Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

wani irin rami zururu ya bayyana akan cikinsa wanda kaɗan ya hana a hango kayan cikinsa.
Djinn yana ƙoƙarin ƙarasa Marganu kenan, ya tuno cewa Isika ya daɗe da farfaɗowa kuma zai iya kawo masa hari a kowanne lokaci.
Djinn ya ayyana a ransa, ƙarshen Marganu yazo. Babu yadda za'a yi Marganu ya rayu da waɗannan mahaukatan raunika dake jikinsa balle har ya taɓuka wani abu a wannan yaƙi.
Don haka sai ya juya wajen Isika domin shima ya ƙarashi.
Ai kuwa yana juyawa yaga ƙiris ya hana sunduƙin Isika ya huda shi.
Kafun ya kauce ko kuma yayi wani motsi tuni wannan sunduƙi ya caki jikinsa.
Maimakon sunduƙin ya ji masa rauni, kawai gani aka yi ya tarwatse ya bi iska.
Cikin zafin nama Djinn ya ɗaga wannan takobi tasa ya yiwa Isika wawan sara a kafaɗa.
Irin wannan nauyi ya sake danne Isika ya ɓalla ƙasusuwan kafaɗunsa.
Isika ya kurma uban ihu, sannan ya durƙushe akan gwiwowinsa a gaban Djinn.
Djinn yana ƙoƙarin sare kansa kenan, yaji an caka masa wata irin takobi a gadon baya.
Gangar jikin Djinn gaba ɗaya ta soma tsatstsagewa tana kumbura. Wata irin iska mai ƙarfin gaske ta soma fitowa daga cikin jikinsa.
Djinn ya fara kwarara uban ihu saboda ya tabbatar da cewa lallai ƙarshen sa yazo. An sare shi da takobin da musamman domin shi aka ƙirƙire ta.
Dukda haka sai da Djinn ya dage, ya waiwaya da baya domin ganin wanda ya sare shi.
Marganu ya gani durƙushe kan gwiwowinsa saboda jirin dake ɗibansa. Ya caka takobin Tarwatsa-Komai a cikin ƙasa domin ta tallafe shi, kada ya bingire ƙasa.
Tsahon rabin sa'a kacal! jikin Djinn ya ɗauka yana tsatstsagewa kafun ya fara bindiga yana rushewa.
Djinn ya ci gaba da kwarara uban ihu, jikinsa yana rushewa a hankali, har ya gama tarwatsewa gaba ɗaya.
Yana gama rushewa wannan daji gaba ɗaya yayi wata irin girgiza, iska mai ƙarfi tayi jifa da Marganu da kuma Isika can nesa da cikin dajin.
Sai bayan kimanin sa'a guda sannan Marganu da Isika suka dawo hayyacinsu.
Marganu ko motsawa baya iya yi, saboda yawan jinin da ya zuba daga jikinsa.
Cikin gaggawa Isika ya dafa shi suka ɓace ɓat!
A cikin duniyar Isika suka bayyana wajen likita Ailuri.
Cikin gaggawa Ailuri ta kwantar da Marganu kan wannan gado sannan ta fara duba shi.
****
Yau *29/04/2023*
Babi na gaba zaizo *01/05/2023* da yaddar ALLAH.RUHIN JARUMTAKA!
*
Babi na 118: *Sirrin ISRABIL*
*
Wannan littafin sadaukarwa ne ga Zahra...
*
U-M-S
*
Saida Marganu da Isika suka shafe watanni uku cir suna jiyyar raunikan da aljani Djinn yaji musu sannan suka warke.
Marganu ya baiwa Isika umarnin fitowa daga cikin wannan duniya tasa. Nan take kuwa suka fito daga cikin wannan duniya, suka bayyana a cikin wani ƙaton daji.
Marganu da Isika suka koma gindin wata bishiya suka zauna domin su tattauna.
"Cikin ayyuka guda biyu da na faɗa maka kwanaki, yanzu mun gama da guda ɗaya. Saura guda ɗaya. A wannan lokaci yana da kyau muje kurkukun AZABA-UKU mu kuɓutar da Firziyya..." inji Isika.
Marganu ya gyaɗa kai ya ce, "Haka ne. Amma ta ya ya aka yi sarki Kuffuru yake samar da mutum-mutumi masu kama da shi sak?"
Isika ya dubi Marganu ya ce, "Sarki Kuffuru ya mallaki wata takobi wadda aljani Djinn ya samar masa. Sarki Kuffuru ya kira wannan takobi da suna SIWOD-DEL-BULOD!
"Takobin Siwod-del-bulod daga jini kala uku aka ƙirƙire ta.
"Jinin ingarmun zakuna guda goma.
"Jinin zaratan sadaukai guda goma.
"Jinin shaiɗanun aljanu guda goma.
"Kasancewar an haɗa wannan takobi da kalolin jini guda talatin yasa take iya samar da halittu guda talatin.
"Ingarmun zakuna guda goma. Zaratan sadaukai guda goma. Hatsabiban aljanu guda goma. Waɗannan su ne abubuwan dake cikin wannan takobi.
"Waɗannan zakuna da hatsabiban aljanu basu da wani asali, zaka iya cewa kawai ƙirƙirarsu aka yi.
"Sadaukan bil'adaman ne suke da asali da kuma tarihi. Kimanin shekaru talatin da uku da suka shuɗe na kaiwa Samazan ziyara mun tattauna akan batun ahalin Infiron."
Marganu yana jin abinda Isika ya ce ya gyara zama domin sauraron wannan bayani nasa cikin nutsuwa.
A halin da ake ciki a yanzu, sarki Kuffuru kaɗai ya rage masa. Yana gamawa da sarki Kuffuru zai tafi daular Gorgon domin taka babban matsayinsa na ISRABIL.
Marganu yasan cewa, sarki Kuffuru ba kanwar lasa bane, saboda haka dole sai an shirya masa.
Sarki Kuffuru baya taƙama da komai face Djinn da kuma Infiron (a ɓangaren tsafi.)
Isika ya ci gaba da jawabi, "Infiron wani gawurtaccen sadauki ne a birnin Denziya. Kwata-kwata Infiron ya saɓawa ƙa'ida. Tsafi ko kaɗan baya tasiri akansa.
"Babu abinda Infiron ya yarda da shi a rayuwarsa kamar jarumtaka. Wannan yasa ya ƙarar da rayuwarsa gaba ɗaya wajen kimtsa kansa da jarumtaka.
"Infiron ya sami nasara domin kuwa saida ya gagara a zamaninsa saboda tsananin sadaukantarsa.
"Sa'adda Djnn yazo samar da takobin Siwod-del-bulod yayi amfani da hikimomi guda uku. Wannan yasa ya ɗebi jinin halittu jinsi guda uku.
"Abinda yasa aka yi amfani da jinin dabbobi wajen samar da wannan takobi shi ne, saboda duk duniya babu abinda ya kai dabbobi juriya.
"Kaga kenan duk wanda keda wannan takobi zaiyi juriya fiye da tunanin mutum.
"Abinda yasa aka yi amfani da jinin aljanu kuwa shi ne, ka san duk duniya babu abinda ya kai aljanu iya sarrafa tsafi. Hakan ne yasa sa'adda sarki Kuffuru ya mallaki wannan takobi kimarsa a ɓangaren tsafi ta bunƙasa ainun.
"Sannan abinda yasa aka yi amfani da jinin Infiron kuwa, babu halittun da suka kaisu jarumtaka da ƙarfin damtse (idan ka cire tau'rin).
"Wannan yasa sarki Kuffuru ya zamo cikakken hatsabibi."
Isika ya yi gyaran murya sannan ya ci gaba da baiwa Marganu labari.
"Aljani Djinn yana da tsananin hikima yasan cewa, nan gaba abubuwa zasu taru su yiwa sarki Kuffuru yawa. Wannan yasa ya saka wani ɗalasimi a jikin waɗannan halittu [Infiron] wanda yake sa wa suna juyewa izuwa kamannin sarki Kuffuru.
"Watannin da suka wuce, nayi bincike akan halin da su sarki Kuffuru ke ciki. Sai na fuskanci cewa, sarki Kuffuru ya juyar da waɗannan halittu guda goma izuwa siffofi masu kama da nasa.
"Ya tura guda ɗaya izuwa birninsa domin ya ci gaba da tafiyar da harkokin mulki kamar shi.
"Ya tura guda ɗaya farautar sarki Ayubu wanda har a wannan lokaci, ba'a ma san ina yake ba.
"Sannan ya turo guda farautarka. Wannan wanda kuka gwabza yaƙi dashi har guguwa mai ƙarfi tayi jifa da kai lambun su Ileisha Gorgon."
Marganu yana jin wannan batu yayi shuru yana tunani. Daga can ya ɗago kai ya dubi Isika ya ce.
"Idan har hatsabibancin sarki Kuffuru ya kai haka, ta ya ya zamu iya shaida shi idan muka je kashe shi? Kada ya bar mutum-mutumi su sake kiran wannan ɗalasimi nasu yayi jifa damu uwa-duniya."
Isika ya ce, "Hakane. Mutum ɗaya ce kawai zata iya shaida mana wanda zamu je yaƙa, asalin sarki Kuffuru ne ko kuma saɓanin haka - ina nufin masoyiyarka Firziyya."
Marganu ya ce, "Motsin mu na gaba kuɓutar da Firziyya daga kurkuku ne. Muna kuɓutar da ita zamu nemi inda sarki Kuffuru yake domin mu hallaka shi..."
Isika ya ce, "Haka ne..."
Marganu ya dubi Isika ya ce, "Ina so ka samo mini ingarman doki, nayi tafiya akansa naje kurkukun azaba-uku, na kuɓutar da masoyiyata."
Cikin tsananin mamaki Isika ya dube shi ya ce, "Ya shugabana, saboda wanne dalili zaka yi tafiya akan doki, alhalin zamu iya zuwa wannan kurkuku a cikin mako guda?"
"Saboda ina so na sake baiwa kaina horon yaƙi ne akan arnan-dajin dake kan hanya da kuma muggan dabbobi." inji Marganu.
Isika ya yi dariya ya ce, "Banda baiwa kanka horo sai dai koya musu hankali dai. Duk jarumtakarka da sadaukantarka ace akwai arnan-daji ko kuma dabbobin da zasu baka tsoro?"
Marganu ya ce, "Koma dai mene ne, akan doki nake so nayi wannan tafiya..."
Bayan ɗan lokaci suna tattaunawa, Isika ya juye izuwa siffar wani tsofo ya shiga wani ƙaramin ƙauye dake kusa dasu, ya sayo doki ya kawowa Marganu.
Marganu ya karɓi wannan ingarman doki ya hau kansa, sannan ya tunkari hanyar da zata kaishi inda aka gina kurkukun Azaba-Uku.
****
Zaune take a cikin wani ƙaramin ɗaki ta sunkuyar da kanta ƙasa tana kuka.
Budurwa ce kyakkyawa musamman idan kayi duba izuwa fuskarta. Dukda cewa jikinta yasha wahala sosai amma fuskarta na nan da asalin kyawunta.
Kayayyakin jikinta sun yi dotti sosai sannan sun yayyage.
Wannan budurwa ta rame sosai, sakamakon yunwar dake damunta.
Kana ganin yanayin wannan ɗaki, zaka gane cewa gidan kurkuku ne. Saboda akwai ƙarafu masu kaurin gaske da suka yi masa raga-raga.
Idan mutum ya samu dama ya matsa kusa da wannan budurwa dake faman kuka zai gane cewa, ba wata bace illa masoyiyar yarima Marganu. Firziyya 'yar sarki Kuffuru.
Wannan kurkuku da aka kulleta a ciki ita ce kurkukun azaba-uku wadda aljani Duksum ke sha'aninsa a ciki.
Tun daga ranar da sarki Kuffuru ya kawota cikin wannan kurkuku take ta faman rusa kuka.
A kullum sai aljani Duksum ya gana mata azabobi kala dabam-dabam.
Bata samun wadataccen abinci a cikin wannan kurkuku. Barci baya isarta. Suturar da aka kawota wannan kurkuku tun daga ranar farko, har a wannan rana su ne a jikinta.
Rayuwar duniya ta gama yiwa Firziyya zafi, ta ji babu abinda take ƙauna a duniya kamar mutuwa.
Musamman idan ta tuno kalaman sarki Kuffuru da yake cewa, "Mun halaka mahaifin Marganu sannan mun halaka Marganun ma."
Sau da dama Firziyya ta sha yunƙurin kashe kanta, saboda taje ta riski Marganu a duniyar da yake. Amma bata samun dama saboda a kullum a ɗaɗɗaure take.
Wannan kuka da Firziyya take yawan yi, ba wai na zafin azabar da ake yi mata bane.
Abinda yasa take yawan kuka shi ne, tasan cewa Marganu baya raye. Idan babu Marganu a duniya, mene ne amfanin rayuwarta?
Kullum Firziyya bata da buri wanda yafi a ce sarki Kuffuru ya dawo wannan kurkuku ya sare kanta, ita dai kawai taje ta riski Marganu.
A wannan rana, an shafe kwanaki uku cir Duksum bai yi mata komai ba.
Duk tsananin rashin imaninsa da baƙin zaluncinsa, ba'a taɓa kawo masa fursuna mace ba.
Duksum ya gana mata azabobi kala daban-daban har ya gaji. Tun tana kuka sakamakon azabar da ake yi mata har ta saba.
Duksum yana zaune a cikin wani ƙaramin ɗaki dake ƙofar shigowa wannan kurkuku, abin mamaki, waɗansu ƙarafu yake gasawa a cikin wuta.
Ashe tsahon kwanaki ukun da yayi baya gana mata azaba, waɗannan ƙarafu yake gasawa a cikin wuta.
A kullum sai ya tsoma waɗannan ƙarafu a cikin wuta, idan suka yi jajazur sai ya fiddo su ya saka su wani jan tsumi.
Washe gari ma ya sake yin haka.
Niyyar Duksum ita ce ya yiwa Firziyya azaba ta ƙarshe wadda zata ga bayanta ya daina kallonta. Idan yaso in sarki Kuffuru ya tambaye shi, ina take yace azabobin da yake yi mata ne suka kashe ta.
Waɗannan ƙarafu Duksum bai taɓa yiwa wani fursuna azaba da su ba, sannan yana da tabbaci cewa, duk fursunan da ya yiwa azaba da waɗannan ƙarafu saiya mutu.
Ana so ya kwana bakwai yana tsuma waɗannan ƙarafu, kafun yayi aiki dasu.
Ranar da waɗannan ƙarafu suka cika kwanaki bakwai Duksum yana gasa su a cikin wannan wuta nasa, sai ya fiddo su daga cikin wannan jan tsumi, sannan ya fito daga cikin ɗakinsa.
Duksum ya tunkari ɗakin da Firziyya ke zaune yana murmushin mugunta.
Saura taku goma kacal ya isa ƙofar shiga wannan ɗaki, ya tsaya cak yayi shuru ya kasa kunnuwa domin sauraron ƙarar da ya ɗan jiwo.
Abin mamaki kunnuwansa suka jiwo masa ƙarar kofaton doki a can ƙarƙashin tsaunin.
Da farko yayi tunanin ko kunnuwansa ne suke yaudararsa, don haka ya sake saurarawa da kyau. Ya tabbatar da cewa lallai ƙaran kofato ne.
Duksum yayi murmushi ya juya da baya ya nufi wata matattakalar bene da aka gina domin sauƙa daga saman wannan tsauni.
Duksum ya fara tattaka matattakalar yana sauƙowa daga saman tsaunin.
Tun kafun ya sauƙo ya ƙurawa ƙasan tsaunin domin ganin baƙon mahayin da yazo.
Wani jarumi ya hango zaune akan wani ingarman doki. Kallon farko Duksum ya yiwa wannan jarumi ya gane wane ne.
Cikin gaggawa Duksum ya rugo daga saman wannan matattakala ya sauƙo ƙasa, ya tsaya a gaban wannan jarumi.
Jarumin ya ɗago kansa a hankali ya yiwa wannan aljani kallon nutsuwa.
Kamar yadda kowa zaiyi tsammani wannan jarumi ba kowa bane illa Marganu.
Marganu da Duksum suka fara kallon-kallo.
Marganu ya dube shi a hasale ya ce, "Ka wulaƙanta ni, kayi min azaba. Kuma don rashin mutunci abin bai tsaya iya kaina ba, har kan matar da zan aura zai tsallako?"
Duksum yayi dariyar takaici ya cije yatsa ya ce, "Wai dama kana raye? Ai dama haushi nake ji da sarki Kuffuru bai ƙyale ni na hallaka ka ba. Saboda babu wanda ya taɓa shiga hannuna ya tsira da rayuwarsa.
"Kaga yanzu ka kawo min kanka, zan ƙarasa abinda na fara... Yau zan kashe ka sannan na kashe wannan budurwa wadda kazo ceto."
Marganu ya murtuƙe fuska ya zaro takobinsa ya ce, "Yau zan ɗauki fansar wulaƙancin da kayi min. Yau ce rana ta ƙarshe a baƙin zaluncinka. Yau zaka zamo tarihi..."
Duksum yana jin abinda Marganu ya ce wadannan gangunan jiki nasa guda uku, dukkansu suka zaro takubba.
Dukkansu suka kwarara uban ihu a tare, cikin haɗin murya sannan suka tunkari inda Marganu ke tsaye.
Marganu na ganin haka ya sauƙo daga wannan doki nasa, sannan shima ya tunkari Duksum.
A wannan rana Marganu ba takobin haske ko takobin tarwatsa-komai ya fiddo. Wata zabgegiyar takobi ce mai girma da nauyin gaske wadda babu ko alamun sihiri a jikinta.
Marganu da Duksum suna haɗuwa a tsakiya suka ruguntsume da azababben yaƙi mai ban tsoro.
Duksum yana wanzu yana kawowa Marganu muggan sara da suka da waɗannan gangunan jiki guda uku nasa.
Shi kuma Marganu saiya wanzu yana karewa gami da mayar da martani.
Tabbas Marganu ya cika mai mugun zafin nama, domin tamkar da halittu guda uku yake yaƙi.
Waɗannan gangunan jiki guda uku na Duksum suna iya kai masa hare-hare guda uku a lokaci guda.
Cikin zafin nama Marganu yake gocewa wasu saran sannan ya kare wasu da takobinsa.
Suka ci gaba da gumurzu har tsahon rabin sa'a, ba tare da ɗayansu ya samu wata nasara ta azo a gani.
Amma Marganu ya soma gajiya, saboda tamkar da aljanu guda uku yake yaƙi a lokaci guda.
Biyu daga cikin gangunan jikin Duksum suka mayar da takubbansu cikin kufe, suka dunƙule hannayensu suka sake rugowa kan Marganu.
A wannan lokaci sai suka canja dabarar yaƙi. Biyu suna kawo masa duka da naushi, daya kuwa yana kawo masa sara da suka da takobi.
Nan da nan suka fara gigita Marganu, ya rasa ta ya ya zai fara yaƙar su.
Kafun a jima sun samun nasarar taɓa shi. Gangar jiki guda ɗaya ta kawo masa sara, yasa takobinsa ya kare, ɗan tsayawar da yayi ya baiwa gangunan jiki guda biyun dama suka doke shi.
Saboda ƙarfin naushinsu, saida Marganu yayi sama ya faɗo acan baya.
Gangunan jikin guda uku suka bushe da dariya a lokaci, suka sake falfalowa da gudu kan Marganu.
Marganu ya miƙe tsaye ya daɗa damƙe takobinsa da kyau. Zuciyarsa ta fara tafarfasa tana daka masa tsawa.
"Kaine ISRABIL!
"Mayaƙin da babu kamar sa a duniya kake da burin kashewa!
"Ya ya ƙananun halittu zasu tsaya ɓata maka lokaci?"
Marganu ya sake fusata. Duksum yana ƙarasowa gabansa, Marganu ya goce cikin zafin nama yai tsalle ya dira a bayan aljanin.
Kafun aljanin ya juyo Marganu yasa takobinsa ya sare kansa guda ɗaya.
Duksum ya kwarara uban ihu da sauran kawunan nasa guda biyu, cikin zafin nama suka sake dukan ƙirjin Marganu da ƙarfi.
Marganu ya sake tsalle baya ya gwaru da wannan ƙaton tsauni. Bakinsa ya fashe.
A fusace ya sake rugowa da gudu kan Duksum. Shima Duksum saiya rugo da gudu kansa.
Koda ya rage baifi taku uku su haɗu sai Duksum ya daka tsalle sama, Marganu yayi kamar shima zaiyi tsalle amma saiya turje ya tafi a ƙasa.
Duksum ya wuce ta saman kansa.
Duksum yana dira a ƙasa kayan cikin gangar jikin nasa guda ɗaya ma suka fara zazzagowa ƙasa. Kan kace kobo gangunan jiki guda biyu sun daina aiki.
Duksum ya rugo da gudu kan Marganu. A wannan lokaci wadannan gangunan jiki nasa da Marganu ya kashe sai suka zamo masa kaya, suka fara hana shi motsi sosai.
Marganu ya tsaya cak bai sake wani motsi ba, ya ɗaga takobinsa sama ta tsaya a cikin iska.
Duksum yana zuwa gaban Marganu ya kawo masa wawan sara da takobinsa.
Marganu ya tsaya cak bai motsa ba. Takobin Duksum ta sari jikinsa ta wuce tamkar haske ta ratsa.
Mutum zai yi matuƙar mamaki idan yaga hakan, saboda a wannan lokaci Marganu bai juyar da jikinsa izuwa haske ba.
To, ya ya aka yi takobin Duksum ta ratsa ta cikin jikinsa tamkar haske?
A fusace Duksum ya ja baya tamkar zaki, ya dako wani wawan tsalle sama. Ya buɗe hannayensa biyu, fankacecen ƙirjinsa ya bayyana.
Niyyar Duksum ita ce yayi amfani da wannan ƙaton ƙirji nasa ya doke Marganu.
Saboda yasan cewa, ƙarfin ƙirjinsa yafi na zaki. Indai ƙirjinsa ya haɗu da na Marganu saiya kakkarya ƙasusuwan Marganu.
Bisa mamaki sai Duksum yaji jikinsa ya sake wucewa ta cikin jikin Marganu tamkar haske ya ratsa.
Duksum ya dira a bayan Marganu, ya tsaya cikin tsananin mamaki.
Komai ƙarfinka da ƙarfin damtsenka ba zaka taɓa samun nasara akan hoto ba. Saboda a wannan lokaci babu abinda zai kwakwanta Marganu dashi kamar hoto.
Ga shi dai Marganu na tsaye a wannan waje, amma bai isa yayi masa komai ba.
Inda ace abin ya tsaya iya mamaki to da sauƙi. A daidai lokacin ruhin Duksum ya soma tsatstagewa yana shirin tarwatsewa.
Jini ya soma zubowa ta cikin kunnuwan Duksum, hancinsa, bakinsa kai har ta cikin idanuwansa.
Bisa dole ya durƙushe kan gwiwowinsa saboda mugun jirin dake ɗibarsa.
Duksum ya kalli Marganu fuskarsa cike da tsananin mamakin, wanne irin hari Marganu yayi amfani dashi akansa.
Harin bai taɓa jikinsa ba. Zaka iya cewa kai tsaye kawai ruhinsa aka kaiwa harin.
Ta ya ya aka yi Marganu yayi arba da ruhinsa harma ya farmake shi?
Sai dai idan Duksum zai sami damar karantar fuskar Marganu zai ga cewa, shima tsananin mamaki yake akan wannan abu da ya faru.
Kafun Duksum ya samu dama ya buɗe bakinsa ya ce wani abu. Tuni ruhinsa ya tarwatse.
Gagarumar ƙara mai cika kunne ta sauƙa a wannan daji. Bishiyoyi da duwatsu suka yi girgiza.
"SIRRIN ISRABIL!"
Marganu yaji wata murya ta furta waɗannan kalmomi, amma bai san daga ina take ba. Daga kowacce ƙusurwa yaji amsa kuwwar muryar don haka baisan ta ina zai fara neman mai muryar ba.
Shi kansa Marganu ya cika da tsananin mamaki domin kuwa sa'adda ya tsaya ɗinnan, niyyarsa ita ce Duksum yana ƙarasowa gabansa zai goce cikin zafin nama ya sare shi.
Amma sai yaji jikinsa ya ƙi bin umarnin, dole ya tsaya takobin Duksum ta sare shi, bisa mamaki yaga bata yi masa komai ba.
Lokacin da Duksum ya wuce ta cikin jikinsa kamar ratsawar haske, yaji wani abu a tsakiyar ƙirjinsa ya ɗau zafi. Da farko yayi tunanin zuciyarsa ne amma da ya nutsu sai yaji sam ba ita bace.
Wani abu ne dabam wanda bai san mene ne ba. Kuma a tunaninsa wannan abu da ya ɗauki zafi shi ne ya tarwatsa ruhin Duksum.
Marganu yaga cewa, tsayawa yayi tunani akan wannan abu ba zai sa ya gane komai ba. Dole yana buƙatar wanda yasan abin sosai, indai yana so ya gane abubuwan dake faruwa.
Marganu ya mayar da takobinsa cikin kufe, ya tattaka matattakalar nan ya hau saman wannan tsauni.
Yana hawowa saman tsaunin, ya shige cikin wannan kurkuku.
Kurkukun tana nan kamar yadda ya santa. Ƙarama ce sosai don kwata-kwata bai wuce ɗakunan fursunoni ashirin da biyar ne kaɗai a cikinta ba.
Marganu ya bi waɗannan ɗakuna ɗaya-bayan-ɗaya yana buɗe su, yana neman Firziyya.
Duk ɗakin da ya buɗe idan yaga ba Firziyya bace a ciki, saiya sallami fursunan dake cikin ɗakin.
Kafun a jima tuni Marganu ya sallami dukkan fursunonin da aka kulle a cikin wannan kurkuku.
Yana zuwa ƙofar ɗaki na ƙarshe ya tsaya cak! wannan ɗaki a ciki aka kulle shi sa'adda aka kawo shi wannan kurkuku.
Kuma wannan ɗaki a cikinsa ne ya binne dungulmin kan mahaifinsa sarki Ratanam wanda sarki Kuffuru ya nuna masa.
Zuciyar Marganu ta soma tafarfasa kamar zata ƙone saboda tuno wannan abin baƙin ciki da ya faru dashi.
Marganu yasa hannayensa biyu ya finciko wadannan manyan ƙarafu waɗanda suka yiwa ɗakin da aka kulle Firziyya a ciki raga.
Damatsan Marganu suka kumburo, jijiyoyi suka yi burɗin-burɗin.
A hankali ya finciko ƙarafunan. Ƙaramin

Please Login or Register in order to submit comment