Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Har suka ƙarasa babbar fadar ƙasar wadda suka isketa ta cika maƙil da tarin mutane.
Dukkan jama'ar dake zaune a cikin wannan fada, suka zaro idanu cikin tsananin mamaki saboda ganin tsantsar kyawun gimbiya Jaanu.
Tsahon daƙiƙu masu yawa, fadar tayi tsit ana mamakin kallon gimbiya Jaanu.
Aymanul Faris da matarsa Jaanu suka ƙarasa a hankali kan karagar mulki, suka zauna a tare sannan suka fuskanci jama'a.
Kafun a fara tafiyar da harkokin mulki, wani dattijon mutum tuƙuf ya shigo cikin fadar.
Saboda tsananin yadda ya tsufa har wani ƙusumbi ne a gadon bayansa, wanda ya sa ya sunkuya tamkar mai ruku'u.
Abin mamaki dakarun dake tsaron wannan fada, sun yi ƙoƙarin dakatar dashi amma yana ɗaga idanunsa yana kallonsu, suka dakata.
Tun kafun ya ƙaraso gaban karagar Aymanul Faris, suka ƙurawa juna idanu, shi da Aymanul Faris.
Jama'ar dake zazzaune a fadar, suka ƙurawa dattijon idanu, cikin tsananin mamaki.
Yana ƙarasowa gaban karagar Aymanul Faris ya zube ƙasa yayi gaisuwa, sannan ya miƙe zaune.
"Ya shugabana! Na zo ne domin na sanar da kai saƙonni guda uku masu daɗin saurare, da guda uku marasa daɗin saurare..." inji dattijon.
Aymanul Faris ya dube shi cikin tsananin mamaki ya ce, "Me kake nufi da wannan magana ta ka? Wane ne kai?"
"Idan na sanar da kai saƙonnin dake tafe dani, zaka gane abinda nake nufi...
"Suna na Halaras ɗan Ƙaizadu, babban boka wanda yayi zamani da babban sarki..." inji mutumin.
Aymanul Faris ya dube shi cikin mamaki ya ce, "Kai ɗan boka Ƙaizadu ne?"
Halaras ya gyaɗa kai, "Wannan haka yake, Ayman Al Faris!"
Halaras yana gama faɗin haka ya matso kusa da Aymanul Faris yadda babu mai jin abinda zai faɗa, idan ba Aymanul Faris da gimbiya Jaanu ba.
"Saƙo na farko: Ina farin cikin sanar da ku cewa, nan da cikar shekaru uku za ku sami haihuwa. Abinda za ku haifa zaizo da sirri mai ban al'ajabi wanda yafi na kabilar Kuyr.
"Saƙo na biyu: Aiki guda ɗaya ya rage maka Aymanul Faris, tau'rin ya zauna a jikinka har abada, yadda ba zai fita ba har ƙarshen rayuwarsa.
"Saƙo na uku: Ina mai farin cikin sanar da ku cewa, Ranganu da Hodon sun tafi wani aiki mai matuƙar wahala amma aikin zaiyi matuƙar burgeku lokacin da suka kammala shi.
"Waɗannan su ne saƙonni guda uku, masu daɗin saurare."
Halaras yana gama faɗin haka yayi shuru, Aymanul Faris ya dube shi cikin mamaki ya ce, "Saboda me kace, sai bayan shekaru uku zamu yi tsammanin haihuwa? Alhalin a cikin shekara guda mace da namiji suna iya haihuwa?"
Halaras ya yi guntun murmushi ya ce, "Ina so na tabbatar maka da cewa, yanzu haka matarka Jaanu tana ɗauke da juna biyu amma ba zata haife shi ba, sai bayan shekaru biyu da rabi.
"Babban sirri ne zai sake bayyana tattare da wannan jariri wanda duniya bata taɓa gani ba,"
Aymanul Faris da gimbiya Jaanu suka dubi junansu cikin tsananin mamaki.
Halaras bai jira suka sake cewa komai ba, ya ci gaba.
"Saƙo na farko mara daɗin ji: Gagarumin yaƙi na nan tafe bada jimawa ba. Ƙasa ta tabbatar mana da cewa, wannan yaƙi babu alheri ko kaɗan a cikinsa, sannan za'a ɓata lokaci mai yawan gaske kafun a kawo ƙarshensa.
"Saƙo na biyu: Hankalin ISRABIL ya kusa karkatowa gaba ɗaya izuwa kan wannan daula tamu.
"Saƙo na uku: Takobin Anjan ta sake bayyana!"
Aymanul Faris da Jaanu suna jin wannan batu, kansu ya kulle. Gaba ɗaya saƙonnin babu guda ɗaya wanda mutum zai fahimta kai tsaye, dukkansu maganganu ne a dunƙule.
"Wanne yaƙi ke tafe, ya kai Halaras?
"Tayaya hankalin ISRABIL zai karkato izuwa kanmu alhalin kowanne lokaci cikin mana tanadi yake?
"Wacce takobi ce, takobin Anjan da ka ce ta sake bayyana?
"Muna buƙatar gamsassun bayanai akan wadannan saƙonni naka guda uku."
Halaras yana jin wannan batu ya sassauta murya izuwa ƙasa-ƙasa sannan ya fara magana, "Na san cewa kun sami labarin sarki Ayubu da sarki Kuffuru sun haɗa kai?"
Aymanul Faris ya gyada masa kai, alamun hakane.
"Yanzu haka sarki Kuffuru ya aikawa daular Gorgon wasiƙar-yaƙi, kuma nan bada daɗewa ba, gagarumin yaƙi zai iya ɓarkewa a tsakaninsu.
"Babu wanda zai iya kintatar yadda wannan yaƙi zai kasance domin kowanne ɓangare suna da ƙarfi sannan sun gama shiryawa. Saboda haka sai abinda aka gani a ƙarshen wannan yaƙi kawai.
"Idan Marganu ne yayi nasara a wannan yaƙi, zai iya faɗaɗa daularsa ya mamaye daular Nehiya, idan ya mamaye daular Nehiya zai mallaki sojojin yaƙin da suka yi saura.
"Haka ma idan sarki Kuffuru ne yayi nasara, zai kame daular Gorgon ta dawo ƙarƙashin ikonsa.
"Don haka koma wane ne yayi nasara a wannan yaƙi, ba alheri bane a gare mu. Maimakon ace abokin gabarmu ya ragu, sai dai ma matsala ta ƙaru.
"Wannan shi ne abinda nake nufi da gagarumin yaƙi na nan tafe, ba da daɗewa ba. Saboda duk wanda yayi nasara a wannan yaƙi da za'a gwabza tsakanin Marganu da Kuffuru, abu na gaba da zai fara tunani shi ne, kawo farmaki wannan daula.
"Abinda nake nufi da hankalin ISRABIL ya kusa karkato kan wannan daula tamu shi ne, ana kammala wannan yaƙi idan ISRABIL ne yayi nasara, babu abinda zai fara tunani idan ba kawowa daular Shaha hari ba.
"Sarki Kuffuru ya kai masa hari bai share ba, Aymanul Faris ya kai masa hari sunyi ragas. Shima zai fara tunanin kawo hari domin rama abinda aka yi masa."
Halaras yana zuwa nan a zancensa ya fiddo wata ƙaramar takarda daga cikin aljihunsa ya damƙawa Aymanul Faris.
Aymanul Faris ya warware takardar sannan suka duba abinda ke cikinta, shi da Jaanu.
Hoton wata zabgegiyar takobi suka gani, mai tsananin tsaho da faɗi. A jikin gaba ɗaya ƙarfen takobin, rubutun ɗalasimai ne masu yawan gaske.
Kallon farko gimbiya Jaanu ta yiwa wannan takobi ta shaidata, cikin tsananin mamaki ta ɗago kanta ta dubi Halaras.
Aymanul Faris yana lura da duk wani abu dake faruwa, shima ya ɗago kansa ya dubi Halaras.
Halaras yayi gyaran murya ya ci gaba da bayani.
"Takobin Anjan, ita ce takobin da sarki Ayubul-Zairiy mahaifin matarka Jaanu yake yaƙi da ita.
"Sarki Ayubu yayi amfani da wannan takobi a yaƙin da kuka yi na farko, sa'adda ya tashe ku daga tsibirin Gazwar.
"Kana wajen komai da komai ya faru, kuma ka cika da tsananin mamaki da baka ga lokacin da ya ɓace ba, harma ya cakawa mahaifinka takobi a ƙirji.
"Abinda duniya bata sani ba shi ne, hatta shi kansa Hasanul Jalwar baisan sa'adda Ayubu ya ɓace ba, harma ya caka masa wannan takobi.
"Takobin bata amfani da ƙarfin iko ko kaɗan, sauri kawai take ƙarawa ma'abocinta.
"Haɗa kai tsakanin Ayubu da Kuffuru babbar barazana ce ga Marganu a wannan yaƙi saboda idan suka haɗa ƙarfi-da-ƙarfe zasu iya gamawa dashi.
"Yana da kyau a wannan yaƙi, mu saka idanu sosai akansa, saboda hakan zai taimaka mana sosai."
Aymanul Faris yana jin wannan batu ya cika da tsananin mamaki, kafun daga bisani zuciyarsa ta fara tafarfasa kamar zata ƙone, musamman idan ya tuno yadda mahaifinsa ya mutu akan hannayensa.
Babu abinda ya sake faɗowa ransa kamar waɗannan wasiyoyyi da mahaifinsa yayi masa, lokacin da yake daf da mutuwa.
"Ka kula da mahaifiyarka, ka sare kan sarki Kuffuru, Ratanam da Ayubu..."
Ya kula da lafiyar mahaifiyarsa, ya bata tsaro yadda ya dace. Amma ɗaya wasiyyar ko guda ɗaya bai cika ba.
Bai kashe sarki Kuffuru ba, sannan bai kashe Ayubu ba. Ga shi har Ratanam ya mutu sannan ba shi ne ya kashe shi ba.
Anya ba zai shiga wannan yaƙi ya hallaka waɗannan sarakuna guda biyu ba?
Wannan shi ne tunanin da Aymanul Faris ya fara yi, amma sai ya tuna cewa, idan ya shiga wannan yaƙi kamar manyan abokan gaba guda uku zai tunkara a lokaci guda.
Sarki Kuffuru. Sarki Ayubu. Marganu, Dukkan waɗannan da ya lissafo manyan abokan gabarsa ne.
Shigarsa wannan yaƙi zata iya sa wa su taru masa gaba ɗaya, su kashe shi.
Saboda haka, batun shiga wannan yaƙi Aymanul Faris ya ajiye shi a gefe.
Aymanul Faris ya ɗago kansa ya kalli gimbiya Jaanu, nan take yayi arba da ita ta sunkuyar da kanta, hawaye kaɗan-kaɗan yana zubowa akan kyawawan kumatunta.
Nan take tausayin ta ya kama shi, ya dubi Halaras ya ce, "A duk lokacin da aka fara wannan yaƙi, ina so kazo ka sameni, mu kalli yaƙin tare..."
Halaras ya risina ya ce, "An gama, ya shugabana."
Yana faɗin haka yayi sallama da Aymanul Faris ya fice daga cikin wannan daula.
Aymanul Faris yasa hannayensa ya sharewa gimbiya Jaanu, hawayen dake zubowa daga idanunta, ya ce, "Kiyi haƙuri, matata. Ubangiji ya ba ki mahaifi mai son kansa. Amma da sannu zai gane kuskuren da yake aikatawa, kuma duniya zata koya masa hankali..."
Gimbiya Jaanu ta dube shi tayi murmushin ƙarfin hali ta ce, "Ba wai kukan baƙin ciki nake yi ba, ina kuka ne saboda tsananin tausayin halin mahaifina. Duk masu irin wannan hali nasa, ƙarshensu baya kyau."
Aymanul Faris yayi murmushi ya dafa kafaɗarta ya ce, "Tabbas kina da halaye irin na sarauniya Arya. Na godewa Ubangiji da ya bani ke..."
Aymanul Faris yana gama faɗin haka, ya kirawo 'yan majalisarsa ya fara tambayar kowa yadda yake tafiyar da ayyukansa.
Ƴan majalisa suka ɗinga zuwa da ɗaiɗaya suna yi masa bayani, a haka har lokacin tashi daga fada yayi.
Aymanul Faris ya kama hannun gimbiya Jaanu suka shige cikin gidan sarautar, suna tafe suna tattaunawa akan saƙonnin boka Halaras.
Suna ƙarasowa ƙofar shiga wannan gida, Aymanul Faris yaji hatimin dake ɗauke da zanen tau'rin ya motsa, cikin gaggawa ya tsaya cak!
Gimbiya Jaanu ta dube shi cikin tsananin mamaki ta ce, "Ya dai, mu ƙarasa mana?"
Aymanul Faris ya ce, "Tun sa'adda na kaiwa ISRABIL hari, babban ruhi ya bar jikina. Amma yanzu ina tunanin ya dawo..."
Bai ƙarasa rufe bakinsa ba, baƙin-hayaƙi ya cika wannan waje gaba ɗaya.
Gimbiya Jaanu ta daina ganin abubuwan dake faruwa a wajen.
Aymanul Faris ya tsaya cak ya rufe idanunsa, ya daina motsi tamkar a wannan lokaci ya zamo gunki.
****
A can wani waje ya tsinci kansa, wanda yake da matuƙar ban al'ajabi.
A wajen babu turbaya, babu sararin samaniya, babu taurari, babu gajimare.
Zaka iya cewa wajen a cike yake da tarin hayaƙi, saboda idan ka duba sama ko ƙasa babu abinda zaka gani idan ba baƙin hayaƙi ba.
Tau'rin yana zaune akan wata baƙar karaga ta mulki wadda ta saje da kalar baƙin-hayaƙin dake wajen.
Aymanul Faris ya bayyana tsaye akan sawayensa, ba tare da ya faɗo ƙasa ba. Kai kace akwai abinda ya taka.
Fuskarsa tana tsaye daidai ta tau'rin suna fuskantar juna sosai da sosai.
"KA TAFIYAR DA AIKI NA BIYU YADDA YA DACE... SAURA AIKI GUDA ƊAYA WANDA SHI NE ƘARSHE..." inji tau'rin.
Aymanul Faris yayi ƙoƙarin bude bakinsa domin bayar da amsa amma sai ya kasa, a wannan waje sarrafa shi ake.
"Kafun a fara aiki na uku ana buƙatar kawar da ISRABIL daga doron duniya, saboda indai yana raye, ba zai taɓa bari a gudanar da aikin ba.
"Wannan shi ne babban dalilin da yasa muka shirya kaiwa daularsa farmaki domin mu ga ƙarfinsa da yadda zamu iya tarwatsa shi.
"A yayin da kuke gwabza yaƙi kai da shi, na ɗauki duk wasu muhimman bayanai nasa, sannan ni ne na tura ka, ka faɗo kansa domin ganin abinda zai faru idan ruhinku suka hadu a waje ɗaya.
"Tabbas ba ƙaramar sa'a dukkanmu muka taka ba, saboda ruhinka shi ne babbar kishiyar ISRABIL a duniya. Ba zasu taɓa haɗuwa a waje guda ba, duk lokacin da suka haɗu tarwatsewa zasu yi.
"Dukkanmu mun tafka babban kuskure da muka bari ruhinku suka hadu a waje guda a wannan fafatawa. Kaɗan ya hana gaba ruhin su tarwatse, sa'a ce kawai ta ƙwace mu.
"A halin yanzu babu buƙatar ku sake gwabzawa kai da Marganu gaba-da-gaba. Saboda hakan ba zai janyo komai ba face mutuwar ragas.
"Na ɗauki bayanan Marganu sannan na gudanar da bincike akan yadda zamu tarwatsa shi, koda ba mu sake haɗuwa gaba-da-gaba ba.
"Manyan abubuwan da Marganu yake taƙama da su su ne:
"RUHIN ISRABIL dake cikin jikinsa, takobin haske ta sadauki ISRABIL, takobin-taswira da takobin tarwatsa komai. Daga waɗannan abubuwa da na lissafo sai matsayin da addinin Bankai suka bashi na sarki a daular su.
"Na gudanar da bincike akan dukkanin wadannan abubuwa sannan na gano wajajen da za'aje a tarwatsa su. Don haka ka ɗauka a ranka, zamu iya tarwatsa ruhin ISRABIL sannan mu tarwatsa takobin haske, takobin-taswira da takobin tarwatsa komai.
"Idan muka gama da wadannan abubuwa ISRABIL zai dawo ba a bakin komai ba, tamkar mun kashe shi ne."
Tau'rin yana zuwa nan a zancensa ya gyara zama akan wannan karaga sannan ya ci gaba da bayani.
Abin mamaki a wannan lokaci, bada baki yake furtawa Aymanul Faris maganganun ba.
Aymanul Faris yana jin maganganun suna shiga ƙwaƙwalwarsa tamkar ya shafe shekaru masu yawan gaske yana haddace su.
"Zaka iya tarwatsa takobin Marganu ta tarwatsa komai, idan ka ɗauki samfurinta ka kaishi tsakiyar garin Yelwa, dake nahiyar baƙaƙen fata. Garin Yelwa anan aka ƙirƙiri wannan takobi, sannan duk nahiyar baƙaƙen fata babu wajen da ya kai garin samun ruwan sama.
"A tsakiyar wannan shekara, masu hasashe suna kyautata zaton za'ayi wata tsawa mai ban tsoro a garin Yelwa. Indai aka yi wannan tsawa, sannan aka ce samfurin tarwatsa komai yana cikin garin, takobin zata tarwatse ta daina tasiri."
Wannan magana ta tau'rin ta shiga kan Aymanul Faris sannan ya haddaceta a ƙwaƙwalwarsa.
Wani ɗan ƙaramin allo na baƙin hayaƙi ya bayyana akan iska, ya rubuta: 'AIKI NA FARKO ZUWA GARIN YALWA DOMIN TARWATSA TAKOBIN TARWATSA KOMAI!'
Tau'rin ya ci gaba da jawabi, "Zaka iya tarwatsa takobin-taswira dake hannun Marganu, idan ka tarwatsa ruhin Barzas wanda ke ajiye a saman tsaunin Jukuzu. Da zarar kaje saman tsaunin Jukuzu kayi ido hudu da wannan ruhi, ƙarfin ruhin dake jikinka zai tarwatsa shi."
Wannan ƙaramin allo ya sake bayyana ya rubuta: 'AIKI NA BIYU TARWATSA RUHIN BARZAS WANDA KE AJIYE A SAMAN TSAUNIN JUKUZU.'
Tau'rin ya sake ɗaurawa, "Hanya ɗaya da zaka tarwatsa takobin haske ta Marganu ita ce, ka disashar da hasken tauraruwa mai nau'in ISRABIL!"
Tau'rin yana zuwa nan a zancensa ya sakawa Aymanul Faris tunanin abinda ya faru a baya a cikin kansa.
*Lokacin da Marganu ya iso wannan waje da Aymanul Faris yake gefen wannan ƙaramin tafki na garin Jilliza, aka nuno sararin samaniya, take Aymanul Faris yayi arba da wata tauraruwa mai haske tana ta shawaƙi a wajen.*
"Wannan ita ce tauraruwar da take baiwa Marganu sa'a a duk abubuwan da ya saka a gabansa," inji tau'rin. "Duk wajen da Marganu yake a duniya, tana biye dashi.
"Tayaya za'a yi haskenta ya disashe? Dole sai an kawar mutane ashirin da biyar dake rayuwa a duniyar ƙanƙara, waɗanda suke bautawa wannan tauraruwa.
"Kaga kenan, tafiya izuwa duniyar ƙanƙara ya kama ka dole..."
Wannan ƙaramin allo ya sake kaɗawa, "AIKI NA UKU DISASHAR DA HASKEN TAURARUWA MAI NAU'IN ISRABIL!"
Tau'rin yana zuwa nan a zancensa ya nuna Aymanul Faris da tafukan hannayensa guda biyu. Nan take hankalin Aymanul Faris ya karkato gaba ɗaya izuwa kansa.
Babu wata ƙofar shiga dake jikin Aymanul Faris da bata nutsu tana sauraren tau'rin ba.
"HANƳA ƊAYA DA RUHIN ISRABIL ZAI TARWATSE ITA CE, KA NARKAR DA DUNIYAR HASKE GABA ƊAYA..."
Wannan baƙin allo ya sake kaɗawa, "AIKI NA HUƊU - TARWATSA DUNIYAR HASKE.'
"Hadimi Halaras zai iya maka cikakkun bayanai akan wajajen da za'a ratsa a isa waɗannan wajaje da kuma cikakkun bayanai akan ayyukan, saboda haka ka neme shi..."
Tau'rin yana gama faɗin haka yayi girgiza ya zamo baƙin-hayaƙi, sannan ya shige cikin jikin Aymanul Faris ta idanunsa.
Gangar jikin Aymanul Faris ta ɓace ɓat daga cikin wannan waje, sannan ya tsinci kansa a daidai wajen da yake tsaye tare da gimbiya Jaanu a ƙofar shiga wannan gida nasu.
Bayyanarsa tayi daidai da lokacin da Jaanu ta miƙa hannu zata dafa kafaɗarsa, a hankali ya buɗe idanu.
Cikin tsananin farin ciki ta rungume shi, sannan suka ƙarasa cikin wannan gida.
Aymanul Faris yayi shuru yana ta tunanin wadannan maganganu da tau'rin ya faɗa, a duk lokacin da yayi duba izuwa sararin samanyi sai yaga wannan baƙin allo mai ɗauke da jadawalin ayyukan.
*****
Yau *06/07/2023*
Babi na gaba zaizo *08/07/2023* da izinin ALLAH.RUHIN JARUMTAKA!
*
Babi na 149: *SUNA NA ISRABIL*
*
Wannan littafin sadaukarwa ne ga Zahra...
*
U~M~S
*
~Daular Gorgon.
*
Saida Marganu ya shafe kwanaki goma sha huɗu yana jiyyar raunin dake kan damtsen hannunsa sannan ya soma warkewa.
Dukda cewa ya soma warkewa amma babu abinda yake yi da hannun, kullum yana ɗaure a cikin itatuwa don kada ƙashin hannun ya ƙarasa karyewa.
A wannan rana da ya cika kwana goma sha huɗu ne, babban likitansa ya shigo cikin turakarsa inda yake kwance.
Likitan ya ƙarasa gaban gadon Marganu ya zauna akan wata kujera.
Bayan ya gama yiwa Marganu gaisuwa da kuma tambayarsa ya jiki, sai ya dubi Marganu ya ce, "Yau ce ranar da zan kwance maka hannunka, domin ina tunanin ƙashin da ya ɗan tsage ya koma ya haɗe kamar da..."
Marganu yayi guntun murmushi ya miƙa masa hannun, shi kuma ya fara kwance igiyoyin da suka ɗaɗɗaure itatuwan.
A hankali ya gama kwance dukkan igiyoyin da suka ɗaure itacen, sannan ya zare itatuwan a hankali.
Hannun Marganu ya bayyana, dukda cewa raunin dake kan hannun ya warke amma akwai tabon saran da takobin BINA-KIL-DEM tayi masa.
Marganu ya fara motsa hannun a hankali kafun ya ci gaba da motsa shi, nan take yaji hannun ya miƙe kamar da.
Marganu yayi ajiyar zuciya ya dubi wannan likita ya ce, "Wannan wanne irin rauni ne, wanda na shafe sama da sati biyu ina jiyyarsa?"
Likitan ya dubi Marganu ya ce, "Wannan rauni da aka yi maka saran takobi ne mai ban al'ajabi. Bayan fasa tsokar damtsenka da yayi, har ƙashinka ya ɗan kuskura kaɗan. Tabbas ba don ƙasusuwan jikinka suna da ƙwari ba, da tuni ya karya shi."
Marganu ya jinjina kai cikin mamaki. Tabbas yana buƙatar samun bayanai akan wannan takobi da Aymanul Faris yayi amfani da ita yaji masa wannan wawan raunin, wanda ƙiris ya hana ya fille masa hannu.
Nan take ya sallami wannan likita sannan ya bayar da umarni a kirawo masa matarsa Firziyya.
Likitan ya risina ya miƙe tsaye ya fice daga cikin turakar.
Jim kaɗan Marganu yana zaune a tsakiyar gadonsa yana cin 'ya'yan itatuwa. Gimbiya Firziyya ta shigo cikin wannan turaka.
Ganin Marganu a zaune lafiyarsa ƙalau, yasa ta rugo da gudu ta faɗa kan ƙirjinsa suka rungume juna.
Kafun gimbiya Firziyya ta gama nuna tsantsar farin cikin da take ciki bisa farfaɗowar Marganu, wani gagarumin haske ya sauƙo cikin wannan ɗaki.
Tun da gimbiya Firziyya take tare da Marganu bata taɓa ganin haske kamar wannan ba, hasken ba wai iya kashe idanu yake ba, har da sanya musu zogi.
Cikin tsananin tsorata gimbiya Firziyya ta sauƙo daga kan wannan gado sannan ta koma gefe guda ta zube ƙasa kan sawayenta.
Wani irin iko na musamman ya soma dukan ruhinta yana ƙoƙarin tarwatsa shi, bisa dole ta zube tayi sujjada.
Jim kaɗan ta fara jin motsi a cikin ɗakin, alamar mutum ne ke tafiya.
Cikin ƙarfin hali da dakewar zuciya gimbiya Firziyya ta ɗago kanta a hankali domin ganin wanda ke wannan tafiya.
Nan take tayi arba da wani saurayi mai tsananin kama da Marganu.
Abinda kawai ya bambanta Marganu da wannan saurayi shi ne, jikin Marganu da tsoka da jini aka samar dashi. Shi kuma jikin wannan saurayi haske da walwali kawai yake bayarwa.
Idanun Firziyya suna arba da gangar jikin wannan saurayi, wani babban iko ya yiwa ruhinta sallama.
Ruhinta ya fara girgiza tamkar zai tarwatse, jikinta ya fara kyarma da karkarwa. Bata san sa'adda ta ɗauke idanunta daga kallon wannan siffa ba.
Saurayin ya ƙarasa a hankali gaban Marganu ya zauna, ya kamo hannayen Marganu da nasa guda biyu sannan suka ƙurawa juna idanu.
A wannan lokaci inda ace mutum yana tsaye a wannan waje, ba zai kalli abinda yake faruwa ba, saboda tsananin hasken da ya lulluɓe ko'ina.
"SUNA NA ISRABIL!!!" inji wannan saurayi dake zaune a gaban Marganu. "Ni ne ruhin dake rayuwa a cikin jikinka, ko kuma nace ni ne ainihin ruhinka..."
Marganu ya ɗago kansa a hankali ya ƙurawa halittar idanu, yana nazarinta.
"Ina da ƙarfin ikon da zan iya tarwatsa kowanne irin ruhi, idan na taɓa shi da hannayena. Ni ne na tarwatsa ruhin aljani Duksum, sarauniya Rauziyya da duk wani mahaluƙi da ka kashe...
"Na shafe fiye da shekaru dubu ina yiwa tau'rin shiri domin na hallaka shi, amma ban samu nasara ba, sa'adda na taɓa shi da hannayena.
"Bari na baka wani ɗan gajeren labari...
"Kimanin shekaru dubu arba'in da suka shuɗe, ni da tau'rin mun kasance mutane kamar kai da Aymanul Faris rayayyu.
"A wancan zamani, akwai wata ƙasaitacciyar gimbiya 'yar wani gawurtaccen attajiri. Ana kiranta da suna Rosnil.
"Gimbiya Rosnil da mahaifinta baƙi ne a ƙasar mu, saboda haka sun bambanta matuƙa da mutanen mu.
"Gimbiya Rosnil tana da ban al'ajabi, a duk sa'adda ni ko tau'rin wani yayi arba da ita, sai ya muji wani ƙwarin gwiwa da azababben ƙarfin damtse na shiga jikin mu.
"A wancan zamani babu wanda yasan tsafi duk faɗin ƙasarmu. Abu guda muka yarda dashi shi ne, jarumtaka.
"Kakana na bakwai a wancan lokaci ya kasance mutum mai yawan bincike akan halittun dake rayuwa a doron duniya.
"Wata rana na ribaci zuciyar gimbiya Rosnil ta amince muka je wajen wannan kaka nawa. Bayan ta tafi kakan nawa ya dube ni ya ce, 'Wannan yarinya tana da ban al'ajabi.
"Akwai babban sirrin dake yawo a cikin jininta, wanda indai nayi mu'amala dashi zan samu babbar kyauta ta musamman. Na yiwa kakana godiya na tafi.
"Daga wannan lokaci na fara ƙoƙarin ƙulla alaƙa da gimbiya Rosnil amma ban samu nasara ba, domin tau'rin ya riga ni.
"Wasa-wasa abin har ta kaimu ga yaƙar juna. Lamarin

Please Login or Register in order to submit comment