. Ikon dake wajen ya danne ƙarfin ikonsa, su sami nasarar kashe shi cikin ruwan sanyi.
Wannan waje na daga cikin manyan dalilan da suka sa, ake tsananin tsoron daular Gorgon.
Zamununnuka masu tsaho da suka shuɗe akwai manyan sarakunan da suka fi sarakunan Gorgon ƙarfi nesa ba kusa ba.
Amma saboda sirrin wannan duniya tasu, babu sarki guda ɗaya da ya tsira.
Komai ƙarfin mutum da cikar shirinsa, indai suka jawo shi cikin wannan duniya. Ta sa ta ƙare.
Ko yaro ƙarami ne a daular Gorgon yayi imani da cewa, babu ikon da zaiyi tasiri a wannan duniya idan ba Gorgon ba.
Amma mene ne dalilin da yasa ikon Samudul Ansari yake aiki a cikin wannan duniya.
Ka cire batun ƙarfin wannan duniya, akwai fa manyan sarakunan daular har mutum ashirin da shida dake zaune a bayan sarauniya Yilan suna ƙara mata ƙarfi ta hanyar karanto ɗalasimansu.
Lallai waɗannan dalilai dole su sa sarauniya Yilan ta girgiza.
Har a wannan lokaci, Gauhan da Kusuf suna can kwance a gefe suna ta minshari saboda ikon wannan duniya dake aiki akansu.
Wannan shi ne ya tabbatarwa sarauniya Yilan cewa, ikon wannan duniya fa yana aiki, domin har ta fara kwakwanton ko ya daina aiki ne.
Abinda ta fuskanta shi ne, kawai Samudul Ansari yafi ƙarfin ikon wannan duniya ne, shiyasa duniyar bata wani tasiri akansa.
Suna cikin wannan gumurzu, sarauniya Yilan ta daka tsalle baya, ta dira a tsakiyan waɗannan sarakuna guda ashirin da shida ta tsaya.
Samudul Ansari yana ganin haka, yayi guntun murmushi sannan ya koma da baya, inda su Kusuf suke kwakkwance.
Yana zuwa ya fara duba Jalwar domin ganin halin da yake ciki.
An cakawa Jalwar zabgegiyar takobi a ƙirji har ta fito ta baya. Lamarin da yasa wawakeken rami ya bayyana akan ƙirjinsa, saboda girman ramin mutum har baya zai na hangowa idan ya duba cikin ramin.
Fatar jikinsa gaba ɗaya ta koma koriya sharr. Idanuwansa suna kafe, jikinsa ya daina motsi.
Samudul Ansari baya buƙatar bayanin komai akan Jalwar. Jalwar ya riga mu gidan gaskiya.
Idanuwan Samudul Ansari suka kaɗa suka yi jawur. Ya sake wucewa kan Husufa ya duba shi, irin abinda ya faru da Jalwar shi ne ya faru da Husufa.
Cikin tsananin baƙin ciki, Samudul Ansari ya girgiza kai, sannan ya wuce kan Kusufa.
Babu abinda ya faru da Kusufa amma saboda ikon dake tasiri a cikin wannan duniya yasa ya kwanta yana ta barci.
Samudul Ansari ya dafa kansa da hannu guda, baƙin hayaƙi ya ɓulɓulo daga hannunsa sannan ya lulluɓe Kusuf.
Tsahon daƙiƙu ɗari da ashirin kacal! Kusufa ya buɗe idanunsa ya tsinci a cikin wannan duniya wadda komai nata kore ne.
Samudul Ansari yana ganin ya buɗe idanunsa ya dafa kafaɗarsa da hannu guda ya ce, "Kayi haƙuri, ɗan uwanka Husufa da Jalwar, sun riga mu gidan gaskiya.
"Ka kula da gawarwakinsu. Bari na sare kan wannan shaiɗaniyar wadda ta raba ni da 'ya'yana..!"
Samudul Ansari yana gama faɗin haka, ya taso sannan ya tunkaro inda sarauniya Yilan take.
Sarauniya Yilan tana tsaye a tsakiyar waɗannan sarakuna guda ashirin da shida. Cikin haɗin murya suna ta karanto ɗalasiman tsafi.
Abin mamaki, gangar jikin sarauniya Yilan ta sandare a tsakiyar waɗannan sarakuna tamkar ta kasance gunki wanda baya numfashi.
Ɗaya bayan ɗaya waɗannan sarakuna suka ɗinga tasowa suna shiga cikin jikinta, suna zamowa abu ɗaya.
Sannu-a-hankali har saida sarki na ƙarshe ya shiga.
Suna gama shigewa cikin jikin sarauniya Yilan tayi bindiga ta tarwatse. Wani koren haske mai ban al'ajabi ya maye gurbinta.
Hasken ya soma ɗaukar launin jikin waɗannan sarakuna, har saida yaje kan na ƙarshe sannan ya sake juyewa izuwa sarauniya Yilan.
A wannan lokaci sarauniya Yilan ta bayyana a cikin babbar siffa, tsahonta da kaurin jikinta ya ninka na da.
A da gashin kanta, macizai guda huɗu ne kacal. Amma a yanzu sun juye izuwa macizai guda ashirin da shida koraye sharr masu jajayen idanu.
Idanuwanta sun ƙara komawa kore mai duhu. Fatar jikinta ta ɗan ƙara duhu wanda ya ƙara mata kwarjini.
Takubban dake hannunta sun ƙara tsaho da kauri sun ninka na da. Wani irin hayaƙi yana ta fita daga cikinsu.
Gajimare koraye shar suka bayyana a sararin samaniyan wannan duniya. Suka yiwa sarauniya Yilan inuwa.
Iko da aminci irin na asalin Gorgon ya fara busowa.
Samudul Ansari ya nuna sarauniya Yilan da tsinin takobinsa ya ce, "Komai ƙarfin shirinki da sharrinki. Yau ce ranar mutuwar ki...
"HUKUNCIN WANDA YA TAƁA IYALAN GIDANA SHI NE: KISA!!!"
Sarauniya Yilan tayi dariya itama ta nuna shi da tsinin takubbanta ta ce, "Ba'a taɓa hukunta sarki! Duk abinda muka aikata a duniya, mun fi ƙarfin a hukunta mu...
"Da sannu zaka yi nadamar kalmomin da ka faɗa, a lokacin da nadamar ba zata yi ma amfani ba."
Samudul Ansari na jin haka ya haɗe gira, ya aikawa sarauniya Yilan saran takobi-mai-tafiya.
Ƙatoton baƙin fai-fai ya fice daga tsinin takobinsa, ya tunkari sarauniya Yilan da gudu.
A wannan lokaci, sarauniya Yilan bata kaucewa wannan baƙin fai-fai ba, sannan bata yi wani ƙoƙari na kare kanta ba.
Tsayawa tayi cak! a inda take tsaye, wannan baƙin fai-fai yazo ya dira a jikinta.
Baƙin hayaƙi ya cika wannan waje, yadda Kusuf dake can baya ya daina ganin komai.
Baƙin hayaƙin yana gama ɓacewa, aka yi arba da sarauniya Yilan tana tsaye cak! babu ko kwarzane a jikinta.
A wani salo na mayar da martani, itama ta aikowa Samudul Ansari saran Bankai-mai-tafiya.
Fai-fai kore sharr ya fice daga tsinin takobinta ya tunkaro Samudul Ansari da gudu.
Shima Samudul Ansari ya tsaya a inda yake bai motsa ba, fai-fan ya dira a jikinsa ba tare yayi masa komai ba.
Samudul Ansari da sarauniya Yilan suka fuskanci cewa, kai hari daga nesa fa babu abinda zai yi musu.
Saboda wannan dalili, suka sake rugowa da gudu kan juna suka runguntsume da azababben yaƙi fiye da tunanin Kusufa.
Saida suka kwana bakwai, suna gwabza azababben yaƙi, ba tare ɗayansu ya sami nasara ta azo a gani ba.
A cikin wadannan kwanaki bakwai, Kusufa yaga masifu da bala'i irin waɗanda bai ma taɓa tunanin zasu faru a duniya ba.
Abinda ya bashi mamaki shi ne, duk ƙarfin takubban waɗannan jarumai guda biyu da kuma hatsabibancinsu basa yiwa jaruman komai koda kuwa sun dira a jikinsu.
A ranar kwana ta bakwai ɗinne, ya ga waɗannan jarumai sun ja baya, cikin tsananin fusata.
Sai da suka shafe daƙiƙu ɗari uku da sittin suna nazarin juna, sannan suka sake falfalowa da azababben gudu kan juna.
Samudul Ansari yana wulwula Saif-Al-Barzaƙ cikin iska. Ita kuwa sarauniya Yilan tana wulwula takubbanta a cikin iska.
Koda ya rage saura taku tara kacal su haɗu, sai suka daka wawan tsalle sama.
Sarauniya Yilan ta cakawa Samudul Ansari takubbanta guda biyu a ƙirjinsa. Gagarumar ƙara ta cika wajen tamkar ƙaton ƙarfe ya haɗu da ƙaton ƙarfe.
Shima Samudul Ansari saiya caka mata takobinsa a ƙirji.
Sarauniya Yilan bata kaucewa takobin ba, saboda tana tabbaci cewa, babu abinda zata yi mata.
Sai dai takobin tana dira a ƙirjinta, taji wani irin mugun zogi ya ratsa ta. Tamkar wuta aka saka mata a wajen.
Idanuwan sarauniya Yilan suka juye daga koraye izuwa jajaye. Ta sunkuyar da kanta ƙasa tayi duba izuwa takobin da ta fasa ƙirjinta.
Nan take tayi arba da takobi jajawur a hannun Samudul Ansari.
Daga mariƙin takobin har zuwa inda ya nutse a ƙirjinta, jajawur ne tamkar garwashin wuta.
A wannan lokaci, idanuwan Samudul Ansari sun juye izuwa jajaye tamkar ƙarfen wannan takobi.
Jan hatimi wanda ke ɗauke da hoton aljani Nara nata haske da sheƙi a jikin Samudul Ansari.
Samudul Ansari ya zare takobinsa daga ƙirjin sarauniya Yilan sannan ya mayar da ita cikin kufe, ya juya ya nufi inda Kusuf ke zaune.
Samudul Ansari yana zama kusa da Kusufa, Kusufa ya dube cikin tsananin mamaki ya ce, "Ya akai haka?"
Samudul Ansari ya dube shi ya ce, "Wannan duniya da muke cikinta, wani ɓangare ne daga cikin kaburburan sarakunan daular Gorgon.
"Babu wani iko komai girmansa, komai ƙanƙatarsa da zaiyi tasiri a wannan duniya. Idan ba na Gorgon ba.
"Manyan sarakunan duniya da dama, da suka fi ƙarfin Gorgon a lokuta masu tsaho da suka shuɗe.
"Anyi amfani da wannan duniya an gama dasu. Duk wanda ya shigo cikin wannan duniya, suna karantar ƙarfinsa da kuma shirinsa.
"Hakan zai basu damar gamawa da mutum cikin ruwan sanyi...
"Sarki Azman na duniyar iska yayi tsammanin zan iya gamawa da sarauniya Yilan da takobin Saif-Al-Barzaƙ hakan yasa tunda muka rabu bai sake nema na ba.
"Amma da ya sake gudanar da wani bincike saiya gano cewa, tun da na fara yaƙi da ma'abota Bankai da Saif-Al-Barzaƙ nake yaƙi.
"Hakan zai sa su ɗauki samfurin takobin, su gudanar da bincike akanta harma su su san yadda zasu yi su kare kansu daga sharrinta.
"Wannan yasa bani kyautar aljanin-wuta wanda yake sarrafa TAKOBIN-WUTA ta sadauki Shiradu.
"Duk duniya, babu wanda ya san wannan takobi ta sadauki Shiradu. Saboda tun sa'adda aka haifi Shiradu kullum a cikin wuta yake wuni yake kwana.
"Komai bala'in mutum da hatsabibancinsa wuta tafi ƙarfinsa. Wannan yasa Azman ya haɗa ni da hadiman takobin-wuta.
"Lokaci na farko da sarauniya Yilan ta fara kawo ni cikin wannan duniya, na yaudareta ta nuna cewa, ƙarfina bai kai na iya ja da ita a cikin wannan duniya ba.
"Sannan ban taho da tau'rin ba, hakan yasa ta saki ranta har ta sami nasarar kashe ni.
"Abinda bata sani ba shi ne, ruhin da ta kashe na jikina, ba'a asalin ruhina bane. Tau'rin shi ne asalin ruhina. Saboda haka tamkar taimaka min tayi wajen dawo da ainihin ƙarfina.
"Lokaci na biyu da ta sake janyo ni cikin wannan duniya, na nuna mata ina tare da ƙarfina saboda na girgizata.
"Na ɗauke mata hankali, ta hanyar yaƙar ta da Saif-Al-Barzaƙ domin na samu damar kasheta cikin sauƙi.
"Waɗancan sarakunan da kaga sun bayyana, su ne suke karantar ƙarfin mutum sannan suyi maganinsa.
"Inda ace da iya Saif-Al-Barzaƙ kaɗai na shigo wannan waje, akwai yiwuwar mu shafe shekaru ɗari mun gwabzawa da sarauniya Yilan, saboda sun gano ƙarfin takobin kuma sun bata maganinsa.
"Saida na bari ta saki ranta, akan cewa, Saif-Al-Barzaƙ zan caka mata, na juyar da takobin izuwa SAIFUL-SHIRADU sannan na caka mata.
"Wannan takobi da na caka mata ita ce, ASALIN SAIFUL SHIRADU.
"Duk wata halitta da aka cakawa wannan takobi. Wuta zata fara ƙone komai da komai na cikin cikinta.
"Yanzu haka ƙwaƙwalwar sarauniya Yilan, zuciyarta, kayan cikinta da komai cikin jikinta yana ƙonewa da wuta.
"Kafun cikar lokaci ƙanƙani, sarauniya Yilan zata zamo tarihi.
"Ba wai ita kaɗai ba, hatta waɗannan sarakuna guda ashirin da shida suka jikinta, zasu mutu. Mutuwa ta har abada, baza su sake tasowa ba.
"Na karya ƙarfin daular Gorgon a duniya. Ba zasu sake tunanin kawowa wani waje hari ba...
"Ina ganin kamar na ramawa matata Zarifa, yayanka Jalwar da Husufa abinda aka yi musu, ko?"
Cikin tsananin mamaki, Husufa ya gyaɗa kai.
"Eh.." ya faɗa a hankali.
Cikin gaggawa ya juya inda sarauniya Yilan ke tsaye.
Nan take yayi arba da jikinta ya fara juyewa izuwa jajawur. Idanuwanta, bakinta da hancinta sai zubar da hayaƙi suke.
Ta gagara zaune ko tsaye, wani lokacin tayi tsalle ta rusa ihu. Wani lokaci ta durƙushe ta shaƙe wuyanta tana ta kakari.
Waɗannan korayen gajimare da suka wajen ɗazu, suka fara haɗewa a waje guda suna komawa hadari.
Kafun a jima aka tsuge da ruwan sama mai ban al'ajabi.
Gaba ɗaya ruwan kore ne shar, sannan baya sauƙa a ko'ina idan ba jikin sarauniya Yilan ba.
Wannan sabon ruwan sama, yasa wutar dake ci a cikin gangar jikin sarauniya Yilan mutuwa. Amma kafun nan tuni wutar ta gama yin tasiri akanta.
Saboda tsananin yadda wannan wuta ta gama cinye jikin sarauniya Yilan, ko miƙewa tsaye bata iya yi.
Tana durƙushe akan gwiwowinta, wani irin mugun zogi na ratsa ta.
Tsahon daƙiƙu goma sha biyar kacal! aka ɗauke wannan ruwan sama da ake.
Sai dai idan ka dubi sakamakon abinda ya faru bayan wannan ruwan sama, zaka ce baida wani amfani.
Anyi wannan ruwa ne domin a karya ikon Shiradu dake tasiri a cikin jikin sarauniya Yilan.
Amma kafun a yi wannan ruwa, tuni Shiradu ta gama tasiri a jikinta.
Babu abinda sarauniya Yilan zata iya taɓukawa a wannan lokaci. Ƙarshenta yazo.
"KODA KUN SAMI NASARAR HALLAKA NI...
"KU SAURARI ZUWAN "ISRABIL"!!!" inji sarauniya Yilan.
Samudul Ansari yayi murmushi ya baiwa Kusufa takobin Saiful-Shiradu ya ce, yaje ya sare kan sarauniya Yilan da ita.
Cikin gaggawa Kusufa ya karɓi takobin, sannan ya tunkari inda sarauniya Yilan ke durƙushe. Yana tafe yana sassarfa, Saiful-Shiradu tana kallon ƙasa.
Kusufa yana zuwa gaban Yilan ya tuno irin yadda ta kashe masa ƴan-uwa har guda biyu a gaban idanunsa.
Cikin tsananin fusata yasa takobin Saiful-Shiradu ya sare kanta.
Takobin ta datse wuyanta, dungulmin kanta yayi tsalle ya faɗi gefe.
Macizan dake kanta suka fara ihu, kafun daga bisani suyi shuru su mutu su ma.
"Ɗakko kanta," inji Samudul Ansari.
Kusufa yasa hannunsa guda ya ɗauki kan nata sannan ya juyo izuwa inda Samudul Ansari.
Kafun ya iso inda Samudul Ansari ke tsaye, wannan duniya da suke cikinta ta fara hazo-hazo tana ɓacewa.
Nan take ƙofar birnin Shaha ta maye gurbin wannan duniya.
Gawarwakin dakarun Samudul Ansari da BES suka karkashe suka bayyana a kwakkwance.
Gawar Jalwar da ta Husufa ta bayyana a wannan waje a kwance.
Amma babu gawar sarauniya Yilan babu alamunta. Sai dai dungulmin kanta yana hannun Kusufa.
Samudul Ansari ya dafa kafaɗar Kusufa ya ce, "Mun yi nasara, aiki guda ya rage mana a yanzu."
Kusufa ya ce, "Me kenan?"
Kafun Samudul Ansari ya bashi amsa, suka ji an buɗe ƙofar birnin Shaha.
Cikin gaggawa suka duba, nan take suka yi arba da sarauniya Arya tare da dakaru mutum ɗari.
*****
Yau *22/04/2023*
Babi na gaba zaizo *24/04/2023* da yaddar ALLAH.RUHIN JARUMTAKA!
*
Babi na 115: *Sadaukarwar Samudul Ansari*
*
***TARIHIN SAMUDUL ANSARI***
*
Wannan

Please Login or Register in order to submit comment